The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KAINUWA* by Ayusher Mohd
#1
? *KAINUWA*?
     ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

  *61*

  Jin bataji saukan mari ba yasa ta bud'e ido a hankali, kallansa tai sannan tai saurin zubewa a kasa ta saki wani irin kuka.

  Turab idanunsa ne suka canza, kallo d'aya zakamai ka tabbatar da tsantsar b'acin rai, maganin nan ya cilla mata.
A tsorace ta d'ago jiginta ya hau karkarwa.
Cikin kakkausar murya yace " Waye ya saki?" ba wai dan baisan amsar bane, a'a yanaso yasan ko tana danasanin abinda takeyi.

  Kasa ta karayi tana kuka sosai tace " Ranka ya dade ka yafe min wlh in na fad'a kasheni za'ai, sannan mahaifina karshensa yazo."

  Magajiya? D'agowa tai da sauri jin abinda yace, yanayin kallan da tai yasan dama abinda yake zargi haka ne, kusa da kafaffunsa ta matso tace " Ranka ya dade wlh nima ba'a san raina nakeyi ba, mahaifina na bukatar aiki na gaggawa a asibiti shine akace in ina sa maganin nan za'a biyamai kud'in aiki, sannan komai ua faru in sanar da ita.

  Fuskarsa ya shafa da hannayensa biyu a ransa yace Inalilahi wa ina ilaihi raji'un.
Zama yai a kan kujera sannan yace " me ya faru tsakanin Hajiya da Magajiya?gaskiya nakeso ki fadamin, ni zan taimakeki, zan kuma bayar da kudin aikin."

  Tana kuka ta girgiza kai tace " wlh ban sani ba, nadai san a ranar da Umma Rabi tazo a ranar ta aika a kira Magajiya, sannan daga ranar aka fara sani aikin."

  Turab ya kalleta yace " naji, zan sa Lantana ta koma dake bangaren Hajiya da kula da ita, zan gani ko kinyi dana sanin abinda kika aikata, sannan ki jira hukuncin da zansa a yanke miki, mahaifinki ni zan taimaka mai sai dai ke dole ki fuskanci hukunci."

  Kuka take sosai tace " na sani Ranka ya dade, na gode kwarai da cetoni da kai daga cikin masifa."

  Turab yace ta tashi ta tafi.
Fitowa yai, ya nufi can cikin gida bangaren kannen mahaifinsa dan zuwa gun Umma Rabi.

Ko Garzali baya yarda ya biyoshi duk da kuwa ya yarda da shi.
  *********

  Khadija kuwa ganin Turab ya shiga bangaren Hajiya yasa ta juya.
Har zata wuce bangaren Abdulmajid sai kuma ta karkata ta shiga.

  Bayan an sanar da zuwanta, Abdulmajid dake zaune abin duniya ya dameshi yace ta shigo.
Khadija ta shiga, kallan bangarensa tai sannan a ranta tace " yafi na ya Turab kyau sosai, da ban kula da hakan ba amma yanzu na gani, ya zakai in kaji kai ba toshen gidan nan bane?"

  Idanu ta kura mai tana wannan tunanin, ji tai tsananin tausayinsa ya kamata.

  Batasan ma ya miko yazo kusa da ita ba, sai jitai yasa kafa ya d'an harbota.
Kallansa tai tace " Yaya."
  Abdulmajid ya hard'e hannayensa ya shiga zagayeta yana kallanta yace " me ya kawoki? Ba dai zuwa kikai akan rabamu da Mairo ba?"

  Hannu tasa ta riko rigarsa tace " Yaya wannan zagayen fa? Ai sai jiri ya kamani."

  Murmushi yai sannan ya koma ya zauna.
Kallansa ta karayi a ranta tace " ya ya zanyi? in har kaji abinda suka maka wace rayuwa zaka shiga? Alokacin ba ka da wanda zaka gani kaji dadi, komai da kake tunanin naka ne a lokacin xakaga babu abu ko d'aya daya kasance naka, dama ace Mairo na sanshi ne....."

Khadija meye hakan?
Abinda ya fadane ya dawo da ita daga tunaninta.
Fara'a ta saki sannan tazo ta zauna kusa dashi tace " Yaya."

  Ya kalleta yace " menene? Nifa na fara shakkar me kikazo dashi naga sai wani kafeni da ido kikeyi."

  Murmushi tai tace " yanzu ace kai ba dan sarki bane wace rayuwa kake tunanin zakai?"

  Dariya ya saki sosai yace " ban taba wannan tunanin ba, dan tun ina d'an shekara uku Umma ta fara horar dani akan magajin sarki, kinga kuwa banda wannan lokacin."

  Khadija ta jinjina kai tace " Haka ne, amma ka taba tunanin rasa mulki?"

  Wani  kallo ya mata yace "Khadija meke damunki? Kinsan tun ina dan shekara uku Umma take sanar dani ni kadai ne magajin sarki, shi kanshi Abba a lokacin nunamin yake nine magajinsa, a haka na taso har sai bayan zuwan Turab sannan na fahimci canji daga gun Mahaifina wanda hakan na kona min rai, sam ya daina wasa dani gaisuwa ce kawai ke had'amu, bayan da shi dakanshi yake aikawa a kirani."

  Yai wani murmushin takaici yace " Khadija duk wani abu na rayuwata a da ina yinsa ne dan faranta ran mahaifina, burina naga ya dubeni yacemin Abdulmajid kayi daidai, sai dai inaa duk wani abu dazanyi bana birgeshi, ko jarabawa ta na kawomai banaji ma yana bud'ewa...."
Wani abu ya had'iya sannan ya kalleta, hawaye ne yaga ya zubo mata.
Harararta yai yace " tausayi na kike?"
Shiru tai batace komai ba.
Yai murmushi yace " tundaga lokacin na tsani Abu Turab tsana mai yawa sannan akoda yaushe Umma na sanar dani shi din fa makiyinane, kar na kuskura ba barshi."
Yai ajiyar zuciya yace " kinsan me?"
Kai ta girgiza alamar a'a
Ya matso alamar rad'a yace " ko kiran mata da nakeyi bangarena yi nakeyi dan in batama Sarki yai ko naki dadin rashin damuwa dani dayakeyi."

   Idanu ta rufe a hankali wasu zafaffan hawaye suka biyo mata, kallanta yai yace " Karki damu Khadija, na saba da rayuwa, kinsan tunda nake a gidan nan ba wanda ya taba tambayata ya nake? Tambaya ta kulawa, ina nufin Umma na ko Abba na, ita burinta shine in zama abinda takeso, shikuma dama bana cikin shafinsa."

  Hawayenta ta share tace " Yaya me yasa baka taba fad'amin ba?"

  Dariya yai sannan ya mike yace " na fizan na zama bad guy, hakan ne zaisa in rage takaicin abinda ke raina, sai dai Khadija kiyi hakuri amma bazan taba ba Abu Turab Mairo ba, ya kwacemin uba, mutane, na bar masa amma banda wannan."

  Jitai tama kasa magana, me yasa itama a koda yaushe takejin zafinsa? Gani take baya kyautawa sannan shidin mutumin banza ne? Ashe bakincikin dake ransa ne yake amfani dashi dan kuntatawa na kusa dashi? Ya zaiyi in yaji sirrin nan?

  Daurewa tai tace " Yaya kana tunanin Mairo zata soka? Bayan kai din mutum ne wanda yake had'uwa da Magajiya su aikata abinda bai daceba na zalunci?"

  Yace "Ahhh zalunci? Hmmm Khadija kenan bana tunanin kinsan Umma."

  Kallansa tai tace " bansan ta ba sannan bana bukatar Saninta, sannan kaima Yaya zuciyarka na neman riked'ewa gaba d'aya ta koma ta Umma, ka gaggauta kaucewa daga sharrinta."

  Murmushi yai sai dai baice komai ba, a ransa yace "hakan na nufin in bijiremata ita kuma ta yarda ni, ita kadan da nake sa rai tana sona itama ta juyamin baya."
Khadija ta mike tare da kallansa tace " Yaya zanje gurin Umma Magajiya ne, akan maganar aurena da Saif."

  Yace " Ya ya? Maganar auren an kusa ne?"

  Kai ta girgiza tace " a'a."
Juyawa tai ta fita, aranta tana mai fatan kub'uta daga sharrin Magajiya da Mahaifinsu."

  ********

  Falon yai tsit kamar ba kowa a ciki, Umma Rabi tai shiru kamar ruwa ya cinyeta sannan ta d'ago ta kalleshi.

  Abu Turab yace " Umma ki taimaka ki sanar dani, Hajiya na cikin wani hali."

  Tace " Turab sirri ne...."

  Yace "wa ke zancen Sirri rayuwar Hajiya na cikin had'ari?"

  Umma Rabi tai shiru kafin can ta d'ago ta kalleshi.
Nan ta sanar da shi abinda ta sani.

  Shiru yai kafin yace "ita waccan d'in wacece? Wacce ta aiko da wasikar?"
 Umma Rabi tace " ban santa ba sai dai kafin Hajiya ta fara rashin lafiya da yamma na koma gunta, a lokacin ne ta sanar dani wani sirri wanda ahi nake tsoron sanar dakai."
 Yace " na menene?"

  Ta dade batace komai ba, yace Umma dan Allah ki fadamin.
 Tace " ka tabbatar zaka iya ja da Magajiya?"
 Yace " kwarai kuwa."
 Yanda yai maganar ya bata kwarin gwiwa tace " Maganin da ake zubawa sarki na hana d'aukan ciki ne."

  Tashin hankali.

  Bakinsa ne ya shiga rawa yama rasa mai zaice.
 Umma Rabi ta kalleshi sai dai itama batasan me zatace mai ba, a hankalu tace " ni kaina ina zargin ciwon Hajiya da Magajiya, sai dai banida shaida sannan bansan wa zan tara da maganar ba."
 
