The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined variable $postsdone - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Trying to access array offset on value of type null - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13301 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13302 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13303 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13304 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13301 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 13302 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 13303 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 13304 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 33 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 33 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 65 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 65 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY*
#3
*11*
sanyi jikin momi yayi ta kasa kai komi bakinta Nura da Usman ne kawai suke cin abinci shima Siraj ya damu sai kallon momi yake,
tashi momi tayi ta nufi gurin daya watsarda takardun ta shiga haɗawa.


saida ta haɗesu guri ɗaya sannan ta kalli Siraj daya juyo yana kallonta tace “Siraj jeka kiran min yayanku”



kai kawai ya ɗaga mata ya tashi ya fice.



Mairo dai sai satar kallonsu take tana tsomen beredi,
guri momi ta samu ta zauna dafe da kai kamar mai mata ciyo.




tana haka Qasin da Siraj suka shigo dining Siraj ya nufa Qasin kuma ya nufota yana faɗin “gani momi”



kujera momi ta nuna masa har lokacin tana ɗafe da kai.



bayan ya zauna ta kalleshi tace “Qasin ka rika hakuri kasan da wadda kake zama Qasin ni bana tunanin saboda ɓata maka suna ko karyarda kai Yarima ya ɗauki kwangila ya baka”
kawar da kai yayi alamar bai jidaɗin maganar ba.




ganin haka yasa momi ta taso ta dawo kusa dashi ta zauna “Qasin ni a ganina kamar ma Yarima yana son ɗaukaka kanfaninku ne”



juyowa yayi ya kalleta “a a momi so yake ya karya ni kawai kuma bazan taɓa yarda da wannan kwagilar ba ba zai taɓa cinma burinsa a kaina ba”
dafashi momi tayi “ban sanka da zuciya haka ba bana son ka runtse ido ka yanke hukuncin da zai zamar maka nadama nafison ka yanke hukunci ido a buɗe




bana son abunda zai saka cikin matsala Qasin”
kallon momi yayi yana nazarin kalamanta can ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya ya sake buɗe idon yace “momi banida mafita sai wannan momi bana son Yarima yayi nasara a kaina momi ki duba min plz”




itama Momi ajiyar zuciya ta sauke tace “baka ganin mayarda kwangilar zai zame maka matsala?”
“zai iya zama kan dan lokacin da zai bada kwangilar tare da yan jarida yazo”




“to karka kuskura ka mayarda kwangilar zai zubar muku da mutuncin kanfani”



“momi ba nida wata mafita sai wannan”



“haba Qasin sai kace kai ba namiji ba kai bakasan yadda zaka sarrafashiba ka bashi kunya ka taka abunda ya taka Qasin ka zama gawurtaccen namiji ba rago ba”
Siraj da tunda ake maganar hankalinsa na gurin tasowa yayi yana faɗin “yes yaya kaima namijine ka ya k`eshi ks kara ɗags martabar kanfaninka kabi shawarar momi plz”
ajiyar zuciya Qasin ya sauke a karo na uku ya kalli momi “momi ba hannuna da nasa ya bani kwangilar ba PA ɗina yaba kuma banida tambas dan zai iya haɗa kai dashi ya cutar dani”




Siraj yace “ka chanja PA kawai”
“haba Siraj how many PA I have to change just because of him? PA 4 na chanja akanshi bazan sake chanja wani ba not anymore”




cikin faɗa yake maganar jijiyar wuyansa na tashi da sauri Usman da Nura suka juyo suna kallon su, Mairo kara sakin baki tayi tana kallonsu daman hankalinta yana gurin,
dafashi momi tayi “ga wata shawara Qasin”




kai ya ɗaga mata ba tare daya kalletaba ‘uhmm’



“mi zai hana ka karɓi kwangilar kayi da kanka?”
murmushi yayi mai cike da jin haushi “haba momi ai zubarda kai ne daɗi zaiji na k`arɓi kwangila da hannuna masa”




“ba faɗuwa kayi ba Qasin cigabane a gareka da kuma ɗaga darajar kanfaninku”



kai ya girgiza “momi ba zaki gane ba”
“kaine baxa ka gane ba Qasin idan kayi haka mutane zasu yaɓeka suce bakada girman kai sannan kodan kwangilar tayi ya kamata kayi haka kuma idan tayi kyau zaka jawowa kanka customers ayaba maka ka kara samun ɗaukaka”




Siraj yace “gaskiya ne yaya ka ɗauki shawarar momi”
ya daɗe zaune gurin kamin ya ɗago kai ya kalleta “shi kenan momi zanyi yadda kikace”
murmushin jidaɗi Momi tayi ta shafa kansa “Allah ya maka albarka ya shige maka gaba”




shida Siraj suka amsa da ‘amin’



tashi yayi ya nufi kofa yana sauke ajiyar zuciya,
da gudu Mairo ta taso ta nufo shi tana faɗin “dan Allah ka je dani yawo inson fita”




fuska a haɗe ya shafa kanta yace “ba yanzu ba” ɓata fuska tayi idonta suka cika da hawaye shirinta na guduwa ya rushe .



