The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined variable $postsdone - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Trying to access array offset on value of type null - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13301 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13302 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13303 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13304 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 13301 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 13302 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 13303 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 13304 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 33 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 33 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 65 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 65 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY*
#2
*6*
tun daga lokacin Gwaggo bata sake bari Mairo ta fita ba.


tallar da take ɗora mata ma bata sake ba kullum tana gida ko fita zatayi saida tare da Gwaggo,
tun abun baya damun Mairo har ya fara damunta




tunani take ko ta saci hanya ta fita in kuma ta tuna da dukan da Halilu yayi mata saita tsorata duk da yake tasan Gwaggo tace mata ba zata sake bari ya dake taba.



tana zaune ta raffka uban tagumi tana tunanin karyar da zatayiwa Gwaggo da zata sa ta kyaleta ta barta fita,



can wata dabara tazo mata



tashi tayi ta koma kofar ɗakin gwaggo ta fasa kuka tana murgemurge



da sauri Gwaggo ta fito tana tamabayarta “lafiya Mairo mi nene?”



“ni gidansu Jummala nake son zuwa ba tada lafiya”



shiru Gwaggo tayi tana kallonta dan tasan rigimar ce ta tashi



“nidai babu ruwana kinsan halin Halilu in yanxu yazo bai ganki ba faɗa zaiyi”



“tho ai ba daɗewa zanyi ba kuma ai ba zaki faɗa masa ba”



Gwaggo bata sake cewa komai ba ta nufi tabarma ta zauna.



Mairo na ganin haka takara ɗaga murya tana ihu



cikin faɗa Gwaggo tace “tashi kije kuma duk kika daɗe babu ruwa daga can kuma karki biya ko ina”



tashi tayi tana dariya daman kukan kawai take ba hawaye.



“amman dai zan biya giɗan tsoho ko tunda kusa ne”



“nidai ba ruwana keda Halilu”



“eh na yarda”



da gudu ta fita gidan
bata tsaya ko’ina ba sai gidansu jummala wuni sukayi suna shiririta basu can basu nan.




sai da bayan magariba sannan ko wannensu ya nufi gida



da fargaba ta shiga gidan tana lek`e2 



bakin k`ofar ɗakin Gwaggo ta hango Halilu zaune farin wata na haskashi.



faɗuwa gabanta yayi ɗan tasan ita yake jira zagi ta shiga zabga masa cikin ransa.



_hege mai katon kai mai kamada zabarmawa ni dai wlh ka takuramin Allah kasa ma ya mutu mai idon mage (mussa) mai kan ɓera_



ta daɗe gurin tsaye tana kallonsa wai ko zai tashi amman sai kara gyara zama yake. 



kamar ta fasa kuka ta shiga kwalawa Gwaggo kira _Gwaggo Gwaggo Gwaggo a dawo_ 



ɗagowa Halilu yayi yana kallon k`ofa yace “to shigo mana aike ake jira”



k`in shigowa tayi ta cigaba da kwalawa Gwaggo kira “Gwaggo ke ki taho mana gani”



ta daɗe tana kiranta sannan ta fito sanye da hijab da alama sallah ta k`are,



har kofar gida tazo ta kama hannunta suka shigo.



tashi Halilu yayi yana k`ok`arin rikota Gwaggo ta tare “kyaleta Halilu ni na aiketa”



“Gwaggo ki daina goya mata baya tana k`ara lalacewa”



“tho mi nayi da zakace na goya mata baya bana son raini fa Halilu”



“wane irin aikene zaki mata tun da maraice sai dare zata dawo”



Mairo ta turo baki tana watsa mata harara “ai bada maraice bane da rana ne”



buge mata baki Gwaggo tayi “ke yiwa mutane shiru dake ake ne”



kai Halilu ya girgiza “yayi miki kyau ai kamaki zanyi saiki faɗi wadda ya aikeke”



kuka Mairo tasa “Gwaggo kinji ko dukana zaiyi”



“ba zai dakeki ba bani na aikeki ba”



“hmmm Gwaggo ina miki tsoron wata rana ki daina goyawa Mairo”



“wai miyasa ka rai nanine Halilu karya zan maka kenan na faɗa maka aikenta nayi”



taɓe baki yayi ya girgiza kai ya fice.
kwafa tayi da taga ya fice “kai mugu bakin azzalumi to zo ka dakeni ɗin”




sakin hannunta Gwaggo tayi ta shiga mata masifa “ban rabaki da rashin kunya ba kuma kinsan saida mukayi dake bazaki daɗe ba kikaje kika zauna har dare”



turo baki tayi “to ba shine daren yayi saurin yi ba kuma kinsan na daɗe ban fita ba kuma…”



bata karasa maganar ba Gwaggo ta katsa mata tsawa “ke dan Allah rufe min baki `yar rashin ji kuma ki wuce kije kiyi sallah kici abinci”



da ture2 ta nufi ɗaki tana gunguni.