  Turab mikewa yai kamar wanda bashida laka a jikinsa.

 Tafiya kawai ya keyi yana tunanin wannan al'amari.

  Jiyai kansa ya d'au wani zafi, tsayawa yai a jikin wata bishiya ya dafata, addu'a kawai yakeyi Dan neman sauki a zuciyarsa.


   Ya dade sosai kafin ya nufi bangaren Hajiya.

  Hajiya kam babu, dan jikinta ba dadi to abune da anriga an gama halakata, ba shakka bai taba ganin mutum irin Magajiya ba, kenan duk wanda yasan sirrita ajali shine zai biyoshi?

  Kallo d'aya zakama Hajiya kasan inaa sai dai wani ikon Allah.


***********

  Magajiya na kwance a d'aki dan tun tafiyar Turab takejinta haka, a kwance take taji sallamar Khadija.
 Daurewa tai ta mike zaune, Khadija ta shigo.
 Bayan ta gaisheta, Magajiya tace " Khadijata ina kika shiga? Kwana biyu sam ban ganki ba."

  Khadija fuskarta a had'e tace "Ina gida."
 Magajiya ta kalleta cikin kulawa ganin duk ta rame, tace " Khadija mai kike tunani akan dawowa nan da zama kafin lokacin aurenki?"


  Khadija ta kalleta duk da gabanta na fad'uwa saboda tsananin kwarjini da Allah yaba Magajiya ta daure tace " Dama zuwa nai in fadamiki akan bazan auri Saifullahi ba."

  Magajiya ta zaro ido tace " mene? Wace irin banzar magana ce hakan?"
 
  Khadija tace " dama abinda nazo fadamiki kenan."

  Magajiya ranta ya b'aci tace " Akan Abu Turab?"

 D'agowa Khadija tai ta kalleta, Magajiya tace " ke kina tunanin zan baki Abu Turab?"

 Jitai zuciyarta ta dake tace " ina fa zance Ya Turab zan aura? In ba so nake ku halakashi ba?"

  Magajiya ta kalleta cikin tsananin takaici tace " in kin san da haka to kiyi gaggawar cireshi a ranki."

  Khadija jitai ranta ya b'aci wato duk abinda sukeyi baya damunsu? Tace zasu halakashi amma ko a jikinta.

  Sun biyu suna neman ruguza rayuwar mutane dayawa, na farko sun gama cin amanar sarki, sun jefa Abdulmajid cikin halaka, suna neman jefata sannan sun takurawa wanda yake jinin gidan, suna neman halakashi.

  Ita kanta batasan tace " To ko Ya Abdulmajid zan aura."

  Jitai gabanta yayi wani fad'uwa, mikewa tai tace " wani irin hauka kike fad'a, bakida hankali ne? Ko kanki me ya zare?"

  Khadija tace " in har ba Ya Abdulmajid ko Ya Turab zan auraba inaso ku barni, banaji zan yi aure har karshen rayuwata dan bazan iya auren wani da hali irin na mahaifina ba."

  Magajiya tace " Khadija? Me kike cewa?"

  Mikewa tai saboda ta fara jin dakewar tata na neman gazawa tace " na barki lafiya."

  Magajiya mamaki ma ya hanata magana sam, anya Khadija ce? Ba waccan tsinanen yaran bane ya zigata kuwa? Yace tace a aura mata Abdulmajid?

  Jitai idanunta sun daina ganin komai sai duhu, baya tai lyuuu kamat zata fadi sai kuma tai saurin rike gadon tana maida numfashi.

  Cikin wata sarkakiyar murha tace " *ABU TURABBBBBBBBB*"


   
  

  Nima na tayata fada *ABU TURAB?*
*KAINUWA*?
     ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

  *62*

  Khadija tana fita ta samu guri a waje ta xauna, jitai jikinta duk ya kaure da rawa, ba shakka wannan ce rana ta farko da tai tafa kukewa tai ma wanda ya girmeta magana irin haka, balle Magajiya mace mai tsananin kwarjini da mulki.

  Mikewa tai a hankali, so take ta samu Abu Turab taji a wani mataki na aure ya d'auka tsakaninsa da Mairo? Dan ba shakka tana san d'an uwanta ya aureta ko dan ranar da wannan sirri ya bayyana ya zama akwai wanda zai gani yaji dadi, ta tabbata in tai magana gani za'ai kamar kishi ne ke damunta sai dai ko d'aya, tasan akwai kishi na wanda take tsananin so shikuma ba ita yake so ba, sai dai a yanzu burinta tai kokarin ganin ta gyara wani abu ko yaya ne na daga cikin laifukan da aka aikata.

   Bangarensa ta nufa, har takai hannu zata kwankwasa ta fasa saboda batasan da wace kalmar zata fara masa magana ba, a hankali ta juya cikin damuwa.

  Idanu ta zaro, kallanta yai sannan ya kalli kofar, miyau ta had'iya sannan tace " Ya Turab."

  Kallanta ya sakeyi sannan yace "Lafiya?" daga bangaren Hajiya yake sam bayasan magana.

  Khadija tai shiru tana wasa da hannayenta, tunanin abinda zata cemai takeyi.
Ta gefenta ya wuce zai shiga ciki ganin batada niyyar magana.
Itama ganin haka yasa tai saurin cewa "Magana nakeso muyi."

  Juyowa yai ya kalleta sannan ya kauda kai yace "Banaji akwai wata magana da zamuyi."

  Kasa tai da kai tare da jinjina kai cikin rashin jin dadin abinda ya fada tace " haka ne, na tabbatar ba wata magana datai saura tsakaninmu, sai dai inaso ka bani ko minti goma ne."

  Harshensa ya zaro kadan ya d'an lashi lab'ansa da suka bushe yace muje.
Mai makon yai ciki sai taga ya juya ya fara tafiya.

  Bata tambayi inda zasuba itama binsa kawai tai a baya.
A hankali suke tafiya yana gaba daga gefen dama, ita kuma tana bayansa daga gefen hagu, tafiya kawai yakeyi. Yana kara tattaro duk wani tugu da ya sani wanda Magajiya ta aikata ita da yayanta wanda ya kasance mahaifin yarinyar dayafiso a rayuwa.

  Ta yaya zai iya zaman aure da ita ko bayan komai ya kamala? In har ya sa akama mahaifinta da Magajiya hukunci ta yaya zai iya kallanta da sunan soyayya? Itama ta yaya zata iya kallan wanda ya ruguza rayuwar gidansu da sunan soyayya? Ai duk san da takemai bai kai na iyayenta ba, shima haka, duk sanda yake mata bazai taba kwatanta shi da wanda yakema mahaifiyarsa ba.

  Juyowa yai ya kalleta, ganin irin kallan da yake mata yasa jikinta yai wani irin sanyi.
Baice mata komai ba sai nuna mata inda zasu shiga dayai.
Kallan gurin tai, inda ya ke hutawa ne, sai daya shiga ta bi bayansa.
    Can yaje ya zauna akan kujerar dake gun.
Rasa inda zata zauna tai dan kujerar gud'a d'aya ce a gun doguwa.
Kallanta yai sannan ya mata alama da kai akan ta zauna daga gefe.

  Nan ta zauna, ta d'an kalli sararin samaniya, kasancewar yamma ce garin yayi luf abin sha'awa, bare lokacin na zafi ne, iska tana kad'awa a hankali.

  Jitai yace " ina jinki."
Khadija ta kalleshi kallo na tsananin kauna, inama lokacin da suke yara ya dawo? Lokacin da suke kullum tare, cikin tsananin bege da kulawa.

Kin kafeni da ido bakice komai ba.

  Khadija ta kakaro murmushi tace " Ba fara'a yanzu a tsakaninmu."
  Kallanta yai sai dai baice komai ba ya maida kansa inda yake kallo da.

Murmushi ta sake yi na tausayin kanta cikin wani yanayi ta fara cewa " sa dayawa ina tunanin ina ma, ina ma ban sanka ba? Ina ma banida had'i da wannan gidan? Inama da naje kano ina karama ban dawo ba."

Tacigaba bayan ta d'an had'a hannayenta gu d'aya. 
"Yaya na rasa wace irin mummunan kaddara ce tsakaninmu? Banida abinda xancema na abubuwan da mahaifana suka aikata, bani kuma da bakin baka hakuri akanshi, sai dai zam baka hakuri akan abubuwa gudan biyu."

  Hawayene suka zubo mata ta sa hannu ta sharesu tace " Yaya kayi hakuri akan abinda Ya Abdulmajid ya maka, ba wai ina baka hakuri bane dan ka yafemai a'a ina baka ne saboda neman sassauci akansa, ina tsananin tausayinka sai dai ina tausayin Ya Abdulmajid."

  Juyowa yai ya kalleta, da alama tasan komai, dama ranad da ta fad'o musu gaban mota tai wannan firucin ya tabbata akwai wani abu da ya sani."

  Idanunsa na kanta yace " kin san komai kenan da alama."

  Hawayenta ta sake sharewa tace " Yaya wancan sokon yayan nawa baisan komai ba, baisan abinda suka aikata mai ba, tunda yake bai taba keran wacce ta d'au cikinsa na wata tara da sunan uwa ba, bai taba yi mata wani abu ba wanda d'a ya kamata yama uwarsa ba, ko magana tamai gani yake matsayinsa ya wuce a nemi bashi shawara, wancan soko yaya baisan matsayin da yake takama dashiba ba nashi bane, matar da yake kokarin faran tawa rai a koda yaushe baisan amfani take dashi dan cikar burinta bawai dan so ba, Yaya Turab sannan wancan sokon ya gama mutuwa akan san wacce bata sansa, tunda yake a rayuwarsa banaji akwai mutum d'aya wanda ya kasance yana kaunarsa kauna ta yanda yake bawai dan tushensa ba ko dan halayensa ba,yaya wancan sokon d'an uwa nane jini nane wanda ni kaina......."

