The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud
#1
????????
*KARAN BANA............*
????????


*ZAHRA SURBAJO*



*BISIMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

*Wannan daban yake da sauran,zaku tabbatar ne yayinda kuka karanta,dan wannan abunda ke faruwa a zamanin nan namu ya kunsa,kubi sannu a hankali ku kamo bakin zaran*


Facebook@surbajo maman yusuf

Instagram@zahra_surbajo1

Whatsapp@?


*1*


 "wallahi yusura tsoro nakeji kar naje ya turmusheni tunda shi dan akuyane"

Dariya yusura tayi kana daga bisani tace.

 "haba tasleem,taya zaki bari ya turmusheki?abunnanfa mun gama tsara yadda ze tafi inde kinbi duka tsarin namu wlh ba abinda ze faru "

Ajiyar zuciya tasleem tayi gamida cewa 

"to Allah yabamu nasara"

"Amin"inji yusura.

Daga haka yusura ci gaba tayi da yiwa tasleem kwalliya.ba karamin kyau tasleem tayi ba.

Bayan ta gama yimata kwalliyarne,ta ciro wasu kaya acikin leda,atamface ja riga da siket,mikawa tasleem kayan tayi tace ta saka.

Ba musu tasleem ta amsa ta saka,abunka da farar mace cikin jan kaya take ta fara haskawa cikin kayan kai kace Leemarh yusuf ko ziauzee ce?(queens of beauty). 

Ita kanta tasleem ta yarda ita me kyauce,kuma tayi kyau acikin kayan,dan haka fara rausayawa tayi yusura na koda baiwar kyanta.

Zuwacan ta dena rawar ta kai dubanta ga yusura tace. 

"ina fatan de kin biya kudin dinkin kamin ki amso? dan kinsan shehu tela beda mutunci kona sisi"

Dariya yusura tayi sannan tace.

 "wlh ban biyaba,sabida munyi dashi da daddare zezo ya karbi kudinshi,kinga zuwa lokacin ke kuma kin dawo daga gurin alhaji,semu biyashi acikin kudin da zaki samo"

Dariya tasleem tayi wacce ta bayya wushiryar dake tsakanin fararen hakoranta,gamida lotsawar kumatunta,wato dimple,sannan tace.

 "amma wlh yusura bantaba ganin mace me wasa da ratuwarta irinki ba,to yanzu idan naje kuma Alhaji be bani kudin ba fa?" 

"Bakinki ya sari danyan kashi insha Allahu zaki samo kudi"

Suna tsaka da maganarne karar wayar yusura ya katsesu,da sauri yusura takai dubanta fuskar wayar,sunan daya bayyana akan wayarne yasata sakin wani killer smile,

*A,T,M,*

 shine sunan da ta gani,nuni tayiwa tasleem da tayi shuru,sannan ta daga waya ta kara volume dan tasleem taji.

Cikin wata kasalalliyar murya,me daukar hankali tace.

"your highness"

Daga can bangaren ya amsa da.

 "Baby "

"naam"yusura ta amsa.

Daga can yace.

"my baby ,nayi kewarki fa"

 "nima haka baby"cewar yusura. 

"baby da wanne lokaci zaki tasone?wlh na kosa na saki a idona,wainnan soft lips din naki ina bukatarsu"


Wani irin jan numfashi yusura tayi wanda duk namijin da akayiwa haka dole se ya hau online sannan tace,

"Wlh your highness tafiyar nan fa tasamu matsala dan zeyi wuya ma na samu damar zuwa" 

"no baby karki batamin budget,fadamin meye matsalar da zata hanaki zuwan?" 

Cikin muryar kukan kirsa yusura tace.

 "ba mummy bace ta kwacemin atm card dina,wai na fiye kashe kudi,dan kawai na sayi ankon kawata 100k,kuma gashi yau weekend babu banki bare naje na yi withdrawing tacan,"

 Ajiyar zuciya yayi jin cewa matsalar ba babba bace,cikin sigar rarrashi yace.

