The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud
#1
????????
*KARAN BANA.........*
????????


*ZAHRA SURBAJO*


*Sharhi akan littafin ne ke karamin kwarin guiwa,*


*Dedicated to Billy Shantaly*




*17*



Tunda suka tafi Auwal ke faman huci,ya kosa yaji labarin abinda ya faru bayan tafiyarshi da har ya maida kanwarsa da kanwar matarsa karuwai.

Ammar cike da jin dadi yacewa Auwal.

 "mutumina nifa naga iri a gidanku,dan Allah ka gyaromin wasan"ya fadi yana dariya.

Da sauri Auwal ya juyo yana kallonshi gami da furta.

 "shashancin banza,kai yanzu har kaga abin so a tattare dasu,toni ba karamin mutum bane wlh bazan yada girma na ba," 

Dariya Ammar yayii sannan yace. 

"Tab ayko ni naga abun so, ba kadan ba,kai da baka gani ba Allah ya makantar dakai,kuma wlh sena gabatar da kaina agurinta"

Cakumoshi Auwal yayi yace cikin fushi.

 "kada ka kuskura kayi gangancin furta kalmar so gareta,dan faruwar hakan raini ze janyo mana kaji na fada maka"

Kwacewa yayi daga rikon da yay masa yace.

 "look Auwal nifa ba ladifi bane,namiji ne ni lafiyayye kaga ko dole seda mace acikin lamarina,naga yusura tayimin ayadda nakeson mace ta kasance,kuma nima inada iko akan yusura matukar kai yayantane,dan haka wlh ba ja da baya,dan dama so daya take zuwa arayuwa"

Tsaki Auwal yayi yace.

 "ay kai wlh adduar mummy ce ke natsar dakai amman da ba karamin dan taure zaayi ba"

Dariya ammar yake harda hawaye,cikin dariyar yace.

 "yau naga masifa,daga na bukaci aure se kuma ace min dantaure,?eh de naji akuyancin da nai shekaru talatin da biyar ban yiba shine nakeso nayi da matata,dan bakin ciki kawai dan kai kasan hanya shine ni kakeso  kar na sani"

Takaici ne ya hana auwal mgn,har suka karaso gidan autyn.

Aunty zainab tayi murna da ganinsu,ta rasa inda zata sasu.

Cikin lokaci kankani  aka cika musu gabansu da kayan abinci kala kala.

Da yake sun kwaso yunwa,zama sukai suna cin abinci.

Bayan sun gama ne,suka zauna hira da auntyn tasu.

Sosai suka ji dadin yadda ta tarbesu.

Yarinyarta ce ta shigo cikin shigar daukar hankali,da dan gudunta taje ta rungume ammar tai masa kiss a kumatu,gamida masa barka da dawowa.

Sannan ta isa gun auwal shima ta rungumeshi tai masa kiss din a kumatu,darab ta zauna kan cinyarshi,tasa hannunta ta sakalo wuyanshi,tana murmushi tace.

 "yaya Auwal kayi kyau  sosai moscow ta karbeka"

Auwal gaba daya ya daburce,zaman da zukekiyar budurwar tayi akan cinyarsa.


Ba abinda yafi daurewa Auwal kai kamar ganin yadda aunty tayi kamar bataga abinda yar ta tayi ba.

Ammar dake gefe dariya ce keson kwace masa yana maida ta,dan yasan anyiwa auwal ba daidai.

Cikin murmushi me kama da yake,Auwal yace.

 "thanks you my sis"

Yarinyar me suna,zaitun,murmushi tayi gamida fari da idanu.

Ganin bata da niyyar dagashi ne yasa yace mata. 

"sis me mummy ke baki ne kike da nauyi haka,nide dagani kar ki karya ni"

Murmushi tayi,gamida rufe ido ta mike ta zauna kusa dashi.

Gaba daya zaman gurin ya ishi Auwal dan haka mikewa yayi,yacewa Aunty zasu su dawo.

Suna fita kofar gidan Ammar yafara dariyar daya tara,cikin dariyar yace.

 "kai mutumina yau fa zaitun ta mori cinya"yasake tuntsurewa da dariya.

Duka Auwal yakai masa gamida fadin.

 "Ay kai dama dan iskane wlh,kuma bazan sake dawowa ba," 

Sosai Ammar kecin dariyar Auwal,a haka suka shiga mota zuwa gidan su yusura.

Tasleem ko tunda suka tafi da danmaliki hotel suka nufa.

Sosai danmaliki ya kwadaitu da tasleem,dan haka nuna mata manufarshi yayi a fili.

Tasleem tsoro ne ya kamata,amman ta daure,cikin dakewar murya tace 

"baby,se rawar kafa kake,kadan jira zuwa anjima mana"

 "baby kedince hot cake,bazan iya jurewa ba zuwa anjiman pls"

Murmushi tayi me kamar kuka tace,

 "To amman ay ni ban shirya ba"

Dariya yayi sosai sannan yace

 "ay shi dama baa shiri dan haka zan saki ki shirya da kyau"

Ganinfa da gaske yake ne yasa tasleem,shiga tashin hankali.

Kokarin hada bakinsu yake guri guda,ita kuma taki yarda,kwace kanta tayi ta fara ja da baya,yana binta.

Nanfa kokawa ta kaure tsakaninsu,idon dan maliki ya gama rufewa burinshi ya biya bukatarshi akan tasleem.

Wayyo tasleem,kuka take iya karfinta,zuwa lokacin ya cire rigar jikinta daga ita se dogon wando da bra.

Ganin ba sarki se Allah ne yasa tasleem bude kofar dakin ta fice da gudu.

Da yake tana da gashi me tsayi kuma ya sakko kan fuskaeta yasa bame ganin fuskarta.

Hannunta kare da boobs dinta ta fice daga hotel din a 360.

Tana isa bakin titi,Auwal da Ammar na isowa dede gurin cikin motar Gidan auntyn su Ammar zasu gidan su yusura.

Tofa ga Auwal ga tasleem ba riga abakin hotel.

Muje zuwa.


*Surbajo for life*

????????
*KARAN BANA........*
????????



*ZAHRA SURBAJO*



*???????ko ina ka leka karan bana gaskiya yau naji dadin comments ba kadan ba kuma jin dadinne ma yasa na baku wannan page din yau,Allah yasa ku dore?*

*Dedicated to Billy shantaly*



*18*



Dan malikine ya karaso bakin titin da gudu yana karasowa su Auwal suma na karasowa.

Fara jan tasleem yayi da yake unguwar GRA ce yasa ba mutane se jefi jefi.

Ihun take tana kai masa duka,shi kuma bawai yana janta dan yaje yayi iskanci da ita bane kawai beso wani ya kallarmasa ita a hakane shine yakeso ta koma tasa kayanta.

Ita kuma da yake ta firgita dashi ne yasa ta dunga yimasa kuka tana dukanshi.

Su Auwal har sin wuce,suka hangi ana cin dambe tsakanin tasleem da danmaliki.

Da Auwal be gane ko waye ba seda dan maliki ya waigo Auwal ya gane dogon wandon da yaga tasleem dazu dashi a airport.

Karar burkin daya takane,yasa tasleem da dan maliki waigawa gurin.

