The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KAINUWA* by Ayusher Mohd
#1
? *KAINUWA*?
     ......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*Na Ayusher Muhd??*

*68*

  Khadija ce ta karasa ciki ta zauna sannan ta gaisheshi.
Kallanta yai yace " Khadija meye tsakaninku da yaran can?"

Kallansa tai sannan tai kasa da kai.
Yace " Khadija me kike tunani? Kinaso kicemin yaran da na tsana shi kike so? A ma bar maganar so tunda nasan dama Kina sanshi amma me kike nufi da aurensa?"

  Khadija a ranta tace " abinda nasan bazai taba yiwuwa ba kenan."
Amma a fili tace " Ya Abdulmajid."

  Cikin fada yace " kinaso ki je gidan sarauta a matsayin kishiyar Gimbiya? Sannan a matsayin matar wancan yaran?"

  Khadija ta kalleshi tace " Yaya wai me yasa ka tsaneshi da ya wa haka?bayan bai taba yima komai ba?"

Abdulmajid ya kalleta cikin b'acin rai yace " na tsaneshi, kallansa ma ba san yi nake ba, duk duniya shine mutum na farko dana tsana."

Khadija batasan sanda tace " bayan shine ya kamata ya maka wannan tsanar?"

  Yace " mene?" khadija ta kalleshi tace "Yaya please ka dinga sa ruwan sanyi a ranka, in har wannan karamar maganar ta b'ata ma rai ya zakayi in babbar magana ta doki kunenka?"

  Yace " babbar magana? Wacce iri kenan?"

Juya kai tai da sauri tace " ina dai fada ne saboda ni banga abin jin haushi a maganar ba."

Abdulmajid ya mike a zuciye yai waje ko zobon baisha ba.

Kanta ta dafe tare da rufe idanunta.
  Hisham kam yana d'aki yana cire Babbar riga Umma ta shigo bakin nan nata a washe, tace "wai ya akai ya biyoka?"

Yace " sai ki rufe bakin ai, kin wani baje baki kamar yau kika taba ganinsa.

  Kasa tai da kai tana murmushi.

  Hisham ya shiga band'aku dan kama ruwa, yana fitowa yai falo inda Abdulmajid yake.

Me zai gani?"

Ba kowa a falon, da sauri ya fito yana kiran Khadija. 
Fitowa tai daga d'aki tace " gani."  
Cikin tsawa yace " ina Abdulmajid?"

Tace ya tafi.
Yace " ban gane ba?"
Shiru tai dan batasan me zata ce ba.
Waje yai da sauri cikin tashin hankali.
Umma ce ta karaso gunta tace " Me kika ce masa da har zai tafi ba ko sallama? Yanzu khadija bawan Allahn nan bai taba zuwa fa gidan nan ba sai yau, amma ki koreshi? Ta ya ya zaki......"

Kasa karasawa tai, Khadija cikin tausaya mata tace "kiyi hakuri Umma amma ba korarsa nai ba."

  Umma tai shiru kafin tai ciki.
Khadija ta bita da kallo cikin tausayawa.

  Abdulmajid yana fita yai gida.
Har zaiyi bangarensa aka sanar dashi kiran Magajiya.
Yana shiga ya taddata a tsaye da alama yawo take a tsakar falon.
Shiga yai ya kalleta yace "Umma ga......"
Wani wawan mari da ta sakar mai ne yasa ya kasa karasawa, tace " Uban me kaje yi gidan Waziri?"

Kasa magana yai sai kuncinsa kawai daya rike yana kallanta.
Magajiya ta kara hasala tace " wato bakajin maganata ko? Na d'auka na sanar dakai ba kai ba keb'ewa da yaya? Wato shine har da zuwa gidansa ko? Ka nunamin yafini matsayi a gunka ko?"

  Abdulmajid yai shiru, tace " fitarmin daga falo, sannan wlh karka kuskura inkarama magana akan wannan zancen, na fadama."

Abdulmajid yai waje jiki a sanyaye, mota ya fada ya ja ta da gudu yai waje.

  Abu Turab na kallan sanda ya fita, ba shakka yasan Magajiya ta haushi da fada ne, a fili yace " am sry, sai dai kaima kayi abubuwa marasa dacewa wanda dolene kaima kaji ba dadi."

  Juyawa yai ya koma b'angaren sa.
Har zai zauna ya fito ya nufi bangaren Umma.

Tana zaune tana ta raba cingam ya shiga.

Yace " Umma amma dai harda 'yan katsina zaki aikama ko?"
Tace " kanaso kenan bikinka ya lalace daga biki zuwa gulma, gulmar da zata zama silar rugujewar komai."
Turab ya kalleta yace " Kina tunanin zasuyi zancen anan?"

Tace " Abu Turab kenan, bakasan mutane ba, kai a ido ne zaka ga kamar 'yan uwa ne amma a zahiri ba haka bane."
Kallanta yai sai dai baice komai ba, a kasan ransa shikansa yana san yaga 'yan uwansa.
Basira ta cigaba, kun had'u da Mai Martaba?
Yace " a'a."
Tace shikenan.
Kallanta yai cikin kulawa yace " lafiya dai ko?"
Tace bakomai.

********

  Abdulmajid kam bai tsayar da motarsa ba sai a kofar gidansu Mairo, kallan kansa yai a madubi yace " baka da inda zaka sai nan?"

  Kofar gidansu ya kalla sannan ya kwantar da kansa jikin sityarin motar ya dade a haka kafin ya tada motar yai gaba.

  Yayanta ne ya shigo lokacin taba tsinke alayahu.
Yace " Yauma kin fita kikai?"
Mairo tace " infita zuwa ina?"
Harararta yai yace " wlh ki kiyayi kanki da wulakanta mutum, mutum ma irin Yarima wanda kalma d'aya zai iya sa rayuwar gidan nan ta ruguje, tun dazu bawan Allahn nan yake waje har ya gaji yai gaba."
Baki ta tabe tace " ni bai aikomin ba dan bansan yazo ba."
Ciki yai tare da yin kwafa.
Mairo ta cigaba da tsinke alayahunta, can tace " me ya kawoshi da ranar nan? Sannan bai aiko ba?" tsaki tai tace " damuwarsa ce."

************

  Washegari kuwa Magajiya tasa aka kira mata Hisham, yana shiga ta rufeshi da fada kai kace itace uwarsa ba ma yayarsa ba balle kuma kanwa.

  Ganin abin ya zo mai wuya yasa yace " Wai Magajiya inada tambaya."
Yaran nan da kike fada akansa na waye?"

  Tashin hankalin da ba'a misaltawa.
Idanunta kadai sun isa su nuna maka tsantsan tashin hankalin da take ciki, tace " Yaya?"
Yace " kwarai ni yayanki ne, sai dai abun ya isa haka, akan yaran nan yaje gidana zaki sani a gaba da fada haka? Cinyeshi nai a gidan nawa ko me?"

  Kallan mamaki takemai yanzu, yauce rana ta farko da Hisham yake maida mata murtani.
Tace " yaya ni kake fadawa magana?"
Yace " an fada miki d'in, duk yanda naso in kyautata miki na kula bakya gani, yanzu kwata kwata kin zama sai a hankali komai fada, ina Magajiyar da na sani wacce tsoro baya cikin zuciyarta?"

  Tace " nikaina bansan meke damuna ba Yaya, sai dai tundaga sanda yaran can ya ce yasan sirrina nakejin kamar komai na rayuwata xai ruguje, yaya ka taimakeni ka kashe yaran nan da uwarsa, ni har itama banasan gani ba shi ba."

Hisham yace " in taimakeki? Duk abinda kike min?"
Tace " amma ai kai kasab burina ko? Dolene mu kawar da duk wata matsala da zata kawo mana kai akan nad'a yaran nan mulki."

  Hisham ya kalleta a ransa yace "Magajiya kenan, zanyi duk abinda kikeso saboda d'ana, sai ya hau mulki in shekaki kema barzaho."

Hannu ya saka zai murd'a kofar shiga, abinda yaji ne yasa ya tsaya cak sai jikinsa da hau tsuma saboda tsananin tsoro da razana.

  Magajiya ce ta katseshi tare da cewa " yaya."
Kallanta yai bai amsa ba.
Tace " na fasa kashe basira, mai kake gani in muka haukatata?"

  Hisham yace " hauka?"
Tace kwarai " idan muka halaka Turab a ranar auransa ita kuma sai musa a haukatata kaga sai ace rashin d'anta ne yasata yin haukar."

  Hisham ya sheke da dariya yace " gaskiya Magajiya ba digon imani a ranki, duk duniya kece mutum ta farko danasan yasan salan mugunta, ko shed'an sai dai ya sara miki."

Murmushi tai tace " ni dai yaya ka taimaken ka kyalemun yarona, wannan shi kadai ne abinda nakeson ka dashi, mu samu komai ya kammala, banasan wani abu ya tare mai hawa mulki."

  Kafafunsa ne suka kasa d'aukansa da sauri ya dafa bango, dan gaba d'aya jikinsa kaurewa yake da rawa......

*Turab*

 
? *KAINUWA*?
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

*69*

  D'aki ya koma da sauri ya shige cikin d'aki shi kadai, labulayen d'akin ya rufe duka, ya shige lungun gado ya kankame kafafunsa.
Kalaman dayaji ne suke dawo masa, a haukata Basira? A kashe Turab ranar auransa?

  Me ke faruwa? Me kunensa yakeji haka? Tsoro da fargaba sun hanashi fita, adaren ranar kuwa da zazzabi ya kwana.
Cikin dare kuwa yayi mafarkin wannan abu yakai sau nawa.

  A zabure ya mike ya shiga cikin bargo, me Umma da kawu suke shirin yi? Kisa? Duk yanda yaso ya daure ko fitowa yai ya kasa.

   Kwanan Abdulmajid biyu ko kofar gidansa bai fita ba, ya rasa menene abinyi dan abin duniya ya dameshi.

*****
Biki na ta matsowa, Gimbiya ansha gyara, gyaran da fadarsa ma bata lokaci ne, kullum Abu Turab na kiranta su gaisa.
Yau ma tsokanarta yai tayi a waya wai bata gajiya da killaceta da akai? Ba dama ko fita tai?
Sai dai tai murmushi tace " itakam bata ga wani abu ba."