 "baby inason shagwabarnan taki,amman yanzu de kiyi shuru,kinji,fadamin nawane kudin mota daga yola zuwa kd?"

 "ni bansaniba sabida ban taba zuwa ba,i hope bade ni kake saran zanyi long journey daga yola zuwa kd a mota ba?"

 "baby rigima,to yanzu laifine dannace kizo a motar"

 "laifine babba,danni ko taraba zani daga yola jirgi nake bi bare kaduna"(uwaki karya)?

 "to naji turomin account no dinki sena turo miki"

 "nida nace ma mummy ta kwace atm dina taya zan cire kudin inka turo,bari kawai na turo maka na bross dina"

 "ok to kiyi sauri dan kisamu jirgin yamma"

Kashe wayar tayi,da yake duk abinda suke fadi tasleem naji,hakanne yasa tana kashe wayar tasleem tayi wani uban tsalle ta fada kanta suna murna.

Seda suka gama rawar murna sannan  tasleem tace.

 "Hajiyata ke bomb ce,in kin tashi tashi bakyayin me kyau"

Dariya sukayi suka tafa,sannan yusura tace.

 "ke bamuga ta zama ba,taso muje gurin garba me gugu mu amshi account dinshi mu tura masa"

Ba musu tasleem ta miki suka sa hijabansu suka nufi shagon garba,

Bayan sun gaisane suka fada masa bukatarsu tason ya basu account no dinshi.

Ba musu ya basu inda yana basu yusura ta turawa Alhaji,bayan ta tura guri suka samu suka zauna zaman jira,zamansu ba jimawa garba ya shaida musu sakonsu ya shigo 50k.

Dan tsananin murna dukansu seda sukai hawaye,jirewa garba shagon sukayi shi kuma yaje ya ciro kudin yazo ya basu,

Dubu biyar suka bashi,daganan suka koma cikn gida,suka sake shafa hoda,sannan suka fito,sede yanzu yusura ce kawai sanye da hijabi,janye da katuwar akwatin kaya wato troley,tasleem wani siririn mayafi ta yafa.

Suna fitowa keke napep suka hau ,zuwa airport.

Sede abinda yaban mamaki,airport din da suka nufa na garin kaduna ne,dake mando.kuma ni naji ana batun tawowa daga yola,

what is going on ne ayam not understanding?

Bayan ramadan yananan tafe.

Nayi posting din ci gaban a shafina na instagram, @zahra_surbajo1 zaku iya zuwa can ku karanta.


Muje zuwa surbajo for life

????????
*KARAN BANA.......*
????????


*ZAHRA SURBAJO*


*Happy sallah to you all in advance.*

*Pls kuyi hkr facebook da whatsapp wlh na manta ne tunda rana nayi posting instagram,so gameso ya dunga karantawa akan lokaci se ka bibiyeni a instagram din @zahra_surbajo1 zaku samu acan,ngd*


*2*


Suna isa airport din,gurin kofar arrivals sukaje suka samu guri suna kallon mutanen dake kai kawo.

Kimanin awa biyu suka kwashe agurin sannan yusura ta kunna wayarta data kashe tun bayan awa guda.

Kamar jira tana kunnawa kiran Alhaji na shugowa,makale murya tayi cikin sigar jan hankali tace. "touch down kd"

Cike da doki Alhajin yace. "oh my god,baby da gaske kike yi" "da gaske mana dear,pls kai  sauri banason jira fa" "give just 30 minutes baby,on my way coming"

Daga haka ya kashe wayar.

Dubanta takai gun tasleem wacce tayi zuru zuru kai kace me gudawa,kallo daya tai mata ta gane a tsorace take,dafata tayi tace. "tasleem cool your mine pls,wlh ba abinda ze sameki,inde kinbi komai yadda muka tsara,ki saki jikinki"

Murmushi tasleem tayi tace. "to yusura," Suna cikin maganar yusura ta hango wata hadaddiyar mota na parking a parking space.

