Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*MATAFIYA UKU* by Bashier Sufyern*
#1
*MATAFIYA UKU*

                 Written:
   _?Bashier Sufyern_
       *?Šarđaunah?*

Dedicated to all Hausa Writters..Auzubillahi minanshaidanin rajeem bismillahirrahmanin Raheem.

_Wassalamu wassalatu ala sayyidina Muhammad (S.a.w)_

*Dukkun Yabo suntabbaga ga Subhanu waataala ubangiji me ikon akan kowa...*


Wannan Labari me suna *MATAFIYA UKU* an wallafasa a shekarar 2019, na qirqireshi ne badan komi ba sedan na nunama jama'a wani karatu, shin wane irin karatu ne to nidai bazaku ji abakina ba sekun karanta, zaka iya neman cikakken littafin a kasuwar littattafan hausa....,??

Page 01

A qasar Misra anyu wani talaka jajirtacce me qoqari wajen neman halalinsa yakware sosai wajen fatauci sunansa Abu Nazif, mutum ne meson jama'a kuma me kyautata ma mutane domin talaucinaa baya hanasa taimakama wanda bekaisa qarfi ba, Abu Nazif yanada wani da guda daya wanda yake matuqar so, sunan dansa Jafar, Jafar yakasance  kyakkyawan saurayi me son labari wata rana Jafar yaje wurin mahaifinsa yana me neman izini akan yabarsa yanaso yai tafiya zuwa wani gari dake cikin Misra.

 Mahaifinsa yace masa yakai Jafar banaso kanisanta dani, amma tunda kace tafiyan acikin qasarmu zakayita to namaka izini kaje kadawo cikin aminci Allah ubangiji yakaika yadawo dakai lapiya..

Washe gari Jafar ya shirya yadauki guzurinsa ya rataye jakarsa yaje yaima iyayensa sallama suka samasa albarka, bayan jafar yayi tafiyan tsawon wuni guda lokacin da rana rakusa faduwa a lokacinne yanemi qasan wani itaciya ya zauna, bayan yazauna yafiddo abincin guzurinsa donufin yafara ci, yadiba zekai baki kawai seyaji wani abu ya fado gefensa yaduba seyaga mutum sekace yamutu daya matsa kusa dashi seyaji yana numfashi, koda Jafar yaga mutumin yana cikin mawuyacun hali na rai da mutuwa, sewani tunani yafado masa ya kwanto goran ruwan yasakamasa abaki, bayan yasha hankalinsa yakoma jikinsa se Jafar yace masa, "Yakai wannan bawan Allah shin wanene kai meye dalilin zuwanka wannan wuri, mutumin ya amsa masa da cewa yakai wannan saurayi ma'abocin taimako tabbaz kaceci rayuwata a lokacin da ina halin muyuwa da rayuwa tabbas ka tambayi labari me qunshe da al'ajabi....

  Mutumin yace Sunana Hashim bn Ahmad ni mutumin qasar istanbul ne, shekarata 62 ni bafatake ne wanda ya ziyarci qasashe da dama a cikin duniya kasani yakai Jafar wata rana na shirta tafiya fatauci zuwa qasar Rum kasancewar daga qasar Istanbul zuwa qasae Rum tafiyan wata uku ne, bayan nataso daga gida ina tafiya tare da bayina munyi tafiya na tsawin sati hudu, muna tafiya muna saye muna sayarwa har Allah yakaimu wani gari me suna Halwash tun kafin mushiga garin muka kama jin kide-kide natshi vayan mun shiga garin muka nemi wurun saukar baki muka yada zango, na tsunduma cikin gari domin kashe kwarkwatar ido...

tau anan zan dakata..

?Taskar Sardaunah
[4/5, 17:29] ‪+234 806 604 6091‬: _*MATAFIYA UKU*_


  ?Bashier Sufyern_
      *?Šarđaunah?*

http://www.bashirsufyan01@gmail.com


Page 02

Hashim Ibn Ahmad yaci gaba da cewa..

