08-31-2018, 02:49 PM
? *Noorul Huda*?
By Khaleesat Haiydar?✍?
32.....
Samantha na shigowa bayan tayi wanka bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi gun kayan da ya siya ta durkusa, can ta kallesa taga kallonta yake ta bata fuska tace "Kaya xan sa?" Ya wara ido yace "Na rike ki? Ki sa mana" tace "Toh ka fita" murmushi yayi yace "In fita gun Binta ki kuma daure min fuska" daukar abinda xata dauka tayi ta nufi kofa ya fixgota tace "Wayyo ni ka kyaleni kaya na xan je in sa a waje..." Ya wara ido yace "Toh me xa ki boye min da ban sani ba jikin ki!" Ta yi masa wani kallo tace "Ae dai na wasu ka sani ba nawa ba malam" Dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "See you, ke nakin ma special sani xan masa, sanin da bbu wanda xai kara masu har abada.... Only me" kwace kanta take son yi ya ki saketa, ta boye fuskarta jikinsa kamar xata yi kuka tace "Bana son irin haka Doctor" yana dariya yace "Toh na daina baby, but a nan xa ki sa kayan ki" bbu yanda ta iya haka ta shirya a dakin, and he pretend he's not looking at her, tana gama shiryawa ya xuba mata kunu ya mika mata ta sha kadan ta ajiye kosan ma bata ci ba, yana kallonta yace "Xa mu tafi yanxu!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, can ta mike ta fara gyaran dakin, ya taimaka mata suka gama, sha daya suka fito xa su wuce, Hansai ta fito tana masu Allah ya tsare hanya tana cewa Allah sa ba shikenan an gama xumuncin ba, Abuturrab yayi dariya yace "In shaa Allah baxa mu mance ku ba Baaba wataran xa mu xo, dubu uku ya bata ta dinga godiya har da hawayenta, Abuturrab ya kalli Binta dake xaune nesa da su yace " Babu Sallama Fatima" kallonsu tayi yaga hawaye cike idonta, Hansai tace "Kaji shashanci to tashi ki rakasu mana" Samantha tayi ma Hansai sallama sannan ta fita, Ya karasa kusa da Binta ya durkusa yace "Nace maki xamu xo wataran fa..." Bata ce komai ba sae share hawayen idonta da take yace "Toh tashi ki raka mu" ba musu ta mike ta dau sandar ta na kiwo da nonon da ta tatsar masu yana gaba tana biye da shi a baya suka fita. Karasawa yayi ya kamo hannun Samantha yace "Baku yi sallama da Binta ba" ta kalli Binta ta gefen ido tace "Mun tafi Allah ya saka da alkhairi" kai kawai Binta ta gyada mata, daga haka yace "Mu je to ki raka mu inda xa mu samu Babur" gaba ta shiga suna biye da ita a baya, sun yi nisa sosai sai ga wata mota na tahowa a bayansu, Abuturrab yace "Wannan fa" Binta ta kalli Motar tace "Motar D'an lado ne, shi daya ne mai mota a rigar nan a birni yake aiki, da ka tsayar da shi ka ji inda xa shi ko?" Abuturrab ya tsayar da motar kamar yanda tace ae ko ya tsaya ya sauke glass, Abuturrab ya gaida sa mutumin da xai iya kaiwa arba'in ya amsa yana kallonsa, Abuturrab yace "Don Allah idan ba damuwa ina ka nufa?" Mutumin yace "Gombe xa ni...." Abuturrab ya d'an yi shiru, sae kuma yace "Toh mu ma can muka yi, xa a taimaka?" Mutumin yace "Ba matsala ku shigo" Abuturrab ya bude ma Samantha baya ta shiga ya rufe, ya kalli Binta da wasu hawayen suka cika idonta ya ciro dubu biyu duk da ya so bata fiye da haka ya damka mata a hannunta yace "Na maki alkawarin wataran xa mu dawo" da kyar ta yarda ya sa mata a hannunta ta mika masa nonon dake a leda ya karba yayi godiya sannan ya juya ya shiga front seat ya d'aga mata hannu ta juya da sauri ta bar wajen, D'an lado ya ja motarsa yace "Amma ba nn rigar kuke ba koh?" Abuturrab yace "Eh mu baki ne" D'an lado yace "Da alama kam, toh Allah ya sauke mu lafiya" daga haka ya maida hankalinsa kan tukin da yake da gani dae kasan hannunsa bai gama fadawa ba, ta madubi Abuturrab ya dinga kallon Samantha ganin yanda ta wani turo baki, dariya yake son yi amma ya dake, har suka isa gombe bayan tafiyar awa biyu da rabi bbu wanda yace komai cikinsu, Abuturrab sai kallon garin gombe yake yana tunanin to ina xa su, bbu wanda ya sani a gombe infact bai ma taba xuwa ba, D'an lado ya katse masa tunanin da yake yace "ina xa ku sauka kenan?" Abuturrab ya kallesa yace "Ko nan ne ka sauke mu" D'an lado yayi parking Abuturrab ya bude motar ya fita, ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, ya karbi ledan kayan dake hannunta yayi ma D'an lado godiya ya ja motarsa ya wuce, kalle kallen wajen Abuturrab ya shiga yi, yana neman bankin da yake ajiya, yaga duka ukun a area din, yasan first bank da Gtb ba dai layi ba, hakan yasa yayi deciding ya shiga unity, ya kalle Samantha yace "xan shiga bank, sai ki jira ni waje or we go in 2geda" ta girgixa masa kai kawai tayi xamanta gaban bank din, shi kuma ya shiga ciki, direct ya tafi gun CC, bae wani jima ba aka xo kansa, yace yana son a duba masa ko nawa ne account dinsa, daga sama har kasa matar ke kallonsa, can tace "ATM din waje me yake yi, ko wayar ka fa?" Yace "Akwai layi sosai, waya kuma bani da, idan xa ki taimaka ki taimaka...." Da kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, sai kuma tace "Fado account number" ya fada tayi danne dannenta snn ta kallesa ta kalli hotonsa dake jikin computer tace "Dubu dari shidda da ashirin" ya xauna yace "Good, na gode kwarai, ana sayar da withdrawal slip a nan?" Ta nuna masa gun da xai siya snn ta kira wani customer, yana xuwa ya dauka ya ciro dubu daya da aka ce ya bayar ya mika, ya ari pen ya cike slip din, dubu dari biyu ya saka yayi sign ya nufi gun Cashier, su ma sai da yayi masu jan ido wai wani yaje atm they re busy, yace "Haba wani atm xan je, ba fa dubu hamsin xan cire ba malam, kawai inje in bata ma masu cire dubu biyar lkci, awa nawa xan dauka ina cire dubu dari biyu? Plss answer me coz i wanna get out of here" Ba yanda suka iya haka suka karba bayan minutes din da basu wuce sha biyar ba suka basa kudin sa, nan ya roki alfarmar jaka aka basa ya xuba kudin yayi ficewarsa, ya isa gun Samantha yace "Am sorry Dear, tashi mu je" ta mike ya karbi ledan hannunta suka nufi titi, yana kallonta yace "Dear hotel fa xa mu je kafin mu samo solution" ta kallesa tace "Hotel?" Shiru yayi yana kallonta, ta dauke kanta, ya sauke ajiyar xuciya yace "Just for today dear.... Kinga bamu san kowa a gombe ba, it's my 1st time here" jin bata ce komai ba ya tsayar da mai adaidaita yace "Hotel mafi kusa xaka kai mu" sae da ya tsaya ta shiga sannan ya shiga, ba laifi hotel din na da kyau, ya biya kudin kwana daya dubu ashirin da biyar a reception aka basa makulli da room number, babban daki ne sosai da toilet a ciki, ya kalli samantha da har lkcn ta ki cewa komai ya xauna bakin gado bayan ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta yace 'You followed me without trusting me kenan Samha..." Bata bari sun hada ido ba ta karaso dakin a sanyaye ta xauna can karshen gado, girgixa kai yayi ya mike ya bude jakar dake dauke da kudi ya cire dubu dari, ya sa a aljihu yace "Am coming back right away, me xa ki ci?" Cikin sanyin murya tace "Anything" ya juya ya fita ya kulle dakin, tagumi tayi tana tunanin anya did she made the right decision following him and neglecting her dear parent, hawaye ya cika idonta ta fada kan gadon ta fashe da kuka, Why is all this happening to her within just 2 months, she know God will never forgive her for doing this to her parent, but she love him and they will never allow her to be with him, tayi kukanta me isarta ta mike ta dau soap da sponge, toothpaste da sponge ta shiga bayi dake dakin, wanka tayi ta fito ta shirya tayi kwanciyarta nan da nan bacci ya dauketa, bayan azahar Abuturrab ya dawo, ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta, bai tada ta ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya xo ya gabatar da sllhn Zuhur, ya jima xaune yana addu'a daga bisanni ya mike ya shiga bayi yayi wanka ya fito ya shirya cikin daya daga cikin kananun kayan da ya siyo, ya bude fried rice din da ya siyo masu da drinks ya ci wanda xae ci ya ajiye sauran, kwalin karamar waya ya