_Washe gari…_



tun safe Mairo tasa Gwaggo gaba tana rokonta tayi mata giɗar siyarwa,



sai faman rantsuwa take mata wai bazata sake yin abunda tayi ba.



sam Gwaggo kin yarda tayi duk da magiyar da tayi ta mata



Mairo na ganin haka ta sawa Gwaggo kuka ba k`akkautawa harda su shak`ewa tana murje murje cikin kasa duk ta bata kayan jikinta.



banza Gwaggo tayi da ita duk da bata son kukanta amman ta daure.



haka ta wuni tana kuka ta kuma yi sa ah Halilu bai dawo gidan ba tun fitar da yayi da safe.  



          saida ta gaji dan kanta ta shi ta dawo kusa da Gwaggo dake tukin tuwo ta zauna tana ajiyar numfashi,
    Gwaggo saida ta gama kwashe tuwon ta kai ɗaki sannan ta riko hannunta suka shiga banɗaki tayi mata wanka.




har suka fito bata daina ajiyar zuciya ba idanuwanta duk sun kunbura sunyi ja



saman gado Gwaggo ta zaunar da ita ta ɗauko doguwar rigar atamfa tasa mata,



ta kwantar da ita saman jikinta tana shafa bayanta



lafewa Mairo tayi in banda ajiyar zuciya babu abunda take sauke



sun daɗe a haka Gwaggo sai buga mata baya take tana son tayi bachi ita kuma taki tayi bachin sai faman sauke wahalallen numfashi take.



kai Gwaggo ta girgiza tace “ni kan Mairo kina bani mamaki ace bakida aiki sai kuka sai ja magana sai masifa haka kawai ki wahallarda kanki dubi yadda kika wuni kina kuka”



nan sabon kuka ya zo mata “to bake bace kika ki yarda kimin giɗa ba kuma na faɗa mki bazan sake ba”



da in’in niyar kuka take maganar tana numfashi da karfi kamar zuciyar zata fito
bubbuga bayanta Gwaggo ta shigayi tana faɗin “halinki nake tsoro Mairo karkije ki sake yin wani abun kuma kina ganin yadda Halilu ya sa miki ido jira kawai yake kiyi wani abun bama hHlilu kaɗai ba harda makota jiraye suke dake Mairo ke kuma gaki baki jin magana”




ɗagowa tayi idonta cike da hawaye tace “wlh Gwaggo na daina na faɗa miki bazan sake ba in kuma na sake Allah yasa na mutu”



rufe mata baki Gwaggo tayi “Subhanallahi Mairo miye haka karki sake faɗan irin wannan maganar kinji”



kai ta ɗaga mata “na daina Gwagho zaki doramin ko gobe zakimin giɗar?”



shiru Gwaggo tayi tana tunani dan tasan Halin Mairo in kuma bata dora mata ba wata sabuwar masifa ce.



kallonta tayi tace “kinmun Alkawari bazaki sake ba bazaki yi abunda zaisa a dake kiba?”



da sauri tace “eh nayi”



“shikenan zn dora miki”



“gobe ko Gwaggo?”



“eh Allah ya kaimu”



“amin”



rumgumeta tayi “na gode Gwaggo”



“Allah yayi miki Albarka”



“amin gwaggo zaki sayamin hancin ligidi?”



“eh  shi kike so?”



“eh”



“to bari na bada a siyo miki”

kwantar da ita Gwaggo tayi ta nufi kafit (wadurup ta da tsohuwar yayi) ta bude fanteka (kwala) ta ɗauko kuɗi ta sa hijabinta ta fice.



*7*
_Washe gari…_



tun da asuba Mairo ta tashi tana yin sallah ta shiga karatun gajerun  surorin data iya inta kare ta sake maimaitawa har rana ta fito.



_8:14pm…_ 



Gwaggo na motsa kunu (koko) Halillu ya shigo gaishe ta har lokacin Mairo karatu take.



mamaki yayi sosai bayan sun gaisa da Gwaggo yace “yau yarki abun k`warai akeji?”



murmushi Gwaggo tayi “ai daman tana abun k`warai indai karatu ne ai kasan Mairo ba baya ba”



“a makarantan ba agida yaushe rabon da tayi irin wannan karatum tunfa da asuba nake jinyo ta ɗakina”



“to ai daman Mairo abunda take ai kuruciya ce data girma dainawa zatayi”



“ai da girmanta Gwaggo yanxu inta kara kaɗan ai aurarda ita za’ayi”
kuka Mairo ta fara wadda ba hawaye ta daina karantun “wlh Gwaggo bana son aure ba zanyi ba”




dariya Halilu yayi “au daman ba karatu kike ba kunnenki na kanmu ai daman nasan karatun munafirci ne”



kamar ta fasa kuka ta kalli Gwaggo “kice ya kyaleni ya tashi ya bar miki ɗakinki”



kofi Gwaggo ta janyo ta zubawa Halilu ta mika masa “karɓi ga kununka kosai na can gindin murhu a kwano”



dariya yayi bayan ya karɓa yace “dan tace ki koreni shine zaki koreni Gwaggo?”



“to naga fitina kake son jami muna zaman mu lafiya”



“ai ni gaskiya ce na faɗa kuma Mairo da kike gani aurene kawai zaiyi mata hankali ta daina abubuwan nan da take”



haɗashi da Allah Gwaggo ta shiga ganin Mairo nason yin kukan da gaske daker ta samu ya fita.



juyawa Mairo tayi zata cigaba da karatu Gwaggo ta shafa bayanta “taso haka yar Gwaggo ki karya (breakfast) ai kinyi karatun da yawa”



murmushi tayi “to gwaggo aI zaki mun giɗar ko?”



