Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*SANGARTATTCE* by* Maman Abd Shakur*
#1
♦♦♦*SANGARTATTCE*♦♦♦

Maman Abd Shakur

1...
Free page

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.


"wayyo Allah na Baba mutuwa zanyi, wayyo Mama huramin cikin" mata biyune suka zagayeta akan tabarman dawasu yara mata guda biyu dake tsakar gidan dayasha simenti kal kal dashi duk sunyi zuru zuru, kana ganinsu kaga tashin hankali kwance akan fuskarsu, chan ta gefen tabarman  kuma wajajen inda kafanta yake wani dan tsohone haka dake sanye da babbar riga dakuma yar hula daya zagayeta da rawani irin na malamai dinan ya rike kofin silver yakara abaki yanata addu'o'i aciki anatse, ihu takara yi ta dage rigarta sama tabude daidai cikinta dake nan kaman bata tabacin abinci ba, ta gefen haggun cikin ya dan kumbura idan kaga wajen saika rantse wani irin babban kurjine yafito ya kumbura haka yay ruwa zai fashe, ihu tasake yi tariko hannayen matan dake kanta tace "wayyo Allah Mamammu na shiga uku, azaba Mama wayyo, azaba yakemin" tasaki hanunsu tana ihu "Baba Baba baba kiranka nakefa, wayyyo Allah na ba banu ni" wani irin ihu take ta rirrike hannayansu gam tana nishi, wajen ciwon cikin kuwa sai balbal yake yanda kasan halita mai rai ne acikin wurin, duk ihun ta yacika gidan, tsabagen takaici ma daya daga cikin matayen wacce itace mahaifiyarta taja tsaki, hakan yasa dayar ta goge zufan datake yi agoshi, takamo fuskarta da hanunta tarike tace "haba Balkisu, iye mai gadon zinare, ki daure mana baga baban kinan namiki addu'a aruwaba, kefa mai dauriya ce, jaruma, kinga Layla da Raiyana zasuce ke raguwa cefa gashima sai kallonki suke" girgiza kai tayi tawani irin kece da kuka da ihu harda shesheka tace "ni kukiramin Baaba wlh, Baaba tazo, Baaba kizo ki taimakeni" tafara shure kafa idanun nan sunyi jajir tace "Baba, Baba, Muji, wayyo Allah na Mujittapa kuzo kutaimake ni, Shato kuzu dan Allah na shiga uku, wayyo Mama dubamin kiga kodai barkewa cikin yakeyi ne?" tawani irin buga ihu hakan yasa mahaifiyarta dake kanta ta buge bakinta da karfi tace "kewai baki iya kiran sunan Allah bane banziya kawai" daidai lokacin Baba ya cire cup daga bakinshi ya kalli Uwargidan yace "dagomin ita Zainaba" dagota tayi ahankali sai wani uban nishi take tana cije baki tace "tsaya tsaya uhmm" tsayawa tayi tana kallonta cike da tausayi, hannu budurwan tasa akan kafadar matar tareda runtse ido da karfi tana nishi tace "tona shirya" har Mama saida tasa hannu suka dagota zaune ahankali wani irin ihu tayi kaman zata mutu "ya isa, ya isa, yayi" suka jinginar da ita ajikin bango, kafamata kofin Baba yay abaki ta kurbi ruwan sosai tasha tana kara dage rigar atampan jikin ta sama, ragowan ruwan Baba ya debo yay addu'a zai shafamata akan kullutun da sauri tarike hanunshi tana ihu tana kuka tace "Baba wlh azaba yakemin, in kanama Allah karka tabamin, kaji dan yarasulullahi" hanunta Mama dake kanta ta buge tana wurga mata wani mugun kallo, hakan yasa Baba ya girgiza kai ya shafamata ruwan awajen tana wani irin shegen ihu da duk yacika musu kunne, tashi Baba yay ya kalli mahaifiyarta ya mika mata cup din yace "bayan awa daya kikara bata Amina, bari nakoma zaure wajen dalibai" jiki asanyaye ta karba tace "to malam" juyawa yayi yay hanyar zaure bude kofa yayi sanan ya daga asabari dazai sadashi da zauren yafita, almajirai ne cike a zauren sunata karatu da alo, ga wasu manya akansu dake rike da bulala suna lura dasu, bangon zauren duk jakunkunan almajiran ne dakuma taburmai dasuke kwana akai dan zauren nada girma sosai, daliban na ganinshi suka kara karfin karatun dasuke, fita yayi daga zauren zuwa kofar gida nan ma wasu almajiran ne akan simentin kofar gidan dayawa sunata karatu da alo, anyi babbar runfa daya kare kofar gidan sabida koda ana ruwan sama dan wasu almajiran anan waje suke kwana, ga robobin almajiran cike akan dankali dan dazaran karfe biyu tayi zasu tsaya sai ayi salla kowa yatafi bara, daga chan gefen kofar gidan kuma lungu ne dayasa suka gineshi dajar kasa aka zagaye suka maida bayi, anan almajiran suke wanka suke dai komi nasu sanan a kofar gidan akwai rijiya da guga dasuke diban ruwa, zama yayi akan tabarma da aka wareshi musamman tashi ce dan akwai yar dadduma mai taushi akai ya zauna tareda yin bismilla yanajan chasbaha, yana bin kowani dalibin dake wurin yana karatu da kallo, wani dalibi babba dan yana daga cikin wayanda ke kula da sauran almajiran ne yazo kusa da malam ya zauna tareda tankawshe kafa yadan dukar dakai yace "Allah taimaki Malam, Allah gafarta ma Malam, Allah kare mana Malam" ahankali Baba ya ijiye charbin ya kalli yaron yace "sun biya karatun da kyau Isyaka?" "i sunbiya  Malam, na muhammadu ne kawai bai kawo da kyau ba amma nakara maimaita mai" murmushi Malam yayi tareda kishingida da bango yace "masha Allah to, daukomin Al Qur'ani na nabarshi a zaure saika biyamin naka inji" dan kallonshi matashin yayi saikuma ya sunkuyar da kai yace "Malam ya jikin Balkisun?" ajiyar zuciya Malam ya sauke yace "da sauki namata addu'a zata sami lpy nan bada jimawaba" cike da damuwa Isyaka yatashi yabar wajen zuwa zauren dan dauko abinda Malam ya aikeshi.

Gyangyadi tafara yi anan wajen a zaune, hakan yasa duk suka sauke ijiyar zuciya, Uwargidan dasuke kira da Umma tamike ta kalli Maman Bilkisun tace "sha biyu tayi bari na daura girki Amina" kallon yaran daduk sai kallon Bilkisu dake nan zaune tana gyangyadi suke tace "ai sai atashi aje ataya Umma aiki ko" hijabi Raiyana ta cire wacce ita kebin Bilkisu shekaran ta 15 tamikama Layla hijabin wacce take auta shekaran ta 8 tace "ungo kaimin daki" karba Layla tayi ta wuce dakin su ta ijiye tafito suka karasa kitchen din jajjage Umma tasa Raiyana itakuma Layla Umma tace "tahura mata wutar ta kama" tafice daga kitchen din zuwa tsakar gida dan tankaden tuwo.
Layla dake fifita wuta ne ta juyo ta kalli Raiyana dake jajjage, ajiye maficin tayi tazo kusa da Raiyana ta tsaya kaman zatai kuka tace "Anty Raiyana maisa Baba bazai kai Anty Baby asibiti ba, kinga ko koyau a makarantar mu anmana primary science fa, ance idan abu yafito acikin ka yay babba har yana motsi operation akeyi, Allah kuwa, Baba kuma yanata mata karatu tanasha da dafa mata ganye maisa bazaice aje asibiti ba" tunda take maganan Raiyana ta tsayar da jajjagen tana kallonta, Umma ne ta shigo kitchen din ta kallesu tace "surutun me kukeyi ba aiki nasaku ba?" baki Layla tabude zatai magana Raiyana ta girgiza mata kai hakan yasa tai shiru takoma gaban murhun tacigaba da fifita, abinda Umma ta shigo dauka ta dauka tafice daga kitchen din, hakan yasa Raiyana tadawo wajen murhun ta tsugunna tace "karki kara fadin maganan nan, Baba bai yarda da maganin asibiti ba kuma idan yajiki kinsan sauran, karki karayin maganan kinji" ahankali Layla ta gyada mata kai kowaccen su tacigaba da aikin da aka sakata.
Wuraren sha biyu da rabi ta farka azabure ta mike Mama dake zaune gefenta tana dama ma malam fura ta kalleta tace "ya cikin" hanyar dakinsu tayi ta daga labule ta kalli agogo sanan ta kalli Mama tace "Mama nakusa lattin makaranta shine baku tasheni ba" turo baki tayi tai gaban rijiya tadau botiki zataja ruwa, tabe baki Mama tayi tacigaba da dama furan ta, agurguje taje tayo wanka tafito daure da zani a kirji tashiga daki da gudu, uwar dakan su ta shiga dake nan agyare ko ina dan gado ne madaidaici sai ledan daki da aka shimfide, tsugunnawa tayi tajawo ganamasgo daga karkashin gado ta bude taciro kayan makarantar ta dake nan agoge, purple dogon wandon tafara sawa sanan tasaka rigar dayakai har gwuiwa fara tana dan bata fuska sabida yanda cikin ke mata ciwo kadan kadan yanzu ba kaman dazu ga, gaban madubi taje ta shafa farar hoda tasaka kwali, basilin ta lakato ta shafa akan pink and black lips dinta, dan lips dinta daga tsakiyar su pink ne sosai sai kasan kuma baki kaman ta shafa janbaki haka suke gashi sunwani irin tattare gwanin kyau and sexy, idan ka kalla kaman nama, komawa gadon tayi tasanya farin hijabin daya wuce gwuiwa, ta maida ganamasgo karkashin gadon tadau yar jakarta da litattafan ta keciki tafito ta zauna adakalin bakin kofa tana kokarin saka safa da takalmin makaranta Umma da fitowar ta daga kitchen kenan tace "Baby yaushe kika warke dahar zaki tafi makarantar allazi boko?" dan murmushi tayi daya bayyanar da beauty point dinta tace "Umma yafa dena fa wlh, kuma kinga nice monitor aji chalk natare dani dole nakai" baki Umma ta kama tace "su manito manya" dariya Balkisu tasaki harda fadawa jikin Mama dake kan tabarma tace "ana monito kina manito Umma" tacigaba da dariya kaman ba ita ke ihu dazuba, rankwashi Mama tasakin mata akai tace "tashi min akan jiki kafin na juye miki furan nan akan kayan makarantar nan" ahankali ta tashi kaman zatai kuka ta zauna kusa da ita Umma ta bude kullin zani taciro naira hamsin ta mikamata tace "gashi kihau mota, daga fillin mallawa zuwa dogon bauchi da shegen nisa keda baki da lpy" karba tayi cike da murna tace "nagode Umma na Allah barmin ke" komawa tayi kusa da Mama tana kallon furan, kaman zatai kuka tace "Mama dan sammin kinga ba'a gama abincin rana ba karnaje makaranta haka da yunwa" hararan ta Mama tayi tace "kwadayayya" dariya tayi tace "eh naji Mama kidan ban" da sauri ta shiga daki ta dauko karamin kofin roba Maman ta tsiya mata dan daidai ta shanye harda saka yatsa tana kakkale kofin ta lashe tass sanan ta ijiye kofin tana goge baki tace "nagode Mama natafi" da sauri tadau jakarta ta leka kitchen taga su Raiyana na kwasan tuwo tace "natafi" atare suka mata addu'a, Mama tace "salla fa?" "a school zanyi Mama" tabude kofa sanan ta daga asabari tafita.
[7/14, 19:55] +234 806 604 6091: ♦♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦♦


Maman Abd Shakur

2 - 3
Free page

 Zaure tawuce tana bin almajiran wajen da kallo kafin ta fita kofar gida tai wajen Baba da tunda tafito ita yake kallo, tsugunnawa tai agabanshi tawani kwaye fuska kaman zatai kuka ahankali tace "Baba natafi makaranta amma ni banci komiba ba'a gama abincin ranaba" girgiza kai kawai Malam yayi sanin halin yar tashi, hakan yasa ya saka hannu cikin aljihun babbar rigar dake jikinshi yaciro dari yabata da sauri ta karba tana murmushi tace "nagode Babana, Allah biyaka natafi" "ya cikin?" ya tambayeta anatse, tashi tayi tana kokarin saka kudin ajaka sanan tace "yadena Baba tundazu, natafi" "adawo lpy" tajuya ta fita tana waige waigen zauren, fitowa tayi tafara tafiya a layinsu daya yawaitu da bishiyoyin dogon yaro, dadan sauri take tafiya sabida takai bakin titi tahau boss dazai kaita school, wani gida dan madaidaici dake nan cikin layinsu ta shiga harda dan gudan ta dan sauri take wata matace yar dattijuwa haka, tana zaune tana tuyan waina anan tsakar gidan ahankali kaman wacce kwai ya fashewa aciki ta karasa kusa da matar wacce batama lura da itaba saidai kawai taji mutum akanta, fashewa tayi da kuka kaman wacce aka doka hakan yasa matar ta rike baki tace "mekuma aka miki iya shagwaba iya sonjiki Bilkisu" kara fashewa tai da kuka tana buga kafa akasa cikin kukan tace "tun safe banda lpy kokizo ki dubani kinata wainar saidawa abinki ko Baaba" arude matar tace "ni? Haba tagidana ai kema kinsan inda nasan bakida lpy tuni xan ijiye wainar nan nazo, dena kukan keko, halan cikin ne yatashi?" gyada kai tayi tana share hawayen Baaba tace "shiga daki ki dauko kular ki nasaka miki wainar ki kitafi kinga yau kinyi latti" da sauri tashiga dakin Baaba tana kokarin daukar kulan tace "Baaba ina Muji?" daga tachan waje Baaba tace "yafita da Keke napep waiko zai sami fasinja, saiyau ya daukota daga gareji" daidai nan tafito tamika ma Baaba kular, karba tayi tazuba mata wainar dayawa sanan ta baza mata kuli dayawa akai ta rufe kulan tabata tareda ciro hamsin tace "gashi adawo lpy" karba kulan tayi tace "kibar kudin Baba yabani, natafi Baaba saina dawo" "adawo lpy yar albarka banda wasa a aji kinji yar gidana" fita tayi tana murmushi tana mugun son Baaba, yayar mamanta ne haka suke kiranta, bayan tai aure data haifi Mujittapa (Mustapha) danta na farko shine Maman su lokacin kafin tai aure tazo tayata raino aiko malam yana ganin Maman su ya like mata ya nace yanaso, bayan wani dan lokaci fa suka tafi kauyen su dake chan hanyar gombe kauyen bojude lokacin tun kafin iyayensu su rasu akai bikin aka kawota gidan malam, Umma bata da matsala hakan yasa malam ya hade kansu suna zaman lpy, yayan malam 8, Umma yaranta 5 duka maza wanda duk malam yatura su nijar wajen wani babban abokin shi malami yin karatun addini awani babbar makarantar shi, yanzu ma watan su daya da tafiya kenan sai bayan shekara biyar zasu dawo dan makarantar har certificate ake badawa inka gama, sai kuma maman su data haifi su uku Balkisu, Raiyana da Layla, dukan su malam yasasu a government girls secondary school ne Raiyana da Layla na safe suke zuwa, itakuma dayake SS ne rana ne nata.

Karasowa bakin titi tayi ta tsaya tana jiran Bus wata makauniya tagani ita da yarta suna ta bara a shagunonin kan hanya wai tun safe basuci abinci ba, ba karamin tausayi suka bataba, tana kallonsu suka koma kan dakali suka zauna yarinyar nata kuka, jakarta ta laluba taciro naira darin da Baba yabata ta karasa kan dakalin dataga sun zauna, yarinyar nata kuka  wai yunwa takeji maman na lallashin ta, ahankali ta duka darin ta mikama yarinyar tareda mata murmushi tace "dena kuka gashi" karba yarinyar tayi tana fadama maman ta bakaramin dadi matar tajiba tace "mungode yar nan, ubangiji Allah ya miki albarka ya raya miki yaranki" dariya Bilkisu tayi sosai tace "Ameen amma nibanyi aure ba mama" washe baki makauniyar tayi tace "to ubangiji Allah ya baki miji nagari wanda zai saki farin ciki sama da wanan dakika samu" ahankali tace "Ameen nagode" ta dagama karamar yarinyar hannu sanan tajuya ta tare bus din dake zuwa ta shiga har lokacin yarinyar nata dagamata hannu itama daga mata hannun tayi har bus yawuce ta daina hangosu.
Allah yasota koda ta shiga school ana gab dafara taran latti, da sauri tafara yin masallaci tai salla sanan tafito tai aji lokacin duk yan aji sun zauna ana ganinta akai tsit kowa nata kallonta hakan yasa tasha jinin jikinta, kujeran layi nabiyu ta wuce ta tsaya agaban sit din ganin duk su Aisha Shehu sun cike Walawa ta zauna awurinta, daure fuska tayi ta kalli Walawa tace "wlh kitashin min daga wuri ai chan ne sit dinki" tanuna kujeran bayan nasu, hararan ta Walawa tayi ta cigaba da zanen flower datake yi a paper, su Aisha Shehu dai sai dariya suke kasa kasa dan dama dagangan Walawa tazauna neman tsokana ne, ganin ko kulata Walawa batayi ba yasa taji abin ya mugun bata mata rai hakan yasa ta fizge byron hanun Walawa afadace tace "badake nake magana ba, kinga kitashi" kaman jira Walawa takeyi ta mike tsaye fuska a daure ta kalli su Fateema da Fa'za dake kusa da ita suma duk suna dariya kasa kasa tace "ku matsamin na fitan ma almasifatu daga wuri" gyaggyara kafa sukayi Walawa tafara tafiya hakan yasa Bilkisu tazo daidai bakin sit din tana jiran Walawa tafito itakuma ta shiga fuskar nan nata adaure fitowa Walawa tayi, saida tazo gab da Bilkisu tasa hannu ta taba mata nono, atsorace Bilkisu ta tsugunna a wurin tareda fasa ihu "wayyo Allah" ta kankame jikinta, aiko duka ajin sukahau ihu da dariya, su Aisha Shehu dasu Fa'iza harda buga benci suna dariya, Walawa ko hanyar kofa tayi ta tsugunna tana dariya harda rike ciki, gabaki daya ajin dariya ake Aisha Shehu tace "babu wacce ba'a tabama nono a ajinan ba, kece kullum kiki yarda yar malam, yaudai an taba dama gasu manya manya" aikuwa kowa dariya suna bubbuga benci irin abun yay musu mugun sugar dinan, saida ta goge hawayen datake yi sanan ta mike tazo gaban Aisha Shehu tace "eh aini kinsan ba yar iska bace irinku ba masu wasan taba nono a school" tana fadin haka tai hanyar kofa wurin Walawa, Aisha Shehu tabita da harara tace "to uban waye yan iskan, ba wasa bane kowa ajin nan an taba nashi saike, koba hakabane?" ta tambayi su Fa'iza da Fateema suma duk dariyan suke harda kama ciki danba karamin dadi abun yamusu ba yau yanda aka kama na Bilkisu yar malam yau, dan ita kadaice bata yarda amata wanan iskancin a aji gashi yau an shammaceta anyi kowa dadi yakeji. Kan Walawa Bilkisu tayi wacce tun kafin tazo kanta tahade hannu tana dariya tace "haba Billy yar malam, yakuri mana kawas ai bankama ba tabawa kawai nayifa dan nasan bakiso wlh bazan karaba, yakuri" kamota Bilkisu tayi ta durma mata duddu abaya daidai lokacin wata malamar english dinsu ta shigo aji hakan yasa duk suka koma wajen zamansu kowa ya natsu.
(oya name abunda kukayi zamanin secondary school?? Barinma wayanda sukayi girls school kadai?)

