Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*SANGARTATTCE* by * Maman Abd Shakur*
#1
SANGARTATTCE


Maman Abd Shakur

11 - 12

 Kasa bashi amsa tai ganin maganin Baba yay aiki gashi yaji sauki, bayan hannu tasa  to goge hawayen dasuka zubo ta juya ahankali tana dingisawa batare data sake kallonshi ba ta tsugunna da kyar sabida kafarta tadau hijabin ta dake kan carpet tasaka tai hanyar fita daga dakin, wani irin fizgota taji anyi arude tajuyo baiyi watawata ba ya dauke ta da mari mai kyau hakan yasa tafasa wani irin uban ihu ta dafe kuncinta tana wani irin kuka, nuna kanshi yay da yatsa yana kallon fuskarta cikin husky voice dinshi yace "ke kinsan wayeni ina miki magana and u dare walk out of me, F*ck!" yawani dunkule hannu ya daki iska, Muji da tuntuni yake tsaye abakin kofa ya shigo da sauri yazo wajen dan tun jiya da daddare ake nemanta agida, hankalin kowa yatashi, dazu dasafe ma su Umma sukazo duba ko agidansu ta kwana, kotadawo da latti tsoro yasa ta kwana amma batanan hankalin Baaba duk yabi yatashi, yanajin haka yadau keke yafito batare da kowa yaganshi ba hakanan zuciyar shi yace yazo yadubata anan. Karasa shigowa yay yabita da kallo yanda take kuka sosai ga hanunta akan kuncinta da sauri Muji ya kama hanun ya cire daga kan kuncinta ya kalla yanda wajen yay ja duk shatin hanunshi sunfito, fadawa kan Muji tayi tana sheshekan kuka da kyar ta iya cewa "mutafi Ya Muji yariga ya warke" Cireta Muji yay daga jikinshi ya kalli Mahaukacin dasu yake kallo, azuciye Muji yace "uban me kanwata tama ka mare ta haka eh adam, butulu kawai, kasan irin dawainiyar datai dakaine mahauka..." da sauri tarufe mai baki tana kuka tace "dan Allah nidai mutafi gida, yaji sauki shikenan ai" ture ta Muji yayi hartana neman faduwa cike da masifa yace "wlh karki bari na daura miki wani marin nima, tun dazu na tsaya anan ina ganin abunda yamiki uban wayeshi dazai mareki haka? aida kinbarshi anan yacigaba dacin abincin bola banza dakiki mai dukan mata" cakumo shi yayi azuciye da idanunshi dasukai mugun ja ya shake Muji sosai, Muji yafara tari abunku daba karfi daya ba, tashi tayi daga tsugunen datake tana kuka tafara dukan kakkarfan hannunshi da karfi tana kuka. "ka sakeshi, ka saken min wana, wlh ka sakeshi, zaka kashe shi" cire hanunshi daya yay daga kwalar rigar Muji yasa hannun ya hankadeta tafadi kasa, wani irin mukurkusu tayi sabida ciwon ta daya kama mata tafasa ihu sosai. "wayyo Allah na cikina, Ya Muji zan mutu, zan mutu wayyo" juyo da kai yay ya kalli Muji da tsabagen wuya idanunshi sunyi ja sosai, jijiyoyin kanshi sun fiffito yace "duk randa ka kara haduwa dani watch ur tongue and know how u speak to me, bana tolerating raini one single bit get it?" ya tambaye shi fuskarshi a mugun daure dan ranshi yay tsananin baci, gyadamai kai Muji yayi ahankali dan ya shaku wlh, hakan yasa ya sake shi yana kai hanun hancin shi yana tsaki, da sauri Muji yay kanta ganin yanda take kuka kaman zata mutu, dagota yay da karfi tareda saka hanunta daya ta bayan wuyan shi ya taimaka mata ta mike tsaye da kyar, fasa ihu tasake yi zata koma kasa. "Ya Muji bazan iya tashi ba, cikina, Wayyo Allah na jama'a, wayyo na shiga uku na lalace ku taimakeni" ta rirrike shi, Muji dayake ji da bakin cikinta dan ita tajamai wanan muguwan shakan gakuma tausayin ganin yanda dukta rikice, ahankali yace "toyi tafiya ahankali muje waje mu shiga napep muje gida" girgiza mai kai tayi tafashe da kuka sosai tace "ni kadauke ni idan nai tafiya barkewa ciwon zaiyi ayanda nakejin yakemini" kwalalo ido Muji yay ya harareta yace "to ta ina zan iya daukan ki wai Balkisu, kinga wlh ko kiyi tafiya konabarki anan baruwa na narantse" kara