The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*CAPTAIN_AHMAD JUNAID* By Khaleesat Haiydar_ ✍?
#1
⚓ *Captain_Ahmad Junaid* ⚓
 
    _By Khaleesat Haiydar_ ?
 
*Dedicated to......*
 
*Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah, Ya ubangiji kamar yanda ka bani ikon fara littafin nan ka bani ikon kare shi cikin aminci da yardar ka, Ya Allah ka min katanga irin ta China da duk wani soul da xai daga min hankali a Media??‍♀ ya Allah ka rabani da sharrin mahassada da duk 'Yan uwana musulmai baki daya, ya Allah ka kara hada kawunan musulmai a duniya ka tsare mu a duk inda muke, Ya Allah ya ubangiji kasa mu gama da iyayen mu lafiya, kasa mu cika da imani da tsoron ka a xuciya don son ma'aiki S.A.W* 
 
Uhnm! my greetings goes to my die hard fans nd frnds dat are alwayz their for me
 
My Phatiemarkh 
Habibah Marafa
Hafsat (Ummu Ilham)
My Humainah bala Abkr?
Eeshatullah Goni?
My Maryam Aliyu
Rukky Usman
Saknah Ibrahim
Sallynah
Ummu Lailah(AY)
My Salmah 
Maman Shakur
Fiddo s dangi
 
Waow to mention but a few, Khaleesat heart you all. Shout out to my lovely fans. Allah bar min ku.
 
1.....
 
Ya jima xaune kan darduman bayan ya kai Ayan karshe a Surah At-tawbah, ganin har shidda da rabi ya sa shi mikewa a hankali ya rufe qur'anin ya ajiye a bedside drawer, jallabiyan jikinsa ya cire ya nufi bathroom, ya dau lkci yana wanka sabulai masu dadin kamshi da shower gel duk ya cika dakin, sanye da bathrobe ya fito yana goge lallausan bakin gashin kansa da karamin towel, gaban mirror ya nufa ya dauko lotions dinsa daga tsaye nn ya shafa, yana gamawa ya jawo mayyukan gashinsa ya shafa  ya shiga combing gashin nasa, closet dinsa ya bude ya fiddo well ironed wear din da xae sa dake jikin hanger, farar singlet ya fara sawa, cikin mintuna bakwae kacal ya gama shiryawa, ya dauki silver wrist watch dinsa kirar Emporio Armani ya sa, shoe rack dinsa ya nufa ya dauki bakar cover shoe kirar Haggioti ya koma gefen makeken gadonsa ya xauna ya sa bakar safarsa na kafa snn ya sa shoe din, duk wnn abinda yake kwata kwata bae da walwala, mikewa yyi ya shiga tucking din farar uniform din jikinsa kafin ya dauki belt ya sa, wayarsa ya dauka da hularsa ya koma gaban mirror ya feshe jikinsa da turarruka ya nufi kofa ya fita, Captain Ahmad Junaid kenan, A Certified seafarer (Merchant Navy)  Kmr bae son taka kasa yake tafiya a makeken compound din, sai yake ga kamar yayi shekara rabonsa da gidan nasu, Where as sati biyar kawai yayi a Egypt, kai tsaye part din Hajiyarsa ya nufa, bbu kowa falon se kamshi me ddi dake tashi da ya hade da kamshin soye soyen da ake a kitchen, falonta ya nufa da sallama cikin sanyayyan muryarsa, fitowarta daga bedroom knn ta amsa sallamarsa, xama yyi kan kujera yana kallonta yace "Gud morning Mumy" ta dan yi murmushi tana kallon agogo tace "Baka makara ba, dubi har bakwae ya gota ko duk gajiyar ce haka" Shafa lallausan gashin kansa yyi yace "Jiya da headache na kwana Mumy duk na gaji" tace "Ba na baka magani ba? Baka sha bne" a hnkli yace "Na sha" tace "Toh taso mu je kayi break, sae ka kuma sha, kar ka makara" mikewa yyi ya bi bayanta suka koma falo yace "Ina su Fatima?" Tace "Sun tafi makaranta" da kanta ta jera masa breakfast kan dinning, ta hada masa tea me kauri, snn ta koma falonta dauko masa magani, ko kan ta dawo ya shanye tean, don ba da xafi ta hada masa ba sanin bae shan abu me xafi, tana tsaye kansa ya kora maganin snn ya mike yace "Mumy bari in tafi am almost late" tace "OK, amma ka shiga ka gaida 'yan gidan, tun da ka dawo baka shiga ba" bude dara daran idanuwansa yyi bae ce komae ba ya kafa hularsa sai dai da gani kasan ransa bai so ba, ta rakasa har bakin kofa don ta tabbatar ya shiga gaida mutan gidan, part din Hajiya Fati ya nufa, ya tura kofar da sallama, xaune ya sameta tana karyawa a babban falo, xaunawa yyi yace "Ina kwana Hajiya" ta dan kallesa tace "lfya lau mutan misra, an ga daman shigowa gaida mu kenan" shiru yayi bai ce komai ba sai kuma ya mike yace "Na tafi aiki" daga haka ya fice daga falon, ta bi sa da kallo ba dae ka iya gane ma'anar expression din fuskarta, ta dan yi murmushi ta ci gaba da cin kwan gabanta, Part din Hajiya Bilki ya shiga, ita kuma ya sameta tana kunduma ma 'yan aikinta xagi kmr xata dokesu, 'yar ta Sadiya na kwance tana danna waya, daga bakin kofa ya tsaya ya dan duka ya gaisheta, harara ta 6alla masa tace "Ehh lallai Ahmad a 6akin kofa ka gaida Uwarka yau d'an rainin wayo, sai yanxu kasan da mu a gidan?" Hade rae yyi wanda hkn ya kara fito da ainahin kyansa na dan fillo, tsaki tayi ta ci gaba da 6abatun ta ma 'yan aikin ya juya yyi ficewarsa, parkin lot ya nufa ya dauki motar da xae dauka ya bar compound din bayan masu gadi sun bude masa gate, today at work was so stressful for Captain Junaid don duk a gajiye yake from yesterday's journey.
Karfe biyar da 'yan mintuna ya isa gida, ya jima xaune cikin mota yana latsa waya, ganin motar da ya shigo compound din ya sa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya nufi bangarensa, tuni itama ta fito daga motar tare da step sis dinsa Sadiya, bin bayansa tayi tana kallonsa cikin sanyayyan murya tace "Ya Junaid Ashe ka dawo!" Juyawa yyi har lkcn bae tsaya ba ya kalleta snn ya dauke kai yana ci gaba da tafiyarsa yace "Eh!" D'aga hka ya shiga balcony din bangarensa, dariya ta ji daga sama ta d'aga kai taga Muhibba dake xaune balcony macbook dinta a gabanta tana taunar cingam ta tabe baki tace "Cusa kai ba kwarjini" Suhaima ta dauke kanta xuciyarta na tafarfasa ta nufi bangarensu kmr xata tashi sama, Sadiya tayi 'yar dariya ta rufe motar ta bi bayanta. Shi kam dakin sa ya nufa ya cire uniform din jikinsa ya shiga bayi, wanka yyi ya fito ya shirya cikin kananun kaya, jeans baki da polo blue duk hankalinsa na gun Mum dinsa, wayarsa ya dauka ya nufi bangaren ta, xaune ya sameta falo ita da kanninsa Fatima da Aysha, gefenta ya xauna yyi mata side hug ya kwanta jikinta cikin murya me shige da ta shagwaba yace "Momyna am back" Fatima ta kalli Aisha suka tabe baki a tare, Mumy kam murmushi tayi ta dauke fuskarta tace "Welcm! ga abincin ka can dinning, ga dai kannin ka suna kallon ka" yayi 'yar dariya yace "Toh ina ruwana da su" gaishesa suka yi a tare, Fatima tace "Ya A.jay ina tsarabar mu" mikewa yyi ya nufi dinning yace "Aiki na tafi ba holiday ba ai" abinci kusan kala uku ya tarar dining din, farfesun naman rago ya soma diba yana ci. Ko da ya gama bai bar dining din ba yana ta danna waya ganin shidda ya kusa ya mike ya dawo parlor yace ma momy xae je gun abokinsa El-Ameen, tace "Maimakon ka huta kai da kake ciwon kai Ahmad!" Girgixa kai yyi yace "Mum ni ba ddewa xan yi ba" tace "toh shikenan Allah ya tsare!" Bangarensa ya koma ya canxa kaya xuwa farar shirt da blue jeans ya dauki makullin motarsa bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito ya nufi parkin lot ya dau motarsa ya bar gidan.  A hankali ya rage gudun da yake ganin d'andaxon jama'ar da ke gefen titi a tsaye, da yawan motoci ma sun tsatsaya gefen titi masu shi duk sun fiffito ko wanne na son ganin abinda ya janyo taron, a hnkli ya gangara gefen titi don a tunaninsa hatsari ne kuma bae ga alamar taimako mutanen dake tsatstsaye suke badawa ba yasan kallo kawae suka tsaya yi, bude motarsa yyi ya fito ya nufi cikin taron jama'ar ya kutsa kai, sae a snn ya dinga jin ihun da wasu ke yi, wata ya gani xaune tsakiyar taron hannunta rike da wani yaro da baxae wuce shekaru goma ba sae dukansa take iya karfinta, ga jini na xuba goshinta ba kadan ba, duk tayi dukun da daud'a cikin wata yagaggiyar doguwar riga, wasu samari biyu ne ke kokarin kwace yaron dake kurma ihu hannunta amma sbda irin rikon da tayi ma yaron suka kasa, da ganinta ka ga mahaukaciya, karasawa Junaid yyi da sauri inda suke ganin xata ma yaron lahani ya fixgo gashin kanta da yyi wani dukun dukun da datti, ta saki kara don ba rikon wasa yyi ma gashin ba, amma duk da hka ta ki sake yaron, kara damke gashin yyi da karfi ae ba shiri ta sake yaron tare da kwala wani k'aran, samarin biyu suka dauke yaron da ya rage kiris ya suma don wahala, ta yunkura xata cakume Junaid, ae da sauri ya hade hannayenta da karfi ya murda su xuwa bayanta, ta dinga ihu tana shure shure, kallon samarin gun yyi yace a samo masa igiya, ae da sauri suka juya xuwa neman igiyan, wata 'yar dattijuwa dake cikin taron ne tace "Baiwar Allahn nn ta kusa shekara unguwan nn bata taba kama d'an mutum tayi masa haka ba sae wannan karan, kuma wllh yaran ne suka addabeta da tsokana shi yasa tayi hkn" wata mata ta karbe tace "Yo dama idan ba tsokanarta suka yi ba me suka mata, dubi goshinta dutse suka jefa mata, yara basa ji sae daukan magana da tsokana, ni ko kadan ban ga laifin Baiwar Allahn ba, sae ma tausayin da ta ban, haba jama'a" nan dae aka dinga jajantawa, ko wa na fadin albarkacin bakinsa, shi dae yana rike da hannunta ta baya, ta sunkuyar da kai, duk farin shirt din jikinsa ya bace da datti, samarin ne suka dawo da igiya babba, da taimakonsu ya shiga daure mata hannu da kafa, ba karamin kokuwa suka sha da ita ba yyi mamakin karfinta hka, Suna gama daureta ya koma baya yana kallonta don ganin ko xata iya kuncewa, hawaye ne ke sakkowa daga idonta, jikinsa ne yyi sanyi yana kallonta, lkci daya tausayinta ya ratsa sa, a hnkli ya shiga kakkabe hannunsa, idonsa ya kai kan goshinta da har ya gaji da fidda jinin da yake ya daskare, ya girgixa kai yana kallon samarin yace "Ku taimaka a sa min ita a mota in kai ta a duba goshinta" 'yar dattijuwar daxu tayi wani k'ara tace "Wani asibitin yaro? Ynda Duniyar nn ta dawo ba gskya ynxu, kai waye? Kuma d'aga wani anguwa kake?" Nan jama'a suka fara cece kuce a wajen ana kallonsa, shiru yyi bae ce komae ba, can ya sauke ajiyar xuciya ya juya ya nufi motarsa cikin rashin kuxari, nn aka bi sa da kallo ana cewa "Kun ga rashin gskyar knn, don da yana da ita da dole xae tsaya ya amsa tambayoyin da aka yi masa, kaiii Allah ya raba mu da sharrin mutum" shi kam motarsa ya shiga ya ja ya bar wajen, nan aka fara watsewa kowa na fadin albarkacin bakin sa, wani tsoho ne ya karasa ya kunce mata daurin yana d'an ja da baya kadda ta cafkesa har ya gama ya bar wajen bata d'ago ba bare ta kallesa.
 
