Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*TAFARU TA K'ARE* by *Billy Galadanchi*
#1
*????TAFARU TA K'ARE??‍♂??‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association*

                     01
.......*******.......
    
     Tunda suke maganar gawar kurun ta tasa a gaba ta dask'are a wurin bata ko motsin kirki, yanda kasan wata statue haka ta tsaya k'ik'am, kowa da abinda yake fad'a amma banda ita kowa yana masa adu'a banda Ameena, zaune kurun take kaman wata icce, kuka take amma bana hawaye ba, kukan zuci takeyi gashi k'iri k'iri ta kasa gaskata mutuwar nan,  ga gawa agabanta tunka a nad'e gawar ta ganta amma tana gani tamkar ba gawar bace ba, muhammad d'inta ze tashi dogon sumace yayi yaya zasuce ya mutu? Su k'ara masa lokaci mana  ze farfad'o...ta ayyana a ranta!!! Mazane suka shigo suka durk'usa suka d'auki gawar ta muhammad dake cikin farin k'yalle, kana an ninninkeshi acikin tabarma a zura a makara!! Mik'ewa tai ta rike makarar

"Me kenan zakuyi? Ina zakuje da muhammad, ku barni ko a haka zanta kallon abuna, kurun ku bud'emun fuskar sa, dan Allah karku tafi dashi, ku k'ara masa lokaci dogon suma ce yai" Tausayinta kowa keji, sun kula bata cikin hayyacinta mahaifi muhammad da mahaifin ta sune sukazo suna k'ok'arin b'anb'are Ameena daga jikin makarar data kama ta rirrik'e hannu bibbbiyu da k'yar da sid'in goshi ta sake shima seda k'wace da k'arfin tuwo! Se sambatu takeyi

"Karkumun haka, Akwai maganar da Muhammad ze gayamun daren jiya, ban saurareshi bane ku barshi ya gayamun, koda iya itace, ku taimakamun muhammad ya sanar dani abinda yakeso ya sanarmun, idan baku barshi ya fad'amun ba  nima mutuwan zanyi, idan munje cen seya gayamun" babu wanda ya saurareta de d'aki aka wuce da ita aka kwantar da ita masu rarrashi sunayi masu ban baki sunayi amma se sambatu take ga alama Ameena batasan ma metakeyi ba ta zauce mutuwar muhammad ta mata dukan a kawo wuk'a kenan!!!! Ganin abun bame k'arewa baneba ya sanya  su daddym Muhammad suka kira likita yazo ya sharara mata allurar bacci.

***************

   Mustapha kabeer sharad'a da kuma Muhammad D'ayyib kagara Aminan junane, tun tasowarsu secondry school d'aya suka halarta  kuma ajinsu d'aya, had'in kansu yakaisu ga zamtowa aminan juna har sukaje jami'a suka karancin building enginearing a tare, lokaci d'aya suka kammala bautan k'asane kurun ya rabasu kowa yaje nasa garin, bayan sun kammala a tare suka soma harkokinsu tunkan su samu aiki, Alhaj mustapha shine ya soma samun aiki a wanj kampani me zaman kansa na gine gine, yayinda Muhammad ya samu aikin sa daga baya a k'ark'ashin gwamnati, seya kasance mustapha yafi muhammad k'arfi haryake taimakonsa daidai gwargwadon iyawarsa, dama cen shi mustapha d'an wanine sunada arziqinsu, yayinda  shi kuma muhammad iyayensa ba masu kudi mahaifinsa ma'aikacine kurun a k'ark'ashin gwamnati me rufin asiri......

   Haka har sukayi aure suka hayayyafa, yayinda Muhammad ya zamto yaro a k'ark'ashi mustapha kasan cewar shi mustaphan yakai ga company nasa na kansa, dukda haka seyawa muhammad manager na company d'in inda shima lokaci d'aga ya bunk'asa kasancewar ana matuk'ar jida sharad'a builder's kasancewar su k'wararru masu iya zane da gini na zamani....basu tsaya anan ba seda suka kaiga kawo kayan gini daga waje wanda akasari acen kurun ake samunsuu kayan qawata gida da sauransu, da wannan suka yada a zango a Abuja harkansu ta tsarin gine gine ya bunk'asa akeji da Sharad'a builder's sosai da sosai....