A lokacin dana tsunduma cikan gari ina ganin yanayin gari har takai ga nashiga kasuwa natadda mutanen garin sunata ciniki, se abin yaban sha'awa, bakomi ne yaban sha'awa ba a garin se ganin yanda kowa yake harkar dake gabansa bame kula da abinda dan uwansa keyi, bayan nagama yawace-yawace na nakoma gidan da muka sauka, na tara yarana gaba daya ina me umartarsu dasu shirya gobe da safe zamu taba ciniki cikin wannan gari, bayan kowa yakoma wurin dana umarceshi sena gishin gida da nufin inhuta, da kwanciyata barci yai awon gaba dani, ban falka ba seda asubahi bayan gari yayi haske muka shirya haja mukaje wurin sarkin garin muka kai gaisuwa yabamu izinin yin ciniki a kasuwar garin.

Bayan munyi ciniki munsamu riba me yawan gaske se muka siya wasu kayayyakin mukai gaba lokacin da muka shiga dokar daji muna cikin tafiya cikin wani daji ne me yawan surkuki kwatsam se muka fara jin ana mana ruwan kibiyoyi, kamun mu farga anmana banna sosai dan ankashe fiye da rabi cikin bayin da muke tafiya tare, bamuyi qoqarin maida martani ba semuka tsaya muna jiran muga ikon Allah.


   Kawai se muga hango wasu  runduna ta barayi sun mana qawanya suna masu unartarmu damu tattaro komi mu miqa masu, bayan sun anshe dukkanin dukiyar da muke tare da ita se suka kadamu suka tafi damu wani yanki na cikin dajin suna masu durfafar wani kogon dutse, koda muka shiga kogon se mukga kogon wani kato ne me girman gaske aciki ma akwai wasu fataken da aka kamo aka tsare, mudai munata kallon ikon Allah domin bamusan manufan mutanen ba da suka kawomu cikin wannan kogo...

   Jim kadan daga shigowarmu cikin kogom sega shugaban rundunan yazo yaname qare mana kallo, koda yazo kaina seya qyalqyale da dariya yana me cewa yakai Hashim kasani nayi shekara da shekaru iname jiran wannan ranan daza ace gashi nakamaka a hannuna, kasani nasha dana maka tarko kana tsallakewa tau yau gashi kazo kgon daba abinda ze fiddaka ciki face kazama gawa, koda naji wannann jawabi na shugaban wannan barayin senaji gaba daya jikina yadau rawa dakyar na tsaida natsuwata nacema shugaban wannan barayi nikau mena maka kakeson maidani tarihi, shugaban dakurun yadaka masa tsawa har saida hantar cikinsa ta kada yace kai hashim ni babu wani adawa tsakaninmu dakai kawai banaso ne naga kana cigaba da rayuwa inada wani boyayen dalili dayasa nakeso in maisheka tarihi, shugaban dakarun ya umarci da akaimu kurkuku akulle, bayan an tafi damu wani wurin daban acikin kogon se aka sakamu a kurkuku se aka hada qafafuwana wuri guda aka daure, nasha wahala me tsaninin gaske, bantaba tunanin sake cigaba da rayuwa ba, bayan munyi kwana uku acikin kogon ana gana mana azaba kala-kala, kwatsam a kwana na uku goshin magarba se muka jiyo sautin gudu na dowakai sun durfafo wannan kogon, koda barayin nan sukaji haka se suka miqe suka dibi makamansu suka futa da shirin yaki, jim da fitansu sega wani daga cikin masu gadin kurkukun da muke ciki, seyazo yabudeni yace yakai wanann mutun me tsawon kwana kasani shugabanmu Sarkin garinku ne yasa yakasheka domin biyan wata buqata tasa daban, kasani nima nan daka ganni wannan azzalumin yakashe man iyaye yakamani a matsayin bawa, zan kubutar dakaine sabida nasan kaiba azzalumi bane, kuma kasani cewa yanzu haka shugabanmu zasu gwabda yaki ne da rundunar birnin Hinal kaga koda bayan sungama bazasu taba tunanin nine na fiddaka ba, koda saurayin yazo nan a maganansa seya fuddo makulle yabudeni yaname nuna man wani saqo daban alamun tanan zanbi..