  Kuka ne ya ci karfinta wanta take yinshi daga cikin zuciyarta kuka mai taba zuciyar mai sauraro.

  Duk yanda yaso ya jure ya kasa dan kukan sosai yake taba ransa ba shakka shi kansa yana tausayin Abdulmajid, mikewa yai ya nemi hanyar fita.
Cak ya tsaya dan jiyai bazai iya fita ba tana irin wannan kukan.

  Handkerchief ya zaro daga cikin aljihunsa na wando ya nufo inda take.
" Ungo." abinda ya fada kenan yana mika mata.
A hankali ta d'ago sannan tasa hannu ta amsa.

Juyawa yai zai fita, da sauri tasa hannu ta riko rigarsa.

  Turab ya tsaya sai dai bai juyo ba.

  Saukowa tai kasa ba tare da saninsa ba ta sanya gwiwowinta biyu a kasa.

  Tace " Ya Turab."

  Juyowa yai kallan mamaki ya mata gani gwiwowinta  biyu a kasa.
Yace " meye hakan?"

  Tace " kasa ama duk wani laifi a cikinsu hukunci sai dai dan Allah yaya ka hakura kaima da abu d'aya, kana da komai a rayuwarnan.
Mulki, uwa ta kwarai, mata, sannan dukiya da ilimi da kuma masoya, dan Allah ka sadaukarwa Ya Abdulmajid da abu d'aya na daga cikin wad'an nan abubuwan da Allah ya azurtaka dashi ka bar masa Mairo kad'ai, ita kadai, in tana tare dashi gani nake ko wani abu ne zai sameshi zai jure sannan ko wani hukunci aka mai zai yi kokarin jureshi."

  A hankali ya furzo da wata iska sannan yasa hannayensa biyu ya d'agota, kallanta yai ido cikin ido, yace" bazan yi miki dogon bayani ba, ba kuma zanyi duk wani abu da kikeso ba, abu d'aya na sani shine duk wani mai laifi zan sa a hukuntashi indai da raina, akan ganin bayan Magajiya even u i will have to use u."
Ba tare da wani tunani ba tace " use me ya Turab, kayi amfani dani ta kowace hanya da kakeso, bazai damen ba, me kake tunanin zanyi?."

  Wani murmushi wanda ni kaina bansan ma'anarsa ba yai sannan yace " even if i hurt u?"

   Kallansa tai sannan ta ce " please yaya hurt me."

  Shiru yai yana kallanta dan tabbas kalmar data fada har zuciyarsa ya jita.

  Murmushi ta mai sannan tace " Yaya a koda yaushe zam kasance mai ma addu'a."
Wuceshi tai ya fara tafiya, tana tafe hawaye na zubo mata, ji take kamar yau shine rana ta karshe da zasuyi magana irin haka, itakam tasan farinciki? Bataji zata sameshi a duniya.

  Idanu ya runtse dan tabbas yana bala'in san Khadija, ya tabbatar yauce rana ta karshe da zasu zauna kamar haka, Allah ka bani ikon yin abinda ya dace, abinda ya fada kenan sannan ya juya.

*********
  Duk yanda taso tai bacci ta kasa, juyi kawai take a kan gado tana tunanin abinda ya cancanta.
Tabbas dolene ta gajarta rayuwar Abu Turab, a ranar auransa dolene ta kaudashi ko ta samu salama, duk sanda bacci ya d'auketa sai taga Abu Turab a gabanta ya sa hannu ya shake mata wuya, dole ta tashi daga barcin.
Wannan abu ya dameta.

  Da safe ta shirya tsaf dan ta gama yanke hukuncin yin komai da Abu Turab zai umarta na lefensa har ta samu a zo bikinshi ita kuma ta sa Hisham ya aiwatar da abinda ya dace.

    Sai yamma ta samu nutsuwa dan tana ta yin aike.

  Ta zuba abinci zataci kenan aka sanar da ita zuwan Abu Turab.
Ta rasa dalili duk sanda taji zuwansa kwanan nan sai taji gabanta na fad'uwa.

  Mikewa tai ta gyara jikinta dan batasan ya fahimci wani abun.
Zama tai irin zaman data saba.
 Turab ya shigo sannan ya gaisheta.
Amsawa tai cikin isa sannan tace " ya akai?"

  Murmushi ya sakar mata yace " na d'auka farin ciki zakiyi da ganina? Banji dadi ba ganin ba kiyi farincikin zuwana ba."

 Tace " ina fa? Ka taba ganin inda uwa tayi bakin ciki da zuwan d'anta?"

  Yace " haka ne fa kuma, ya an fara had'a lefen?"
 Ta kalleshi sai dai batace komai ba.
 Yace " Jiya naga Khadija ai, nan tazo ko ganina tazo yi kadai?"

  Magajiya wani abu ne yazo mata ta kalleshi tace " gunka ta fara zuwa kafin tazo nan ko?"
 Turab ya kalleta dan bai fahimceta ba, tace " ai na sani, dama ni nasan yarinyar nan da ba ruwanta ba yanda za'ai tazo min da wannan banzan zancen."

  Turab ya fahimcu Khadija magana tai da Magajiga wanda da alama abin ya sosa ranta.
 Yace " hmmm ai banyi tunanin wannan abin zai b'ata miki rai ba......"

 Magajiya tai dariya kadan tace " kana tunanin in ka zugata karta auri saif zan amince dakai ne? Meye manufarka da neman had'a auran ta da Abdulmajid?"

  Sai yanzu ya fahimta baisan sanda yai wata dariya ba, Khadija? He can't believe that naive girl can......
 Magajiya ce ta katseshi da cewa " In har kanasan Sirrin mahaifiyarka da kuma auranka ya yiwu karka kuskura ka kara sa Khadija cikin al'amuran mu."

  Turab ya kara murmusawa yace " me? Akwai wani dalili ne dazai hana auransu?"

  Idanu ta zaro tace " baka da hankali ne?"
 Ya dan tabe baki yace " ban fahimta ba? Akwai dalili ne?"

  Magajiya ta kalleshi tace " ba wani dalili kana san ka hadasu aure bayan ba san juna suke ba?"

  "Ooooo soyayya? Banaji dama a aure irin namu ana neman soyayya, kinsan da haka kike neman had'a Abdulmajid da Gimbiya? Hmm banaji kema auran so kikai."


  Mikewa tai da sauri tai wani murmushi wanda yake iya lab'anta tace " in ma hakan ne ina tunanin bakada hakki akan auransu, Khadija da Abdulmajid ina tunanin duk 'ya'yanmu ne basuda had'i dakai."

  Turab ya jinjina kai yace " kuma haka ne fa."

  Tace " ba sai ka kara zuwa bangarena ba, in na gama had'a lefenka zan aika ma uwarka ta gani."

  Ta juya tai ciki.
 Turab ya bita da kallo.........




*TURAB
? *KAINUWA*?
     ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ??‍♀*

*63*


Kallansa tai tare da yin ajiyar zuciya tace " wai ni Abdulmajid mai na tsare maka ne?"
  Kallanta yai sai dai baice komai ba, tace " saboda kai yanzu ko gaida Umma Basira ba na iya yi, na fadama banaso dan Allah ko ana so dole ne?"

  Kai ya rangwada gefe ya sakar mata wani lallausan murmushi yace " Mairo inaso inga kina fada, kyau yake miki."

  Rasa ma mai zatace tai ta saki baki cikin takaici tace " Dan Allah nidai na rokeka ka kyaleni."

  Abdulmajid ya matso hakan yasa tai baya da sauri dan ta san halinsa.
  Sai da takai jikin bango sannan tace " matsa menene hakan?"

  Abdulmajid fuskarsa a had'e ya sako fuskarsa saicin kuncinta.
 Tsoro yasa tasa hannu biyu a kirjinsa ta turashi.
 Hannayenta ya rike yace " Mairo sai yaushene zaki daina wahalar dani?"

  Gabanta ne ya tsananta fad'uwa, ga dare ne soron ba haske, tace " ban fahimceka ba, wahalar dakai name?"

  Jawota yai saura kiris ta had'u da jikinsa gashi ya rike mata hannaye duka, yakai bakinsa saicin kuncinta kamar wanda zai sumbata, da sauri ta runtse idonta cikin tsananin fargaba tare da sa kafa ta taka mai kafarsa.
 Ko gezau baiyi ba sai dayai bakisa daf da kuncinta sai kuma ya saki dariya yace " Mairo kinganki kuwa?"

  Gabanta sai wani irin fad'uwa yake ta kalleshi, hannayenta ya saki yana cigaba da dariya yace " sry, wlh ba abinda zan miki kawai so nake naga yanda zakiyi."

  Lab'enta na kasa ta ciza sannan ta sa kafarta ta kara taka  kafarsa da karfi.
 Kara ya saki sannan yai baya da sauri yace " Mairo amma dai ke wlh da a india kike da film zakiyi, boss zaki zama."

  Harararsa tai tace " Allah Abdulmajid ka kiyayeni."
 Kansa ya shafa yace " ba laifi ai in namiji ya kiyayi matarsa."
 Ta makamai wata hararar tace " mijin tace kawai."
 Ta fada tare da juyawa zatai gaba.
 Gabanta yasha da sauri yace " Sai da safe, gobe zan sake magana a fada dan na gaji da jira."

  Tana kokarin bashi amsa yai gaba, tsaki taja sannan tai gaba, haushinta ma da mahaifiyarta ta sata ta fito da ai ta ce ko yazo bazata sake fitowa ba.
 Tana shiga ta wuce d'akinsu ta fada kan gado.
 Ummanta ce ta leko tace " kin dawo?"
 Mairo tace " Umma ni dai ko yaran nan ya dawo dan Allah karki kara cewa in fita, ni wlh bana so."

