The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined variable $postsdone - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Trying to access array offset on value of type null - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 17348 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 17349 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 17350 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 18347 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 17348 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 17349 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 17350 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key 18347 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 33 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 33 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 65 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 65 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KASUWANCI NA* by ASMABAFFA
#4
????
????

   KASUWANCI NA






          96-100






Official









AsmaBaffa








     
     MEENAL AMFAL and MMN ADNAN ths page is for u tnx


   MMN AMATULLAH Ina turo gaisuwa me tarin yawa.

 REAL MAMAN WALEEDA jinjina da godiya Littafin yana Sweet yanda kika fara Lfy Allah ya baki ikon gamawa lfy tare da mu masu karatu,Allah ya kara Basira.



    Kuyi Hakuri Fans yan ASMABAFFA FANS CLUB ne suka ce sun bani hutu na kwana biyu weekend na huta ba laifi na bane su suka jawo muku,kuma ko yau suka ce na huta zan huta?





      Na wuce gidan su Sayyah inda Mum dinta ke koya min yanda ake kula da miji etc sannan ta fara min Gyaran jiki ina shan na tsumi,sai wurin Magrib nayiwa Driver waya yazo daukana muka tafi gida Sayyah sai tsiya take min an kusa gamawa Aayan ya kwashi harka, ina dawowa na Iske Aayan da Ameer suna hira a palo kamar wa da kani na jini da Alama wata muhimmiyar magana sukeyi ta sirri, Ameer yace sannu da zuwa Anty nace yawwa ya hutu,Ya Aayan nace tare da daga masa hannu zan wuce Bedroom ya yafito ni da hannu ina karasawa ya miko ko min kumatu nasan me yake nufi cut nabashi kiss a kumatu na wuce, duk da cewa tunda yayi Tafiya ya dawo bama wani shiri dashi dan Romancing dinma da mukeyi ya daina taba jikina ko da wasa akan nace jikina yake so shine zai nuna min ba jiki na yake so ba,da dare da kyar muke iya bacci Sabo da mun saba idan mun kwanta muna yin abubuwa masu dadi tare da shiga rai,ina ta faman gyaran jiki Amma baya nuna min komai ko irin nayi kyau ko Ya rude a akaina abin yana kona min rai Amma ai ni na jawo.
    Wanka nayi tare da shiryawa cikin wasu arnayen kana nan kayan da ya kawo min daga tafiyar da yayi,nayi kyau na fitar asiri sai Hijab na Sa har kasa Sabo da Ameer,Kitchen na shiga na fara shirya mana abincin Dare kamshin girkina ya cika gidan.

    Ameer kuwa tuni Aayan ya bashi mota guda fyalleliya yana shiga su Abbi sai mamaki sukeyi,Daddy kusan kullum sai naje na gaisar da shi mun sha hira abinmu in ta bashi labarin mu,Sameera yar daba dukansu tare da yaranta an yanke musu hukuncin a gidan kaso na watanni 8 Sabo da Sameera me kudi ce ta basu cin hanci maimakon na shekaru sai na watanni kuma a hakan ma sunce baza suyi 8 mnths ba wata daya ma za a sakesu Sabo cin hancin da ta basu,kasar nan ba gaskiya a cikinta, Aayan kaji wai 8mnths kacal za suyi nace masa ina tura baki,yace Hmm bana son halaka ne da sai na Bada kudin wanda yafi nata a barta a ciki to Allah ya hana cin hanci da me karba da me bayarwa akwai ranar da Allah zaiyi maganinta gaba daya,Amma in kina so a bayar hakan to? Nace ae a bayar kawai dan ubanta ai akan gaskiya ne,a Bada kudin a tabbatar musu da hukunci me tsanani,Kanwata guda da aka bar min Amana nice kamar Uwarsu fa ai wlh Bazan yarda ba da Ammah na da rai kake jin zata yi alfahari dani Na karasa ina zare masa idanu kamar shine Sameeran,Dariya yayi yace to ke mene tunda Allah yasa ta fito lfy? Bazan yarda ba sam kamar kudin ubana haka nake fada Bazan yarda ba dole na tsaya a tabbatar da gaskiya a sharia ka bani kudin Kasuwanci na sai na biya dashi a tabbatar da anci uban Sameera a gidan kaso,yace za a baki tsigai,nace ae a bani kuma dole muje da kai ka wuce gaba ayi komai da kai,yace an gama Uwata, da kansa yaje ya kashe case din ya biya kudi masu mugun yawa aka canjawa su Sameera shekaru Har uku ba tare da nasan anyi ba,sai da ya dawo ya sanar min,nace kash Uku kacal? Laifin Kidnapping tare da niyyar kisan rai? Uku fa ai wlh ba a ci uban Sameera ba sam baza ta koyi darasi ba,sai kace kasar turai da suke da Imani,a Nigeria muke fa inda ba Imani ba a dauki dan Adam da daraja ba,Dariya ya dinga yi to so kike a kasheta wai ko ba a kashe ta ba nafi so ta tsufa a prison,sai gashinta yayi fari tass lokacin na kusa aurar da yan biyun da zan Haifa nan gaba yan mata,Aayan ya bude baki dama har yan biyu kike so ki Haifa?Nace ae Insha'allah su dinga min girki kullum,Aayan yace sai ki dage ki haifo su ai,Wai Ya Aayan ta ina ake Haihuwa kuwa? Yace ta cibi zaki ga ta bude kawai jariri ya fado,dariya nayi nace ba wahala ashe ma.yana ta min dariya yana tunani Allah yasa ya warke ya yi maganin gaba daya.