Bude motar yayi yafice zuciyarshi na kuna ya isa gabansu.

Danmaliki,tass ya gane auwal jikinshi ne ya fara bari kamar mazari yanaso ya ambaci sunan auwal amma ya kasa.

Shiko Auwal ko kulashi beyi ba,hannun da ya rike tasleem yasa hannu ya cire.

Janta yayi da duk karfinshi,yayinda ita kuma se kuka take,tanason kare boobs dinta ba hali tunda ya rike hannun.

Mota ya jefata,yana shiga be jira ammar ya shigo ba yaja motar da mahaukacin gudu.

Se alokacin natsuwa tazowa dan maliki ya tuna Auwal yatafi masa da tasleem.

Da gudu ya bi bayan motar yana.

 "noooooo ka tsaya ka saukemin ita,dani zakayi ba ita ba"

Ina Auwal bemasan yanayi ba.

Ammar tsaye ya rasa guein zuwa dan haka waya ya ciro yakira auntynsa yay mata kwatancen inda yake ta tura masa direba.

Danmaliki da gudu ya koma cikin hotel din ya dauko motarshi yabi bayan Auwal.

Sede Auwal ya bace masa  be ganshi ba.

Kuka yake harda hawaye sabida bakin cikin ganin masa tasleem da auwal yayi ba riga.

Zuciyarshi na zafi kamar zata fashe,ya rasa yadda zeyi.

Auwal ko da tasleem be zame ko ina da ita ba se tsohon gidansu na rigasa.

Akwai mukulli ajikin kofar gidan amman duka daya yay masa ya bude ya wurgata ciki.

Yana shiga ya maida kofar ya rufe.

Tasleem mamakin dawowar yaya auwal din take,dan ta ganeshi.

Auwal belt din jikinshi ya zare ya fara tunkarota yana huci.

Baya ta fara ja tana fadin.

 "yaya me nayi naga kamar zaka dakeni"

Shimfida mata daya yayi a cinya,wayyo tasleem,ay tuni ta saki hannayen data kare boobs dinta ta fara sosa gurin.


Ci gaba yayi da dukanta yadda yaga dama,ihu take iya karfinta amman be kyaleta ba,seda jini yafara fita ajikinta sannan ya nemi wani tsohon turmi ya zauna akai,

Tasleem ko na kwance tana kukan bakinciki.

Wayarshi ya ciro yace mata. "bani number yusura"

Ba musu ta karanta mishi dan tana masifar jin tsoronshi yanzu.

Kira daya yusura ta dauka.

 "yanzu kizo tsohon gidanmu ki sameni,in kika bata lokacina zaki sha mamkin abinda zan miki"

Yana fadin haka ya kashe wayar.

Wayyo yusura cikinta ne ya karta seda ta zaga sannan tazo tasha babban hijabi?ta tafi kiran da ya Auwal ya mata.

Tayi gumi kashirban kamin ta isa sabida tsoron haduwa dashi.

Har ta iso kofar gidan bata dena ambaton Allah ba.

Tura kofar tayi ta shiga,gidan nanan yadda suka barshi sede kurar da yayi.

Ganin tasleem kwance jiki duk jinine yasa yusura fara kuka tun kan ta gama karasawa cikin gidan.

Ayko tana karasawa ya rufeta da duka itama seda yamata yadda yawa tasleem,sannan ya tirkesu su shaida masa abinda ya faru bayan baya nan.

Kuma yabasu tabbacin in suka masa karya seya musu abinda yafi haka.

Cike da dumbin danasani suke shaida mishi duk abinda ya faru.

Dan tsananin takaici seda yayi kuka.

Seda yadan natsu tukuna yace.

 "gidan da ya baku yau zaku baroshi ku dawo nan,banzaye marasa hankali,ubanme kudinshi zasu muku,da har zaku zubarwa kanku mutunci sabida su," 

Haka yay ta balbala balai yadda yaga dama,sannan yace su sundawo kenan,zeje ya dauko umma da mubashshir,kan ya dawo su tabbatar sun gyara gidan.

Yusura ce me kwarin amsawa amman tasleem ba baka se kunne dan ba karamin dakuwa tayi ba a hannunshi.

Ficewa yayi ya kullesu acikin gidan,ya nufi wanxan gidan domin dauko umma da mubashshir.

Muje zuwa.


surbajo for life.

????????
*KARAN BANA..........*
????????



*ZAHRA SURBAJO*



*Wlh inajin dadin comments dinku sosai,Allah yabar mu tare ina yinku akoina kuke Allah yabar zumunchi*


*Dedicated to billy shantally*


*19*



Da kyar yusura tasamu ta daga tasleem suka shiga gyaran gidan wanda yusura ce karfin yin aykin dan tasleem har jiri ke dibarta.

Auwal na fita can gidan yanufa,koda ya isa be jira komaiba tafara jidar kayan sawar su yana kaiwa mota seda ya gama sannan yazo yacewa umma wacce tun dazu bakinta ke bude.

 "taho umma kubar gidannan dan be dace daku ba"

Ba musu umma taja mayafi ta kama hannun mubashshir,suka nufi kofar gidan.

Suna fita sukaci karo da dan maliki yazo gurin yusura yaji ko tayi waya da tasleem.

Kallon kallo suka tsaya yiwa juna,zuwa can de danmaliki,ya fara murmushi ya matsa kusa da auwal yace.

 "naji dadin ganinka Auwal Mun nemeka har mun gaji bamu ganka ba,ashe da rabon zamu gana "

Kallon arziki Auwal be masa ba ya budewa su umma kofa suka shiga ya shiga ya tada motar,sannan ya leko yacewa danmaliki.

 "matsiyaci ga gidanka nan sun bar maka ka ƙara akan sauran,watakila ka mallaki dukiyar da karuna be mallaka ba"

Yana kaiwa nan yaja motar tabar dan maliki aguerin.

Ay da gudu danmaliki ya fada mota,yabi bayanshi dan yanaso ya fada masa inda yakai masa bakuwarsa?. Auwal na kallonshi ta mirror yana binsa amman ko ajikinshi har suka karaso gidan.

Su Auwal shiga ciki sukayi,shima danmaliki kanshi tsaye ya shiga yana fadin.

 "kai Auwal duk yadda kakeji da rashin kunya ni babankane,wlh ka taka a sannu,ni ba saanka bane,dazu ka tafi min da bakuwa ina ka kaimin ita,?" "na kaita gidansu"cewar Auwal yana huci. "kutumar uba,uban waye yace ka kaita gidan?kaine keda iko da ita koni da tazo gurina?" 

Dariya Auwal yayi sannan ya kwalawa tasleem kira da yusura.

Jiki na bari suka fito rungume da juna,dan sin dauka wani dukan zasu sha.

Suna fitowa Auwal yace.

 "Na fika iko da tasleem shiyasa na daukota zuwa gida,tasleem kanwa ce ga maryam matata uwa daya uba daya,da yake kai baho ne yasa baka gano hakan ba,na dauka bayan tafiyata hisham kwakwalwarka ta fara ayki ashe dakikancinka ba iya karatu ya tsaya ba,har akan muaamala da mutane kai dakikine,yusura da tasleem sun maida kai sekace rakumi sunyi wasa da rayuwarka yarda ya dace,sun tabbatar maka da cewa kai jaki ne," 

Tunda Auwal ya fara magana danmaliki ke gumi,jikinshi na rawa.