  ?
*Haske Writers Association* ?
 
⚓ *Captain Ahmad Junaid* ⚓
 
      _By Khaleesat Haiydar_?
 
2....
 
Junaid na isa gidan su El-Ameen yyi parking daga waje ya shiga, Sumayya kanwar El-Ameen ya  samu xaune falo da kawayenta biyu, ya karasa cikin falon cikin tafiyarsa ta k'asaita, yi tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take, gaida shi kawayen nata suka yi suna kallonsa, don Capt Junaid ko namiji bae masa kallo daya, ya amsa gaisuwar su ba tare da ya dube su ba yana kallon Sumayyar yace "Ke yayanki na gida?" Ba tare da ta kallesa ba tana yatsine fuska tace "Nima bn sani ba" wayarsa ya ciro aljihunsa ya shiga kiransa, Kawayen nata biyu duk suka xuba masa ido, El-Ameen na d'agawa Junaid yace "are yhu at home?" El-Ameen yace "Yea are you coming?" Wani kallo ya watsa ma Sumayya ya katse wayar ya nufi dakin El-Ameen, Husnah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kai Sumayya waye shi, ya hadu wllh, don Allah ni dae ki hada ni da shi, yyi min ni dae plss" Sumayya tayi dariyar rainin hnkli tace "Uhm Kinga gayen nn irin mace masa da nake a da, na so shi kmr raina amma he looked into my face nd told me baya sona, I cried my life dat day, gashi i downgraded my sef telling him I love him" bude baki duk suka yi suna kallonta, Fiddausi tace "Tabdi! Toh meye hadin ku da shi? D'an uwanku ne?" Tsaki Sumayya ta ja ta dauki lemon gabanta ta shiga sa.      Xaune ya samu El-Ameen kan laptop da siririn farin glass a idonsa yana danne danne, El-Ameen ya kallesa yace "Uhnn! Our great Capt Ahmad Junaid Murnai, kaga yanda ka kara kyau ka koma kamar wani Egyptian kuwa" Junaid ya tabe baki ya xauna gefen makeken gadon dakin yace "You will neva change" El-Ameen yyi murmushi ya tura laptop din gabansa ya juya yana fuskantarsa yace "I missed you a lot frnd, am glad you are back" Junaid ya shafa kansa yace "Sai kace gaske," El-Ameen ya kura ma farin shirt din jikinsa ido yace "Wait! Ciwo ka ji Captain" Junaid ya kalli shirt dinsa da sauri ya ga jini daga gefen shirt din, El-Ameen ya mike yace "What's dat? The shirt looks dirty ma" girgixa kai Junaid yayi ya shiga unbuttoning din shirt din yace "Wata mahaukaciya ce wllh" El-Ameen ya kwalalo ido yace "Mahaukaciya kuma" Junaid yace "Yea!" Nan ya ba El-Ameen lbrin abinda ya faru a hanyarsa ta xuwa, El-Ameen yace "Eyya! Poor her, but kai me ya kai ka rike mahaukaciya ma banda abun ka" Junaid bae ce komae ba ya mike ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito sanye da Bathrobe din El-Ameen ya goge jikinsa ya bude wardrobe ya fiddo wasu kayan abokin nasa ya sa.  Bayan Magrib yace ma El-Ameen xae koma gida, El-Ameen yace "Haba frnd baxa ka raka ni gun Iman ba plss, wllh ban san me xan ce ba idan na je, gashi Mami fushi take da ni, escort me plss, dama jira nake sai ka dawo sai mu je" Junaid yyi d'an murmushi yace "Ohk buh bari in kira mumy kar taji shiru har ynxu" Bayan isha suka bar gidan bayan Capt Junaid yyi ma Ummin El-Ameen sallama, A motar Junaid suka tafi El-Ameen na tukin, El-Ameen ya lura da yanda Junaid ya kafa ma tagar motar ta inda yake xaune ido yana kallon waje, El-Ameen xae yi magana ya ji Junaid yace "Dr d'an tsaya nn don Allah in ga ko an kwance mata igiyar, it's gud ace anyi hkn" El-Ameen ya kafa masa ido sae kuma ya tabe baki ya daga shoulder ya gangara gefen titi yyi parking, Junaid ya bude motar ya fita, tana nn xaune kan bolan, rike da wani bakin Leda a hannunta, rungume hannayensa yyi yana kallonta, El-Ameen ya dafa sa yace "let move on Capt, they've freed her" juyawa Capt Junaid yyi suka koma motar suka bar wajen, suna isa gidan El-Ameen ya kira Iman da nmbr da Ummi ta basa, kanwar ta ce ta fito tayi masu iso har falo ta cika su da drink, mahaifiyarta ta fito suka gaisa ta bar palon, ba a dau lkci ba Iman ta fito sanye da wata doguwar riga me adon stone blue da gold, tayi rolling kanta da plane blue mayafin kayan, kyakkyawa ce ba kadan ba, ta karaso falon kamshin turarenta ya cika ko ina ta xauna, kallon Junaid El-Ameen yyi, Junaid ma ya kallesa, suka shiga kallan kallo, ganin El-ameen yaki cewa komai Junaid ya d'an yi gyaran murya yana kallonta yace "Ina yini Hajiya" amsawa tayi ba tare da ta kallesu ba, Junaid ya d'an taba El-ameen alamar yyi magana mans, a hnkli El-Ameen ya matso kusa da shi murya can kasa yace "Me xan ce mata plss" ae Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba, El-Ameen ya tsaya kallonsa sai shi ma ya saka dariyar, nan suka dinga dariya kamar tababbu suka yi me isan su suka yi shiru, Junaid ya shafa kai yana kallonta yana murmushi yace "Ehm dama Ummi ce tace in rako El-Ameen wajen ki.... Shine muka xo" El-Ameen yace "Eh Ummi ce tace in xo gurin ki shine ya rako ni" kala bata ce masu ba, Junaid ya mike yace "Toh shknn mu xa mu koma sai mun sake dawowa" El-Ameen ma ya mike yace "Eh xa mu koma, sae wani lkcn, mun gode kwarai" mikewa tayi tace "Allah ya kiyaye" daga haka ta haura sama ta bar su tsaye parlon, dariya suka dinga yi cikin motar barin Junaid, El-ameen ya ja motar suka bar anguwar daga karshe, sae da El-ameen ya kai kansa gida sannan ya fita suka yi sallama Junaid ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, yana isa inda mahaukaciyar take yyi parkin yana kalle kallen inda xae ganta daga cikin motar, sae bae bae ganta ba ya ja motar ya nufi gida. Yana jiran masu gadi su bude masa gate kiran mum dinsa ya shigo wayarsa, jan motar yyi ya shiga compound din ya nufi parkin lot yyi parking snn ya fito, ganin motar Abba yasa shi kallon agogon wrist dinsa ya ga har goma ya kusa, bangaren mumy ya nufa, tsaye ya sameta palo tana rike da wayarta ta rungume hannu, yyi murmushi yace "Ga ni na dawo Mum," ta hade rai tace "Daga ina kake hka Ahmad?" Ya shafa kansa yace "na gaya maki Gidansu El-Ameen na tafi mum, na raka sa xance ne" yana murmushi ya k'are maganar, mumy tace "Zance! Lallai ba ayi abun arxiki ba kenan" dariya yyi lkci daya ya hade rai yace "Allah mum mun yi magana me ma'ana, infact ni ne ma nayi don shi shiru yyi wai kunya" Mumy tayi dariya tace "Au, kace ka kora masa budurwar knn in har kai kayi magana, tab!" Dariya shi ma yyi ya mata side hug yace "Kai Mumyna ni din ne ban iya magana ba" murmushi tayi tace "Kaje gun Abba yana neman ka" ya saketa yace "Ohk Mum" kofar da xae sada sa da part din dad dinsa ya nufa, xaune ya samesa babban falonsa yana kallon