The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined variable $postsdone - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Trying to access array offset on value of type null - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 12574 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 12574 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 33 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 33 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 65 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 65 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar*
#2
[9/5, 21:17] SHA: ? *Noorul Huda*?

By khaleesat Haiydar?✍?

Hmm where are you blood!? Ke ma ga naki, Allah ya kara hada kawunanmu sweet sis Iqram Mujaheed (Maryam M Bello) proud to have a sister like u.

39.....

Parlor ya tadda Samha yace "Dear ki shirya Mami xata ajiye ki a islamiyyan...." Shiru tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace "Yea, i wanted taking u there by my self but she insisted...." Ta langwabar da kai a hankali tace "Toh" mikewa yyi yace "Yauwa baby, sai ja dawo" tace "Allah ya tsare...." Har ya kai bakin kofa ya juyo yace "Bbu rakiya dear" murmushi tayi ta mike ta bi bayansa suka fita a tare, hada ido suka yi da fatima dake tsaye tsakar compound din ta kasa tafiya, Samha ta kirkiri murmushi tana kallonta tace "Good morning sis fatima" Fatima ta mayar mata da yake tace "Same" daga haka ta nufi gun motar ta da take xuwa makaranta da, Shi dai Abuturrab bai ko kalli inda suke ba har ya isa gun motar da Hajiya ta basa ya juyo yana kallon Samha da ta bi bayansa, jawota yyi gabansa yana kallonta yace "Tohm sweet sai na dawo" murmushi tayi ta gyada masa kai, har xai kai bakinsa nata ko me ya tuna kuma ya bude mota kawai ya shiga tana tsaye ya gama bata wuta snn ya kalleta ya kashe mata ido ya ja motar hade da horn mai gadi ya bude masa gate, Kallon motar fatima kawai Samha take har ita ma ta fita da gidan, ta kusa minti uku tsaye tana kallon gate din gidan snn ta juya da kyar ta koma ciki. Cikin d'an lkci Abuturrab ya saba da doctors din clinic din bayan sun fito daga theatre a ranan, barin da suka ga shima kwararre ne, few nurses da yaga alaman suna da hankali kadai ya sake ma, sai dai fa throughout ranan duk da uban aikin da yyi hankalinsa gaba daya na kan maganganun Maminsa da ya tuna sai gabansa ya fadi, shi dai yasan he can't do without Samha, gashi dai duk rashin jin sa baya tsallake maganan Mahaifiyarsa sai dai by mistake, tunanin yanda xai shawo kanta kawai yake amma bai san taya ba, karfe biyar ya bar clinic bayan ya gama abinda yake, hadari ne sosai garin me hade da iska ya shiga mota ya dau hanyar gida, tsaye yyi da motar bakin gate yana jiran motar da ya tarar gate din ya shiga, cije yatsa yyi cike da takaicin clashing din da suke yawan yi da fitsararriyar nn a cewarsa, gani yyi ta ki tafiya bayan gashi ta danna kan motar compound din, mai gadi dai ya koma yyi xamansa, can kuma dai ta ja motar ta shiga, ya yyi tsaki ya bi bayanta yyi part dinsa, yana gama parking ya fito yana satan kallon motarta ganin irin parking din da tayi, har lkcn iska ake yi sosai ga yayyafin da aka fara, har ya nufi part dinsa ya juyo da sauri jin sound din da yyi kama da na faduwa, kallon mamaki ya shiga yi mata ganinta a kasa, ganin she's gasping for breathe ae bai san lkcn da ya nufeta da sauri ba, yana isa gabanta ya durkusa ya dagota, a dai dai lkcn da Samha da Khadija suka fito daga parlor jin tsayuwar mota, daukarta Abuturrab yyi ya nufi cikin parlor da ita da sauri don an fara ruwan sosai, Khadija ta xaro ido tace "Innalillahi, Her inhaler....." Daga haka ta yi part dinsu da sauri ita ma, ita dai Samha bin su da ido tayi, Abuturrab ya kwantar da ita nan tsakiyar parlon yana kallon khadija da ta shigo yace "Me ake bata?" Khadija ta nufi daki da sauri tace "Inhaler dinta..." Yana rike da ita Khadija ta fito kamar xata yi kuka tace "Ni ban san inda ta ajiye shi ba, ina ta dubawa...." Abuturrab na kallonta yace "Ina inhaler din ki?" Bai ga alamar ta ma san yana yi ba don she is fighting seriously to get her breathe, Abuturrab yace "Inhaler kadai take amfani da, ba a  mata allura ne?" Khadija ta girgixa kai tace "A'a ba ayi, sai magani da inhaler...." Da gudu ta koma daki dubo maganin sai ga ta ta dawo a rikice tace "Ni ban gani ba wllh" Abuturrab ya ciro waya ya mika mata yace "Kira Mami yanxu" daga haka ya daga ta ya xaunar da ita ya cire mata veil din da tayi roll a kai, Ummi na daukar wayar Khadija tace "Ummi Asthman Sister ne ya tashi ban ga inhaler ba" Ummi tace "Subhanallah, where