A fusace yaje ya shake Auwal yana mgn cikin cije baki. 

"in kana mgn ka dunga tuna cewa ni yayanka ne,kuma ko ma menene sukamin ni agurina ci gaba ne tunda hakan ya zama sanadin haduwata da tasleem,inason tasleem son da bana yiwa kowa kamarsa,ciki har da ni kaina,sanin wacece ita ya karamin jin sonta araina,dan haka kasan dawa kake mgn,danmaliki nake"

Auwal kwacewa yayi daga rukon da hisham yamasa sannan yace.

 "Allah ya tsinewa soyayya irin taka,inde irin hakane so to Allah ka tsinewa duk wani meyin so,kana son natane kamaida ita karuwar ka?"

 Azabure tasleem ta dago tana duban Auwal wasu hawaye masu zafi nabin idonta,yauce rana ta farko datayi dana sanin haduwa da danmaliki.

Shiko Auwal ko ajikinshi yaci gaba da cewa. 


"Duk namijin dake son mace domin Allah gidansu yake binta,bawai ya ajiyeta a hotel suna fasikanci ba,dan haka kadena cewa kai me sonta ne," Yana kaiwa nan ya wuce yabarshi tsaye agurin.

Yusura kama tasleem tayi suma suka tashi suka shige daki,dama ita umma tuni ta shige tana kukan takaicin halin da danmaliki ya jefa tasleem.

Danmaliki rasa yadda zeyi yayi,dan haka ficewa yayi agidan ya nufi gidanshi ranshi na kuna.

Auwal ko mota ya shiga,se alokacin yaji natsuwa aranshi,tunowa yayi da ammar,wani murmushi yayi,dan yasan zesha masifa.

Kiranshi yayi awaya,ayko kamar jira ammar ya dauka yace. 

"Wlh kaide akwai bakin mugu me raba masoya,sabida tsabar wulakanci ka tafi da mota kabarni a titi inda masu satar mutane sunzosun sasheni baka da asara,wlh sena maka rashin mutunci,kuma kazo kadaukeni gidan aunty muje in ga masoyiyata"

Dariya Auwal yake tunda Ammar ya fara mgn,

Seda yabarshi ya gama sannan yace.

 "da girmanka waye ze sace ka,?ay nace ma bazan sake zuwa wannan gidan ba sede ka fito waje inzo in daukeka"

Hakade Ammar yayta zazzaga masifa har Auwal din yaje ya sameshi,ya daukoshi bedena balai ba.

Har suka karaso gidan.

Lokacin ankira sallar ishai dan haka masallaci suka nufa,suka bi jam'i

Bayan sun idar ne suka shiga cikin gidan.

A tsakar gida suka sami umma da yusura da mubashshir,suna hira,

yayinda tasleem kecan daki sunan karuwa da Auwal ya kirata dashi ya hanata sukuni,ga jikinta dake zafi sabida dukan daya mata.


muje zuwa


surbajo for life.

????????
*KARAN BANA.........*
????????



*ZAHRA SURBAJO*



*dedicated to Billy shantaly*



*21*




Suna shirin kwanciya kiran mummy ya shigo wayar Auwal.

Duk abinda ke faruwa ya sanar mata,sosai ta tausayawa auwal din dan tasan yana son yan uwansa.

Bayan sun gama wayane suka kwanta,Ammar na mitar sauron dake cizonsa.

Washe gari,tasleem ta farka da sauki jikin nata,yusurace ta taimaka mata tai wanka tai sallah,amman ta kasa cin abinci.

Umma ma tazo ta rarrasheta taci abinci amman taki,ga boobs dinta dake mata ciwo sabida dukan da aka mata akai.

Koya ta motsa ji take har kanta.yusura ta rasa yadda zatayi da tasleem,

Suna nan tsaye su Auwal suka shigo cikin gidan.

Tasleem ce ta fara ganinsu,tunkan su karaso ta zabura ta tsuguna tana fadin. 

"ina kwana ya Auwal"?????

 Kadan ya rage yusura ta kwashe da dariya,ganin ya auwal dinne ya hanata yi.

Ko kulata beyi ba bare ya amsa,dukawa sukai suka gaida umma ta amsa cikin sakin fuska.

Yusura ma datayi gaisuwar be amsa ba,se ammar ne ya amsa yana murmushi.

Dubanshi yusura tayi har yanzu ba riga ajikinshi se singlet.

Abunka da fari duk ga tabon cizon sauro nan ya bayyana ajikinshi,sosai taji tausayinshi ya kamata.

Ficewa tayi ta nufi inda ta shanya rigar tashi,ta shiga dakin umma ta fesama rigar turare.

Bayan fitar yusura,ledar magungunan da ammar ya siyo jiya Auwalya dauko,ya ciro kayan dressing ciwo.

Dama tuni umma tabar dakin daga shi se tasleem dake tsugune kamar me neman gafara da ammar.

Yana gama fito da kayan,yakai dubansa gurin ammar yace. 

"likita na bakin ayki seka bani guri ko"

Dariya ammar yayi yace.

 "ay ko baka fadi ba zan baku"

Juyawa yayi ya fice daga dakin yana dariya.

Fitarshi tayi daidai da fitowar yusura daga dakin umma,sede be ganta ba ya nufi zaure.

Binshi tayi da sauri,tana zuwa kusa dashi kan ya juyo ta yafa mishi rigar akan kafadarshi ta yadda xira hannu kawai zeyi.

Da sauri ya juyo ita kuma ta juya zata bar gurin.

Hannunta daya riko ne yasa ta tsaya cak.

Janta yayi ta dawo kusa dashi.

Sunkuyar da kai tayi,hannu yasa ya dago habarta yace. 

"ni da na cire ay sa miki nayi,ke me yasa kika ajiye a kafadana kuma kika juya ba tare da kinmin mgn ba?" 

Duk ta gama daburcewa dan haka baki na rawa take fadin.

 "Aa dama naga sauro sun cijeka ne shine yasa na kawo maka"

Murmushi yayi sannan yace.

 "au har kallemin jiki kikeyi kenan?"

 A tsorace ta dago ido tana kallonshi baki na rawa tace. 

"aa ba kallonka nake ba"

 "in baki kalleni ba taya kika ga sauro ya cijeni?" 

Shuru tayi ba amsa,kunya duk ta gama kamata,dama tasani bata kawo mishi rigar ba.

 "au ba zakiyi mgn ba?"

 "don Allah tsautsayine kayi hkr bazan kuma ba"tayi mgnr kamar zatai kuka.

Murmushi yayi yace.

 "na miki afuwa yanzu,amman ba na hakura bane,next time kika kuma nima kawai ramawa zanyi"

Da sauri ta kwace hannunta ta ruga cikin gida tana tafiya tana waigenshi.

Dariya yayi ya karasa ficewa daga zauren.

Acan kuryar daki kuwa,tasleem ji take kamar ta saki fitsari sabida tsoron yaya auwal.

Shiko ko ajikinshi hada magungunanshi yake tayi,seda ya gama,yasa safa a hannunshi sannan yakai dubansa gurinta.