  Bayan nayi tafiya me tsawin gaske rannan se Allah yakaini ga wata qofa data bulla bayan kogon, koda na fita senaga babu wani abu bayan kogon se rairayi gaba kuma ruwa ne iya ganin ido, koda na huta sena fara tunanin mezan bayan na matsa wurin taikun senasha ruwa nayi wanka, nakama bingaba da nufin ko Allah ze hadani da wasu mutanen..

Nayi tafiya me tsawon gaske can zuwa goshin magriba sena hanki hayaqi na tashi, senace bari naje wurin hayaqin can wataqila Allah yasadani da mutane, na yanki hanya naita tafiya nakusa zuwa wurin dana hangi hayakin nan senaga ashe se an tsallaka ruwa, bayan na tsaya ina tunanin yanda zanyu na tsallaka ruwan, can se dubara tafado man naje na kakkaryo itace nazo na kama aikin hada  kwale-kwale bayan nagama daddaure itacen senaje na karyo ganyayyaki masu fadi na dora na daure, lokacin dana gama wannan aikin dare ya raba sena yanke shawaran bari seda safe in tsallake, nakoma can gefen wani itaciya me duhu na kwanta, koda kwanciyata se barci me nauyi yadaukeni  ban falka ba se goshi asubahi bayan natashi na kintsa na tsinki 'yayan itatuwa senaje gefen taiku nai wanka lokacin da gari yafara haske sena dakko jirgin dana sassaqa najefa cikin ruwan na haye da shigata bansani va ashe igiyar ruwace me qarfin gaske tajani tai cikin teku dani, hankalina yatashi matuqar tashi dan natube rai da rayuwa nakama addu'o'in dasuka fado man dan banama tantance iya addu'an danakeyi, bayan nayi tafiya me tsawon gaske nagaji bana ko ita motsawa hannuna rannan bansani ba bacci nayi ko suma nayi nidai bansani ba sedai na falka na ganni baki wani tsuburi, natashi naja jikina da qyar na fita cikin kwale-kwalen na tsinci 'ya'yan itace naci bayan nahuta qarfina yadawo sena tashi na cigaba da yawatawa cikin wannan tsubiri iname tu'ujjibi na al'amarin ubangiji, bayan nagama kashe kwakwar ido sena kama hanya naita tafiya har Allah yakaini wurin wani dogon dutse na yanke shawaran naje wurin dutsen ko Allah yahadani da mutane, bayan naje wurin dutsin danaje sena taddasa dutsene baqiqqirin sekace an shafeshi nakam zagayawa jikin dutsen ina cikin zagayawa sena tadda wata qofa, banyi tunanin komi ba na kunna kai ciki, ina shiga naga wani abin al'ajabi bakomi nagani ba face yanayin tsarin dutsen kamar qaramin gari, nakama zagaye ciki banga kowa ba se qananan dabbobi irinsu beraye da sauransu, can na hangi wani gida wanda yafi kowane kyan tsari da kyau nace bari naje can wataqila nasamu mutane ciki koda na kama hanya nashiga gidan ananne naqara cika da mamaki domin masarauta ce amma bakowa ciki nakama dube-dube lungu da saqo banga komi ba, harna tube tsammani sena jiyo sautin nishi a wani wuri daban nace kowanene wancan bari inje ingani.....

Anan ne bacci yakama Hashin Ibn Ahmad yayinda yakeva Jafar Labarinsa...

©Taskar Sardaunah.

[4/5, 17:29] ‪+234 806 604 6091‬: _*MATAFIYA UKU*_


 _?Bashier Sufyern_     
    *?Šarđaunah?*

         ❣ShagaLi❣

_Happy Birthday Sharyfat Umman Bilal._

 *Ina alfahri daku masoyana wadanda nasani da wadanda bansani ba, matuqar godiya agareku yanda kuke nunamin soyayya ta gaskiya.*

❣ _Sakon gaisuwata ga gidan radion VConnect yanda kuke nuna soyayyanku agareni Allah kuma yadaukaku, inajjn dadin kasancewa daku har abada muna tare_ ??

Page 3

Hashim Ibn Ahmad yaci gaba da cewa....