 juya tayi  tana kallonsa har ya fice.
tashi momi tayi ta nufi up stairs tana faɗin “Maryam in kuka k`are ki haɗa kayan ki kai kicin ki wanke kuma ki share parlour nan ki goge”


kara ɓata fuska Mairo tayi abunda ta rsana kenan hawayen dake makale a idonta suka zubo



*12*
bachi Mairo take saman kujera ta wani turo baki sai numfashi take da k`arfi,
Momi na saukowa ta tadata “ke ke ke Maryam”



a firgice ta farka ta kara turo baki fuskartar momi ta rik`o “kinyi wanke2?”



kai ta ɗaga tana murza ido momi tace “tashi kije kiyi wanka”



tashi tayi kamar ta fasa kuka ta nufi up stairs zuciyarta cike da tsoro, 



rik`e k`arfin tayi ta rumtse ido tana tafiya a hankali har ta haye.
        “`*  *  *“`




Momi na kicin tana girki taji uhun Mairo da sauri ta aje robar dake hannunta ta nufi up stairs.



tsakiyar ɗaki ta tararda Mairo sai juye2 take tana kuka jikinta ba kaya kikata momi tayi “ke lafiya miya faru?”



kasa magana tayi sai toilet take nunawa momi tana tuma,
da sauri momi ta nufi toilet ɗin,




kalle2 ta shiga ta rasa dalilin dayasa Mairo kuka hankalinta bai kai gurin shower da take kunne ba sai gab da zata fita sannan idonta suka kai gurin juyowa tayi ta nufi shower da niyar kashewa,



nan hannunta ya taɓo ruwan dake zuba da sauri tayi baya baya da yar k`ara saboda ta fasasshin ruwan da suka taɓa mata hannun,
ta daɗe tsaye cikin toilet ɗin tana duba hannunta,




 sannan tasa hannun hagu ta kashe shower.



koda ta fito duk`e ta tararda Mairo sai faman kuka take tana kiran ta bani ta shiga uku ta data momi tayi tana faɗin “sannu Mairo ni wlh na manta da yadda shower take mantawa ma nayi na haɗa miki ruwan da kai na yi hakuri kinji”



kai ta ɗaga tana kuka tace “ni a kaini gida gurin Gwaggo”



hakuri momi tayi ta bata daker tayi hakuri momi ta haɗa mata wasu ruwan tayi mata wanka ranar har kanta saida momi ta wanke,
da suka fito momi ta rasa kayan da zata saka mata dan ita bata ga wasu kayan kwarai da zata sa mata ba haka dai momi ta ɗauko wata tsohuwar a tamfa tasa mata,




momi ta kalleta tace “hau gado ki kwanta”



da sauri ta nufi gadon ta faɗa rub da ciki,
momi na gab da wucewa Mairo ta ɗago da jajayen idanunta ta kalli momi “mumo ko zaki aikeni?”




juyowa momi tayi “aike kuma Maryam kamar ya?”



tashi tayi zaune “in siyo miki wani abu ko aike”



murmushi momi tayi tace “a a ni babu abunda za’asiyo min koma abu zan siya saidai na aiki direba ko yara su siyo”



komawa tayi ta kwanta tana zubarda hawaye.



kai kawai momi ta girgiza ta fice.
Mairo tunda ta kwanta take wahalallen bachi sai uku da rabi ta farka koshi dan momi ta tadata ne.




hannunta Momi ta riko ta suka nufi bathroom kin shiga tayi ta lak`e kafaɗa “ni bazan shiga ba”



“yi hakuri ni zan haɗa miki ruwan ba zakiji zafi ba”



 daker momi ta lallaɓata ta yarda suka shiga,
 brush momi tasa tayi tare da alwala sannan suka fito,




tsareta momi tayi saida tayi sallah sannan ta riko hannunta suka nufo downstairs.
zaune suka tararda Qasin yana cin abinci laptop na gefensa yana aikin danne2.




tsaki momi taja bayan ya jama Mairo kujera ta zauna,



ɗagowa yayi yana kallon Momi “lafiya dai momi?”



saida ta zauna sannan tace “hala baka ci abincin ba?”



sosa kai ya ɗanyi yayi murmushi “indomi ce ta ɗafa”



taɓe baki momi tayi “to Allah ya kyauta ya sawwake”



kasa amsawa yayi saima kallon Mairo da yayi yace “bakida lafiya ne hala?”



kin masa magana tayi saima faman cin abincinta da take tana sauke ajiyar zuciya,
momi ce ta kalleshi tace “k`onewa tayi da ruwan zafi shine take fushi”




“ayyah sorry kijin injin bata jimu ba?”



“bata jimuba zafin daine ya raɓeta”



kanta ya shafa “sannu kinji?”



kai ta ɗaga masa tana aika lomomi,
suna haka Usman ya fito ɗakinsa ya nufi kofa.




kiransa momi tayi “Usman”



“na’am Momi”



“dan Allah jeka ɗaki ka ɗauki ATM ɗina kaje nan Damary plaza ka siyo ma Maryam kayan sawa”



“owk momi”



da sauri ya nufi upstairs.
tashi Mairo tayi jikinta na rawa tace “zan bishi mumo ina zuwa”




momi kamar tasan plan ɗinta ta zauner da ita “a a ba yanzu ba ba kasuwa zaije kuma ba daɗewa zaiyi ba”
da kuka tace “thom”




ta sunkuyarda kanta tana hawaye.