maida hanun nata bayan wuyanshi yayi tana kuka, ya jata da karfi dayaji kaman zasu fadi dan kin tafiya tayi sabida ciwon dake mata sosai, yafita da ita daga ginin ya sakata a keken yana hararan ta yace "ai Allah yakara uwar taimakon cikin ma yafashe banziya kawai" ya watsa mata mugun hararan jiyake kaman ya gwabje ta, ya shiga gaba azuciye danhar yana buge kai, harya kunna keken yakasa hakura ganin yanda take kuka daga gani bakaramin buge ciwon tayiba gakuma wuyan shi daya rikemai dan har yanzu bai dena zafiba. Wlh bazan yarda ba" fita yay daga keken yay hanyar ginin daidai shima mahaukacin yana fitowa sai wani kyankyani kyankyani yake yana kallon kuturun takalmin kafarshi injishi, ganin bolan wajen yasa yay turus ya tsaya yana tunanin yanda zaibi ya wuce, ganin Muji yadawo yasa ya zubamai mayun idanunshi masu kama dana mage, dan komawa baya kadan Muji yayi dan yaune rana tafarko dayaji mahaukacin nan ya mugun cikamai ido, sanan ya  kallai yace "wlh Allah ya isa bamu yafema ba dukan mu dakayi, kaga yarinyar chan daka tado mata da ciwo" ya nuna Bilkisu dake cikin keke ta cusa kanta a cinya tana kuka yace "da kana mahaukacin ka, duk uban dattin dakayi bata kyamace kaba ta kula dakai, ta gyara inda kake zama, tasaka ledar dakake kwana dinchan aciki wanda tundaga gida ta dauko, kullu yaumin saita debo abinci daga gida takawo ma kaci sabida dukan ka ake idan kasatoma yan shaguna buredi, tafasa asusun ta tasiyo ma wanan takalmin dake kafarka sabida yankewa dakayi akafa sabida  rashin takalmi, tasaima wanan rigar jikin naka dan na jikin ka yagama yawo, sanan ta karboma addu'a wajen Baban ta, tabaka kasha ka warke shine ka zanemu ko, to Allah ya isanmana wlh, da marinta da shakeni dakuma fama mata ciwon ta bamu yafeba" yana fadin haka yajuya da gudun bala'i ya shige keken dayariga ya kunna yabar wajen dan gani yay kaman zai biyosu.


 Wani irin dogon tsaki yaja kafin yakara kallon bolan yana rufe hanci yafi minti uku ahaka yana tunanin yanda zai tsallaka da kyar yabi bolan tareda runtse ido "jeez, i hate dis sh*t" saida ya tsallake sanan ya bude ido tareda sauke ajiyar zuciya yana tofar ya yawu, kallon dogon layin yayi yana tunanin yanda zai iya tafiya akafa ya shanye layin, sanan ya kalli kayan jikinshi, sake runtse ido yayi tareda shafo kanshi da duka hannu biyu, abinda yatuna na karshe shine yana garden yanacin white rice da pepper soup. Ajiyar zuciya yakara saukewa mai sauti kafin yafara tafiya ahankali dan gabaki daya jinshi yake very very weak ko rabin layin bai shanye ba ya zauna akan wani dakali yana mayar da numfashi, cije lips dinshi yayi kafin ya dunkule hannu yadaki iska. "f*uck wats all dis sh*t?" tunda yake baitaba dogon tafiya akasa hakaba, maganan yaran dayaji agabanshi yan kananu haka suna leken fuskar  shi yasa yabude ido ya kallesu, sunata mai dariya suna waka "waye barawon buredi?" sauran suna amshi "mahaukacin nan shine barawon buredin shagon malam liti mai shayi" saisuyi dariya suna mai gwalo, binsu yay da kallo kafin ahankali ya yunkura zai tashi aiko suka kwasa a guje suna ihu "wayyo mahaukacin yabiyomu Maman mu" bai sake kallon suba yacigaba da tafiya aiko yaran suka cigaba da binshi sunamai wakan mahaukata, ahaka haryakai bakin titi yarasa inda xaisa kanshi baimasan wani gari ne nanba saida garin bai mishi kama da kano ba, haka yadinga tafiya yana tare abin hawa babu wanda ya kulashi, yafi awa biyu dan harya fidda rai saiga wani dan xpress ya tsaya daga ganinshi kasan dan wiwi ne yace "kai yane mahaukaci lpy ka tsaya akan titi? Kosai wani ya kwashe ka ya aikaka lahira?" wani irin kallo yama dan Xpress din hakan yasa mai machine din yace "wayihuhu kai wlh kafadama aljanun kanka nafi karfinsu dasuke min wanga kallo dama na tsaya ne nazaci ko wani abu kakeso dan naga tuntuni kake tsaye anan ashe duk cikin haukan ne" burga machine dinshi yayi zaitafi, ganin shine only hope dinshi yace "tsaya" authoritatively yay maganan, kallonshi dan acaban yayi yace "kace mene kai mahaukaci?"  