  Suna gama waya ya ajiye kan wayar sannan ya kalli Sabi'u yace " ya ya irin wannan sa ido haka? Ko kishi kake ne?"

  Sabi'u yace " Gaskiya Turab da alama kanasan Gimbiya."
Turab yai murmushi yace " bai kamata in so ta ba?"
Sabi'u yace " ina na isa? Kawai dai da na d'auka kamar tursasa ma akai, amma yanzu naga kamar san ranka ne."

  Turab yai murmushi tare da mikewa tsaye yace " Sabi'u kasan menene abinda ke halaka rayuwar zaman aure?"
"a'a."
Turab yace " nunama mace kiyayya."
Sabi'u ya kwashe da dariya yace " lalai Ango da alama ka fara shirye shiryen canza rayuwa."
 Turab a ransa yace ina zaka gane abinda hakan ya jawo? Jiya da daddare ya dade yana tunanin wani abu, idan ya duba menene ya sa Magajiya ta zama tsantsar muguwa ba shakka rashin nuna mata damuwa da Sarki yai ne tun farko, wannan shine yasa take neman ta kwatarma kanta 'yanci na samun duk abinda takeso, tare da sashi ya so ta ya kuma kaskanta a gunta, wanda hakan ne ya jawo tai ta tafka kura kurai tare da kauce hanya, gashi yanzu tayi nisa wanda ta manta ma da dalilin dayasa ta cikin wannan halin tun farko.

  Ajiyar zuciya yai tare da kallansa yace " Sabi'u kenan."

************

  Gobe ne ake sa ran tafiya kano dan d'aurin auren Abu Turab, shirye shirye ake sosai da sosai, dan ma masu shirin suna Kano, masarautar kano kam ta cika ta batse da 'yan uwa na jini, na mulki da kuna na siyasa, Sarkin kano sosai yake cikin farinciki.
 Dan ana sauran kwana hudu daurin aure yasa aka kiramai Turab ya kara bashi amanar 'yar tilon 'yar tasa da yake ji da ita kamar nama d'aya a cikin miya, yayyinta ma haka sukai ta bashi amanar ta, ba shakka ya fahimci tsantsar gata da ji da Gimbiya Bilkisu da akeyi, sai dai ko ina kalma d'aya yake fad'a _Baiyi alkawarin santa ba kamar yanda suke santa ba, sai dai ya musu alkawarin kula da ita, da kuma kaucema duk abinda zai sata dana sanin auransa._

  Magajiya kuwa da Hisham sun gama shirinsu tsaf, ta rasa gane kan Abdulmajid dan sai yai kwana biyu kafin yazo gaisheta, inyazo kuwa gaisheta kawai yakeyi ya mike ya tafi, sai dai batasa wannan a ranta ba dan tana ta faman shirin yanda zasuyi gun halala Turab.

  A ranar d'aurin auransa ne Abdulmajid sai zarya yake a d'aki, mai ya kamata yai?
 Duk yanda yaso ya cire abin a ransa ya kasa, shi gani yake menene nashi a ciki? Sannan shima ai ba san Turab yake ba, sai dai gani yake kamar duk saboda shi Magajiya da Hisham suke neman halaka Turab, dan ya hau mulki ya kuma auri gimbiya, sannan su salwantar da mahaifiyarsa wanda take tushensa.
  
   Har wajen karfe takwas yana ta zarya, gashi a lokacin mutane duk sun shirya ma sunyi gaba.
 Magajiya ce ta aiko akan yai wanka yai shiri sosai na gani na fada.
 Bai musa ba kuwa ya je yai wanka, kayan data aiko mai ya saka, kaya ne masu tsananin kyau da tsada, wanda ya tabbata ankashe kudi sosai a kansu.

  Harya fita ya koma ciki tare da yanko yar takarda ya rubuta kamar haka _Ka tabbatar ka sanar ma mahaifiyarka kar taci komai yau, in har ba ita tai da kanta ba, kar kuma tasha komai._

 Fitowa yai ya samu wata baiwarsa wacce take kurmiya, ya mika mata yace taje waje ta ba yaro ya kaima Abu Turab, sannan ta tabbatar bata fadama kowa ba wanda ya aikota sannan karta bari a ganta.

  Hakan tayi kuwa, dan kurma Allah ya bashi iya rike sirri da kuma alkawari.

  Turab yana zaune, Sabi'u na ta wani fesa mai turare kamar zai juyemai kulbar a jikinsa.
 Turab yayi kyau na ban mamaki, Magajiya ta aikomai had'adun kaya sai dai bai sa ba, dan wannan Mahaifinsa ne ya aikomai.

  Dole ne in ya wuce sai ka kalleshi saboda tsantsar kyan da yai, kwarjininsa da zatinsa kadai xai sa ka kalleshi ta baya.

  Turab ya fizge turaren dake hannun Sabi'u yace " Ka bari in akazo naka auren sai ka fesa turare har a cikin bakinka ma, ba damuna zaiyi ba, amma ba ni ba."

  Sabi'u yai dariya.
Shigowar Garzali ne yasa Turab ya kalleshi yace " Garzali ba na baka kaya nace ka saka ba?"
 Kansa ya sunkuyar yace " Ranka ya dade kayan ai sunfi karfina."
 Sabi'u ne yace " Gaskiya Turab ka d'au mataki da alama Garzali ya fara daina jin maganarka."

  Da sauri Garzali yai kasa yace " Tuba nake ranka ya dade, yanzu zan saka."
 Mikamai takarda yai yace " gashi inji wani yaro."
 Turab ya amsa tare da bud'ewa.

  Abinda ya ganine yatada masa hankali, yace " Garzali ina yaran yake?"
 Yace " ya tafi."

  Turab da sauri yai hanyar waje, dafashi Sabi'u yai yace " Lafiya?"

  Turab yace " ina zuwa."

 Waje yai da sauri sai dau ba yaran ba kuma alamunsa.
 Fitowa yai ya nufi bangaren Mahaifiyarsa tana zaune kasanta mutane ne suna ta kukula Kayan robobi da su dubulan da zasu raba.

 Mairo ya gani a gefenta, alama ya mata da hannu akan tazo.
 Mairo ta mike ta fito.
Waje suka fita sannan ya kalleta yace " Mairo kina nan ai yau cir anan ko?"
 Tace " a'a anjima nakesan tafiya."
 Tai maganar fuskarta a had'e, irin wai kishin nan, balle yanda taga yasha kyau, haka kawai tana sanshi ba tun yanzu ba amma wata can a sama tazo zata aureshi...(?nace Mairo ai dama haka rayuwa take, Matar mutum...Lol) dan itakam dan Basira ma ta aika tazone amma da bazata zo ba.

  Turab ya mika mafa takardar nan, tana karantawa ta d'ago cikin tsananin tsoro tace "Yaya mekenan?"
 Yace " ban san meke faruwa ba, sai dai na tabbatar akwai abinda ake shirin yi, ki tabbatar Umma bataci komai na gidan nan ba, ko ruwa in zatasha ki sa a kawo kara daga gidanku."

  Tace " ko ruwa?"
 Yace " bazai yiwu haka ba, yanzu bari nasa amaida ta kawai gidan Abba dake cikin gari, inaji hakan zaifi sauki."
 Tace " mutanen da zasu nemeta fa?"

 Kai ya dafa sannan yace " ko waye ma yazo nemanta ace batada lafiya tana asibiti."


  Mairo tace "to."
 Yace " ta fito yanzu ba sai kin fada mata ba, kawai kice wani guri nace a rakata ta gani, zan turo garzali, in yaso in kukaje gidan kya fada mata."
 Tace to


 Nan tai ciki, sai dayaga fitar Mahaifiyarsa sannan hankalinsa ya kwanta.

 Haka suka kammala komai suka fito, sai dai jikinsa gaba daya yayi sanyi, inhar Magajiya zata cutar da Mahaifiyarsa ya tabbata ta kanshi zata fara, ya tabbatar akwai abinda take shirin yi masa.

  Kansa ya dafe, da alama yayi sakaki da sharrin Magajiya, ya yi sake dayai tunanin bata isa yi masa komai yanzu ba.
  Abdulmajid yana kallansa a tsaye, cikin mutane suna ta gaigaisawa, sai dai ya tabbatar shima abin na damunsa, dan murmushin da yakeyi inka kula da kyau iya l'abansa suke basu kai har zuciyarsa ba.
  Ya tsani yaran can, amma me yasa yakeji bazai iya bari a kashe shi ba?
 
 Kai ya girgiza yace " ba wai saboda shi bane, ni raine bazan iya gani a d'auka ba, Allah ne kadai ya isa yin wannan."

  Cikin isa yazo ya wuce ta gun Abu Turab ko kallansa baiyi ba, shima Abu Turab ganin haka ya juya mai baya, Abdulmajid na zuwa ya bud'e had'adiyar motar Sarki wanda ya bada dan tafiyar Ango ya shiga.

  Sannan ya kallu mai tukawar yace " mu tafi."
 Kallansa yai yace " Ranka ya dade amma ai....."
 Katseshi yai cikin fada yace " ina sasa dakai? Ko kanasan yanzu insa a kulleka?"

  Da sauri ya shiga motar ya tada.

  Yai gaba, Turab yana kallan sanda Abdulmajid ya shiga sai dai bai d'auka tafiya zaiyi ba.

  Ganin sunyi gaba ya bi motar da kallo, lalai Abdulmajid, wannan kuma wani sabon wulakanci ne?"

 Sabi'u ne ya kalleshi yace " kaga mai ya faru?"
 Turab yamai alama da hannu yace " yai shiru kar aji, ba komai shi ya tafi a motar sa."
 Sabi'u yai kwafa yace " amma wancan anyi mara mutunci wallahi."
 Turab ya wuce ya shiga motarsa sukai gaba.

 Tafiya suke sai dai gaba d'aya hankalinsa ya kasa kwanciya.

 Me Magajiya take shirin yi? Yayi niyyar zuwa gunta kafin ya fito sai dai bangarenta taf yake da mutane.

Abdulmajid kam tafiya kawai sukeyi su biyu a mota, ya tabbatar duk wani abu da zatayi daga kan hanya zata yishi.

  Sunyi nisa da tafiya wajen jeji kawai sukaga an tare gabansu.......