  Tace " Mairo shifa aure da kike gani ba wai mutum ne yake zab'awa kansa ba, babu yanda za'ai wani ya auri matar wani, haka kuma babu yanda za'ai wata ta auri mijin wani, duk wanda kika ga sunyi aure to fa dama akwai aure a rubuce a kaddarar rayuwarsu, inhar yaran nan ba mijinki bane cikin ruwan sanyi sai kiga kun rabu bawai fadanki bane zai sa ku rabu."

 Mairo ta turo baki, tana san magana taga Umma tayi waje, kara komawa tai ta kwanta a fili tace " Ya Allah!"


   ************
  Magajiya kuwa a daren yau ta tsaya sosai tayi tunanin al'amarin dake faruwa, yanzu ta fahimci Abu Turab bai san sirrinta na Abdulmajid ba, tunda a tunaninta da hankalinsa bazai yi tunanin had'a auren Abdulmajid da Khadija ba in har yasan wannan sirrin, tunda yasan ba abu bane mai yiwuwa.
 To wanne ya sani? Maganin nan ta tuno da abinda ya fad'a mata a lokacin, mikewa tai zaune tace " yasan sirrin ba Hajiya magani." da alama wannan shine sirrin da ya sani.
 Washegari da sassafe tasa aka kira mata wannan yarinyar, yarinyar ta shigo jikinta sai tsuma yakeyi, ta shiga ta zauna a falon da ba kowa.
 Magajiya ta shigo sanye da rigar bacci dan ko wanka batai ba, karfe 6 ne na safe.
 Magajiya ta kalleta tace " ina abinda aka baki?"
 Da sauri tasa hannu a lalitarta ta d'auko maganin.
  Magajiya ta kalleta tace " akwai wanda ya kamaki da wannan maganin?"
 Kai ta girgiza alamar a'a tace "ba kowa, ina kuma zuba mata kullum."

  Magajiya ta kalleta tace " kin tabbatar? Kinsan dai mahaifinki na cikin wani hali, kuskurenku d'aya zai jawo masa ajali."

  Da sauri ta sunkuya tace " tuba nake rankiya dade amma ba wanda yasan maganar nan."
Magajiya ta amshi maganin sannan tace" jeki."
 Mikewa tai tare da karayin godiya.
 Tana fita tai ajiyar zuciya, kalan Abu Turab ta tuna sanda ya ce karta kuskura ta nuna yasan komai, sannan ya bata maganin saboda gudun zargi."

  Magajiya tai shiru bayan ta fita, tace " to me yake nufi? Ta tabbatar akwai wani sirri da ya sani, sannan ko baisan maganin nan ta hannun yarinyar nan ba ta tabbatar yasan da zancen maganin, dan tabbas irin wannan ne a hannunsa.

  Ajiyar zuciya tai tace " mai ya sani yaran nan?"
 Tun kafin asiri ya tuno gwara ta salwantar da maganin, sannan yarinyar nan ta turata wani garin ita da mahaifinta.
 

*********

  Abu Turab zaune kusa da Hajiya wannan yarinyar tanamai bayanin komai, ya jinjina kai yace " hakan yayi, sannan ki shirya zan canza ma mahaifinki asibiti sannan ke kuma ki koma ki kula dashi, kafin lokacin da zaki bada shaida yayi."
 Tace " to."
 Turab ya kalli Lantana yace " Lantana akwai wacce kika yarda da ita a gidan nan?"
 Tace " eh akwai wata yaruwata da aka kawo."
 Turab yace " ki dawo da ita nan sannan ke ki koma gun Umma dan kar Magajiga ta fahimci wani abin, ina tsoron kar ta ma Hajiya illa ta wani gun."
 Lantana tace "to."
 Mikewa yai ya wuce bangarensa, yana shiva Garzali ya sanar dashi kiran da Mahaifiyarsa take masa.
 Turab ya juya.
 Sai da ya gaisheta sannan yace " Umma gani."
 Ta kalleshi tace " Abu Turab me yasa baka zuwa gub Mahaifinka?"
 Kansa na kasa bai d'ago ba baikuma ce komai ba.
 Basira tace " Mahaifinka na nemanka, yana san ganinka."
 To, kawai yace, sannan ya kalleta yai murmushi yace "zanje Umma, shikenan?"
 Fuska ta saku tace " ko kaifa?"
 Kansa ya sunkuyar yana murmushi, tace " Ya maganar Mairo?"
 Kallanta yai sannan yace " Hmmm Umma yanzu ba wannan bane matsala, sai dai insha Allah shima ba wani matsala."
 Tace " to, amma Turab nidai kayi a hankali da Magajiya dan wlh wannan matar bala'i ce."
 Yace " Nasani Umma, bala'in gaske ma kuwa, sharrinta ya wuce duk yanda kike tunani, zan sanar dake komai sai dai ba yanzu ba."
 Tace "shikenan."

  Sai yamma sannan ya nufi gun mahaifinsa, sai daya gaisheshi sannan Sarki ya kalleshi yace " Turab ina ka shiga ne haka?"

  Turab yace " ina nan, abubuwan ne sukai yawa." kansa na kasa yai maganar nan.
 Sarki ya kalleshu yace " kasan tunda ka shigo baka kalleni ba?"
 Turab a ransa yace " ina na isa? Nima ai mai laifine tunda nima na b'oyema sirrin nan "

 Katsemai Tunaninsa yai da cewa " na aika abin bukatu na lefen."
 
  Kansa na kasa yace "to, angode."

  Mamaki ya kama mai martaba yace " Umarni sarki zai baka ka d'ago ka kalleshi."

 Turab ya d'an runtse ido kad'an sannan ya d'ago a hankalu ya kalli Mai Martaba.
 Sarki yace " Turab menene?"
 Abu Turab ya kakaro murmushi yai sannan ya girgiza kai yace " ba komai, sai dai jikin Hajiya da ba dadi, ne yasa baza'a kaita asibiti ba a kwantar da ita?"
 Ajiyar zuciya yai sannan yace " Hajiya mace ce mai masifar kishin al'adarta, ko sanda za'a kaika asibiti sai datai ta fada wai akan me za'abar maganin hausa a koma maganin bature? Ita ko mutuwa zatai bata yarda a kaita wani asibiti ba."
 Turab yai shiru sannan yace " Amma Abba yanayin jikinta ne ba dadi."
 Yace "haka ne ni kaina har banasan zuwa dubota."
 Turab yad'anyi shiru kafin yace " Ko za'a maidata cikin gari? Sai a tafi nata da masu kula da ita?"
 Mai Martaba yace " Turab kenan, nan d'in ba'a kula da ita?"
 Kai ya girgiza alamar a'a yace "ba haka bane kawai dai gani nake zatafi jin dadi in tana can."

  Sarki ya kura mai ido ya tabbata akwai dalilinsa ma fad'ar haka, sai dai baisan menene ba, yace " shikenan, zansa a maidata a satin nan."
 Turab yai saurin cewa " a maidata gobe, dan Allah."
 Sarki ya kalleshi yace " Akwai abinda kake b'oyemin ko?"

  Turab yai kasa dakai, Sarki yace " na sanka da taurin kai tun kana yaro, jn har bakaso fad'ar abu ba to fa bazaka tab'a fada ba, zanyi yadda kace sai dai ka tabbatar ka sanar dani abinda ke faruwa nan kusa ba da dadewa ba."
 Yace "godiya nake, sannan insha Allah zan sanar dakai."

  Nan ya mike ya fito.

 Hakan kuwa akai washegari da safe a ka d'auke hajiya, wanda ba wanda ya sani sai Turab sai Sarki da masu d'aukan, Jakadiya kuwa sai dariyar mugunta take kasa kasa dan ta tabbata akwai wani abu da Turab yake shiryama Magajiya tunda taga ta zake tana shirya mai lefen auren da tace ko zata mutu bazata bari ayishi ba.


  *"*******

  A duk bayan kwana biyu Turab suna waya da Bilkisu, shakuwa ce a hankali take shiga tsakaninsu, duba da yanayin gidan da suka taso da kuma aminta ta yarda dake tsakaninsu.

  Magajiya ta shiga tashin hankali, ta rasa wannan yarinyar wato Zakiyya sannan an d'auke Hajiya wanda ba wanda yasan inda aka kaita, da farko ta aika gidan cikin gari sai dai bata nan, shikansa Turab baisan inda Mai Martaba ya kai ta ba.
 Sai dai yasan Sarki ya fahimci Uwarsa na cikin wani halin ga tsufa, ya san hakan ne yasa ya d'auketa.
 Magajiya ta gama had'a lefe wanda ta yishi na gani na fada dan ita d'in yar kwallisa ce ta gaske, an kashe kudi kam, hankalin Magajiya a kwance take had'a kayan nan, dan itada Hisham sun gama tsara yanda zasu shirya komai.

  A b'angaren Turab kuwa jira yakeyi a tsaida rana dan shima ya fara aiwatar da nasa shirin kamar yanda suma suke nasu shirin, Magajiya ta gama yanke hukunci akan Halaka Turab dan wannan ita kadai ce hanya, ganinsa ma batasanyi sam.


  An tsaida lokacin biki nan da wata d'aya.

  Magajiya ta sa Hisham ya hana Khadija fita, yanzu ko nan da nan ba a barinta fita.


  Wannan kenan.

  

? *KAINUWA*?
     ......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

   

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*Na Ayusher Muhd??*

  *64*

    Abdulmajid yau tun safe yai wanka tsaf ya shirya ya nufi bangaren Sarki, Mai Martaba ya bashi izinin shiga.

  Ya dade rabon da ya keb'e da mahaifinsa irin haka, shiga yai a hankali kamar ba shi ba sannan ya gaisheshi.
Sarki ya kalleshi yace " Ya akai?"
Ba shakka har cikin ransa sai dayaji ba dadi, ya akai? Abinda uba ya kamata ya fara tambayar d'ansa kennan sannan kuma fuska a d'aure?