Qasin ya shafa kanta yana murmushi “yi hakuri bari ranar da nake free sai muje yawo ko ki zaga gari?”
kai ta ɗaga mishi ba tare data kalleshi.




murmushi momi tayi ta kalli Qasin tace “Qasin ya akayi da batun kwangilar?”



“na karɓa ni da kaina zanyi kuma baza a samu matsala ba insha Allah”



daɗi sosai momi taji “Allah ya taimaka ya shige maka gaba”
tashi Qasin yayi ysns faɗin “Amin momi bari naje part ɗina nayi wani aiki”




kai kawai momi ta ɗaga mishi ya fice rik`e da laptop.



*13*


da ɗare Usman ya kawoma Momi kayan (tufafi) data aikeshi ya siyo,

aiko murna gurin Mairo ba’a magana sai tsalle take tana wani shafar tufafin tana jefasu sama tana rawa.

duk wani bachin rai dake ranta ranar gushewa yayi sai faman godiya take yima momi.

tun abun naba Momi dariya har ya koma bata tsoro ganin irin murnar da take kamar zata haukace sai faman uhu take, tana daredare harda hawaye,
momi dai da taga ba kanta baro mata ɗakin tayi ta sauko k`asa,


nan ta tararda Qasin yana aikin rubuce2,

 guri ta samu ta zauna suka soma fira.
Mairo na jin muryarsa ta kwaso tufafin ta nufo downstairs da gugu tana faɗin “Qasin kaga tufafina da-”


kasa karasa maganar tayi saboda wani mugun kaye da tasha saman tile aiko nan kuka ya chaja salo ta koma yin na gaske,
dariyace tazo ma Qasin haka ya matseta ya nufeta ya tadata tsaye yana bata hak`uri yana murza mata gurin data gimu.
momi kan faɗa ta hau yi mata “yarinya ba kai sai bak`ar hauka tun ɗazu take murnar tufafin nan kamar mahaukaciya kekan kauyenciki yayi yawa Maryam”


Qasin na dariya yace “haba momi koni ai murna zanyi inna samu sabon tufafi zuwa fa tayi ta gwada min ko?”

kai ta ɗaga masa tana kuka, handkerchief ɗinsa ya ciro yana share mata hawaye.

“ya isa haka jeki gwada tufafin mugani suna miki kyau”

da ininniyar kuka tace “thom”

ta nufi ɗaki.
tana shiga ta cire kayan jikinta ta ɗauki wata diguwar riga tasa da gudu ta fito ta nufo parlour.


bata tararda shiba sai momi dake zaune saman kujera tana kallon tv,

gurinta ta nufa tana nuna mata kayan, koɗata momi tayi tana yaba yadda kayan suka karɓeta nan dariyarta ta dawo ta rik`a tsalle tana mulmula a k`asa saida momi ta soma yi mata faɗa sannan ta tashi ta nufi ɗaki.

       “` *   *   *“`

tun daga lokacin Mairo bata k`ara saka tufafinta na kauye ba saidai wayanda momi ta siya mata,

kuma ba laifi Usaman ya iya zaɓi dan duk tufafin data saka saisun yi mata kyau sun k`arɓi jikin ta,

kyau ta ma ba laifi da farinta sai kara fitowa yake ga gashin kanta kullum sai momi ta gyara mata shi,
 taci maikyau tasha maikyau tasa maikyau wasa wasa cikin wata 2 tayi bulbul kamar ba itaba,


aiki kan yanzu Mairo ta ɗan fara sabawa dan kullum tare da momi suke haɗa breakfast kuma duk wani karamin aiki ita momi take sawa tayi tun tana fushi har ta gaji ta daina sai in taje ɗaki ta rika kuka tana zagin momi da cire mata albarka,
zancen guduwa yanzu ta daina tunda taga momi bata bari a fita da ita kuma in zata fita bata zuwa da ita babu yadda batayi ba momi tak`i yarda duk wata dabara ta ta saita rushe ta daina ma yima momi zancen ta hakura,


*_3 months later….._*

yau da far’ah Mairo ta tashi saboda tayi markin Gwaggo,

koda Momi ta shigo ta tasheta zaune ta tararda ita harma tayi alwala tana sanye da hijab,

da mamaki momi ta shiga bathroom bayan ta ɗoro alwala ta fito ta nufi waduraf tana faɗin “Maryam ya akayi yau kika rigani tashi?”