   Bayan na gama girkin daren nawa Ameer yau bai dawo da wuri ba daga ni sai Aayan muka ci,.  8pm nayi shirin bacci da komai a dakinsa shi kuma naga yana ta cin kwalliya kamar ranar daurin aurensa sai fesa turaruka yake faman yi,nace ina zaka je? Yace wajen yarinyar nan ta Us ce tazo kuma a Hotel ta sauka ba dadi Budurwa kamarta ta zauna a Hotel ai ba mutunci ko kawai zanje dakko ta ne ta zauna damu kafin ta koma.

   Kamar ana zuba min ruwan zafi haka naji a zuciyata,ji nayi kamar zanyi hauka gaba daya hankalina baya jikina Sabo da tsananin kishi,nace idan an Isa Allah ya dau raina yau ba sai gobe ba, nace Wayyo Jama'a ga Kwarto,Ameer ya dawo yana kasa yana juyowa ina ta ihun Kwarto a sama,shi dai yasan Aayan yana gida Amma yace bari ya gani kar ko wani ne daban da Sauri ya karaso Saman yace Anty Mufeeda lfy waye,Aayan ne ya fito cikin shirinsa yace kyaleta jeka kuruciyarta ce ta motsa,Ameer yana dariya yace Ya Aayan kaine kenan Kwarton Aayan yace ae fa gani,Ameer ya juya yayi tafiyarsa yana dariya a ransa yace Mufeeda itama irin yan fulanin garinsu ce kenan,Ni dai ko a jikina na fara kuka yana daukan Agogo zai fita na dakko Jambaki da Sauri na bude shi na dinga shafa masa a rigar ta ko ina na jefar da jambakin na kama rigar na dirje lips dina da ita kalar pink jambaki ga wancen Red,yace kinyi ta banzan dole zanje ya bude kofa kenan na jawo rigarsa ta baya,ina ta uban nishi ina Hawaye,hakan baza ta kaini ba na tsuguna na kwaso kafafunsa Amma ko motsi baiyi ba,sai ya biye min ya tsaya don yaga me zanyi masa tunda Hannunsa nake ta ja da karfi,sai ya biyoni tunanina ni nake jansa ta karfi ina nishi na jawoshi har Jikin Bed,ya tsaya kuwa,nace kwanta to dan Allah kaji ina ta kukana,yaki kwanciya na kara mikewa na danna shi kan Bed ta karfi,nan ma gani nake ai karfi nane ya kwanta sharab,yana kokarin mikewa na fada kansa na kwanta daf daf tare da rufa mana bargo tare nace ka dubi girman Allah ka kwanta,Sabo da me? Aljanune suka ce kar na barka ka fita kana fita zaka samu matsala,a lokacin kuma da Aayan yake son fita lokacin Abbi ya barbada masa Wani garin magani a kofar fita wajen part dinmu suna jira ya taka wajen,mu harga Allah bamu san da wannan ba kishi na ne yasa na hanashi fita.