“sosai ma ai dole nayi miki bana miki alk`awari ba anjima kaɗan zanyi miki”



daɗi ne ya lumluɓe Mairo da sauri ta ɗauki kayan karatun ta aje gefe ta kwanto jikin Gwaggo ta soma bata kunun tana sha cike da jindaɗi.



_2:00pm….._



Mairo ta fita tallar giɗar k`inbi tayi hanyar da tabi ranar duk da zuciyarta na raya mata ta ɗan lek`a taga ko yana nan gashi har k`anshin goribar birni takeji tana tuna yadda take cinta.
haka dai ta daure ta nufi bakin kasuwa gurin data saba zama tana siyarda giɗar. wata yarinya na zaune a gurin tana ganin Mairo ta tashi da sauri ta koma gefe dan tasan halin Mairo indai matsifa ce saida ka barmata balle yau da fuskarta take a haɗe kamar anyi mata mutuwa.
koda la’asar tayi Mairo siyar da bakin rai ta nufo gida tana tureture baki kamar ta fasa kuka sai wata tafiya take kaɗan kaɗan.




haka ta ido gida ko sallama babu tun a bakin kofa tayi jifa da turen ta ta karaso idonta ciki da kwallah ta zauna kusa da Gwaggo dake Sallah,
tana sallamewa ta kalleta “lafiya Mairo waya taɓa ki?”




soshe soshe ta shiga yi tana tunano karyar da zatayi “ni..ni…ni….ɗan ta malele zan siya?”



shafa kanta Gwaggo tayi tana murmushi “haba Mairo sai kace wani abu harda su kwallah? ɗauki kuɗi kije ki siyo ki haɗa da kifi yadda zaki jidaɗin cinsa”



kai ta ɗaga “tho amman sai in zanje makaranta”



“tho inkin huta ki watsa ruwa sannan kije makaranta kinji”



kai ta ɗaga mata ta mika mata kuɗin giɗar.



“eyeee Mairo yau duka aka siyar gaske naji kin jefar da ture tun kofa”



murmushi Mairo tayi “yau nawa zaki ban?”



“hamsi zan baki ashiri kisa a susu talatin ki siye ɗan ta malele”



ta karasa maganar tare da mika mata 50 ɗin.,
da zumuɗi ta karɓa ta tashi ta nufi ɗaki da guɗu yau an sami abun sawa a susu mai tsoka.




    “`*** *** *** *** *** ***“`



     tun daga lokacin kullum sai Gwaggo tayiwa Mairo giɗa ita kuma bata fashin zuwa gurin siyarwa so ɗaya ta je gurinda aka bata goribar birni koda taje bata tararda kowa ba tsoro taji sosai babu abunda take rayawa a ranta sai aljani ne
 “kai aljanine wannan mutunen da gaskiyar Gwaggo tunda gashi ban sake ganinshi ba kuma duk goriba karfine da ita amman tashi taushi ne da ita kuma na riga naci” 




a fili take wannan maganar can ta tsaya tana tunani “inda ba aljani bane ai bazai zo cikin dajin nan ba har ya zauna kuma fa….”
bata karasa maganar ba ta watsa da gudu saboda motsin da taji cikin itacen dake gurin tana faɗin “karku biyoni na daina bazan sake zuwa ba wayyoh Gwaggo”




ihu take tayi da kuka tana gudu rabin giɗarta na zubewa,



 har tabar gurin bata daina kuka ba dan gani take kamar sun biyota saida ta isa baki kasuwa sannan ta ɗan natsu ta soma numfasawa daidai,
tun daga lokacin bata kara tunanin zuwa gurin ba




 duk ta ɗauko tallar giɗarta sai dai ta nufi bakin kasuwa inta siyar ta tayi ta shiririta ita da abokanin talla ko inta dawo ta biya gidansu jummala suyi gantalin da suka saba daman haka take so,
fagen neman magana da matsifa ba babba ba yaro kowa ta raina musamman inta ga ta girmeka ko kana tsoronta,




        Gwaggo in banda goya mata baya babu abunda take.



Halilu yayi faɗa harya gaji amman a banza kamar ma kara turata yake,
gashi Gwaggo ta hana ya daketa sai in ya faki idonta ko ya haɗu da ita can waje.




harta saba inta ganshi saita chanja hanya haka suka rika wasan ɓoya ita dashi.
*_3 months later….._*




yau da wuri Mairo ta siyarda giɗarta kuma yau bata jin wasa saboda dukan da Halilu yayi mata jiya dan yanzu har bakin kasuwa yake zuwa da ya tarar tana wasa ya fatattaketa da duka har gida,
duk yadda abokanin shashacinta sukaso ta tsaya kiyawa tayi dan tsan sai yazo gurin kuma Gwaggo tace mata da ta siyar ta dawo gida dan kar halilu ya daketa,




sallama tayi musu badan sunso ba dole suka kyaleta wasu kuma suka wuce gida dansu inba da Mairo ba basa jindaɗin wasa,
_Aysha adon gari ga Hajara adon gari ni Maryam adon gari inba ni ai ba gari Khadija Abubakar nake Candy kunji laqani gani tafe da’ayari yan mata a dandali_(MY UP COMING SONG INSHA ALLAH)


Mairo na tafe tana rera wak`a mak`ale da turenta na giɗa.
tunda kamin ta k`araso ta hango wata kafirar mota baqa mai shek`i fake kofar gidansu yara sun zagayeta sai shafa suke.