carbi ta nunawa momi tana wani gyaran murya kamar wata babbar mace wai ita mai tasbihi ba a magana,
“hmm Maryam manya”


momi ke faɗar haka tana k`ok`arin ɗaura zane,

hijab tasa ta shimfiɗa carpet ta rik`a carbin tana salati har aka tada sallah sannan suka bi zan’in masallacin dake kusa dasu,

suna karewa bayan suyi yan addu’o’e suka nufi kicin.
*_8:45am_……*


Mairo ta shiga jera breakfast a dining sai tsaki take tana faɗin “mumo yau munyi rana”

tsayawa tayi tana kallon agogn dake manne gefen gurin tana tunani yadda momi ta koya mata,
ta daɗe a tsaye tana kallon agogon ganin bata tuna ba yasa ta shiga shirmen ta “kinga fa mumi har wannan mai laulaye tayi (8) da mai k`afa ɗaya (4) da mai kai sama (9) gaskiya munyi rana yau”


da dariya momi ta fito kincin ta nufo dining tana faɗin “waike Maryam yaushe zaki daina wannan shirmen naki ne? ke kullum ana koya miki abu amman kamar kara toshe miki k`wak`walwa ake”

turo baki tayi ta nufi kujerar data saba zama ta zauna,

momi bata sake cewa komai ba ta shiga zuba mata abincin harsu Usman da Nura da Siraj suka fito suka nufo dining,
bayan sun zauna kowannensu ya shiga zubama kansa,


har suka fara ci Mairo bata ci nata ba sai kunbure2 take tana harararsu duk da momi ce take son ta harara amman ba dama.

babu wadda ya tanka mata sai Siraj dake k`ok`arin zaunawa,

“waike lafiya kike hararar mutane?”

saida tayi kwafa sannan ta kalleshi tace “ina ruwanka dani”

tashi yayi da niyar ya doketa momi ta tareshi “ai tace maka ina ruwanka da ita bai isaba?”

“tho momi baki ganin yadda take hararar mutane”

“ba da kai take ba ni take son harara bata da dama saboda nace bata gane agogo”

 komawa yayi ya zauna yana dariya “LOL yarinya aike kullum liki minandak`u ce kulli yaumin ɗifɗif”

kifa kanta tayi da dining tana kuka,
momi ta kalleshi da siffar masifa “wai Siraj mi yasa kake wasa da ita ne bafa tabashiyarka bace mahaifinta da naku uwa ɗaya uba ɗaya suke”


hannu ya ɗaga “tho momi kice ta daina wasa dani”

“ai kai ka soma wasa da ita gashi har sauran suna son yi”

jan zib yayi a bakinsa alamar bazai kara cewa komai ba,



*14*
sai a lokacin Mairo ta ɗago kai ta soma cin abinci,
_GOOD MORNING EVERYONE_



yau da abunda Qasin ya shigo dashi kenan fuskarsa ɗauke da murmushi ya ware hannayensa hannunsa ɗaya rike da wasu file.



duk juyowa sukayi suna kallonsa rabon da suji muryar irin wannan ta farinciki daga gareshi harsun manta,



wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar momi dan tasan duk yadda akwai abun farincikin daya faru,
yana karaso ya mika ma momi file ɗin yana faɗin “lafiya kuke kallona hakane?”




murmushi sukayi suka ci gaba da cin abincisu dan sun san ko minene dole a fasa kwai suji,
a rikice momi take karanta har tana tsalleke wasu saboda daɗi tana kare karantawa ta mike tsaye ta rumgumeshi idonta cike da hawaye




“ai daman na faɗa maka Qasin duk ka ɗauki hawarana bazaja taɓa jin kunya ba kuma ka gani”



rumgumeta yayi yana dariya “haka ne momi na”



ko wannensu kasa cin abincin yayi sai murna suke suna yaba masa suna rumgumarsa,
Mairo kan ido ta sakar musu kamar tana cin abincinta dan ita mahaukata ta ɗaukesu tunda bata gane abunda suke yiwa murna,
saida tayi tsaki sannan suka tuna da tana gurin 




ɗagata momi tayi saboda murna ta tsayar da ita saman dining tana faɗin “me kike yiwa tsaki yata? yau ranar farinciki cefa”



“to ba duk kunata murna ba kuma kunk`i ku faɗa min dalili”



“ayyah to yi hakuri bari na faɗa miki yayanku ne yaci nasara akan kwangilar da aks bashi har mutumen ya yaba masa da kalamai masu daɗi”



“to minene kwangila?”



“sashi akayi yayi gini sai kuma yayi sa’ah shine muke murna”



fashewa tayi da dariya “hahaha nima Qasin nayi murna”



“to ai ba haka akeba uhu ake ana tuma”



aiko kamar jira take ta soma yin sama tana yin kasa saman dining,
juyawa momi tayi tana kallon Usman da yayi maganar “kasanfa bana son iskanci dan ba hankaline da ita ba”




juyowa tayi ta sauke Mairo tana faɗin “ke kuma kinsan na rabaki da kiran sa Qasin ko to daga yau karna sake ji”



bata fuska Mairo tayi ta soma kuka,
dafata Qasin yayi “haba momi miyasa zaki sata kuka yaufa ranar farinciki ce”




share mata hawaye ya shiga yi yana faɗin “yi hakuri yi shiru kinji?”



makkale kafaɗa tayi “ni bazanyi shiru ba”



“aiko in bakiyi shiru ba ba zanje dake yawo ba kindai san kinfi kowa son yawo ko kina so naje dake?”



kai ta ɗaga tana share hawaye.



Qasin yace “good to ysu zanje dake kodan farinciki danake”



da far’ah tace “yanzu ko?”