   Sai da Abbi Sani ya Kira Aayan a waya wai ya fita yanzu ga abokan Daddy nan sunzo duba Daddy daga Abuja kuma karya yake burinsu kawai suga Aayan ya taka maganin kafin gari ya waye,idan har gari ya waye to ya karye maganin ko an taka bazai yi ba,shine suka rasa yanda zasuyi ya fito suka hada abin da Wai Bakin Daddy sun san yanda yake kaunar Daddy dinsa.

     Ta inda Allah ya tsare Aayan sai a ransa yace bari ya tsokaneni yaji shine yace ai wajen wata zaije,ni kuma uwar kishi shine sai da nasan yanda zanyi na hana fitar ta dole,a hankali na kai bakina zan masa kiss yace karki taba ni,why? Kince Sabo da jikinki nake taba ki so na daina taba ki,to Sabo da me kake tabani? Fadi gaskiya naji?  Murmushi ya saki sannan yace Do not judge a person by their looks or the things they have. You do not love some one for their appearance or their nice cloths but because of their personality, their thoughts etc u have to Understand kinji?
   Shuru nayi ina jin dadi yaci gaba Sometimes people don’t tell you how they truly feel about you but they will always show you so pay attention ki gane ba sai ance kullum ana sonki ba kamar yarinya ku yan mata haka kuke.

 Baki na turo tare da cewa ni dai duk da yanzu ina jin turanci kayi min da Hausa yafi shigata sosai kai turancinka na turawa kakeyi duk a harde, murmushi yayi yace Ok ku mata sai kuyi shekara yafi goma tare da mutum yana ta nuna muku yana sonku Amma wai in dai bai ce i love u ba to kawai ba sonku yake ba,wani ma sai ayi ta cewa ai kawana ne,kuma in ka sake kana gani zata auri wani ta barka,sai kace daga baya ina sonki tace me yasa baka fada min da wuri ba bayan duk abubuwan da ka nuna mata na zallar so ne.

   Murmushi nayi nace uhm munfi so muji gar da gar, kumatuna yaja da dan karfi sai da nayi kara sannan yace I LOVE YOU......I DO REALLY LOVE YOU,I NEED U,I LOVE EVERYTHING ABT U,U ARE MY SOULMATE BABYNA ya karasa furtawa tare da hade bakinmu waje daya yana sha,Dadin da nake ji ya wuce a fade shi,nan take na kara kankameshi,naji yana nema ya zarce nace bari nayi fitsari,a hankali ya sakeni na shiga toilet,na kulle tare da jingina da jikin kofar ina sauke numfashi da ajiyar zuciya bakina yaki rufuwa Sabo da murna,dama Sabo da kar ya gano ni yasa na gudo toilet Sabo da nayi murnata ni kadai,harda tsalle da murna ina yarfe hannun dadi,sai da na dade ina murna sannan na hade rai na fito daga toilet irin ko a jikina bana murna, gefensa na kwanta ya kalleni tare da saka hannunsa cikin nawa Baki ce komai ba Baby, akan me fa na furta ina yanga,do u love me too? Yatsina fuska nayi tare da cewa sai nayi tunani na duba naga ko ka dace,Murmushi kawai yayi tare lumshe ido ya jawo ni jikinsa Amma Sabo da iya shege sai na ja baya kadan tare da kwace jikina.

     Shima bai takura min ba ya kyaleni kawai tare da daukan wayarsa dake uban ruri sunan Abbi ne a jiki,sai yanzu ya tuna Abbi ke neman Sa yaje tarbo Bakin Daddy,amma abin mamaki baki daga Abuja su rasa lokacin zuwa sai dare kawai dai yace gani nan yanzu su jirani,Abbi yana ta masifa ka wulakanta mutane Sabo da kai ga me kudi ko to kayi gaggawar fitowa,burinsu ya fito ya taka maganinsu,Ni kawai ban yarda da fitarsa ba kishi nake ko wayo zai min macece da yace daga U.S take,nan take na fashe da kuka ganin ya mike da gaske fita zaiyi, a hankali yace mene ne? Ni..Allah ba inda zaka fita,Indai ka fita Bazan kara tayaka kwana ba kawai baka so na,mirmushinsa me tsada yayi tare da cewa kina jin yanda Abbi ke fada bakin Daddy suna jira na kiyi hakuri naje naga ko su waye mana,Yanzu wasu bakin kirki ne da Dare haka ni Dai Allah baza kaje ba na sani ko wajen budurwarka zaka je.