    D'agowa yai jiki a sanyaye yace"dama maganar Mairo ne....."
Katsehi Mai Martaba yai yace " maganar Mairo a me kenan? Kana tunanin kayi daidai a zuwa cikin tsakiyar fada kace kana san auran Mairo? Bayan ni naka sameni ba?"

  Abdumajid yai shiru, Sarki yacigaba " Na rasa wani irin hali ga reka, gani kake komai naka ne kamar Magajiya ko?"

  Abdulmajid ya d'ago idanunsa sun ciciko sosai da kwalla yana tsananin ganin kwarjinin mahaifinsa amma ya daure yace " menene laifina? Abba ni ba d'anka bane? Me yasa komai sai dai Abu Turab? Ka samomai mata yar mulki, gashi yanzu har an tsaida rana ana ta shirye shirye, nine fa babba ba shiba, amma bance komai ba, sannan nace ga wacce nakeso itama an kasa bani, ko itama Abu Turab din za'a ba?"

  Sarki ya kalleshi yace " Kana tunanin duk abinda kukeyi kai da mahaifiyarka sani ne banyi ba ko ka d'auka karfina tafi? Sanda kukama Turab sharri kana tunanin bansan ku kuka aikata ba?"

  Abdulmajid yai shiru, sai dai zuciyarsa na tafasa da tsanar Abu Turab tsantsa.
Sarki yace " Maganar auren Mairo ni har yanzu ban yanke hukunci ba, zamu zauna da mahaifinta muga wanda ya dace da ita."

  Abdulmajid ya d'ago sai dai baice komai ba amma kana kalla idanunsa zakaga tsantsar b'acin rai.
Mikewa yai yama mahaifinsa sallama ya fita.
Cikin tsananin takaici ya nufi bangaren Magajiya.
Tana zaune tana shan madarar shanu, wanda takesha duk safiya dan gyara mata fatarta.
  Ko sallama baiyi ba ya afka ciki.

Magajiya ta kalleshi har ya zauna, baigaisheta ba yace " Umma nikam na gaji da abinda Abba yakemin, wlh zan d'au mataki a kaina."

  Magajiya bata daina shan madarar ta ba ta kurb'a sannan tace " me ya faru?"
Abdulmajid ya kalleta yace " Umma ni kam na tsani yaran can, me yasa ne komai nake so a rayuwa sai ya kwacemin?"

  Tace " karka damu ka kara hakuri na wasu 'yan lokuta, sannan ka shirya nan da wani satin dan zuwa ganin yar sarkin daura."

  Kallanta yai yace " inganta in mata me?"
Kallansa tai tace " tambaya kake?"
Kansa ya maida kasa sannan yace " Amma Umma kinsan ai ni M......."

  Kallan data masa ne yasa yai shiru, ajiye kofin tai sannan ta juyo ta kalleshi tace " me yasa kake neman canzawa? Da baka tambayata akan abinda na sharadda maka amma yanzu naga alama yar iskar yarinyar nan tana neman canza maka hali, a kanta ka fara neman canzamin."

  Kansa na kasa yace " Amma Umma."

  Mikewa tai tsaye tazo kusa dashi ta sa hannu a kafadarsa tace " Abdulmajid ka zama mai bin duk abinda na sharadda maka, komai da kakeso a rayuwa ni zan baka, in nace komai ina nufin komai d'in, kai dai kabi ni."

  Shiru yai, ita kuma tana gama magana ta juya tai ciki, ya dade a zaune kafin ya mike ya fita.

  ********

  Turab yau da kansa yaje fada ya dade a can sai dayaga fitowar Waziri sannan shima  ya mike ya fito.
Yana kallan Hisham ya shiga mota ya wuce gida, shima ya shiga tasa motar wanda dama ya sa Garzali ya jirashi ya bi bayansa.
  Hisham na kokarin shiga gida, Turab ya fito da sauri ya biyoshi.
Hisham na shiga aka cemai wai yayi bako, yayi mamaki sai dai bai yi tunanin Turab bane yace " ace ya shigo."

   Turab ya shiga cikin falo ya zauna, sannan Hisham ya shigo.
Mamaki ne ya kamashi na ganin Abu Turab.
Karasawa yai ya zauna yace "Yarima lafiya?"
Turab ya gaisheshi sannan yace " biyoka nai ai daga fada."
Hisham yace " wani abin ne ya faru da baka sanar dani a can ba sai da ka biyoni gida?"

  Turab yai kasa dakai yace "ai yanzu a matsayin siriki mai neman 'yarka nazo."

  A zabure ya kalli Turab cikin raahin fahimta yace " me kake nufi?"
Turab ya d'ago idanunsa yace " zuwa nai maka da abinda zai taimakeka ya kuma taimakeni."

  Hisham ya bishi da kallo, Turab yace " khadija zaka auramin kaga nan gaba ko da komai naka ya kare a kalla 'yarka tana da matsayin da zata kwace ka."
  Ran Hisham ya b'aci yace " Ta karemin kamar ya?"

Turab ya d'an furzar da iska irin damuwar nan yace " Badai kana tunanin in Abdulmajid ya hau mulki Magajiya zata barka da matsayinka ba ko ta barka kayi yanda kakeso da d'anta ba?"

  Hisham yace " wannan banaji yana daga cikin damuwarka."
Turab yace " Hake ne sai dai inaso kayi tunani sosai kaga mafakar da zata bul'ema, ka fini sanin kanwarka ka kuma san halinta, kana tunanin zata barka ko shawara ne kaba Abdulmajid? Inka bada ma shawarar kana tunanin zata bari yai aiki dashi?"

  Hisham ya mike tsaye cikin takaici yace " koma menene damuwatace ba taka ba, sannan kana tunanin ni zan kai 'yata a ta biyu gidan wani? Sannan ni ban taba tunanin had'a zuri'a dakai ba kuma bazan yi ba har abada."

  Turab yace "kumafa gaskiya ka fada, ni kaina bansan me yasa nazo ma da zancen ba, inaso ka sanar da 'yarka hukuncinka saboda mu hakura da juna."
Ya mike yamai sallama ya fito daga falon.
Yana fita yai wani murmushin gefe yace " nazo neman iri ne na auran 'yarka? Inji wa? Kai dai na tabbatar abinda na saka a kwakwalwarka ya shiga zai kuma fara aiki."
Ya juya, Karo suka kusa yi da Khadija wacce ta taho da tirw daga kitchen rike da tire wanda yake d'auke da juice.

  Kaucewa tai saboda ganin zata bugeshi, garin kaucewa bata kula da kafarsa ba ta taka ta tafi kamar zata fadi, da sauri ya rikota ta baya.
  Ajiyar zuciya tai da karfi dan tabbas ta d'auka fad'uwa zatai.
Juyowa tai a hankali, nan taga wanene idanunsu ne suka had'u da juna.
Sai da 'yan wasu dakiku suka wuce a haka kafin Turab ya daure yace " Baki bige ba?"

  Gyara tsayuwarta tai sannan ta kalleshi, a hankali ta d'aga kai, kallanta ya sakeyi yaga ta rame, ita kuma tana san tambayarsa abinda ya kawoshi, a tare sukace "Nace me......"
Ganin yanda sukai maganar a tare basu san sanda sukai dariya ba, Turab yace " fara magana."
Kallansa tai tace " a'a ka fara." yana kokarin tambayarta yaji murya ance " Khadija me kikeyi anan baki kai ba?"
Juyowa tai ta kalli Ummanta tace " yanzu zan kai."
Kallan gun yai, mahaifiyarta ya gani, suna tsananin kama da Khadija sosai, da ace itace Abdulmajid to fa yasan tabbas zargi zai bayyana.

    Gaisheta yai sannan ya fita, Hisham kam Turab na fita ya kumburo baki yana tunani, tabbas dolene ya fara jan d'ansa a jikinsa dan sai yanzu ya farga ya san Magajiya sarai tabbas gaba ma neman ma hanashi zuwa gidan zatai.

  Ko tabin bayan Khadija data shigo baiyi ba ya shiga cikin d'aki.

  **********

   A can kano kuwa shiri sosai akeyi na auren Gimbiya, auren da babu kamarsa agunsu domin ita kadai ce 'yar sarki mace, shiri ake sosai wanda yasa kishiyoyin Fulani jin kishi dan komai ita keyi, Bilkisu kuwa an shiga gyara, dama ba zancen zance dan in suka fara gyaran jiki to ango bazai ga amarya ba saboda so ake inya tashi ganinta yaga kamar ba ita ba.
Turab kam na kiranta sosai suna waya.

  

   Hisham ya gama tsarawa dan yau yana tashi daga fada ya nufi bangaren Abdulmajid........

: ? *KAINUWA*?
     ......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

   

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

_Sakon ta'aziyya gareki kawar arziki BillynAbdul Allah ubangiji ya jikan Mahaifinmu yasa Aljanna ce makomarsa.....(Ameen)_

*Na Ayusher Muhd??*

_Masu san karanta Matar Fayrouz na AsyKhaleel da sauran litattafanta su duba ta a wattpad @asykhaleel.??_

  *65*

    Hisham yana fita yai bangaren Abdulmajid, baya nan ma sai ya zauna a falo ya aika a nemoshi, yace " in an ganshi kar acemai shine yake nemansa.

  Abdulmajid ya fito daga bangaren Magajiya kenan aka sanar dashi yanada bako.

  Yana shiga yaga Hisham, ya karasa ya zauna sannan ya gaidashi, Hisham ya washe baki yace " Abdulmajid sai ka ganni ko?"
Kallansa yai yace " Kawu me ya kawoka? Naga baka taba zuwa bangarena ba."
Hisham yai murmushi tare da kallansa yace " yauma wucewa nazoyi sai na fahimci ban taba shigowa ba."