dan shiru yay rasa maima zaice, shi baisama roko ba, bai iya neman taimako ba, jin karan ya kunna machine zai wuce yasa yasake kallonshi yace "inane nan wurin?" "kaman ya inane nan wurin, bakin titi mana?" dan lumshe ido yayi kafin yabude su ahankali yace "wani gari ne nan?" "zaria" dan acaban ya bashi amsa atakaice yana fito "ya muje ne" yanama wani singnal dake tsallake ko tafiya ne yaje sutafi, mayar da dubanshi yay kanshi, kai tsaye yace "ban aran wayan ka?" karkato bakin glass daya saka a idonshi yayi ya kalleshi yace "wayyo ni iskokan kanshi na sona, kai mahaukaci ni wayata na wajen chaji aida nabaka naga uban me mahaukaci na iya da waya" runtse ido yayi jin maganganun shi gakuma zafin rana dake dafamai fata, gakuma gajiya, atsanake ya bude idon ya saukesu akan mai machine din yace "zaka kaini kano chan GRA?" yay maganan yana dafe kanshi sabida saramai dayayi, bin shi da kallo mai machine din yayi yace "ka warke newai? Naga kanata min magana kaman mai hankali, nafa saba ganin ka dan liti nacin ubanka idan kasato mai buredi, yanzu kai to da baka da kosisi mezaka bani idan zan kaika Kanon?" tattaba aljihun shi yayi kafin ya shafa wuyanshi jin chain dinshi na nan yasa yaciro da sauri ya mikama mai machine din yace "24 karat gold chain ne, made in Austria ??, worth millions, gashi ka rike ka kaini kano yanzu" hanunshi mai machine din har rawa yake ya karba yana dubawa, gold ne har gold, ga chain din doguwa sosai irin ta maza dinan yan iska, kasa rufe baki yayi ya kalleshi yace "hau, hau muje tasha inada aboki mai mota nasaka aciki mu kaika" kiri kiri yakasa hawa machine din dan baitaba hawa machine arayuwan shiba tunda aka haifeshi, ganin hakan yasa mai machine din yace "dafani saika ware kafarka kahau" dafashin yayi kaman bayaso yana kallon rigar jikinshi da tsabagen datti tai annakiya sanan yay yanda yace saida yakusa fadin da machine din da kyar mai machine din yay controlling ya gyara zaman shi yace "kai kacika karfi" sanan yatada machine din yawani jaa machine din tareda yin awizo ganin yana neman faduwa yasa ya dafa kafadar mai machine din yana yatsine fuska, wani gareje suka je suka sauka mai machine din yay parking machine din suka karasa wajen wani mota, cikin minti goma suka tada motar suka ce ya shigo ya shiga sai kano.
[7/14, 19:55] +234 806 604 6091: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

13 - 14

Daidai kofar gidansu Muji yay parking keken, lokacin duk daliban sun fita bara dan karfe goma dama ake tashin su, Baba da Isyaka ne duk a tsaye a kofar gidan sunje dogon bauchi makarantar su tsakanin jiya da yau yafi sau hudu nemanta, amma duk basu ganta ba, ganin keken Muji ya paka ga Bilkisun sai rusa uban kuka take yasa Baba yay azamar zuwa wajen daidai Muji yafito daga keken, anatse Baba ya kallai yace "a ina ka ganta Mujittapa?" kame kame Muji yafara yama rasa wani karya zai shararo da sauri ya juya yafara kokarin fito da ita yace "chan hanyar gidan kawarsu na ganta awani lungu asume Baba" "subhanallah" yafada yana kokarin cirota daga keken da kyar suka fito da ita dan kasa tsayuwa tayi sabida cikin, da taimakon Baba da Muji sukai cikin gida da ita, Isyaka yabisu hankali atashe dan bazai iya daurewa ba ya shiga gidan ganin duka matayen tsaye a tsakar gidan ba lullubi yasa yajuya da sauri yakoma zaure danba karamin kunyan su Mama yakeba.