Number motar shi ya shaida mata wanda ke ciki. 

*DAN MALIKI*  

Shine sunan dake jikin number motar.

Da sauri ta mike tace wa tasleem. "get ready tasleem,he is arrived"

Da sauri tasleem ta mike tasa glass dinta sannan tadan kara zazzago da wuyan rigarta ta yadda saman boobs dinta suka bayyana a waje,cingam ta wurga a baki ta fara taunawa.yayinda ta rike troley din tadan matsa gaba kadan ta yadda ze hangota.

Yusura ko boyewa tayi acikin filawowi.

Fitowa yayi cikin takun kasaita da takama,sanye cikin shiga ta alfarma,yanufo inda take.

Kare mata kallo yayi daga nesa sannan yadan kai dubansa fuskar wayarsa.

Wani murmushi ya saki,sannan ya tako zuwa gurinta.

Yana zuwa tsayawa yayi gabanta yana murmushi yace. "that's my girl"

Wani killer smile tasleem ta saki,gamida matsawa jikinshi sosai ta yadda jikinsu na taba juna tace cikin muryar shagwaba. "your highness garinku kwai nisa"

Wani dadi ne ke tsirga masa har kai,cike da kulawa yasa hannu ya tallafo ta kadan jikinshi yace. "muje mota baby,nan akwai mutane"

Ba musu tabishi janye da troley dinta,suna zuwa ya bude bayan motar tasa kayan sannan ya bude mata gaban motar ta zauna.

Zagayawa yayi yatashi motar suka fice daga airport din.

Komai akan idon yusura ya faru,fitowa tayi daga inda ta boye
Hawayene masu zafi kebin fuskar yusura,wanda na rasa dalilinsu.

Fitowa tayi ta samu napep,tahau zuwa gida ranta abace.

Ita ko tasleem,nacan sun dauki hanyar unguwar rimi ita da Alhaji,

Janyota yayi da daya hannunshi yayinda dayan ke driving,

Kwantar da kanta tayi akan kafadarshi cikin shagwaba tace. "baby na gaji da yawa wallah,gaskiya kd da dan nisa"

Murmushi tayi gamida dora hannunshi kan cinyarta,yace. "karki damu babynki nanan ze matsa miki duk inda kikeji gajiyar,kinji baby na"

Gaban tasleem seda ya fadi amman seta daure tace, "wow dako ka burgeni"

A haka suka karaso 17 hotel dake  unguwar rimi kaduna.

Yana parking ya fita ya bude mata kofa,maimakon ta fito da kanta,se miko mushi hannu tayi ba musu ya dagota suka fito.

Troley din kayanta ma shi ke janye da shi har zuwa cikin hotel din.

Da yake shi customern su ne har ajiyayyen daki gareshi,key kawai ya amsa suka hara sama inda dakin yake.

Suna shiga,ya maida kofar ya kulle,sannan ya kamo ta gaba daya ya rungume yana shinshina wuyanta.

A zabure tasleem ta kwace kanta jin yana kokarin hada bakinsu.

Kan gado taje ta zauna tana murmushi,wanda can kasan zuciyarta kuka take,

Bin ta yayi da ido,da kyar yace. "why baby"

Wani murmushi tayi gamida gantsaro kirji gaba tace. "haba baby,ay se kacemin akan guiwa kake,wannan sauri haka," Dariya yayi yace. " Baby I must confess to you that wlh ban taba ganin boobs irin naki ba. Ina sonsu sosai wlh
 Gasu full, succulent, juicy and tender to the touch,wai a haka ma kenan baby inaga kuma kin budemin"

Waiyyazu billahi,tasleem take bayyanawa azuciyarta,yayinda afili kuma murmushi tayi gamida sake gantsarosu tace. "thanks you baby,"gamida sa hannu taja rigarta sama ta rufesu ruf ta yadda baya gani.