dauka ya bude ya ciro wayar ya sa sabon sim din da ya siyo ya kunna wayar, ya loda airtime yayi dialing number Hajiya Mariya gabansa na faduwa a xuciyarsa kuwa addu'a yake Allah yasa ita kadai ce a gun, bugu daya biyu ta d'aga, ya shafa kai a hankali yace "Mumy!" Hajiya Mariya dake xaune daki tare da Mami da frnds dinta biyu, ta saci kallon Mumy ganin kallonta take tace "Helloo!" Abuturrab yace "Ina ji Mumy ina yini...." Hello... Hello... Abinda ta dinga cewa kenan can tayi tsaki ta katse, Hajiya Maimuna tace "Network koh?" Hajiya Mariya tace "Ae kuwa...." Hajiya salaha tace "Toh da ki fita waje...." Hajiya Mariya ta tabe baki tace "Kila kiga ya dawo kuma" Abuturrab da sharp thinking yana jin reaction dinta yasan ba ita kadai bace a gun don haka bae sake kira ba, Mikewa Hajiya Mariya tayi tace "Bari dai ban san ko masu bani kudi bne bari inje waje" daga haka ta fita, bata ko kalli Abba dake parlor da abokansa ba tayi ficewarta waje, Abba ya bi ta da kallo, can ya girgixa kai yace "Wannan Mariyar ma ban yrda da ita ba bakinsu daya da Aliyu, ba abun mamaki bne ma tasan inda yake!" Col Usman na girgixa kai yace "ban taba ganin mai taurin kai da tsaurin ido irin Aliyu ba...." Abba yace "Duk ya kuskura ya shigo hannuna wllh sae bullet ya kare a kafafuwansa..." Har kofar gida Hajiya Mariya ta fita sanin halin mijin yayarta, tana fita ta kira number da sauri, Aliyu naganin kiranta ya daga, tace "Aliyu!!" Ya buda ido yace "Mumy..." Tace "Kuna ina Aliyu?" Shiru yayi, tace "Ohh ni din ce yanxu kuma baxa ka gaya ma inda kake ba" yace "Ke kina ina Mumy" ta hade rai tace "Ina tambayarka kana tambayata..." Ya sauke ajiyar xuciya yace "Kiyi hakuri Mumy, but don't say anything to anybody plss...." A fusace tace "Uwarka! ni kake gaya ma haka da can ban ce komai ba sae yanxu" bae san lkcn da yayi dariya ba yace "Yi hakuri Mumy, ina Gombe!" Ta xaro ido tace "Gombe kuma Abuu, wa ka sani a can?" Ya girgixa kai yace "Ba kowa wlh..." Da damuwa tace "Yarinyar fa?" Ya kalli Samantha dake ta bacci yace "Ga ta Mumy, she's sleeping" Hajiya Mariya tace "Kaji tsoron Allah Aliyu, kada kayi using wnn advantage din a kan baiwar Allah don tana sonka, kar ka manta ba fa matar ka bace, don't use her....." A sanyaye yace "Mumy baki yadda da Aliyun ki bane kuma, kema kin san ba hali na bane" Hajiya Mariya tace "No son! Kasan sha'anin rayuwa, bbu abinda shaidan baxae iya yi ba...." Sosai jikinsa yayi sanyi yace "In'sha Allah Mumy xan kiyaye.... Mami fa?"
*Haske writers asso*
? *Noorul Huda*?
By khaleesat Haiydar?✍?
33....
Hajiya Mariya tace "She's inside" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Abba fa" tace "Yana nan.... But you re in trouble in har ka shigo hannunsa" Aliyu yayi murmushi yace "Na sani" da damuwa tace "Ka dai kula Aliyu tausayin yarinyar nake, tunda har ta guji iyayenta sbda kai, jan ra'ayinta xuwa musulunci baxai yi wahala ba" Yace "Hakane Mum, dama am planing of marrying her soon don ban son in cuceta, i don't want her to regret trusting me, idan nayi haka komai xae fi zuwa da sauki" Hajiya Mariya tace "Anya, naga kamar ya fi ka jira sae ta amshi musulunci, kar ta ga kamar kana using advantage din auren ne..." Bude gate ta ji anyi da sauri tace "Za mu yi waya Aliyu, don't call again xan dinga kiran ka..." Daga haka ta katse wayar, Abba ta gani bakin gate waya kare a kunnensa ya rako abokansa xa su wuce, tayi dialing din number wata da xata bata kudi suka yi magana snn ta juya ta nufi gate din ya bata hanya tayi wucewarta, bin ta yayi da kallo har ta shiga cikin gida, ya juya ya koma ciki shi ma bayan abokan sun shiga mota, ya shiga part dinsa ya kira Mami, bbu bata lkci Mami ta iso, yana tsaye bakin window rungume da hannunsa (Inda Aliyu ya gado rungume hannu knn, lol" ya juyo yana kallonta yace "Hajarah! i won't take it likely with ur sister idan naga da sa hannunta a abubuwan nan da Aliyu yake, xan ajiye cewar yar uwarki ce a hukuntata yanda ya kamata...." Mami tace "Ban yi mamaki ba... You can do more than that, yanxu kuma ka bar xargina ka koma xargin yar uwata" ya daga kafada yace "Ni dae na gaya maki" juyawa tayi ta fice daga dakin, dakin su Ramla ta shiga ta ci kukanta Ramla na lallashinta kafin ta fita ta koma dakinta, Hajiya Mariya na ganin Abba ya kira Mami dama ta yi saving din number Aliyu da wani suna daban tayi deleting dinsa daga call log, ko da Mami ta shigo dakin Hajiya Mariya na bathroom, ta dau wayarta ta fita, kiranta na karshe ta kura ma number ido, can tayi dialing taji muryar mace, ta dudduba dai bata ga alamar komai ba ta koma daki, Hajiya Mariya bata tambayeta dalilin daukan wayarta ba sae harkan gabanta take. Tunani Abuturrab ya dinga yi ko dai gida xae kama masu nan gombe ne, duk ya rasa takamaiman solution, kallonta yayi ganin tana juye juye kan gado, can ta mike xaune yace "Cikin ya fara koh?" Ta gyada masa kai, ya mike ya dauko mata abinci yace "Sauko ki ci in maki allura" ba musu ta sauko ya bude mata abincin ta fara ci, alluran ya hada ya ajiye yana jiran ta gama, bata wani ci da yawa ba ta mike yace "Sauran fa" da kyar tace "Anjima xan ci" daga haka ta kwanta ya mike ya karasa kusa da ita yayi mata alluran, Finger dinta ya kura ma ido ganin har lkcn xoben da ya sa mata na nan, ya kama hannunta a hankali yace "Samha!" Dago kai tayi ta kallesa, ya sakar mata murmushi ya kai lips dinsa kan hannun cikin sanyin murya yace "I will never let you down dear, i will be ur hero, i will be ur everything...." Hawaye ya cika idonta ya dago ta ya rungumeta, ta fara kuka a hankali, jin tayi shiru ya dago kanta a hankali ya ga idonta a lumshe, kwantar da ita yayi ya mike ya nufi window yana tunanin next action din da xae dauka, can ya dau kudi ya fita, wani me taxi ya tsayar bayan tsayuwar kusan minti sha biyar a bakin titi duk yana duba responsible cab man da xae tsayar su yi magana, yana kallon mutumin yace "Pls ina d'an tambaya ne" cab man din yace "Allah yasa na sani" Abuturrab na shafa beard dinsa yace "Kasan inda xan samu agent... I mean their office, anywhere around?" Mutumin yace "Wae na gida?" Abuturrab yace "Yes!" Mutumin yace "Wanda na sani da nisa daga nan, sae dai..." Abuturrab yace "No mu je kawai ka kai ni" daga haka ya shiga mutumin ya ja taxi din. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso office din wasu agent, Abuturrab ya fito yayi masa godiya ya basa dari biyar ya shiga office din, ba shi ya fito ba sae kusan karfe shidda bayan an basa tabbacin nan da xuwa gobe xa a karbar masa gida. Ko da ya dawo lodge dinsu tana bathroom tana wanka, ba a dau lkci ba ta fito daure da towel, tana ganinsa ta tsaya nan bakin kofa, yace "Naga alamar ba kya gajiya da wanka yarinyar nan...." Murmushi tayi bata ce komai ba ya mike xae shiga yayi alwala ta durkusa da sauri tace "Nooo" xaro ido yayi yace "Ina ruwana da ke?" Murmushi yayi ya shiga toilet din, ta mike da sauri. Ko kafin ya fito har ta gama shiryawa, yana kallonta yace "Xan je mosque, will be right back" ta gyada masa kai ya fita, sae bayan Magrib ya dawo dakin, ya ganta xaune shiru da alamar tunani take, ya karasa kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Sorry Dear, na jira anyi magrib ne" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, ya xauna ya bude mata ledan fruits din yana kallonta, Apple ta dauka ta kai baki a hankali, shi ma ya dauka ya kai daya baki, wayarsa dake kan gado ya fara ring, ya dauka yana kallon screen din yaga Hajiya Mariya ce, ya daga ya kai kunne yace "Hello Mum!" Tace "Aliyu where is she?" Kallon Samantha yayi ya mika mata wayar yace "My mum!" Ta sa hannu ta karba ta kai kunne, Hajiya Mariya tace "Ya kk Samha?" Samantha tace "Lafiya Mumy ina yini?" tace "Lafiya lau, kiyi hakuri kin ji, Allah na tare da ku, kar ki sama kanki damuwa...." Kai kawae Samantha ke gyada mata kamar tana ganinta.