"La'ilaha illallahu maiya sameta malam?" Baaba tai magana kafin ta kalli Mama dake gefenta tace "dauko tabarma Amina a shinfideta akai" daki Mama takoma ta fito da tabarma ta shinfida anan bakin kofa sabida nanne da inuwa, nan Baba da Muji suka kwantar da ita, da kyar ta kwanta dan kafe musu tai a tsaye wai zafi, Baba zai juya yaje daki yadebo ruwan addu'an daya mata ta kamo hanunshi gam tarike. "Baba, Baba to ina zaka wlh azaba yakemin yamafi na ranan nan, dan Allah ka tsaya kusa dani kaji Baba" tafara daddaga dayar hanunta saman tana neman ruko wani, dan haka take inhar tana rashin lpy to bata barin mutane tabuka komi duk kakkama su zatayi ta rike muku hannu hakan nasata jin kaman ciwon ya ragu, hannun Baaba takamo ta rike gam cikin kuka tace "Baaba kene ko rikeni to, dan Allah kema karki tafi" tasake sakin wani ihun tareda damke hannayen nasu gam. "wayyo Allah na Mama, Mamaaa, Raiyana, na shiga uku Umma, Umma Umma zo kibude min cikin yasha iska" jiki a sanyaye Umma ta tsugunna ta nannade mata rigar makarantar zuwa sama aikuwa wajen yadan kumburo kaman tahadiye karamin kwai a wurin, tagumi Mama tai ta zubama Baaba ido hakan yasa ahankali Baba ta juyo ta kalli Malam dake gefenta ya tsugunna yana mata addu'a sanan ta kalli Muji dake kallon yanda Bilkisu ke kuka tace "wuce katafi nema zataji sauki kaji dan arziki" fita yay daga gidan jiki asake, Malam nagama tofa mata addu'an ya mike tsaye zai shiga daki hakan yasa Baaba tabi bayanshi, sallama tai yabata izinin shiga, zama duk sukayi sanan tafara koromai zance anatse. "Malam wata yar magana nakeson nama dama, bawai inaja da Allah bane kokuma inaso nama shishigi ba, zancen ciwon Bilkisun ne dama, naga tun fa tana shekara sha bakwai abinnan yafara fitomata dan karami kullum saidai aita mata addu'a aruwa tasha ya lapa, gashi har yanzu tana sha takwas amma ana kan abu daya saima kara girma yake, ni dama cha nayi ko za agwada na turawa ne mugani koya kagani malam?" shiru yayi yanadan dogon tunani kafin yace "da yardan Allah haka za'ayi amma akwai wani maganin gargajiya dazan karbo mata wajen wani abokina anjima inhar tasha babu chanji to zamuje asibitin" murmushi jin dadi tayi ganin Allah ya dorata akanshi dan Maman Bilkisu tasha fama dashi akai yarinyar asibiti yaki yarda hakan yasa tafito daga dakin rai fes ta sakan musu murmushi tareda kallon Bilkisun dake baccin wahala har wani irin nishi takeyi abaccin.