news lkci daya yana shan fruit salad din dake kan d'an table gabansa, Hajiya Fatee na xaune gefensa, sae step sisters dinsa su uku gaba daya suna palon, xaunawa yyi kasan lallausan rug din yana kallon Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa daga ina kake naga baka duty ae" yace "Naje gidansu El-Ameen ne Abba," kallon Hajiya Fatee yyi yace "Ina yini Hajiya?" Tayi murmushin da bai kai ciki ba tace "Lfya lau, ya aikin" yace "Alhmdllh" Muhibbah ce ta shigo falon da sallama rike da bowl din kankana da akayi slicin, ta duka ta ajiye gefen Abba, xama tayi tana kallon junaid da ya maida hankalinsa kan Tv tace "Ina yini yaya" amsawa yyi ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Fatee sae kallonsa ta gefen ido take, mikewa Junaid yyi yace "Sae da safe Abba" Abba yace "Yauwa ka ba Muhibbah dubu ashirin xa tayi amfani da su a makaranta gobe wae," yace "toh Abba" daga nn yyi ma Hajiya Fatee sae da safe, kanninsa ma suka yi masa sai da safe ya fice daga falon rai a bace, mikewa Muhibba tayi ta bi bayansa, bae tarda mumy a palo ba, hka yasa ya nufi bedroom dinta ya sameta har ta kwanta, xauna wa yyi daga gefenta yace "Kin kwanta mum?" Tace "Har ka fito?" Yace "Eh mum" peck din goshinta yyi yace "Gudnyt mum, xan tafi in kwanta" tace "Toh Allah tashe mu lfya, make sure kayi alwala kayi addu'a kafin ka kwanta" yace "In'sha Allah mum" mikewa yyi ya kashe mata wutan dakin ya rufe mata kofa ya fita, dakin da kanninsa suke ya bude, Aisha ce ke waya ita ko Fatima tayi bacci, ya rufe kofar ya fito parlor, xaune ya tarda Muhibbah tana jiransa, yyi mamakin rashin ganin Hijab a jikinta don da hijab ta shigo palon Abba, kauda kai yyi ya fita daga parlon ta mike ta bi bayansa, yana isa part dinsa ya bude ya shiga ya juya yana kallonta ganin tana kokrin shigowa yace "Ki jira ni a nn malama" rufe kofar yyi, ta hade rae ssae tana kallon kofar, tsaki tayi ta bude ta shiga, ganin bae palon ta nufi bedroom dinsa, ya dauko kudin zae fito suka kusa cin karo, wani tsawa ya daka mata yace "Are yhu insane xa ki biyo ni daki" kallonsa ta tsaya yi, yyi tsaki ya bangajeta ya fice a fusace, bin bayansa tayi ba tare da ta ji haushi ko kadan ba, a palo ya jefar da kudin ya nufi kofa ya bude yace "Leave yanxu!" D'an tsaki tayi ta duka ta dauki kudin ta fice, ya kulle kofarsa ya sa key don wani mugun haushinta yake ji a gidan. K'asa bacci yyi daren ranan, duk juyin da xae yi sae mahaukaciyar nn ta fado masa, hankalinsa ne ya tashi don shi dae bae mata komae ba illah taimakon yaron da yyi, mikewa yayi daga karshe ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida pray mat ya shiga nafila, sae kusan Karfe uku da rabi bacci ya daukesa. Da asuba ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, kmr jiya yau ma bae fita mosque sllhn asubahin ba sbda ruwa, ruwan dumi ssae ya hada yyi wanka don ko kadan bae son sanyi shi, ya shirya cikin uniform dinsa ya dauki babban kadigan na uniform  me kalan Navy blue ya sa snn ya fito falo rike da rain coat dinsa, sae da ya tabbatar wayoyinsa na aljihun wandon uniform din jikinsa snn ya fito balcony ya saka rain coat din da hulansa ya nufi bangaren Mumy, a balcony ya cire rain coat din ya bude kofa ya shiga, tana kitchen da mai aikinta sai fatima suna hada breakfast, ya shiga kitchen din ya gaisheta ta amsa da cewa "Ka tashi lfya, ya ruwa?" Yace "Alhmdllh mumy" Fatima ta kallesa tace "Gud morning ya Ahmad" yace "Morning" ya fita kitchen din, tea kawae ya sha da kwae shi ma sae da mum ta takura sa wae ya makara xuwa aiki, har balcony ta rakosa tace "Baxa ka shiga gaida 'yan gidan da Abba ba kenan" ya dan tsuke fuska yace "Am late mum," tace "Toh Allah ya tsare" rain coat dinsa ya sa yace "Ameen" snn ya nufi parkin space, kusan a tare suka jero da Suhaima dake rike da lema tayi shirin makaranta, ko kallonta bae yi ba ya bude motarsa ya shige ta nufi tata motar tana kallonsa, jan motar yyi ya danna horn aka bude masa gate ya fice. A hnkli ya ke driving din har ya iso inda mahaukaciyar jiya take, samun kansa yyi da parking gefen titi yana kalle kallen inda xae ganta idonsa ya sauka kanta, xaune take cikin ruwan ta hade kai da gwiwa, duk ta jike da alama tun da ruwan ya sauko bata bar wajen ba, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera yana ci gaba da kallonta, duk jikinsa yyi sanyi, da kyar ya iya jan motarsa ya bar wajen ganin yana bata lkci, shi mutum ne me tausayi da raunin xuciya kamar mace, har ya isa office bae da sukuni, colleagues dinsa duk suka lura da shi suka kuma tambayesa ko Lfya yace bai jin ddi ne, Karfe biyar saura ya bar gun aikin, driving kawae yake cikin rashin kuxari, bae bi hanyar da xae ga mahaukaciyar ba ya canxa hanya, ko parking din arxiki bae yi ba ya bude motar ya nufi part din mumyn sa, kwanciya yyi kan dogon kujera ya rufe idonsa gam, Mumy ce ta fito daga kitchen ganinsa a kwance tace "Lfya Ahmad" jin bae ce komae ba yasa ta karasa kusa da shi tace "Ahmad!" Bude idonsa da ya kada yyi ya mike xaune ya dafe kansa, taba jikinsa ta shiga yi da damuwa tace "baka da Lfya ne?" Lumshe ido yyi ya kwanta jikinta ta rungume sa tace "Talk to me mana son, me ya faru?" A hnkli yace "Kai ne ke man ciwo Mumy" tace "Ci abinci mu tafi asibiti" da sauri yace "No mum, xan sha magani" hade rai tayi tace "Wani maganin xa ka sha, sau nawa kke sha bae maka aiki ba, so kake ka dauko min magana gun Abba koh" shiru yyi ta mike ta nufi dinning ta dawo rike da kulan abinci da plate da spoon, fried rice din ta dibar masa ta ajiye snn ta koma kitchen ta hado masa tea, bae son mum din tasa ta daga hankalinta shi yasa ya daure ya dinga cin abincin don kwata kwata bae da appetite. Mikewa yyi da ya gama Mumy tace "Ka tafi ka canxa kawae mu tafi clinic" yace "Toh" snn ya fita xuwa bangarensa, wanka yyi ya canxa uniform din jikinsa xuwa kananun kaya, ya d'an kwanta yana tunanin karyar da xae ma Mumy ta hakura da xuwan su asibiti, dubara ce ta fado masa ya mike da sauri ya dauki wayarsa ta fita, xaune ya sameta palo ta shirya tana jiransa, murmushi yyi yace "Mumy ynxu El-Ameen ya kira ni, I told him m nt ok, shine yace I shud cum over ya duba ni" hararansa Mumy tayi tace "Yhu should come over dai kuyi hira, my frnd mu wuce clinic" marairaice mata yyi ya mata side hug yace "Haba mum, ga ni da amini likita kice mu je clinic, kinga baxae ji ddi idan ban je ba plss"
 