     Lokacin dana fara jin sautin nishi a wani daki senace bari naje naga ko wani me rai ne aciki, bayan naje dakin da shigata senaga wata kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance kamar wata dan daren goma sha biyar, na matsa gareta namata sallama ta ansa mini sallama na tambayeta labarin garinsu  senaga ta fashe da kuka me tsanani bayan tayi shiru hankalinta ya komo setace yakai wannan bawan Allah kasani cewa dukkan garinnan sun mutu a sakamakon wata annoba data fado mana nikadai ce narage a raye kuma nasan bakomine ya kubutar daniba face ubangijin musulinci, iyayenmu sun kasance suna bautar wani gunki me suffar jemage, kasani kimanin shekara bakwai dasuka gabata munyi wani bakon malamin addinin musulinci yayinda iyayenmu sukai kunnen uwarshegu dashi har takai ga anamai cin mutunci daga qarshe sukace matuqar  be dena tallata wannan addinin nasaba  zasu kasheshi, koda naji haka sena kamu da baqinciki me tsanani domin na fahimci wannan addini na baqon malamin shine gaskiya kuma iyayenmu sun sani, koda nayi dogon nazari senaje wurin wannan malamin a sirrince yaqara fahintar dani har takai ga na amshi addinin musulinci na kasance ina ziyartar malamin tsawon lokaci batare da kowa yasani ba, wata rana nagama shiri zani wurin malamin domin daukan karatun danake zuwa, ashe mahaifina yahadani da wata kuyanga dan taga menakeyi, bayan natafi koda kuyangar taga munje wurin malamin seta sulale taje tagayama mahaifina, yatask dakansa yazo yataddamu a wannan lokacin yasa aka kama malamin akaje aka banqare da nufin in safiya tayi a kasheshi, nikuma yasa aka sakani wannan dakin dakazo kataddani.

  Washe gari tunda sassafe aka kama kide-kide bayan an dauki lokaci me tsawo anayi koda rana tafara fitowa sega mahaifina sarki yafito yazo yace "yaku jama'ata kusani wannan mutumi yazone da nufin ya canja mana addinin da muka gada shekara da shekaru namai gargadi akan yadena amma yayi watsi da kashedin danai mai, to gashi zan kasheshi sabida ya rainamu kuma beji magananmu ba a matsayinmu na masu mulki a wannan birni, sarki yabada umarnin a kashe malamin koda malamin yaga wasu barade sun durfafoshi seya bude yaname cewa yaki wadannan batattun mutane kusani mutuwata bakomi bace face masifa da bala'i iname kiranku daku karbi addinin gaskiya inba hakaba zaku tabbata a tsinuwar Allah, kuma kusani kasheni bazai amfaneku da komi ba face tashin hankali da bala'i, koda sarki yaji haka seya dakama baraden tsawa yace ku kasheshi koni na kasheku sannan na kashehi, baraden suka harzuqa suka kashe malamin bayan shekara hudu, munhadu da annoba kala-kala mutane sunta mutuwa hankalin sarki yatashi matuqa da mutuwan da mutane sukeyi sakamakon  annabar data afko masu, bayan shekara biyu se akai wani ruwa me yawan gaske seda akai kwana hudu anayi batare da andaga qafa ba, a kwana na biyar ne ruwan yadauke kamar ba'atabayi ba, a kwana na shida munga bala'i da tashin hankali domin wani ruwa akai me zafi kamar an dafashi, babban tashin hankalinmu shine ruwan yanata tafiya da mutane cikin wani kogo dake bayan wani dutse, nidai babu abinda nake face addu'a da neman kariya a wurin ubangijin musulinci, shiyasa ni ubangiji yakareni, bayan ruwan yakwashe mutanen gabadaya duk se suka rikide suka zama wasu kalan kifaye da ido be saba gani ba, kasani yakai wannan baqo zankaika har wurin wannan dutsen domin ka kagani da idonka..