*TURAB?*

 ? *KAINUWA*?
     ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

  *70*

   Motar suka kalla da kyau da yanda aka nuna musu suka tabbatar itace, tsaida motar sukai ta hanyar tsayawa agaban titin tare da manyan sanduna da makamai.

  Tsoro ne ya shiga jikin Abdulmajid l, shikansa driver din ya tsorata sosai.
 Katon cikinsu ne ya bud'e motar ya cillo da driver din waje shikuma ya shige ciki.
 Nan yaja motar sukai gaba, can cikin wani daji suka shiga dashi.
 Abdulmajid ya kasa magana sai tsantsar fargaba dake damunsa, me ya kaishi? Amma dagaske su Umma abinda sukai shirin yima Abu Turab kenan? Lalai shikam yasan kwanansa ya kare, ashe bazasuyi sallama da Maironsa ba zai tafi kabari, dan tunda yaji wannan maganar a d'akin magajiya bai ko kara zuwa yaga Mairo ba.

   Sai da sukai tafiya mai nisa sosai, wani gida ne kwaya d'aya a tsakiyar dajin, gida ne karami, mutumin ya tsaida mota ya bud'e bayar motar ya fizgo Abdulmajid.

  Yana shiga ya cillashi ciki da karfi, jikake gum, ya buge, jikinsa ne ya shiga rawa ganin ba imani ko kadan a idan wannan mutumin, jawo kofa yai ya rufe, bai dade da fita ba yaji karar wata mota da alama ragowar ne suka iso dan ihu yaji sunayi kamar tab'abu.

 Tsoro ne ya kara shigarsa, idanunsa sun firfito da tsananin tsoro.

 Jiyai an banko kofa da karfi suka shigo.
 Ogan cikinsu ne yazo inda yaje ya d'aga sanda ya makamai a kafa da karfinsa.
 Wani mugun kara Abdulmajid ya saka wanda sai da dajin yai kara, tsananin azabar dayaji je yasa yasan anma kafarsa illa babba.
 Zufa ta ko ina take ketomai, hawaye ne ke zubomai sosai saboda rad'adi so yake ma yace musu su kira wanda yasasu aikin dan ba shi bane amma ina...Azaba ta hanashi magana sam.

  Murkususu yakeyi, ogan yasa dariya yace " ance mu wahalar dakai kafin mu shekaka bar zaho."
 Suka tuntsire da dariya......

**********

  A motar Abu Turab kuwa tafiya suke amma gaba d'aya hankalinsa ya kasa kwanciya, sai dayaga sun isa kano sannan yaji ya d'an samu sauki kadan a ransa.

  Yana isa ya tadda masallacin masarautar nan taf take da jama'a, sai kiranshi ake suna gaisawa da mutane.

  Har Saif ya gani a gun taron, sai dai kallo d'aya yamai ya d'auke kai yai kamar bai ganshi ba.
  Yanda Hisham yai a sanda yaganshi yasa yasan da wani abu, kusa da Hisham ya karasa yace " Waziri lafiya?"

  Shidai Hisham yana bayan motar sarki kadan, saboda dama anyi daga zarar motar ta fito tayi gaba sai ya bisu a baya, yana kallan aka cilar da driver din sannan wanj ya shiga yaja motar, sannan yayo gaba.

 Kallan Turab yai a razane yace " motar Sarki ba a ciki ya kamata kazo ba?"

 Turab yace " a ciki ne amma Abdulmajid.........."

 Yanda yaga idanun Waziri sunyi ne yasa ma ya kasa karasawa, kallansa yai yace " ya akai kasan a motar sarki zanzo?"

  Hisham kam baimasan me yake cewa ba shidai juyawa yai da sauri zai fita.
 Turab yasa hannu da sauri ya riko rigarsa yace " ina Abdulmajid?"

  Hisham ya gama rikicewa kai kawai yake girgizawa.
 Turab yace " ina Abdulmajid?"
 Hisham ya fizge rigarsa yai waje da gudu.
 Sabi'u ya taba yace " yi sauri kabi Waziri kaga ina zaije." nan sabi'u yai waje.

 Turab nan ya dunga kutsawa cikin mutane yana neman Abdulmajid sai dai bashi ba labarinsa.

  An d'auran Auren Gimbiya Bilkisu da Yarima Abu Turab a ranar Asabar da misalin karfe goma sha d'aya na safe, a massalacin dake gidan sarki na kano.

  Abu Turab kawai dai yake yakeyi amma gaba d'aya hankalinsa baya jikinsa, meke faruwa?

  Hisham kam mota ya shiga ya dinga zabga gudu, sabi'u na bayansa yana ta binsa, a ransa yace " ko dai zariya zai koma?"
 Har yai tunanin juyowa ganin suna ta tafiya ba tsayawa, gani yai ya gangara ya sauka daga kan titi ya nufi wani lungu cikin daji.

 Tsayawa yai yana tunani kafin ya ajiye motar ya fito yabi bayansa cikin dajin, dan ya tabbatar inyashiga da mota hisham zai ganshi.

  Hisham na isa wannan d'an gidan ko kofar motar bai rufe ba ya fito cikin hanzari.

  Buga musu kofa yai tayi da karfi sai dai ba alamar kowa a ciki.
  Ya gama rikicewa gaba d'aya dan ya gama sadaukarwa an gama kashe mishi d'a, zama yai a waje kawai yasa wani irin kuka.

  Sabi'u ne ya karaso duk ya gama gajiya, hango gidan dayai ne yasa ya tsaya, Hisham ya gani a zaune yana baza wani irin kuka.

 
  Boyewa yai jin shewar mutane, Hisham na jinsu ya taso a zabure ya cakumi wuyan ogan cikin su yace " ka kasheshi ko? Ka kashemin d'ana ko?"

  Ogan ya kwace rigarsa yace " Malam me kenan? Kai kabamu kwangila sannan yanzu meye na zuwa mana da wannan zancen?"

 Hisham cikin karaji yace " Abdulmajid kuka kama ba Abu Turab ba."

  Kallansa sukai sukace " anma ai shine a cikin motar."
 Hisham a rikice yace " bud'e min kofar, kun kasheshi ko?"

  Bud'e kofar sukai, da sauri ya shiga ciki, yanda yaga Abdulmajid a yashe yasa ya gama rikicewa, cikin tsoro ya karasa gunsa, durkushewa yai a gub yana kuka sosai yace " najama kaina masifa, na kashe d'ana na cikina da kaina saboda wani buri nawa na shirme, nikam na shiga uku na...."

  Oga ne ya matso yace " tab amma Allah ne ya kiyaye dan har naso mazgemai wuya nai tunanin barinsa zuwa anjima, ba shakka da anyi tsiya."

 Hisham ya kalleshi a tsorace yace "kana nufin yanada rai"
 Sosai ma sai dai kafarsa d'aya banaji zatai aiki.
 Abdulmajid dake kwance yana fitar da numfashi sama sama kalaman Hisham suka daki kunuwansu, d'ansa?na cikinsa? Sai dai ba wani abu da zai iya yi dan ko magana ya kasa yi saboda dukan da sukai tamai da kafa.

   Hisham ya d'ago Abdulmajid ganin yana numfashi yasa yace su taimaka mai ya sashi a mota.
 Nan suka fito.
Ogan yace " Kayi hakuri yallabai, yanzu ya za'ai mu kama d'ayan?"

 Hisham ya buga musu kallo yace " ku tabbatar kun bar garin nan kafin wani abu ya faru, ai dama na gama biyanku kudinku.

  Nan ya shiga mota.

 Sabi'u na kallansu, Abu Turab sukaso kamawa kenan su halaka? To ya akai Abdulmajid ya shiga motar? Da alama yasan da shirinsu kenan?

  Lalai mutanen nan basuda imani.

 Sai da Hisham yai gaba sannan shima ya fito, ya fita ya shiga mota, har zaiyi Zariya sai ya koma Kano.

  Abu Turab yana cikin jama'a bayan an gama aka shiga cikin gida dan yin walima wacce yayun amarya suka shirya musu.

 Suna gamawa ya fito kenan sai ga Sabi'u.

 Da sauri ya matsa gunsa yace " ya ya?"
 Sabi'u yace " Abdulmajid suka kama sun d'auka kaine, da alama Waziri ne yasa a kamaka."

 Turab ya shaka fuskarsa da hannu biyu, ji yai idanunsa sun ciciko, mai yai wa mutanen nan, mai ya tsole musu a duniyar nan, duk abinda yaji game dasu, mahaifin Khadija? Magajiya? He will never forgive them, kallan Sabi'u yai yace " ya jikin Abdulmajid din?"

  Sabi'u ya girgiza kai yace " da alama ba dadi abin dan naga kaishi mota akai."

  Turab ya d'aga kansa sama saboda hawaye dake neman zubomai, sannan ya kalli Sabi'u yace " Da alama yasan abinda suke neman aikatawa, how can i forgive those people?"

  Duk yanda yaso ya kore abin saj da hawaye ya zubomai ta kwaryar idanunsa, Sabi'u ya dafashi yace "Amma dama haka kake rayuwa cikinsu?"

 Turab yai wani murmushin takaici sannan ya cije lab'ansa, wato su sukai su kasheshi sai su ba Basira magani suce hauka take saboda na mutu? Tabbas sai yanzu ya had'e puzzle din.
  

  Hannunsa ya dunkule kai kace wani zai kaima naushi...........

 Nikam ina ganin haka nai waje da gudu dan na d'auka ni za a make dan yanda naga idanun turab? Ba sauki......


*Turab*
? *KAINUWA*?
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*


*71*

  Magajiya kam tana zaune cikin mutane anata hidima, sai dai ta rasa gane kan dalilin dayasa akace mata wai Basira bata gidan, aikenta uku amma duk maganar d'ayace wai bata nan, ba haka taso ba lalai d'an iskan yaran can ne ya d'auke ta, to menene dalili? Inta tuna haka sai tai dariya tace " bakasan gani na karshe zaka mata ba.
  Kowa yazo sai ya yaba kyan datai, saboda tsananin kyan datai, ga wani annashuwa da jin dadi dake fita daga fuskarta, tasha kwalliya, tasha lalle,hmmm abin ba a magana farinciki biyu take jira a kawo mata, na mutuwar Turab dana auran Abdulmajid da Gimbiya, taga uban da zai nemi kwace mulkin d'anta.