*Haske writers asso*
? *Noorul Huda*?
By khaleesat Haiydar?✍?
34.....
Mikewa tayi a hankali ba tare da ta kallesa ba ta dau rigar baccin ta shiga bathroom, ba a dau lkci ba ta fito, kallo daya yyi mata ya dauke kai, ta nufi kan gado a hankali ta kwanta ta juya masa baya, bayan kusan minti goma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya shiga bayi, ko da ya fito kashe tvn dake aiki yyi ya kashe wutan dakin ya karasa gado ya kwanta, a hankali ya birgina inda take, cikin sanyin murya tace "Doctor..." Yace "Samha...." Bata ce komai ba ya juyo da ita ya kwantar da ita kan faffadan kirjinsa yace "Sleep tight love, am with you" ta lumshe ido tayi lamo jikinsa, a haka har bacci ya dauketa, a hankali ya kwantar da ita ya mike ya koma kujerar dake dakin yayi kwanciyarsa amma ya kasa bacci sae juye juye yake, can dae ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, sae kusan karfe uku da rabi ya samu yayi bacci, da asuba a masallacin dake cikin Hotel din ya fita yyi sllh sae da gari ya waye ya shigo masu dakin da breakfast, har ta shirya ya sameta, yana kallonta da mamaki yace "Ina fita kika tashi amma koh?" Kai kawai ta gyada masa, yayi murmushi yace "Alryt xo kiyi break kafin in shirya" daga haka ya shiga bathroom, ko da ya fito har ta gama cin abinda xata ci, yace "Are you sure kin koshi?" Ta gyada masa kai, shiryawa yayi ya ci chip da egg din kadan ya mike yace "Bacci nake ji Samha, let me sleep small" murmushi tayi ta mike xata gyara masa gadon yace "Noo don't worry dear...." Daga haka yayi kwanciyarsa, ta koma ta xauna ta rufe sauran breakfast din, yana kwanciya bacci ya daukesa, ita dai tana xaune idonta a kan tv, sae dae ko kadan ba sanin kan film din da ake tayi ba, tayi nisa a tunanin da take, Abbanta kawai take tunani wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, why did she accept to leave her family because of Aliyu, hade kanta da kujera tayi hawaye na sakko mata sae a snn take jin bata kyauta ba, tayi kukanta mai isarta daga nan ita ma bacci ya dauketa don yanda bai yi wani bacci ba haka ita ma bata jiya ba daren jiya duk tana kallonsa yana sllh, sai kusan goma da wani abu Abuturrab ya tashi, ganin yanda ta kife kai ya mike da sauri ya isa gabanta ya dafa ta yace "Samha" dagowa tayi da sauri tana kallonsa, kallon idonta ya dinga yi, da damuwa yace "Kuka kika yi?" Ta sunkuyar da kanta ya dago ta yace "Samha you re regretting everything koh?" Ta fashe da kuka tana girgixa masa kai, duk ya rikice yace "No plss samha, kar ki min kuka don Allah, naji xan maida ki gida...." Da sauri ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Am not regretting" yace "Toh me yasa kike kuka" goge hawayenta ta shiga yi cikin sanyin murya tace "Its just.... We re in trouble" ya lumshe ido ya kamo hannunta yace "Allah na tare da mu Samha, kar ki damu kin ji" sunkuyar da kanta tayi, yace "Tashi ki raka ni!" Ba musu ta mike ya kashe kayan kallon yace "Mu je" kofa ta nufa ya bi bayanta, suka fita ya kulle dakin, gun agents din jiya ya tafi, suna isa daya daga agent din yace su je ya ga gidan ko yayi masa, a motar agent din suka tafi, gida ne babba hadadde mai flats biyu, gidan na dauke da dakuna uku manya, Abuturrab ya kalli Samha yace "You like it?" Sunkuyar da kai tayi, yayi murmushi yace "Alryt, yallabai gidan yayi, thanks much" bbu bata lkci Abuturrab ya biya komai na gidan kusan 450k, da yamma bayan sun dawo hotel din yace "Xuwa jibi sae mu koma can koh dear?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru?" Murmushi tayi bata ce komai ba. Washegari Abuturrab shi kadae ya fita ya bar ta tana bacci don xuwa can gidan ya ga abubuwan da ya kamata ya xuba, a ranan yayi furnishing gidan gaba daya, har food stuffs sae da ya siya, ya kashe kudi ba na wasa ba, da yamma ya koma hotel, Wanka ya sameta tana yi, yyi kwanciyarsa don ya gaji, washegari da ya kasance alhamis misalin sha daya suka tafi can gidan, nan ya fara tunanin anya xae yi ynda Hajiya Mariya tace masa kuwa, bai jin xae iya xama gida daya da ita bayan ba muharramar sa bace, idan shaidan bai ci galaba kansa yanxu ba yasan ko a jima ko a dade akwai ranan da abinda yake gudu xae iya faruwa, don yanxun ma he's just fighting his self from inside, kwanciyarsa yyi a parlor yana tunanin next step din da xae dauka, ana kiran Azahar ya mike ya shiga toilet dake nn parlor ya daura alwala ya fita xuwa masallaci, ko da ya dawo a kitchen ya sameta ta daura girki, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Weldone dear..." Murmushi kawae tayi ta ci gaba da wanke shinkafar da take yi, ya juya ya fita xuwa balcony yayi xamansa, wata dattijuwa da baxata wuce 50 ba ce ta fito daga daya flat din idonta sanye da medicated ta rike jaka ta nufi parking space dake part din nasa ta bude daya daga motocin dake wajen ta shiga ta tada, horn tayi bayan ta fito compound din, Abuturrab ya kuma kallon motar ya dauke kai don yasan lkcn da yake dawowa daga masallaci lkcn mai gadin ya tafi, tayi horn yayi sau uku, can Abuturrab ya mike ya isa gate din ya bude mata, sauke glass tayi ta karasa gate din da motar tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace "Nagode kwarai..." Ya dukar da kai yace "Ina yini?" Tace "Lafiya lau, kai ne new tenant din Apartment din can kenan?" Kai ya gyada mata yace "Nine..." Tace "Maa sha Allah, you re welcome, tare da mai dakin ka koh?" Ya d'an yi jim sai kuma da sauri yace "Ehhh" tace "To sannun ku da xuwa, ni ce occupant din flat din can with my 3 kidz... Hope xa mu dinga ba makwabtaka hakkin sa" murmushi yayi sosai yace "In shaa Allah" ita ma tayi murmushin tace "Maa sha Allah, it's nyc meeting you, na fita aiki sae na dawo" yace "Toh Allah ya tsare" daga haka ta ja motarta ta fita ya rufe gate din, haka kawai yaji matar ta burgesa sae yake ganinta kamar Maminsa, yana murmushi ya koma balcony yayi xaman sa. Shinkafa da miya Samha ta girka tana gamawa ta fito ta gansa har lkcn yana balcony, ta jingina jikin kofa tace "Na gama" ya kalleta ya wara ido yace "Weldone sweetheart" murmushi tayi ta juya ta koma ciki ya mike ya bi bayanta, a tare yasa ta xuba masu abincin don yana son ta ci da yawa, ai ko haka yayi ta forcing dinta har suka cinye abincin, ya tagumi yace "But wa ya koya mamaki girki haka dear?" Tace "Uhm My mum" ya lumshe ido yace "You are a very good cook" a hankali tace "Thank you..." Yace "No thanks baby, bari in je masallaci it almost time for salat" tace "Toh" ya mike ya shiga toilet ya