Carab idanunsu suka hadu guri guda.agigice tasleem ta runtse ido.

Tabe baki yayi sannan yace.

 "oya taso ki matso nan ki cire wannan rigar ta jikinki"? Balai?


? Idon tasleem kamar goruba haka ta watsa masa su tana kallonshi.

Sake maimaitawa,yayi agigice tace.

 "ya Auwal iya rigar ce kawai fa ajikina" 

"to se me cewa nai kicire ki matso nan"

Cikin in ina tace.

 "ba ba ba ba bra aciki ya auwal"

 "ay ban tambayeki ba,kuma dama ko akwai zaki cire,ciwon dake kan boobs dinki zanyiwa dressing"ya fadi cikin hada gira.

 "What!!!dressing a kan boobs dina"tasleem tayi tambayar ba tare da tasan tayi ta ba. 

"yess and so fucking what"Auwal ya bata amsa

 "wlh ya Auwal,ni banaso kabarshi kawai"

 "dallacan kwaila dake ma ubanme zan gani ko zanji danna gani,taimakonki zanyi,kina batamin lokacin,zaki matso koko sekinji ajikinki" ?? karya kake@xianoxy

Kan ya rufe bakin ma ta karaso kusa dashi,rigarta a hannu.jiki na bari.

Wayyo tasleem wannan kayan kunya har ina,

Sata yayi ta kwanta sannan ya shiga wankewa,ga azaba ga kunya abun biyu ya hadar mata.

Shiko kamar gaske ka rantse da Allah tayar mota yake wankewa,ba milk factory ba.?a yadda ya nuna.

Haka ya gama yasa mata bandeji se kuka take mara sauti.

Yana gamawa yasa kai ya fice ba sannu bare Allah ya sauwake.

Muje zuwa


Surbajo for life.


*KARAN BANA*
????????


*ZAHRA SURBAJO*



*mmn baby?,mummy pheenat,daga surbajo novels,surbajo na gaisheku Allah ya barni tare daku cikin aminci,#Ana mugun tare*

*Salma b? sabida ansamin recharge card na 200 shine ake bina inyi godiya inyi godiya,to ga godiyar nan zanyi?,salma b me kan goruba,salma b buhun kenkeso,salma b me hancin roba,ta jb me warin gawasa????????????ay dama nace miki zaki ga godiyata?,amma fa duk da haka ina sonki salameme na?*


*Dedicated to Billy shantaly?*



*22*


Kai tsaye gurin ammar ya nufa ya daukeshi suka shiga gari domin neman boutique da zasu samu kayan sawa.

Basu dawoba se da rana tayi.

Wanka sukayi kowa ya sauya kaya.

Sannan suka shiga gida suka yiwa umma sallama akan zasu dawo wani satin.

Kudi dubu hamsin Auwal yaba umma sabida hidimar gida.


Umma se albarka take ta sa mishi.

Sosai Auwal yaja kunnen yusura gameda danmaliki.


Har sun kai zaure ammar ya dawo yacewa yusura.

"kanwata bani no dinki sabida gaisawa da umma in mun tafi"?

Ba musu yusura ta bashi,ya fice yana daga mata hannu.


Mota suka shiga zuwa airport dan duk yadda Ammar yaso suje gidan Aunty Auwal yaki yarda sabida zaituna.

Suna isa airport ajiyar motar suka bayar gamida kiran auntyn ammar ya shaida mata ta turo direba ya dauki motar su sun tafi.

Aunty seda tayi fada akan tafiyar tasu ba sallama.


Da laasar suka isa gida,mummy ta rasa inda zatasa kanta dan jin dadin ganinsu.

Nanfa suka shiga hirar kd.

"Auwal tunda ka rabosu da gidansa,wannan gidan da ka maidasu zasu kuntata,dan haka akwai tsohon gidanmu sanda muna kd,zansa auntyn ku ta nemi maaikata,aje agyara gidan asa duk abinda yadace dan ba komai aciki kuma ya jima a rufe,inyaso sati me zuwan da zaku koma se ku maidasu cikinsa,ammar yasan gidan"

Sabida tsananin farinciki Auwal rungume mummy yayi yana godiya,harda hawayenshi.

"wannan godiya tayi yawa dan gidan mummy,kode baka daukeni uwa bane"cewar mummy tana shafa kanshi.

"mummy na daukeki uwa,dan yanzu aduniya kece kawai uwata mummy,kuma ko lahira inaso Allah ya hadaki da mahaifiyata amatsayin iyaye agareni,mummy kinmin komai"yayi maganar yana share hawaye.

Itama hawayen ta share tace "Amin dangidan mummy"


Ranar wuni sukai tare da mummy se dare sukai mata sallama suka nufi dakin baccinsu.

Kowa nada dakinshi amman shakuwarsu tasa basa raba gurin bacci.

Suna shiga daki Ammar ya fada kan kujera yazaro wayarshi yana fadin.

"Allah yasa batai bacci ba"

Kallon rashin fahimta Auwal ke masa,amman bece komai ba.

Ammar number yusura ya kira,wacce alokacin zaune take ita da tasleem suna hira.inda tasleem ke fadin.

"yusura ya Auwal yamin dukan da tunda nake aduniya ba wanda ya taba yimin irinshi,ki dubi yadda ya sauyamin halitta"tayi maganar hawaye nabin fuskarta.

Murmushi yusura tayi sannan tace.

"hakane Tasleem,amman in mukai duba da hukuncin nasa abinda yamana daidai nesabida se yanzu nake ganin hatsarin da muka so jefa rayuwarmu ciki,yanzu kinga da da tsautsayi zaki rasa virginity dinki,gaba mukaci ko baya,taba jikinki da hisham yakeyi ay ba daidai bane"

shuru tasleem tayi tana kallon yusura alamun batun ya shigeta,ajiyar zuciya tayi sannan tace.

"hakane yusura,amman ay kp turmi da tabarya ya kama mu irin wannan dukan yayi yawa,kidubi yadda ya ajiyemin tabo akan boobs,wanda inba saa ba har in mutu baze bace ba,wannan ay cutace,kinga yanxu wannan tabon ze janyo duk mijin da na aura ya tambayeni ya akayi naji shi,ni wlh ya cuceni"


Dariya yusura keyi harda hawaye ita ko tasleem hawayen takaici takeyi.

Suna hakane wayar Ammar ta shigo.


Ganin bakuwar number yasa yusura kin daga wayar ta tsinke ya sake kira.

A karo na biyune yusura ta daga dan taji waye,cikin sassanyar muryarta tace.

"hello"

Ajiyar zuciya Ammar ya saki jin muryarta,dan haka shuru yayi yana jinta tana sake fadin.

"Hello wai wake mgn,"

"yayanki ne"


Take ta gano muryarshi,dan haka a hankali ra furta

"ya Ammar"ba tare da tasan sautin ya fita ba.

"Ashe kinsan sunana?"ammar ya tambaya yana gyara kwanciyarshi.

Murmushi tayi me sauti,ba tare data bashi amsa ba.

"me kikeyi har yanxu da baki bacci ba?,ina fatan ba zance kika fita ba ko?"

Cike da shagwaba tace.