    Hakura yayi kawai da fita Sabo da yaga da gaske tunanina yana da budurwa gudun Zargi sai yace Ok na fasa to,murna na fara yi tare da kashe wayoyinsa gaba daya na ajiye gefe,shi kuma yana zaune gefen Bed na zagayo ta bayansa tare da Zura hannayena ta cikinsa na rungumeshi gaba daya a jikina,bai san sanda ya lumshe ido ba jin yanda Albarkatun kirjina suka sauka a bayansa,Kasa jurewa yayi ya juyo tare da matsane a kirjinsa gaba daya kamar zai fasa min Kashi, gaba daya ya tafi dani ban san sanda na biye masa ba alhalin nace na daina yarda yana taba min jiki yanzu sai na bashi wahala Amma sai gashi na kasa jurewa,har mamakin kaina nakeyi yanda nake da Feeling me karfi kan Aayan bana jurewa.
   Da Zafi zafi muke Sarrafa juna kowa na nuna kwarewarsa Har Aayan ya dauki Hanyar Cinma burinsa Amma sai kawai sha'awarsa ta tsaya cak ya gagara komai,ni kuwa dama gyaran jikin da nayi nace shike nan na hakura ya samu abinda yake so Sabo da son kudi na bana so nayi asarar kudin gyaran jikina gwara ko mutuwa zanyi kawai ya Mori kudinsa tunda dama danshi nayi gyaran idan ba ayi ba ai na rafka asara tare da bata lokacina.

     Kallonsa nayi da tausayi sosai Sabo da yana da sha'awar abin Amma kuma bazai iya ba wannan Masifa ce,sai dai yayi ta shan wahala,shuru kawai naga yayi ya fada dogon tunani,Nace Man ya akayi ne? Har yau baka warke ba ko? Kai kawai ya daga min,da kyar yace min am so sorry na kasa baki hakkinki shi yasa bana son auren nan,amma kiyi hakuri idan kinga da matsala ko zaki shiga wani Hali tunda ban san ranar warkewa ta ba ki fada min duk da ina sonki nasan da kyar idan zan rayu babu ke zan iya hakura, Hawayen tausayinsa ne ya ziraro min nan take nayi Sauri na rufe masa baki nace karka kara ambata in Bazan iya ba zamu iya rabuwa ka daina ba kai ka daurawa kanka ba Allah ne kuma watarana zaka warke,kayi hakuri itace Kaddararmu ba shi nake so a tare da kai ba wlh ko shekara nawa zakayi a duniya zan iya hakura mu zauna tare,Allah idan har kaji ni Mufeeda nace ka sawwake min ko mu rabu ko zan bar gidan nan abu na farko da zaka min kawai ka kaini gidan malamai masu Rukiyya kawai ba kalau nake Ba ko Aljanu sun shafe ni ko an min asiri kaji na rantse.
   Ka daina damuwa ko kasawa kanka tunani, na gode Baby Na gode yake ta maimaitawa I love u so much My wife,yanzu in naji kince mu rabu ko zaki barni na...da Sauri na karasa ka kaini Ruqiyya wajen Malamai kawai asiri aka yi mana,Dariya yayi kadan tare da kara kankameni a jikinsa.

      Can kuwa su Abbi suna ta faman kiran Aayan a kashe ma wayar,Abbi yace iyyeeeeeee ehhh lallai yaron nan fa ya fara tsallake iyaka dan muna daga kafa ne kawai idan mukayi sake muna jiran Hajja to lokaci zai kure mana,da gani yar iskar matarsa ce ta hanashi fitowa wlh bazai wuce ita bace,Abbi Sani yace dama naga Alama yanzu sai abinda tace Gwara mu fara maganin shegiya,akwai Maganinta Hanifa ko Sajeeda zan bawa aikin su zuba mata a abinci inda da kanta zata bar gidan a nemeta a rasa taje can tayi ta garari a duniya.
   Abbi yayi dariya sannan yace ai har kannenta kar a bari su dawo tunda sun tafi dangin ubansu to su zauna can ko su Bita ita Mufeedan su karata can,da banyi niyyar kulata ba Amma yau ta shiga gonarmu,Washe gari da Safe Saturday Ameer yana Bedroom muma haka na hada mana break na shirya a Dining na koma ina taya Aayan shiryawa Sajeeda ta samu yanda zatayi ta bude kofar ta shigo a hankali tare da kallon gefe da gefe ta tabbatar ba kowa a wajen sannan da Sauri ta karasa saman Dining ta bude duk kalolin abincin dana shirya ko wanne ta barbada garin maganin sannan ta rufe a hankali ta juya zata tafi duf Numfashinta ya dauke na wasu dakiku sakamakon ganin Ameer da tayi tsaye a bayanta ya harde hannaye a kirjinsa,yana mata wani wulakantaccen kallo.