  Kai ya d'aga kawai baice komai ba, yau ce rana ta farko da suka kebe su biyu haka shiyasa yakejin abin wani banbarakwai kamar ba kawunsa ba.
Hisham ya kalleshi yace " ya maganar auren naka da Mairo? Har yanzu Magajiya bata sauko ba?"

  Hisham ya kalleshi kallan mamaki, cikin rashin fahimta yace " eh kasan halin Umma ai "
Hisham yace " karka damu inaso kome ke damunka ka dinga sanar dani, ni zan yi iya kokarina wajen ganin na taimaka maka, Magajiya bazata taba bari ka auri yarinyar ba, sai dai ni zan san yanda zanyi in har kanasanta."
  Ya kasa fahimtarsa, mamaki yake na yanda yake mai, Abdulmajid yace "Nagode, amma kana tunanin Umma zata yarda?"
Hisham yace " karka damu, kai daj ka yarda dani, duk wata matsala taka ka dinga zuwa kana sanar dani, ni zan taimakeka akan komenene, kawai dai ka dage kar ka taba bari Turab ya kwacema mulkinka."

   Abdulmajid kallansa kawai yakeyi, Hisham ya matso yace " inaso a sati ka dinga zuwa gidana cikin gari, zansa Maman Khadija ta dinga shiryama duk abincin da kakeso, kaga sai kazo ayi hira, hakan zai ragema kewa ya kuma kara mana zumunci."

  Shekarata nawa da haihuwa? Da can ba'ai zumuncin ba sai yanzu? Abinda ya fada kenan a ransa, sai dai a fili kallan Hisham yai kawai baice komai ba.

  Hisham ganin yanda Abdulmajid yake yi yasa ya mike yace " ni zan koma sai mun ganka ko ran Juma'a ko asabar,sannan karka fadama Magajiya zuwana da zancen da mukai, ka santa."
Uhm hmm, kawai yace.
Hisham yai waje.
Kallansa Abdulmajid yai sannan ya mike yai ciki.

Hisham kuwa na fita ya jinjina kai yace " a hankali zan jawoka jikina, ai tsakanin Uba da d'a sai Allah."

Yana fitowa yai wuf yai kwana ya wuce, Abu Turab wanda yana shiga bangaren aka sanar dashi zuwansa ya fito dama yana jiran fitowarsa.
Yana hangoshi ya taho kamar irin bai ganshi ba d'in nan, Hisham na hangoshi ya tsaya tare da neman inda zai b'uya, dan dai girma ya kamashi ne amma da gudu zai saka, juyawa yai da sauri dama abinda yasa ya bi ta baya saboda bangaren Magajiya ne ta gaba, yana tsoron kar aganshi.
Abu Turab yana kallan ya juya yai wani murmushin jin dadi.

Hisham ya shiga bangaren Magajiya.
Tana kishingide ta bashi izinin shigowa.
Hisham ya shiga yana dariya yace " Magajiya ikon Allah hutawa kikeyi ne?"

Wani banzan kallo tamai hakan yasa yai shiru sannan yace " Magajiya barka da yamma."

  Idanu ta d'an juya bata amsa ba, zama yai sannan yace " na lekone mu gaisa."
Tace " ka sandai muna da abinda ya kamata mu shirya na ranar auren yaran nan ko? Ga lokaci yana matsowa amma sam ka ki shigowa ayi magana."

  Yace " haka ne, nima ai ba mantawa nai ba, yanzu ya kikeso ayi?"

Ta bud'e baki zatai magana aka sanar da ita zuwan Abu Turab.

  Fuska ta canza tare da yin wata karamar kwafa, ba shakka itakam ta gaji da jin ko sunan yaran nan.
Shigowa yai ganin batada niyyar bashi izini.
Yana shigowa yace " Umma bakiji isowar d'anki bane?"

  Murmushi ta saki sannan ta koma ta gyara zamanta tace " banyi tsamannin zuwan ka bane."

  Zama yai sannan ya kalli Hisham yace " da alama sirri kukeyi da Kawun namu au ko ince Babana."

  Magajiya ta had'e fuska, shima Hisham yaci mazu, Turab ya d'aga hannayensa yace " Tuba nake Babana kar in bata ma sirikin nawa rai kafin abani Khadija."

  Magajiya ta kalleshi cikin takaici tace " kai dai ka nutsu akan auranka da Bilkisu ka daina wata banzan magana wacce bazata amfaneka ba."

Turab yace "Haka ne Umma, nayi..." yai alamar zip a bakinsa.
Kallan Hisham yai yace "Amma waziri kamar daga bangaren Abdulmajid na ganka ko?"

  Hisham ya zaro ido, da sauri ya kauda kai gefe irin mara gaskiyar nan yace " a'a wucewa nai ba shiga nai ba."

  Turab ya jinjina kai yace " kayi kokari sai naga kamar tacan yafi nisa."
Hisham yace "Hmm." da sauri ya kuma cewa " bari nikam na koma." ya fada dan kawar da zancen.

Turab yace " a'a bari ni na tafi da alama Umma akwai abinda zata cema, da na d'auka ma d'anka kazo ba gun Umma ba shiyasa na shigo."

  A tare gabansu ya amsa da rass, Magajiya cikin tsananin tsoro tace " D'ansa?"
Hisham kam har zufa ta fara afko masa, Turab yasa dariya yace " menene hakan? Da ba d'ansa bane?"

  Ai tuni Hisham kansa zuwa wuyansa ya cika da zufa, Magajiya kam a ranta tace "shikenan ta faru ta kare."
Turab ya karayin dariya yace " lalai Umma ba kara? Na d'auka d'anki a ka'ida d'an Waziri ne saboda jininku d'aya."

  Bakin Hisham har rawa yake gurin cewa " sosai ma haka ne."

  Magajiya kam idanu ta bud'e ta kurama Turab tana kokarin ganu abinda ke b'oye a ransa da gaske abinda yake nufi kenan?"
Turab ya kalleta yace " Umma lafiya? Naga kinata kallo na."
Idanu ta d'auke tare da cewa " ba komai, ya shirye shiryen biki?"
Yace "Thanks to you, komai na tafiya daidai."
Kai ta d'aga tace " yayi kyau."
Turab yace " Ayi hira lafiya."
Ya juya ya fita, yana fita ya kara kallan kofarsu ta gefe, "Haka ne nima ba mantawa nai ba, yanzu ya kikeso ayi?" kalaman Hisham da yaji sanda ya iso gun ne ya kara dawo mai, tabbas akwai wani mugun abu da suke kara shiryawa, ya tabbatar.

  Juyawa yai ya fita.

Yana fita Hisham ya saki wata ajiyar zuciya ya kalli Basira yace " kinji hanjin cikina?"

Magajiya ta kurama kasa ido kafin tace " Inaji ya kamata mu maida Khadija kano."
Yace " Kano? Kamar ya?" 
Tace "kasan Mahaifiyar Saifullahi ta kirani jiya da daddare tace wai Khadija tace ma Saif akwai wanda takeso, dolene mu maidata kano in taga bata gani yarancan sai ai auren, inba haka ba intaga mutuwarsa abin zai baci, ka san dagar da akai da ita sanda tana karama ma bare yanzu."

  A ransa yace " ni da 'ya'yana sai dai a dinga sharada min abu, da girmana amma a dinga kaskantar dani"
A fili yace " hakan yayi."
Nan suka cigaba da tsarinsu.....

*********
    Basira zaune a falonta, gabanta kuma leda ce irin mai karfin nan, da alama kaya ne a ciki. 
  Amsa sallamar Turab tai sannan ta kalli kofar da ganin shigowarsa.
Turab ha shigo sannan ya zauna yace "Umma gani."
Kallansa tai tace " Dama aikenka zanyi."
Kallanta yai sannan ya kalli ledar gabanta, sai kuma yar murmushi yace "Gun 'yarki?"
Tace " eh, Mairo zaka kaimawa, sa wa nai a d'inka mata na bikinka."

  Murmushi yai yace "Umma kenan."
Kallansa tai tace " Amma baka tunanin hakan yazo da kamar wulakanci ko?"
Turab yace "wulakancin me?"
Tace "  Na kaimata kayan da zata sa a bikinka bayan akwai wata a kasa."

  Turab yace " Lalai Umma, ni bansan wannan ba ki tambayi Lanta....."
Da sauri yai shiru tare da kallanta, Kallansa tai itama tace " Turab har yanzu ba labarin inda Hajiya take? Bare Lantana?"
Kai ya d'aga alamar eh.
shiru sukai ganin haka yasa ya jawo ledar yace " Zanje in anyi Magrib."

  *********

  Garzali ne ya kaishi, yana cikin mota Garzali ya fito ya aika a kirata.
Ta gama kunce lale kenan wanda tayi a hannunta, aka sanar da ita zuwan Turab.
  Wankewa tai dama ba sallah zatai ba ta saka hijab ta dan murza hoda sannan ta fito.
Tanaji 'yayan kishiyar babarsu na  mata habaici, ko ta kansu bata biba tai waje.
  
  A jikin soro ta tsaya dan bata fita waje zance, ka'idar gidansu ne haka.
Turab sai da ya hangota sannan ya bud'e motar ya fito, rike da ledar.

  Tundaga nesa take murmushi har ya iso, Kallanta yai sannan ya karasa cikin soro yace " Hajiya Maryam an fito?"
Kallansa tai tace " Yaya ina wuni?"

  Bai amsa ba sai cewa dayai " kwana dayawa?kin bata bat."
Fuska ta d'an rufe tace " wlh inasan zuwa gaida Umma magana ce banaso."
Leda ya mika mata yace " ga sakonki inji Ummanki."
Amsa tai tana murmushi tace " oh ni, me na samu?"
Yace " kayan bikin yayanki ta d'inka miki."