Wuraren 4 suka fito break da salla, bayan sunyi salla duk tare suka tayata cin wainar dan dama sune kawayen nata Aisha Shehu Walawa da Fa'ixa saikuma Fateema, bayan sungama ciyeciyen su sanan suka koma class, sai wuraren biyar da rabi aka tashe su duk suka fito suna tafiya har suka gangaro bakin titi suka shiga bus kowacce tai gidansu.
Gidan Umma tafara biyawa ta ijiye kulan sanan tafito akofar gidansu tahadu da Isyaka yana alwalan sallan magriba, murmushi tamai hakan shima yamata murmushi da sauri ta shiga gida ta gaida Baba sanan tawuce cikin gida. Babu kowa a tsakar gidan duk sun shiga daki hakan yasa taja ruwa tazuba a buta tai bayin su bayan tafito ta tsugunna a makwarara tai alwala sanan ta shigo dakinsu, salla taga Mama dasu Raiyana nayi hakan yasa ta zauna akan kujera tana kokarin kunna fitila, kunnawa tayi ta ijiye daidai lokacin sun sallame Layla ce tafara tasowa Raiyana tabiyo ta abaya duk suka zauna kusa da ita Layla tace "me kika kawo mana daga school Anty Baby?" murmushi tayi ta bude jakarta gwaiba taciro da topi ta basu duk suka karba cikeda jin dadi Mama ta ballamata harara tace "aikin kenan" dariya tayi ta tashi tasaka hijabi tai sallan magriba tana idarwa ta daura kanta akan cinyar Mama ahankali tace "yunwa nakeji Mama sosai" mika hannu Mama tayi ta dauko kular tuwo dake gefenta tace "gashi nan zuba muku kuci keda kaninki to" tashi tayi ta dauko faranti ta zuba tuwon tasa miya asama ta kalli su Raiyana tace "ku sakko muci" sakkowa sukayi zasu sa hannu Mama ta harareta tace "bazaki je kicire kayan makaranta bawai" kaman zatai kuka ta tashi tawuce uwar daka tacire kayan ta fito daure da zani  akirji ta zauna tana turo baki sanan suka saka hannu duka suka faraci.

  Dr ne akan wani magidancin da akalla zaikai 75 years sa'an Baba buhari? acikin wani katafaran falo sai sumbatu yake yana "Dr Ayaan dina zaka kawomin, Ayaan" shiru yayi sabida alluran da likitan yamai daidai lokacin wani security dake sanye cikin uniform ya tsaya agaban falon yana sallama, izini matar dake falon cikin shiga ta alfarma tamai, hakan yasa ya shigo hanunshi rike da wata ipad, Karasowa yayi gefen Baba Sule wanda shine kanin magidancin dabaida lpy, cike da girmamawa yace "Alhaji wanan shine CCTV footage din natun ranan da Ayaan yafara rashin lpy abangaren shi, da lokacin daya fita daga gidan" ya kalli matar datai tagumi tana kallon fuskar mara lpy yace "Hajiya akwai bukatar kema kizo ki kalla dan wata da kayan yan aikin gidan nan ne tafara kawomai abinci lokacin yana garden tace kece kika aikota takawo mai, to ayanda dai CCTV footage din yanuna yanacin abincin yafara rashin lafiya saikuma..." yadanyi shiru cikeda damuwa yace "zodai ki kalla dakanki wata kila ki gane yarinyar dan munemo ta dole zatasan wani abu kan batar shi" tashi matar da aka kira da Hajiya tayi ta dawo gefen Baba sulen ta zauna jiki asanyaye tana kallo, tunda tafara kallo ta dafe zuciyar ta tana buga salati saikuma tafashe da kuka sosai ta kalli Baba Sule tace "Baba Sule ina dana yayi? Yanzu adai yanda yafitar nan a ina zamu ganshi, innalillahi wa innalillahi raji'un wanan wace irin musib.." shiru tayi ganin mara lafiyan yakara farkawa yarike hanun Dr dake kanshi yace "ina Ayaan dina? Eh Ina ka kaimin shi?".
[7/14, 19:55] +234 806 604 6091: ♦♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦♦ 

Maman Abd Shakur

4...
 Free page 
Alluran bacci Dr yasake mai sanan yay bacci, matar takara fashewa da kuka, Baba Sule da Security suka fita daga dakin dan zuwa police station danjin ya ake ciki.

Layla ne ta shigo dakin  ta kalli Bilkisu dake kwafe note tace "Anty Isyaka na falon Baba yana jiranki" satan kallon Mama dake tsefema Raiyana dogon gashin ta tayi taga ko kallonta batayi hakan yasa taidan murmushi tadau dogon hijabin ta tafita daga dakin, dakin Baba tai sallama ta shiga, daki ne mai fadi wanda kusan littatafan addinine suka cikashi, koina agyare ga kamshin turaren wuta, daga gefe kuma isyaka ne dayaci gayu cikin normal shadda abinshi sai kamshin turaren duri yake yanata kallonta akunyace ta zauna nesa dashi akan tabarman tana wasa da hijabi tace "ina yini" kara gyra zama yayi tareda lankwashe kafa ya hade tafukan hanunshi yana murzawa yana murmushi yace "barka da zuwa Bilkisu gimbiyata, gimbiyan duka matayen garin nan, gimbiyar dake mulka zuciya ta, saurayinyar mata mai gadon zinare" dariya tayi ta kawad dakai dan ba karamin kunyan shi takeji ba, Isyaka amintaccen almajirin Baba ne, tun yana karamin yaro aka kawoshi almajiran ci wajen Baba harya girma, shekaran shi 25 yanzu, yanada aikin hannu dan ya iya aikin hula da aikin su shadda, Baba yariga yabashi Bilkisu tun tana yar yarinya, yanzu haka ita yake jira dazaran ta zana jarabawa za'ayi auren su yakoma da ita kauyensu nachan hanyar sokoto.
Dan gyara murya yayi yace "bakice komiba mar'autul saliha? Ya karfin jiki" anatse tace "Alhamdulillah na warke ai tun dazu" wata torchlight phone yaciro daga aljihun rigar shi yazo gabanta ya ijiye mata akan hijabi yace "gashinan ki rike inaso mudinga waya tanan" da sauri ta kallai sai kuma ta make kafada ta kwaye fuska kaman zatai kuka, ashagwabe tace "a'a nidai bazan karba ba, Baba bayason muna amfani dawaya Allah kabarshi nagode" tunda take maganan yakafe ta da ita hakan yasa ta dukar da kanta kasa, dan ajiyar zuciya ya sauke kafin ahankali yace "har yanzu kinki dena shagwaban nan ko, dan Allah kidena mini ji nake kaman zan mutu idan kinayi, ina kaunar ki dayawa Bilkisu, yanzu dai Baba yariga yaga wayar ai yama yarda nabaki saisa nakawo miki, gwara munayi munadan taba waya ko? Muma muyi soyayyar yan gayu" gyada mai kai tayi tana murmushi daya bayyana fararen hakoran ta tace "nagode" dariya shima yayi cike da murna yace "bari namiki waka" dan zaro ido tayi tana kallonshi yamata wani irin kallo yace "dukda ina malami ai dole na koyo waka nama gimbiyata dan na faranta mata rai" dariya ta sake yi harda rufe fuska, dan gyara murya yayi hakan yasa ta tsayar da dariyar  tana kallonshi, yawani kalleta yana nuna ta da hannu yace "Bilkisu na yarda dake, dauki amanata ki rike, kin dace da zama dani, Bilkisu gimbiyar raina, Bilkisu hasken idaniyata, Bilkisu ina kaunarki, Balkisu tauraruwan raina, Bilkisu abun kaunataaa" bakaramin dadi wakan yayi mata ba sosai ta dinga dariya tareda boye fuskar ta cikin hijabi, "ya isa haka dariyan to yawan dariya baida kyau a addinin mu, tashi kije ki kwanta akwai school gobe" addu'a yayi sanan ya mike tsaye yace "saikuma gobe ko, kiyi alawa kafin ki kwanta zan kiraki tawaya cikin dare sabida kitashi kiyi salla ko" gyadamai kai tayi yafita daga dakin yana mata murmushi, hakan yasa itama ta tashi sanin Baba nadakin Umma yasa takoma dakinsu ganin Mama tai bacci da Layla aka gado, yasa ita tadawo falo ta kwanta kan dagon kujera 3 sitter wacce dama anan take kwana itakuma Raiyana 2 sitter take kwana kokuma wani zubin su kwana akasa.