"kai ya Ammar wanne irin zance kuma,ay ni banma da lokacin samarin inbanda karya ba abinda suka iya,ka fita kasha sanyi abanza su cikama kunne da karyar banza"

Dariyar Ammar yakeyi harda kyakyatawa,jin tayi shurune yasa yace.

"to me ya hanaki bacci?"

"Tunani"ta bashi amsa.

"tunanin me ?"

"Yaya Auwal mana,wlh ya ammar inde yaya Auwal yace irin dukan daze dunga mana kenan wlh mu guduwa zamuyi"tayi mgnr tana kuka.

Sosai yaji tausayinta,kukanta na taba zuciyarshi,runtse ido yayi yana jinta.

Tasleem dake zaune tana jinsu da sauri ta kwace wayar a hannun yusura,tace.

"yaya Ammar pls,kaba ya Auwal shawara"

jin tasleem na mgn yasa Ammar sa wayar a handsfree,dan Auwal yaji.

"wacce shawara zan bashi tasleem?"

Da sauri Auwal ya dago kai jin Ammar ya ambaci tasleem.

"Ya ammar ka bashi shawara,yadena dukanmu haka,mu bafa yara bane mun girma,ni wlh ko alabari ban taba jin andaki yanmata kamar mu ba,,duk kyauna yanxu ya Auwal ya maidani kamar wata dodanniya,fuska akumbure,yayiwa kowacce gaba ta jikina illa,kuma wlh Zalincine,kuma kace mishi ni ba karuwa bace wlh,yaje can yanemi karuwai amman ba niba"tana maganar tana kuka.

Shiko Ammar dariya yakeso yayi amman ya danne.

Auwal ko kamar kurma haka ya koma.

"A gaskiya be kyauta ba,kice ya maidake mummuna kenan?"cewar Ammar yana murmushi.

Abunka da yarinta ay tasleem cewa tayi.

"mummuna ay da sauki,kamar dodanniya ya maida ni,inma kishi yake nafi budurwarshi kyau ay da bemin dukan mutuwaba,sabida yin Allah ne,nide kawai na barshi da Allah kuma wlh wuta bal bal"

??????


Dariya Ammar yake harda tuntsirawa,

Auwal duk yadda yakai da mazewa seda yayi murmushi,jin ance mishi wuta balbal.

Mikewa yayi yaje ya amshi,wayar hannun Ammar yace.

"Baki yafemin ba ko,kuma wuta bal bal,zan hadu dake ne"


wata kara tasleem ta saki gamida zabura ta yarda wayar fadi take.

"wayyo yusura mugun Ashe yana jinmu,na shiga uku,dama karyanine kawai beyiba,wlh in yadawo nasan dagargazani zeyi"

Yusura ma jin muryar ya Auwal seda hantar cikinta ta kada,dan haka da sauri ta kashe wayar gaba daya.

Ammar ne keta kokarin sake kiransu amman wayar akashe dan haka mikewa yayi ya isa gaban Auwal yace.

"kai wlh da sake,taya zaka maida yara sekace filin training,in zakayi zalincinka ka tsaya kan tasleem me jan kunnen nan,kadena hadawa da yusura ehe,haba sabida tsabar zalinci ji yarda yara suka rude daga jin muryarka,ina tsaka dajin dadin rayuwata ka katsemin dan haka kaje kawai nima irinta tasleem din,wlh wuta bal bal"????


Wata dariya Auwal ya fashe da ita gamida kaima Ammar duka,yace.

"Ay wlh ko ita setasan tacemin hakan"

"can ta matsema nide kawai kai da Allah wlh"cewar Ammar sanda ya kwanta kan gado yana tsaki.

Auwal be sake mgn ba shima yabi bayanshi suka kwanta,

Tuni Ammar yay baccinshi.

Sede shi Auwal kiyamul laili,ce ta kamashi,koya ya runtse ido muryar tasleem yakeji tana fadin.

"wuta bal bal"

da zaran ya bude kuma zuciyarshi na hango mishi,hoton su sanda yake mata dressing ciwo.

Yadda yaga rana haka yaga dare yarasa me ke damunshi.

muje zuwa

surbajo for life.


KARAN BANA.........*
????????


*ZAHRA SURBAJO*

*Instagram @zahra_surbajo1,domin samun post dina da wuri follow my ig acct*


*Dedicated to Billy Shantally*


*nayi mistake din number last page yanzu 24 zamu tashi*


*24*


"shine zaki tafi bayan kin ganni?"cewar ammar bayan ya saketa.

Murmushi tayi ta dukar da kai sannan tace.

"ba haka bane ya ammar,kawai de inason in tseratar da lafiyata ne"

Murmushi yayi sannan yace.

"yayi kyau,to jirani in gaida umma in fito"

Yana fadin haka ya juya ya nufi dakin umman bayan sun gaisa Auwal zama yayi suka ci gaba da hira da umma.

Shiko Ammar ficewa yayi zuwa gurin yusura da ke kofar gida tana jiran ko ta kwana,dan ta kasa imanin jiranshi acikin gidan.


Fitowa yayi ya sameta tana leken cikin gidan yace.

"tsoron ki yayi yawa Wallahi"

Murmushi tayi tace.

"tsoro halak,bazaka gane bane ya Ammar,ya Auwal fa so yake ya fasa jikina kamar yadda ya fasawa tasleem"

"ayko da yaga masifa dan bazan yarda yacimin mutuncin jikin ki ba wallahi"cewar Ammar yana dariya.

Cikin rashin fahimtar inda zancan nashi ya nufa tace.

"to meyasa ya Ammar?"

"sabida inasonki yusura,ina son ki zama matata ta aure,kinga ko inya dakeki ayni ya daka"ya bata amsa cikin wata murya da bata dauka yana da ita ba.

Juyawa tayi da sauri zata bar gurin,hannunta ya ruko yana murmushi yace.

"kar ma ki fara andena wannan yayin tun su xianoxy suna matasa,bare yanzu da suka tsufa,kawai in kina sona ki amsa min pls"

Kokarin kwacewa take shi kuma yaki sakinta,cikin muryar shagawaba tace.

"pls Ya Ammar lets me go"

"Answer me first bf you go"ya bata amsa yana murmushi.

Ganin da gaske baze kyaleta bane yasa tace.

"Ina sonka Ya Ammar"cike da kunya tayi maganar 


Sosai yaji dadin amsa mishi da tayi,addua da fatan alkhairi yayiwa soyayyar tasu,ita de yusura da so samune ya barta ta tafi gidan su Binafat amman yaki barinta ya tsareta da hirar soyayyarshi.


Malama tasleem ko ba sallama ta shige gidan su jameesha tana haki.

Jin motsin shigowarta ne yasa jameesha lekowa taga waye.

Ganin tasleem na haki ne yasata mamako gamida karasawa gurinta tace.

"yarinya me kyau lafiya kuwa kike?"

"hmm bari kedai,annoba ce ta sauka agidanmu,shiyasa nake gudu"cewar tasleem cikin alamun gajiya.

"Annoba wacce iri kuma tasleem?"jameesha ta tambaya a dan tsorace.

"Yaya Auwal ne fa yazo"

Dariya jameesha tayi sabida tasan labarin dukan da ya musu kwanaki,cikin dariya tace.