Bata rai yayi yace. "why baby" "maida wukar baby kaida yau tare dasu zaka kwana meye na doki,kawai de naga sun dauke maka hankaline daga fahimtar in bako yayi doguwar tafiya yana bukatar abinci da wanka"

Dariyace ta kubce masa yace. "oh yes,kina da gaskiya,wlh na manta ne,bari inkira restaurant a waya"

Gefen gadon yaje gurin side drower yasa no din restaurants din cikin hotel din ya kirasu yayi order na abincin.

Mude ke zuwa fans


Surbajo for life.

????????
*KARAN BANA.........*
????????


*ZAHRA SURBAJO*



Instagram @zahra_surbajo1


*3*


Yana gama wayar ya dawo kusa da ita ya zauna yana wani shuumin murmushi.

Murmushi itama tayi gamida fadin, 

"good,kayi daya saura dayan"

Murmushi yayi yace.

 "anya baby tana da kunya kuwa,nifa basarakene,yanzu ni zan hada ruwan wankan?"yakarasa maganar yana janyota jikinshi.

Murmushi tayi gamida shafo fuskarshi tace.

 "komai sarautar sarki baby,ay gurin matarsa bafade ne,so dan haka jeka hadamin ruwan wanka,jikina ciwo,yake danni wankanma sede kamin dan bazan iya ba"

Wani sanyin dadi ne ya ratsashi,jin ance shi zeyi wankan,da sauri ya mike ya wuce, toilet din yana 

"baby baby"

Yana shigewa toilet,da sauri tasleem ta ciro wayarta,ta matsa number yusura ta kirata,tana dagawa tace.

 "ki kirani nan da 3 minutes"

Tana gama fadi tai saurin ajiye wayar,ta koma ta kwanta,kamar  ba ita ba.

Tana ajiyewa yana fitowa yana murmushi ya nufe ta,daga kwancen da take ta bude masa hannu alamar yaje jikinta. ???su @xianoxy banza ta samu ay jiki har bari yake ya nufeta.

Rungumeshi tayi kamar gaske,ze rungumeta kenan wayarta ta fara,ringing,dan basarwa tayi,shiko tsayawa yayi sokoko yana tunanin waye ke kiranta awannan lokacin.

Mika hannu yayi ya dauko mata wayar.

*MY SIS.*

Shine sunan daya bayyana,mika mata yayi yace. 

"baby kiran ki ake ki daga"

Dan bata rai tayi,sannan ta daga wayar gamida sata a handsfree,

Tun kan tai mgn,yusura wacce ta sauya murya ta rigata.

Magana take cike da tashin hankali,tace.

 "tasleem,mun shiga uku,kina inane kizo ga mum ciwonta ya tashi,mun kaita asibiti,ance se anbada dubu dari gashi mu bamusan pin dinta na banki ba,don Allah ki taho"yusura ta gama maganar cikin karajin dake nuna tashin hankalinta.

A 360 tasleem ta diro daga kan gadon agigice ta saki wayar tana fadin.

 "wayyo na shiga uku,mummy na karta mutu,yau yazanyi"

Dan tsananin nuna ta rude har faduwa kasa takeyi.

Sosai danmaliki tausayinta ya kamashi,janyota yayi tana diddirjewa tana kuka,dakyar yasamu ta dan natsu,sannan yace.

 "look baby ki kwantar da hankalinki kinji ko,ba abinda ze sameta,taso muje na kaiki airport asan duk yadda zaayi ki tafi yola yanzu,in yaso next time kya sake zuwa"

Cikin kuka tace. 

"to amma baby kai fa,banason tafiya na barka"

Murmushi yayi yace

 "dont worry baby i will manage"

Hakade ya lallabata dakyar ta yarda zata tafi.

Shi ya gara mata shigarta,data hargitse,sannan yaja troley din kayanta,wanda daya bude ba komai ciki se katon dutse shima dan yayi nauyi suka sa.