Da asuba bayan sunyi salla duk dakin Baba sukaje karatu ya koya musu Qur'ani, hadisi da fiqhu, bayan sun biya wanda yabasu jiya harsai wajajen karfe shida sanan suka fito, kitchen  ta shiga dan hura wuta Raiyana kuma taja ruwa dan wanke bayi da makwarara, itakuma Layla tadau tsintsiya sharan tsakar gida, suna gamawa duk suka diba ruwan zafi sukaje wanka sukaci dumamen su da kokon da Bilkisu ta dama sanan suka tafi makaranta. Gyara dakin Mama tayi fess ta kunna turaren wuta sanan tawuce dakin Baba ma ta gyara tana gamawa yafito daga dakin Umman hakan yasa tawuce nan ma ta gareshi Umma sai shimata albarka take, dakinsu ta dawo tadau hijabi tasa ta kalli Mama dake shan koko tace "indanje gidan Baaba Mama?" dari biyar din kan kujera Mama ta dauka ta mikamata tace "gashi nanma daganan kibata kice nace kudin zubi na nayau" da sauri tafita saida takara gaida Baba da wasu alamajiran data gani taredashi sanan ta wuce ta tafi, akofar gidan ta hango Muji yana kokarin tada keke da sauri ta karasa wajen ta daure fuska tace "biyani dari biyuna yaya Muji" saurayin wanda da kadan yafita tsawo da jiki ya dago kai tareda daure fuska har zaiyi magana saiya ga wayar hanunta da sauri yasa hannu yakar ba yana jujjuyawa yace "iyye waya saimiki waya dan aramin?" make kafada tayu tace "bindi salon kaje kabata min, jiya jiyan nan fa Ishak dina yabani" tsaki yayi yace "yarinya anjima nan nima zan dawo da tawa sabuwar wayar yau xan bada karamar tawa na siyo mai camera ma, soft touch, tunda hakane bazan baki daniba, kuma bazakimin hoto dawayar ba" tabe baki tayi tace "kai Yaya Muji Karya kasa, a ina kasami kudin siyar irin wayar nan daka kira wurin dubu ashirin fa ake sayar da irin wayoyin nan?" dariya yayi yace "kinga tafiya ta nidai, kuma bazan biya daribiyun ba" yana fadin haka yaja keken shi yay gaba, fashewa tai da kuka ta shiga gidan tafada jikin Baaba daduk ta rude tana tambayan ta lpy cikin kuka tace "ba yaya Muji bane yaki biyana kudina ba" share mata hawayen Baaba tayi tace "bari yadawo saiya baki dan gidansu, tashi kitayani wanan wankin dama dukna kosa kizo" karban wankin kayan tayi tama Baaba tsaf tana gamawa Baaba ta zubo mata shinkafa da miya zama tayi ta cinye harda kari kai Bilkisu badai ciba wolla.

 Wuraren shadaya da rabi tabaro gidan ta dawo gida wanka tasake yi sanan tafara shirye shiryen school Mama tamika mata dubu biyu tace "idan zaki dawo daga makaranta ki sauka a tudun wada ki kaima balaraba dillaliya kudin samiran ta dana siya, ki tabbatar ita kika bama kudin ba yayanta ba, karki manta fa kinga ta dameni nakawo mata saiyau babanku yaban kudin" karban kudin tayi ta cusa chan kasan jaka tace "bazan manta ba Mama" sanan tafita daga dakin tareda mata sallama tana karban kudin mota, wurin Baba ta tafi bayan tabiya gidan Baaba ta karbi wainarta a kula.
Tana shiga aji tasami su Walawa na wasan nonon su as usual, tsaki tayi takoma ta zauna hakan yasa suka dinga ihu Fa'iza tace "yar malam haba mana ki bari muji naki manyan nan" ko kallonta batayi ba saima bude jakarta datake yi tana kokarin ciro littafin biology dan sake karanta wa danyau sunada test, Aisha Shehu tabude jakarta cingum taciro guda shida ta mika mata tace "kinji share Fa'iza Billy, ga cingum din bikin Fateema" dan zaro ido tayi ta kalli Fateema daketa sussune kai tace "dama aure zakiyi koki fadan mana" Walawa tace "toke kin fadan mana nakine da Ishak dinki?" raurau da ido tayi tace "to ai ni sai mun zana waec tukunna za' ayifa ba yanzu bane kuma ainafada muku" hanunta Aisha Shehu ta chapke ta sakamata cingum din aciki tana kallon tafin hanun nata yanda yay zufa sosai sabida taushi tace "kedai kin more Billy jikinki taushi kaman na jaririya wai wani mai kike shafawa ne, jibidai fatar hanunki taushi kaman auduga" yatsine fuska Bilkisu tayi tareda zuba cingum din cikin jaka tace "yaushe ne bikin" "ran Saturday, amma fa 4 cingum ne naki, biyu na Raiyana biyu na Layla muna gayyatar su" murmushi tayi tace "aiko zamuzo in sha Allah" zasuyi maganan wani malamin dake musu physics ya shigo hakan yasa duk sukai shiru suna sauraron karatun, koda aka tashi break goruba tasaima su Raiyana guda hudu da topi duk ta zuba ajaka, sanan tawuce wajen su Walawa tare sukaci wainar nata sanan suka koma aji. Wuraren biyar da rabi aka tashe su, tareda su Walawa suka jero suna dandarawa zuwa bakin junction inda zasu sami mota, daidai wajen wani mai shayi sukaga wani mahaukaci yazo da gudu yadau biredin kan table ya gudu gefe kan wani dakali ya bude yawani yago kato yakai baki yanaci yana sosai kai, dariya su Aisha Shehu sukayi sukace "Allah sarki yunwa mahaukacin yakeji, amma nasan idan mai shagon nan yafito yakama shi wlh bazaiji dadadi ba, innine shi yanda Allah ya ciyar dashi dinan yagudu kawai" gani sukayi ya yayyago biredin ya tura baki rabi yazube akasa sanan yakara tashi ya koma shagon da gudu ya kara dauko biredi har biyu yana yayyaga ledan jikinsu yana kokarin yago buredin daidai lokacin mai shagon yafito daga cikin dakin shagon yana ganin mahaukacin yafito daga shagon tareda daukan katon iche daya riga yakama da wuta yayo kan mahaukacin daya zauna akan dakalin yanata cin biredi zai kwalamai da gudu Bilkisu tai wurin hakan yasa Fa'iza tace "ke Bilkisu maizakije kiyi a wurin Allah sa mai shagon yahada dake, mudai mu wuce mutafi ba ruwan mu" juyawa duk sukayi sukai tafiyan su suna maganganu, fizgo mahaukacin mai shayin yayi azuciye ya chakumo rigarshi yana jijjigashi yace "dan uwarka kasan buredin nawa kaci yanzu nan dari shida fa, kowani daya naira dari biyu ake saidawa, dan kaga jiya kazo ka dauka na barka sabida tausayi" shidai mahaukaci ko kallon fuskarshi baiyiba saima cin buredin yake kaman an aikoshi hakan yasa wani zuciya ya dauki mai shayin ya daga itchen zai bugamai Bilkisu da isowarta wurin kenan tace "dan Allah malam ka yakuri karka dakai zan biyaka nawane biredin?" ture mahaukacin mai shayin yayi ya kalleta yace "dari shida" jakarta taciro ta kwaso duka yan kudinta ta kirge su tass harda na motan ta dari uku gareta nakanta ta mikamai kaman zatai kuka tace "dan Allah ka yakuri karbi dari uku ga makarantar muchan karka dakai kaga baida lpy baimasan mekake cewaba gobe idan nazo zan kawo ma ragowar kudin" tana maganan ne tana rataya jakar tata ahannu akan saman hijab, karban kudin mahaukacin yayi yace "wlh kin taimakai dayau wlh namai lilis hakanan zaijamin asara ba gyara ba dalil..." kasa karasa maganan yayi sabida fisge jakar Bilkisu dayaga mahaukacin yayi ya ruga aguje yay kasan layi arude Bilkisu tace "na shiga uku jakata Malam" tabe baki mai shayin yayi yajuya yace "aisai ki bishi awani gida da ba'a gama ginewa ba naga mahaukacin yake kwana anan kasan layi, kije tun kafin ya salwantar miki da jakan school" shigewa shagon shi yayi yacigaba da aikin gabanshi, sosai jikinta ke rawa tabishi da kallo yanda yake gudu yana tsalle yana wulla jakar nata sama, arude ta dafa kirjinta ta kwalalo ido tace "na banu kudin Mama" da gudu tabishi gashi yay mata nisa, hangoshi tayi ya shiga wani gida da ba'a gama ginewaba, karasawa wajen ginin tayi jikinta na rawa tana kuka arude tana bin ginin da kallo ganin anma maida wajen wurin bola, ahankali ta tsallake bolar da bismillah tadan leka cikin ginin dakai tana goge hawayen dake zuba, hangoshi tayi ya zauna akasa ya zazxage jakan nata ya barbazar da komi naciki yadau cingum yana cusawa abaki batare daya bare bawon  ba, ga kudin Mama agefe akasa suma iska sai kadasu yake, kasa shiga ciki tayi jikinta sai kakkarwa yake tana goge fuska, shiko baima lura da itaba cingum dinshi yakeci yadau goruba yanata jujjuyawa yana kallonshi yana kaiwa baki  ya yatsine fuska ya jefar, ya dau kulan wainar ta yanata jujuyawa yakasa budewa, jijjigawa yahauyi yana karawa a kunne yanajin karan dayake yi hakan yasa yafara bubbuga kulan abango yana dariya kaman an aikoshi, babu inda baya rawa ajikinta ita bama ta damu da littafan ba note ne xata iya kwafewa kudin Mama ne kawai takeso hakan yasa takara fashewa da kuka mara sauti tana share fuskar jikinta na bari, gani tayi ya tsaya chak da dena buga kular a bango yadena dariyar haukan dayake yi, lokaci daya kawai taga yajuyo dakai ya kalleta hada ido sukayi, wani irin faduwa gabanta yayi dasuka hada idon gashi yaki dena kallonta, ahankali tafara komawa baya tana daddafa bango jikinta na rawa, turgude kafa tayi, tai mugun faduwa kanta ya bugu da karfe dake kan bolan hakan yasa ta buga ihu daganan bata sake sanin inda kanta yakeba.
[7/14, 19:55] +234 806 604 6091: ♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦Maman Abd Shakur

6 & 7

Keken suka shiga yatada sukabar wajen saida yadanyi nisa da tafiya sanan yace "tayaya jakanki yazo nan Bilkisu?" maida kanta kan titi tayi tana kallon yanda motoci ke gudu abunsu tace "jiya nefa damuka taso daga school na hango wani mai shago zai dakeshi sabida ya daukomai beredi yaci, wlh ba karamin tausayi yabani ba kana ganinshi kasan yunwa yakeji kato dashifa shine mai shagon dakokaika baiyiba yawani chakumo shi zai daka, wlh inda ace lpy shi lau ai daga ganin mahaukacin nan bazai dakun maiba, mutane basuda kirki da tausayi, shine nikuma nabashi 300 nace zan cikamai 300 yau danwai bread din 600 yaci, shine shikuma mahaukacin ya fizge jakana ya gudu" shiru tayi kafin ta share hawayen daya dan zubo ta kalli Muji da shima ita yake kallo ta madubin keken tace "wlh ko, da'ace ni wata mai kudi ce dana kaishi asibitin mahaukata da wanan gararin dayake tayi agari ba abinci, aita dukan shi dan sunga shi baya dukan mutane" saikuma tafashe da kuka tana goge fuska da hijabi, wani dogon tsaki Muji yaja yace "wlh bantaba ganin banziya wawiyar mutum irin kiba, aisai ki kaishi tunda kanin ubankine, irin kune kesa kanku a bala'i da sunan taimako, nidai inane gidan balaraban kafin haushin ki yasa na wuce ban bansaniba" nunamai gidan tayi yay parking tafito tabarshi akeken ta shiga ciki, yabita da kallo yana girgiza kai.   
  Yanada shekara uku aka haifi Bilkisu kusan tare suka taso, Bilkisu akwai tausayi ko minti yaganta dashi lokacin suna yara idan ya tambaye ta hanshi to karyan rashin lpy zaimata yafashe da kuka, hakan zaisa cike da tausayi tabashi tace yama shanye duka taitamai sannu.
Wuraren shadaya da rabi suka koma gida hakan yasa ta shiga wanka tafara shirye shirye shabiyu da rabi nayi tawuce tatafi.
Wuraren biyar da rabi ta shigo gidansu tana yin salla ta dauko wayar da Isyaka ya bata ta kunna "Balkisu" Mama takirata dake uwar daka ajiye wayar tayi ta tashi ta shiga dakin akan gado taga Mama a zaune rike da kofi karasawa wajen tayi tace "gani Mama" kofin ta mikamata tace "Malam ne yamiki wani sabon addu'a sha saiki rage na shafa miki akan ciwon" karba tayi ta sha da bismilla sanan ta mikama Mama kofin, kaman zatai kuka dan batason abinda zai taba ciwon nan nata danko ta tashi wanka bata ma zuwa wajen balle ta wanke, hararan ta Mama tayi tace "dagamin rigarki" ahankali ta daga rigar tana kallon fuskarta ganin yanda ta daure yasa ta natsu, debo ruwan addu'an Mama tayi takai hannu zata shafa akan ciwon da sauri ta dafe hannun Mama tareda zaro ido atsorace tafashe da kuka tace "Mama wlh kina tabawa zai faramin zafi ne, kinga tun ranan nan baisake min zafi ba yawarke dan Allah kiyakuri" hannun nata Mama ta kabar ta shafa mata ruwan ahankali sanin mugun rakin ta, ihu tayi wanda saida yasa su Layla da Raiyana dake falo suna home work suka shigo dakin da gudu, tsaki Mama tayi bayan tagama shafawa tarufe cup din ta ijiye agefe ta kalli yanda ta zube awajen tana kuka tace "wlh Balkisu kibi asannu fa inba hakaba zan cimiki mutunci dama kinsan taraki nake ko, yarinya sai iskancin banzan dako kanninki basayi zan mugun saba miki, tashi ki fitanmin daga daki" tashi tayi ahankali da taimakon Raiyana suka fita daga dakin tana kuka, yanda ta tsani mutuwa haka ta tsani abinda saisa ataba mata ciwon nan, suna kowama falon ko kallon wayar bata karaba tacigaba da kuka ahaka taci kukanta bacci yay gaba da ita, koda Isyaka yazo saidai Layla taje dakin Baba tacemai tariga da tai bacci. ******************

       Banko kofar dakin da akayi bako sallama yasa duka mataye biyun dake bedroom din zaune kan katafaren gadon dakin dago kai, wata matace tashigo tadan mayyanta dan akalla zatai 55, ta kalli daya daga cikin matayen afusace tace "haba Firdausi daga tafiyata biki yau duka duka kwanana biyar bana gidan nan shine zan dawo na tarar da wanan mummunan labari Ayaan ya bata ba'a ganshi ba, sabida nimai kula dashi baninan, ke wace irin uwa cewai? Kin haifi yaro kin kasa janshi jiki, kullum tsakanin ki dashi kyara ce da fada, ba so ba lallami, halama bayan tafiya na fada kikamai shine yabar gidan" tafashe da kuka saikuma ta nunata da yatsa tace "wlh inhar ba'a ganoshi ba wlh saina mugun saba miki nidake zamusa kafar wando dai ne, kuma bari Alaji ya warke za'asan nayine, muguwar mata mai bakin hali kawai" tafashe da kuka tafita ta bugo mata kofa, tagumi wacce aka kira da Firdausi tayi hakan yasa matar dake kusa da ita wacce kawarta ce tazo mata jajen abinda yafaru ne taja tsaki ta kalleta tace "keda danki dakika haifa da cikin ki har wata step mum ta isa tazo tana gayamiki magana haka? , Ita tasan yanda kikeji ne shine kekuma kika mata shiru iya hakuri" wani handky mai kyau dake gefenta ta dauka ta goge kwallar daya zubomata ta ijiye sanan tai murmushi ta dafa kan hanun kawartata tace "Ummu Haneef bahaka bane ai abin dadine wanda ba ita tahaifi yaronka ba hartazo tana fada dakai akan danka, wanan alamune na soyayya yanzu kinga ko bayan raina nasan Hajiya Ashferh nason dana hankalina ya kwanta" tabe baki Ummu Haneef tayi tace "lallai ni bansan irin zuciyar kiba Firdausi, anfa kiraki muguwar uwa da sauran su shine kike wani yabonta haka ai yayi kyau kicigaba" murmushi tamata tace "bahaka bane kokema kinsan halin Ayaan da Hajiya da Alhaji sun mugun bata yaron, ya lalace, sabida ina yawan mai fada da kokarin gyrashi shine suke ganin ina takura mai" handky takara dauka tasake goge wasu hawayen kafin ta kalli hadadden agogon dake bangon dakinta tace "lokacin maganin alhaji yayi bari naje nabashi ina zuwa" tashi tayi tafita daga dakin Ummu Haneef ta bita da kallo cike da tausayin yanda dukta  lalace.
Tana dawowa bayi ta shiga ta dauro alwala tafito Ummu Haneef tace "sallan mezakiyi warhaka?" Ahankali tace "addu'a zanyi dukma inda Ayaan yake Allah ya tsaremin shi, ya bayyanar dashi, ya kulamin dashi, yakuma dawo dashi lpy" tashi itama Ummu Haneef tayi ta daura wayarta akan gado tace "bari nima nayo natayaki".