"kice fiya fiya maganin kananan kwari"

"koma de me zakice eh shine yazo,dan haka bazan koma ba se anjima in ya fita"

Dariya jameesha take ta mata haka taja hannunta zuwa gurin mamanta dake daki.


Yusura da Ammar hirar soyayya tayi dadi,dan haka daukarta yayi a mota suka shiga zaga gari.

Auwal fitowa yayi daga dakin umna,ganin ba kowa agidanne yasa yagane sun gudu sabida tsoronsa.

Murmushi yayi daya tuno diramar da sukayi.

Dakin zaure ya wuce,ya rage kayan jikinshi,dan so yake yay wanka,

da yake akwai bayi a jikin dakin shiga yayi yayi wankan da ruwan sanyi dan yasan in yace ruwan zafi ze jira bame dora masa se umma shiyasa yayi da na sanyin.


Kanin jameesha da Tasleem tasa gadi in yaga fitar bakar motar kofar gidansu yazo ya fada mata,shine yaga wucewar Ammar da yusura,dan haka da gudu yaje ya shaidawa tasleem masu motar sun fita.


Da sauri ta mike taiwa su jameesha sallama ta nufi gida cike dajin dadin zata shige daki kamin su dawo.

Koda tazo kofar gidan sake tabbatarwa tayi basanan,kai tsaye ta shige cikin gidan.

Har ta wuce kofar dakin zauran,se ta dawo ganin kofar dakin turota kawai akayi.

Zuciyarta ce tabata shawarar ta tura kofar ta leka taga yawan kayan dasu ya Auwal din sukazo dashi dan ta fahimci ko zasu jima kan su tafi.

?????

Turawa tayi a hankali,ta tura kanta ciki,batare da tunanin komai ba.


tana shiga laptop ta gani akan katifar dakin,jikinta har bari yake ta karasa gurinta.


Budewa tayi gamida adduar Allah yasa ba password.

Ayko tana budewa lafiyayyen hoton ya Auwal ne a fuskar yana murmushi.

Ay budar bakinta se cewa tayi.

????

"An fa mori fuskar zuciyarce baa mora ba,"

???

sake kallon hoton tayi sannan tace.

"bakar zuciya kamar firauna,in banda dukan mata a boobs ba abinda ya iya,dan rainin wayo kuma wai yazo dressing sabida tsabar iskanci,sunan yana likita amman besan ran mace na hade da boobs dinta ba,wlh in ya kuma duka na,zesha mamaki,"ta karasa maganar cikin nuna masa yatsa.

????


Auwal da tun shigowarta ke zaune yana shafa mai,kallonta kawai yake yana dariya a zuciyarshi,dan yasan da zata ganshi yanzu may be tayi kashin da tace.

Hankali kwance ta shiga cikin laptop din tana ta bincikenta,tanayi tana lekawa ta window gudun kar ya dawo ya sameta.

Har ya gama shafa man tasleem bataji motsin shi ba.

Gashi kayan daze saka akansu ta zauna,dan haka nufarta yayi yace.

"Dan dagamin kayana zan saka"

?????


kuyi hasashen next page.

Muje zuwa


surbajo for life.


*KARAN BANA........*
????????



*ZAHRA SURBAJO*


*IG @zahra_surbajo1*


*tun ina rubuta surbajo na dena tura novel ta pc,kudena wahalar tambaya bana turawa iyakata in tura group sabida nasan inada masoyan da inkun wuni tambaya zasu wuni turawa,Adding numbers a group ma banayi sauran admins dinne keyi,so ku dinga tambayarsu don Allah,kaf admins dina bame wulakanci,kuna tambaya zasu saku,pls,inkunji haushin fadin hakan kuyi hkr,gaskiya na fadi*



*dedicated to billy shantally*



*25*




Cak tasleem ta dauke hannunta daga kan laptop din.

Sede yadda jikinta ke rawa zaka dauka ranta zaa zare.

Mikewa tayi tsaye ba tare data juyo ba,hannu a sama alamun tayi saranda.

Waigowa tayi bakinta na makyarkyata,tanaso taga inda gaske muryarshi taji.

Koda ta waiga,tsaye yake dagashi se gajeran wando se tawul dake rataye a wuyanshi.ya kafeta da shanyanyun idanuwansa.

 "ya ya ya ya ya ya ya au........."tasleem ke kokarin kiran sunanshi amman ta kasa hada kan sunan.

Idanunta ne suka fara yin sama,ga wata shakuwa data kamata.

Luuuuuuuu ta tafi zata fadi,da mahaukacin gudu Auwal ya isa gareta ya tareta ta fado jiknshi.

Jijjigata ya shigayi yana dan marin kumatunta yana fadin.

 "ke ke tasleem,tasleem tashi ba abinda zan miki open your eyes pls"yana fadi yana girgizata.

Amman ina ko motsi batayi,Auwal sosai ya gigice rasa abinda zeyi yayi,janta yayi zuwa gefen katifar ya zauna sannan ya kwantar da ita kan cinyarshi,yana ci gaba da kiran sunanta amman shuru kakeji.

Ruwa ya mika hannu yadauka  ya bude ya shafa mata a fuska amman dif kakeji.

Fifita yake mata amman tasleem kamar gawa,zuwa lokacin zufa har diga take ajiikin  Auwal.

Ga shi Ammar ya fita da mota bare ya kaita asibiti danshi gaba daya ya gama susucewa yama rasa abin yi.

Zuwacan tunaninsa ya basa wata shawarar,dan haka dagota yayi ya rungumeta da kyau ya hada bakinshi da nata ya shiga hura mata iska ta cikin bakin.

Hhhhh ay su @xianoxy sabida irin wannan agajin gaggawan aka shiga aykin likitancin????. 

Tari  ta fara yi da karfi dan iskar taso kwareta.

Idonta ta bude a hankali tana kallonshi.

Sakale yayi da ita ahannunshi labbanshi akan nata,yana kallonta.

Tsananin mamakin inda take da kuma jikinta da ba kwari ne ya hana Tasleem yunkurin kwace kanta ajikin Auwal.

Komawa tayi kamar wata wawiya,ido take zarewa bada wasa ba.

Yadda take kada idonne  ya shagaltar da auwal gurin kallonta.

Kamar wacce aka tsikara ta tuno a kan cinyar wa take.

Da dukkan karfinta ta shiga kiciniyar kwacewa tana kuka tana fadin.

 "wallahi bada kai nakeba,don Allah kada ka dukeni,kayi hakuri ya Auwal don Allah karka dakeni kaga batamin jiki kake da duka mijin da zan aura baze ji dadin ganina a haka ba"


Shi yadda take motsa bakin ma burgeshi take,itako dauka tayi kallon da yake mata duka zata sha.

 "to naji ki natsu ba dukanki zanyiba"ya furta a kasalance.

Ido ta ware tana kallonshi,bakinta na kakkarwa,tace.

 "wlh matukar ina kan cinyanka bazan taba natsuwa ba pls ka kyaleni na gudu don Allah"tayi maganar hawaye nabin fuskarta.

 "is ok zan kyale ki amman ban amince ki fita ba kinji ko"

Yadda take gyada kai kai ka rantse,kadangare ne ya hangi abincin manja?. 