*8*
da gudu Mairo ta karaso gurin ta shiga korar yaran duk da bata san mai motarba ɗan kawai ta ganta kofar gidansu ne kuma taga yara sun zagayeta suna shafa ita yar neman masifa,
shafa motar itama ta shigayi tana dariya tana kallon kanta ta madubin motar harda zira halshe tana lasa glass tana tale idanunta (fitar da ido)



tafi kafin minti 3 ahaka sai fana dariya take kamar wata taɓaɓɓiya,
 yaran sai kallonta suke suna son su kwakwayeta suna tsaron tayi musu masifa tunda taɓa motar ma ta hana su.
can ta juyo ta kallesu ta hade rai taja tsaki “mtssss ku dan Allah ku ba mutane guri kauyawan banza kawai kowa ya bar mana k`ofar gidan mu ko naa muku hegen duka”




maganar take tana wani ɗageɗage da marmaɗen ido.



          duk ja yaran sukayi da baya dan sunsan halin Mairo indai masifa ce ba baya ba



yarinya ɗaya aka bari tana watsawa Mairo harara harda kai hannu ta shafa motar tana faɗin “an shafa kema ai yar kauyece da hegen kanki”



kai Mairo ta girgiza tana dariya “hee ni kike faɗawa wannan maganar  zaki ko ci ubanki yanzu”



ɗankwalinta ta cire ta k`ulle kuɗin giɗar dake hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a k`ugunta (kwankwaso) tayi cikin yarinyar suka hau faɗa da juna,
kaye huɗu yarinyar tayiwa Mairo dan ta fita girma kuma k`arfi ba ɗaya ba gashi  daman can  Mairo ba wani k`arfi ne da itaba sai yar banzar masifa.




ɗukan k`warai Mairo tasha a hannun yarinyar tun tana iya jurewa har takai ga fasa kuka tana faɗin “azzaluma wlh sai naci ubanki hegiya-”



Mairo bata rufe baki ba yarinyar ta kai mata wani mugun shuri.



nan Mairo ta faɗi ta fashe da kuka



 da gudu yarinyar tabar gurin gudun kar Gwaggo ta ji ta fito.
kuka Mairo tayi tayi tana kallon kofar gidan ganin babu wadda ya fito yasa dole ta tashi rik`e da ɗankwalinta a hannu kanta kuma duk k`asa ta shiga gida,




da kuka ta shiga gidan ta nufi gurin Gwaggo dake bakin murhu tana eza wuta.



da sauri ta ɗago ta rikata “lafiya Mairo Halilu ne ko?”



kai ta girgiza mata ta shiga faɗa mata abunda ya faru,



ɗankwalinta Gwaggo tasa tana share mata hawaye “haba Mairo miye na wani korar yara dansun taɓa mota kuma in banda fitina inake ina faɗa da wannan yariyar?”



turo baki Mairo tayi ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka 
“shigar mata kikayi ko Gwaggo?”
“a’a wani nan na shigarwa wata na bar Mairo dukan da ta miki ne ban jidaɗiba”
“kuma harda wani mugun shuri tayi mun ina jin zafi har yanzu”
“barta da Allah kijin”




kai ta ɗaga “Gwaggo motar wace kofar gida?”
“yan birni ne suka zo ganin gida”
kusa da ita Mairo ta matso “yan bunni Gwaggo gurin wa sukazo ina suke”
“sun tafi ganin sauran dangi”




“lahh daman Gwaggo kina da yan uwa yan bunni?”
“eh kema ai en’uwanki ne tun kima karama marabinsu da nan”




risinawa Mairo tayi zatayi magana sukaji Sallama.
Gwaggo ce ta amsa masa Mairo kan ido ta sakar masa kamar bata taɓa ganin mutane ba,
harya karaso tsakar gidan shi take kallon tana masa dariya shidai kallon kawai yake kamin ya kalli  Gwaggo yace “Sannu da aiki Gwaggo”




“yauwa sannu qasin kai kaɗai ka dawo?”



“eh ina gabansu ne suna hanya suma”



tabarmar dake shinfiɗe k`arkashin ecce ya nufa ana k`ok`arin zaunawa yayiwa Mairo magana



“ke baki eya gaida mutane ba?”



tasowa tayi da gudu tazo kisa dashi ta zauna.
“na eya ina wuni?”




“lafiya kalau ya sunaki?”



saida tayi dariya sannan tace “Mairo sunana Mairo”



murmushi yayi ya kalli Gwaggo “Gwaggo ni bansan wannan yarinyar ba yar gidan nan ce?”



daga can Gwaggo ta amsa mishi “eh gidan nan take ear uwarka ce ai yar wajen margayi ce”



“wane margayi?”



“malam tanimu wadda koda kukazo gaisuwarsa bakayi aureba ita kuma tana k`arama”



shiru yayi yana kallon Mairo data washe masa hak`ora,
“na ganeta Gwaggo daman ke kike rik`onta?”




sallamar dasu Abbah sukayine ya hana Gwaggo amsa masa tambayarsa.