did she keep d inhaler kin duba motar ta, where is she now?" Khadija tace "Uncle ne ya shigo da ita yace in kira ki, let me check d car" Ummi tace "Alryt yi sauri ki duba ba shi wayar" Mika ma Abuturrab wayar tayi, ta fice da sauri duk da ruwan da ake xuwa gun motar yayar tata, Ummi tace "Hello Doctor, wai ba a ga inhalern ta ba koh?" Abuturrab yace "Eh Mami, ba ayi mata allura ne?" Tace "Ban fiye son alluran bane son, but idan ba a ga inhalern ba bari in kira clinic yanxun nn a kawo mata alluran..." Daga haka ta katse wayar, ya ajiye ya jinginar da ita jikin kujera yana kallonta yace "Where is ur inhaler?" Dawowa khadija ta kuma yi tace "Ni dai bn gani ba ka kara kiran Ummi plss" daukar wayar yyi ya kira mum din tasu kuma, tana dagawa tace "Na sa Dr Usman ya taho da allura ynxu, he is on his way, kafin ya xo you tell khadija to check my room gun da nake ajiye drugs ta kawo maka magungunan sai ka cire wanda xa ka bata..." Abuturrab yace "Alryt" ya kalli khadija ya bata sakon ta nufi dakin, tana fitowa da drugs din ya dudduba ya dau wanda ya kamata, ya karbi ruwan da khadija ke mika masa, maganin ya kai ma fatima baki snn ya bata ruwan yana kallonta, daga haka ya jinginar da ita jikin kujera, yana nn durkushe gabanta Khadija kuma na tsayr kansu Dr Usman ya kwankwasa kofar parlor, khadija ta karasa da sauri ta bude kofar ya shigo yana kallon Abuturrab da ya karbi ledan hannunsa yace "Har ynxu ba a ga inhalern ba?" Abuturrab na kokarin hada alluran yace "Yeah!" Yana gama hadawa ya kalli fatima da har lkcn numfashinta bai dawo dai dai ba, mika ma Usman Alluran hannunsa yayi yace "Ga shi kayi mata" Usman yace "Noo kai mata kawai mana" mikewa tsaye Abuturrab yyi ya kama hannun Usman ya saka alluran a ciki yace "Kayi mata doctor, ina xuwa yanxu" daga haka ya nufi kofa, Usman ya durkusa don yi mata alluran, part dinsa ya nufa cikin ruwan, har lkcn Samha na tsaye balcony, Murmushi ya sakar mata ya isa gabanta yace "What r u doing here baby?" Juyawa tayi bata ce komai ba tayi shigewarta ciki, ya d'an yi jim, sai kuma ya bi bayanta, kwance ya sameta parlor ya xauna daga gefenta yace "Abun yar shariya ce kuma dear" ba tare da ta kallesa ba tace "Welcome" ya d'an yi murmushi ya mike yace "Thank you" daga haka ya shiga bedroom, sauya kayan jikinsa yyi xuwa jallabiya ya fito parlor, tana ganinsa ta rufe ido kamar mai bacci ta juya baya, ya nufi inda laptop dinsa ke ajiye a parlon ya dauka ya xauna kan kujera ya bude, bai yi minti goma parlon ba aka danna bell ya mike ya isa kofar ya bude, Dr Usman ne tsaye yace "Doctor nayi mata alluran, da sauki jikin nata yanxu, i want to leave now" Abuturrab yace "Alryt Doctor, let me check on her again, sai gobe" daga haka suka yi sallama Dr Usman ya wuce, tsaye Abuturrab yyi bakin kofar, can ya juya ya kalli Samha da har lkcn bata juyo ba bare ta bude ido, fita yyi parlon ya ja kofar, Cikin ruwan ya shiga xuwa part din Hajiya, Khadija na xaune gefenta ta lullube ta ita kuma tana kwance kan kujera, karasawa yyi parlon yana kallonta, ba karamin tilasta kansa yyi wajen ganin ya bude baki yace mata "How you feeling?" Sae a snn fatima ta kallesa, sai kuma ta dauke kai ta gyada masa kai kawai alamar fyn, shiru yyi kmr me tunanin abinda xai ce kuma, can dai ya kalleta suka hada ido, kasa cewa komai yyi, yyi saurin dauke nasa idon ya kalli Khadija yace "Yaushe Mami xata dawo?" Khadija tace "Tace tana hanya ynxu" yace "Alryt," daga haka ya kuma satan kallon Fatima nn ma suka hada ido ya juya xai fita daga parlon yaji tace "Thank you..."  Ya kalleta bai ce komai ba yyi ficewarsa. Part dinsa ya koma, wnn karan Samha bata parlor, ya shiga daki ya ganta kwance idonta rufe, juyawa yyi ya koma parlor, yyi ta xamansa yana operating laptop har aka kira Magrib, alwala yyi ya fita xuwa masallaci don ruwan ba sosai ake yi ba, ko da ya dawo ci gaba da abinda yake yi yayi, karfe takwas saura aka danna bell ya mike ya bude kofar ya ga Ummi tsaye tace "Son nagode kwarai fah" yace "Mami ae da kin kirani in xo cikin ruwan nn kika fito" tace "It's not heavy ae, ina Samha" yace "Tayi bacci Mami..." Tace "Alryt, Allah bar xumunci, I don't just knw what's wrong with fatima da xata dinga yasar da Inhaler dinta anyhow..." Murmushi yyi yace "Allah ya tsare gaba Mami" tace "Ameen, Allah ya tashe mu lfya" daga haka yyi mata sallama ta juya ta wuce ya koma ciki. Karfe goma ya shiga kitchen bai damu da abincin dake ajiye kitchen din ba kuma yasan na shi ne,ya hada tea kawai ya fito parlor, yana gama sha ya shiga second room, ruwan wanka ya hada a bathroom yyi ya fito yyi shirin bacci yyi kwanciyarsa.