      Nan take jikinta ya fara mazari, ba zato taji mahaukacin Mari ta ko ina,zafi ya hada ta kamar an dosana mata wuta a fuska,Fisgo wata waya yayi ya fara tafkarta yana Ball da ita,tun tana neman agaji har ta garara,ni kuwa munji kamar hayaniya amma hankalinmu bai kawo ba,Ameer ne ya samu Kwalaba ya fasa tayi cako cako ya jawo Sajeeda kiiii har palo ya zauna saman Kujera,Fuskarta ya rike da karfi tare da dagata,tana kuka tana bashi hakuri tasan Ameer bashi da Imani zai iya yankar jikinta da Kwalaba,kamar me aski ya fara karta mata Kwalaba tun daga goshi jini na tsatsafowa,Sai yanzu muka fito nan muka hango irin muguntar da Ameer ke aikatawa,Aayan ne yayi magana da karfi Ameer me ya faru wannan wanne irin rashin Imani ne?

    Gashin Sajeeda ya fisga da karfi tare da cewa confess dan uwarki,nan take Sajeeda tana kuka ta fara tonawa kanta asiri da Abinda Abbi ya sata aikatawa,Ni Mufeeda Salati na fara nace Ameer hada da kirjinta duk ka karce shege a Zane mata ko ina,Aayan yace no..Ameer kyaleta taje mun godewa Allah ma haka tunda ya nuna mana,baki na turo nace ni dai baza a barta ba sai an cire mata farcen kafa na Babban yatsa ta karfi zan tsige shi,Aayan yace ba a nan gidan ba ke tashi ki tafi,tana mikewa na damkota  tare da yarda ta kasa Aiko Sajeeda ta fini karfi kawai sai ta rufeni da Duka sosai na koma neman a taimakeni,Aayan yace au Sajeeda naji tausayinki an barki shine zaki dukar min Mata to na fasa,Sajeeda da fuska duk zanen Kwalaba da jini tace ae din tare da gallawa Aayan Harara kafin ta maida idonta ya kafeta da Mari hagu da dama tare da bude kofa yayi short da ita waje ya maida kofar ya rufe,Ameer yace na fada ma basu da kunya.

    Nace ai wlh sai naci ubanta idan na kamata sai na karya mata hakori sai na tsoma mata yatsa a ruwan zafi, dariya Aayan yayi yace ai tafi karfinki gashi zata ji miki rauni a banza nan nace ai kyaleta nayi kawai Amma mu fada a wajenmu harda na siyarwa dan Babanta. Kwashe abincin nayi gaba daya na juye a leda na kai Dustbin Ameer ya fita dasu waje,haka na dan dafa mana saukakakken abinci abincin mu me dadi muka karya,s ai mita nakeyi na hana kowa sakewa.

    Tunda Hajja da Abbi suka ga abinda aka Yiwa Sajeeda suka shirya Tafiya can kasar Kudu cikin wani kauye wajen Babban sabon bokan da aka basu lbr anyi,
   Har wanda ya basu labarin bokan gaba daya da shi aka shirya yayi musu Rakiya banda Hajja ta dai ce Abbi yayi komai.
   A jirgi suka sauka a Enugu daga nan suka dauki Taxi wai ya kaisu wani daji ko a garin Enugu tsoron bin hanyar Dajin akeyi Sabo da matsafa sunyi yawa a dajin, Driver yayi ta Maza yana Tafiya dasu yana tsoro ko yan yankan kaine,yana Tafiya yana jan tsaki yana Chaiiiiii Alaji,suna jinsa har dai ya kaisu dai dai inda zasu dan shiga dajin da kafa mota ko machine basa shiga sai da kafa,Suka sauka tare da bashi kudi yace Alaji always making juju Money,go and Meet ur Malam is Better than to visit ths land wooo, u have to be very careful with ths place,ahhh see me see troble because of Money so people can do anything in ths world they can even kill them self,Abbi yace Abeg carry ur Wahala and Go stupid Taxi Man,shi dai me Taxi ya figi motarsa bayan ya gama surutunsa.
     Dan cikin dajin suka shiga kadan sannan Me Rakiya yace anzo wajen,Abbi yace ya sunansa kace? Mutumin yace sunansa SHAKYLGANCY sai kace dan India cewar Abbi,ai a india ya koyi har kar nan Alhaji cewar me Rakiya.