  Gani yai ta d'ago da sauri, sannan yanayinta ya canza, yace " Badai Umma tayi lefi ba?"
Ya ke tai tace " a'a."
Kallanta yai zai yi magana aka dallesu da fitilar mota.
A tare suka kalli motar, Turab ya sa hannu ya rufe idanunsa dan sam bayasan a haskashi irin haka saboda idanunsa.

  Mairo ta juya kai tare da jan tsaki.
Turab ta kalla ganin yanda ya rufe idanunsa yasa ta taho dan nufo mai motar.

Har ta iso sannan ya kashe, tare da fitowa daga motar.
Kallansa tai tace " Abdulmajid me ke nan?"
Kallanta yai fuskarsa a d'aure yace "me kike a can?"
Tace " ko ma me nakeyi banaji ya shafeka amma wannan dallenin da kai da fitila fa?"

  Kallan inda Turab yake yai bai amsa mata ba taga ya nufi inda Turab yake.
  Abdulmajid na zuwa ya d'aga hannu zai naushi Turab, Abu Turab ya sa hannu ya tareshi.
Kallo kallo sukai kafin turab ya sakar mai hannu sannan yace " ka kiyayi kanka da san duka, sannan ka kiyayi kanka da saurin hawa Da kuma kishi "

  Abdulmajid yace " Kai waye da zaka bani shawara?"
Turab ya kalleshi ba shakka yana tausayamai alokacin da yasan sirrinsa shiyasa baya neman fada dashi a wannan lokacin.
Mairo ce ta karaso ta kalli Abdulmajid, zatai magana Turab yace " Bari na wuce."
Ya karasa maganar tare da wucewa ta gaban Abdulmajid.
Biyoshi tai tace"Yaya kama Umma godiya."
Juyowa yai ya kalleta sannan ya kalli Abdulmajid dake tsaye yace " Mairo."
Kallansa tai bata amsa ba, yace " karki dinga zafaffama Abdulmajid."
Tace " Yaya na fadamai ba so nake ba, na rasa dalilin takurar."
Shiru yai tare da cigaba da kallan Abdulmajid yace " ba yanda za'ai?"
Kallan mamaki tamai tace " yanda za'ai me?"
Kai ya girgiza da sauri yace "ba komai."
Ya karasa mota ya shiga.

  Shiru tai tana kallansa har sukai gaba, ba yanda za'ai? Me yake nufi?"
Karasawa tai inda Abdulmajid yake.

  Kallanta yai yace " Mairo mai ya kawoshi?"
Ledarta ta nuna mai tace " abu ya kawomin, ko da wani abun?"
Abdulmajid yai murmushi yace " Mairo lalen ki yayi kyau sai kika fito kamar amarya."
Harararsa tai tace " kamar Ango ne ba amarya ba."
Dariya yai yace " in kika zama kamar ni Angon ki ai ba wani abin bane."
Baki ta d'an murguda tace " Ka manta."

*********
Turab kam kansa ya kama a cikin mota wanda yaji yana sarawa, yace " Ya Allah! Ka kawo komai da sauki, kada ka bani ikon cutar da wanda bashida hakki akan al'amarin nan, ka bani ikon aiwatar da komai yanda ya kamata.

Nace Ameen

*TURAB*
  

 ? *KAINUWA*?
     ......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

   

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*Na Ayusher Muhd??*

 _Haly(Mom Farhan) Allah ya kara lafiya yasa kaffara ne....Wish u quick recovery_

  *66*

   Abu Turab idanunsa ya bud'e a hankali ya shiga kallan d'akinsa kafin a hankali ya furzar da wata yar karamar iska daga bakinsa. 
  Sannan yasa hannu ya dafa gadon ya mike ya zauna, idanunsa ya rufe ya shiga karanto addu'oin safiya, kafin ya sauko daga kan gado.

  Yau saura sati 3 bikinsa, dayake gidan maza ne ba wani abu special ake aikatawa ba, an dai kammala ginin bangaren da zasu zauna da gimbiya.

  Saukowa yai daga kan gadon sannan ya nufi bandaki dan kama ruwa da yin alwala.

  Bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yai ta tilawar al-qur'ani har sai da gari yai haske, wannan al'adar haka yake yinta dan koyar wace ta ma'aiki S.A.W.
  Sai wajen karfe goma yaci abincin safe sannan ya fito.
 B'angaren Mahaifiyarsa yaje sukai 'yar hira kafin ya fito.
  Yana kokarin komawa bangarensa ya hango Baiwar da take kula da bangaren Abdulmajid wanda ya shine ya sakata a bangaren dan kawomai rahoto akan Hisham.
 Karasowa tai cikin hanzari sannan ta gaisheshi, tana yi tana kalle kalle.
 Turab ya kalleta yace " lafiya da safen nan?"
 Tace "banga d'an aike bane, dama Waziri ne ya zo yanzun nan, sannan rike yake da lefa katuwa, da ya shiga ciki na amshi laidar sai naga kula ce sannan ga kamshin abinci nan."
 Turab yace " yayi kyau, koma bakin aikin ki."
 Tace "Yarima Abdulmajid ya......"
 Dakatar da ita yai yace " na tambayeki rayuwar Abdulmajid? Ko kuwa a sanda na baki aikin nan nace ki dinga kawon zancensa? A iya sanina ce miki nai kawai in Waziri yazo ki sanar dani."
 Tace " Tuba nake ranka ya dade."

  Turab ya sallameta sannan shikuma ya shiga ciki.
 A bakin kofa ya tadda Garzali da alama fita zaiyi.
 Turab ya kalleshi yace " in zaka fita ka biya bangaren Sarki gub Jakadiya."
 Garzali ya kalleshi yace " Jakadiya?"
 Turab yace " ka sanar da ita Hisham na bangaren Abdulmajid."
 Garzali cikin rashin fahimta yace " to." dan bazai iya tambayarsa dakili ba.

  Garzali ya garzaya yaba Jakadiya sako.
 Ita kanta kallab Garzalin tai tace " abinda yace kawai ka fadamin kenan?"
 "iya kacinsa kenan."
 Ya juya.

 Jakadiya tai shiru tana kara maimaita kalmar kafin daga baya ta fito.
 Bangaren Magajiya ta nufa, Magajiya na karyawa ta shigo.
 Sama sama ta amsa gaisuwarta tanayi kamar bataso.
 Sannan tace " me ya kawoki?"
 Jakadiya ta miko mata leda tace " maganine aka kawo na gyaran fata."
 Magajiya ta kalli maganin dake cikin farar leda sannan ta kalleta tace " ni ce miki akai ko wani kare da doki ya bani magani amsa nake?"

  Jakadiya tace "badai haryanzu baki hakura ba?haba Hajiya Magajiya, matar sarki, uwar sarki, kakar sarki."

 Magajiya ta wani juya kai sannan tace " Me ya kawo ki? Dan na tabbata ba wannan bane kadai abinda ya kawoki."
 Jakadiya ta dan shafi fuska sannan ta matso tace " hmm dama na kasa fahimtar wani abu ne, Na rasa me yasa nake ganin Waziri yanzu yana zirya bangaren yarima Abdulmajid."
  Magajiya ta kalleta tace " ban gane ba.."
 Jakadiya tace " Tuba nake Ranki ya dade amma nifa hankali ya kasa kwanciya da zuwansa."

  Ruwan da ta gama sha ragowar cikin kofun tai kamar zata zubo mata har ta rufe idonta ta d'auka ita zata zuba ma.
 Magajiya ta ajiye cup din sannan ta kalleta tace " najiki inaso kuma ki fita."
 Jakadiya ta had'iyi yawu sannan ta mike tai waje.
 Magajiya tai shiru tana tunani, dama kwanaki Turab ya sanar da ita ya ganshi amma shi ha musa, sannan an fada mata rannan an ganshi, sannan yau Jakadiya ta fada mata, me Hisham yake tunani? Tamai magana akan kai Khadija Kano ma ya mata burus sannan yanzu ya fara kewayewa yana zuwa gun D'anta?

  Turab kam zama yai a falo yai zama cin abinci sannan ya rufe idanunsa, yana kada 'yan yatsun hannunsa, Magajiya! Ki jira juyawar bayan duk wani na kusa dake, a hankali zan ruguza miki duk wani abu da kike takama dashi....Slowly ya saki murmushi sannan ya bud'e idanunsa, ta ya zakuyi kisa ku cigaba da zama kamar wad'anda basuyi komai ba? Kun halaka rayuwar mutane dayawa amma ko tunawa bakwayi.

 Hannunsa ya dunkuke sannan ya kalli bakin kofa cikin tsananin kunar rai.
********

Abdulmajid na mikewa daga kan gado aka sanar dashi zuwan Hisham, baiyi mamaki ba dan ya kula yanzu wata gulma ce take damunsa, inba haka ba da can me yasa bai mai haka? 
 
 Sai dayai wanka sannan ya fito.
 Hisham ya sa an jeramai abincin dayasa matarsa tai, ita kuwa tanayi tana farinciki dan yauce rana ta farko da zatai abinci domin d'anta Shikadai.
 Kallan abincin yai sannan ya karasa ya zauna, ya gaisheshi.
 Hisham ya amsa fuskarsa a washe yace "Ashe bacci kake?"
 Abdulmajid yace " eh wlh, kayi hakuri na barka kai kadai kawu."
 Hisham yace ba komai, zauna kaci abinci, goggonka ce ta dafa ma.
 Abdulmajid ya kalleshi sannan ya kalli abinci yace "Kawu me kakeso?"
 Hisham yace " name kenan?"
 "na tabbatar abu kakeso a gareni shiyasa kake nunamin kulawar da baka nunamin da, badai so kake in auri Khadija ba ko wani abun ba?"