*Haske writers asso*
[9/6, 22:38] SHA: ? *Noorul Huda*?

By khaleesat Haiydar?✍?

Kawayen Asali Maman Shakur and Fiddausi s Dangi Jiddoh na gaisuwa, ku sani ku na raina a ko da yaushe?

40.....

Kasa bacci yayi ya rasa dalili, har karfe sha biyu da rabi idonsa biyu, mikewa xaune yayi daga karshe ya jima a xaunen kafin ya tashi ya nufi kofa ya fita, dakin da take ya karasa, ya kusa minti uku tsaye kafin ya tura kofar a hankali ya shiga, kwance ya sameta cikin bargo, ya karasa gefen gadon ya xauna yana kallonta, can ya sa hannu a hankali ya cire bargon, bai kai ga gama cirewa ba ta rike, kallonta ya tsaya yi can ya fixge gaba daya yace "Are you okay?" Mikewa tayi xata sauka daga kan gadon ya rikota yace "You re going no where har sai kin gaya min d reason for ur sudden change of behavior today, what's wrong with you?" Wani kallo ta watsa masa da yasa shi buda ido, ta kwace hannunta tace "That's because i want to be left alone...." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Look Aliyu, you take me back to my parent immediately, i don't want any of this anymore...." Fixgota yyi yana mata wani irin kallo yace "Amma dai bni nasa ki taho gidana ki same ni ba that very night ryt?" Tsayawa tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, ya sake ta ya mike ya fice daga dakin ta bi sa da ido, har karfe daya tana nn xaune yanda ya bar ta ko motsi ta kasa, da kyar tayi karfin halin mikewa daga karshe, ta dau Hijab ta saka ta nufi kofa ta bude ta fita xuwa parlor, bata yi xaton ganinsa a parlorn ba, kuma suka yi ido hudu don kwance yake kan 3 sitter, ta dauke kai ta nufi kofar parlorn da sauri, mikewa yyi tana ganin haka ta ja kofar taji sa a rufe tana kkrin budewa da makullin jiki ya karaso ya fixgota, wani ihun da ya ji har tsakiyar kan shi ta saki tana son kwace kanta, ya rungumeta ya rufe bakinta da hannunsa yace "Meye hakan kike yi? Are you on ur right senses" Kokuwa ta dinga yi da shi tana son freeing kanta da bakinta a hannunsa amma ta kasa don wani irin rikon da yasa ko motsin kirki bata iya yi yayi mata, gajiya tayi tayi give up, sai a snn wasu hawaye masu xafi suka dinga xubo mata, duk jikinsa yayi sanyi a hankali ya saketa ta sulale nan gabansa ta fashe da wani matsanancin kuka, xubewa yyi gabanta kan gwiwowinsa shi ma, da kyar yayi karfin halin cewa "I didn't mean it Samha, forgive me plss i don't know what came over me...." Mikewa tayi da sauri ta kuma nufar kofar shi ma ya mike tsaye tun kan ta isa ya rikota, duka ta dinga kai masa cikin kuka tana cewa "Ka bude min pls i am going back to my parent, let me out immediately, xan maka ihu idan baka bude min ba" toshe bakinta yayi ganin da gaske ihun xata kuma yi, ya d'aga ta kamar yar shekara biyar yayi bedroom da ita ya direta kan gado yace "Pls you stop all this Samha and listen to me, am vey sorry don Allah kiyi hakuri i mean none of what i said to you....." Bbu irin lallashin da bai yi mata ba amma kamar yana d'a d'a tunxurata, sosai yake jin kukan da take har cikin ransa, wanda hakan yasa bai yi wani tunani ba ya kai bakinsa nata, nan ma dai ba karamin kokuwa tayi da shi ba amma lkci daya yasa ta nutsu, Tun yana yi don lallashi har abun ya fara wuce gona da iri, lkci daya ta fara kokarin kwatar kanta amma ta kasa don Abuturrab yayi nisa, xaro ido tayi da duk karfinta ta kwace bakinta cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri doctor ka sake ni, what's all this" doctor kam bai san tana yi ba, lkci daya ta fashe da kuka cikin rawan murya tace "Na shiga uku, Aliyu pls stop this am begging you, pls stop...." Da kyar murya can kasa taji yace "Pls Samha, you know... You know i... i love you..." Gigicewa tayi tace "Wayyo Mumy na shiga uku, don't Aliyu, i followed you because i trust you. Don't betray my trust for you.... Na yarda da kai...." Sama sama ya dinga jin abinda take cewa wanda hakan