*************************

*Kano*
 Agaban wani Mansion yasa sukai parking, wanda girman gidan kadai yayi girman wani anguwa fita yay daga motar, su dan acaban sai kallon gidan suke hakadai suka kunna mota sukabar unguwar, tunkarar gate din yayi wanda securities sunfi biyar biyu agaban gate sauran kuma suna tsattsaye akowani bangare na wajen duk shi suke kallo, hanyar gate yay zai shiga securities din suka tareshi da fuskokin su da babu alamun wasa sukace "wakake nema agidan nan?" wani irin kallo yamusu tareda rungume hanunshi akirji ya zuba musu mayun idanunshi, dayan ne yafara cewa "innalillahi, kai sir ne, he is back" gabaki dayan su tsugunnawa sukai suna bashi hakuri baiko sake kallonsu ba yatabe baki ya shige cikin gida. Bababan gidane dake dauke da motoci kala kala, different part ne agidan har hudu, da sauri yay part din parents dinshi yana kwalama baban shi kira. "Popsy, Popsy" Abba dake zaune a bedroom dinshi ga karin ruwa a hanunshi wanda yakusa karewa ya kalli Mami dake zauna a gefenshi tana bashi yankanken fruits abaki dayake ci da kyar dukya fita hayyacin shi, kaman daga sama sukaji muryan shi. "Popsy" hakan yasa ya ware ido tareda dagama Mami hannu dan yaji ko gizo kunenshi kemai jin muryan Ayaan, sake jin muryan shi yana "Popsy" yasa yamike ya cizge karin ruwan daga hanunshi yafice daga dakin Mami na biye dashi itama.

Shigowa katafaren falon mai kama da aljannar duniya yayi, yan aikin dake sanye da uniform suna kokarin gyara dining suka bishi da kallon waye wanan ammadai basuyi magana ba. "Popsy, Popsy" yakara kwalama baban nashi kira, baki zai bude yakara kiranshi sai yay turus yana kallon fuskar shi ta jikin uban show glass din dake falon da aka jera wasu hadaddun verses aciki, madubi ne gabaki daya, yanda gashin kanshi suka wani mummurde kaman dada ga gemushi busu busu da yanda fatar shi tai wani irin mugun baki ya tsaya kallo shi kanshi yana mamakin shine haka, dan yama kasa gane shine. "Boy!" yaji Abba yakira shi da irin muryan manya dinan wayanda suka kwana biyu aduniya da sauri ya juya yaga Abba akan stairs ya tsaya tareda kama karfen stairs din dan baida karfin tsayawa complete ga Mami itama tsaye a gefenshi duk sun kafeshi da ido.
"Pops" yafada kaman zaiyi kuka yay hanyar benen da sauri, Abba ma yafara tattakala stairs da sauri kaman bashine mara lpy ba. "Boy, Mah Boy is back, Ayaan is back" da gudu da Ayaan yafada jikin Abba ya kankame shi sosai, hakama Abba ya kankame shi ya sumbaci gefen fuskarshi batare daya damu da warin da fatarshi yakeba, sunfi minti kusan biyar ahaka yan aiki sai kallonsu suke suna murna da yau sunsan zasu sami special kyauta dan gatan alhaji da aketa nema yadawo, sakin juna sukayi Abba yay cupping fuskar shi yakara sumbatar goshin shi kafin ya kara rungume shi akaro nabiyu ya sauke ajiyar zuciya, murmushi yay wanda  daga rashin yake anya akwai abinda yakeso a duniyar nan kaman Pops dinshi kuwa, sakinshi Abba yay yakara cupping fuskarshi kaman zaiyi kuka yace "maiya faru dakai Boy? Babu wani gidan talabijin da gidan radio dabamu sanar da bacewar kaba, da saka hotunan ka aduka gidan talabijin din Nigeria nan, waye yama wanan abun Boy, yaushe ka girma mema kasani dahar mutum saiso cutarmin dakai, kuma agidana ma, koma waccece maid dinan data baka abinci ranan da sunan ka mahaifiyar ka sai annemota zata gane ta tabamin kaine wlh azim" zame fuskar shi yay daga hannun Abba yawuce ya rungume Mami daketa kallon su tareda daura kanshi akafadar ta ahankali yace "i miss you Mami na" wani kwalla ne yazo mata kafin itama ta ciroshi ta sumbaci goshin shi daidai lokacin Baba Sule ya shigo da Hajiya Saratu (uwar gida) data shigo da kuka sosai  ta tsaya agaban shi takai hannu tana shafa fuskar shi tafashe da kuka sosai cikin kuka tace "maiya sameka d'ana, Ayaan haukacewa kayi ashe da gaske