08-22-2017, 12:18 AM
YAN NAJERIYA NA MATUKAR FARIN CIKIN DAWOWAR SHUGABAN KASA,MUHAMMADU BUHARI.
A safiyar jiya asabar muka wayi gari da labarinda jami'in yaɗa labarai a fadar shugaban kasa wato Femi Adesina a inda ya bayyana cewa anasa ran dawowar shugaba Buhari Najeriya a jiya. Ɗumbin mutane sunyi tururuwa zuwa filin jirgi na Nnamdi Azikwe dake Abuja da kuma bisa hanyar zuwa fadar shugaban ƙasa don nuna farin cikin dawowar shugaban bayan yayi fiyeda kwanan ɗari a birnin Landan don jiyyar rashin lafiya da yayi fama.
Galibi dai yan Najeriya da dama suna nuna kaunar shugaba Buhari ne saboda sunce mutum ne mai adalci da kuma kyamar cin hanci. A yayinda shugaban ya tafi Landan don neman lafiya, da yawan Yan Najeriya suka dukufa wirin yi mashi addu'a da kuma fatan dawowa cikin koshin lafiya.
A yanzu dai ana saurare zuwa ranar litinin ina ake sa ran Shugaba Buhari zaiyi bayani. Allah kaimu litinin lafiya, Amin.