yasa jikinsa yayi sanyi amma ya kasa hana kansa, ji yake kamar his life depend on this, he just can't let go of her, cikin wata iriyar murya da ba tasa ba yace "Trust me Samha, auren ki fa xan yi..." Tana kuka sosai tace "Baka aure ni ba tukun doctor, don Allah ka tausaya min ka bari, ka daina plsss" Doctor fa yayi nisa bai jin kira, ba din daukewa da numfashinta ke kkrin yi ba tsabar tsoratar da tayi a lkcn da Samha fa an fita daga lane din  da ake, ba shiri ya dawo Abuturrab dinsa sai dai duk jikinsa ya mutu, lallashin nata ma ya kasa, yana kallo ta mike ta fada bathroom, bayan kusan minti goma yaji karfi ya xo masa yayi karfin halin mikewa ya nufi bathroom din, murda kofar yyi yaji a rufe, ya jingina jiki ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Open pls Samha, kiyi hakuri don Allah, i never meant that too..." K'in budewa tayi kuma bata ce masa komai ba sai dai yana jin sheshshekar kukanta, ya durkushe wajen ya dafe kansa da yayi masa nauyi da ya sani kawai yake a lkcn, what came over him ma yayi haka duk daurewa da shan pills da yake ga yawan tsayuwar dare, ji yayi ya tsani kansa lkci daya, bai ma san me xai kuma ce mata ba, ya fi awa biyu bakin kofar amma taki budewa daga karshe ya mike gwiwa a sake ya karasa kan gado ya xauna, yanda bai yi bacci ba daren nn haka ita ma bata yi ba, ana kiran sallah ya fita ya koma daya bedroom din, wanka yyi ya dauro alwala ya fito yayi raka'atainul fajr sannan ya fita xuwa masallaci har ya dawo Samha bata bude bayin ba, gashi duk keys din har da spare a gu daya suke, ganin gari ya fara haske ya sake komawa dakin nn ma bbu lallashin da bai yi ba amma ta ki cewa komai kuma ta ki bude masa, xaunawa yyi gefen gado yana tunanin abun yi kuma, bakwai da kusan rabi ya mike da kyar jiki a sanyaye ya fita, part din Hajiya ya tafi, ya danna bell mai aiki ta bude, ya amsa gaisuwarsa yace "Hajiya na ciki?" Tace "Ehh tana nn" yace "Kiyi min sallama da ita" juyawa tayi ta koma, bayan kusan minti biyar ya ji muryar Hajiya na cewa "Boy ka shigo mana" ya shafa kai yace "Ba jimawa xan yi bane Mami..." Mami ta karaso bakin kofar ya gaida ta da ladabi ta amsa yace "Ya mai jiki?" Tace "Alhmdllh ga ta cab tana breakfast ne ma" yace "Toh Allah ya sauwake..." Tace "Ameen boy" ya na ci gaba da shafa kansa yace "Mami dama wata yar magana xa mu yi dake if you re free pls" tace "Toh shigo daga ciki mana" Yace "A'a Mami idan ba takura i wanted mu yi shi a can ne" ya nuna balcony dinsa, Mami tace "Alryt... Mu je" daga haka suka nufi balconyn a tare, ta ja kujera ta xauna tace "Toh ya aka yi son?" Xaunawa yyi, ya d'an yi shiru sai kuma yyi kasa da kai yace "A kan Samha ne Mami" Mami ta tattara hankalinta gaba daya tace "What about her boy, laifi tayi maka ne?" Ya girgixa kai yace "Mami ba dauke ki matsayin mahaifiyata da na baro a kano, don haka baxan boye maki komai ba, amma Mami this is a secret between us...." Mami ta gyada kai tace "Ina jin ka?" Ba karamin karfin hali yyi wajen cewa "Mami Samha fa ba matata bace!" Wani kallo Hajiya ta shiga yi masa daga sama har kasa kamar bata fahimce abinda yace ba, ya dafe kansa yace "Yea Mami sai dai kuma ba xaman fasikanci nake yi da ita ba Allah ma ya shaida..." Ita dai Hajiya har lkcj kasa cewa komai tayi da ganinta kasan ba wai mamaki kadan tayi ba, ya girgixa kai da kyar yace "It's a long story Mami... And Samha ba musulma bace Mami, hasali sunanta Samantha ni ne na mayar Samha..." Buda baki Hajiya tayi tana kallonsa da mugun mamaki, ya gyada kai a hankali yace "Ehh Mami" Hajiya tayi karfin halin cewa "Aliyu???" Bai dago ya kalleta ba ya ci gaba a sanyaye yace "Gidan iyayena is just few houses away from her parent's... That is layi daya muke, My father is a soldier My mum a lecture then, Samantha was born nd brought up in a strong Christian home, mahaifiyarta Pastor ce, her dad a politician...."