*********

Wuraren 12 tafita daga gidan Baaba bayan ta karbi wainar ta data saka mata akula, mota tahau zuwa school dinsu sai tunane tunane take har aka kawo ta sauka tafara dandarawa, kallon layin da mahaukacin nan yake tayi taji takasa cigaba da tafiya ta tsaya chak, kulan wainar da Baaba tabata ta kalla saikuma ta kalli layin jitayi takasa wucewa ta tafi makarantar hakan yasa tai layin tana tafiya ahankali danji take kaman wani abu na fizgarta zuwa kaimai abincin nan, ahaka har takai ginin da mahaukacin yake tsayawa tayi chak tanabin bakin kofar wajen da kallo ganin dige digen jini da sauri ta shiga cikin ginin tanabin trace din dige digen jinin, hango shi tayi a tsakar wajen ya zauna yanata hura iska akafar shi dataga yana jini sosai kaman wani abune ya yankeshi, yanata yarfe hannu,  yana cije baki, yana jijjiga kafar da dayan hanunshi alamun abun namai ciwo sosai, dena jijjiga kafar yayi yadebo kasan dake wajen ya kwarara akan ciwon yana huhhurawa da baki dan har miyau yake fita yana yarfe hannu yana runtse ido kaman xaiyi kuka, da sauri ta karaso gabanshi kaman tafashe da kuka dan mantawa ma tai da tsoron datake ji tayi ta tsugunna tana kallon kafar tace "yanama zafi?" dago kai yayi ya kalleta suka hada ido da sauri ta dauke kai jin gabanta yakara faduwa ta kalli kafar yanda kasa kebin jinin dake fita tace "kadena saka kasa to zaikarama zafine" jakarta tabude taciro dan ruwan data zuba a goran fanta dan dashi take alwala a school taciro da sauri tabude saikuka take ta kalleshi gani tayi ita yake kallo hakan yasa ta karanto addu'o'i aranta, kaman yana gane abinda take cewa tace "bari na wanke ma ciwon" tsiyaya ruwan tayi akan ciwon hakan yasa yaja kafar arude danhar yana buge mata hannu, ahankali tace "sannu da zafi?" tai maganan tana share kwallan dataji yazubo mata, kara dan matasawa kusa dashi tai kadan tace "kawo nakara sa wanke ma kasar saina shafama rob inada rob ajaka" ko kallonta baiyiba saima juyamata baya dayayi yanata pipita duka hanunshi akan kafar dakuma hurawa da baki, kana ganinshi kasan yanajin azabane, hawaye takara shareware dasuka kasa tsayawa sabida tausayi da sauri taciro kular wainar da Baaba tabata tunawa dayana son abinci ta bude ta zagayo ta gabanshi ta mikamai tana murmushi aiko ya fizge kulan da sauri yafaraci yana sosa kunne, hakan yasa ta dauko rob ajakan nata da ruwan tadawo ta gaban shi ta tsugunna ta tsiyaya ruwan kan ciwon tsayawa yay dacin wainar yana kallonta atsorace tadan koma baya tace "yakuri" ganin yacigaba dacin wainar yasa ta karasa wankewa tass ta ijiye ragowan ruwan agefe sanan ta lakato rob ta shafama ciwon tai tagumi tana kallonshi dan jira take yagama tadau kulan ta tafi, cinyewa yay tass kafin ya wurgar da kulan yana dariyan mahaukata saikuma yay shiru yanata kallon ruwan data ijiye gefenta kallon gefen nata tayi ganin abinda yake kallo yasa tadau ruwan ta mikamai da sauri ya fizge danhar saida ruwan yakusa zubewa ya kafa abaki yana sha yanagama sha ya wurgar yana dariya saikuma taga ya buga kanshi akasa ya baje awurin yay wani katon hamma kafin ya lumshe ido sai bacci, tagumi takarayi ta bishi da kallon tausayi tana share hawayen dataji yazubo da bayan hannu "to baida iyayene dasuka barshi shi kadai sai wahala yake? Ashe ciwo yaji saisa Allah ya turota ta kula dashi? In sha Allah daga yanzu kullum saina kawoma abinci kaci, Allah yabaka lpy". daukar kulan da goran tayi tarufe ta saka ajaka sanan tabar wajen tana waigenshi.
[7/14, 19:55] +234 806 604 6091: ♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦


Maman Abd Shakur

8 - 10

Tafito tawuce school, tun daga gate tahango Sargent na dukan latti. "innalillahi wa innalillahi raji'un" kasa shiga tayi ta tsaya anan gate tana kuka har saida Sargent yagama dukan duka yan lattin sanan ya dago kai suka hada ido tana kuka yace "ke bazaki shigo amiki naki bane ko komawa gida zakiyi?" girgiza kai tayi ta shigo tana hawaye ta mikamai hannunta tana kokkomawa baya tana kuka, Chau! Ya zuba mata daya wani irin ihu tayi tana tsalle wanda yasa harshi Sargent din saida yakoma dabaya yana kallonta "ke lpyn ki kuwa?" ko kallonshi batayiba saima sosa tafin hanun take dayay jajir tana kuka kaman zata mutu, "kawo hannun saura uku" yafada yana matsowa kusada ita, hijabi tasa tana goge fuska ta makale ajikin bango. "dan Allah ka yakuri karka karamin, dan Allah" kanta yayo hakan yasa takara makalewa ajikin bango tana ihu daidai nan principal dinsu tafito tace "Sargent bar dukan turota ta gyaramin office" tun kafin Sergent dinma yay magana ta tashi da gudu tabi bayan principal tana kuka haka ta gyara office din kafin takolma aji lokacin har angama first period, ranan haka takaraci zamanta a aji tana kuka gashi a ranan ne aka manna musu time table din waec dinsu dazasu fara nan da wata daya.