“a’a sai an jima inna shirya harda tufafi ma xan saiya miki kiyita tsalle”



wata irin dariya ta saki tana tunowa da momi yasa ta karasa ba ta rufe baki,
ɗagowa yayi yana murmushi ya kalli momi “thank you more. momi”




“ur welcome Qasin nafika farinciki”



“momi ai har a tv aka nuno dan da yan jarida yaje dan yayi zaton zan to zarta”



“kwata2 yau bamu kunna tv ba bamu gani ba”



“ai tun jiya ne da dare ai”



hannu momi ta daga “oh nidai Alhamdulillah ai tunda anyi nasara”



     “` *   *   *“`



ranar wuni sukayi suna farinciki momi harda rabon kuɗi ta rikayi ko abincin rana ma kasa ci tayi saboda farinciki,



*_2:30pm……_*



Qasin ya shigo sanye da kananan kaya,



zaune ya tararda Mairo tasha doguwar rigar fakistan momi ta mata farkin ɗin kanta kamar wata balara sai ɗan gyale na abayar da take rike dashi,



ta wani hakinci kamar wata princess ga bakinta yasha mai yar girace kawai momi batayi mata ba,
tsayawa yayi yana kallonta kamin ya kai hannu yaja hannunta su taɓe “eyye yarinya haka momi ta gyara ki?”




da sauri ta tashi tsaye “eh daman kai nake jira tun ɗazu”



murmushi yayi “to yayi kyau bari naga momi sai muje kinji?”



kai ta ɗaga masa ya nufi stairs.



bai daɗe ba ya fito ba mairo ta mika masa hannu ya rika suka fice yana yaba kwaliyarta,



suna kaiwa parking space ya buɗe mata giɗan gaba ta zauna shi kuma ya shiga driver seat. yayima motar key suka fice,



wuni sukayi suna yawo duk gurinda suka ga wani abun kwadayi sai ya tsaya ya siya,



Qasin yasha dariya saboda Mairo take murna kamar wata taɓɓabiya.



*_4:52pm….._* 



suka nufo gida Mairo sai surutu take masa shidai tun yana dariya harya koma murmushi,
daf ta zasu shiga gida ta tuno da Alkawarin da yayi mata na siya mata kaya,




aiko nan tasa mai kuka dole ya juya ya nufi Dubai mall. suna isa ta shiga k`ok`arin rigansa fita amman ta kasa dan bata san yadda ake buɗewa ba,
saida ya fita sannan ys buɗe mata kofar ta fito sai dariya take tana yaba kyaun gurin,




suna shiga ta nufi wani gurin saida ya riko hannunta suka nufi sashen yara,



sannan ya saketa ya ɗauki basket ya mika mata ya riko kunnenta “karki kuskura wuce ɗauko kala uku uku kawai zaki ɗauko kinji ni ai?”



kai kawai ta ɗaga mishi badan ta fahimci mi yake nufi ba dan hankalinta nacan gurin kayan data gani,
haka ta nufi kayan tana wani leko harshe kamar karya tana shafa kayan.




tafi karfin minti 20 tana duba kayan sannan ta ɗauko kala biyar ta nufoshi tana dariya “duba kaga suna da kyau sosai”



ɗaya bayan ɗaya ya rika dubasu “haba Maryam har huɗu keda nacewa uku?”



“nidai su nake so”



“a rage kinji?”



lake kafaɗa tayi “a a nidai duka”
bai sake cewa komai ba ya nuna mata gurin biyan kuɗi “ɗauki ki kai can”




da sauri ta ɗauki kayan ta rigashi isa,



ana cikin lissafi ta ɗauko wata riga ta ɗora “harda wannan inaso”



bakin baki Qasin yayi yana kallonta can dai yaji tsoron ta sake ɗauko wani abun ya nuna mata kofa “Maryam jeki gurin mota ki tsaya harna fito kinji?”



ba musu ta fice ta barshi,



tsaye tayi jikin motar tana wasa da hannayenta duk wadda zai shiga saita faɗa masa akwai kaya masu kyau a ciki,



wasu basa kulata wasu kuma suyi ta dariyarta,



tana haka Yarima yazo shiga cikin wasu tufafi na alfarma fadawansa na take masa baya,



nunashi Mairo tayi tana faɗin “kai ma kayi sa’ar zuwa nan kayan suna da kyau”



kwatakwata bai lura da itaba sai a lokacin ya juyo ya kalleta a ransa yana _wani sabon tsari suka samune nasa yara sunayiwa mutane welcome_



suna haɗa ido Mairo tayi waje da ido “lahhhh kaine”



kayanshi ta shiga shafawa tana ɗaga masa gira.



can ta shaa nata kayan tana juyi tana rawar kai “ni ka gani yanzu kaya masu kyau nake sawa”
shikan kallonta kawai yake yana tunanin gurin daya santa. dan jikinshi yana bashi ya santa,




saidai ta ɗan kwanta masa lumshe ido yayi yana tsusar hot pink lips ɗinsa faɗawansa dai sai kallonsa suke da k`warorin mutanen dake guri
bai buɗe idon ba sai da ya tuna da murmushi ya rika fuskarta “ya akyi kikayi kyau haka? waya kawoki nan?”




saida tayi dariya sannan tace “yaya kuma momi ce tamun kwaliya”



“wane yaya?”



kamin ta bashi amsa Qasin ya fito ya nufosu fuskarsa ɗauke da mamaki.
nunashi Mairo tayi “gama shi nan”




kai ya ɗaga mata yana wani shu’umin murmushi.