  Lokacin da mukaje wurin dutse naga yanda kifayen suke sena kama da al'ajabi nayi mamaki matuqa, nace mata shin kintaba roqama iyayenku afuwa a wurin Allah kuwa? tace dani "a'a" nace ba shakka wannan bala'in yafaru ne sakamakon kashe wannan malamin da iyayenku sukaye zamu roqa masu Allah akan yamaidasu ainifin halittansu...

  Bayan mun roqa masu Allah ya yafe masu jim kadan se suka klma ainifin halittansu bayan nabasu labarin tabbas annobar tafaru ne sakamakon kashe malamin dasukai, sena nemi dasu tuba sukoma bautar ubangijin musulinci, bayan sun anshi addinin musulinci Sarki ya nemi dana auri 'yarsa bayan anyi shagalin biki kowa yawatse akabarni nida amaryata, munzauna cikin farinciki har bayan wata shida, rannan senaje wurin sarki nace masa inaso inje gida ga matata nan zan dawo bada dadewa ba, sarki yaman shatara na arziqi na kamma hanya, mamadin in kama hanyar gida sena kama wata hanyar daban nabi ayarin wasu fatake muka tsunduma cikin teku muna tafiya duk inda muka tadda gari ko tsubiri semu tsaya mu taba ciniki, mundauki tsawon lokaci a tafiyarmu mun sami riba sosai, rannan muntaba ciniki a wani tsibir dake tsakiyar teku bayan munshiga jirgi se iska ta kada tozayen ruwa suka motsa iska me qarfi tta tashi hankalinmu yatashi muka kama addu'a ansamu tsawon lokaci muna cikin wannan hali, lokacin da teku ta lafa iska ta kwanta yayinda tozayen ruwa suka kwanta munyi farinciki matuqa 
, ashe bmu saniba hallakace da durfafo mu...

   A lokacin da madugun jirgi ya fahimci lallai iska ta canja mana ta farki seya dibi ruwan teku yashiga bincike bayan wani lokaci se mukaji madugu yatashi yana sallallami yakama marin fuskansa yana tuge gemunsa, koda mukaga haka se hankalinmu yatshi murna takoma ciki, muka tambayi madugu meyake faruwa yace tabbas mun futa a jan tafarki mun fada mahaukaciyar taiku kusani yaku jama'a tarihi ba'a taba samun wanda shiga wannan taikun yafuta a raye ba, koda mukaji haka se hankalinmu yatashi muka kama koke-koke, bayan wanu lokaci se mukaji an tsuge da ruwan sama ruwa me qarfin gaske, koda aka dade ana ruwan se mukaji girginmu yabuhi wabi abu kamar dutse, ashe wani kifi ne yabangaji jirginmu, girman kifin yawuce musali, bayan wannan kifin yabugi jirginmu se mukaji an dauki jirgjn caff anyi sama damu, mudai muna ciki muna jiran ikon Allah, zuwa can semukaji ansako jirgin yafado kan wani dutse jirgi ya ratattake 'yan uwana fatake suka mutu, zuwa can sena hangi wani allon jirgi senakama iyo harna taddasa na hayr nakom iyo da hannuwana ashe akan kallon akwai wasu mutun biyu dasuka hau, bayan mungaji da tukin jirgin semuka sena tuqin muka kama addu'o'i, iska da tozayen ruwa kuma kama turamu Har Allah yakaimu ga bakin gaba gefen wani tsubiri bayan mun sauka hankalinmu yakoma muka tashi muka kama zagaya cikin tsibirin muna mamaki, bayan mungama kashe kwarkwatar idonmu se mukaje gindin wata itaciya muka kwanta da kwanciyarmu bacci me nauyi yadaukemu, koda aka dau lokaci muka dau lokaci muna baccin zuwa can se mukaji wata iska me qarfin gaske, muka falka a tsorace, koda falkawarmu se muka qame kamar gumaka sakamakon ganin wani maciji sekace bishiyar rimi, macijin yataho saqaqa kamun mu farga mu gudu har macijin ya suri daya daga cikinmu yayi mai loma daya, sedai mukaji ruququss yana tauna qasusuwan dan uwanmu hankalinmu yatashi matuqa ganin irin mutuwar da dan uwanmu yayi muka kama kuka muna cewa da acikin teku muka mutu da mutuwan tazo mana da sauqi, bayan macijin yajuya yatafi se muka tashi muka kama hanya mukaita tafiya har dare yamana ananme muka fara neman gurin kwanata har zamu kwanta nacema abokin tafiyata sam bacci be ganmu ba dan bamusan iya hatsarin dake cikin wannan tsubiri ba...