?
*Haske Writers Association*?
⚓ *Captain Ahmad Junaid* ⚓
 
                      
  _By Khaleesat Haiydar_?
 
3.....
 
Wani kallo Mumy tayi masa tace "Kaga ka kiyaye ni Ahmad, baxa ka gun El-Ameen din ba asibiti xa mu" shiru yyi yana kallonta sanin baxae taba convincing dinta ba, a hankali yace "Toh kiyi hkuri mumyna mu tafi asibitin" jakarta ta dauka tace "Sake ni mu tafi" saketa yyi dai dai lkcn da wayarsa ya fara ring, fiddowa yyi a aljihu yana kallon me kiran nasa ya ga El-Ameen ne, ya juya ya kalli Mumy ya ga kallon wayar take, d'agawa yyi ya kai kunne daga daya bangaren El-Ameen yace "ya ne captain, kana gida yau?" Junaid ya d'an saci kallon Mumy ya ga kallonsa take, yace "Noo! Don't worry frnd Mumy tace mu tafi clinic kawae ba sai na xo ba" El-Ameen yace "What are yhu talking about guy?" Junaid yace "No ba komae wllh, kawae dae tace mu tafi asibiti ne" tsaki El-Ameen yyi yace "HeyJunaid are you ohk, wat are yhu sayin?" Junaid yace "Ohk Tnx for ur care frnd!" D'aga hka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya mayar aljihunsa yana sinne kai, Mumy tace "Don me xaka ce Mumy tace, maimakon kace Abban ka ne yace kaje clinic" Junaid yyi shiru yana kallonta, komawa tayi ta xauna ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn, ka tafi can ya duba ka, amma yana prescribing maka magunguna ka dawo Ahmad, I repeat my self ka dawo" farin ciki ya lullubesa sae dae yyi kkrin boye hakan yace "Toh Mumy I promise" har bakin motarsa ta rakasa tace "Drive carefully" yace "Sure mum" tana tsaye har ya bar gidan snn ta juya xata koma bangarenta, xaune ta ga Hajiya Fatee da Hajiya Bilkee a balconyn Hajiya fateen suna kallonsu, Mumy ta karasa tayi masu sannu da xama, Hajiya Bilki kadae ta amsa da yauwa a dakile, juyawa Mumy tayi xata bar wajen Hajiya Fatee tace "Ynxu an ma hana d'an gwal din xuwa gaida mu tsabar mulki" juyawa Mumy tayi tana kallonsu tace "Ayya Bashi da lfya ne, ynxun ma gun likita xa shi" bbu wanda ya tanka ta cikinsu, ta nufi bangarenta ba tare da ta sa ma kanta damuwarsu ba.  Junaid na isa ya tarda El-Ameen na clinic, bae so hkn ba amma bbu ynda ya iya hka ya nufi Babban asibitin Dad din El-Ameen din, don shima kwararren likita ne da yyi fice a Nigeria, da yake Nurses din sun san tsakanin Junaid da El-Ameen, bbu wanda ya dakatar da shi xuwa office din El-Ameen din, murda kofar yyi ya shiga babban office din, El-Ameen dake xaune yana dube duben files sanye da farin glass a idonsa ya dago yana kallon Junaid, ajiye pen din hannunsa yyi ya rike ha6a yace "Kan ka daya kuwa captain?" Dariya junaid yyi ya xauna kan table din office din yace "Kai da ban yi hka ba da Mumy bata bari na xo ba yanxu ai" El-Ameen ya girgixa kai yace "Mummy's boy, na ga randa xaka girma ka samu freedom din kanka" murmushi yyi yana shafa kansa yace "Uhm am 30 ynxu kace ban girma ba, ae kila har in mutu baxan samu wannan freedom din gun momma na ba" El-Ameen yyi dariya yace "Idan kayi aure xa ka samu" murmushi Junaid yyi yace "Aure kuma" kallonsa El-Ameen yyi ya cire glass din idonsa yace "Amma ba ka jin ddi koh, you look weary?" Junaid ya lumshe ido ya bude da damuwa yace "Kinda frnd! Am just disturb, bani da kwanciyar hankali kwana biyun nn, M just nt my self..." Rike kai yyi ya kasa ci gaba, El-Ameen ya dafa sa yace "What's wrong frnd, tell me ur problem, 'Yan gidan ku ko?" Junaid ya d'aga kai yana kallonsa cike da damuwa yace "No! Wnn mahaukaciyar ban san ko laifi nayi da na kwace yaron nan a hannunta ba, duk na kwanta ita nake tunawa nake gani, k'asa bacci nake yanxu duk bani da sukuni" El-Ameen ya ja tsaki ya mayar da glass din idonsa ya jawo files din gabansa yana ci gaba da dubawa yace "Thought it to be something better ma, wai mahaukaciya" wani tsakin ya kuma ja, Junaid ya runtse ido  ya watsar da files din yace "Haba Dr in ce maka bana iya bacci kace min yhu thought it was somethin better," El-Ameen ya rike chin dinsa yana masa wani irin kallo da mamaki yace "Wae halan kana da dangantaka da mad woman din nn ne junaid" a fusace Junaid yace "Wa ya sani" wani dogon tsaki El-Ameen ya kuma ja yace "Kaga ka rabu da ni, I have meaningful things doing ynxu, aikin gaba na ma ya ishe ni stop bothering me plss da wata mahaukaciya can." Kallonsa junaid ya tsaya yi na kusan minti biyu kafin ya sauka daga kan table din da yake ya dauki wayarsa da makullin mota ya juya ya nufi kofa, bin sa da kallo El-Ameen yyi kafin ya birkita lallausan gashin kansa a xuciyarsa yace "What's wrong with Junaid da xae damu kansa ya damu wani da wata gagarumar mahaukaciya can" mikewa yyi da sauri tun kan ya fita ya kulle kofar office din yace "Look Captain, to ynxu me kake son ayi da rashin baccin naka, ko kuma dai kawai mu je ka ba mahaukaciyar hakuri?" Junaid ya kallesa yace "bude min kofa" El-Ameen na 'yar dariya yace "Of course No baxan bude maka ba sae ka gaya min dalilin ka na xuwa gu na, which help do yhu want me to render yhu, mu je ka nemi gafararta mad woman din ne" tuni idon Junaid ya sauya kala, still behaving gently yace "Bude min kofa nace" El-Ameen yace "Noo!" Wani kara yyi ya cakumo sa yana huci yace "Bude min kofa Ahmad!" Murmushi El-Ameen yyi yace "Naki! ka xama Zaki a nn in ga" turasa da karfi Junaid yyi ya koma kan dogon kujera ya xauna ya rike kai, El-Ameen yyi dariya ya koma kan office chair dinsa ya xauna, sae bayan kusan minti goma Junaid ya dago kansa, ya kalli El-Ameen dake ta aikinsa, El-Ameen yace "Har iskokan sun sake ka kenan" Junaid bae ce komae ba ya kauda kai, mikewa El-Ameen yyi ya dawo gefensa ya xauna yace "Now tell me, ya kake son ayi?" Junaid ya sauke ajiyar xuciya cikin sanyi ya fara magana, "Frnd! May be tana son in taimake ta ne, shi yasa take bi na, she want me to help her" El-Ameen ya kwalalo manyan idanuwansa yace "Kayi me?" Shiru Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen ya girgixa kai yace "Yhu must be crazy Junaid, meye hadin ka da wata mahaukaciya can har kake tunanin taimakon ta, kai ka daura mata haukan, ko kasan me ya haukatar da ita? Wait! which help ma xaka iya rendering dinta tukun, taking her to psychiatry nd staying with her there ko yaya?" Junaid ya tabe baki yace "Ae dan Mumy da Abba baxa su yrda bne da nayi hkn wllh" El-Ameen yyi dariya sosai yace "Ehh lallai Junaid ka ja ma kanka" Junaid yyi kasa da murya yace "Listen to me plss Dr, ban da kai akwae wanda xan kai ma damuwar da na k'asa gaya ma mahaifiyata duk kusanci na da ita, why kake min hka frnd?" El-Ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Noo ba hka ba Junaid, ynxu tell me ya kake son ayi, hw did yhu want me to help in here?" Cikin kwantar da murya junaid yace "yhu are a Neurologist as well as a qualified MD, I knw yhu can cure her by the grace of Allah idan ka sa kanka, yhu neva can tell where one's reward Lie's" wani matsiyacin kallo El-Ameen ke yi masa kafin ya mike yace "Gaskiya ka janyo ma kanka fitina ka ja mana muma da muke tare da kai Ahmad, dama ban da abun ka me ya kai ka kama mahaukaciya kai da kake tuki a mota, Ohh My God! ga irinta nn ka tabo aljana, don Wllh yhu are not on ur right senses" Mikewa Junaid yyi shi ma yace "Stop this El-Ameen, meye illar taimakon Baiwar Allah da xa mu yi? Haba idan wani yace min xaka yi hka I won't believe wllh," El-Ameen yyi shiru yana kallonsa baki bude, cike da mamakin aminin nasa, Junaid ya juya ya nufi kofa rai bace, girgixa kai El-ameen yayi yace "listen Captain" ko sauraransa Junaid bae yi ba ya fice daga office din, ya birkita kansa ya bi bayansa da sauri, a tare suka isa inda motar Junaid yake, El-Ameen yace "Haba frnd listen to me, ynxu mu koma ka min bayani sosai yanda zan gane abinda kake nufi don wllh am confuse" hararansa Junaid ya shiga yi yace "Ka dae san ba kai kadai bane abokina likita ba koh?" El-Ameen ya d'an yi murmushi yace "I know" hannunsa ya rike suka koma asibitin dae dae lkcn da wayar Junaid ya shiga ringing, fiddo wayar yyi yaga Mumy ce ke kiransa, El-Ameen yace "Mummy's boy" d'agawa Junaid yyi daga daya bangaren Mumy tace "Ka kyauta Ahmad" Junaid ya marairaice yace "Ohh Ummata, drip karami yake kara min ne fa, nd am feeling much beta ynxu har na ci abinci kuma" Murmushi Junaid yyi bayan ya gama sauraranta yace "in sha Allah mum" daga hka ya katse wayar suka nufi office din El-Ameen. 
El-Ameen ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yana kallon Junaid yace "ina jin ka, Allah sa ka dawo senses dinka yanxu, ya kake son ayi kace?" Junaid ya lumshe ido ya bude yace "Wae da cure dinta nake son kayi ko nawa ka bukata xan biya ka" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh i see, A can kan bola xan dinga tafiya ina samun ta kenan" Junaid ya ce "Noo of course, dauko ta xa mu yi" El-Ameen ya bude ido yace "Mu kai ta ina? Gidan ku?" Hararansa Junaid yyi yace "Plss frnd be serious, a gidan ka xa mu ajiye ta, ni idan nace xan ajiyeta a nawa gidan dole sae su Mumy sun sani, barin ma ni da nake da 'Yan sa ido, kai kam bbu me sa maka ido" El-Ameen ya buga table din gabansa yace "Wnn ne kuma baka isa ba Malam, I can't keep a mad woman in my house, the house that's meant for my wife!" junaid yyi shiru yana kallonsa, a hnkli yace "Ohk let me rent an apartment" Tsaki El-Ameen yyi yana Mamakin Matsalar Junaid, anya kuwa kansa daya, Junaid yyi murmushi yace "I knw u are thinking if am alryt at all, tausayi ne ba wani abu ba frnd, naga yarinyar is too young ace hakan ya sameta duk da ba a ja da ikon Allah, baka san inda rayuwa xae yi da kai ba wataran frnd, it really pays to be kind, and you neva can tell where one's reward lies! ni xuciyata daya nake son taimakonta saboda Allah, I will pay yhu wat ever amount yhu require for the bill, ni dae fatana ta samu lfya ta nemi 'yan uwanta" wani dariya El-Ameen yyi yana tafe hannu yace "Toh governor Ahmad Junaid, don this is the government's job not urz" mikewa Junaid yyi yace "What ever, ynxu dae let me start lookin for an apartment" El-Ameen ya daga kafadarsa yace "Left to yhu, amma ina guje maka reaction din yan gidanku idan suka ji shirmen da kake shirin aikatawa" Junaid yyi tsaki yace "Ni dae nemo plaster ka sa min a hannu am leaving, gobe I might come back idan na sami apartment" El-Ameen ya mike ya dauko plaster ya mika masa yana kallonsa cike da mamakinsa, a tare suka fito, El-Ameen yace "Yi Dropping dina a gida kawae, na mance key a office" a hanya El-Ameen ya kwashe da dariya yace "Tabdi wa ya ga Capt Junaid da taimakon mahaukaciya, but idan taimako kake son yi Why not kaje orphanage home kayi ne" share sa Junaid yyi, yana parking kofar gidansu ya juya yana kallonsa fuskarsa daure yace "Sae da safe" El-Ameen yyi dariya ya bude motar ya fita sanin har ya ji haushi ne.
 