“amin wa’alaikassalam alhaji harku dawo?”



“eh wlh kinga kara mu kama hanya da wuri tunda munga dangi”



momi ce ta amsa mata.



bayan sun xaune Gwaggo ta nufosu tana faɗin 
“ai nikan ban yaba miku ba ace mutum shekara ds shekaru rabonsa da gida amman yazo ɗai rana ai kamata yayi ace kuzo ko sati ɗaya kuyi ko biu”
ɗariya sukayi Abbah yace “har yanzu dai Jamila baki chaja ba halinki nanan na masifa”
“yau ni wani haline dani daga faɗar gaskiya”




momi tace
 “karki damu jamila insha Allahu zamuzo muyi sati anan yanzu bamuzo.da shirin kwana ba kuma kinga sauran yara suna makaranta sai anyi hutu tukuna”
taɓe baki Gwaggo tayi “nidai nawa idone ai rana bata karya”




dariya suka sake yi har Mairo sai a lokacin ta gaishesu.



duk suka amsa Abbah ya shafa kanta “Maryam am girma ko?”
“ashe zaka iya gane ta ai ɗaukar ka manta”




cewar Gwaggo
murmushi yayi yace “haba dai yar tawa zan manta ko yanzu da mukaje gurin tsoho saida mukayi maganarta”




mansura ta kalleta tana murmushi tace “oh Abbah itace yarinyar da ake magana”
momi tace “eh itace yar marainiya”




“Allah sarki Allah ya jikan mahaifa”



duk suka amsa da Amin.
sun ɗan juma suna fira daga bisani Gwaggo ta kawo musu abinci.




gudun masifar Gwaggo yasa dole suka ci badan sunso ba koshi kaɗan sukaci dan tuwon dawane ba wani sonshi suke sosai ba.
kuɗi Abbah ya ciro aljihunsa masu ɗan ɗama ya ajewa Gwaggo “gashi ayi wata lalurar”




“haba Alhaji bancin abin alkharin da aka kawo?”



“babu komai jamila a daici da hak`uri”



godiya sosai Gwaggo tayi masa momi da mansura sukayi mata sallama.



suna shirin fita Mairo ta laqe kafaɗa ta bata fuska ita saita bisu.
Gwaggo ce ta shiga lallasarta “haba Mairo wane irin binsu kuma bunni fa zasuje”




“eh ina son zuwa bunni nidai saina bisu”



“kinason ki daina ganina?”



“a a ai dawowa zanyi”



Abbah ne ya dafata “kiyi hakuri Mairo kinga Jamila bata so kije ki bari har wani lokacin inmun dawo sai muje dake kinji?”



kuka ta fasa “a a ni saina biku yanzu”



Qasin ya kalli Gwaggo yace “Gwaggo ki bari aje da ita tunda tana son zuwa”



faɗa Gwaggo ta soma “babu inda zataje ita kenan ina ganinta ina jindaɗi saiku ɗauke ta to baza taje ba”



juyowa Gwaggo tayi gurin Mairo ana lallasarta ba
aiko.kamar tana kara turata sai uhu take kaar wadda aka yiwa wani abu.




Abbah tsaye yayi yana lallaɓata shima



duk yadda Momi taso su tafi kiyawa yayi dan bayason barin Mairo tana kuka gashi Gwaggo ta hana aje da ita.
suna Halilu ya shigo aiko da gudu Mairo ta tashi tayi bayan Gwaggo tana kuka,




nan ya shiga tambayar abunda akayi mata momi ce ta faɗa masa,
nan ya hau Mairo da masifa “Allah in baki yiwa mutane  shiru ba saina miki shegen duka yar iskar yarinya”




kara buɗe baki Mairo tayi tana kuka kamar wata karamar yarinya,
Gwaggo ta kalli Halilu “kaga ko ana neman tayi shiru kaxo kana mata masifa ko”
“to Gwaggo in tana son xuwa ki barta taje mana in kuma ba zataje ba su su kama hanya kar dare yayi musu”
“to waya hanasu tafiya ai sune suka hure mata kunne tace saita bisu”
Qasin yace “a a Gwaggo karkiyi zargin kowa itace kawai dan kanta tace saita bimu”




momi dai haushine yasa ta fice ita da mansura suka bar Abbah da Qasin.
Halilu yace “ni wlh da kina yarda da kinbarta taje su da kansu zasu dawo da ita dan mugun halinta”
kin yarda Gwaggo tayi saida taga su Abbah zasu wuce gashi Mairo na kuka kamar ranta ya fita sannan ta amince.


aiko Mairo kamar ta zuba ruwa k`asa tasha da gudu ta nufi ɗaki ta shiga haɗa kayanta cikin bakko (ghana most go).