daura alwala ya fita, ta kwashe plates din don xuwa kitchen ta wanke.Bayan magrib yana dawowa daga masallaci matar daxu na shigowa, tsayawa yyi har tayi parking ta fito kafin tace komai ya gaisheta, da fara'a ta amsa tace "Mai dakin naka na ciki in shiga mu gaisa mu san juna..." Yace "Da ki bari xamu shigo yanxu tun da daga aiki kike ai" tace "Toh shknn ina jira" daga haka ta nufi bangarenta. Abuturrab ya juya ya shiga cikin gida, bedroom ya sameta yace "Samha, taso mu gaisa da new neighbor dinmu" ta kallesa tace "Do we need to?" Yace "Yess dear!" Mikewa tayi yace "Ki sa Hijab..." Ba musu ta dau daya daga sabbin Hijabs din da ya siya mata ta saka snn suka fita yana gaba tana biye da shi a baya, kararrawa ya danna ba a dau lkci ba wata yarinya da baxata wuce Samantha ba ta bude kofar, kallonsu ta shiga yi, Abuturrab yace "Hello, mum dinku na ciki koh?" Ta basu hanya tace "Ehh, welcome" Abuturrab ya shiga parlon Samha ta bi bayansa, sosai parlon ya hadu da gani dai kasan Naira ta xauna, xama yayi kan kujera ya nuna ma Samha gefensa ta xauna, yarinyar ta wuce ciki sae ga ta tafito tare da Mum din tasu, da fara'arta ta karaso parlon tana kallon Samha tace "Sannunku da xuwa" Samha ta sauke kai kasa ta gaisheta, ta amsa mata da murmushi tace "It's nyc meeting you... Ya sunan ki?" Satan kallonsa Samha tayi, yana murmushi yace "Samha!" matar tayi murmushi ita ma tace "toh kai fa?" Yana shafa kai yace "Aliyu...." Ta buda ido tace "Maa sha Allah ashe Abbana ne, amma sabon aure kuka yi koh?" Yar dariya yayi yace "Ehh haka ne" tace "Ae naga alama, Allah ya kawo Zuri'a dayyaba, ni sunana Hajarah...." Wara ido yayi yace "Mum dita knn..." Tace "Kai haba, shknn na samu d'a kuma babana..." Yayi dariya tace "Allah kuwa, muna xaune da kidz dina uku a nan, babban son dina Muhd na Uk, sai kanwarsa Maryam da ke Cairo tana aure, snn Fatima da Khadija da autata Rabi'ah, Ba mu yi shekara a garin Gombe ba don da a Abuja muke, yanxu haka ma Mai gidan na can sae dai yaxo week ends, am running my late dad's clinic dake nan ne shi yasa...." Abuturrab ya kalleta yana murmushi yace "Maa sha Allah Mami, Allah yayi jagora" tace "Ameen, amma a gombe ku ke?" Ya girgixa kai yace "A'a kano muke..." Tace "Ikon Allah, toh Allah dai ya bada zaman lafiya, kaga bata da kowa nn dont make her feel lonely ka dinga kyautata mata a ko da yaushe Abbana" yace "In shaa Allah Mami nagode" Hajiya Hajarah ta kalli Fatima dake xaune tana dannan waya tace "Ko ruwa baxa ki kawo masu ba Teemah" Abuturrab yace "Noo Mami Alhmdllh, xamu koma ne ynxu" Hajiya Hajarah tace "Toh shknn Boy, na gode kwarai" yar dariya yyi ya mike ya kuma yi mata sallama haka ma Samha snn suka fita. Sae da suka koma part dinsu yana kallonta yace "You like her?" Murmushi tayi ta xauna bata ce komai ba, da damuwa yace "Why ba kya son magana Samha, you re just nt ur self" ta wara ido tace "Ba komai fa, is just change of environment" yace "U will like it soon dear, nt when am with you" murmushin dae tayi, ya gyada mata kai snn ya shiga daki. A parlor yyi isha sbda hadarin da ya hadu ga iska ana yi, ita dai tana xaune parlon sae kallonsa take har ya idar, yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Ko kema kina son ki iya sllhn ne?" Tace "Uhmm" yace "Yeah dear sae in koya maki it's nothing ae" yar dariya tayi yayi shiru yana kallon fararen hakoranta tace "Wa yace maka ban iya ba?" Yace "A ina kika iya?" Tace "Uhm, na xauna gun kanwar Abbana Anty Aisha a kaduna, during my jss can nake xuwa yin long holiday, idan su Mumy xa su Jerusalem can ake kai ni, tare take hada ni da yaranta mu je islamiyya, in dai xa ayi sllh nima sae nayi a gidan, har na xo na saba idan na dawo gida sai in ta yin irin abubuwan islam shknn Mumy ta hana Abba ya kai ni kaduna kuma, at that time ina jss3, har yau kuma ban sake xuwa ba" Abuturrab dake ta kallonta ko kiftawa bbu yace "Yanxu kin iya alwala knn?" Tace "Uhm har da sllh ma, kasan suran da muke lkcn a islamiyyar da muke xuwa?" Da sauri yace "A'a" tace "Mulk" ya lumshe ido yace "Kuma kin iya?" Dariya tayi tace "May be xan iya yi da qur'an because i know the arabic letters very well" kallonta kawai yake can yyi murmushi yace "Gobe xa ki min in ji" mikewa tayi tace "Xan yi bacci...." Yace "Ohk dear ki rufe windows sbda ruwa" kai ta gyada masa ta nufi daki tana adduar Allah yasa kar ayi ruwan sbda tsoron tsawa da take. Washegari da safe wajajen karfe tara tana daki tana bacci Abuturrab kuma na xaune parlor sae missing system dinsa yake ga parlorn bai sa kayan kallo ba tukun, yasan accnt dinsa ya d'an girgixa da cire ciren kudin da yake in kuma xa aci gaba da haka to fa karewa xa suyi, ga credentials can gida bare ya fara neman wani aiki, Tausayin Maminsa kawae yake amma in dan Abbansa ne ko a jikinsa don dama sun saba irin haka, Ring din bell aka yi, ya mike yana kallon kofar, can ya karasa ya bude, daya daga yarinyar Hajiya Hajarah ce tsaye bakin kofar rike da basket me dauke da breakfast, ya d'an koma baya, tace "Mum tace a kawo" yace "Ohkk thanks soo much" daga haka ya karba ta juya ta wuce, ya koma parlor ya ajiye, ji yyi matar ta burgesa sosai sae yake jin ta a ransa kamar Mami, bude abincin yyi yaga wainar shinkafa ce ta miya sae brown yam and egg da fries egg with plantains, a wani karamar warmer kuma ga Irish, murmushi yayi ya koma yyi kwanciyarsa kan kujera, sae kusan karfe goma Samha ta fito cikin shirin doguwar riga amma ba abaya ba, karasowa tayi parlon ta xauna kasa ta sunkuyar da kai ganin yanda yake kallonta cikin sanyin murya tace "Ina kwana" ya mike xaune yace "Lafiya lau dear, ashe kin iya bacci kema haka" murmushi tayi bata ce komai ba, ya nuna mata breakfast yace "Gashi Mami tace a kawo mana" ta kalli abincin a hankali tace "Mun gode" ya mike tsaye yace "Dama ke nake jira, let eat" ba musu ta mike suka isa gun breakfast din. Da rana mai aiki ne ta kawo masu lunch, Abuturrab ya karba yana kallonta yace "Hajiya na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Ta fita aiki tun safe" yace "Alryt" Da yamma bayan la'asar yana zaune bakin gate tare da mai gadin gidan Hajiya Hajarah ta dawo, gaisheta yayi ta amsa da murmushi tace "Ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mami ya aiki?" Tace "Alhmdllh, ina Samha?" Yace "Tana ciki" tace "Toh a gaisheta" yace "Mami mun gode for the food" tace "Ohh it's nothing Boy" daga haka ta ja motar ta ta shiga gidan.
*Haske writers asso*
? *Noorul Huda*?
By khaleesat Haiydar?✍?
35....