************
   Muhammad  sunusi shine babba awurin Alhaj muhammad, yayinda yakeda k'annensa susu 4....Yusuf shine me binsa se kuma Bunyameen daganan se yara mata Salma da zuhra, matarsa d'aya wannan ya sanya suke uwa d'aya ubansu d'aya...

Alhaj Almustapha kuwa ya jima da aure be haihu ba, dan kuwa har muhammad sunusi yakai shekaru 12 aduniya be haihu ba, seda yakai kusan 13 sannan aka haifi Ameena yarinyace da akeji da ita wanda seda ta share shekaru goma sha hud'u tukunna mahaifiyarsu ta haifi wani Namijin dayaci sunan kakan sa Kabeer anace dashi Kb junior.

*Mom Nu'aiym*

Na sadaukar da wannan littafin ga member's na k'ungiyar haske writer's Asso.
[6/8, 18:48] +234 903 923 3534: *????TAFARU TA K'ARE??‍♂??‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                          02
*Wani lokaci can baya kafin mutuwar Muhammad*

     Ameena ta kasance yarinya mafi soyuwa ga iyayenta, yayinda mahaifinta ke ganin baze tab'a iya aurar da ita a wurin dabe sani ba, shida kanshi ganin ta kammala secondry school ga kuma girma ya taso mata ya sanya kai tsaye yawa Alhj muh'd magana akan yanaso a had'a auren Ameena da muh'd sunusi, beja dogon surutu ba kuwa ya Amince inda suka had'e kan 'ya'yan su suka gaya musu k'udurin su, lokaci d'aya Muhammad sunusi ya aminta da wannan batun amma Ameena seta kafe akan bata sansa, iyayenta basu biye mata ba, Alh mustapha sam baya baiwa yaro daman yin iskanci koda yake a sangarce Meena ta tashi sam ba kwab'a ita a harkan ta...wannan kenan

****-----****
   Meena yarinyace me matukar rashin kunya, batada kirki kam zance sabida batajin kunyar gaya maka magana komai girman ka, koda yake sam ita shiga hurumin mutane ba halinta bane, bata shiga sha'anin kowa batada ma yawan surutu sedai kam idan aka tab'ata batada hakuri ko nan dacen,ga yawan masifa dakuma rainawa mutum, babban dalilinta nacewan batasan muhammad be wuce  na ganin mahaifinsa a k'ark'ashin mahaifinta yake ba, takuma rainawa shi kansa aikinsa na Lecturing yakeyi, dukda yake yana sana'o i iri iri, yana ma shagonsa kacokam na siyar da wayoyi da kuma na siyar phone accesories, sosai shop d'in yake babba kuma ba laifi an sanshi a Abj Sannan kuma ambassador ne  na samsung galaxy kacokam yana musu ciniki sosai, duk kaiwan ka k'arshe wurin hasada baka isa kace muhammad baida abin hannunshi ba daidai rufin asiri, amma dukda haka meena ta raina ajinsa da dukiyar sama kacokam wannan kenan.

    Sosai ta tarnak'e fuskar nan agaban ya moh kaman yanda ake kiran sa kowa da kowa qannensa, friends nashi ma moh suke kiransa, shi kuwa bawan Allah ya rausayar da kannan wane ze mata kuka

"Haba My meena, dan Allah ki saki ranki, ki tausayamun mana, laifi nayishi amma kiyi hakuri"  wani mugun kallo ta wurga masa   sannan tace

"Kaje ka tara mata a office d'inka kuna iskancin daka saba ni mezesa kazo ka bani hak'uri?, ni kaddai ka kuskura ka k'ara cewa na bar motana a gida zaka wuce dani school, tunda seka gama sallaman dadironka kake saurarona" da sauri ya d'ago ya kalleta cikin jin zafin kalamanta, amma yaya zeyi da sanyin halinsa be iya fad'a ba, kazalika sam shi soyayyar meena bazata barshi yaci zarafin taba, se kuma ya mayar da dubanshi zuwaga student dake wurin parking lot d'in sun kashe kunne suna saurararsu, sadda kanshi yae a k'asa ya furta