   Anan bacci yatadda Hashim ibn Ahmad yayinda yakeba Jafar labarinsa...

©taskar Sardaunah

Fatan muna tare...
[4/5, 17:29] ‪+234 806 604 6091‬: _*MATAFIYA UKU*_


     _?Bashier Sufyern_
      *?Šarđaunah?*

Ubangiji ya Allah ka daukakamu daga cikin daukakarka, ya ka karemu daga sharrin maqiya, mahassada..

*Jinjuna ga dukkanin marubuta yanda kuke man Allah kuma yai maku, makaranta ma ina gaisheku??

_Gaisuwa agareku_

*JANAF*
*MAMAN JABEER*
*MAMAN USWAN*
*KHADYLURV*
*JAMILA ARMANIA*
   Alheri ne yahadamu??

Page 4

Hashim Ibn Ahmad yaci gaba da cewa...


Bayan macijin ya cinye abokin tafiyarmu, se mukai gaba har dare yayi anan nefa muka fara neman gurin kwana dan bamusan iya hadarin dake cikin tsibirin ba.

  Muka yanke shawarar muci gaba da tafiya har muka hango hasken wuta nacema abokin tafiya muje wurin wutarcan wataqila mutanene a wurin, muka kama hanya muka doshi wurin da isarmu se mukaji anata kide-kide koda mukaga mutanen se muka tsorata ainun, bakomi yasa muka tsorata ba se ganin qirar mutanen ko a mafalki bamutaba jin akwai irinsu ba, wasu kalan mutane ne tiqa-tiqa idanuwansu jajir kaman wuta akwai qaho guda data akansu gasu da bindi, koda mutanen suka jiyo suka ganmu se sukayo kanmu da wasu makamai wanda bamu taba jin labarin akwai irinsu ba, koda suka qariso se suka kamamu suka daddaure suka jefa cikin keji, washe gari da sassafe suka fara firfitowa koda suka gama futowa se sukai tsaye cirko-cirko jim kadan sega sarki yafito sukai gaisuwa daya daga cikinsu yafito damu cikin keji ya warbar aqasa sekace tsumma, bayan sarki ya qare mana kallo seya tuntsire da dariya yace nayi farinciki matuqa da samun bil'adama wannan alamace ta sa'a da rabo agaskiya nayi farinciki da samun bil'adama a ranar bikin qarin shekarata.

  Sarki yai umarnin adauki daya daga cikinmu agasa masa, dukkan wuri yadauki shewa, koda wanda yazo daukar wanda sarki ya umarceshi  koda yazo se kawai yadauki abokin tafiyata  yadagasa ya fyada da qasa ko shurawa beyi ba, akaje dashi aka gasa, koda ganin haka se hankalina yatashi kwallo talama kwaranya a fuska nace babu jibi babu dabara sega Allah madaukakin sarki nace dama macijinnan yahadiyemu da irin wannan wulaqantattar mutuwa.

Bayan angama gasa abokin tafiyata aka miqama sarki yaci yaba muqarrabansa seyai unarnin amaida masa ni seya futo wurin shagalin yamma se agasa masa ni (sekace wani kifi??)  sarki yajuya yashige gida jim da shigarsa se aka kama ruwan sama tare da iska masu qarfin gaske dukkan kejikan da aka sakamu suka wargaje koda naga haka sena kama wani yanki daban naita gudu cikin ruwa da iska batare da nasan inda nadosa ba nasha wuya matuka ina cikin gudun sedai kawai naji na yanke jiki na fadi bansani ba suma nai kome nene nidai kawai na falka naganni kan gado na alfarma, koda falkawata senaga ashe cikin wata qasaitaciyar fada nake, koda tashina sena kama hanyar inda qofa take na bude da fitowata senaga ashe na fito ne daga dakin dake cikin dakunan fada, na isa wurin sarki nagaisheshi yace barka da tashi daga baccin kwana 23 kasani yakai wannan me tsawon kwana yau itace rana ta ashirin da hudu da zuwanka wannan gari me suna Suljad, nayi mamaki matuqa dajin cewa nayi bacckn kwana 23 batare dana falka ba, sarki yaci gaba da cewa ykai wannan baqo me tsawon kwana mun tsinceka ne agabar igiyar ruwan da take fitowa daga cikin tsibirin Samnash atarihin wannan tsibiri ba'a taba samun ko tsuntsu ya gifta ta samansa ba yawuce a raye kabamu labarin abinda ke ciki..