?
*Haske Writers Association*?
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
 
      _By Khaleesat Haiydar_?
 
4.....
 
Washegari Karfe hudu da wani abu Junaid ya baro office, tun safe dama ya kira agents din Abbansa yace su sama masa apartment ko me dakuna biyu ne but kar su yrda Abba ya sani, driving yake yana kokarin kiran daya daga agents din yaji ko an gama komae, mutumin na d'agawa ya gaishesa snn yace "Yallabai an samu, amma xaka iya xuwa ka ga ko ya maka" Junaid yace "Alryt! Ohk, na gode" katse wayar yyi ya nufi asibiti gun El-Ameen sanin yana clinic, xaune ya samesa yana attending to wata patient, Junaid ya nufi bedroom dinsa da ke office din ya kwanta, bayan minti talatin El-Ameen ya shigo ya cire farin lab coat din jikinsa yace "Uhnn! Ko uniform baka cire ba tsabar xumudin taimakon mahaukaciya kenan" Junaid ya mike xaune ya hade rai yace "Yea daga office nake, na kuma samu apartment" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh dats gud for yhu" Junaid yace "But yau da nyt xa mu dauko ta ko" wani kallo El-Ameen yyi masa yace "Xa dae ka dauko ta malam, kai da wa xa ku dauko ta" shiru Junaid yyi yana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh naji xan dauko ta" mikewa yyi yace "i will be on my way, but ina son ka min favour daya, plss motar ka xaka bar min a layin ku sae ka bar min key din karkashin motar ko in btwn flowers dake kusa da motar, I will then cum over to take it sbda Mumy baxata bar ni in fito so late ba" El-Ameen ya bude ido yace "What? A motar tawa xa a saka mahaukaciya, kuma tsabar walakanci sae in bar motar at risk da makulli a waje, you are dreaming" Junaid ya girgixa kai yace "Ka dae san ba sonka Allah ya fi yi a kanta ba da ya barka da hankalinka ita ya gusar mata da nata koh?" El-Ameen yace "Toh preacher, amma ni baxan bada motata ba period!" Junaid bae ce komae ba ya fice daga dakin, tunanin wa enda xa su taimaka masa ya dauko mahaukaciyar ya dinga yi, sae da ya biya ya duba apartment din da aka samar masa ya ga ba laifi snn ya nufi gida. Da daddare yana xaune palon Mumy yana cin tuwon shinkafa da lafiyayyen miyar vegetable da tayi masa, sae dae duk bae da appetite turawa kawae yake, ya kalli Fatima dake kwance parlon yace "Xo dauke abincin nan" ta mike tace "Baxa ka ci bane yaya?" Bai ce komai ba hakan yasa ta kwashe tray din tayi kitchen da shi, takwas da rabi ya mike ya shiga bedroom din Mumy don mata sae da safe, tace "Yau ba hiran kenan" yayi yake yace "Bacci nake ji momma" tace "To Allah ya tashe mu lfya, make sure yhu ablute nd pray b4 going to bed, kuma ka rufe windows ka ga hadari" yace "In'sha Allah mum" fita yyi daga bangaren nata rike da wayarsa. Bedroom dinsa ya shiga ya canxa kaya cikin hanxari snn ya fito, gate ya nufa yana yi yana waige waige har ya fice, da kafa ya karasa titi iska na kadawa sosai ga walkiya alamar ko da yaushe ruwa xae iya sakkowa, yana tsaye yana jiran abun hawa abinda bae taba yi ba duk tsawon rayuwarsa a iya saninsa, bae ma san ta ynda xae tsaida adai daitan ba sae kalle kalle yake gashi kuma sae wucewa suke, yayyafi aka fara yi sosae, ya lumshe ido ya bude yana kallon motocin dake wucewa, wata farar lafiyayyen mota ce tayi parking gefensa, wata kyakkyawan yarinya ta fito sanye da hijab tana kallonsa tace "Bawan Allah shigo in rage maka anya if its ok by yhu, ka ga its raining kuma ruwan xae iya karfi at anytime, na wuce daxu xanje pharmacy na ganka kuma na dawo na kuma ganin ka" kallon motar yyi snn ya kalleta, yarinyar baxata wuce 18 ba, ta d'an bude ido tace "Noo! Am just being helpful" daga hka ta juya xata koma motar ta, sanin bashi da wani alternative yasa ya bude gaban motar ya shiga, dai dai lkcn da ita ma ta shiga maxaunin driver, ta kallesa ta ja motar suka bar wajen, tana tuki tace "Ina ka nufa?" Ba tare da ya kalleta ba ya gaya mata, tace "Ohk" wayarsa ce ta fara ring ya ciro a aljihunsa ya ga El-Ameen ne, da kmr baxae daga ba sae kuma ya d'aga ya kara a kunne yyi shiru, El-Ameen yace "Ya ka samu fitowan?" Cikin kaushin murya yace "Ba Matsalar ka bne wnn" El-Ameen yyi dariya yace "Haba name same, naga baka xo daukan motar bane har ynxu" Junaid yace "Ehh xan je in karba na Faisal" El-Ameen yace "Kai na fa fito maka da motar Wllh come over, yhu knw I can be annoying a times" Junaid yace "Noo dnt wrry ina hanyar gidan ynxu" El-Ameen yace "Look stop this plss junaid, na fito maka da mota Wllh, just teasing yhu daxu" Junaid yyi shiru sanin baxae iya fushi da abokin nasa ba, lumshe ido yyi ya bude yace "Ohk" snn ya katse wayar. Juyawa yyi ya kalli yarinyar ya gaya mata anguwarsu El-Ameen yace nn xani, tace "Ohk" dai dai bakin gate yasa ta tsaya ya juya yana kallonta yace "Thanks a lot" tace "Yhu are welcm!" bude motar yyi xae fita duk da ruwan da ake tsugawa, sae kuma ya juya ya kalleta, wayarsa ya ciro ya mika mata yace "Sa min digit din ki so I can thank yhu some other time" tace "Do yhu need to? Its ohk ba sae ka kuma gode min ba, it payz to be kind" murmushi yayi ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ohk Allah saka da khairan" juyawa tayi bayan motar ta dauko raincoat ta mika masa tace "Hope yhu will cope with this" karba yyi ya kuma mata godiya ya fita daga motar, ta ja motar ta bar wajen. Bin motar yyi da kallo dai dai lkcn da aka dallara masa wutan fitilar mota, juyawa yyi yaga motar El-Ameen ce, karasawa yyi da sauri yana rike da raincoat ya bude front seat ya shiga, El-Ameen yace "Wani mota ce wannan?" Junaid yace "A good Samaritan" El-Ameen ya tabe baki yace "Ynxu ka mana adalci kenan Junaid, ko wani mahaluki na cikin bargo cikin ruwan nn kasa muna tsaye a titi?" Junaid yace "Look! Ni ae bn ce ka fito ba xaka iya komawa abun ka" El-Ameen ya hararesa yace "Ehh In koma ka ji haushi na koh" Junaid yace "No Baxan ji ba" tsaki El-Ameen yyi ya tada motar suka bar layin, sae da suka hau kan titi snn yace "Ynxu ina xa mu bi?" Junaid ya gaya masa suka kama hanyar inda mahaukaciyar take, banda tsaki bbu abinda El-Ameen yake, shi dae Junaid bae ce komae ba har suka iso, Junaid ya fara kalle