"Meena na mushiga mota, mui magana aciki kinga akwai mutane anan" kallon mutanen tayi cikin ko ajikina

"Hmmm to ai agabansu kake tara 'yan mata a office, ni ina ruwana su jiyo mu mana" Shiru yai na wani lokaci kanya shige motar ya zauna yasani masifar ta zesa ta shigo dan bata k'arisa fad'an ba, zama tashigo tayi wanda da sauri ya locking motar bayan ta zauna ya balbala AC ya kalleta

"A har kullum Ameena ina miki magana akan rashin ganin girman na gaba dakai, ya kamata ki sani kodan inasonki bashi bane ze baki daman rainani har haka ba, ki gane mana nifa yayankine sannan kuma abinda yake bak'anta raina dake shine koda anyi taron Idi ne babu ruwanki zaki daddage kicimun mutunci" kallon mara kyau ta wurgo masa

"Kafasa auren mana ko dole ne sena aureka" river yayi ya haura hanyar barin school d'in gaba d'aya

"Bazan tab'a fasa aurenki ba, koda zakimun fiye da abinda kika mun yanzu, 'yan matan dakike cewa ina tarawa a office wannan kema kinsani ba halina bane ba sam, students ne kuma akwai abinda ya kaisu office d'in wanda ya shafi karatun su, a har kullum kiyi komai dan Allah kuma ki bari dominsu, sanya tsoron Allah aranki akan dukkan komai shinake so kiyi Wannan yazama first priority naki" Shiru tamasa yanzu kam batada abin cewa, seda suka kai k'ofar gidan su ya parka ya miyarda dubansa kacokam zuwa gareta

"Yau zanzo bayan isha inshaa Allahu, idan dai ina cikin masu rai da lapiya" hararar sa tai

"Mtsew se anyi magana kadinga kirawa mutane Allah, ka sani wlhy duk yanda zanyi senayi naga baka auren ba, sabida wlhy muhammad bana sonka da aure dai, damacen mutuncin damuke aidan ka tsaya matsayin da Allah ya ajiyeka ne, banda haka muhammad aini d'innan matar manya ce ba irin ku" Sadda kanshi yae k'asa yana sanya murmushi a fuskarsa, shi harga Allah zan tuttukan meena yana d'aurasune a matsayin k'uruciya tuburan dukda ya kula hadda hali mara kyau na rashin sanin darajar d'an Adam...seda yaja fasali ya nisa sannan yace

"Ban isa na hanaki tunanin abunda kike so kiyi tunani ba, amma dai ki d'aukaka kalmar nan ta d'am adam, so dubu miliyan me kud'i ya talauce kazalika so miliyan ba adadi talaka ya zarce yayi kud'insa, banawa kaina fatan k'azamar dukiya amma nasani ina daga cikin masu nasara, shallake tunaninki wurin kasa gane darajar d'an Adam abune dayakemun ciwo fiye da yanda kike yayyab'amun magana.....a har kullum zantuttukan danake furta miki nuni ne da lokaci yayi daya dace ki dage ki saisaita nutsuwarki ki gane kin soma girma ki baiwa d'an adam darajar sa" tsaki taja

"Koda wane lokaci seka rik'a zazzagamun zance tamkar a wurinka aka k'irk'iro hausa, kodaya ke ba abin mamaki bane ba dan kare yayi haushi ka gaza gane inda ya dosa, danni harga Allah bana fahimtar kalma ko d'aya acikin wa 'yannan zantttukan naka marasa kan gado" nisawa yayi yace

"Kin kyauta sosai da kika kirani da kare, bazaki gane haushin kare ma wani zubin yanada ranar saba se sanda aka yasheki dankin gagara gane zantuttukan hikimar dake cikin haushin na musulmin kare ba, ina jiye miki ranar da *ZATA FARU TA KUMA K'AREWA* me raina halittun mahalicci, wlhh kowa da ranar sa, wani zubin idan nayi nazari naga yanda mutane dubun dubata dana taso dasu ban rayu dasuba, dubun dubatar dana girma dasu ban gansu ba a yanzu, dubu miliyan da fuskarsu ta zamemun tarihi sena sassautawa kaina wahalar dake cikin jin zafin kalmomin mutane da Allah ya ni'imtani dasu a yanzu, mutane da yawa na rasa su  a lokacin da nake cikin tsananin buk'atar  su a kusa dani, kisan wannan"