  Aikowa akai akan Waziri nasan magana da ita, tace " a sanar dashi ina cikin taro, dan itakam ta san me zai sanar mata. Dama kuma abinda take jira kenan."

 Sau biyu yana aikowa akan yana nemanta daga karshe tace " wai akan me tana cikin taron mutane zai dinga aikawa tazo?"

  Murmushi tai a ranta tace " nafisan in zan fita anjima infita da kukan mutuwar d'ana Turab.
 Jin haka ne yasa Waziri yaga in ya biyema jiran Magajiya d'ansa zai karasa, fitowa yai ya ja mota ya wuce asibitin ABU Gun abokin Mai Martaba.

  Cikin tashin hankali da tausayawa aka shiga dashi cikin emergency.

*********

  Tana zaune akan kujerarta
  Sai da sukai ta sallama da mutane sannan aka barshi ya taho.
 A hanya addu'a kawai yake akan Allah yasa ciwon Abdulmajid ba mai lahani bane, motar tasu tsit har suka isa kamar ba motar Ango.
 Suna isa ya fito bai bi takan masu mai busa ba yai bangaren Magajiya.

  Yana shiga aka fara gaisheshi, ganin gidan a cike taf yasa ya rasa yanda zaiyi, ga shi mata ne fal, juyawa yai ya fita tare da dafe kansa.

 Kallan Sabi'u yai yace " muje gidansa, da alama ba nan yayo ba, dan ba alamar sun san wani abu."

  Nan yai waje, sunje gidan Waziri  tare da sanar da masu kula da kofa akan neman sa da suke yi, nan suka sanar dasu ai baizo ba.

 Turab yace " muje gun Umma in sanar da ita sai mu shiga duba asibiti, dan na tabbatar tunda aka kaita wannan gidan a tsorace take."

  Nan sukai gidan Mai martaba na cikin gari.

  Mairo tana cire mata lalen data mata suna yar hirarsu sama sama, sukaji sallamar Turab.

  Wani lallausan murmushi ne ya bayyana a fuskar Umma dan ba shakka zuciyarta a d'arare take, Mairo ma ta mike tare da d'auke robar lalen.
 Turab ne ya shigo ya kalli Mairo cikin jin dadi yace " kanwata ina godiya sosai."
 Murmushi tai tare da sunkuyar da kai.
 Umma ta kalleshi tace " Alhamdulila, sai yanzu hankalina ya kwanta."

 Turab ya zauna tare da cewa " umma ke sai yanzu kikai lalen bikin?" ya fada yana kallan Mairo ta gefe.
 Fuska ta hade tace " itadai Umma lalle tai ba wai na biki ba, ko Umma?"
 Basira ta d'aga kai tace " ina na isa yin lalle abikin Turab ai ni bikinki ne kadai zanyi Lalle Mairo."

  Mairo tace " yauwa Umma." ta juya tai waje.
Turab ya kalli Umma yace " Umma kin tsorata ko?"

 Kai ta girgiza alamar a'a tace " Turab taya zan tsorata akan abinda nasan kana da dalili na aikata shi?"

  Murmushi yai sannan yace " Umma da matsala Amma."

  Tace " tame kenan?"

 Mairo ce ta d'auko mai lemon zubo da tai tare da abinci, tana kokarin shiga taji yana cewa " Abdulmajid inaji yana asibiti."

 Basira tace " mene?"
 Turab ya kwashe komai ya sanar da ita.

 Idanu ta runtse tashiga fadin Inalilahi wa ina ilaihi raji'un.

 Mairo kam jikinta ne ya shiga kakkarwa, daurewa tai tai sallama.
 Turab ya amsa tare da juyowa.
 Ajiye tiren tai ta mike zata fita.
 Turab ya kalleta, yana kallanta ya fahimci taji me yace, nan yace mata "Abdulmajid na asibiti."


 Kanta na kasa tace " Me ya dameni Yaya? Fatan sauki ne namai Allah ya bashi lafiya."

 Mikewa tai ta fita.
 Turab ya mike ya biyota tana kokarin shiga kitchen yace " kin tabbatar bai dameki ba?"

 Kai ta d'aga mai sannan ta shiga ciki.
 Kallan Umma yai wacce gaba d'aya komai ya mata zafi yace " Umma karki damu yanzu zanje mu duba inda yake."

 Basira tace " ka cire babbar rigar."
 Nan ya zareta sannan yasa akan kujera."
 Tace " abincin fa?"
 Kai ya girgiza yai waje.

 A kofar kitchen din ya tsaya, Mairo ya kalla tana tsaye ta juya baya, ba abinda take a kitchen din, da alama tunani take.
 Yace " Mairo zo ki rakani."
 Kallansa tai tace " ina?"
 Yace " neman Abdulmajid."
 Tace "ni kuma meye nawa?"
 Turab yai murmushi yace " wai dole ne sai an nunamin akwai dakakkiyar zuciya? Bayan ni ina ganin rauninta?"

  Mairo ta juya kai, yace "wuce muje."

 Fitowa tai tasa takalmi suka fita.
Sabi'u na cikin motar turab ya shiga gaba.
 Ita kuma ta bud'e baya ta shiga.

  Sabi'u ya kalli Turab ya kuma kalli Mairo ta madubi sai dai baice komai ba.
 Turab yace " mu fara da asibiti babba ko?"
 Sabi'u yace " ni nasan ma yana ABU dan shikadai ne asibitin da zasu(?nace da wannan lokacin ne da bakace haka ba, yanda asibitoci sukai yawa.)"

 Turab ya jinjina kai.

  Sun isa asibitin ABU, suka nufi emergency, Mairo tana tsaye bakin kofar shiga, gabanta ne kawai ke faduwa, wanda ita kanta batasan dalili ba.

 Can suka hango Hisham, Sabi'u ya taba Turab tare da nunamai Hisham.

 Nan suka nufi gun.

  A kwance yake kamar mai baccu sai kafarsa da aka gewaye da katako, kallo d'aya zaka ma gun ka fahimci karayace a gwiwarsa sannan ga bandage da aka nad'e kasan gwiwar dashi alamar ciwo, duk fuskarsa ma an masa dressing guri guri.
 Hisham kam kallan Abdulmajid kawai yake ya baza tagumi.

  Turab na isa gun ya kalli Hisham cikin b'acin rai.
 Baimai magana ba ya kalli wani nurse dake gun yace " ya jikin shi?"

 Yace "duk an gyara ciwokan da kuma karayar yanzu ma d'aki za'a maidashi dan neman samun sauki, saboda Director yace kar a barshi anan."

 Turab yace " to."
 Nan suka turo gadon.

 Ta gabanta sukazo suka wuce, gaba d'aya jitai komai na jikinta ya dena aiki, kana kallansa kasan yana jin jiki sosai.

 Binsu kawai take har suka isa d'akin, a baya ta tsaya ganin d'akin da suka shiga.
 Hisham na kokarin shiga turab ya tare kofa tare da kallansa.
 Yace " Waziri mai kake anan?"
 Hisham ya bishi da kallan mamaki, wannan wace irin tambaya ce? Ya kawo yaro asibiti amma a tambayeshi me yakeyi anan?"
 Turab ya kara cewa " waziri mai kake yi anan?"

 Hisham yace " bam gane ba?"

 Turab yace " saboda tsaro da kuma yin bincike na ke sanar dakai abu d'aya in har kanasan kaga Abdulmajid sai ka bi abinda nace."

Mamaki ya hana Hisham magana, Turab yai wani murmushi yace " ko kana tunanin bansan ni kukaso a ma illa ba?"

 Gaban Hisham ya yanke ya fadi.
 Turab yace " kaje gidanka yanzu, ka jirani zuwa gobe."
  Hisham samun kansa yai da cewa to, ya juya yai gaba jikinsa a sanyaye, yanayi yana waiwayen kofar.


  Kallan Abdulmajid Turab yai, ya dade yana kallansa, tsananin tausayinsa ne ke ratsashi gashi duk jikinsa ciwuka banda karaya, kamar ba shiba sam.

 Turab ya kalli Sabi'u yace " zo muje gun likitan."
 Sabi'u yace " karkuma abarshi shi kadai."
 Kallan Mairo Turab yai da take rakube a gefe yace " akwai wanda ahi kansa mara lafiyar yafisan ya gani."

 Bai fahimta ba sai dai ya gane akwai wanda zai zauna har suje su dawo.
 Sai da sukazo inda taks Turab yace "ki shiga ki duba shi."

 Sukai gaba.

 Mairo a hankali ta tura kofar d'akin ta shiga.

  Jikin gadon ta karasa sannan ta kalli fuskarsa, gaba d'aya an mata faci.
 
  Fuskar ta kurama ido tana tuno abubuwan da suka dinga shiga tsakaninsu.

  Sam bata san sanda hawaye suka ciciko a idanunta ba, a hankali wasu siraren hawaye suka gangaro kan fuskarsa.

  Jin ruwa a fuskarsa ne yasa ya dan motsa idanunsa kadan, a hankali ya bud'e idanunsa da suka kumbura idanunta a rufe suke, yana kallanta ya maida idanunsa ya rufe.

 Ina ya isa ya kalleta a cikin wannan halin? Ba ma wannan halin ba, ina ya isa yi mata magana bayan bai gama sanin wanene shi ba? Menene matsayinsa? 

  Idanunta ta bud'e a hankali sannan ta juya baya, tare da zama akan kujera, itadai so take ta karyata zuciyarta akan kukan nan tayine saboda tausayin d'an Adam ba wai saboda wani Abdulmajid ba.

  Shikam ji yake inama ba wani babban sirri agabsa yaga Mairo tana nuna damuwa haka a gabansa? Meke shirin faruwa dashi?
 Wasu zafafan hawayene suka gangaro ta gefe idanunsa.



********

 A can kuwa Magajiya takaici ya isheta, har yanzu busa takeji da wasanni a gidan sarauta bata fara jin koke koke ba.



_TURAB_

 ? *KAINUWA*?
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

*72*

   Turab ne ya kalli likitan sannan yace " kana nufin kafarsa bazata dawo dai dai ba?" 
Kansa ya girgiza alamar a'a yace " ba wai bazata dawo daidai gaba d'aya ba, sai dai dawowarta daidai din abu ne mai wahala, a yanzu inya warke zamu had'ashi da sanduna dan taimaka masa gun tafiya, idan har Allah yayi sai kaga a hankali kafar ta warke in yana samun kulawa."  