*9*
bayan Amimcewar Gwaggo saida akaje gurin tsoho tare da Mairo aka faɗa masa shima kin amincewa yayi saida yaga abun na Mairo bana wasa bane sannan ya yarda sosai Abbah ya jidaɗi daman tun rasuwar kanensa yaso a bashi ita Gwaggo ta hana,
sai goshin magariba (kusan magariba) suka kama hanya



so huɗu ana tsayawa Mairo nayin amai jikinta sai rawa sanyi yake nan da nan zazzaɓi ya rifeta saida aka kashe ac ɗin motar,



*_9:37pm….._*



suka isa Sokoto koda Qasin yayi farkin Mairo na rungume jikin momi tana bachi.



saida kowa ya fita sannan momi ta tasheta 



a firgice ta fito motar tana ɗaga kanta hankes ya cika mata ido,



gidan sama ne mai hawa ɗaya ko ina an manna gulof murza ido Mairo ta shigayi dan gani take kamar mafarki take.
bayan momi ta fito Qasin ya rufe motar shida Mansura suka nufi part ɗinsu daman Abbah tuni ya wuce nashi part ɗin,
Mairo na tsaye tana kalle2 momi ta rik`a hannunta zasu shiga ciki Mairo tayi tsaye tana kallon kofar farlon da alama tsoro take ji,
faɗuwa gaban momi yayi tana tsoron kar kuma tace bazata shiga ba.




“lafiya zomu shiga ciki mana”



shiru Mairo tayi ta lakkafe kafaɗa



saida Momi ta maimaita sannan tace “nan ne gidan?”



“eh nan ne zo mu shiga ciki”



tsaye tayi kamar bazata shiga ba



momi bata bi ta kanta ba taja hannunta suka cigaba da tafiya.



jiki a sanyaye Mairo ta shiga farlon tayiwa hannun momi mugun rik`o Usman na kwance saman doguwar kujera yana bachi siraj kuma na kallo,
shine ya taso ya tari momi da far’ah “sannu da zuwa momi”
“yauwa sannu siraj baka kwanta ba?”
kayan dake hannunta ya k`arɓa yana faɗin “eh ban kwanta ba wacece wannan momi?”
kallon Mairo momi tayi “qanwarka ce”
“daga can aka zo da ita?”
“eh bari na shiga ciki”
Up stairs momi ta nufa Mairo na rik`e da  hannun Momi,




suna shiga bedroom Momi ta faɗi zaune saman bed ita da Mairo,



 har lokacin tana  rike da hannunta 
bayan sun ɗan huta Momi ta nunawa Mairo tawel “jeki ki ɗauki ga tawul can ki ɗaura sai kiyi wanka kici abinci ki kwanta”




kai Mairo ta girgiza “a’a nidai Gwaggo wanke min kafafu kawai take in zan kwanta bata min wanka”



“to mu wanka muke in zamu kwanta tashi ki cire kayanki”



tashi Mairo tayi ta nufi gurin da Momi ta nuna mata.



itama Momi tashi tayi ta shiga cire kayanta
saida ta gama wanka sannan ta kira Mairo tayi mata




tare suka fito  Mairo bata tsaya jiran komai ba ta faɗa saman bed



Momi kuma ta nufi waduraf tasa kayan bachi ta ɗaura zane sama bayan tasa hijab ta kabbarta sallah.
koda Momi ta gama sallah Mairo tayi bachi.




tana cire hijab ɗinta ta nufi down stairs.



bata daɗe ba ta shigo ɗakin da plate din abinci a hankali ta shiga tada Mairo amman hakan bai hanata farkawa a firgice ba.



“k`arɓi ga abinci kici saiki kwanta”



kin k`arɓa tayi ta tsurawa Momi ido can kuma ta mayarda su gurin abinci.
sakwarace da miyar agutsi da namomi hannun tasa ta k`arɓa “ni bazan iya cinyewa duka ba”




“ci kibar saura”



kusa da ita Momi ta zauna tana amsa waya.
saukowa Mairo tayi kasa ta hau cin abinci




cikin yan mintuna ta kare ta tashi tana suɗar miyar dake plate ɗin duk ta ɓata gurin da miya kamar mai ɓararen baki.



 nunawa Momi hannunta tayi “na kare ina zan wanke hannuna?”



toilet Momi ta nuna mata



tana gyaran ɗaurin tawul ta shiga toilet ɗin
koda ta fito Momi ta gyara gurin tana mopping




tsaye tayi har momi ta kare ta nuna mata gado “hau ki kwanta”



ba musu ta hau Momi taja zanen rufa ta lulluɓa mata.



ta kashe wutar ɗakin ta kunna ta bedside lamp ta nufi kofa,



 Mairo na ganin zata fita ta tashi da sauri “ni kaɗai zaki bari nan?”



Momi daga gurin da take tsaye tace “tsoro kike jine?”



“eh bazan iya kwana ni kaɗai ba”



“babu abunda zai sameki ki kwantar warki kiji?”



“aa ni bazan yarda ba”



saukowa tayi ta nufo Momi.



Momi tace “to bari na kunna miki wutar saiki kwanta kamin nazo yanzu zan dawo jeki kwanta”



lake kafaɗa tayi “a a ni bazan yarda ba”



tsawa momi ta katsa mata “wuce kije ki wanta nace”



jiki na ràwa Mairo ta faɗa saman gado ta ɗanne fuskarta cikin katifa,



Momi na ganin haka ta taja kofa ta fice
kuka Mairo tayi tayi kaɗankaɗan kuma ta kasa ɗago kan dan tsoron kar taga wani abu har bachi ya ɗauketa.
*_washe gari….._*




tunda asuba Momi ta tada Mairo



 a firgice ta farka jikinta sai rawa yake hannun momi ta rika suka shiga banɗaki tare sukayi alwala.



bayan sun fito Mairo ta nufi yar zakarta ta zazzage ta ɗauki wata atamfar kauye tasa tare da hijab ta fara sallah,
tana sallamewa komai bata tsaya yiba  ta koma bachi.




sai 8 da minta ta farka koshi dan siraj ya tada tane.



da murje murjen ido ta tashi tana mik`a idonta a lumshe tana soma kiran gwaggo.