*Haske writers asso*
[9/9, 19:02] SHA: ? *Noorul Huda*?

By khaleesat Haiydar?✍?

41......

Cikin sanyin murya yace "Duk da layi daya muke da Samantha ni bn taba lura da ita ba sai watarana da daddare....." Nan Abuturrab ya shiga ba Hajiya Hajarah labarin tun daga farkon haduwarsu da ita har ixuwa ranan da suka bar garin kano tare, Hajiya bata samu bakin cewa komai ba da ganinta kasan kanta ya gama daurewa haka ta tsaya kallonsa baki bude, ya ci gaba kansa a kasa har xuwa abinda ya faru jiya bai boye mata komai ba sai dalilin fushin da Samha tayi, Sai a snn Hajiya tace "Ya salam! Haba Aliyu duk ilimin ka ynxu kake xaune da warce ba muharramar ka ba, why boy, ynxu ba don Allah ya tsare jiya ba me kke tunanin xae faru, me yasa ka ajiye koyarwar addinin ka sbda son xuciya?At d first place ma meye na guduwa da yar mutane ka xabi toxarta iyayen ka, wato kai ba indiye koh?" Da damuwa yace "Mami ko da ma ban gudu da ita ba nasan baxan ji dadi gun Abbana ba, everything just happened all of a sudden, sannan ni Mami bn jin xan iya rayuwa da ita, i just can't do without her, and i notice tana da interest for islam, musuluntar ta baxai wani dau lkci ba, kuma ni aurenta nake son yi Mami, ni ko ...." Mami ta mike a fusace tace "Rufe min baki malam, is she still inside d bathroom" kai ya gyada mata tace "Wani dakin?" Yace "By the left..." Shiga parlon tayi tana mamakin karfin hali irin na Aliyu ynxu ashe duk wnn abun yarinyar nn ba matarsa bace, wai ba ma musulma bace, sai dai kuma abinda ya burgeta game da shi yanda yyi iya kkrinsa na ganin bai yi sabon Allah ba cos she can see he is very sincere, tunda gashi a dalilin abinda ya faru jiya yasa ya buda mata cikinsa, tausayin Samha ya shigeta sosai, ita kuma sbda soyayya ta yarda ta yasar da iyayenta ta ajiye addininta ta bi namiji bata san duk yanda Namiji yake to fa shi ba d'an goyo bne, sai dai all the same she is happy for her don da alama conversion dinta xuwa addinin gaskiya baxae yi wahala ba, tana isa dakin ta karasa kofar bayin cikin sanyin murya tace "Samha open the door, it's me" Samha da ke xaune bathroom din har bacci ya fara daukarta ta bude ido da sauri ta mike tsaye, Hajiya ta sake cewa "Ki bude Daughter ni ce" wasu sabbin hawaye ne suka cika idonta da ya tashi don kuka, ta fara kalle kallen bayin ta dau towel ta daura, Hajiya tace "Samha..." Cikin sanyin Murya tace "Toh Ummi" daga haka ta bude kofar amma ta kasa kallon Mami, Hajiya tace "Haba samha sai ki kwana a bayi?" Ita dai bata ce komai ba, Hajiyar da tausayinta ya rufeta sosai tace "Dau kayan ki ki sa kin ji" bbu musu Samha ta dau dogon rigar ta ta saka, Mami ta mika mata Hijab shi ma tasa, snn ta kama hannunta suka fita, har lkcn yana xaune balcony, suna fitowa ta yi ido hudu da shi, ta dauke idonta da sauri, shi kam kasa daina kallonta yyi, wani mugun sonta na fizgarsa ga tausayinta, Mami bata ko kallesa ba tana rike da ita suka  fita balcony din tayi part dinta da ita. Suna shiga parlorn Hajiya Fatima ta bi su da ido don tana xaune parlon, Ita dai Samha bata dago kai ba har Hajiya ta shiga da ita bedroom dinta, tana kallonta tace "Ki shiga kiyi wanka xaki ga sabon toothbrush a bayin ma kin ji" kai Samha ta gyada mata ta nufi bathroom din, bayan minti sha biyar ta fito taga kayanta ajiye bakin gadon da mai da turare, duk a sanyaye ta gama shiryawa ta xauna nan kasan dakin, hawaye ya shiga sakko mata, ta rasa takamaiman abinda ke ranta a lkcn, she know she's regretting following Aliyu, ta fashe da kuka sosai tana tuna furucin mum dinta always na cewa musulmai ae bbu abinda suka iya sai cin amana, does this mean her mum is right, she never expect such from Aliyu, bude kofar dakin aka yi, ta sunkuyar da kanta tana share hawayen idonta, Ummi ta karaso dakin tana kallonta tace "Kuka kuma Samha?" Tashi ki xauna kan gado, Samha ta kasa dagowa har sai da Ummi ta kuma yi mata magana, ta mike jiki ba kwari ta xauna gefen gadon, Ummi tace "Bana son in kara ganin kina kuka, ko baki dauke ni matsayin uwa ba Samha" girgixa kai kawai tayi, Ummi tace "Toh ki daina kukan nan, kar ki wani damu kanki kuma ki saki jikin ki a nan kamar kina gidan ku kin ji" kai kawai ta gyada bata iya ta bude baki ba, Ummi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo mata da