09-22-2017, 01:49 PM
Tuwon Girma Miyarsa Nama!!
Akwai wani mutum yana da mai yi mishi wanki 'washman' wanda ya yarda dashi kuma yake bashi wanki kullum.
Watarana duk kayan gidanshi sunyi datti (wato nasa dana matarsa dana 'ya'yansa) sai ya kwashe gabadaya ya kaiwa mai wankin.
Mai wanki ya wanke gabadaya ya goge, ya shiga bandaki kenan kafin ya dawo ya samu gabadaya an sace, ya nema sama da kasa bai gani ba sai ya yanke shawaran yaje ya fadawa Alhajin kawai. Yaje gidan Alhaji ya fada mishi abinda ya faru, koda matar Alhaji taji haka sai ta rinka yi masa fada amma sai Alhaji ya hanata yace ta bari don haka Allah ya kaddara. Sai Alhaji ya waiwayo yace da mai wankin "Babu damuwa zaka iya tafiya" amma sai yaga mai wanki yana zaune bai tafi ba. Alhaji ya kara ce masa "Babu damuwa kaje kawai" sai mai wanki yace "Alhaji kudin wankin yake jira...!!
Idan kaine Alhaji me zakayi masa??