kallen inda xae hangota, bae ganta wajen ba hankalinsa ne ya tashi, shi dae El-Ameen kallonsa kawae yake, ya juya ya kalli El-Ameen yace "Frnd bn ganta wajen ba kuma" El-Ameen yace "Toh me xan yi ni kuma, haka kawae ka shiga hakki na ka hanani kwanciya cikin sanyin nn" bude motar Junaid yyi ya fita cikin ruwan, ya fara nemanta, lkci daya ya jike jagab, can ya hangota rabe jikin bango kusa da wani kiosk duk ta jike jagab ta takure waje daya, wani tausayinta ne ya rufe sa jikinsa yyi sanyi sosai, ya kusa minti biyar tsaye cikin ruwan yana kallonta snn ya juya ya koma gun motar ya bude yana kallon El-Ameen cikin sanyin murya yace "I've seen her" El-Ameen yace "Gud for you, sai ka bude baya ka dauki igiya ka daureta ka dauko ta ai" shiru Junaid yyi yana tsaye cikin ruwan yana kallonsa, can yace "Ka xo ka taimaka min toh" El-Ameen yace "What! cikin ruwan nn xan taimaka maka, Noo" Junaid bai kuma cewa komai ba ya bude bayan motar ya dauki igiyan da ke nan ya rufe ya koma inda mahaukaciyar take, k'asa karasawa yyi don gabansa sae faduwa yake, da kyar yyi shahada ya isa gabanta, kallonsa take tana kara takurewa waje daya, sae a snn ya lura da rawan sanyin da take, a hnkli yace "Kiyi hkuri baiwar Allah, am only trying to help" kamar ta ji me yace ta yunkura ta mike xata bar wajen da gudu, fixgota yyi ya rike ta gam, ta shiga kokuwa da shi tana ihu, El-Ameen na daga mota yana lekansu, ban da dariya bbu abinda yake har da kyakyatawa, ba karamin wahala ta ba Junaid ba don da kyar ya kai ta k'asa ya daure hannunta shima din ba wae dauri sosae ba don taki tsayawa ga wani karfi dake gareta, bude mota El-Ameen yyi ya fito cikin ruwan ya karasa inda suke da sauri, karban sauran igiyar yyi junaid na rike da ita ya daure ta gam, ihu ta dinga masu tana shure shure, El-Ameen ya mike yace "Ae sae ka dauketa Mr Do good" bbu musu Junaid ya dauketa, ko kadan bata da nauyi ya nufi motar da ita El-Ameen na biye da shi a baya yana 'yar dariya, ya bude baya ya saka ta ciki ya rufe, yatsine yatsine El-Ameen ya shiga yi ya nufi driver seat, muryoyi suka ji daga bayansu duk suka juya, wasu matasa suka gani tsaye da gora da adda a hannayensu, da ka gansu ka ga masu gadi, cikin tsawa suka ce "Maxa ku fito da ita ynxun nn" kallon Junaid El-Ameen yyi, El-ameen ma haka, ae kan kace me sae ga Junaid cikin mota ya rufe, El-Ameen na ganin hka shi ma ya shige motar ya tada da sauri, samarin suka taho da gudu, cikin hanxari El-Ameen ya ja motar suka bar wajen, bin motar samarin suka yi da guda suna buga ma motar gora da karfi, El-Ameen ya dinga cewa "ya Salam! ya salam! ya salam!" har suka bar anguwar abinda yake maimaitawa kenan, juyawa yyi yana kallon Junaid dake ta kallon mahaukaciyar dake fixge fixge tana son freeing kanta, a fusace ? yace "Kai ka ji irin ynda suka tarwatsa min bayan mota kuwa Junaid" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Xan gyara maka motar ka idan Allah ya yarda"  kwafa El-Ameen yyi yace "Better, kuma ka dinga lura da ita kar ta cafko ni mu shiga uku, ynxu ina muka nufa?" Junaid ya gaya masa ya kama hanyar anguwar, cikin minti goma suka iso, har lkcn ruwa ake, parking El-Ameen yyi yana kallon Junaid ya bude motar ya fito, fitowa yyi shi ma suka shiga gidan a tare, gidan babba ne ba laifi, junaid har yasa anyi furnishing gidan kar ya tsaya empty, El-Ameen yyi tsaki yace "Lallai! A wannan gidan xa a ajiye mahaukaciya? ba sae ta balla windunan nn mara karfi ba ta yi ficewarta, bugu daya idan tayi ma kofar nn ficewa xae yi wllh" Junaid ya shafa kansa a hankali yace "Toh shi suka samo min ya xa ayi" El-Ameen yace "Oho, amma idan ta gudu wallahil Azim ba da ni xaka je nemota ba" da damuwa Junaid yace "Toh hw are we going to do it ynxu ga shi mun dauko ta" El-Ameen yace "Oho it's left to yhu" xama Junaid yyi ya rike kansa, can yace "Ohk, let bring her in I will stay nd guard her till 2morrow kafin nn sae a samo mata wani gidan." El-Ameen ya shiga hararansa can ya ja tsaki yana kallon agogo yaga har goma ya wuce, yace "Kaga mu je can gida na, don ni na gaji sanyi nake ji kar in yi ma kai na illa haka kawai" daga hka ya fice daga palon, junaid ya bi bayansa ya fita ya kulle gidan. Har suka isa gidan El-Ameen bbu wanda yace komai sae Junaid dake juyawa lkci lkci yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen ya dauko makulin gidan dake motarsa ya fita ya bude gate don bbu kowa gidan, dawowa yyi cikin motar ya shiga compound din da motar, yana gama parking ya juya yana kallon Junaid yace 'Ohhw ni! yanxu mahaukaciya ce mace ta farko da xata fara shigar min gida bayan mahaifiyata maimakon matata" Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen yyi tsaki yana girgixa kai ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, Junaid ya fito ya bi bayansa, a balcony ya tsaya ya canxa change over din gidan don akwae wuta, ya juya yana kallon Junaid yace "Toh ni xan fito maka da mahaukaciyar?" Junaid ya girgixa kai ya juya ya koma gun motar, bae sha wahalan daukota ba don sosae El-Ameen ya daureta kuma duk tayi laushi, ihu take tana shure shure har suka shigo falon ya direta k'asa yana kallonta, El-Ameen ya rike haba yana kallonta yace "Ikon Allah, muna xaman xaman mu Junaid ya ja mana!" Juyawa Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen yyi tsaki ya nufi stairs, Junaid ya lumshe ido ya bude ya bi bayansa, daki ya samesa ya bude drawern kayansa da alamar kaya xae canxa, Junaid yace "It's late ynxu, muyi freeing dinta sae mu wuce koh" El-Ameen yace "wait tukun! Wae kai xaga dinga tsayawa da ita a gidan?" Junaid ya d'an yi shiru yana kallonsa, sae kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "No, xan sa a samo min yar dattijuwa dat will be staying, nd I will hire a gate man" El-Ameen ya kyabe baki ya cire jikakken shirt din jikinsa da wando ya fiddo wasu kayansa ya sa, sae a snn ya juya ya kalli Junaid da ke xaune gefen gadon dakin yana kallonsa yace "Kai baxa ka canxa kaya ba?" Mikewa Junaid yyi ba tare da ya kallesa ba ya fice daga dakin, dariya El-Ameen yyi sanin haushin sa kawae Junaid ke ji.
 