Suna shiga mota yaja suka nufi airport,tasleem se kuka take.

Suna shiga airport din shi yafara fita,yaje yasamu maaikatan gurin,dayake fitaccen mutum ne ganinsa yasa kowa se dukawa yake yana kwasar gaisuwa.

 "ticket nake bukata,yanzu yanzu zuwa yola,kar acemin babu pls"

Cewar dan maliki cikin nuna isa.

Rusunawa ogan masu saida ticker din yayi yace. 

"Ranka ya dade,da akwai,ticket din,dan anjima kadan jirgin ze tashi"

Bunch din 1000 yaciro ya mika masa,jiki na bari ya amsa,ya rubuta ticket din ya bashi.

Dawowa yayi gurin tasleem  wacce tun bayan fitarshi take kyalkyala dariya,yana dawowa taci gaba da kukanta.

Bude motar yayi ya shiga,yadan janyota jikinshi yace, 

"baby kinaso nai kukan ne nima ko?" 

Kai ta girgiza masa,

 "to kiyi shuru,ga ticket dinki,,nanda yan mintuna jirginki ze tashi kinji ko,ki kula da momy da kyau,in akwai bukatar taimakona karkiji komai ki fadamin"

Kai kawai ta gyada masa.

Handbag dinta,ya amsa ya bude sannan yasa,hannu a aljihunsa, ya dunga ciro bunch yana sawa aciki  kai kace zango na kirga kudin cocacola,??? 

Yana gama sawa ya mika mata jakar,sannan ya fita ya bude mata kofa ta fita,yaja troley dinta zuwa cikin reception.

Suna shiga ya mika mata ticket dinta,lokacin an fara kiran pasinger dan haka juyowa yayi,ze tafi,

da gudu tasleem ta dawo ta rungumeshi tana kuka,tace. 

"i love you baby, am going to miss you seriously baby"

Sosai zancenta ya taba zuciyarshi,dakyar ya cireta a jikinshi,sukai sallama ya fice ita kuma tayi ciki kamar gaske.

Ay tana hango ya fice itama ta juyo da saurinta ta fice.

Tana kallo yatada mota yabar airport din,

Ita ma napep ta tsayar,ta hau tace 

"HAYIN RIGASA"

 ????wayyo ticket din yola ya zaayi dashi,su @nazeefi_bm anyi asarar dubu dari abanza.

Muje zuwa

Surbajo for life

????????
*KARAN BANA.........*
????????



*ZAHRA SURBAJO*



*Instagram @zahra_surbajo1*


*bata da zance kullum se tawa tawa,ko so daya na gaza kiranta da sunan tawa nima,hakan besa ta dena kirana a tata ba har gobe,kiranki a matsayin tawa kawai baze nuna matsayinki agurina ba,ayau nima zan gwada nuna miki tawa soyayyar,BILLYN SHANTALY,wannan littafi gaba dayanshi sadaukarwa ne agareki,badan na biyaki ba sedan in tambatar miki da a zuciyar surbajo kina da guri na musammam,ina yinki tawa?*



*Dedicated to Billyn shantaly*


*4*




A daidai wani jirkitaccen gida ta sauka,da sauri ta biya me napep kudinshi ta shige cikin gidan.

Da sauri yusura ta taso daga inda take tazo ta rungume tasleem,hawaye nabin fuskarta. 


"ina fatan an dace tasleem"cewar yusura da hawaye kebin fuskarta.

Share hawaye tasleem tayi sannan tace.

 "An dace yusura,kuma kudin nada yawan da zasu isa komai da yardar Allah."

 Murmushi yusura tayi sannan taja hannun tasleem zuwa wani daki.

Wata matace kwance akan wata shimfida wacce seda na kura ido da kyau na fahimci tana numfashi.

Kanta ko kwayar gashi babu,yayinda nakai dubana jikin matar da sauri na dauke idona.