  Turab yai godiya suka mike, kallan Sabi'u yai bayan sun fito yace " Sabi'u muje ka kaini gida, sai ka d'auko Khadija ka kawo asibitin ta zauna jinyarsa, ni akwai abinda zanyi."

  Sabi'u yace " wacce muka kaifa?"
Turab yai murmushi yace " kana tunanin zai sake a gun yarinyar da yake so?"

Gaba yai daga fadar haka, mota suka shiga ya kaishi gida, akan inya d'auko Khadija sai ya maida Mairo.

  Magajiya kam ana zaune a waje dan an fito waje wajen wani had'aden kwalliya ta sarauta da aka zagayen gun dashi, matane manya ke ta kid'an kwarya na ruwa, sai gaishe gaishe akeyi.

  Turab yana shiga ya wuce bangarensa wanda yanzu komai nashi an kwashe daga bangaren, wanka yai sannan ya bud'e drawer da ya ajiye wata shadda a ciki dan dama ya ajiye ne saboda zuwa bangaren Amarya da ita, jawota yai tare da kallan d'ankwalin daya biyo bayan shaddar.

  D'ankwalin Khadija ne, sawa yai a aljihunsa dan yau zai maida mata d'ankwalinta, inhar ya maida mata kuwa to yana nufin komai na alakar dake tsakaninsu ta tsaya kenan.

  Fitowa yai daga bangaren, rawani yasa akamai, sannan yasa a d'aukomai dokin da Sarki ya bashi.

Had'aden dokin da mai martaba ya bashi ya hau, yasha ado na ban mamaki, Turab ya hau kai sannan ya nufi inda ake ta mai hawan dawakai.

  Yana Isa masu busa suka canza salan busarsu aka saki wani kiraki.

  Magajiya tana zaune labari ya iso mata na hawan da Ango yake yi.
Kallan yan aiken tai tace " Turab ne?"

Sukace sosai ma, duk da dai rawanun dayai bazai bari mu tabbatar shi bane amma ai kowa yasan Ango ne.

Tsaki tai a ranta tace " zancen banza kenan, Ango? Ai Abdulmajid ne angon."  

  Yana gama hawa dan ba dadewa yai ba ya nufi inda Magajiya take.

Aiko mata akai akan d'anta yazo kwasar gaisuwa.

Murmushi ta saki tace " ace ya shiga ciki ina shigowa."
Nan aka sanar ma Turab.
Ciki ya shiga ya samu guri ya zauna.
Magajiya ta mike cikin yauki ta nufi ciki.
Murd'a kofar tai ba tare da ta kula ba saboda bayansa ya juya tace " Ango kasha kamshi, dafatan yanzu ka hakura da aura........."

  Juyowar da Turab yai tare da cuge rawanin ne yasa ta tsaya cak da maganar, jitai wani abu tundaga tsakiyar kanta har kafarta.

  Turab ya tako cikin isa ya karaso inda take, hannu yasa ya tura kofar d'akin data rike da karfi bai cire hannunsa daga kai ba yace " Kina mamakin ganin wanda ya kamata ya mutu ne a tsaye a gabanki?"

Magajiya ta kakaro murmushi tace " me kake nufi? Kaine Angon mana, ko akwai wani aure da akai da ban sani ba?"

  Turab ya girgiza kai yace " ina fa? Ai ni kadai ne a gidan nan aka d'aurama aure yau sannan aka Wani asibiti."

Magajiya tace "asibiti kuma? Me kake nufi?"

Turab idanunsa ne suka canza kala ya juyo ya kalleta yace " sa mayafi mu fita."
Tace " mene?"
Yace " abinda kikaji shi zakiyi."

Wata muguwar dariya ta saki tace " mene?kai harka isa ka sani nayi abinda banyi ra'ayi ba?"
Murmushi ya mata yace " daya wannan lokacin kuwa duk wani abu danai ra'ayi shi xakiyi."

Ranta ne ya baci matuka ta d'aga hannu zata wanka mai mari.

Jitai yace " Ya Abdulmajid zai ji in yasan kece kika sa aka kusa kashe shi?"

  Hannunta ta tsayar kusa da fuskarsa, tace " Abdulmajid? Me ya sameshi?"
Turab yace " me ya sameshi? Yana kan gadon asibiti numfashi ma banaji yanayi, ko kin manta ke kika sa a kasheni? "

  A rikice tace " to meya kawo Abdulmajid ciki?"
Turab yace " wannan kuma ke zan tambaya, ya zakiyi? D'an da kike gwagwarmaya a kansa gashican nufashinsa na neman d'aukewa."

Wani irin ihu ta saka ta kama kwalar rigar Turab tace " kana nufin d'an nawa ba ma tabbas ko yana da rai?"
Turab yace " ke nake jira muje ki ganshi kafin mu mikashi gidansa."

  Wani irin ihu ta kara sakawa tace " kai har ka isa? Waye ya baka damar cewa d'ana numfashinsa na neman yankewa? Amma ban taba ganin mutum mara imani irinka ba, d'an nawa ka tura a ka kusa kashewa?"

  Turab yai dariya yace " mara imani? Na tura? Magajiya na kasa fahimtar wa kikema inkiya a wannan maganar, ko kinaso kicemin Waziri shi kadai yai abin ba tare da kin sani ba?"

  Magajiya ta kalleshi tace " Hisham? Eh shine yasa akai komai, ni meye nawa na neman ganin bayan rayuwarka?"

Turab yai wata dariya yace " dama ta ina zaki yadda kece sila bayan ni nasan wacce ke? Duk abinda Hisham ya miki kenan kanki kawai kika sani?"

  Fuska ta had'e tace " bugar cikina kazoyi kenan?"

Turab ya bi kwayar idanunta da kallo, tace " me? Akwai wasu daka b'oye a d'akin nan? So kake kaji me zan fada?"

Turab yace " me kike san kice?"

Tafin hannunfa ta d'aga tace " ka san me yasa muke da zane kala kala a hannun mu?"
Yace " kwarai, kissa ta biyo akan mata ne lokacin Annabi Yusuf......"

  Ta matso kusa dashi sosai yanda shikadai zai iya jin ke take cewa tace " mata ko? Amma tunda kasan wannan kissar kasan me matar da ta sasu tai ko?"
Kallanta kawai Turab yake, tace " mace aka ce, ni kuma a matan ma dabamce. Sharri na da sanin duniya da nai ko rabinta bakai ba, kai baka isa ka shiryamin ramin da zan afka ba."
Hannu tasa ta ture hannunsa ta bud'e kofa tai waje.

  Turab ya ciji lab'anbansa.
Mahaifinsa dake jikin d'ayan d'akin ne ya fito.
Bazaka taba cewa sarki bane dan Shadda ya saka ba rawani a kansa sai hula, shida Sabi'u ne.
Abdussamad ya matso ya dan daku kafadar Turab yace " ya kafadar jarumin d'ana zata yi kasa?kana tunanin daga bugun farko zakasa magajya tai kasa? Da daddare naje naga jikin nasa, sannan mayi maganar abinda ke faruwa a hankali, yanzu in aka kula na dade bama fada za'ai zargin wani abu."

Turab yace " Tuba nake."
Sarki yai murmushi yace sannan yai waje.

  Turab ya tuno plan dinsa.
Sanda Sabi'u zai tafi d'auko Khadija ya sanar dashi akan in har yanasan ganin d'ansa to yaje ya sanar da Sarki akan Magajiya na san ganinsa ganin gaggawa dan da matsala,  saboda shi a ka'ida bai isa yaje fada yasa mahaifinsa tasowa.
Idan mahaifinsa yaji haka ya tabbatar ransa zai baci, sai dai bai isa nunawa ba saboda girmama matarsa kuma uwar gida.
To in ya fito sai Jakadiya ta sanar dashi shigar burtu.
To yasan mahaifinsa inyaji haka yasan Turab ne ya shirya wani abu.
Ita Jakadiya zatazo bangaren magajiya ta tabbatar ta sa mutane sun fita gun kida da wayau, shikuma Sabi'u yana dawowa sai ya taho raka sarki yanda ganinsu tare bazai sa mutane susan sarki bane.

Turab ya kalli Sabi'u yace " da alama nayi gaggawa akan yin plan dina, bazata taba yarda ta a sake fooling dinta twice ba."

Sabi'u ya girgiza kai yace " wacce kake yi da ita ne tafi karfin plan din bawai kayu gaggawa ba."

Turab ya shafi kansa yace " ka kai khadijan?"
Yace " eh, na kuma maida Mairo gun Umma."

Turab yace " nagode."
Sabi'u yace " gobe fa Amarya zatazo haka zaka tarbeta jiki a sanyaye?"

Turab yai murmushi yai waje.


*********
Magajiya na fita tai bangaren Abdulmajid tasa a kira mata Hisham.

Gabanta sai faduwa yake ba kakkautawa, inka kula da hannunta ma rawa suke yi.
Yana shigowa ta taso a rikice tace " Me ya samu Abdulmajid?"

Hisham yace " tun yaushe nake aikawa kizo?"
Tace " meya sameshi?"

Hisham yace " yana asibiti gun Turab."

A rikice tace "wani irin hauka nakeji haka?"
Ganin baiyi magana ba cikin tsawa tace " uban waye ya dakarmib d'a? A kuma wani dalili ne zai kasance gun Turab??"




*Turab*

  
 ? *KAINUWA*?
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

*73*

    Ta gabansa ta wuce a zuciye tai waje.
B'angaren Turab ta nufa, ba kowa a bangaren sai mai kula da kofa, gaisheta yai ya sanar da ita ai ba kowa a nan.
Juyawa tai hankalinta a tashe, ina ya kaimata d'anta? Itakam mai makon wannan ranar ta zama ranar farin ciki yau kam wannan ranar ta gama zame mata ranar bakin ciki.

  Ga magrib ta kawo kai.....