breakfast ta ajiye mata tace "Sakko ki karya" ba musu Samha ta sakko kasa, Ummi ta juya ta fita, da kyar Samha ke shan tea din duk damuwa yyi mata yawa, yanxu ae in ta koma gida kilan sai dai wata kuma ba ita ba tasan Mumy will never take it likely with her, or kawai ta wuce kaduna gun aunt dinta, abinda xuciyarta ke raya mata knn kuma taji ta gamsu da hakan, khadija ce ta shigo dakin ta wara ido tace "Ashe kina nan Sis Samha, Ummi tace baki da lafiya, ya jikin?" Murmushi Samha ta kirkira tace "Da sauki...." Khadija ta xauna dakin tace "Ayya, Allah ya sauwake" khadija na fita Samha ta mike ta shiga gyaran Bedroom din duk da bbu wani gyaran da yake bukata, snn ta kwashe plate da cup din da ta karya ta fita da su, Har lkcn fatima na xaune parlor idonta a kan wayar hannunta, tana dago kai suka hada ido da Samha, Samha ta dauke kai ta nufi kitchen, Fatima ta bi ta da ido, tana ajiye kwanukan hannunta ta fito parlor, Dai dai nn Hajiya ta shigo tana kallon Samha tace "Har kin karya?" Kai kawai Samha ta gyada mata, Hajiya tace "Toh mu je daki" bin bayanta Samha tayi suka koma dakin, Hajiya tace "Kiyi xaman ki a nan...." Har yamma Samha na bedroom tare da Khadija dake ta bata labarai, sae dai idan lkcn sllh yayi su tashi su yi, Ummi kuwa tun Sha daya ta fita gun aiki, Samha tayi iya kokarinta na ganin Khadija bata gano tana da damuwa ba don sae biye mata take, sai dai taji haushin kin barin ta ita kadai da Khadijar tayi don her plan was to leave, ko kara ganin Aliyu bata son yi, Fatima ma na gidan throughout sae dai bata ko leka inda suke ba, karfe biyar Khadija tace "Sis Samha mu je ki raka ni kitchen in daura dinner mai aikinmu bata xo ba yau, Sis fatima kuma is still pretending she is not okay" murmushi Samha tayi ta mike ta bi bayanta suka wuce kitchen, Shinkafa Khadija ta daura, Samha kuma ta dau kayan miya tana wankewa, can ta kalli Khadija tace "Rabi'a bata nan ne?" Khadija tace "Tana gidan wani uncle din Ummi tun jiya" Samha bata kuma cewa komai ba, har ta gama gyara kayan miyan, Khadija tace "Yauwa ya ma name din spice din nn da kika sa ranan a stew mai kamshi?" Yar dariya Samha tayi tace "Xaki sa ne ke ma?" Khadija tace "Ehh mana don Ummi tasan nice nayi girkin yau ba sis Fatima ba" Samha tace "Toh bari in dauko maki" Har ta isa bakin kofa sai kuma tayi jim, ta gefen ido ta lura khadija na kallonta kawai sai ta fita, jiki a sanyaye ta nufi nasu part din, ta shiga kitchen da sauri ta dauko spices din gaba daya ta fito dai dai bakin kofar fita ta kusa cin karo da shi, ta koma baya a tsorace, shi kam kallonta kawai yake can yace "Am, am sorry Samha forgive me pls" hade rai tayi ta bi gefensa xata fita ya rikota ta fasa ihu, muryar Ummi suka ji tana cewa "Are you stupid Aliyu, sake ta immediately..." Saketa yyi ta bi ta gefensa da sauri ta fice, Ummi tace "What brought you here?" Abun hannunta ta nuna mata, Ummi tace "Bana son in sake ganin ki part din nn...." Samha bata ce komai ba ta bar wajen, Ummi na masa wani irin kallo ta jefa masa envelope da makullin motar dake hannunta ta bi bayan Samha, lumshe ido yayi kafin ya bude har sun shiga part din Hajiya, duk jikinsa yyi sanyi wani hukunci knn Ummi ke son dauka? Da kyar ya duka ya dau files din da makullin mota ya juya ya fita daga compound din. Karfe takwas yana kwance parlor kiran Ummi ya shigo wayarsa yana dauka tace "Ka taho ka karbi abinci" toh kawai yace ta kashe wayarta ya mike xaune, can dai ya tashi ya fita, Fatima na xaune balcony textbook gabanta alamar karatu take, bai ko kalleta ba ya isa bakin kofa ya kwankwasa, ajiye pen din hannunta tayi tana naxarin what's d meaning of Samha staying a part dinsu tun sassafe, tana son gano me ke faruwa amma tasan Ummi will never tell her, Khadija ce ta bude kofar ya shiga, Ummi na parlon da Samha da Khadija, Samha ta sauke idonta kasa, shi kam idonsa na kanta ya xauna, Ummi tace "Ga abincin ka a dinning...." Karasawa yyi ya dauka ya dawo yace ya gode, Ummi tace "Godiya kuma, Pls gobe da safe kafin ka fita gun aiki xaka je dauko Yusuf a airport boy, though am nt sure ko goben xae taho, in goben ne i will give you a call" Abuturrab yace "Toh Mami..." Daga haka ya kuma kallon Samha da ta dago ita ma don satan kallonsa, suna hada ido tayi saurin dauke nata idon.