Domin ilahirin nonuwanta gaba daya a rube suke ga tsutsotsi na bin jikinta,ga wani wari kai kace mushe ne agurin.

Tana ganinsu ta miko musu hannu,idonta na zubar da kwallah,

Da sauri suka nufeta batare da kyama ba suka rike hannunta duka kukan sukeyi.

Cikin karyewar zuciya yusura tace. 

"Aunty ki dena kuka da yardar Allah zaki warke,yanzu zamu kaiki asibiti kinji"

Tasleem ce ta amshi zancen da cewa.

 "Aunty bazaki mutu ba,wallahi zamuyi iya yinmu dan ganin kin sake taka doron kasa da kafafunki"kukan da yaci karfinta ne yasa tayi shuru taci gaba da kukan.

Da kyar matar tace

 "komai zakuyi,karku zubar da mutuncinku,kada ku jefa kanku cikin sabon Allah,rayuwata tana hannun Allah Amman inada tabbacin bazan sake jimawa a duniya ba"

Tasleem jakarta ta bude ta ciro kudin da ya bata,

Dukansu ba karamim mamaki abun ya basu ba,dominko kudine har nera milyan guda.

Ana gama kirga kudin yusura ta yanke jiki ta fadi sumammiya.

A gigice tasleem ta debo ruwa tana shafa mata afuska gamida kiran sunan ta.

Bayan yan wasu mintuna  sannan yusura ta dawo cikin hayyacinta.

Cikin kuka tasleem tace.

 "inda sabo yusura ya ƙamata ace kin saba,har zuwa yaushe ne lamarinsa ze dena baki mamaki,don Allah ki kwantar da hankalinki ki taso muje da aunty asibiti"

Cikin kuka yusura tace. "tasleem duk yadda kike zaton bakin cikina ya wuce haka,ban taba ganin azzalumi irinsa ba tasleem,"

ta karasa maganar cikin kuka.
Tasleem rarrashinta ta shiga yi da kyar tayi shuru.

Mikewa sukayi suka fita zuwa bakin titi,suka kira me napep,

Shigowa  ciki sukayi suka dauki auntyn da kyar zuwa napep

Tunda suka tafi me napep din ke musu masifa akan shifa da yasan mushe ze dauko da wallahi be zoba.

Hakuri sukai ta bashi,da kyar ya hakura,

Asibitin barau dikko suka kaita.

Sede ganin farko likitan ya shaida musu wannan lamaein yafi karfinsa sede su tafi 

*AHMADU BELLO TEACHING HOSPITAL ZARIA WATO SHIKA.*

acanne kawai zasu iya bata kulawa.

Yusura kuka tasleem kuka,rasa yadda zasuyi sukayi,

Suna da tabbacin babu wani me mota daze yarda ya dauki aunty zuwa zaria da wannan tsotsotsi da warin da takeyi.

Ganin basu da mafitane yasa suka tuntubi mahukuntan asibitin game da ambulance.

Dubu hamsin suka caje su,akan inde sunaso akaita a ambulance din,

Jiki na bari,suka ciro kudin suka biya,

Koda sun biya din seda aka gama yimusu yawo da hankali sannan akasa su a motar zuwa shika.

Bayan sun isa shika,ayki jane gabansu kamin suga likita.

Duk wani kokari sunyi amman abu yaci tura.

Hakanne yasa yusura kiran daya daga cikin masu bude file,gefe tace masa.

 "malam ni yar nigeria ce,ina fatan kaima dan nigeria ne?"

 Murmushi yayi yace.

 "dan nigeria ne gaba da baya na"

Fari tayi da ido sannan tace.

 "ah to ta kwana gidan sauki,tunda yaren daya ake amfani dashi tun daga saman vila har kasa a nigeria"

Murmushi yasake yi akaro na biyu yace

 "ban fahimceki ba."