***********

  Duk yanda Khadija taso da ya bud'e ido amma inaaa, ya kasa,yana kwance idanunsa a rufe, itakam gani take kamar baya haccinsa, sai dai shikam bayaji zai iya bud'e idanunsa yaga maike faruwa a wannan duniyar, bayasan ya bud'e idanunsa yaji abinda kwakwalwarsa bazata iya d'auka ba.
Khadija zama tai a gabansa duk ta rame a 'yan kwanakin nan dan itakam sam yanzu rayuwar bata mata dadi, tace " Yaya ka taimaka ka farka."

A can gidan Barde kuwa kwance take a kan gado banda juyi ba abinda takeyi, ta rasa menene ya hanata bacci, ta dade tanata juyi ta gaji ta mike zaune tare dayin dogon tsaki tace " Allah ya isa? Wannan wace irin muguntace? Haka kawai ku samu mutum ku hau dukansa ba gaira ba dalili?"

Ahh ashe fa akwai dalili tunda Ya Turab akaje daka shi kuma ya shiga motar?
Hannu tasa akan kirjinta tare da turo baki gaba tace " Allah sarki, ashe mutumin nan nada tausayi, sannan zuciyarsa ba wai mara kyau bace duka, me yasa muka kasa gani?"
Ajiyar zuciya tai ta tuno sanda take mai rashin mutunci shi kuma yake nuna ba komai, batasan sanda ta sa murmushi ba, tunowa datai yanda ta ganshi a kan gado yasa jikinta yai sanyi.
Idanunta ne taji ya ciciko, da sauri ta kwanta taja bargo ta rufe duka har kanta.

***********

   Mai Martaba ne ya kalli Turab yace " ya akai Abdulmajid ya kasance cikin wannan halin?"
  Turab ya kalli Abdulmajid da ke kwance yana bacci, karfe shida da rabi ne na safe dan ana sallar asuba suka taho shida Mai Martaba.
Khadija na kwance akan sallaya rike da karamin kur'ani izu biyu da alama tana karatu bacci yai gaba da ita.
Yace " Tuba nake ranka ya dade amma ni akaso halakawa."
Sarki ya kalleshi yace "Shi kuma yaji kenan?"
Turab ya d'aga mai kyai.
Idansa ya runtse kadan sannan ya juya.
Turab yace " Abba bazaka shiga ba?"
Kai ya girgiza yace " kana tunanin zaiso gani na? Ko kana tunanin zai so ganin kowa? Bayan yaji da kunnensa mahaifiyarsa na neman yin kisan kai? Me kake tunanin yana ayyana wa a kwancen nan da yake?"
Turab ya kalli Andulmajid cikin tausayawa.
Sarki ya kamo hannun Turab yace " Abu Turab!"
Turab ya kalleshi sai dai bai amsa ba.
Sarki cikin wata irin murya yace " na girma, sannan ko ban girma ba haka na taso a rayuwar auranmu da barin Magajiya taci galaba akan dukkan lamuranta, saboda bata taba barin evidence dazai nuna tabbas itace ta aikata abu, sannan inba wanda ya san halinta ba ba wanda zai yanda akan abin da zata iya aikatawa, ina rokonka daka taimakama wannan mahaifin naka ya aiwatar da babban harkar shari'a ta gaskiya na karshe akan gadon mulkinsa, ka kawomin hujjojin da zasusa Magajiya ta fuskanci hukunci akan mayyan laifukan da ta aikata, wannan shine babban burina da ya ragemin a duniya in hakan ta faru inaso inyi murabus in baka mulkin nan, in d'auki mahaifiyata da matata mu ziyarci ka'aba dan ziyarar d'akin ma'aiki sannan mu jira sanda in karasa rayuwata cikin al'umma ina kallan yanda kake tafiyar da naka mulkin wanda shine abinda nafisan gani."

  Turab yai shiru yanajin kalaman mahaifinsa,can ya d'ago yace " Abba insha Allah wannan d'an naka bazai baka kunya ba, sai dai maganar murabus mayi daga baya in komai ya kamalla."

  Sarki yai murmushi sannan ya kara kallan Abdulmajid cikin tausayawa sannan yai waje.
Turab ne ya murd'a d'akin jinshi a kulle ya kai hannu zai kwankwasa.
Yanda yaga khadija tana bacci ne yasa ya sauke hannu tare da fasawa, ya tabbatar tana bukatar hutu.

  Maida kayan mota yai ya zauna a cikin motar tare da kwantar da kansa jikin kujera.
Garzali ya saukemai glass, a hankali shima bacci ya zareshi.

*********

  Magajiya kam wannan rana a zaune digirgir ta mata, babban tashib hankalinta duk inda ta aika a nemomata Turab sai ace baya nan, a wani hali Abdulmajid yake ciki? Dan itakam batasan wani abu ya sameshi, yanzu in matsala ta sameshi ta tabbatar shikenan ba shi ba hawa mulki, in hakan ta faru kuwa to wallahi sai dai kowa ya mutu dan Abu Turab bai isa hawa mulki ba sai dai su mutu tare.

  Karfe bakwai tai wanka tai kwalliya tsaf kai kace ba matsalar dake damunta ta kintsa ta fito.
Masu kula da ita mutum biyu tace " su biyota."
Wajen karfe takwas tasa driver dinta akan ya wuce da ita ABU, manta wa ma tai ta tsaya tunanin ina aka kaishi.

  Suna isa asibitin cikin sa'a ta hango motar Turab a waje.
Driver dinta ta kalla tace " je ka kiramin Garzali."
Nan yai waje, bai dade ba sai gasunan tare, Magajiya ta kalli Garzali tace " me kuke a waje haka?"
Yace " Yallabai ne ya samu bacci."
Tace " ayya, gashi shi yace inzo asibitin mu shiga tare gun Abdulmajid, kuma ba dadi yana bacci a tasheshi, ga ba wanda yasan gun, da alama sai dai ka taso shi din ko?"
Garzali yace "gun Yarima zaku?"
Tace " eh, kasan jiya ina cikin taro ban samu nazo ba sai yanzu."
Sunkuyawa yai yace " nasan d'akin in ba damuwa sai na kaiku kafin ya tashi."

Tace " shikenan."
Ta fada tare da fitowa.

  Sun isa har d'akin, ta sa aka kwankwasa kofar.
Khadija dake kwance ta mike tare da zuwa bakin kofar tace waye?"
Magajiya tace " Bud'e."
Kallan masu kula da ita tai a Garzali tace "su juya."

Gaban Khadija ne ya fadi dan Turab ko Ummansu bai bari tazo ba, a hankali ta bud'e kofar
Suna juyawa ta d'aga hannu ta wankama Khadija wani gigitacen mari.
Kuncinta ta rike saboda azabar da taji, shikanshi Abdulmajid sai daya farka daga baccin, dukda dai bai bud'e ido ba amma yana jinsu.

Magajiya tace " Wato ke kin zama rikakiya ko? D'ana bashida lafiya dan tsabar rashin mutinci baki aikomin ba, bare insa ran zaki sanar dani inda yake."

  A yanzu ji take zata iya yin komai dan kare d'anta, duk kuwa da yanda takesan Khadija.
Wucewa tai ta kusa da ita ta nufi gadon da Abdulmajid ke kwance.

Kallansa ta shiga yi sannan ta sa hannu kan kafarsa tace " wa ya saka? Wayace ka shiga motar da ba taka ba? Da kai nake magana, ka bud'e ido ka bani amsa ko sai ranka ya b'aci?"

  Gaban Abdulmajid ne ke ta faduwa.
Muryar Khadija taji tace " Haka Uwar kirki ya kamata ta fada ma d'anta dake kwance ba lafiya?"
Magajiya ta juyo ta kalleta tace "mene?"
Khadija tace " girma ana bawa wanda yasan darajarsa ne sai dai wanda baisan darajar ba banaji ya cancanceshi, bansan me kike nufi ba da cewa Wayace ya shiga mota ba amma banaji haka ya kamata uwar da danta ke kwance ta fadama d'anta."

  Magajiya cikin gadara ta fara takowa inda Khadija take, ba shakka yarinyar nan Turab ya gama lalatata.
Kusa da ita tazo ta d'aga hannu zata kara wanka mata mari.
Har Khadija ta runtse ido jin bataji saukar mari ba yasa ta bud'e idanunta a hankali.

  Magajiya ce ta kalleshi tace " me kakeyi hakan?"
Turab ya kalli Khadija yace " bamu guri ko?"
Khadija tai waje.
Turab ya sauke mata hannunta yace " me kike anan?"
Tace " kaine kasa d'ana a cikin motar daya kamata ka tafi ko?"
Turab yace " mene?"
D'anki?

Hannu yasa akasan hancinsa yace " a da banso kisan abinda na sani ba sai dai kunnuwana sun gaji dajin muryarki tana cewa d'an da batasan zafinsa ba da sunan d'anta."

  Idanu Magajiya ta zaro, a tsorace tad'anyi taku biyu baya.
Turab yace " me? Kina mamaki ne? Wato kinaso ki halaka asalin d'an sarki ki saka d'an d'anuwanki akan mulki shiyasa kika sa a kasheni?"

  Magajiya bakinta ya fara rawa tace " bansan me kake cewa ba, sannan zance kasheka bansan wannan maganar ba, sai dai ka tambayi Hisham."

  Turab ya kalleta yace " banyi mamaki ba, dan dama nasan cewa zakiyi shine ya aikata hakan."

  Shiyasa ana sanar dani zuwanki nasa Garzali ya kirashi, bari yazo sai muji wanene yasa a kasheni, daga nan sai mu nufi turakar Sarki."

  Magajiya tsoro da fargaba ne suka dinga ratsata, inza'asan komai nata bazai dameta ba amma banda sirrin Abdulmajid, komai zata iya kwatar kanta inhar d'anta nada matsayinsa.

  Abdulmajid dake kwance a kan gado a hankali wasu zafafan hawaye suka gangaro mai.

Turab ne ya kalli kan gadon, ko tunanin me yai sai ya kalli Magajiya yace "ahhh yau Gimbiya zatazo banaji ya kamata in zauna anan, ina tunanin maganar a gida ya kamata muyi."

Ya juya da sauri yai waje.
A can gefe ya hango Khadija, gunta ya nufa fuskarnan a d'aure yace " Abdulmajid ya farka bayan na tafi?
Tace "a'a."
Bai jira mai zata kara cew ba yai gaba.