Sakinta yayi,da gudu tayi birgima ta sauka akan cinyarshi,kamin yayi mgn,tuni se bayanta ta ranta ana kare tayi cikin gida.

Kai tsaye dakinsu ta fada,kan gado ta haye ta kwanta tana ta jero ajiyar zuciya.

Bayan fitarta murmushi Auwal yayi ya mike,yaci gaba da kintsawa.

Sosai kayan sukai masa kyau,ba kadan fa,kyanshi da tsarin zubin halittar jikinshi suka kara fitowa.

Takalmi yasa sannan ya fesa turare,yaja kofar ya nufi cikin gida dan ya kara firgita yar darun shi?. 


Umma ya tambaya ina take ta sjaida mishi tana dakinsu dan haka dakin ya nufa,cikin takunshi me burgewa.

Daga labulen kofar yayi ya shiga,lokacin tana zaune tana hada kayanta a jaka.tana fadin.

 "wallahi bazan zauna ba gwanda inje kauyenmu yako in kaiwa inna uwani ziyara,in ya tafi na dawo,dan naci gaba da zama ciwon zuciyane ze kamani"tana maganar tana share hawayen ta.

Tsayawa yayi yana binta da kallo,sam beji dadin tafiyar da takeson yi ba sabida shi.

Motsinshi taji ta waigo,a gigice ta mike rike da kayan undies dinta da takeson sawa cikin jakar,kan gadon ta haye ta mike tsaye takai karshen bango,jikinta na tsuma.

Wani kallo ya wurga mata wanda yasa tsigar jikinta tashi,da sauri tayi kasa da kanta.

Takawa yayi ya taka shima yahau kan gadon so yake yaga me take boyewa a hannunta da tayi baya dashi,ayko hakanne yasa ta sake boye hannun nata abayanta,

Daya lura da gaske bataso yaga abin hannunta tsayawa yayi yana kallonta yace

 "tunda bazaki bari in gani ba to sakko ki zauna zanyi mgn dake kinji ko"

Ba musu ta sauka ta zauna gefen gadon tana kara boye hannunta,nanko gurin sauka batasan yaga abinda take boyewar ba.

Sauka yayi shima ya zauna akusa da ita.

Azabure ta sauka kasan gadon tana binshi da kallo.


muje zuwa.


Surbajo for life.


*KARAN BANA.........*
????????

*ZAHRA SURBAJO*



*i loves you Hamidan Hamma for no reason,koya ranki ya baci surbajo na rasa sukuni,fushinki na jefani cikin wasi wasi,kici gaba da hakuri dani my other half,Allah ya albarkaci rayuwarki data zuriar da zaki haifa mana,yabarki cikin so da kaunar juna keda hamma,alkhairinki gareni is unforgetable*

*Dedicated to Billy shantally*


*26*




 Bin ta yayi da shanyanyun idanuwansa,fuskarshi dauke da murmushi,yace cikin tausasshiyar murya.

"ina wari ko?"

A tsorace ta dago ido tana kallonshi,tanaso ta gasgata daga inda taji maganar.

Murmushi yamata gamida lumshe ido yasake maimaita tambayar.

A sukurkurce tace.

"Aa ya Auwal ni ban ce ba"

Wani murmushin yayi sannan yace.

"in ba haka bane me yasa kika bar kusa dani?"

A tsorace tace.

"banso ne kana kawomin duka ina kusa dakai,gwanda ina nan kan ka karaso zan iya guduwa"


Murmushi yayi daya kara kawata kyawun fuskar sa sannan yace yana bin ta da kallo.

"ce miki akayi ni banda ayki sena duka?"


Bakinta na rawa tace.

"Aa ba cemin aka yi ba,aykinka ne ya nunamin hakan"

Shuru yayi yana kallonta,gaba daya a tsorace take dashi,jikinta se rawa yake.dole ya kauda tsoron nan nasa daga zuciyar tasleem,shine abinda ya fadi aransa.

Mikewa yayi,ay tun kan ya taka itama ta mike a zabure zata falla da gudu.

Cikin zafin nama ya damko hannunta,

Waigowa tayi tana hawaye tace.

"Don Allah ya Auwal karka dakeni,wlh banason duka yana wahalar dani"


Sosai tausayinta ya kamashi,matso da ita yayi kusa dashi yasa hannu yana share mata hawayen yana fadin.

"Tunda bakyason duka,bazan kara dukanki ba,kinji ko,namiki alkawari"

Cikin rashin gamsuwa ta dago kai tana kallonshi,tace.

"Da gaske kakeyi?"

murmushi yayi yasa hannu yaja kumatunta yace.

"da gaske mana"


Shuru tayi itade tana binshi da ido.

Ganin tana kokwanto ne yasa Auwal yashiga kwantar mata da hankali gamida bata tabbacin baze kuma dukanta ba,har seda ta gamsu.


Wata kara tasaki kana daga bisani ta shige jikinshi ta rungumeshi,tana murna mara misaltuwa tana fadin.


"thanks you thanks you thanks you"tana gama fadin haka ta sakeshi ta ruga da gudu tsakar gida,tana murnar samun yencin kai.

Shiko Auwal tana sakinshi ya fadi kasa tim,dan kafafunshi sun kasa rikeshi,?sabida wannan ne karo na farko da mace ta fara rungumeshi.

Ko matarshi maryam bata rungumeshi dan kunya sede shi ya rungumeta,zamanshi kasar waje kuma ba ruwanshi da mata bare har ya barsu su rungumeshi.


Wani bakon alamari ne ke yawo ajikin Auwal,wanda rabonsho da yaji hakan tun yana tare da matarshi maryam.

Duk yadda yaso ya daure ya tashi ya kasa dan gabobinshi gaba daya sunyi sanyi.

tasleem ko ganin be fito bane yasa ta koma dakin dan taga me yakeyi.

Zaune ta sameshi akasa ya rike kanshi.

"ya Auwal da fatan de komai lfy ko?"ta fadi sanda ta shiga daki.

Dago kai yayi ya dubeta da jajayen idanuwanshi,da sauri taja baya,sabida ta tsorata da ganin idon nashi,dan yanxu ta fita ta barsu farare yanzu gashi ta dawo sun sauya.


Murmushin karfin hali yayi sannan yace cikin dasasshiyar murya.

"ba kece kika kada ni ba?"

Murmushim karfin hali tayi sannan tace.

"ya Auwal ban yar dakai ba fa"

murmushi yayi yace.

"to na fadi ne,zoki daga ni"ya karasa maganar gamida mika mata hannayensa.

Dariya ta tsaya tanayi,gamida rufe ido tace.

"wlh bazan iya daga ka ba ya Auwal,sabida in na janyoka ay banda kwarin dazan iya tsayawa,kana tashi ni zan fadi"

murmushi yayi yace.

"Bazaki fadi ba"


Kama hannayen nasa tayi da dukkanin karfinta ta janyo shi ya mike,ayko yana mikewa ita tayi baya zata fadi.

da sauri ya ruko kugunta,ta dawo ta tsaya cik.

Dariya tayi tace.

"ka gani ko?"

Murmushi yayi yace.

"banga komai ba"

Kasa jure tsayuwa adakin yayi dan haka ficewa yayi zuwa zauren gidan ko ya samu saukin damuwarshi.