  "Dazaka taimaka ka sauya akalar harshenka zuwa yaren nasara wataqil dazanfi fahimtar inda zantuttukan suka dosa, nifa sunusi wlhy kana bani wahala Dan Allah ka dena damuna" Murmushin dai ya sake k'awata kyakyawar fuskar sa dashi

"Meena wai mesa kika rainani? Ina kinsan koba komai ni yayankine" Guntun murmushi tayi

"Gaskia kai yaya nane, am zan iya shiga ciki?" Bece mata k'ala ba ta b'alle murfin motan ta fice kurun

   Barin gidan yayi zuwa gida yana tunanin halin Ameena, ko k'awayenta suke zugata oho.

***********

    Bayan isha yazo gidan, yana daga zaune acikin kujerun da aka zagaye hot na gidan dasu, dayi shiru cikin fad'uwar gaba ya sani sarai duk yazo gidan ransa a b'ace yake komawa, Dress ce ajikinta kalan tokan murhu, se mayafi siriri data yane kanta dashi, tana zuwa taje kusa dashi ta sumbaci kuncinsa had'e da rungumesa kanta koma ta zauna

"Sannun kafa ina fatan yauka shirya nunamum soyayya, dan naga kasha wanka, koda yake gidadancin a zuci yake" murmushi yai

"Harse yaushe zan miki magana newai kiji?, ki gane nifa har yanzu ba muharraminki bane ba, ya kamata ki dena k'ok'arin tab'ani ko sumbata na" mtswww taja masa dogon tsaki

"Sarkin tsoron Allah yan duk duniya, ko larabawa da aka tsatsafo musulunci daga gunsu sukan rungume junansu da sumba, kaifa wlhy mugun bak'auyene muhammad" kallonta yai

"Suma larabawan ba kowa suke hugging ba meena, mesa ne a rayuwa kullum kin fiso mui fad'a ne wai?"

Ni wlhy Daddy ya cuceni, friends d'ina kullum zakaga samarinsu suna rungunarsu sumba har abaki amma bagidaje ne kai na k'arshen tarihi, bakin ciki kakemun na rage zafi bayan kowa tanan ne yake ragewa" kallon ta yae, wato dai bilhaq sauyawar sauyawa halayen yarinyar nan hadda friends wannan wace irin fitsara ce mace da kanta take roqon namiji ya tab'a ta, tamasan kalmar rage zafi me take nufi kuwa? Meena shekarunta sha bakwai yaushe tasan maza har haka, sassauta muryar sa yae

"Ki Gane nufina Meena na bawai banaso nake rungumarki bane konake kiki sumba, abubuwane haramtattu da Allah ya haramta a tsakanin mu, be dace ace munayi yanzu ba kyau ya dace ki tsaya ki gane cewan komai yanada lokaci,idan lokacin mu yae sekiyi yanda kikeso dani" kallon sa tae

"Me zanyi dakai muhammad? Karka gayamun wani makamancin had'a shinfid'a, muhammad aiko aure mukayi ba wannan tsakanina dakai, kurun dai wannan d'in ni a wurina gaisuwa ce tsakanin saurayi da budurwa damma kai kyakyawane damezan runguma kona sumbata a jikinka?" yanzu kam dariya ta bashi ya kula abubuwan na turawa sha'awa suke bata yace da ita

"Naga message naki akan sabuwar waya kike so, haba Ameena, wayarnan dududunta wata biyu fa, mesa zakice se an siya wata? Kyau ai tayi ko 6 month ne kodai a k'alla one year" 

"Kagafa matsalan ka, wannan ne ya sanya arayuwa we never get along, Kana kallo fa zulfa wayoyinta uku, ta qarshen satinta biyu aka kawo mata sabuwa, amma ni wayoyi biyu kuma duk sanda na nemi canji sekamun wulaqanci, kasani dai bawai karkashin kowa ubana yake ba gashin kansa yakeci mesa kake mun haka, idanda yanzu zance ga abunda nakeso zemun, kurun dai ina dubawa ne naga kowacce fiancee d'inta ke mata abu"  shiru yai yasani zaginsa tai a fakaice amma shi babbane baze biye taba, seda ya had'iyi wani yawu me d'acin gaske sannan yace