Wuraren biyar da rabi ta shigo gidan nasu atsakar gida Umma data fito daga kitchen ta tareta tace "maiya sameki idanunki suka kumbura haka?" shiru tayi takasa magana dan ta tsani yin Karya, sai hawaye tafada jikin Umma tana kuka, Umma dukta rude tacirota daga jikinta tace "cikin newai?" girgiza mata kai tayi ahankali tace "dukana Sargent yayi amakaran ta" tai maganan tana nuna mata hannun dayay jajir "wayyo Allah sannu kinji Allah zai saka miki, jekiyi wanka kizo nazuba miki tuwo, Maman ku dasu Raiyana suna gidan Baabar ku" daki ta shiga ta cire kayan makarantar ta dauro zani akirji tafito rike da kayan makarantar ta zuba abotiki, kan window kitchen takoma ta dauko omo ta zazzaga aciki ta jawo ruwa daga rijiya ta wanke kayan fess ta shanya kafin takara dauraye botikin taja ruwan wanka tai bayi, tana tafitowa Umma ta zuba mata tuwo nan tsakar gida ta zauna ta tadashi tass dan miyan kukar harda wake yau akasa aciki, tana gamawa ta wanke hannu takai kwanon kitchen ta shiga daki ta dauko wayarta ta kunna, aiko kiran Isyaka ya shigo dauka tayi yay mata sallama anatse. "Assalamu Alaykum gimbiyar zuciyata, waya tabamin ke amakaranta idanunki sukai ja haka?" kaman zatai kuka ta harari bangon dakin tace "ba Sargent din school dinmu bane ba, yawani dakeni da bulalar inji a hannu" dan lumshe ido Isyaka yayi akan dakalin waje dan duk dalibai sun fita bara sai bayan sallan Isha'i za'a cigaba da karatu, malam ma bayanan, ahankali yace "kece kin dage saikin yi karatun nasara, mezaki yi dashi? Kinada ilimin addinin ki kin sauke yanzu kina kan hadda wacce kin kusa gamawa, kin haddace hadisai da dama kin iya littatafai da dama duk wanan ilimin addinin naki kika dage saikiyi na nasara, mezakiyi dashi, ai dole kisha duka haka kam, mutumin daba muharmin kiba yakama yana dukan ki, danba wanan makarantar ba dayanzu munyi auren mu natafi dake garin mu anya Bilkisu kina tausayina kuwa?" gyadamai kai tayi tace "kayakuri kaga watan gobe ma zamu fara jarabawan, muna gamawa komi yazo karshe" dan ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan Allah ya bada sa'a, sanan gobe zamuje school din saina koyama Sargent din hankali waye shi dazai tabamin gimbiyar mata, mar'atu saliha" dariya tayi sosai tana auna Isyaka da Sargent hakan yasa yace "mekike ma dariya?" murmushi tasake yi tace "babba nefa Sargent din?" "kina nufin banda karfin dukan shine kome?" zatai magana taji yakatse wayar, wayar tabi da kallo kafin ta fashe da dariya harda rike ciki tace "to daga fadin gaskiya Sargent ai babba ne kaiko bama kakai girman Sergent ba balle nasa rai zaka iya ramamin" kwanciya tayi kafin ta ijiye wayar akan kujera ta lumshe ido haka nan taji tana tunanin mahaukacin nan.
Wuraren 9 ta shigo dakin nasu dan daga dakin Abba take ta tsugunna agaban Mama dake kada lagwani, "Mama inje gidan Baaba?" "saikin dawo" da sauri ta zuri hijabin ta dake kan kofa har kasa tasaka sanan ta wuce uwar daka ta tsugunna karkashin gado ta ciro asusun ta tadawo palo ta zauna kan kujera tana jijjigawa, Mama ta kalleta tace "mezakiyi da asusun?" adan tsorace tace "fasawa zanyi Maman mu?" "kiyi meda kudin?" Mama takara jefa mata wani tambayan kasa amsawa tayi saima wasa da hijabin ta tahauyi, kafin ta dago kanta a tsorace tace "gidan Baaba zankai" dauke kai Mama tayi daga kallonta tacigaba da abinda takeyi hakan yasa ta saci kallon maman nasu kafin tadau asusun tafita daga dakin da saurin ta.
Akofar gidansu Baaba ta tsaya ta fasa asusun dayake na katsa ne, ta tattare kudin ciki ta kirga dubu biyu da dari uku ne sanan ta shiga gidan, Baaba ta gani gaban murhu Baaba tace "yar arziki kinzo" shiga dakin Muji tayi tace "ina zuwa Baaba" samunshi tayi yana shiryawa zai fita hakan yasa tazo kusa da shi tawani yi laushi dan tasan halin shi, ahankali tace "Ya Muji inkanama Allah ka kaini muyi aikin lada" "aikin ladan mene?" ya tambaye ta yana kokarin daukar sabuwar wayarshi daya saya ta gionee, wayar tabi da kallo kafin tace "dan Allah ka kaini muje muba mahaukacin nan abinci sanan in sharemai wurin nan dayake bacci kaji" wani kallo Muji yabita dashi hakan yasa ta tsugunna agabanshi tafashe da kuka, cikin kuka tace "ya Muji karka manta akwai karuwar data shiga aljanna sabida kare, taimako da kyautatawa sune dabi'un dakowani musulmi yakamata yanada shi, bamusan dame Allah zai dubemu yaji kanmuba yasamu a aljanna, kaji dan Allah, kuma karka fadanma Baaba sirrin mune wanan dan Allah ka kaini, nibanaso naje ni kadai ne, tsoro nakeji kaga jiyama ya yanke sosai akafa saisa nafasa asusu na musaimai takalmi ahanya da riga sabida ya chanxa yagargiyar jikinshi" kudin datake nunamai ya kalla mamaki dukya kasheshi ya tabe baki yace "lamarin ki akwai ban mamaki, daga ganin mutum saikace ubanku daya, nidai mutafi karki batamin lokaci" wani dadine ya kasheta ta shiga dakin Baaba, kula ta dauko tazo tukunya ganin baba na bayi ta bude dafadukar taliyar hausa ta gani ta deba sanan tarufe suka fito ta ijiye a keke sanan takoma ciki Muji yace "ina kuma zaki" bata bashi amsaba saidai tafito da jarkan ruwa da tsintsiya dawani ledan daki da Baaba tacire dan tasa sabo, dukta saka akeken Muji yabita da kallo, tai murmushi mai karamata kyau tace "muje" kunna keken yayi suka tafi. Ahanya suka tsaya tasaimai bakin takalmi kito size 43, irin takalmin nan damasu noma kesawa inzasu gona wanda yake arufe sanan tasai babbar t-shirt blue suka taho. 
Tun kafin suyi parking ta hango shi abola yanata tsintse tsintse, ahankali tafito daga keken bayan sunyi parkin rike da kulan, mahaukacin na hangota yataho da gudu har saida takoma baya da sauri amma ya bita ya fizge kulan hanunta yana dariya, da sauri ta kalli Muji daya bisu da kallo tace "kama gani yaganeni wlh" tabe baki Muji yayi yataya ta daukan jarkan ruwan itakuma ta dauko tsintsiya da leda suka shiga gidan. Yana zaune akasa sai kiciniyar bude kulan yake hakan yasa ta budemai ya fizge da sauri zai saka hannu ta rike hanun nashi gabanta na faduwa tace "tsaya in wanke ma hannun da datti" ta kalli Muji hakan yasa ya tabe baki yakaraso wajen yabude jarkan ya daga itakuma takai hannunshi tana wankewa Muji na zuba musu ruwan sanan ya fizge yahau ci, murmushi tayi tana kallon ciwon kafar nashi sanan ta yayyafa ruwa a wajen tasa tsintsiya tafara shara har takai waje ta shinfida carpet din dayadan yayyage, nan da nan wurin yay kyau, yana gama cin taliyar yayar da kulan da sauri ta mikamai ruwan ya karba yasha sosai yay wata irin katuwar gyatsa, takalmin ta dauko tazo ta gabanshi tana kallon kafarshi daduk yay datti, ruwan tasa ta wawwanke mai kafar yanata kallonta kafin ta saka mishi takalmin aiko yamai  daidai, ya mike tsaye yanata tsalle yana kallon takalmin, ta kalli Muji kaman zatai kuka tace "toka sakamai rigar dan Allah" atsorace yace "ni? Ni wlh tsoro nakeji" dariya tai tace "Allah bazai maka komiba baya komi" ta mikamai rigar suka karasa kusada shi tare, ya juyo yana kallonsu duk suka tsaya chak suna kallon juna, daga mai rigar Muji yayi yana juyawa asama hakan yasa yadinga bin rigar da kallo sanan Muji yasa hannu zai ciremai ta jikinshi da sauri ta juya musu baya saida Muji ya ciremai sanan ya samai wacce suka siyo aikuwa tamai daidai, da sauri Muji yace "juyo kigani" murmushi tayi tana dafa Muji tace "laaa ashe na cinka size din daidai" ganin yanda yaketa tsalle yasa muji yace "bari namai hoto" ciro wayarshi yay yadinga daukan shi hoto yanda yaketa tsalle tsalle ya kalli Bilkisun daketa dariya yace "dalla malama mu matsa kusa dashi dukmuyi selfie, selfie da mahaukaci" yay maganan yana dariya yana janta har inda yake ai kuwa mahaukacin na ganinsu ya dena tsallen yana kallonsu duk suka tsaya a gefenshi, Muji ya dau hoton. Tace "zomu tafi to tunda mungama" fita sukayi suka barshi yanata tsalle tsalle. Yau kwana ta biyu kenan bataje wurin shi ba sabida weekend gashi ba makaran ta, sanan Baaba nama wasu dalibai daya yaye walima aiki suketa yi bata samu daman fita daga gidan ba, haka tai kwanaki biyun nan tunanin shi koya yake oho koma yaci abinci oho duk tabi ta damu sosai.
Yau Monday tun shadaya ta shirya Mama tace "da wuri haka zaki yau Bilkisu?" gyada mata kai tayi tace "eh inaso nai karatu ne sosai Mama jarabawan mu yakusa" kudi Mama tabata sanan tafito ta karbi kudin mota wurin Baba kafin ta wuce gidan Baaba dayawa ta dibi wainar yau tazuba ruwa agora tafito har bakin titi kafin tahau mota dazai kaita sabon gari. Sauka tayi ajunction sanan tafara dandara wa har zuwa layin mahaukacin, babu kowa a wajen wurin hakan yasa ta shiga ginin tana karanto addu'o'i, a kwance ta hangoshi abinda bata taba zuwa ta tarar dashi haka ba kenan, idanunshi sunyi jajir kaman ma rawan sanyi yake, da sauri ta karasa ciki ta tsugunna agabanshi tace "menene?" ganin ko dago kai baiyiba yasa takai hanunta dake rawa sosai tadan taba wuyanshi da sauri tajanye hanun jin wani irin zafi da jikinshi yayi, fashewa tai da kuka sosai tace "kayakuri bankawo ma abinci jiya da shekaran jiyaba halama saisa kake ciwo, zokaci abinci" hannu tasa zata da gashi ya tunkude ta har saida tafadi ya cigaba da rawan sanyi yana jan hanci, sake dawowa gabanshi tayi tana goge hawaye tadau kulan wainar ta bude ta nunamai sanan ta ijiye gefe tasa hannu ta dago shi ya tashi ta jinginashi da bango, wani irin rawan sanyi yake tadau kulan ta bashi amma yakasa fizgewa yanda yasaba yi, wani irin mugun tausayi yabata tafashe da kuka sosai, hannu tasaka ta dauko wainar daya tace "ci" bude baki yay kadan yakarba daga gani kasan yunwa yake ji, biyu kawai ya iya ci daga nan bai kara bude baki ya karba ba, hakan yasa ta bude ruwa tabashi shima yasha kadan ya ture har saida ruwan ya zuba afuskar ta bata damuba ta share fuskar, kwanciya yakara yi saikuma taga yafara mimmikewa yana wani irin iri dabaki kaman yanason yay magana amman yakasa, sai kallon sama yake yana wani iri dabaki, matsowa tai kusa dashi duktama rude hakan yasa ta mike tsaye tafita daga wurin dagudu tana kuka har bakin layi, mota ta tare tahau sai gida, Koda takai gida Baba bayanan Mama ta kalleta tace "lpy kika dawo tun yanzu?" hawaye tasake shareware tace "Baba nake nema" tabe baki Mama tayi tacigaba da kwashe kayan datake yi daga kan igiya tace "ai siki jirashi yaje wani jana'izar abokin shi daya rasu ne" to kawai tace tama fita daga gidan taje chan kofar gida ta zauna tanata kallon almajiran dasuke karatu tana share hawaye Allah Allah kawai take Baba yadawo, sai wajen karfe uku da rabi Baba yadawo tun akofar gidan yace "maiya dawo dake Bana riga nabiya kudin makaranta ba" dan azaton shi ko an korota ne, girgiza mai kai tayi saikuma tafashe da kuka hakan yasa yace "baki da lpy ne?" girgiza mai kai tayi, ahankali ta shiga goge hawayen sanan tace "Baba kawata yar makarantar mu yayan ta mahaukaci ne, yau haukan shi yatashi baida lpy sosai, sai wani iri yakeyi da baki kaman yana magana dawasu, shine suka ce nazo dan Allah kamusu addu'a aruwa dazasu bashi ko zaiji sauki" "sabida hakane kike wanan uban kukan" girgiza kai Baba yayi yace "Allah ya shiryaki, je gida ki kawo ruwa mai kyau agora namiki addu'a aciki saiki kaimusu abashi" da sauri ta koma cikin gidan ta debo ruwa mai kyau agora sanan tafito takawo ma Baba dake zaune akan tabarman shi na Zaure, karba yayi ta zauna kusa dashi, kara ruwan yay abaki yafara karanto addu'o'i daban daban da karatu, yafi awa daya ahaka sanan yay topi aciki yarufe yabata yace "gashi nan ki kaimusu subashi, idan yasha su tofa mai ayatul kursiyu kafa bakwai aka, kulhuwallahu kafa uku a ka falaki da nasi uku aka, inhar sihiri ne wanan addu'a zai Karya shi, inkuma haukar ciwo ne daga ma'aiki to wanan kuma duk lokacin da ubangiji yaso warkar dashine zai warke, amma dai inhar sihiri ne zai karye yabar jikinshi da izinin Allah, i maza jeki kai musu" hamsin yakara cirowa yabata ta karba tawuce harda gudunta takai bakin titi tahau bus, sosai ake traffic dan wai hatsari akai a hanya ba ita takai ba sai wuraren magrib, tana sauka a bus din takara kwasa da gudu zuwa layin da addu'a da shiga ginin.