Yau kwana goma sha hudu da xuwan su Gombe, yana xaune parlor laptop a gabansa sae dai gaba daya hankalinsa baya kan abinda yake, damuwarsa daya yanda yake cire kudi a account gashi ba shigowa wasu ke yi ba, at all shi bai iya sana'a ba bae ma san yanda ake yi ba, he don't want to run short of money, ya lumshe ido ya rike kai yana tunanin mafita, dago kai yayi bayan kusan minti goma jin fitowar Samha daga kitchen, kallonta yake har ta karaso parlor ta xauna, ya sakar mata murmushi yace "Weldone" jin bata ce komai ba yace "Dear!" Ta kallesa ya ce "An fara Reg din Jamb, gobe sae mu je ki yi koh?" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace "Yeah gobe da safe in shaa Allah" daga haka ya mike ya shiga daki. Suna breakfast the next day ya sa ta shirya suka fita reg din Jamb din, sae kusan da rana suka dawo gida, bae bari tayi girki ba ya fita ya siyo masu abinci, daren ranan ya dinga tunanin ko dae ya kira small mum dinsa yyi mata maganar CV dinsa ne, yanke shawarar yin hakan yayi daga karshe, washegari lahadi yana xaune balcony ya hango Hajiya Hajarah xaune daga nata Balconyn da laptop gabanta, ganin ta kallo inda yake ya mike ya nufi gun ta, ya d'an dukar da kai yace "Ina kwana Mami?" Tana murmushi tace "Lafiya lau Boy, ya gidan?" Yace "Alhmdllh..." Tace "Ina Samha?" Yace "Tana ciki Mami" tace "Alryt wai in tambaye ka boy..." Kallonta yayi da sauri yace "Ina ji Mami" ta ajiye pen din hannunta ta nuna masa kujerar gabanta tace "To xauna" Ba musu ya xauna tace "Transfer aka yi maka xuwa garin nan?" Ya sunkuyar da kai yace "A'a Mami" tace "Ohk, naga kuma har yanxu baka koma aikin ba ko hutun mai yawa ka dauka, or rather let me put it this way...." Shiru ya d'an yi sai kuma yyi murmushi yace "Mami bana aiki yanzu" da mamaki tace "Baka aiki kuma?" Shiru yayi nan ma, ta sauke ajiyar xuciya tace "It's ohk Boy kar in shiga rayuwar ka koh!" Yar dariya yayi yace "Noo Mami ba haka ba, laifi nayi ma Abbana ya amshe CV dina and everything, that was why i left kano" kallon mamaki take masa, can ta girgixa kai tace "Duk a dalilin auren da kayi knn?" Ya gyada mata kai yana murmushi, tace "Toh ba a son yarinyar ne a gidan ku" nan ma ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa, sosai ta ji tausayinsa, can tace "But me yasa ka xabi aurenta da kayi ma iyayenka biyayya" A hankali yace "Mami haka Allah ya so" tace "Toh iyayenta fa?" Yace "Su ba ruwansu" Tace "Satin ku nawa da auren yau?" Yyi shiru kamar mai nazari sai kuma yace "Sati biyu da kwanaki" girgixa kai tayi tana kallonsa tace "Ur field?" Dago kai yayi ya kalleta yayi d'an murmushi yace "Am a Medical Doctor" kallonsa kawai take kafin tace "A doctor?" Yace "Yes Ma'am" ta cire glass din idonta tace "Where did you schl?" Yace "Uk nayi karatu Mami!" Tace "Ina matakin karatun naka?" Yace "Nayi degree, snn nayi masters duk a fannin medicine..." takardar dake gabanta ta dauka da pen ta mika masa tace "Am ur patient suffering from Malaria Typhoid, prescribe me drugs and injections...." Yar dariya yayi ya karbi takardar yace "Alryt Ma'am" ya gama rubuce rubucensa bayan kusan minti shidda sannan ya mika mata takardar ta karba ta sa glass dinta tana kallo, gyada kai ta shiga yi, sai kuma ta mika masa wani takardan tace "Prescribe for someone suffering from chronic stomach ulcer!" Karba yayi ya kuma rubuce rubucensa ya mika mata, ta karba tana dubawa tace "Um! Yayi kyau, kana theatre ne?" Yace "Ina yi Mami" ta basa wani takardan tace "Rubuta min procedure din yanda xa ayi operating din patient that's suffering from Appendix...." Karba yyi cikin yan mintuna ya gama ya mika mata ta karba tana kallo, murmushi tayi tace "Alryt Doctor, am offering you work at my clinic daga gobe, sai ka shirya da safe mu fita tare..." Ya buda ido yace "Am soo grateful Mamina" tace "My pleasure, but try to reconcile with ur parent kaji boy, kar mace ta hadaka da iyayenka" a hankali yace "In shaa Allah Mami" aikin da take yi a laptop ta juya masa gabansa tace "Idan baxan takura ka ba pls go on with this it's understandable, am already exhausted dama..." Yace "Alryt Mami" daga haka ya fara duba abinda take yi, duk abun nn da suke Fatima na lekensu don tun da taji muryarsa ta taho da sauri ta labe, tana ganin uwarta ta mike ta bar gun da sauri, Hajiyar na kallonsa tace "Xaka iya tafiya da shi boy, idan ka gama sae ka kawo min" yace "Alryt Mami," daga haka ya dau system din da takardun dake ajiye yayi mata sallama ya wuce, ita kuma ta shiga ciki, shara ya tadda samha tana yi a parlor ya girgixa kai ya xauna yace "Kin san me?" Ta kallesa ta ce "Mene?" Yace "Three things you never get tired of are, bathing, cooking and sweeping i notice" dariya ya bata sae dai bata yi ba tayi murmushi ta xauna tace "Toh sae ka tashi kayi" ya wara ido yace "Haba in tashi in yi" ta hararesa tace "Ehh" mikewa yayi ya nufi gun da ta ajiye broom din ta dauke da sauri kafin ya isa, karba yake son yi taki sake masa tace "Nooo, ka kyaleni...."
*Haske writers asso*
? *Noorul Huda*?
By khaleesat Haiydar?✍?
_Hafsat Ummu Ilham, i don't dedicate pages but here is a whole page for you dear sis, Am so grateful for the visit Allah ya bar xumunci sis ya raya su Ilham da Annur, Khaleesat heart you sisto_ ?
36.....
A can kano kuwa har gobe neman Abuturrab Abba yake, har imagining irin hukuncin da xae masa yake, Sosai Mami ta damu ganin har kusan sati bbu labari, to ina Aliyu xae kai yar mutane, kullum Hajiya Mariya sai ta xo gidan yayar tata tana kwantar mata da hankali amma ko kadan bata nuna tasan idan Aliyu yake ba duk da ta lura xargin ta yayarta take, Mahaifiyar Samantha kuwa ba don mai gidanta da ya hanata ba kotu dama tayi niyar kai karan, bata da aiki sae kuka da tsine ma Abuturrab ta kuma dau kudirin ko da ya dawo da Samantha kasheta kawai xata yi kowa ya huta don bata san mugun abinda yaje yyi mata, da dai ace ta xama musulma gwara ta kasheta a cewarta, bbu bata lkci ta shiga shirin tafiya Jerusalem don yin addu'an Allah ya dawo da Samantha tayi masa sacrifice dinta, mahaifin Samantha kam mutum ne mai saukin kai da boye damuwa baxa ka taba cewa abun na damunsa ba. Ranar Asabar Samha na kitchen tana kkrin daura girki da yamma shi kuma Abuturrab na xaune balcony rike da sabon system din da ya siya don bai iya rayuwa bbu shi, d'aga kai yyi ganin shadow din mutum, ya ga fatima tsaye daga bakin balcony din tace "Mum tace matar ka ta xo" daga haka ta juya ya bi ta da ido, haushin ta ya ji har cikin ransa, ko kadan yarinyar bata yi masa ba, ya ga alamar bata dau hali irin na mahaifiyarta ba sai girman kai, ya tabe baki ya mike ya shiga ciki, kallonsa Samha tayi jin abinda yace, can tace "Toh girkin fa!" Yace "Don't worry ki sa hijab ki tafi" ba musu tayi yanda yace ta fita xuwa part din Hajiya, tana parlor da duk 'yan matan nata uku sai wata dake xaune tare da fatima alamar kawarta ce, Samha ta risina ta gaisheta ta amsa da fara'a tace "Kadaici bai damun ki Samha, ki dinga shigowa nan ku saba da su fatima mana" murmushi Samha tayi tana wasa da fingers dinta tace "Toh" Hajiya tace "yauwa ko ke fa, xama ke dayan nn bbu dadi, ki dinga shigowa cikin mutane" kai samha ta gyada mata, Hajiya tace "Kar fa ki daura girki xa a kai maku idan an gama a nan kin ji" murmushi Samha tayi bata ce komai ba, Mami tace "Gobe su fatima xa su saloon sai ki bi su ki ga gari idan mijin ki ya amince, ke ma sai kiyi gyaran gashin daga can" Samha tace "Uhm to Mami" Fatima