 Gantsaro kirji tayi gaba gamida sa harshe tana laso saman lebenta,sannan tace.

 "nigerianci zamuyi,inaso ne mara lafiyana taga likita yanzu,shin biyanka zanyi da kudi koko kana da dakin da zan kawo maka tsiyara,"tayi zancan cikin salon daukar hankali.

Gaba daya ya susuce yama rasa abun cewa,to abunka da dan nigerian na asali,kunsan de cikin tayin data masa dole ze dauki daya,dan haka.

Murmushi yayi yace. "Dakin na kofar kibo,ina fatan zaki iya zuwa"

Wani killer smile ta saki tace,"why not," 

Murmushi yayi yace,

 "ya sunan mara lafiyar?"

 "Maryam hashim"ta bashi amsa.

 "Me ke damunta?"ya tambaya. 

*"BREAST CANCER"*
ta bashi amsa.

Da sauri ya juya zuwa gurin bude file ya dauko ya rubuta sannan ya kira wata nurse ya bata,

nunawa tayi bazata amsa ba,dubu biyu ya dora akan file din,ay ba musu ta amsa ta shige dashi dakin likitan.

Baa jimaba aka kira su suka shiga,dan gwaje gwaje likitan yayi,sannan ya basu gado.

Muje zuwa


Surbajo for life.

????????
*KARAN BANA........*
????????


*ZAHRA SURBAJO*



*Dedicated to billyn shantaly*


*5*



Duk wani taimako daya dace shi aka mata.

Basu gama yawon yin gwaje gwajenba se washe gari da safe.

Sanda akazo wanke nonon duk wani me imani idan yagani se ya tausaya mata.

Sabida tsananin azaba har suma,tayi,su tasleem ko kai zakace jikinsu ake tabawa.

Dan yusura tuni zazzabi ya rufeta.

Bayan angama sannan ta farfado,lokaci guda gaba daya ta sake ramewa.

Allurar kemo aka mata.sannan aka sa mata karin jini.

Seda ta samu bacci sannan su yusura suka dan fita wajen dakin su sha iska.

Fitarsu kenan,sega mutumin da yusura taiwa alkawarin zuwa gurinshi.

Ya nufota yana murmushi.itama murmushin tai masa.

Yana karasowa yace.

 "ya me jikin?" 

"da sauki"yusura ta amsa.

Sannan yace. 

"to ya batun alkawarinmu?"

 Dariya yusura tayi sannan ta kara matsawa kusa dashi tace. 

"malam jiya wanne yare ma nace maka zamuyi?"

 Murmushi yayi yace.

 "nigerianci" 

"Good,to kaje ba inda zani"

cewar yusura tana dariya. 

"amman fa alkawari kikamin yazaki karya?"

cewar mutumin cikin damuwa.

 "yaren nigeria nace zamuyi,wanda kasani nasani,tun zamanin sardauna aka dena cika alkawari,dan haka ba inda zani kai gaba ko in tara maka mutane,"

 ??to @xianoxy haka ya juya jiki ba kwari,yana waigenta,yaga samu yaga rashi,dan da har abokinsa @nazeefi_bm yace ze gayyato,??????to se gashi ta bare.

Bayan tafiyar shi dariya suka kwashe da ita yusura da tasleem.

Suna nan zaune wayar yusura ta fara kara,koda ta duba me kiran.

Atm ne.

Dagawa tayi cikin muryar kuka tace.

 "baby i miss you," 

Cikin sigar rarrashi yace.

 "i know baby,kiyi hkr,ya jikin maman yake?"

 "da sauki ta bashi amsa"

Hakade yay ta kwantar mata da hankali har tai shuru.

Sallama yay mata akan ze kira anjima.

Tana kashe wayar,ta ciro wata wayar a jakarta ta sake kiranshi.

Seda ta bashi ten missed calls sannan ya dauka cikin fada yace.