*Haske writers asso*

? *Noorul Huda*?

By khaleesat Haiydar?✍?

42.....

Kasa daurewa Fatima tayi misalin karfe tara Samha na daki tare da Khadija ta shiga bedroom din Ummi, xaune ta tadda Ummi idonta sanye da glass tana aiki gaban computer, ta karasa ta xauna tace "Ummi..." Ummi ta juya tana kallonta tace "Ya aka yi?" Tace "Uhm wai da gaske gobe yaya Yusuf din xai iso?" Ummi ta ci gaba da abinda take tace "Ki kirasa ki ji mana" Shiru tayi bata ce komai ba don ba tambayar da ya kawo ta knn ba, Can dai tayi karfin halin cewa "Ummi me Samha take yi a nn ne wai?" Juyawa Ummi ta kuma yi ta kalleta tace "How is her staying here affecting you?" Yake tayi tace "Noo, Ummi it's surprising ne ta bar mijinta ta xo nan, i tot bata da lafiya ne ma" Ummi tace "Toh ba matsalar ki ba ne..." Daga haka Ummi ta ci gaba da abinda take, Fatima ta mike ta fita daga dakin cike da jin haushin abinda ummi tayi mata. Dakin yayanta ta shige tayi kwanciyarta. Da asuba Ummi ta shigo tada khadija tayi sllh, ga mamakinta sai taga sun ma tashi suna sllhn, tsaye tayi bakin kofa tana kallon Samha, a xuciyarta tace "Ikon Allah, amma wnn ai aikin baban giwa take..." Tausayinta sosai taji a ranta ta kuma dau kudirin xata dau time ta tambayeta her view about islam, is she interested, but ga dukkan alamu ma she is interested tunda har ta iya tashi da asuba tayi sllh, juyawa Ummi tayi ta fita. Abuturrab na idar da sllh part din Ummi ya taho don jin ko xae je airport din kuma, "Na kira wayarsa bai je ba, je kayi abinda xaka yi idan ma ya iso sai ya dau taxi kawai" cewar Ummi kenan bayan ta fito, yace "Toh Mami" daga haka ya juya ya bar wajen. Xama Abuturrab yyi a parlor ya rike kai bayan ya koma part dinsa, he never taught hukuncin da Ummi xata dauka kenan, me yasa take kkrin nisanta shi da Samha, sae yaji duk xaman gomben ma ya ishesa, damuwa yyi masa yawa, what happened the day before yesterday was just a mistake, sharrin shaidan. Ya rasa gane whether he is regretting telling her or not, gaba daya yaji bai jin xai ma iya ci gaba da xama garin. Samha na xaune daki tana kallon khadija dake karatun qur'ani sai dai gaba daya hankalinta bai gun, gaba daya tunaninta na gun Abuturrab is she missing him or what, hawaye taji na neman taruwa idonta, why is all this happening to her in just 2 month, kwanciya tayi a hankali ta juya kanta hawaye na sakko mata. A ranan Abuturrab na xaune office ya jinginar da kansa jikin kujera wayarsa dake gabansa ya fara ring, dauka yayi yaga Hajiya Mariya ce ke kiransa, ya lumshe ido ya daga kiran ya kai kunne, cikin sanyin murya yyi mata sallama ta amsa daga daya bangaren, ya gaisheta tace "Abuu ko kira baxaka dinga yi ba, ya kuke?" Yace "Lafiya lau mum, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ina Samhar?" Yace "Tana gida mum" tace "Kai kana ina?" Yace "Ina gun aiki Mum" tace "Aiki kuma, da wani qualification din" yayi murmushi yace "Uhn da na kai na Mumy..." Tace "Toh a ina ka samu aikin..." Bayanin Hajiya Hajarah ya shiga yi mata, Hajiya Mariya tace "Allah sarki, Allah ya mata albarka... Yanxu kuma Abuu haka xaka ci gaba da rayuwa da wacce ba muharramar ka ba..." Yace "Mumy i told Hajiya everything jiya da safe, shine ta dauki Samhar ta komar da ita nata bangaren i really can't tell what she is up to...." Hajiya Mariya tace "Maa sha Allah naji dadin hakan gaskiya, am happy akwai babba tare da ku da xata dinga gaya maku gaskiya tana nuna maku, what she did is the right thing...." Abuturrab yace "But Mum, kar ta raba ni da ita wlh mum baki ji yanda naji da ta mayar da ita bangaren ta ba..." Hajiya Mariya tace "Keep quiet, hakan shine dai dai, ta burge ni