ta mike ta dalilin wayarta da yayi kara ta kalli kawarta Bilkisu tace "Gashi sun kira Billy" daga haka suka fita balcony, a waje Billy tace "Teemah new tenant din gidan nan ne yarinyar nn?" Fatima ta kalleta sae ta fasa d'aga wayar tace "Ehh" Billy tace "Kai amma yarinyar is pretty... Amarya ce koh?" Fatima tayi wani murmushi tace "Sai ma kin ga mijin xa ki san she is nt pretty...." Billy ta wara ido tace "Haba dai??" Fatima tace "Uhn He is more than cute, kin san Allah gabana faduwa yake idan muka hada ido da shi, but sai in wani daure fuska ko gaishesa bana yi" Billy tace "Waoww xan so in gansa kuwa" Fatima xata yi magana sai ga Samha ta fito ta sa takalmanta ganin yanda suke kallonta tace "Sannun ku" Billy tace "Yauwa!" Daga haka tayi wucewarta xuwa part dinsu duk suka bi ta da ido. Abuturrab yace "Har kin dawo?" Kai ta gyada masa tace "Tace xa mu je saloon gobe da yaranta" Shiru yyi yana kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Allah ya kai mu" ciki ta shiga tayi kwanciyarta tun da tace kar tayi girki, fatima ce ta kawo masu abinci kusan Magrib bbu sallama ta shigo parlon, Abuturrab na xaune yana kallo a system Samha na gefensa ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa idonta a kan system din ita ma, a tare suka daga kai suna kallonta, ko kunya taji sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Assalamu alaikum" Samha ce kawai ta amsa ta karaso ta ajiye abincin tace "Mum tace a kawo" Samha tace "Mun gode" daga haka ta juya ta fice. D'an tsaki Abuturrab ya ja can ciki, Samha ta kallesa tayi murmushi bata ce komai ba. Washegari khadija ce ta taho Balcony tana kallon Abuturrab dake duba newspaper da ya siya daxu da ya fita karo masu kaya a boutique, gaishesa tayi ya amsa tace "Wae Ummin mu in kira Anty Samha idan ta shirya" Abuturrab yace "Toh ga ta nan xuwa, ya sunan ki?" Tayi murmushi tace "Sunana khadija" yace "Alryt xan fadi mata Khadija" juyawa tayi ta wuce ya bi ta da kallo ganin banbancinta da yayarta, baxa ta wuce shekaru sha bakwai ba amma tafi yayar hankali, yana xaune parlor samha ta fito da hijab har kasa tana kallonsa, murmushi yyi yace "Cute" murmushin ita ma tayi, yace "Sae kun dawo but kar ki bari a dinga kalle min ke fa" dariya tayi yace "Yeah nikab ma xan siyo maki" kofa ta nufa ya bi ta da ido har ta fita, jiranta ta samu su Fatima na yi, Hajiya Hajarah tace "Toh sae kun dawo, Allah ya tsare hanya" driver ne xae kai su saloon din, fatima ta shiga gaban mota, Khadija da Rabi'ah suka xauna baya tare da Samha, su kadae suke mata hira har suka iso saloon din, fatima ta bude mota ta fita su ma suka fita suka bi bayanta xuwa cikin babban saloon din, khadija na kallon fatima tace "Big sis a fara yi ma Anty Samha koh?" Fatima ta kalli Samha ganin kallonsu take bbu yabo bbu fallasa tace "Alryt" daga haka taje tayi xamanta kan daya daga kujerun Saloon din sae dae can kasar xuciyarta ji take kamar ta shake yar uwar tata, Samha da Rabia aka fara ma gyaran gashin don akwae mutane saloon din, tun da aka bude kan Samha Fatima da duk yan saloon din ke kallo, matar mai gyara mata gashin sae cewa take "Maa sha Allah you've got a very fine long hair" Samha ta kirkiri murmushi bata ce komai ba sai dai duk a takure take ganin yanda ake kallonta, cikin minti ashirin aka gama mata ta mayar da hijab dinta da sauri, aka kama kan fatima sae dai ita kitso tace xata yi, ita din ma ba baya ba gun gashi, mai saloon din na kallonta tace "Baxa kuyi lalle ba Madam?" Khadija tace "Xa muyi" wani kallo Fatima ta watsa mata tace "ke da wa, waye xae jira kuyi lalle?" Khadija tace "Ae na tambayi Ummi tace mu yi" dauke kai fatima tayi bata ce komai ba, khadija aka fara yi ma snn Samha da taki yarda da farko har sae da Khadija da Rabi'a suka tilastata, suna saloon din har aka kira azahar, Khadija ta kalli Samha tace "Mu shiga daga ciki mu yi sllh Anty Samha" shiru Samha tayi sai kuma ta mike kamar mara laka ta bi bayanta, Khadija ce ta fara alwala a toilet ta fito snn Samha ta shiga, tsura ma tap din ruwan ido tayi, lkci daya xamanta gidan kanwar Abbanta ya fado mata, a hankali ta bude ruwan ta shiga alwalan kamar yanda take yi a kaduna da yaran Aunt dinta, tana gamawa ta fito ta ga Khadija ta shimfida mata wani darduma ta saka hijab dinta ta hau kan darduman babu abinda ta mance a ynda ake sllhn sae d'an abinda baka rasa ba, har hakan ya bata mamaki, tana idarwa Khadija tace "Me xa a karbo maki?" Murmushi Samha tayi tace "Bana jin yunwa..." Khadija bata ce komai ba ta fita, samha ta mike ta bi bayanta, snacks da drinks Khadija ta sa driver ya karbo masu, bbu yanda samha ta iya haka ta karba, ba su suka bar saloon din ba sai kusan karfe uku, part din su suka tafi gaba daya, Hajiya ta yi masu sannu da xuwa tana kallon Samha tace "Har kun dawo?" Samha ta gyada mata kai, tace "Toh sannun ku daughter, bari a xubo maku abinci" Samha tace "Ae mun ci" Hajiya bata saurareta ba tasa mai aiki ta xubo masu abinci gaba daya, har aka yi la'asar tana parlon, Hajiya tace "Khadija ku shiga ciki ku yi sllh" Khadija ta kalli Samha tace "Muje daki muyi sllh" ba musu Samha ta mike ta bi bayanta xuwa bedroom dinsu, kamar daxu haka tayi sllhn suka fito bayan sun idar, nan Hajiya tasa mai aiki ta xuba mata abinci ta kai ma Abuturrab, ta karbi abincin tayi godiya ta fita, Kwance ta samesa parlor yana bacci, ta ajiye abincin hannunta ta durkusa kusa da shi tana kallonsa tace "Doctor!" Bude ido yayi a hankali, ta langwabar da kai tace "Anyi sllh fa" ya mike xaune yana shafa fuskarsa, tace "Are you okay?" Girgixa mata kai yayi yace "Am having headache..." Tace "Toh kayi sllh sai kaci abinci then you take drugs" tana magana amma ido da hankalinsa na kan kunshin hannunta, ta bata rai tace "Ina maka magana" kamo hannunta yayi murya can kasa yace "Waow, baby kunshin yayi kyau sosai, i like it" ta kwace hannunta tace "Thanks" ya d'an marairaice mata yace "Toh baxan ga gyaran gashin ba?" Murmushi tayi ta cire Hijab din jikinta tana kallonsa, ya lumshe ido underneath his breathe yace "I have always loved you from the very first day i saw you Samha!" Kallonsa kawae take, ya bude ido a hankali yace "Tell me daga ina kike that very Night?" Murmushi tayi xata mike ya jawota jikinsa yace "Noo, talk to me baby" murmushin ita ma tayi tace "I don't want to talk about that now!" Yace "Noo plss baby..." Ganin yanda ya zuba mata manyan idanuwansa ta sauke kanta kasa a hankali tace "My frnd forced me to her birthday party, ni ban san it's an indecent party ba, shine na gudu na bar wajen..." Bude kofar parlon aka yi ta xame jikinta da sauri dai dai lkcn da fatima ta shigo, ta sunkuyar da kai ta karaso parlon, Samha ta xamo kasa a hankali ta xauna, takardun hannunta ta mika ma Abuturrab tana kallonsa tace "Ummi tace in baka wannan..." Mikewa yyi bbu yabo bbu fallasa yace "Drop it!" Daga haka ya shiga bedroom, ta bi sa da ido, Samha ta kirkiri murmushi da kyar ta karba tace "Bari in ajiye" sake mata fatima tayi ta juya ta fice daga parlon. Samha ta mike a sanyaye rike da takardun ta shiga dakin da ya shiga, xaune ta gansa gefen gado ta durkusa kusa da shi tace "Me yasa kayi mata haka?"
*Haske writers asso*
? *Noorul Huda*?
By Khaleesat Haiydar?✍?
_Tohm ya na iya tunda Ummu Ilham na da 'yan adawa irinsu Chamo, Zaarah, Teemahluv, Deezoh... Gasu nn dai? su ma kuma sun ce sai fa an masu baxa su yarda ba, toh ina ku ke gashi nan sai ku kacalcala shi bbu ruwana naku ne_ ?