  Dawowa yai inda take, kallansa tai, hannu yasa a aljihunsa ya ciro d'ankwalinta ya mika mata.
Ya juya yai gaba, bakinta ta saki tana kallansa.
Kallan bayansa tai har sai da ya bace mata, kwallar data zubo mata ta share.

Sannan ta kurama d'ankwalin ido, ita kanta dan dai ya bata d'ankwalin ne yasa tasan nata ne, amma ita kanta ta manta dashi.
Hawaye ne suka shiga zubo mata, in har Turab zai ajiye abinda ita kanta ta manta dashi to ba shakka yana santa.
Amma meye amfanin san da bata tashi sani ba sai lokacin da bazai mata amfani ba, ko da yaks da can ma ko ta sani ma ba zai musu amfani ba.

  Jingina tai da bango tanajin zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i na azaba........



  *******

Magajiya kuwa Turab na fita ta rufe kofa da makulli ta zauna kusa da Abdulmajid tace " Uban waye ya isa ya ce ba ni na haifeka ba?"

  Inhar kana tare dani ba abinda ba zan iya ba, dan haka ka gaggauta mikewa, Mairo kake so ko? Ka farka zan baka ita, mulki? wannan dama dole ne, sai me? Turab? Karka damu ko me zai faru sai naga bayansa, bazan taba bari yafadama wani sirrin nan nawa ba.
Ko mai zai faru banaso kasan komai, ni dai kawai ka tashi.

Sam hankalinta ya kasa kwanciya ganin Abdulmajid ko motsi baya yi.

  Shi kuwa Abdulmajid samun kansa yai da Addu'a mara amfani, baisan sanda yace " Allah ka d'auki raina......"




*******

  A can kano kuwa anata shirin zuwa kawo amarya, dan wasu ma yau da wuri suka taho dan kara gyara gidan Amarya da kara duba jeren da akai, Amarya Gimbiya Bilkisu kuwa yau tun safe ake ta gyarata, gyara mai sunan gyara na gargajiya bawai irin na xamani ba......

*TURAB*


? *KAINUWA*?
     ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*


  *74*

   Turab gidan Umma ya wuce inda take, yana isa ya tadda ta shiryamai abinci, nan yaci sannan ya kwanta akan kujerar falo.
Fitowa tai daga d'aki ta kalleshi tace " Turab meye hakan? Ta ya zakaci abinci ka kwanta?"
Mikewa zaune yai yace "Wlh Umma kaina kemin ciwo."
Zama tai gefensa tace " Ba dole kanka yai ciwo ba, tun da ka tafi d'aurin aure har yanzu banaji ka samu isasshen hutu na awa biyu cikake, ni na kasa gane me kake tayi a waje haka, gashi ni kace in zauna anan."
Turab ya kalli falon sannan yace "Umma ni dama ki dawo nan da zama."
Kallansa tai tace "akwai abinda kake b'oyemin ko?"
Turab yai kasa dakai yace " Ni Umma haryanzu Abba bai fad'amiki inda Hajiya dasu Lantana suke ba?"

Umma tace " Bai fad'amin ba, sai dai inaji kamar fa har yanzu jikin Hajiya ba sauki."
Turab yace "dama nayi tunanin haka, dan da ta warke da ta sanar dashi wani abu."
Basira ta kalleshi tace " me kenan?" 
Kai Turab ya girgiza sannan yace " In kawo miki masu aiki daga can? Naga waccan kamar aikin zai mata yawa."

Tace " karka damu, ni ma zaman haka kawai damuna yakeyi, yanzu kai haka zaka zauna har a kawo Amaryar?"
Turab yace " name?"
Tace " ko ma dai menene, ka samu ka huta sosai kafin suzo, kar suzo suganka a haka."
Murmushi yai yace " a haka kamar ya?"
Tace " oho dai nidai na fad'ama in ba so kake su juya da ita suce dama Ashe Angon ba shida jini a jika."

  Dariya ya saka sosai, yace " lalai Umma, kawai kice kinaso in huta amma wannan sharhin babu shi."
Tace " haka kace?"
Yace " hmm, ni kam Umma akwai abinda nakesan sanar dake."
Tace " name kenan?"
Yace " Umma so nake idan komai ya kammala in d'aukeki da Bilkisu muje kauyen da na taso."

  Umma ta kalleshi cikin jin dadi, tace " Ni kaina inasan zuwa sai dai ina tunanin me zance ma Sarki."
Yace " ki jira in gama abinda nakeyi, sannan ki kara min addu'a akan Allah ya bani ikon gurfanar da masu laifi, ya kuma kareni daga sharrinsu, sannan karya bani ikon cutar da wasu saboda wani buri nawa."

  Basira cikin kulawa take kallansa tace " Insha Allahu Allah na tare dakai, sannan muma bazamu daina maka addu'a ba."
Haka sukai ta dan hira sama sama kafin daga baya ya kwanta.

  Bacci sosai ne ya d'aukeshi wanda shi kansa bai san jikinshi ya gaji haka ba.

  Bai tashi ba sai karfe biyu na rana.

*********

  A can gida kuwa Magajiya ce zaune a kuryar d'aki ita da Hisham ta kalleshi tace " Yaya Yaran can yasan komai."
Hisham yace " name kenan?"
Magajiya tace " yasan Abdulmajid ba d'ana bane."

Hisham yai kasa dakai wato shiyasa ya ce mai haka? Sanda ya koreshi daga asibiti?"
  Magajiya ta kalli Hisham tace " yaya duk yanda za'ai inaso ka tabbatar baka bari an san nice na sa a kama Turab ba, inaso ka yarda akan kaine kai komai, ni zan san yanda zanyi karyai magana akan Abdulmajid."

  Tsananin mamaki ne ya kama Hisham ya kalleta yace " ban gane ba?"
Tace " inaso ka ce kaine kasa a kama Turab in Sarki ya tambayeka, ni zansan yanda zanyi kar a hukuntaka."

Tsananin mamaki yama hanashi magana sai kallanta kawaj da yakeyi.
Magajiya tace " Sannan inaso a maida Khadija Kano, duk sauran matsalar daga baya ni zan san yanda zanyi, kai dai kai wannan abun guda biyu."

  Ta mike ba tare da ta jira amsarsa ba tace " bari naje na kara shiryawa asibiti zan koma, dan bazan iya barin D'ana a can ba."

Hisham yabi bayanta kawai da kallo Baki a bud'e.

Ya dade a zaune kafin ya mike yai waje cikin tsananin takaici.

  Gida ya wuce, ya shiga d'aki ya baza uban tagumi.

  ***********

   Mairo kuwa tana gama aikin gida da takeyi tai wanka ta shirya ta cema Ummanta zataje gun Umma Basira, nan ta fito, sai dai me? Asibiti ta fara wucewa.

   A jikin windown d'akin ta tsaya, ba kowa a d'akin, batai niyyar shiga ba dama, gani tai yana kokarin motsi da hannunsa da alama idanunsa a bud'e yake kuma abu yakesan d'auka.

  Da sauri ta shiga ciki, yana jin motsi ya koma ya kwanta tare da rufe ido.
Mairo ta karasa gunsa da sauri tace " me kakesan d'auka?"

Ta fad'a tana kallan gefe, ruwa ta gani a jarka da alama shi yakesan d'auka.
Tace "Ruwa zaka sha?"

  Jin shiru yasa ta matsa daf dashi tace " nice bakasan gani?"

  Ganin bashida niyyar bud'e ido yasa haushi ya kamata ta juya zata tafi, jitai an riko hannunta.
Tsayawa tai ba tare da ta juya ba, Abdulmajid a hankali yace "Karki fad'awa kowa na farfado, na rokeki."
Cikin mamaki ta juyo ta kalleshi, gani tai yayi wani mugun fadawa, tace " bakasan asan ka farfado?"
Kai ya d'aga mata, tace "ban gane ba? Abinci fa? Ruwa fa? Kashe kanka kake sanyi?"

   Maimakon taga ya bata amsa gani tai yana murmushi, tace " murmushi ma kake?"
Yace "in kina fada kyau kikeyi."

  Kallan mamaki tamai, sannan ta d'auko ruwa a cup ta mikamai tace ungo.

 Sam ya ma manta abinda ke gabansa ganin Mairo, yace " bazan iya tashi ba."

 Harararsa tai sannan tace " ta ya ya ma zaka sha ruwa? Ai kullema ciki zaiyi."
 Ta karasa tare da ajiye ruwan.
 Inda kayayyakinsu yake ta shiga dubawa, kular abinci ta bude ta zubo shinkafa miya wacce taji naman kaji.
 Abdulmajid yace " so kike inaci wani ya shigo?"
 Tace " wai me ke faruwa?"
 Idanunsa nd suka kada yace " ban cancanci cin abinci ba, magana ma bancancanci yimiki ba, Mairo."

  Mairo ta kalleshi tace " nima ce maka akai ina san yi maka magana?"
 Yace " haka ne, amma yanzu in wani ya shigo fa? Dan Khadija ma fita tai taje ta dawo."
 Bata amsa mai ba kawai yaga ta kukule window ta sa sakata a kofa, sannan tazo ta taimaka mai ya zauna ta mikamai abinci.
 Hannunsa ya nuna mata tace " to me kakeso ai?"
 Yace " shiyasa nace bazan ci........"

 Abincin data samai a baki ne ya hanashi karasa abinda zai fada.

 Haka ta shiga bashi abinci, tana bashi ruwa, daga zaiyi magana zata ballamai harara.


**********
 Turab na farkawa yaga Sabi'u a kujerar gabansa.
 Kallansa yai yace " kai kuma fa?"
 Sabi'u yace "gaskiya ban taba ganin ango irinka ba, ana can ana ta hidima a gidan sarauta amma kai baka nan, Ummanka bata nan, yayanka bayanan, nikam yau an ka wahalar dani."

 Turab yai murmushi yace " dama ko muna nan ai jama'a ne masu hidimar ba mu ba."
 Sabi'u yace " ka tashi ka shirya mu tafi, 'yan uwan Amarya sun fara zuwa.
 Yace" to ni mai kake nufi inje?"
 Sabi'u yace " au bazaka ku gaisa ba?"
 Turab yace "amma lalai kafi kowa, a ina aka taba haka?"
 Sabi'u yace " haba? Ba haka ake ba?"
 Turab ya girgiza kai yace " kai in anzo naka kayi, yanzu ina Umma?"
 Ya fada tare da mikewa.
 Sabi'u yace "ta tafi gun 'yan uwan Amarya, tace in fadama inka tashi, insun watse ta taho."