*Sai dai da aka rushe katangar Chinan dai, ko wani katanga xan kuma cewa Allah yayi min da su*??‍♀ 
    ?
*Haske Writers Association*?
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
 
 
 
      _By Khaleesat Haiydar_?
 
 
5.....
 
Falo El-Ameen ya sakko ya samu Junaid tsaye bayan kujera yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen yace "Toh ae sae ka dauketa ka kaita spare room ka ajiye ta ka kunce rope din" karasawa falon Junaid yyi, yyi yanda El-Ameen yace masa, yana kunce igiyar a daki ya fice da sauri ya ja kofar, kulle kofar palon El-Ameen yyi bayan sun fito, har lkcn ruwan da ake bae tsaya ba, El-Ameen ya d'an yi tsaki ya sa kai ya shiga ruwan ya nufi gate, bin sa Junaid yyi a baya ba tare da ya damu da hakan ba, sae a snn ya dinga jin sanyi na shigar sa ba kadan ba, El-Ameen ya kulle gate din daga waje bayan sun fito suka shiga mota, suna hawa kan titi El-Ameen yyi murmushi ganin yanda Junaid yake rawan dari, yyi kwafa yace "Ai baka fara rawan sanyi ba tukun malam, sai randa 'Yan gidan ku suka samu labarin mahaukaciyar nan I assure you oven ma yyi kadan yasa ka daina rawan sanyi" Sharesa junaid yyi, El-ameen yyi dariya yana kallonsa yace "Mu je can gidanmu, idan ya so da asuba sae ka koma gida, don kana komawa gida ynxu Mumy ta kama ka har duka na tabbata xata iya maka, ni kam na girma bbu abinda Ummina xata ce min" yana maganar ne yana kyalkyala dariya, shi dae Junaid bae tanka sa ba don sanyin da yake ji ma kadae ya ishe shi, kuma yasan gskya ya fadi yana komawa gida ynxu Mumy xata daga hnkli baxa kuma ta barsa ba sae ya fadi daga inda yake cikin ruwan nn. El-Ameen na gama parkin a parking lot din gidansu ya juya yana kallon Junaid yace "Let move in frnd" bude motar Junaid yyi ya fito ya nufi cikin gidan da sauri don ba karamin sanyi yake ji ba, bbu kowa palon ya nufi dakin El-Ameen, bathroom ya shiga ya hada ruwa me dumi sosae yyi wanka, ko da ya fito El-Ameen na xaune yana shan tea, ya fiddo rigan sanyi babba a closet bayan ya goge jikinsa ya sa, wayarsa ya dauka yana dubawa ko bae jike ba snn ya ajiye gaban mirror ya dawo yyi kwanciyarsa ya ja bargo ba tare da ya kalli El-Ameen ba, El-Ameen yace "Baxa ka sha tea'n ba?" Share sa Junaid yyi, El-Ameen yyi murmushi sanin baxae kulasa ba yace "Toh fa gwara ka tashi ka sha magani kar ka k'asa tashi gobe, ana kuma tambayata ba'asi xan tona wllh" Dariya El-Ameen ya dinga yi jin Junaid bae tanka sa ba still, ya mike ya dauko paracetamol ya dawo da Goran ruwa ya xauna gefensa yace "Look frnd, tashi ka sha drug kafin ka kwanta kar ka tashi da mura gobe, yhu knw I may be annoying a times" yana murmushi ya kare maganar, mikewa Junaid yyi ya karbi maganin da ruwa ya kora ya koma ya kwanta don shi kansa yasan without dat baxae tashi lfya ba gobe.  Washegari da asuba kafin ayi sllh Junaid yace xae tafi bayan ya daura alwala yyi Raka'atainil fajr, bae yarda ya dau motar El-Ameen ba don yasan hkn na iya tona masa asiri, ko mum din El-Ameen bata san yana gidan ba, El-Ameen ya rakasa bakin titi ya tsayar masa da a dai daita don ca yyi bae iya ba. Ana kokarin tada sllh ya iso anguwarsu na Government reserve area, masallaci kawae ya shiga, ana idarwa ya dde xaune yana Azkar har ya ga fitan Abbansa snn ya mike ya bi bayansa, part dinsa ya nufa ya gaishesa ya amsa masa snn yace "Kana mura ne Ahmad?" Junaid ya girgixa kai yace "Ya ma yi sauki Abba, ina shan magani" Abba yace "Gud! Babu damuwa ko?" Junaid ya shafa kai yace "Ehh Abba!" Abba yace "To Allah maka albarka" Junaid yace "Ameen Abba," Abba yace "Gobe xan fita xuwa Germany, tafiyar ya xo min da gaggawa ne, as usual am handing the family over to yhu son" Junaid yace "Toh Allah kai mu Abba, journey mercy dad, in'sha Allah" Abba ya shafa kansa yace "Ameen dear son" mikewa Junaid yyi yace "It's almost daybreak Abba, bari in je in shirya xuwa aiki" Abba yace "Its ohk, stay blessed" fita yyi ya nufi bangarensa, cikin mintunan da basu fice ashirin ba ya shirya cikin uniform dinsa na dark navy blue trouser da light blue shirt, kadigan yasa navy blue bayan ya feshe jikinsa da turare ya rike hularsa a hannu, waow yyi kyau har ya gaji lips din nan nasa kamar ya shafa jan baki, ya bude manyan idanuwansa sanin bae shafa komae ba ya daga kafada ya fita xuwa side din mum dinsa, fatima dake shara a balcony ta gaida shi, ya amsa ya shiga parlon, Mumy na jera masa breakfast dinsa a dinning ya sameta, ya nufi dinning din ya mata side hug ya kwanta jikinta a hankali yace "Sabahul khair Ummu na" Mumy tayi murmushi tace "How are yhu, baka rufe windows bne jiya naji kmr mura na neman kama ka" shagwabe mata yyi yace "Na rufe mana Mumy," ta hararesa tace "Toh ka bar Ac a kunne ko" ya girgixa kai yace "Not at all mum, kinsan ynxu lkcn ruwa ne kuma tun da na dawo ciki nake fita aiki shi yasa kmr muran ke son kama ni" tace "Toh I will get yhu an umbrella don ban ga amfanin Raincoat din da kake sa wa ba" yace "A'a ni nafi son raincoat dina, umbrella sae kace mace mumy" tace "Toh idan na baka kar kayi amfani da shi" langwabar da kai yyi ya xauna yana kallon ynda take hada masa tea, plate din potatoe'n da ta xuba masa ya jawo ya shiga ci yace "Aisha ta koma ne Mumy?" Mumy tace "Tun jiya" daga haka ta bar dining din ta shiga daki, a hnkli junaid ya ajiye fork din hannunsa tunawa da mahaukaciyar da suka dauko jiya da yyi, har Mumy ta fito bai kuma cin komai ba, ta kalli agogo ta kallesa tace "Kana kallon agogo dai koh" yyi yake ya ci gaba da cin potatoe'n, tutturawa kawae ya dinga yi don neman appetite yyi ya rasa, ya mike yana goge bakinsa da tissue yace "Allah amfana momy, thnks a lot" tace "Welcm, but make sure ka shiga ka gaida mutan gidan yau" d'an hade rae yyi amma da yake baya mata musu cewa yyi "Toh mumy" ta rakasa har balcony, yyi side din stepmums din nasa, bangaren Hajiya Fatee ya fara shiga tana xaune da Muhibba a palo da Rabi'a dake gugan Hijab, ya xauna kan kujera hannunsa rike da hularsa me kaman face cap me dauke da symbol din captainship a jiki, yyi k'asa da kai yace "Ina kwana Hajiya" a dakile tace "Lfya lau d'an gwal" hade rae yyi yana jujjuya hular hannunsa, Rabi'a tace "ina kwana ya Ahmad?" Yace "Lfya lau ya sch?" Tace "Alhmdllh" Muhibbah dake ta kallonsa ko kiftawa bata yi ganin ko kallon inda take bae yi ba cikin wani siririn murya tace "Ina kwana ya A.jay" ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae kuma ya