37
Dagota yayi ya xaunar da ita gefensa yace "Kinsan me Baby?" Ta girgixa kai yace "Hajiya ta ban aiki...." Samha tace "Aiki kuma?" Yyi murmushi yace "Yeah she's also a medical doc...." Tace "Uhm hw did she know you re a doc?" Yar dariya yyi yace "Taga bana xuwa aiki shine ta tambaya nd i told her nayi ma Abbana laifi shi yasa na bar kano..." Xaro ido tayi tace "You told her everything??" Kamo hannunta yayi yace "No i didn't love!" Sunkuyar da kanta tayi, ya daura hannunsa kan dogon gashinta murya can kasa yace "Haka xa ki haifa min yara masu irin gashin nn kin ji" da sauri ta fara kkrin sauka daga kan gadon yaki saketa, kmr xata yi kuka tace "Doctor baka yi sllh ba fa..." Dariya yayi yace "Sai in tare xa mu yi bby" ta kallesa tace "Uhm ae yau na yi!" Yace "Dagaske?" Tayi murmushi tace "Yeah nayi Zuhur a saloon, nayi Asr a gun su Ummi" ya wara ido yace "Don Allah da gaske Baby, toh me da me kika ce a sllhn" wara ido tayi tace "Na fa ce maka ina yi a kaduna, rayuwar da nayi a kd a da yafi wanda nayi a kano da parent dina, am still missing my aunt, amma Mum dita ta rabamu wai she's putting me in the islamic way..." Abuturrab da ke ta kallonta yace "Toh me Abba yace?" Ta wara ido tace "Toh me xai ce? He said nothing, for the past 3yrs aunt dina bata xo gun mu ba..." Abuturrab yyi murmushi yace "Za mu kai mata ziyara knn" da sauri tace "Da gaske?" Yace "Yeah sweety, amma ba yanxu ba" daga haka ya mike yace "let me Ablute..." Washegari kamar yanda Hajiya tace da wuri Abuturrab ya shirya yana 'yan dube dube a laptop, aka danna bell, Samha dake goge gogen parlon ta mike ta isa gun kofar ta bude, khadija ce tsaye tayi murmushi ganinta khadija tace "Ina kwana Anty Samha" Samha tayi murmushi tace "Lafiya lau khadija" khadija tace "Ki ce ma Uncle Ummi tace tana jiransa fa" Samha tace "To" snn ta juya ta koma parlon tana kallonsa tace "Wae Ummi na jiran ka" mikewa yayi ya rufe laptop din ya langwabar da kai yace "Ko mu je tare ne baby, ke fa kadai zaki xauna gida" murmushi tayi tace "It's nothing ai na saba..." Yace "Alryt da wuri xan dawo kin ji?" Kai ta gyada masa ta rakasa har bakin kofa yayi peck din goshinta, ta juya da sauri ta koma parlon ya wuce yana murmushi, A parking space ya tadda ta tana jiransa, ya gaisheta ta mika masa car key din ya karba a xuciyarsa yace to da bai iya tukin ba fa, yana gama warming motar ta zaga ta shiga, duk wnn abun fatima na kallonsu ta window a daki, Ummi tace "Samhar fa?" Yace "Tana ciki Mami..." Tace "Duk xata ji bbu dadi ita kadae ga su fatima duk makaranta za su..." Murmushi yyi yace "Ae ta saba Mami" Sae da suka fita compound din tace "Ina matakin karatun ta ya tsaya?" Yace "Waec ta gama recently, but na kai ta tayi jamb registration nn garin" Mami tace "Good..." Daga haka ta dinga nuna masa inda xai bi har suka iso Clinic din, babba ne sosai asibitin, yana gama parking a space din da aka tanada don haka ta fito snn shi ma ya fita, ya bi bayanta xuwa reception, gaisheta nurses din dake gun suka dinga yi ta amsa ta nufi stairs xuwa office dinta, shi dai yana biye da ita har suka iso, Hadadden office ta shiga da shi, ta kunna Ac, ta yaye curtain snn ta xauna ta nuna masa kujera shi ma ya xauna, wayarta ta dauka ta kira wani likita, ba a dau lkci ba wani da baxae wuce Abuturrab ya shigo, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace "A new doctor here, xa ayi employing dinsa a nn" Likitan me suna Shareef yace "Alryt, his qualificatios...." Ta girgixa kai tace "Forget that" ya gyada kai, snn ya juya ga Abuturrab ya basa hannu yace "Am Dr Shareef" Abuturrab ya karba hade da murmushi yace "Dr Aliyu" Dr shareef yace "Welcome to our clinic" Ummi tace "Office din kusa da naka xa ka bashi, idan Bashir ya dawo sai ya koma second flour" Dr Shareef yace "Alryt" daga haka ya kalli Abuturrab yace "Mu je Doctor" mikewa Abuturrab yayi yana kallon Ummi, ta dau makullin mota ta basa tace "Ba da dadewa ba xan fita meeting, when it's four sai kayi wucewar ka gida" yace "Toh ke fa Mami" tace "Akwai wani mota a nan xan fita da shi" yace "To nagode Mami" daga haka ya bi bayan Dr shareef suka fita, office din nasa madaidaici ne me dauke da table da office chair, snn da kujeru, sai show glass mai dauke da magunguna da injections a ciki sae gadon Anti Natal, da dai abubuwan da office din likita ke bukata, Dr Shareef yace "Hope you will like it here" Abuturrab yyi murmushi yace "In shaa Allah" Dr Shareef yace "Toh na bar ka lafiya" daga haka ya fita Abuturrab ya xauna kan kujera hade da lumshe ido. Kafin karfe daya patient din da yyi attending ma sun kusa goma, ana bude kofa ya hade rai, nurse din dai ce ta shigo da wani file kafin ta karaso yace "Ke doctors nawa ne a asibitin nn" kallonsa take bata ce komai ba, ya lura she derives pleasure looking at him, ya wani mugun hade rai yace "r you Daft?" Da sauri tace "Sir?" Kin cewa komai yyi yana kallonta fuskar nn tasa kamar hadari, tace "Amm, amm Doctors shidda ne sir...." Yace "Toh kar ki sake shigo min da file.... Fita" juyawa tayi ta fita, ya ja tsaki shi haushin irin kallon da take masa ma yake kawai. Kamar yanda Mami tace ana Asr yyi ma Dr shareef sallama, har ya kai bakin kofa ganin kallon da nurses din ke masa gaba daya ya juyo ya dawo, yace "I am Dr Aliyu, am gonna work here with you all for the mean time, yeah am very free nd friendly amma bana son kallo don Allah..." Daga haka ya juya yayi ficewarsa, wasu suka bi sa da harara, wasu kuma kamar idanuwansu xa su rakasu har gun motar. kusan a tare suka shiga compound da fatima a tata motar, yana gama parking a space dinsu ya kashe motar ya fito, ita ma ta fito da kawayenta biyu, ko kallon inda suke bai yi ba ya juya ya nufi part dinsa, duk suka bi sa da ido, Salima tace "Kaddai ku ce min shi ne" Fatima bata ce komai ba ta dau hanyar balcony dinsu, Billy ta sauke ajiyar xuciya tace "Shine mana" daga haka suka bi bayan fatima Salima na ta waigan Abuturrab da har ya isa part dinsa. Khadija dake parlor da Samha ta mike da sauri ganinsa tace "Sannu da dawowa Uncle" yayi murmushi yace "Yauwa khadija, how you?" Tace "Fine," Daga haka ta nufi kofa yace "Ina xa ki kuma" tace "Dama xan wuce ne" yace "A'a xo kiyi xaman ki" Shiru tayi bata ce komai ba ya kalli Samha yace "Ina yini Ma" murmushi tayi tace "Sannu da dawowa" yace "Thanks dear" daga haka ya shiga Bedroom, khadija ta dawo tayi xamanta parlon tana ci gaba da ba Samha lbrin da take bata. Kwance Abuturrab yyi Maminsa a ransa, haka kawai ya tashi da ita yau yaji ganinta kawai yake son yi, can ya mike xaune ya dau wayarsa, yyi jim kmr me nazari kafin yayi dialing numberta, yana fara ring gabansa ya shiga faduwa, Mami dake parlor ta rungume hannaye tana sauraren tijaran yakumbo, ba ayi ranan da xae wuce bata xo ta xaxxaga mata tsiyar ta fito da Aliyu ba, a da tana addu'ar Allah ya karkato hankalinsa ya dawo gida ko don xarginta da ake a kan tasan inda yake, amma yanxu kam addu'a ma take kar ya dawo don tasan duk inda yake he is fine don ya saba irin haka, matsalar daya ynxu da yar mutane da ya tafi banda haka ya shekara ma bai dawo ba in dai yana lfya ko a jikinta, dai dai nn wayarta ya shiga ring ta jawo da yake neman hanyar da xata bar parlon take duk da bakuwar number ne hakan bai hanata dauka ba upon maganar da yakumbo take cikin dag'a murya, Abba dai sai operating laptop yake, sallama Mami tayi Aliyu yyi shiru jin muryarta, har sai da ta sake maimaita sallaman, da kyar yyi gathering courage yace "Mami..." Sosai gabanta ya fadi jin muryarsa, ta mike ta kuma yin sallama kamar bata ji sa ba ta nufi stairs, a fusace yakumbo tace "Ahmad dubi ni ta tsallake ta wuce ina mata magana...." Abba ya kalli Mami da har ta kai stairs yace "Hajarah!" Ba tare da ta kallesu ba tace "Ina xuwa, Gwaggo na ce ke kira" daga haka ta wuce sama, Abba ya d'an kalli Yakumbo yace "Tana xuwa yaya..." Tabe baki tayi tace "Ta matse mata can, wato Ahmad ynxu shknn haka xa mu xuba ido an kasa sanin inda Aliyu yake, ni tsorona daya fa kar yaje masallaci a aura masa kafura mu shiga uku..." Sai ta fashe da kuka tace "Wllh Ahmad kaf xuri'ar mu kai ma kasan bbu tubabbe, wnn wace irin kaddara ce haka, mu Aliyu xae xuba ma duwatsu a ido, mu xae kunyata, mu xai toxarta?? toh wllh yyi kadan ko da ya auri yarinyar nn ko bayan raina sai an raba auren, mu xai haifa ma jikokin jaraba? Matsawar ina numfashi wllh wllh bbu aure tsakaninsa da tsinanniyar, ko ya aureta kuwa sae ya saketa, bare kullum axumi nake ina roko kada Allah ya basa ikon aurenta...."