     Suna zuwa wajen anyi Ado da komai Red Abbi yace Shakylgancy.....Shakylgancy.....Sai ga Shakylgancy bugul ya bayyana kamar Aljani wani me mummunar suffa,Cikin harshen turanci Abbi ya koro baya nansa,Shakylgancy ya kece da daria sannan yace shima cikin turancinsa yace 1million Amma baza a biyashi sisi ba sai in magani yayi suka ce Shakylgancy baza mu iya dawowa nan ba karbi kudi kawai ko yayi ko baiyi ba karbi kawai zamu dinga contacting dinka a waya idan ta kama dole nayi kokari mu dawo,Shakylgancy ya washe hakoransa tare da wani hancinsa kato kamar tattasai ya karbi kudi yace suje zasu ga aiki.

    Bayan su Abbi sun fito gefen titi tare da Dan Rakiya suna neman Taxi wata mota ta yan Mafiya matsafa ta shararo da gudun tsiya dan Rakiyar su Abbi shine a gefen titi motar na zuwa tayi gaba dashi ta markadeshi a titin fit kansa ya dinga gare gare kamar Ball a saman titi,su Abbi sunyi mutukar firgita shi da Abbi Sani nan suka ga fa an kashe banza motar ko slow down bata yi ba,aiko su Abbi suka take da gudu suma suka mike titi sambal suna ta yi kamar yan tseren gudu basu san sanda suka watsar da takalma tare da babbar rigarsu ba,dama Abbin Sajeeda cewa yayi suje sun wakilceshi shi tsoron zuwa kudu yake yi tunda watarana a Crossriver akasace wani a gaban sa shike nan ya firgita.

     Sai da su Abbi suka yi Nisa sannan suka samu Taxi da kyar ta kaisu Har airport a Hanya suka siyi Sababbin takalma Amma Sabo da rashin Imani ko Jimamin Mutuwar abokin Rakiyar tasu basu yi ba sai Abbi da yayi karfin halin daukan hoton gawar a waya Sabo da ya nunawa iyalansu gashi wancen talaka ne shi da iyalansa Amma an mutu a shirka,nan ba aci ba can ba a ci ba,a kiyaye talaka ka lallaba kanka ka samu a Aljanna.

    Yau ni kuwa shirye shirye mukeyi Su Meenat zasu dawo daga Maiduguri Ameer yafi mu Zumudi wurin Magrib sai gasu kuwa da kaya Niki Niki sun shigo sai murna lokacin Yarima yazo sun finta tare da Aayan,sai hira mukeyi muka ci muka sha,Ameer yace Duk kunfi kyau a Kauyen Rimin Gado har kumatu kuka yi,Meenat tace ai baka kyauta ba tunda ka wani gudo,yana dariya yace tab ina wani zan iya zama a wannan garin toilet ce tashin hankali ana kallonka a waje,ga wata katifa kamar ta jariri,dariya mukayi gaba daya muna haka sai ga Aayan tare da Yarima,Yarima yana ganin Ma'eesha wani sanyi ya fara ratsa shi ita kuwa Ma'eesha kunyarsa takeji kwarjini yake mata wata uwar signa ya mata da ido ai ko Nan take gaban Ma'eesha ya fadi rass Sabo da lokacin Ma'eesha ta cire Ameer dama shakuwace Sabo da yawan mu'amula da sukeyi ganin kuma kamar shi wata mace bata gabansa yasa tace ke Ma'eesha shafawa kanki ruwa,
    Ma'eesha tana Satar kallon Yarima ta gaisheshi ya amsa cike da fara'a, duk ta kasa sukuni ni kuwa ina gefen Aayan nayi shuru na lula tunanin asara da zata hau kaina kwanan nan na gama kashe kudin gyaran jiki mijin bai mora ba,danni a kan ayi asarar kudin nan gwara na kusa mutuwa na farfado kawai.
   a hankali Aayan yace ya akayi? Ya rada min a kunne,ajiyar zuciya na sauke nace kai dai bari kawai asarar kudade nake ta yi kwanan nan,ina ta zuba adashin da ba a dauka,Aayan bai gane me nake nufi ba yace ke na rasa inda kika gado son kudi haka wacce asara kikayi na biya ki? Nace baza ka gane ba a bar zancen Amma ko ka biyani Bazan iya daina tunaninsu ba,tunda har yau me kayan ma bai yabe su ba ko da baki yace kayan nan sunyi sun kuma hadu etc ba a ce min kala ba bare naji dadi da kwarin gwiwar karbar asarar danayi tunda bai samu damar siyan kayan ba.