“ke tashi momi na kiranki nace”



‘to’ tace tana turo baki kamar ta fasa kuka



 shidai bai tsaya jiranta ba ya fice,
saida ta gama gunguninta sannan ta tashi ta nufi kowa duk jin take bata son gidan,




tana fitowa ta hango farlo down stairs.



wani irin ihu ta saki saboda juwa data gani tayi bayabaya tana kiran “na shiga uku wayyo Gwaggo na bani mutuwa zanyi”
duk kai suka ɗago sun Kallonta daga dining area siraj ne ya fara tambaya “lafiya?”




cikin kuka tace “na bani bazan iya saukowa ba na shiga uku Gwaggo”



duk fashewa sukayi da dariya banda siraj da yaja tsaki sai kuma Momi data hau mata faɗa “ke wai wane irin iskancine dake haka haka kawai zaki rika yiwa mutane uhu”



Qasin dake tsaye ya kalli Momi yana murmushi “tsorone taji momi kinsan yar kauye ce”



“to dan taji tsoro sai tayiwa mutane ihu iskancin da takeyi can kauye nan bazan ɗauke shiba”



tea cup ɗin dake hannunshi ya aje ya nufi up stairs.
hannunta ya riko ta rumgumeshi iya karfinta ta kulle ido gam sannan suka sauko.




har suka isa dining bata buɗe idon ba saida taji an zauner da ita sannan ta buɗe ido tana kare musu kallo,
da Qasin ta fara sannan Usman, Siraj sai kuma ta juyo gun Nura.




kofin tea Momi ta aje mata idonta cike da hawaye ta ɗauka ta kai baki



bata ajeba saida tasha rabin kofin Siraj da Nura da Usman sai dariyarta suke Qasin Murmushi yayi ya kalli agogon hannunsa yace “Momi ni bari na wuce gurin aiki”



“to Allah ya tsare”



“Amin”



saida ya kara kurɓa tea ɗin sannan ya fice.
Usman ya kalli Mairo yana driya yace “bakison bredin hala?”




banza ta masa har Momi ta kare cin abincinta da Usman suka tashi.

sannan ta ɗauki bredin tana hawaye ta rika somawa kamar turo da miya tana ci.



*10*
Siraj dai sai kallonta yake can yaji bazai iya zurewa ba yace “wai mi kike yiwa kuka?”



cikin kukan tace 



“ni gida nake so”



dariya yayi “gida?”



“eh”



“mi aka miki to?”



“bana son gidan nan bana son gida a sama kuma mumi faɗa take min”



fashewa sukayi da dariya Nura yace “hala baki taɓa ganin gidan sama ba?”



“eh nidai bana sansa”



tashi nura yayi yana faɗin “amman gaskiya kauyancinki yayi yawa”



k`ara turo baki tayi kuka nason fito mata fili Siraj dai kallonta kawai yake har ya kare cin abinci ya tashi,
Mairo tasowa tayi ta dawo kusa da doguwar kujera dake parlour ta zauna har lokacin hawaye take.




jin tafiyar momi yasa ta ɗago kai tana kallon up stairs “lafiya kike kuka?”



fuskar momi a haɗe take mata tambayar



 “gida nake so gurin Gwaggo”



murmushi momi tayi “karya kike yi ai ke kika dage saikin biyomu jiya jiya muxo yau kice a kaiki gida babu yadda bayiba akan ki zauna kika ki”



hannayenta ta haɗe tana rokon momi 



“na daina mumi bazan sake cewa a zo dani ba”



“uhmm tashi muje kicin kiyi wanke wanke”



lake kafaɗa tayi “ni ban iya wanke wanke ba”



kunneta momi ta kamo “ke bari kiji na faɗa miki iskancin da kike can kauye nan bazaki min shiba”



kuka Mairo tasa sai kiran Gwaggo take.
haka momi taja hannunta suka nufi kicin.




gurin wankewanke momi ta nuna mata ta “oya sa hannu ki wanke” kallon momi tayi idonta cike da hawaye tace “wlh ban iya wanke wanke ba”



“dukanki dai kikeso nayi kamar zakice baki iya wanke wanke ba kuma rikon kauye ba birnin ba koki wanke shi ko na miki dukan tsiya” momi na kaiwa nan ta juya tabar kicin ɗin,
 haka Mairo ta hau wankewanke tana kuka




sama take wankewa dan har ga Allah bata iya ba tunda Gwaggo bata sata aikin komai inba sharaba koshi inta ga damane take yi.



haka ta wankesu samasama kofukan da akasha tea ma ɗaurayisu kawai tayi ta aje,



koda ta kare ta fashe tea cup ɗaya kuma duk ta ɓata gurin da ruwa ɗan kwalinta tasa ta goge ruwan ta jefashi bayan firjin.



jikinta a sanyaye ta nufo parlour tsaye tayi tana kallon momi dake zaune saman kujera.



ganin bata kula taba yasa ta karaso kusa da ita “na kare”



sai lokacin momi ta kalleta “to wuce kiyi wanka”



“ina?”