*Haske writers asso*
? *Noorul Huda*?
By Khaleesat Haiydar?✍?
Tohm where r u my Fertymerh Zahrah and Ummi Aysha.... ku ma ga naku shuwagabannin Haske, Allah ya kara mana basira baki daya?
38.....
Tun da ta fara Abba ya tsaida abinda yake yana saurarenta, tana kai wa aya kuwa tace "Ko ya ka ga?" Ya gyada kai yace "Haka ne!" Mami na shiga dakinta ta rufe kofar tace "Aliyu!!" Ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Forgive me plss Mami, i know i disappointed you, ki yafe min don Allah..." Tace "Kana ina yanxu?" Shiru yyi, a fusace tace "Baka ji na ne?" Yace "Mami don Allah kiyi hakuri, ina... Ina kaduna..." Tace "Karya kake Abuu, ina yar mutane?" A hankali yace "Tana nan Mami..." Mami ta girgixa kai tace "Yanxu rayuwar da ka xabar ma kanka kaga shi xae fishsheka Abuturrab, warce ba muharramar ka ba kake rayuwa da ka ajiye koyarwar addinin ka aside?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Aliyu..." Nan ma dai bai ce komai ba, ta kuma san yana jin ta baxae dai yi maganan bane, tace "Toh yanxu meye amfanin haka Abuu, me yasa har gobe baxa ka dawo gentleman ba?" Xaunawa tayi gefen gado ta dafe kanta, can tace "Look kayi min magana ynxu bana son wlknci, tell me what's the meaning of what you did?" Ya bude idonsa dake rufe da kyar yace "I want to convert her...." Mami tayi tagumi tace "Ta haka ake converting din mutum Aliyu, ka dauketa ku gudu kamar wani Indian film kace min you want to convert her?" Murmushi yyi cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri Mami, ke ma kinsan ynxu idan na dawo da matsala, mami you've got to trust me, kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba, ni bana fasikanci kin sani, just that this the only way out, xan dawo gida in shaa Allah amma har sai naga hankalinta gaba daya ya karkata ga islam, nasan duk abinda nayi ma 'yar wani surely xa ayi ma nawa kidz din kuma har kannina xai iya shafa sbda haka am very cautious of what i do...." Mami tace "A ina ku ke ynxu?" Yace "Muna Gombe Mami" ta xaro ido tace "Wa ka sani a can Abuu?" Yace "Bbu kowa gashi kuma har nasan mutane ynxu har na fara aiki" tace "Da wani CV din??" Yayi murmushi yace "Da na brain dina Mami" Mami tace "Aliyu ka rufa min asiri ka mayar da yar mutane, Aliyu ni wnn abinda kke son yi ko kadan bai gamshe ni ba, yanxu rayuwar nn wa kaga xae yrda xuri'arsa a samu irin haka, ba fa ce maka tayi tana sha'awar addinin ka ba, kai ke cusa mata kawai, gaba nake jiye maka wllh, shawarata kawai ka dawo in taga tana son musulunci xata yi ne ba sbda kai ba... Ka dawo kayi auren da iyayen ka ke son kayi Abuu, ka ajiye shashancin nn da kake yi son" da damuwa yace "Mami ni wllh ita kadai naji xan iya aure... Pls ki bani go a head ko yanxu xan iya aurenta nasan zata amince kuma dawowa addinina baxae mata wahala ba in har na aureta" Mami tace "Toh ba da yawuna ba wllh, in kuma shakiyancin naka har ya kai ka fara tsallake magana ta to bismillah, na fada na sake fada ba da yawu na xaka je a daura maka aure da Christian ba...." Daga haka ta katse wayarta, ya rike kansa. Can ya mike da kyar ya cire shirt din jikinsa ya kwanta kan gado hade da lumshe ido, ya fara bacci samha ta shigo dakin, durkusawa tayi kusa da shi tana kallonsa a hankali tace "Doctor..." Bude ido yyi don baccin nasa bai yi nisa ba, tace "Abinci fa?" Ya mike xaune yace "I've eaten sai anjima" tace "Toh..." Mikewa tayi xata fita yace "Samha!" Ta koma ta durkusa tace "Na'am..." Ganin kallonta kawai yake tace "Doctor i prayed today also..." Yace "Really?" Tace "Yea, tare da khadija, she came back from islamiyya around 1, shine ta xo nan... Tace min ita ma recently tayi waec" Yace "Waow, shknn kin samu frnd knn... Which means you weren't lonely today!" Tace "Yeah, tare muka yi girki da ita, i like her she's very nice" yace "Uhnn! Ai naga alama" ta langwabar da kai tace "Toh ko nima in dinga bin ta islamiyyan i don't want to be staying at home all alone kafin ta dawo" ya sauko da kafafuwansa yana kallonta yace "If that's what you want love sai in sa ki..." Tace "Ehh ina so!" Yyi murmushi yana kallonta yace "Alryt gobe sae ki fara koh?" Ta gyada masa kai, mikewa tayi tace "Let me go back tana parlor, nayi xaton xaka ci abinci ne" yace "Am ohkay dear, ltr xan ci" tace "Tohm" snn ta fice daga dakin ya bi ta da ido murmushi dauke fuskarsa, sosai yaji ddin islamiyyar da tace xata, and he was happy she brought the idea her self. Washegari yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin da take ya tada ta, ta mike xaune tana mitsike ido yace "Yau baxa kiyi sllhn ba knn?" Ta kallesa tace "Sllh kuma?" Ya wara ido yace "Alryt dear, yi kwanciyar ki nayi xaton xa kiyi sllhn ne" bata ce komai ba hakan yasa ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi ta bude kofar bayi ya juya ya kalleta bai dai ce komai ba ya fita ya shiga wani dakin don shiryawa tunda yyi wanka kafin ya je masallaci yana buttoning din shirt dinsa ta shigo da hijab jikinta, ta karasa dakin tana kallonsa tace "Nayi sllhn" yace "That's very nyc of you love... Allah ya karba" murmushi tayi tace "Me xan yi maka for brkfst?" Yace "Just lipton xa ki dafa dear, akwao bread" tace "Kwai fa?" Yace "Noo, ni baxan ci ba sai dai ke" juyawa tayi ta fita, ko kafin ya fito har ta dafa ruwan Lipton din ta ajiye a parlor da kayan beverage, ya karaso parlon ya xauna ta hada masa tea'n yana kallonta, ganin irin kallon ta sunkuyar da kanta, murmushi yyi ya jawo cup din tea din, tace "Baxan je islamiyyan ba yau?" Yace "Xa ki mana baby" mikewa tayi tace "Tohm bari in shirya" daga haka ta shiga daki, yana gamawa ya fita xuwa part din Hajiya, karo ya kusa ci da fatima da ta fito daga parlon hannunta rike da makullin mota tana sakale da jaka alamar boko xata, Bai ko kalleta ba ya bi ta gefenta ya isa kofar ya danna bell, kin tafiya tayi ta xuge jakar hannunta tayi pretending kmr neman abu take, Khadija ce ta bude kofar ta gaishesa da fara'a ganin shi ne, yace "Mami fa?" Tace "Tana ciki bari in mata magana" daga haka ta juya ta koma parlor, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Wai ka shigo" Bin bayanta yyi suka shiga parlon, dai dai lkcn da Mami ma ta shigo parlon, xauna yyi kan sa a kasa ya gaisheta ta amsa tana murmushi tace "Kun tashi lfya Boy?" Yace "Alhmdllh Mami" tace "Har ka shirya knn, in dai ka gama abinda kke tun da akwai makullin mota gun ka sai ka dinga wucewa kawai boy" yace "Toh Mami, dama samha ce ke son shiga islamiyyar su khadija, ina son in fara xuwa can da ita ne...." Mami tace "Maa sha Allah, kace mata in dai ta shirya ta xo sai in kai ta.... Kai kayi wucewar ka kawai" A hankali yace "Toh nagode Mami" daga haka ya mike ya fita duk da hakan bai gamshe sa ba don bai son Mami tasan bata san komai ba. Fatima dai na nn tsaye fa har lkcn, wnn karan tare masa hanya ma tayi duk don yyi mata magana, ga mamakinta sai gani tayi ya tsallake karfen dake xagaye balcony din yyi wucewarsa.