Qasin na karasowa Yarima ya mika masa hannu “thanks to yhu once again My Men for the contract”



kallon hannun kawai Qasin yayi fuskarsa babu yabo ba fallasa ba tare daya amsa ba yace “ur welcome the perfect one”



murmushin fuskar Yarima ne ya kara faɗaɗa,



Qasin bai saje kylashi ba buɗewa Mairo mota “ke shiga muje”



da sauri ta shiga tana ɗagawa Yarima hannutana sama byebye.
da wani irin karfi Qasin yaja motar har saida Mairo taji tsoro,


Yarima yayi tsaye yana kallon motar har suka bace masa.

*15*
tunda suka shiga motar Mairo kasa magana tayi saboda tsoro saima rike bel ɗin motar da tayi,



shima bai tanka mata ba saida suka kusa isa gida sannan ya soma magana ba tareda ya kalleta ba “ina kika sanshi Maryam?”



shiru tayi kamar ba zata amsa ba saida ya sake maimai tawa sannan tace “can gida na sanshi harda kuɗi yake bani da goribar bunni ba na taba faɗa maka wani yaban goriban bunni ba?”



kai ya ɗaga mata “eh ina ya haɗu dake?”



“can gida”



“gida ina?”



daidai nan suka iso gida yana yin parking ta yinkura zata taji bazata iya buɗewa ta juyo ta kalleshe “buɗe min zan fita”



yana kallon kallon fulawoyin gidan yace “sai kin faɗa min gurin da kika sanshi?”



kamar ta fasa kuka tace “bana ce maka can gida ba”



sai a lokacin ya kalleta “to ai baki min bayani yadda zan gane ba”



ganin babu sarki sai Allah dole tasa ta faɗa masa tun farkon haɗuwarsu,
“to tun daga lokacin baki sake ganin shi ba sai yanzu?”




“eh nidai buɗe min na fita”



“to ya akayi ya ganeki?”



“nidai ba shine ya ganeni ba ni ban saniba”



bai sake ce mata komai ba ya buɗe motar ya fita,



ya zagayo gefenta ya buɗe mata ta fito da guɗu ta nufi parlour. bayan ya rufe motar ya rufa mata baya,
parlour suka tararda momi da gudu Mairo ta faɗa jikinta “kinga yaya ya simin mai kyau”




dubawa Momi ta shigayi tana yabawa “eyyye yar yayanta duk ke kadai?”



“eh ni kuma na zaɓo kuma mukaje yawo”



“amman gaskiya yana ji dake to injin kin masa godiya?”



“eh na masa ko yaya?”



kai ya ɗaga mata yana murmushi



“eh kinyi bama iyaka”



“naji je ɗaki ki aje”



“to”



tashi tayi tana dariya ta nufi ɗakin.
momi ta kalli Qasin tace “magana nake son muyi dakai Qasin mai muhimmanci”




agogonsa ya kalla “owk momi amman fa kamar lokacin Sallah yayi”



agogon ɗakin momi ta kalla “inaga ma an soma sallar wani gurin jeka masallaci kawai nima bari na tashi nayi sallah gobe mayi maganar”



‘to’



kawai yace ya tashi ya fice jiki yake baya son maganar duk da bashi da masaniya akan abunda zasu tautauna,



*_washe gari….._*



da safe Qasin bai lek`a part ɗin momi ba ya wuce gurin aiki,



bai shigo gidan ba sai dare part ɗinsa ya fara wucewa saida yayi wanka ya sauke gajiya sannan ya nufo part ɗinta,



zaune ya tararda momi tana hamma Mairo na kasan carpet tana bachi Usman da Nura ma duk bachi suke saman kujera,



ta dasu Qasin yayi yana faɗa “momi sai ki rika barinsu suna miki bachi saman kujera manya dasu kuma maza”



“ai nasha musu magana har na gaji”



masifa Qasin yayits musu da suka farka basu dai ce masa uffan ba daya kare suka tashi kowane ya nufi ɗakinsa,
tsaki yaja ya zauna yana faɗin “shi yasa Siraj yake burgeni wlh shi halinsa da ban yake”




momi tace “ai Siraj yasan kansa gadai wata nan da take son biye musu”



kallon Mairo yayi “gaskiya momi ya kamata asa maryam makaranta dan inaga Gwaggo ba k`arɓarta zatayi ba”



“eh ai inaso ma maka maganar daman jira nake naga yadda zaman zai kasance dan kar asata daga baya tace abata yarta amman kaga yanxu tunda bata tambaya ba ai sai a sakata”



“ina gafa Gwaggo fushi ne tayi kinga ai ko waya bata kira duk da son da take yiwa Maryam”



“fushi kan ai da gani”
momi na yunkurin tashi Qasin yace “momi wace magana ce kikace zamuyi jiya?”




da idon bachi momi ta kalleshi “bachi zanyi ba wani magana yanzu yau ma ko leko nan bakayi ba bakayi breakfast ba ka fita”



“eh kirana akayi shiyasa kuma tunda naje nake aiki sai da magriba na samu kaina”