    Aayan iya tunaninsa ya kasa ganewa me nake nufi wani kuma waye wani?to Business sukeyi? Nan fa kishi ya cika shi tab yasan zata iya indai Mufeeda ce zata iya, Yarima Ya rasa inda zai saka kansa dama yake jira kawai su dan kebe da Ma'eesha ya karbi Number ta kullum cikin tunaninta yakeyi,Sai ko Ya mike yace zan tafi Aayan sai mun hadu,Aayan yace bari na rakaka,a'a zauna ban son Rakiyar Katon Gardi ni Ma'eesha kawata ce zata rakani,Dariya mukayi gaba daya Ameer yace da Alama Ya Yarima girma ya fadi ka fada akan yar wannan yarinyar,Meenat tace Ss1 kawai fa,Ma'eesha ta harari Meenat tace Gwara dai ni ko a hanya duk mutanen kirki ke tareni suce suna so ke kuwa fa Kwaja,Fela etc ku bari na dawo wlh na fasa rufa miki asiri dama kince kar na fada na yarda to na fasa Bari na dawo na baku latest a Maiduguri da Rimin Gado,Ameer dama kadan yake jira yace muna jira Sauri yau wlh komai dare bazan kwanta ba sai naji.

   Aayan yana Dariya yace gaskiya a rufa mata asiri,Meenat tayi mukus tasan yau Tata ta kare,Yarima ya dan jima yana jan Ma'eesha da hira sama sama duk shima akwai ji da kai bai fiya magana ba Number dinta ya karba ya bata tasa sannan ya bata kudi taki karba,babu yanda baiyi ba Amma taki karba nan ta kara birgeshi sosai.
   To yan mata pls a rage nuna zalama wajen Saurayi ko idan kika ga mutum ya fiye yi miki kyauta dan Allah watarana ki dinga jayayya kice baza ki karba ba ko da kina so ki dan dinga kai zuciya nesa sai ki kara birgeshi,sai masu jarabar Rokon Samari abu kawai yan mata Direct kice yi min Kaza ko bani Kaza ko yaushe kuma ba kunya ba komai wlh ba tarbiya ce ba,kina zubarwa kanki mutunci da na iyayenki a dinga daga kafa ana hakuri da yanayi na  Babu ba har ayi ta roke roke ba, ko ina wasu zakiji suna wancen ina ba yar manya bace Bazan iya ba na tsani me roko etc.

     Ma'eesha na dawowa Ameer yace matso nan Hajiyata ki bamu mu musha,Meenat tace Sis Mufee kin gansu ko,Mufeeda tace nima baza kunne nayi yarinya, Babbar banza cewar Aayan,dukan wasa na danyi masa kadan tare da kwanciya a cinyarsa , Ma'eesha tace kai Allah ya bawa Meenat farin jini samari iri iri tun daga Rimin gado yan fulani suka dinga cika kofar gida.