Bayan fitar ya Auwal ajiyar zuciya tasleem tayi sannan tace.

"Allah nagode maka"

Yusura da Ammar seda suka tsaya suka siyo kayan kwadayi sannan suka dawo gidan.

Da daddare su Auwal suka kwashesu zuwa sabon gidan da mummy ta basu.

Umma har kuka tayi najin dadi,

Su tasleem ko sunfi kowa murnar samun sauyi,dan aganinsu ajinsu yafi gaban wancan gidan,

Muje zuwa

Surbajo for life.



*KARAN BANA...........*
????????



*ZAHRA SURBAJO*




*Maman Gidado,tawa ina gaisheki,kuma ina ganin kima da girma da darajarki fiye da tunaninki,kece farkon fara ganina face to face?kaf social media,ina alfahari da hakan my sweety,wallahi ina matukar kaunarki,Allah yabarmu tare ya tsaremu ya tsare mazajanmu da zuriarmu daga sharrin duk abun ki,we are together for ever????*


*Dedicated to Billy shantaly*

*whatsapp no dina kenan,08093235081 gaisuwa kawai,karkice insaki a group karkice in turo miki novel,ba nayin daya daga ciki?,ko kin kira bazaki samuba,whatasapp kawai nakeyi da ita*

*Ig @zahra_surbajo1*


*Wlh na rasa nomba dinki wacce kika bani recharge card,na gani na gode,Allah ya kara arziki*



*27*


Auwal duk yadda yake tunanin lamarin tasleem ze zo masa da sauki abun ba haka bane.

Duk yadda zeyi wajen ganin ya cireta a ranshi amman abun yaci tura.

Ita ko Tasleem zuwa yanxu ta fara son danmaliki so na gaskiya da Amana.

Sabida sosai yake nuna mata kulawarshi,shiyasa zuciyarta ta gamsu dashi.

In suna waya har bataso su dena sabida sonshi.


Yau ne ta bashi damar zuwa sabon gidan da suka koma,dan haka tun safe take hidimar tarbar shi,se girke girke take masa.

Ammar da yake ya samu Ayki a Abuja yasa,be fiye zuwa kd ba se weekend.

Shima ya Auwal yasamu ayki a Abujan Amman ya nuna bayaso yafiso yasamu a kd ta yadda ze kula da gidansu.

Mummy bata musa ba tasa a nemar mishi.

Shiyasa kusan kullum yana kd yana fama da zuciyarshi akan tasleem.

Fitowa yayi daga dakin da yake training,yaji kamshin girki duk ya cika gidan.

Da sauri yayi hanyar kitchen din dan dama yunwa yakeji.

A tsaye ya sameta tana soya kaza.

Tsayawa yayi yana kare mata kallo,kana daga bisani yayi gyaran murya.

Waigowa tayi adan tsorace.

Ganin shi ne yasa ta saki murmushi tace.

"ya Auwal a kitchen?"

Murmushi yayi ya fara takawa zuwa cikin kitchen din yana goge zufar jikinshi da tawul.

"eh nine da kaina,naji kin kaure gidan da kamshi yasa nazo naci nawa a kitchen din"ya karasa maganar sanda ya isa,gurin kulolin abincin yakai hannu ze bude.

A zabure tasleem ta karasa kusa dashi,ta ruko hannunshi.

Waigowa yayi yana kallonta yana murmushi.

Ita ko cikin inda inda tace.

"don Allah ya Auwal karka taba wainnan,na bako na ne,ka bari in yunwa kakeji yanxu zan dafa maka indomie"

Maganar tata dariya ta bashi,dan haka yana dariyar yace.

"ni zaki dafawa indomie,cemiki akai ni yaro ne?,wannan wanne bakone da yafini a gurinki da bazaki bani abincin naci ba?"

Cikin murmushi tace.

"ya Hisham ne ze zo anjima,kuma yacemin anan zeyi dinner lunch shiyasa"

Take yanke annurin fuskarshi ya kauce,zuciyarshi ta shiga tafasa azuciye ya fisge hannunshi daga nata ya juya ya fice daga kitchen din.

Tasleem tsaye tayi tana bin bayanshi da kallo,tanason tasan me yasa yay fushi,ganin ta rasa amsa ne yasa ta daga kafada sama,ta juya taci gaba da girkin ta.


Auwal ko gaban shi be gani haka ya haura sama,dakinshi,kan gadonshi ya fada,yana huci.


"Dole in dauki mataki,wlh ya hisham bazaka samu tasleem ba,nasha bar maka abinda nakeso,amman bazan bar maka tasleem ba,zanyi duk me yiwuwa wlh"

Yana kaiwa nan ya mike ya fice ya nufi dakin umman tasleem din,yana shiga yasameta zaune tana kallo.

Zuwa yayi ya kwantar da kansa kan cinyarta ya fashe da kuka?????

A gigice umma ke tambarshi me yasameshi,amman Auwal fafur yaki mgn kuka kawai yakeyi harda hawaƴensa?

Ashe maza sun iya kirsa???

Da kyar tasamu ya fara mgn cikin kuka.

"umma kinmin alkawarin duk abinda nakeso inkina dashi ko kina da iko dashi zaki bani?"

Da sauri umma tace tana share hawaye.

"Auwalu na maka alkawari ko menene ka bukata zan baka"

"Umma tasleem nakeso ki bani na aura"

Murmushi umma tayi,dan dama ranar kawai daze furta take jira,dan ta juma da sanin Auwal nason tasleem.

"Yanzu akan tasleem din kake kuka?"

Kai ya gyada mata gamida cewa.

"Eh umma in kuma kika hanani nan gaba rami zaki haka ki sani"

Dariya tayi sannan tace.

"Auwal ko ba kai ba,dama ay kaine madaurin auranta,kai keda ikon ba wanda kakeso,dan haka kaba wanda yadace"

Dariya yayi yace.

"Nafi kowa dacewa da ita umma,dan haka naba kaina,umma kin amince?"


"Na amince Auwalu ko gobe ne ka fito ayi auranku"

Wata kara yasaki gamida rungume umman yana mata godiya.

Mikewa yayi ya fice,cike da nishadi,yayin da umma tabi bayanshi da kallo tana dariya.


Yana fita dakinshi ya koma yayi wanka ya shirya,ya fice yawon zaga gari,zuciyarshi fess,dan ya lashi takobin ze auri yasmin ko bata sonshi.?

Muje zuwa.



Surbajo for life.
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 2 36,320 09-14-2018, 12:13 PM
Last Post: Gimbiya
  *KANO TO JIDDAH* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 9 111,928 09-05-2018, 06:57 PM
Last Post: Gimbiya
  *Y'ar Bautar K'asa* A Youth Corper*by Zahra Surbajo Gimbiya 1 17,110 08-10-2018, 01:58 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 18,162 07-26-2018, 12:53 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 13,366 06-26-2018, 01:07 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 15,622 06-19-2018, 01:08 PM
Last Post: Gimbiya
  *KANO TO JIDDAH* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 1 73,766 12-07-2017, 03:17 PM
Last Post: Gimbiya
  *AMANA TA BARMIN* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 42,148 11-30-2017, 11:25 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)