“to nidai bachi zanyi kuma ko gobe bani da time dan gobe abbanku zai dawo”



tashi yayi yasa hannayensa aljihu yana faɗin “Allah kawoshi lafiya ni bari naje na kwanta”



“to saida safe ta damun maryam kamin ka wuce”



ɗaki momi ta nufa tana hamma,
a hankali Qasin ya shiga data ita ganin bata motsaba yasa shi girgiza ta. ciki magagin bachi ta rika faɗin “mumi kinga Siraj ko”




“ba Siraj bane nine tashi kije ɗaki ki kwanta”



sake komawa tayi bachi haka yasashi data ita tsaye yana girgizawa “ke momi tace kije ɗaki ki kwanta”



“aa barni ni nan zan kwanta”



girgizata ya rikayi da karfi daker ya samu ta buɗe ido aiko tana ganin shine ta kara zube masa, dole ya ɗauketa ya kaita ɗakin yayiwa momi saida safe ya fuce.



*_4:21pm….._*



momi na zaune ita da Siraj suna fira sukaji an buga k`ofa. kofar momi ta kalla tace “waye?”



shiru akayi ba amsa nan ta kalli Siraj “jeka duba”



tashi yayi ya nufi kofar yana buɗewa yaga Yarima tsaye cikin kananan kaya yasa hannayensa ciki aljihu sai kanshin turare yake fuskarsa na kallon wani gurin.



kasa masa magana Siraj yayi shima kin juyo fuskar yayi ya kalleshi,



juyowa Siraj yayi ya nufi ɗakinsa tambayarsa momi ta shiga “lafiya wanene?”



yana gaf da shiga ɗakin yace “gashi nan waje nima ban sanshi ba”



tashi momi tayi ta nufi kofar, yadda Siraj haka ita ta tararda shi tsaye murmushi momi tayi tace “Yarima ne yau a gidan?”



sai a lokacin ya juyo ya kalleta shima fuskarsa ɗauke da murmushin “nine Momi”



“kuma ka tsaya a waje”



“to ai ba amin iso bane”



kai momi ta girgiza “Yarima ai naga gidan ba bakonka bane gidan nan ai gidanku ne tunda kai ɗana ne”



momi na cewa haka ta juyo ta dawo cikin parlour.



kai ya ɗaga yana karewa bakin kofar kallo kamar sannan ya taka kafarsa ya shiga cike da takama,
yana zaunawa momi ta dire mishi drinks.




“yau Yarima an tuna damu? kodai wani abun ne ya kawoka?”



da kanshi ya shiga zuba drinks ɗin yana faɗin “ziyara ce na kawo muku momi”



momi tayi dariya “aiko ka kyauta ya aiki to ya kuma gida?”



saida ya kurɓa drinks ɗin kusan so uku sannan yace “Alhamdulillah”



kallon parlour yake ta ko ina kamar mai neman wani abu.



can ya kalli momi yace “gaskiya momi Siraj bashi da tarbiya”



ko kaɗan momi bata jidaɗin maganar ba amman haka ta haɗiye tayi murmushi “yayan zamanine sai hakuri kannen naka”



taɓe baki yayi ya juyarda fuskar wani gefe.



momi zatayi magana Mairo ta fito kicin rike da abu a hannu tana faɗin “mumi kinga ni duk na wanke shuwakar kuma ta fita” maganar take tana kallon kujerar da Yarima yake zaune dan bata gane ko wanene ba,



momi tace “thom naji jiki gani nan zuwa”
yana juyowa suka hada ido murmushi ya sakar mata.


waje Mairo tayo da ido ta buɗe baki ta nufoshi da gudu rike da shiwakar da sauri momi ta tashi tsaye kamin ta rikota ta rumgumeshi har cup ɗin dake hannunshi ya faɗi.



*16*






fisgota momi tayi ta jefar k`asan carpet “lallai Maryam baki da hankali daga ganin mutun baki san inda ya fito ba ki wani rumgumeshi dubi yadda kika bata masa riga”



momi ta kalli yarima “dan Allah Yarima kayi hakuri hankaline bata da”



cikin kuka Mairo tace “nida hankalina niba mahaukaciya bace”



hannu momi ta ɗaga zata ɗaketa Yarima ya rik`e “no momi plz”



hannu yasa ya ɗago Mairo yana bata hakuri,







kuka Mairo tace yanzu ta fara daman mai nema a duhu balle an yada duk yadda yaso tayi shiru k`iyawa tayi.



fuskarta ya kama da hannayensa biu ya rik`e iya karfinsa ta kasa juya fuskarta shi kawai take kallo.



“yi shiru kinji in kina son na baki apple da abu mai daɗi”



kai ta ɗaga “to na daina”



“good girl”



handkerchief ya ciro ya share mata hawaye ya cire mata majina,







juyawa tayi tana hararar momi k`asak`asa ta gefe Yarima yayi murmushi ya rika hannunta ya “muje ki raka ni”



lakkame masa hannun tayi “ba kace zaka bani abun daɗi ba”



baice mata komai ba ya kalli momi yana murmushi yace “ni ban wuce momi in Qasin yazo ki gaishe shi”



fuska a sake momi ta amsa mishi “to zan faɗa miki mun gode a gaida gida”



kuɗi ya ciro masu ɗan dama ya aje mata sannan ya fice rike da hannun Mairo.







motarsa ya nufa harya buɗe rike yake da hannunta yana zaunawa ya kama ɗayan hannum ya rike “faɗa min miye dan gantakarki da gidan nan?”



turo masa baki tayi “to ni nasan mi kake nufi ne”



shiru yayi yana tunanin yadda zai mata ta gane “faɗa min momi mamar suwa ce?”



kai ta ɗaga sama “maman yaya da Siraj da Usman da Nura su kenan”



“good ke kuma ina mamanki?”