“inda kika ga na miki jiya”



lake kafaɗa tayi tayi baya baya “ni bazan hau sama ba gaskiya”



taɓe baki Momi tayi ta cigaba da kallon tv.
*****




ranar Mairo wuni tayi tana kuka saboda faɗan da momi tayi mata kuma ta hana mata abincin rana saboda takiyin wanka.
da magariba Mairo na gefen kujera zaune Momi ta nufi kofa da sauri Mairo ta tareta tana “ni ki bani abincina yunwa nake ji”




tureta momi tayi saida ta faɗi wani mahaukacin ihu ta saki momi saida ta rufe kunnuwanta ta hau shurenta.



“lafiya?”



Qasin na shigowa abunda ya fara tambaya kenan
momi ta nunata da yatsa “rainin wayo ne da ita so nake na gyara mata zama”




karasawa yayi ya tada ta “mi tayi momi?”



“iskancin da take can kauye ne take son tamun”



kallon Mairo yayi “mi kika mata?”



cikin kuka Mairo tace “ban mata komai ba muguwace azzaluma ƙk`atuwar banza kuma ban yafe miki b-”



da sauri Qasin ya rufe mata baki “ke karna sake ji ba mamanki bace”



kai ta girgiza tana hawaye “ni ban sonta ba mamana bace”



kwafa momi tayi “aiko kashinki ya bushe cikin gidan nan”



“wai minene mafarin wannan abun ne momi?”



momi tace “rantsuwa nayi duk batayi wanka ba bazan bata abinci ba”



kallon Mairo yayi “ke mi ya hana miki wanka maryam kin fi son ki zaina da k`azanta?”



“a a itace tace saina hau saman sama sannan nayi wanka ni kuma tsoro nake ji”



kallon momi yayi yana murmushi “kinji momi tsoro take ji kinsan ko ɗaxun saida aka saukarda ita”



“ba wani tsoro iskancine kawai”



“ba iskanci bane ko?”



ya tambayi Mairo kai ta ɗaga yace “bata hakuri sai kuje tayi miki wanka kuma karki kara rashin kunya kinji”



saida ta daɗe sannan ta kalli momi kasa2 tace “yi hakuri bazan sake ba”



da ita da dashi duk tsurawa momi ido sukayi sunajiran abunda zatace
saida ta watsa masu harara sannan ta fixgi hannun Mairo suka nufi up stairs.




kankame momi Mairo tayi ta rumtse ido nan momi ta sakar mata hannu “wuce da kanki”



kuka tasa nan momi ta katsa Mata tsawa dole ta rike karfen ta rika hawa da rumtsen ido har ta haye.



momi ce tayi mata wanka Mairo kan ana mata wanka tana tunanin yadda za ayi ta tsera ta gudu ta bar gida,



bayan sun fito momi ta wulgo mara kayanta ta sauka downstairs ta ɗebo mata abinci.



*_washe gari….._*



tun asuba momi ta tada Mairo bayan sunyi sallah bata barta ta koma bachi ba suka nufi kicin.



tare suka haɗa komai na breakfast ranar momi batayi mata faɗa ba dan tare sukayi komai duk da ba wani iyawa tayi ba daman momi abunda bata so ta saka aiki kaki da kuma kuka.
*_8:30am….._*




suka kare hada komai momi ta nunawa Mairo gurin da zata jera.



ba musu ta rika jera abinci badan ranta yaso ba sai dan gudun matsifar momi aranta kan ɗebima momi albarka kawai take tana aiban ta’ta.



Mairo ce ta fara zama bayan ta jere breakfast ɗin sannan momi,



Usman da Nura dake zaune saman kukera suka nufo dining.



Siraj sai janta yake ita kuma ta wani haɗe fuska kamar ta fasa kuka .



momi da kanta ta zubawa Mairo breakfast su kuma suka shiga zubawa kansu.



Nura ya kalli Momi yace “yau yaya ba zai karya nanba ?”



momi tana k`ok`arin zuba ma kanta tace “zaizo mana ai kasan nan yake karyawa kila bai tashi bachi bane”
kamar daga sama sukaji an banko kofar parlour duk juyawa sukayi suna kallon Qasin daya shigo fuska a haɗe.




yana karasowa momi tace “lafiya?”



takardun dake hannunsa ya nunawa momi cikin zafin rai yace “kwangila ce Yarima yakai a kanfaninmu”



murmushi momi tayi “wow…-”



tare numfashinta yayi ya juyarda fuska “haba momi kamar bakisan Yarima ba he just want to ruin my life kuma deal ne between me and him saina gani tsakanin ni da shi who is going to be loser”
tashi momi tayi ta daga hannunta da niyar yi masa magana sai kuma ta kasa jefarda takardun yayi ya fice cike da bacin rai.
Reply


Messages In This Thread
*MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:30 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:33 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:36 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:36 AM
RE: *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* - by Gimbiya - 10-11-2018, 11:38 AM

Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 859 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 781 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 749 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 889 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *MAIRO*BY*KHADEEJA CANDY* 0 794 Less than 1 minute ago
Last Post:



Users browsing this thread: 1 Guest(s)