 Turab ya d'aga kai alamar gamsuwa.
 Sabi'u ya kalleshi yace " dazu waziri ya aiko inje."
 Turab yace " me yace?"

"yace zaiyi tunani akan abinda kace mai."
 Turab yai murmushi a ransa yace " ko kayi tunani dolene ka amince da abinda nace dan nasan halin magajiya maida komai kanka zatai, in har kanasan taimakon d'anka da kuma kanka dolene kabi abinda nace."

 Sabi'u ne ya kalleshi yace "me kace mai wai?"
 Turab yace " ba komai."
 Yai ciki.
Wanka yai ya saka kayan da Sarki ya aikomai.
 Yadi ne mai masifar kyau, kallo d'aya zaka mata kasan tsadarsa.
 Farin yadi ne, ya saka aikin babbar rigar kayan, yasa hula da takalmi ya fito.

 Tafi Sabi'u ya saka yana ganinsa yace "kai Ango, yaufa ba dama, da alama Gimbiya yau sai an tausaya mata."

 Turab ya kalleshi yace " yo ai dole a tausaya mata tunda Amaryar Sabi'u aka kai."
 Sabi'u yace "anma kafadamin magana."

Haka suka taso suka fito.

""********

  Zaune take a cikin mota, sai kuka takeyi, kanwar Fulani na gefenta da kishiyar Fulani.

 Wani had'ad'an leshi na da mai nauyi da tsada, ta sanya, tayi kyau sosai da sosai sai dai kukan da takeyi yasa duk kwalliyar fuskar tata ta tafi.

  Haka har suka isa garin na zazzagawa.

  Suna isa gidan aka saki wani busa na sarauta.

  Su Magajiya dama sun shirya dan tarbar ta, tana isowa suma suka fito suka zo inda suka tsaya.

 Magajiya ta dafa ta saboda fuskarta a lulube take ruf.
 Nan suka shiga har bangarenta, ana tafe ana zabga guda.

  Magajiya na ajiyesu ta tabbatar komai ya kammala ta fito.

  Tana san ganin fuskar Amarya amma hankalinta na gun Abdulmajid.

  ********

  A asibiti kuwa Mairo tana gama bashi abinci, tana bashi ruwa aka fara kwankwasawa.

  Nan ta tattare kwanukan ta ajiye a kasa, shikuma ya kwanta.

  Kofar ta bude tana addu'a Allah yasa ba Magajiya bace.
 Ajiyar zuciya tai ganin Hisham ne da Khadija.

 Khadija ta kalleta tace " saukar yaushe?"
 Mairo tace " d'azu, har abinci ma naci, dan sanda ma taho ban tsaya naci abinci ba."

 Hisham ta gaida, jiki a sanyaye ya amsa ya shiga ciki ya duba Abdulmajid sannan yai waje.

 Mairo ta kalli Khadija tace " are u okay?"
 Khadija tace " name kenan?"

 Mairo tai murmushi tace " yau ake tariyar ya Turab."

 Khadija kanta ta sunkuyar sannan ta d'ago tace " ke zan tambaya ai duba da yanayin dake tsakaninku na shakuwa, ni dama mun dade a haka."

  Mairo ta kamo hannunta cikin tausayawa ganin yanda idanun Khadija suka ciciko, tace " Khadija ya Turab na bala'in sanki, in nace so tofa so d'in gaske nake nufi, tun kina karama yake sanki sai dai da alama har zuwa wannan lokacin bai bayyana miki ba."

  Kallanta khadija kawai takeyi, idanunta na zubo da kwalla.
 Mairo tace " Ya Turab a matsayin kanwa ya d'aukeni, kece zabin ransa ban san me yasa soyayyar ku ta koma haka ba."

  Khadija ta runtse ido tare da share kwallar ta tace " Mairo inaji dama can Allah baiyi akwai wata rayuwar jin dadi ta soyayya ba a tsakaninmu, soyayya ta zamantakewa bazata taba shiga tsakanina da yaya ba, mahaifina da Kanwarsa sun zalunceshi sunmai abinda na tabbatar bazai iya mantawa ba (nace wanda ma kika sani kenan), ta ina kuwa zamu iya zaman aure dashi?"

  Mairo tace " to amma ai ba ke bace kikai, kuma laifin wani ai baha shafar wani."

  Khadija tai murmushi tace " haka ne sai dai........."
 Kallan Abdulmajid dake kwance tai, a lokacin ta tuno da kalaman Turab, a sanda take juyawa zata tafi d'azu daya ce ta fita.
 Kamar Magajiya yake tambaya akan ciwon yaya.
 Mikewa tai da sauri tai waje da gudu, Mairo cikin mamaki ta kalleta.

 Abdulmajid na kwance duk yana jinsu, hawayen tausayin kansa dana kanwarsa ne ya ziraro mai ta gefe.


  Khadija can ta hango mahaifinta da karfi ta kwalla mai kira, ko takalmi babu a kafarta.
 Tsayawa yai yana kallanta, da gudu ta karaso tana hakki tace " Baba kai da Umma Magajiya kuna da hannu a ciwon Yaya?"

  Kallanta yai sai dai baisan me zaicw ba, tace " Ya Turab kukaso ama haka, amma Ya Abdulmajid ya tare?"

  Hisham ya kalleta yace " Khadija..." ya fada tare da kokarin kai hannu ya riko ta, da sauri tai baya tana zare ido tare da girgiza kai, dan yanda ya kira sunanta ta ya bata amsar tambayarta.....


*TURAB*

 ? *KAINUWA*?
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

*75*

  D'akin da Abdulmajid yake ta koma, tana shiga ta taradda Mairo dake tsaye tana jikin kofa da alama nemanta take.

Yanda ta ganta yasa tasan ba a hayyacinta take ba, Mairo ta ja hannunta ta shiga da ita ciki sannan ta zubo ruwa a kofi ta mika mata, tace " naga kina bukatar kad'aicewa ni bari na wuce."
Khadija bata tanka mata ba haka kuma bata sha ruwan ba sai daj yana rike a hannunta.

  Tashi tai taje kusa da Abdulmajid tana kallansa, hawayene kawai yake zubo mata, ganin kukan na neman kamata tai ban d'aki da gudu.

  Tana gama kukanta ta fara wanke fuskarta, taje zata bud'e kofa ta fito taji muryar Hisham na cewa Khadija? Da alama shigowa yai nemanta, bayan kofar bandakin ta labe da sauri, shi kuma jin shiru yasa ya d'an bud'e ban daki, da yake a rikice yake bai yi tunanin zata iya b'oyewa ba, kawai sai yai tunanin bata ciki.

  Juyowa yai zai fita, Magajiya ce ta shigo, ko ta kanta baiyi ba ya fara kokarin wucewa, ba abinda ta tsana irin a ganta ai kamar ba'a ganta ba, a xuciye tace " Waziri meye hakan?baka ganni bane?"
Yace "na ganki, sai dai abinda ke gabana yasa idanuna suka rufe."
Ganin yana neman fita a xuciye tace " Yaya Tsaya!"
Tsayawa yai sannan ya kalleta yace " bakiji nace idanuna sun rufe ba? Alama ce ta ba lafiya ai."
Tace " wannan ba damuwa ta bace, damuwar ka ce, sai dai inaso in sanar ma inma ka nuna baka ganni bane saboda abinda na fadama na cewa ka tabbatar kace kaine sanadin komai, kake neman yadda ni to kada ma ka soma, ka fi kowa sanin nice yar uwarka kadai a duniya nice sirrinka kuma nice reshenka."

  Ran Hisham yakai makura yace " reshen da bai dade ni da komai ba sai wahala? Sanar dani me wannan reshen yamin a rayuwa?"

  Magajiya tace "mene? Ni kake fadama haka yaya? Ni kake tambaya me na maka? Duk daula da jin dadin da kake zaune a ciki waye sanadi? Kana tunanin karfinka da matsayinka ne yasa?"
Cikin takaici yace " daular banza daular wofi, daular data sa 'ya'yana suka tarwatse? Daular da ta ke rinjayata nake aikata abinda bashi bane? Daular da tasani kisan kai?"

  Jikin Khadija ne ya kaure da rawa, batasan sanda ta tsugunna a bandaki ba, kisan kai?
Abdulmajid kam gaba d'aya jiyai gab'obin jikinsa sun daina aiki.

  Magajiya ce ta sa dariya tace " ashe kasan da wannan, na d'auka ka manta da mumuman abinda ka aikata."

  Hisham fuskarsa ta canza sosai yace " kina tunanin duk abinda nake miki kyaleki nake ko dan ina tsoranki? Dama ina jurewa ne saboda d'ana, yanzu kuwa abinda nake jurewa dominsa na kwance ba lafiya, kina tunanin akwai abinda zai tsayar dani?"

  Kallansa tai tace " me zaka iya yi in baka jure ba? Sanar da abinda muka aikata? In haka ne kaine a ruwa dan kai kasan ni da kaina ban taba kaahe mutum ba haka kuma bantaba sawa da bakina a kashe wani ba."

  Hisham kallan tsananin mamaki kawai yake mata, yace " mene?"
Tace " ni na saka kaje kashe Turab sanda aka haifeshi?ko nice na saka ka sama gidansu wuta ka kashe yayan mahaifiyarsa da matarsa?"

  Abdulmajid ji yai kansa na wani irin juyawa, yanasan yai kara yace musu khadija na bandaki sai dai
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KAINUWA* A Historical Fiction* by Ayusher Muhd Gimbiya 1 15,759 08-21-2019, 01:53 PM
Last Post: Ebony Lacklock
  *JALILAH* by Ayusher Mohd* Gimbiya 0 20,165 09-10-2018, 09:03 PM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 3,758 06-16-2018, 10:17 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 6,907 06-16-2018, 10:16 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 3,349 06-16-2018, 10:09 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 3,717 05-07-2018, 11:04 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 3,636 04-30-2018, 01:16 PM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* A Historical Fiction* by Ayusher Muhd Gimbiya 0 4,614 03-29-2018, 11:44 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)