“mu bamuda mama sai dai Gwaggo tana can gida”



“yauwa to faɗa min ya akayi kika zo nan gidan?”



“da sukaje can suka zo dani nan gidan”



“to faɗa min Qasin yace miki wani abu da ya gamu tare?”



“a a baice komai ba”



banɗir ɗin 500 ya ciro ya dora mata saman hannu yana faɗin “karki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake kinji”



da karfi tace “to bazan faɗa ba” tana wani kallon kuɗi tana dariya.



har kasa ta duka tana masa godiya,



kunnenta ya kamo yana faɗin “duk kika faɗawa wani saina ɓata dake kuma bazan sake miki komai ba”



ɗagowa tayi tana kallonsa “wlh ba zan faɗa ba ko za a kasheni”



murmushi yayi “yauwa jeki kar moni taga kin daɗe”



tashi tayi da gudu ta nufi cikin gida.







saida yaga shigewarta sannan yayi ma motarsa key.



kaura suka tashi yi da Qasin daya kunno kai cikin gidan shi kuma yana k`ok`arin fita da sauri Qasin ya bashi hanya dan yasan shi ba jaye mishi zaiyi ba, saida ya fita sannan Qasin ya karaso parking space a ransa yana mamakin abunda ya kawo Yarima yanzu,







da sallama ya shigo parlour momi ta amsa masa Mairo ta nufeshi da gudu tana nuna masa kuɗin “yaya ka gani Yarima ya bani duka kuma ni kadai”



kuɗin ya karɓa ya duba yana kokarin zaunawa yace “momi miya kawoshi yanzu kuma”



“jiyara ta kawoshi kuma yace a gaishe ka”



“a gaishe ni? yanzu fa kasa bari yayi na shigo saida na kauce masa”



momi tace “to ai kasan halin kayan ka”



Mairo ta riko hannunsa “yaya kuma harda mumi yaba kuɗi masu yawa”



lakatar mata hanci yayi “ke wai ba ance miki momi ake cewa ba ki daina cewa mumi”



turo baki tayi tana kallon momi “to kuma yaya momi tace mun banida hankali”



kamin Qasin yayi magana momi tace “ai ba kida hankaline Maryam”



kara ɓata fuska Mairo tayi “kaji ko?”



Qasin yayi dariya yace “haba momi Maryam fa nada hankalinta komai na hankali take dan Allah ki daina ce mata mahaukaci”



“Allah ni bana mata ɗaukar masu hankali kaga abunda tayiwa Yarima yanzu?”



“mi ta masa?”



“bata fa sanshi ba daga ganinshi ta tazo a guje ta rumgumeshi ga hannayenta ba kyau har cup ɗin hannunshi ya faɗi”



Qasin ya kalleta “amman ya dakeki ko?”



momi tace “bai mata komai ba dama zan daketa hanani yayi inajin yan k`aurai ne bisan kai harda fa kuɗi ya bata”



murmushi Qasin yayi ya shafa kan Mairo.



yace “ya santa ne shiyasa”



“ina ya santa?”



nan ya bata labari kamar yadda Mairo ta faɗa masa da kuma haduwar da sukayi Dubai Mall,



Momi tace “shiyasa kika rumgumeshi ni ai nayi mamaki yadda naga ya sakar mata fuska harda share mata hawaye”



uhum kawai Qasin yace yana kallon siraj dake saukowa downstairs.





“Maryam faɗa min mi Yarima yake ce miki daya rike miki hannu?”



wani irin ɓata fuska tati ta ɗago tana kallonshi “ni baice min komai ba kawai yace yace yace yana siyomin kayan daɗi kuma kuma yana in yana gaida momi”



taɓe baki yayi “aikin banza”



momi tace “kaga halin nan naks Siraj sam bana sonsa ai kodan girmanka da yayi yaci ake ka gaisheshi amman kaki”



“wlh momi matukar bai sauke wannan girman kan dake tare dashi ba to baza mu taɓa haɗa hanya ba”



cikinsa momi tayi da faɗa “bana fason shashanci Siraj bai girmeka miye abun girman kai a ciki mutun ya tako kafarsa har nan cikin parlour nan ka kasa yi masa magana kaifa da kanka ka buɗe masa kofa ina ruwanka da girman kansa”



murmushi yayi ya nufi kofa “Siraj”



kiran Qasin ne ya juyo dashi “na’am yaya”



“nasan bai fika da komai ba amman ka rika masa magana tunda momi bata so”


kai ɗaga masa ya fice.
Reply


Messages In This Thread
*MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:30 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:33 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:36 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:36 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:38 AM

Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 859 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 781 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 749 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 889 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 794 Less than 1 minute ago
Last Post:



Users browsing this thread: 1 Guest(s)