"Wacce kikeso yanzu?" Gyaran zaman mayafin ta tai

"6+ nakeso shine d'an yayi, dakuma samsung galaxy note 6" Jinjina kanshi yae

"Na hannunki fa, ki bani zan bada su" kallon sa tai

"Ina kyauta ka kawomun su? To ina ruwanka kuma da abinda zanyi dasu?" Murmushi yae

"Hakane shikenan ki bani nanda 1 week zan kawo miki, seme kuma kikeso?" Ya tambaya yana me kallonta cikeda k'auna"

"Wani lace ne kuma na gani dubu dari da goma shima inaso, qawata ke siyarwa" jinjina knsa yae
."meena na seme kuma?" Kallon shi tai so takeyi ta koreshi kamar yanda su zulfa ke bata shawara idan ta zama too demanding ze gudu ne amma kullum tana bashi wahala se kara tambayar ta yakeyi

"Shikenan kawai, se turaren kalan wanda ka kawon ranar nan, ina zanshi" 

"Duk za'a kawo, lace kuma sena miki transfer a bank ko?" Murmushi tayi

"Allah ya k'ara arziqi a soma siyamun da dari biyu haka" Ameen itace kalmar daya furta kurin

Mom Nu'aiym

Ayi bkin salla lapia.
[6/8, 18:50] +234 903 923 3534: *????TAFARU TA K'ARE??‍♂??‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                    03
"Zulfah wai kinsan sosai moh yakeda kafiya, wannan da kika gani wlhy da kafiri ne se yayi wuyar musukunta, wasu abubuwan danake sakawa yana siyamun  wlhy badan nai amfani dasu bane ba, amma mutumin baya tab'a nunamun gajiyawar sa, wani zubin daya fara zuba wa'azin sa zam dirza rashin m seyace toshi kenan, ke bama wannan ba zan ambaci abun dubu d'ari uku seya ce banda shifa? Akwai wani abu ya masifar k'ular dani" murmushi zulfa tai

"Lallai ma Meenal, tukunna baki gama ganewa halin man d'in naki ba, shifa koda komai nashi ze k'are akanki toze miki lalura ne, jarabace Allah yamai akanki, amma yanzu ke me kika gani, nifa bawai muni yakeda shiba indai kyakyawane kyakkywane ajin farko ma kuwa, matsalar sa d'aya k'auyanci kofa k'ananun kaya baya sakawa kullum da manyan kaya sekace babban malamin izala, ranar wata juma'a segashi hadda rawani da wandon sa a d'angale sekace limamin k'auye, iyaka dai shikam yadin nan na jikinsa fari ne k'al se k'amshin turarensa na oud al arab ke tashi duk inda yabi, sannan se tsafta har gulman motanshi nakejin student nayi ko lokacin damina bata datti wai sekace me wani isimin" Dariya suka sanya a tare tace 

"Iyakaci dai suce yanada tsafta kuma kyakyawa ne, to se meye? Nifa wlhy na tsani k'auyancinsa" 

"Nima haka, semun tara friends na auren 'yar sharad'a builder's azo aga wani bak'auyen miji" murmushi tai ranta yana sosuwa amma batai magana ba, kasancewar zancensa ya isheta haka...

**************
     Abubuwa sunwa Muhammad yawa ainun, yarasa sukuninsa kwana biyu  ma beko lek'a b'angaren na Meenal ba, kuma ko wata waya basui ba sosai  sabida ayyuka sun masa yawa ga skul gakuma harkan kayan wayoyinsa da suka iso yana clearing komai da kanshi, yana tsakiyan aikinsa wayansa ya k'ara, yasha mamakin ganin meenal ce aranshi yace "Meena!" Yasani Meena sam bata kiransa a waya seda wata babbar buk'ata, d'auka yai ya amsa kiran

"My Meena" d'an gajeran tsoki taja

"Yaa moh bafa meena ake cewa ba kace Meenal mana yanda kowa ke fad'a" murmushin sa me sanyi yae