Hashim yaba sarki labarinsa duka tundaga fitowarsa Sarki yayi mamaki matuqar mamaki dajin labarin al'ajabi da suka sami hashim, sarki yaimai shatara ta arziqi daga yace mai daganan zuwa birnin rum tafiyar wata biyuce in kanaso kazauna damu muna maraba dakai inkuma zaka cigaba da tafiya to muna maka fatan alheri, bayan kwana 2 Hashim yaje wurin sarki yaimai sallama sarki yaqara masa shatara ta arziqi yasa aka dorasa a hanya yakama tafiya ba dare ba rana har tsawon kwana shida..

 A kwana na shida ne Hashim  yashiga wani daji mani'imanci ko qoramai na guduna ruwansu gwanin dadi ga 'ya'yan itatuwa Hashim yayi farinciki da shiga wannan daji sedai kuma dayasan hadarin dake cikin dajin dbai shigaba, ashe sanda akasa hashim kan hanya yabi ta wata mararrabar hanya ya fita ta farkin hanyar data dace.

 Hashjm yacigaba da tafiya cikin wannan dajin yayi tafiya me tsawo sanann ya iso wani barayi na dajin wurine me ganyaye masu duhu ashe besani ba ya biyo ta wurin wani zaki me hadarin gaske, koda yazo ta wurin se zakin na yataso nan ya hayayyaqo mai har Allah yabani sa'ar ba tserema zakkn muga saka tsere nidai kawai abinda na tuna nakama hanya da gudu bansan inda nadosa ba kawai nidai na farfado ne na ganni anan inda kasameni.

Jafar yayi mamaki matuqar mamaki dajin labarin Hashim, anan suka qulla abota shima jafar yabasa labarinsa da dalilin zuwansa wurin yakuma gayamasa inda zaije, hashim yacd ba shakka tunda Allah yahadamu semu tafi tare...

 Bayan Jafar da Hashim sun dauki hanya se sukai ta gabas suka kama tafiya har Allah yakaisu wani birni me suna Nishwar birnin nishwar na daya daga cikin manyan birane na qasar Misra garine mani'imanci su jefar suka shiga suka kama zagaya gari har suka isa cikin kasuwa ananne fa suka zama sekace wasu 'yan qauye, bayan sun dauki wani lokaci me tsawo suna zagaye-zagaye cikin birnin Nishwar har takai da sungaji suka nemi qarqashin bishiya suka zauna, jim kadan da zamansu se suka jiyo wani sauti me dadin gaske na tashi koda sukaji wannan sauti se Jafar yace nikau zanzo ace naga me wannan busa da idona, suka tashi suka kama hanya sunabin ta inda sautin ke fitowa, basu ankara ba ashe har sunfito cikin garin, seka kama bin sautin har takai ga sunje bakin wani kogo na dutse, basu jira komi ba suka fada cikin kogo daga isarsu suka tadda mutum a yashe sukai masa sallama ya amsa masu, suka tambayesa labarinsa yace sufara bashi ruwa yasha tukun suka bashi ruwa da abinci yaci yasha bayan ya kammala hankalinsa yakomo yafara basu labari kamar haka..

  Sunana Anwar Bn Hamid daga qasar Istanbul mahaifina Hamid Shine sarkin dake mulkin Qasar Istanbul...

©taskar Sardaunah
Www://bashirsufyan01@gmail.com
Reply
Users browsing this thread: 1 Guest(s)