mike ya nufi kofa yace "Na tafi aiki Hajiya," bata tanka sa ba har ya fita, Muhibba ta kalli Hajiya tace "Hajiya kinga ko amsa gaisuwata bai son yi ma" Hajiya Fatee tayi wani murmushi mai wuyar fassara ba tare da tace komae ba, Rabi'a tayi 'yar dariya tana guganta tace "Aiki" harara uwar ta wurga mata, ko sanin tana yi bata yi ba, part din Hajiya Bilki Junaid ya nufa, bbu kowa palon ya nemi gu ya xauna yana kallon agogon wrist dinsa, daga kitchen khadija ta fito ta d'an wara ido tace "Lah ya Ahmad ashe kana nan, Gud morning" yayi murmushi yace "Morning lil sis, ya sch?" Ta karaso kusa da shi ta shagwabe murya tace "Lfya lau, plss yaya ka d'an min transfer din 5k frnd dita na birthday gobe xan siya mata perfume" yace "Kije ki samu Abba mana ae bai tafi ba" ta d'an bata rai tace "Shekaranjiya fa ya canxa min phone" yace "Ohk ltr" Hajiya bilki ce ta shigo palon, kallo daya tayi masa ta dauke kai, tana kallon Khadija tace "Ke don uwar ki me ya hada ki da Suhaima kike mata fitsara?" Khadija ta hade rai ta juya ta koma kitchen, junaid yyi k'asa da kai yace "ina kwana Umma" ba tare da ta kallesa ba tace "lfya lau" Suhaimah ce ta shigo palon da alamar muryarsa taji, tace "Ina kwana ya Ahmad" mikewa yyi yace "Lfya lau" daga hka yace "Na tafi aiki Umma" bae jira cewarta ba ya fice, ta bi sa da harara, Suhaimah ta samu waje ta xauna ta xabga tagumi tana kallon Umman. Junaid na xuwa gun aiki ya dauki permission Karfe sha daya ya fito, driving yyi xuwa clinic din dad din El-Ameen, Yana rike da hularsa ya haura sama xuwa office din El-Ameen, Nurses din suka bi sa da kallo ko kiftawa bbu, yana attending to patient ya same sa, ba tare da ya kallesu ba ya shige bedroom, xama yyi yana addu'ar Allah yasa baxae dau lkci da patient din nasa ba, ko minti biyar ba'ayi ba sae ga El-Ameen ya shigo yana kallonsa yace "Ya? Duty din naka ya kuma shifting xuwa yamma ne?" Junaid yace "No of course, yarinyar da muka bari kulle a gida fa?" El-Ameen ya hade rai ya galla masa harara yace "Kaga xaka fara daga ma mutum hankali da sassafen nn koh, Toh me xa ayi mata ynxun? Ba sae xuwa yamma in mun gama aiki ba" Junaid ya girgixa kai yace "Yanxu fisabilillah da xaka fito baka yi breakfast ba Dr? Ita ba mutum bace da xa a bar ta ba ruwa ba abinci har xuwa yamma?" El-Ameen yyi masa wani kallo yace "Toh wai wa ya hana ka xuwa kai mata abincin ynxu, iyaka ka xo kace in baka makullin gida in baka, pls let me be Captain, am getting sick of you," Junaid ya lumshe ido ya rike kansa don walakancin El-Ameen ya fara isan sa, mikewa yyi ba tare da ya kallesa ba yace "Ohk! Bani keyn" El-Ameen ya d'an shafa kai yace "Alryt am sorry, haka ne kuma fa ya kamata a kai mata abinci, tun da ita ma mutum ce kamar Junaid" ficewa Junaid yyi ya bar masa dakin, El-Ameen yyi dariya ya bi bayansa, makullin gidan dake table dinsa ya dauka ganin Junaid ya bar office din shi ma ya fita, kusan a tare suka iso gun motar junaid, El-Ameen ya bude gaba ya shiga, junaid ma ya shiga ba tare da ya kallesa ba yace "Kaga hand me dat key ka fice min a mota" El-Ameen ya gyara xama yace "Toh fitar da ni mu ga" Junaid ya fi minti biyar bae tada motar ba, El-Ameen kuma yaki fita, sanin ba fitan zae yi ba kawae ya tada motar ya ja suka bar asibitin, wani eatry ya fara biyawa ya siyo abinci da ruwa sae hollandia drink, El-Ameen ya rike kai ya dinga dariya da ya ga hollandian, shi dae Junaid bae tanka sa ba, sae da suka dau hanyar gidan yace "kaga malam da ka rufa ma kanka asiri ka bude hollandian nn mu shanye kawae, dama am thirsty, banda haka a ina ta san wani hollandia in ba neman magana irin naka ba" driving kawae Junaid yake bae tanka sa ba, El-Ameen yyi dariyarsa me isarsa yana mamakin Junaid, a waje suka yi Parkin motar, El-Ameen ya bude gidan suka shiga, kallon Junaid yyi da ya tsaya yace "A'a Toh ka shiga gaba mana goga" murmushi Junaid yyi bae ce komae ba yana shafa kai don shi har ga Allah tsoro yake, El-Ameen ya dinga kyalkyala dariya har suka isa kofa Junaid na biye da shi a baya, El-Ameen na bude kofar ya koma baya da saurinsa ya fiffito da ido, Junaid na ganin hka kan kace me sae gashi a tsakiyar compound cikin 'yan sakwanni, El-Ameen ya rike kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya nanata hakan ya kusa sau goma,  Junaid na daga tsakiyar compound sae tambayar me ya faru yake, cikin tsawa yace "Junaiddd xo ka ga abinda ka jawo min"
 
  ?
*Haske Writers Association*?
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
 
El-Ameen ya juya yana kallon Junaid ganin ya ki karasowa da karfi  yace "baxa ka xo ka ga abinda mahaukaciyar da ka sa na kawo gidana tayi ba, ya Salam!" Junaid na jin hka ya karaso da sauri yana leka parlon, kwalalo ido yyi yana kare ma palon kallo, palon komawa yyi kamar wanda aka yi karamin yaki, don duk ta tarwatse plasman palon da frames gaba daya, lafiyayyen centre table din ma bata raga masa ba, ko ta ina kwalabe ne a falo, duk ta tuttuge labulaye da karafunansu, kujeru kam upside down ta juyasu dukka, Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba har da rike ciki, El-Ameen ya bude baki yana kallonsa idon nan nasa ya kada, fixgosa yyi yana huci yace "Yhu see wat you've caused koh Ahmad, gud! this mad woman is adding not a minute more in my house" yana fadin hka ya turasa ya shiga palon, da sauri junaid ya hadiye dariyarsa ya rikosa yace "Haba frnd, Chill plss ka mance mahaukaciya ce ita kamar yanda kake kiranta, I promise wllh duk xan siya maka abubuwan da tayi damage, that's a promise frnd!" marairaice masa Junaid yyi yace "Plss!" El-Ameen yyi kwafa yace "Yanxu naji bayani, kuma ga motata ma can a gida bbu kyan gani, kasan yanda xa kayi da shi, I need it the way it
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  ⚡Heedayah⚡By Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 14,580 07-08-2021, 05:08 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 29,503 09-10-2018, 08:20 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 11,459 08-18-2018, 01:15 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 24,858 08-10-2018, 01:18 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 20,044 08-10-2018, 12:48 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 24,871 08-05-2018, 11:27 AM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat haiydar Gimbiya 0 53,300 08-03-2018, 05:26 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)