"Ni kuma ina zan iya fad'an wani Meenal, ni bazan fad'a ba danban iya ba" kwab'e fuska tai

"To kaika sani" ta fad'a a fusace, gyaran zaman sa yai yana murmushi

"Meena nine kuma nina sani yau? Wayene ya fusatamun ke kike k'ok'arin saukewa akaina" harara ta chillawa wayayr tamkar yana ganinta

"Yau kusan kwanan 4 bakazo munba, na jejje office baka school nakira wayoyinka a kashe se jiya na samu baka picking ba, baka kuma kira misd col nawa ba kozan iya sanin mesa?" Nisawa yai dama yasani akwai rigima kwance a qasa inhar muddin suka had'u

"Auu dama yousufa dana aiko bazoba, wayan ne fa ya lalace mun kuma kinga wlhy nace ya sanar dake, tafiyan dole ya kamani" 

"Haba mana yaa moh, yanzu fisabilillah duk fad'in abuja a gunka suke siyan waya amma kace dami wayanka ya samu problem na tsawon kwana hudu, wane irin tsiyane wannan" kalmar ta tsiya ta daki k'irjinsa seya wayance kurin

"Akwai wayar danakeso ta kampanin samsung kurun sena tsaya jiran isowar ta, kuma se jiyan ta iso, sanda kika kira bata guna ana sakamun abubuwa" Shiru tai kantace

"Nima akawomun idan tanada kyau" be kula zancen ba yace

"Yau bayan isha inshaa Allahu zanzo na ganki my meena" batace masa komai ba ta yanke call d'in gaba d'aya tana mejin zafin sa, yau idan yazo zasuyita ta k'are....tana nan junior ya shigo

"Adda Meenal kizo inji daddy" seda k'irjinta ya doka haka ta mik'e ta soma tafiya tamkar wacce k'wai ya fashewa aciki zuwa parlor d'in...da sallamar ta ta shiga ciki taje cen kusa dashi sosai ta zauna na langwabar dakai

"Daddy gani" kallon ta yai

"Zancen zuwanki dubai had'o kayan d'akinki keda Momynki ya tashi gaskia, sabida biki nanda watanni biyu ne, so inaga sedai kuje shop na Mal kameel nama masa waya seki dauka komai daya miki a show room d'in" kallon daddyn tai idanta harya kawo ruwa

"Haba mana daddy, kayiwa Allah kabari sena kammala degree na, yanzu fa nake aji d'aya dudu wai shekaru na nawa? 17 fa daddy dan Allah karkamun aure yanzu kuma wlhy ni banason yaa muhammad dinnan" wani kallo ya wurga mata seda tashiga taitayinta

"Baki isa kinsa na sauya magana naba wlhy, ko kinaso ko bakyaso shi d'in dai shi zaki aura shasha kawai dabatasan ciwon kanta ba, kuma kinmayi sa'a dana barki kika soma xuwa jami'an, kika b'atan raina wlhy zan dakatar da karatun, muhammad kuma akan qiyayyar sa idan na kaiki gidansa washe gari inga gawarki tsabar k'iyayya" kuka ta saka inda Momynta ta b'ata rai kici kicin  sabida itama bason auren take ba, musamman dayake yarinyar batasan yaron an takura mata karshe, bar musu parlor d'in yae gaba d'aya ta janyo 'yarta  ta rubgume tana rarrashin ta

"Shi muhammad d'in shi zak'i k'unta tawa, seyace baya sanki, danni kaina baso nake ki aure wanda bakya soba"  bata kula mommyn bama tai shiru abunta tana kukanta...