dai? Innalillahi wa innaillahi raji'un, duniya ina zaki damu?" cikin kuka takara kallon Alhaji daketa shafa kan Ayaan din kaman zai hadiye shi dan so, tace "Alhaji wlh ko bangon duniya ta shiga anemo maid dinan data bashi abincin karshe" tasake fashewa dawani irin kuka tafada jikin Ayaan din, dago da kanta yay ya girgiza mata kai tareda sa hannu ya goge hawayen dake zuba daga idonta yace "stop crying Big Mummy, am okay now" gyadamai kai tayi kafin tai murmushi tace "to ya akayi kaji sauki, CCTV footage damuka kalla ya nuna a haukace kafita daga garden din, ya akayi ka warke?" yatsine fuska yay tareda dafa kanshi da sauri Abba ya rikeshi ya kalli Big Mummy yace "ki barshi haka da tambayoyin nan daga dawowan shi muje side dinka ka huta" yarike mai hannu tareda kallon Baba Sule yace "muje Sulaiman" Baba Sulaiman yabisu abaya suna sauka kasa Abba yafara kwalama chief of staff din gidan kira "Mike, Mike" da sauri mutumin yafito shima sanye da uniform yace "call for home service masu massage, manicure, pedicure, da kuma barber dakemai aski be fast" dukar dakai Mike yay yace "to Alaji" ya juyo ya kalli big Mummy yace "kekuma kira Dr Hassan yaduba min shi" ashagwabe ya kalli Abba ya turo baki yace "Pops no basai yazo ba, zanyi prescribing drugs din danake bukata Mike yaje yasiyo min a pharmacy" ahankali Abba ya shafa kanshi yace "are u sure, likita fa baya duba kanshi saidai wani likita ya dubashi" dariya yay a sangarce ya kalli Baba Suleman yace "Baffa tell Pops to leave me alone" duk dariya sukayi kafin Abba yace "shikenan Boy tunda hakan kakeso baza'a kirashin ba" yasake juyowa ya kalli Mami dahar lokacin take tsaye sai kallon dan nata take yace "jekimi shi fevorite dinshi Firdausi, kinsan bayacin abincin yan aiki" da sauri Big Mummy tace "Alhaji tabarshi ni zanmai" girgiza kai yay yace "a'a Saratu, kinsan Boy bayason spicy food kuma girkin ki is way too spicy for his liking, kibarshi Firdausi ta dafamai" yana fadin haka yajuyo ya kalli Mama jummai wacce itace mai gyara bangaren Mami, yanzu ma tagama aikin tane zata tafi taga Ayaan yadawo ai da sauri ta tsaya dan tasan yau akwai buduri zasu sha kyauta harda na innanaha abunka da alhaji mai kyauta bare yau da dalili, Abba yace "Mama Jummai konawa kikeso ga Sulaimanu nan zai baki, kinajina direba ya daukeki kije kasuwa, inaso ahadamin gagarimin girki sanan dukan ku" ya kalli duka yan aikin yace "harda su securities dukku fada musu su gayyaci koma wasukeso azo anjima bayan sallan magriba akwai walima anan" Yasake kallon Baba sule yace "Sulaimanu inaso kaje office kai order motoci dari, and kai contacting dangote company inaso akawo min trailer daya na buhun shikafa araba ma marasa karfin gari Boy yadawo" duka yan aikin sai murna suke, sake kallon Ayaan din yayi dake kallon mahaifin nashi yana murmushi, ya saki hanunshi kafin ya tsugunna yay sujjadan godema Allah na amsa mai addu'a dakuma bayyanar mai da danshi, aiko dakin yadau kabbara kowa saida yay sujjada ganin Abba yayi banda shi gogan daya tabe baki ashagwabe yace "Pops am tired of standing fa" kama hanunshi Abba yay kaman wani yaro ya sanya dayan hanunshi yakamo kafadarshi ya kwanto da fuskar shi kan shoulder dinshi yana murmushi ya shafa uban gemun daya tarun mai yace "sannu dan albarka, muje kahuta kaji" fita sukai daga dakin Mami da Big Mummy dama kowa na dakin suka bisu da kallo, girgiza kai Mami tayi kafin ta sakko ta karaso inda Big Mummy take tace "barka da rana Hajiya" "barkan mudai" Big Mummy ta amsa mata awulakan ce, murmushi tayi tawuce kitchen kasancewar ta mace mai hakuri ko sau daya bata taba biyema Hajiya Saratu sunyi fadaba koma ko mezatayi.
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *SANGARTATTCE* by* Maman Abd Shakur* Gimbiya 0 5,292 07-19-2019, 10:59 PM
Last Post: GimbiyaUsers browsing this thread: 1 Guest(s)