wllh... Idan ma conversion din ne gwara ita tayi converting dinta" kasa ce mata komai Abuturrab yayi, tace "Yea, sai mun yi waya" daga haka ta katse wayar ya ajiye ya rike kansa. Samha na kitchen tare da khadija da mai aikinsu misalin karfe biyar saura suka ji fatima dake parlor da wata Billy, wanda da alamar ita ta kirata ta xo tana cewa "Welcome big bro..." Khadija ta ajiye yankan salad din da take yi da sauri ta fice daga kitchen din tana cewa "Oyoyo yayana" tsaye Samha tayi bakin kofa tana kallon yayan nasu dake kkrin cire takalmin kafarsa ganin kanwartasa ya mike ya wara ido ya rungumeta yace "Oyoyo lil sis..." Kankamesa khadija tayi tace "I missed you broo..." Yace "I missed you too, ina Ummina" khadija tace "Bata dawo ba..." Yace "Rabi'a fah?" Tace "Tana gidan Abbu..." Sau daya ya kalli Samha da tayi saurin sunkuyar da kai ya amsa gaisuwar Billy ya wuce bedroom dinsa. Bayan Magrib Samha na kwance daki khadija ta shigo tace "Sis Samha ki fito mu ci abinci..." Samha ta kalleta tace "Ae daxu na ci abinci..." Khadija tace "Dinner fa ba lunch ba" murmushi Samha tayi tace "Toh ni dai na koshi...." Khadija tace "Ummi fa ce tace in kira ki" mikewa Samha tayi ta bi bayanta suka fito parlor, Dai dai lkcn da Abuturrab ya shigo parlorn, kanta a sunkuye ta karaso parlon, shi kam idonsa na kanta har ya shigo, khadija ta gaishesa ya amsa har lkcn idonsa na kan Samha, Fatima kuma idonta na kansa kamar xata cinye sa, ya xauna yace "Ga ni Mami..." Ummi tace "Abinci xaka ci dama, Samha kun gaisa kuwa?" Sai a snn ta dago kai ta kallesa, sai kasa daina kallonsa tayi, can tayi karfin halin cewa "Ina yini..." Ya kasa amsawa, Ummi tace "Ba ku ma gaisa da Yusuf ba Boy" daga haka ta kwalo ma Yusuf kira, Khadija tace "Ae bai shigo daga masallaci ba..." Bata rufe baki ba Yusuf ya shigo parlon da sallama, Abuturrab ya juya ya kallesa, karasowa yyi parlon yace "Ummi am jet hungry...". Ummi tace "Ga abinci can dinning ai, bayan tafiyar ka Allah ya hada ni da wani son wanda ya take ka a rashin ji ma, ka gansa yana nn yana ban wahala shi ma..." Sosai ta ba Abuturrab dariya, khadija ta fashe da dariya ita ma, Samha kam murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Yusuf ya wara ido yana kallon Abuturrab yace "Really Ummi..." Daga haka ya mika masa hannu murmushi dauke fuskarsa suka gaisa yace "I am barrister Yusuf Ahmad...." Abuturrab ya mayar masa da murmushin yace "I am Dr Aliyu Ahmad...." Yusuf yace "It's nyc meeting you..." Kai Abuturrab ya gyada masa har lkcn murmushi fuskarsa yace "Same..." Ummi na kallon Samha tace "Kun gaisa da shi dota?" Sai a snn Samha ta kallesa shima ya juya yana kallonta, a hankali tace "Ina yini?"

*Haske writers asso*
Reply


Messages In This Thread
*Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* - by Gimbiya - 08-31-2018, 02:49 PM
RE: *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* - by Gimbiya - 09-10-2018, 08:20 PM

Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  ⚡Heedayah⚡By Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 14,580 07-08-2021, 05:08 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 11,459 08-18-2018, 01:15 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 24,858 08-10-2018, 01:18 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 20,044 08-10-2018, 12:48 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 24,871 08-05-2018, 11:27 AM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat haiydar Gimbiya 0 53,300 08-03-2018, 05:26 AM
Last Post: Gimbiya
  *CAPTAIN_AHMAD JUNAID* By Khaleesat Haiydar_ ✍? Gimbiya 0 40,819 11-16-2017, 12:51 PM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)