*************
    Princess menene? Naga kinyi kici kicin da fuskar nan, ko wani ya tab'aki ne?" Idanta dayake ja jajir ta d'ago ta kalleshi 

"Yaa muhammad dan sanka da Allah ka taimakeni kacewa su daddy ka fasa auren nan bakasona, idan kamun wannan taimakon bazan tab'a mantakaba arayuwa ta" Da mamaki ya kalleta

"Mezesa na fad'a hakan meena? Akanme zanyi k'arya ni ina sanki, ke kije kice bakyasan nawa mana,idan har suka yarje mana namiki alqawarin zan janye daga neman auren ki har abada" harara ta wurga masa

"Dan kasan bazasu sauraraeni bane ba, shisa kace haka mugu kawai" murmushi yae

"Basu saurareki ba keda kike mace seni danake namiji? Tayaya zasu saurareni? Ta yaya kike nunamun hanyar shiga wuta k'iri k'iri, ina zanbi inga haske idan na kuskura na bijirewa umarnin iyaye na? Nisam bazan iyaba wlhy, kuma ki sani zuciyar muhammad cike take soaai da son wanda ke k'inta a halin yanzu yaya zata cutar da kanta da hannun ta?" Ta jima tana kallonsa bata k'ifta ba

"Dukda yake ka soma lailayo zance acikin harshen dabana ganewa, amma ga alama kamaso kace dani bazakayi yanda nake soba ko?" Murmushi yai

"Kin kusa soma gane zancena ashe, e haka nake nufi bazan yadda ba, bazance bana sanki ba hasalima aurenki idan kikaga banyiba tsarin me tsari ne hakan" Tafi mintuna biyar yaukam tana tunanin mezata ce masa se can tace

"Banji kana zancen kayan lefe naba" kallon ta yae

"Kayan lefenki suna nan hana kan had'awa" 

"To idan kuma aka sakamun abubuwan dabasu nake soba fa? Kallon ta yai

" seki wurgar ko?" K'ura masa na mujiya tai tamkar batason k'iftawa, taga alamar soyake ya rainata danyaga ankusa aurensu, banda hakan aida baya mata haka

"Milyan biyu nakeso ka bani, zansiya jakunkuna da takalmi da mayafai da kayan bacci" murmushi yae

"Zan iya baki 500k dudu lefen aina 2.5 ne zanyi" da sauri ta kalleshi

"So kakeyi ka bani kunya kenan muhammad? A rainani ace lefena beyi kyau ba?"  Yana murmushi ya kalleta

"To yaya zakiyi da abinda yazo daga iya k'arfina ni bana k'arya sune zarafina" batace masa komai ba tai shiru....ita datake shirin siyan jakunkuna na 50k guda goma sha biyu me 500k zata mata lallai ma gayen nan ya rainata 

"Yayi kyau idan bakada wani abun fad'a zan shige ciki" mik'ewa yai

"Nizan wuce my meena! Sekuma na dawo gobe" mik'ewa tai itama 

"Zancen wayana fa, irin naka" kaman bazeyi magana ba sekuma yace

"Yana mota meenal" kallonshi tai tasan baya fad'an hakan

"To muje ka bani" hannunsa ya zura acikin aljihun wandonsa yace

"Amma meena na wayoyi har uku a hannunki anya be miki yawa ba, kina auna yanayin tafiyar rayukan mu idan fa mune yau bafa mubane gobe, tsadaddun wayoyi har uku kije ina dasu my meena, dan Allah ki ringa d'aura abubuwa bisa mizani me kyau kike lissafi a komai na rayuwa, wlhy babu abinda bazan mallaka miki ba a duniya amma ina jiye miki ranar da bana nan" kallonsa tai

"Danla malam idan bazaka baniba ka rabu dani da wannan hausan na ustazan tsiya, meye aciki? Qawayena har masu wayoyi biyar akwai sekai kazomun da zancen kawai" shiru yae yana nazarin yanda zamansa da meena ze kasance yana rok'on Allah ya shiryeta Ameen......

"Muje na baki sauri nake" tsoki tayi

"Kaje da abarka banaso kaine matsiyaci, kuma zancewa daddyna ya siyanmun" bace komai ba se kallonta da yakeyi, harta karaci fad'anta ta juya kurun....a wannan lokacin daya je motarsa kifa kansa yae asaman stiring motar ya dinga rusa kuka tamkar wani karamun yaro, sosai soyayya tazo masa da rashin adalci yazamto mutum mara zuciya dabesan ya duba darajar kansa ba sam, ya dinga k'yale yarinya k'arama tana cinye masa zarafi son ranta....shi ciwon daya damesa ma ya damesa amma ba komai.

Mon Nu'aiym
Reply
Users browsing this thread: 1 Guest(s)