    Farko mun fita siyo pure water muka hadu da wani zai je kiwo da shanunsa ya tare mu yana washe baki idan kun ganshi abin dariya yana busa hayakin wiwi Yace hooai Yan Birni aradu wagga Bingel tana Burgeni, wannan ke nake so ya nuna Meenat tare da cewa Sunana TSITO, nan muka fara dariya jin sunansa Ma'eesha tace in kun ganshi wlh yaci sunansa Tsito wani siriri ne kamar a busheshi gwara Kwaja ma yana da Katon ciki Amma Tsito shi ba dan cikin ma,Meenat tace to Dan Uwarki ai Tsito yafi Kwaja lfy da ganin cikin Kwaja ai na cuta ne,kuma Tsito kyakyawa ne,Ameer yace mu dai ba ruwanmu Tsito muka sani,Ina dariya nace karki kara zagar mana Uwa akan kice dan Uwarki gwara kice dan Ubanki Better,Make min baki Aayan yayi shi Abban shine ba a so ba kyau,baki na turo cike da shagwaba nace da zafi fa...Zan rama ne.

    Ma'eesha tace Daga Tsito kuma sai NA AGWAGWAJI  shi kuwa a yan fulanin ma dan Daba ne duk wanda yaga Meenat tayi masa magana sai ya farfasa masa jiki,Ameer yace kice dan karamin yaki ta hada,Meenat tace Allah ya bani ya zakuyi dani ehe,Dariya muka dinga yi Jin har Dan karamin Saniya Na Agwaji ya bawa Meenat tana can gidan Inna an daureta za a sata cikin Shanu ana kiwata mata ita,Nace Business Sabo Sarkin Kasuwanci cewar Aayan jin yanda nake ta murna Meenat ta samo Saniya zata girma ta Haifo yayanta.
    Ma'eesha tace Arzikin Meenat bai tsaya a nan ba kullum samarinta suna hanyar kawo mana kaji da zabbi muna yankawa mu sha farfesu iri iri,Na ciji yatsa nace me yasa kika cinye a ciki banzaye maimakon ku siyar ku tara kudin ku kawo min ko dankunnen Gold na siya muku dan karami,Aayan ya kalleni baki bude yace da kudin kajin? Nace of Course.

   Ameer yace inye to wannan buhun kayan naku fa? Ma'eesha tace duk Samarin kauye ne suka tara mana su danyar Gyada,gero,wake etc,A Maiduguri kuwa samarin Meenat harda Conductors na mota,yan Napep etc me dubu daya me dubu biyu haka muka cinye musu kudi,Nace to ke kuma fa in haka ne kece me bakin jini,Meenat tace tsakani da Allah duk wani me kudi indai kinga rantsatsiyar mota ta tsaya to ba shakka wajen Ma'eesha aka zo zance,ni dai Meenat ina ga asiri akayi min daga me kaji sai me Saniya,gyada da gero tare dasu waken Suya hhhh muka dinga dariya,Aayan yace sorry Sis zaki samu wanda yafi kowa kudi kuma na gari kema,ni kuwa nace Meenat haka Allah yake lamarinsa ni kam Ruwa ta sha aradu,Rankwashi Aayan ya zuba min,Ameer yace ni wlh ji nayi gwara haka ita ba iyayi ba dama Allah yasan manufar jaki shi yasa ya hanashi kaho.

     Meenat ta gaji da abinda Ameer yake mata ta mike cike da shagwaba tayi kansa wai zata kwala masa spoon ya mike suka fara zagaya mu a palon muna zaune, sai da na gaji nace Meenat kun damemu can u stop ths Nonsense pls? Meenat tace ai kuna jinsa abinda yake ce min kun kasa yi masa fada,Maeesha ce abar duka ai ba Ameer ba tunda ita ta fada mana,Haushi Meenat taji ta jefar da spoon din tayi Bedroom abinta .

     
AsmaBaffa
Reply


Messages In This Thread
*KASUWANCI NA* by ASMABAFFA - by Gimbiya - 01-28-2019, 10:29 AM
RE: *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA - by Gimbiya - 01-28-2019, 10:30 AM
RE: *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA - by Gimbiya - 01-28-2019, 10:31 AM
RE: *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA - by Gimbiya - 01-28-2019, 10:32 AM
RE: *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA - by Gimbiya - 02-22-2019, 08:04 AM

Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 1 32,229 03-26-2019, 10:46 AM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 7 60,141 01-20-2019, 01:58 PM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 0 7,552 01-18-2019, 09:17 AM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA 0 2,511 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA 0 3,072 Less than 1 minute ago
Last Post:



Users browsing this thread: 1 Guest(s)