 "yusura wallahi in kika kuma yimin kira irin haka se naci ubanki,bashin ubanme kike bina da zaki ajiyemin missed calls har guda goma"

Cikin rawar murya tace.

 "yaya kayi hakuri,dama jikin aunty maryam ne yay tsanani, ba kudin zuwa asibiti shiyasa na kiraka" 

"au yanzu dama sabida maryam din kike kirana haka,to kinyi na farko kinyi na karshe,shasha kawai,ni na dora mata ciwon?"

Kasa daurewa yusura tayi kawai seta rushe mishi da kuka,cikin kukan take fadin.

 "yaya kaji tausayinmu,bamu da kowa sefa kai,wakakeso muje gurinsa ya bamu"

 "kibi titi zaki samu"

ya bata amsa gamida kashe wayar shi.

Rushewa yusura tayi da kuka ta fada kan tasleem wacce tun dazu take kukan,rungume juna sukai suna kuka,me isar su.

Kiran da nurse tai musune yasa suka mike da sauri zuwa cikin dakin,

Aunty maryam ce ke aman jini har ta hanci,gunta suka nufa,a gigice,sede likitoci sun hanasu zuwa kusa da ita,sabida suna kokarin ceto rayuwarta.

Duk da halin da take  ciki haka ta dunga miko musu hannu,sede ba halin su isa gareta,sabida naurorin da suka zagaye jikinta.

Kuka suke daga inda suke sun rungume juna,suma suna mika mata,hannu,

Wayyo gidan duniya ba matabbata ba,yadda Allah yaso yakeyi asanda yaso koda kuwa ba wanda yaso.

Akan idonsu Aunty maryam ta amsa kiran Allah.

Yanke jiki yusura tayi ta fadi sumammiya,

Da gudu tasleem tai kanta tana kiran sunanta tana kuka,dole likitocin suka bata taimakon gaggawa.

Koda ta farko kuka ta rushe dashi,tana fadin.

 "Aunty kin wahala damu dashi gaba daya,se gashi shi yagaza tallafawa rayuwarki,shi wanne irin shaidanine,da baya iya tausayin na kusa dashi,me muka masa me zafi irin haka da yajanyo sanadin mutuwarki aunty"

kukane yaci karfinta kawai ta fada kan gawar aunty maryam din tana kuka me tsuma zuciya.

Tasleem ko ta gaza kukan se na zuci,shuru kawai tayi tana kallon gawar yar uwarta abar kaunarta,wacce bata da kowa gidan duniya sama da ita, 

"aunty Allah yamiki rahama yasa iya karshen wahalarki kenan,,sede aunty baki mutu banza ba wlh,inde ina da rai zan dauki fansar abinda aka miki aunty "cewar tasleem da take maganganu kamar ta zare.

Hakade suka gama koke kokensu suka biya kudin motar daukar gawa akasa gawar aunty ciki zuwa kaduna,

Kamin su isa duk sun kira yan uwa sun shaida musu dan haka suna zuwa wanka aka mata aka mata sallah,sannan aka kaita gidanta na gaskiya.

Kowa na kukan rabuwa da ita sabida mutunci da kirkinta.  

*ASALIN LABARI.*

muje zuwa.

Surbajo for life.
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 2 36,320 09-14-2018, 12:13 PM
Last Post: Gimbiya
  *KANO TO JIDDAH* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 9 111,928 09-05-2018, 06:57 PM
Last Post: Gimbiya
  *Y'ar Bautar K'asa* A Youth Corper*by Zahra Surbajo Gimbiya 1 17,110 08-10-2018, 01:58 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 18,162 07-26-2018, 12:53 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 33,643 07-16-2018, 03:44 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 13,366 06-26-2018, 01:07 PM
Last Post: Gimbiya
  *KANO TO JIDDAH* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 1 73,766 12-07-2017, 03:17 PM
Last Post: Gimbiya
  *AMANA TA BARMIN* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 42,148 11-30-2017, 11:25 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)