Juye juye ta sameshi yanata yi akasa Allah kadai yasan meyake mai ciwo, da gudu takara sa gaban shi ta tsugunna ta dukar dakai tana kallon fuskarshi dataga idanunshi sunyi ja sai rawan sanyi yake yana atishawa, kama hanunshi tayi hakan yasa yadan dago kai, da duka karfin ta tajashi tamaida shi kan carpet har tana buga baya da bango ta zauna a gefenshi, goran ta bude takaimai ruwan baki ta kafamai, karba yay yasha sosai dan dama kishi yakeji, saida yasha kusan rabi sanan ya cire bakin yasake kwanciya tareda buga kanshi akasa saida ta runtse ido, ta rufe goran ta ijiye, sake matsowa kusa dashi tayi ta karanta mai su ayatul kursiyu da Baba yace ta karantamai duka ta tofamai aka, takoma ta zauna agefen shi tana kokarin bude jaka dan bashi cingum din data tahomai dashi kozaidan ci, gani tai ya zabura ya mike ya dafe kanshi da duka hanunshi biyu yarda jakan tai tadan matso kusa dashi ta kallai, buga kai taga yay da bango ta fashe da kuka tareda daura hanunta akan nashi tace "kadena kanka zai fashe" buge hanunta yayi yawani kwanta akasa tareda rike cinki shi yana numfashi sama sama kaman zai mutu, bakaramin tashi hankalin ta yayi ba, rasa abinda zatayi yasa tafita da gudu kozata ga wani amma babu kowa a wajen sai karan speaker wani massallaci dake bayan layin dan wa'azin bayan sallan magriba akeyi, kakarin aman dataji yasa tadawo ciki da sauri cikin shi taga yarike sai amai yake kaman zai amayar da hanjin cikinshi, tsugunnawa  tayi kusa dashi dan jitake kaman ta daukemai ciwon, duka wainar dayaci saida ya amayar saikara kakarin aman yake amma babu abinda ke fitowa ragowan ruwan ta dauko takawo mai ya bude tasaka mai abaki yadansha kadan sanan yakara komawa ya kwanta akan carpet din yana wani irin mugun rawan sanyi fiye dana da, daga gani kasan mugun sanyi yakeji rasa mezatayi yasa tacire hijabin makarantar dake jikinta ta rufamai, yarage  daga ita sai faran rigar makarantar mai dogon hannu da purple dankawalin makarantar dake kanta ta zauna ata kanshi tana sake tofamai addu'a ganin bai dena rawan sanyin ba, tashi zaune yayi azabure yafada jikinta yawani irin kankame ta yana wani irin nishi da ita kanta saida taji kaman zata suma wajen tsoro ga jikinshi wani irin mugun zafi, duk wani addu'a dayazo bakinta karantashi takeyi tana kokarin tureshi amma takasa sabida wani irin kankameta dayayi fuskarshi akan wuyan ta, sunfi minti goma ahaka ganin gari yasoma duhu sosai dan bamata iya ganin fuskar shi sosai yasa tafara kokarin tureshi danya saketa tatafi gida amma takasa, danko motsa hannu takasa, kuka tafashe dashi sosai tace "ka sakeni natafi gida" ganin baimasan metake cewaba saima jikinshi da ko ina ke rawa yanata wani irin nishi ya kankameta yasa tai shiru tana kuka ahankali zafin jikinshi na kona ta sosai, wani irin tsoro ma taji tanaji yanda takejin kukan abubuwa daban daban awurin tafara karanto addu'o'i tana kuka kasa kasa, jujjuya kanshi taji yanayi awuyan ta yana wani irin nishi kafin yafara bubbuga kanshi akan kafadarta da karfi, tafashe da kuka sosai dan bakaramin zafi buga kan kemata ba, dena wa yayi kafin ya burkito ya gangaro da kanshi kan kirjinta, ya kwantar da kanshi awurin ya kankameta sosai dan kaman zai shige jikinta yana rawan sanyi, wani irin kuka takeyi gabaki daya yawani irin riketa danko motsi, ko numfashin kirki ma bata fitarwa, kuka tacigaba dayi har wani irin wahalallen bacci yay gaba da ita azaunen.


Ahankali yake bude idonshi dayaji sunmai wani irin shegen nauyi ga kanshi dake wani irin fitinannen sarawa, daga hannunshi dayaji yay mai nauyi yay yadaura akanshi yafi minti biyu ahaka kafin yakara sa bude ido gabaki daya yana karema wurin kallo daya cika da hasken rana, bin gabaki daya wajen yay da kallo kafin ya sauke idonshi a inda kanshi yake da sauri ya janye kanshi daga kan kirjin wata faran kakkywan yarinya dayaga ta takure abango gawasu busassun hawaye dasukai layi layi a fuskarta, da sauri ya mike tsaye ganin ajikinta yake yabi gabaki dayan wurin da kallo yana kare hancin shi sabida wani irin wari dayaji wurin nayi, yana komawa da baya da baya, champal dayaji akafan shi yasa ya kalli kafar da sauri yaga kafarshi cikin amai yasa yay wani irin ihu "Fuck! Wah! Ewww" yawani yatsine fuska, afirgice ta bude ido jin ihu tabi wurin da kallo kafin ta sauke kanta akan mahaukacin dataga sai kallon kanshi yake yana mikar da hanunshi sama yana kallon hanun nashi dama duka jikinshi gabaki daya, kokarin tashi tayi amma takasa sabida yanda kafarta yay mugun tsami dan kafarta alankwashe suke daya kankameta jiya, kiciniyar tashi datake yi takasa yasa yajuyo kai ya zuba mata idanun dayasa taji kirjinta yabada wani irin duma dum! Zuwa wajen yay azuciye yawani irin fizgota har saida tai kara sabida yanda kafarta yay kara tace "wayyo Allah kafata" kawad da kanshi yayi tareda saka hannu daya yana kare hanci saikace kashine yazo gabanshi, dan matsawa yay nesa da ita yana kakkare hanci tareda mata wani irin banzar kallo dayasa taji kaman zatai fitsari, nuna ta yay daga sama har kasa da yatsa yace "who d f*ck are u?".
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *SANGARTATTCE* by * Maman Abd Shakur* Gimbiya 0 5,888 07-19-2019, 11:08 PM
Last Post: GimbiyaUsers browsing this thread: 1 Guest(s)