 Da sauri Hisham ya zaro ido yace "ka auri khadija kuma? Wannan wani irin shirmene? Auzubillah."
 Abdulmajid yayi mamaki yanda yaga yayi, sai dai bai kawo wani abu ba yace " to inba shiba menene? Na tabbata akwai dalilinka na yin haka balle ma kace kar na dinga sanar da Umma zuwanka."

 Hisham yai shiru yana tunani kafin yace " ko d'aya kawai dai ina ganin ya kamata mu saba da juna ne, na ga ko aboki baka dashi."

 Abdulmajid ya kalleshi baice komai ba ya fara cin abincin.

 *******

  Magajiya kam Jakadiya na fita hankalinta ya kasa kwanciya, mikewa tai ta shirya ta fito ta nufi bangaren Abdulmajid.
 Da yake ta baya ne bata wani dadeba ta isa.
 Ana kokarin sanar da isowarta tace ayi shiru.
 Kai tasa tare da tura kofar a hankali.
 Hisham taji yana cewa " Na d'auka wancan sati zaka zo, sai naga baka zo ba."
 Abdulmajid wanda ya gama cin abinci ya kalleshi tare da wanke hannu yace " ya su Umman da Khadija?"
 Hisham yace " suna lafiya, zakazo ran juma'ar?"

  "Yaje ina?" abinda sukaji kenan da ga bayansu.
 A tsorace suka mike, Abdulmajid ya kalleta yace " Umma."
 Kallansa tai sannan ta kalli abincin da ya gama ci tana gani tasan Hisham ne ya kawo dan ga kuka nan a gabasa, sannan ita ba irin abincin da aka kawo mata ba kenan.

  Ba shakka ranta ya baci sosai, dan idanunsa sun canza fuskar nan tata ta had'e ta tamau.
 Kallan Hisham tai tace " Yaje ina?"
 Hisham ya kalleta sannan ya kallu Abdulmajid, kallan Abdulmajid tai tace "  ina zaka?"
 Abdulmajid yace " Umma."

  Kallan abincin tai sannan ta kallu Hisham tace " me kenan? Waye ya baka ikon kawomai abinci?"

  Hisham ya kalleta yace " dan na kawo mai abinci wani abin ne?"

  Cikin d'aga murya wanda ni kaina sak dana razana tace " wani abin ne babba ma kuwa, yaya me ke damunka?"
 Abdulmajid wanda ransa ya dan sosu ya daure yace " Umma dan ya kawomin abinci wani abun ne? Kawu nane fa na tabbata bazai cutar dani ba."
  Kallan Abdulmajid tai tace " ta ya kasan bazai cutar dakai ba? Dan yana kawunka kawai?"

 Hisham yace " mene? Kina nufin ni zan cutar dashi?"

  Cikin bacin rai tace " yaya biyoni inasan magana dakai."
 Tai gaba.
 Abdulmajid ya dafa kai, sannan ya kalli Hisham wanda yama rasa mai zaiyi.

 Yana kallan Hisham yai waje.
 Komawa yai ya zauna jiki a sanyaye.

 Ita kuma suna shiga d'akinta ta juyo cikin tsananin bacin rai zatai magana.
 Hisham ne yai saurin cewa me kike nufi da zan cutar da abinda na haifa?

 Wata irin dariya ta saki mai razanarwa, sannan ta tsuke bakinta lokacin d'aya ta matso kusa dashi tace " me? Abinda ka haifa? Inji wa kenan?"
 Hisham yace " mene?"

  Tace " ahhh dalilin kenan da yasa kake neman kula dashi yanzu? Saboda d'anka ne? Ko saboda kanasan amfani dashi nan gaba?"
 Hisham yai kasa dakai.
 Tace " idan har kana san kanka da arziki ka fita harkar d'ana, shine magajin sarki banasan wani abu ya faru har sai ya hau mulki, in kuma har kana tunanin wani abu kama daina dan zan iya sa Abdulmajid ya daina ko gaidaka ne kai kasani."

  Kallanta kawai yake yama rasa mai zaice.
 Hannu tasa ta shafi fuskarta sannan Tace " Yaya banaso muna fada akan abinda bai kai ya kawoba, ban hanaka kula Abdulmajid ba amma bance ka shishigemai ba, d'ana ne banasan wani abu na shakuwa ko sama da haka ya shiga tsakaninku."

  Sam yama kasa magana, sai mamaki kawai da yake na kalamanta.
 Magajiya tace " Yaya na aika da kayayyakin bikin Abdulmajid gida, sannan karka manta da shirin mu na ranar d'aurin aure, wannan shine abinda ya kamata muyi ba fada ba."

 Ta karasa maganar tana murmushi kamar ba abinda ya faru.

  Hisham  " to." kawai yace ya mata sallama ya fita.

 Tabbas daga Abu Turab sai ke zakisan ni kikama haka, ba uwa d'aya uba d'aya ba ko 'yatace ke wlh sai kinsan nikikama haka.



*TURAB*
? *KAINUWA*?
     ......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

   

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*Na Ayusher Muhd??*

_I sincerely apologize to u ?_

  *67*

  Basira ce ta kalli mai martaba tace " Barden ya amince ne?"
Takawa yai shiru alamar tunani sannan ya kalleta yace " Basira kiyi hakuri, nasan yanda kika d'auki Mairo na kuma san halin Abdulmajid, yanda Magajiya ta raineshi a haka yake, yaro ne wanda bai yarda da babu ba, sannan duk abinda yakeso gani yake dolene sai ya samu, hakan ne yasa nake nunamai ba haka ba, nake kuma janyeshi daga jikina saboda banaso yai tunanin komai nasa ne kamar yanda Uwarsa ke koyar dashi, sai dai nayi tunani dakyau yaran yanasan yarinyar sannan Mahaifiyarsa ba so take ba, ko dan Magajiya taji ciwon bijire mata da d'anta yai ina tunanin Amincewa."

  Basira tace " ba wai naki aminta da kai bane sai dai meyasa nakeji kamar kanasan had'a auren ne bawai dan farincikin d'anka ba ko dan karfafa zumunta da Barde ba, ya nakeji kamar dan cikar burinka na kuntatama Magajiya kake san had'a su?"

  Sarki ya kalleta yace " wannan tunanin shine babban dalilin dayasa na dage akan auren Turab da Bilkisu."
Tace " bangane ba."
Yace " a masarauta dolene ka sadaukar da wani abu dan samun wani abun, bazai yiwu ka samu komai ba, inhar inaso Turab ya zama Sarkin da naso na zama dolene na samarmai mace jinin sarauta wacce tasan sadaukarwa."

  Basira ta kalleshi tai murmushi dan ta fahimcu a fakaice magana ya gwab'a mata, tace " Allah ya baka hakuri."
Hannunta ya kamo duka biyun yace " inaso ki zama mai karfafamin gwiwa akan al'amurana, bawai dan Magajiya ba kawai nake san had'asu, inaji a jikina zata zama mata ta gari agareshi."
  Shiru tai dan batasan me ma zatace ba, amma itakam dan ba yanda zatai ne, bataso Magajiya ta zama sirika a gun Mairo.

************

   Yau kwanan Abdulmajid biyu kenan Magajiya bata kulashi, gaisuwarsa kawai take amsawa.
Yau dai abin ya dameshi bayan ya gaisheta yaki tashi.
Ya dade a zaune kafin yace "Umma nikam sai yaushe zaki huce ne?"
Bata kalleshi ba bare yasa ran amsawa, yace " kema kinsan ba ji nace ya kawomin abinci ba, sannan gani nai Kawu Hisham yaya yake a gunki kinga kuwa Uba yake a gurina......"

  A gun wa yake uba?"
Kallan mamaki ya mata yace " Umma kinsan kwanan nan kin canza kuwa?"
Kallansa tai tace " na canza ko ka canza?"
Yace " Umma yanzu na kula kamar akwai abinda ke damunki, abinda bai kai ya kawoba sai inga kinji haushi, a da kuwa kina dadewa kafin inga b'acin ranki."

  Shiru tai ita kanta tasan haka ta rasa me yasa takejin ta akoda yaushe kamar intai sake Abu Turab zai ruguza mata rayuwa.

  Abdulmajid ya taso yazo gabanta yace " Umma meke damunki?"
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace " Abdulmajid."
Naam Umma.
"inaso kamin alkawari a koda yaushe cikin ko wani hali zaka zama a bayana, bazaka taba juyamun baya ba."

  Murmushi yai wanda sainda hakoransa suka bayyana yace " bakyasan indinga shiga jikin Kawu?"
Kai ta girgiza alamar a'a tace " kawai dai banasan inga wani yana neman janye min kai ne."

Yace " Umma kenan, wa ya isa ya janye miki d'anki? Nifa d'anki ne ba kuma wanda ya fimin ke duk duniyar nan."
Tace"ka tabbatar ka ajiye wannan kalmar a kasan zuciyarka."

Kallanta yai yace " Umma na kasa fahimtar dalilinki na yin hidimar bikin Turab, akan me wacce ta haifeshi bazatai ba sai ke?"

Magajiya tai shiru a ranta tace" kwalliya zata biya ai kud'in sabulu."
Amma a fili tace " karka damu nice uwargidan Sarki, hakkinane na kula da hidimar bikin 'ya'yansa."

  Abdulmajid ya dai kalleta ne kawai amma zuciyarshi bata gamsu da wannan sharhin nata ba.
Haka ya taso ya fito.

Da yake juma'a ce massalaci ya wuce, bayan an idar da sallah Abu Turab na cikin mutane suna ta gaigaisawa ana tsokanarsa akan ya kusa zama ango.

  Abdulmajid na zaune yana hangoshi, shi kansa Abu Turab baya minti biyu sai ya kalli inda Abdulmajid yake saboda yanasan ganin Hisham kusa dashi.

  Abdulmajid ya miko yazo shima aka fara gaisawa dashi.
Hisham ne ya karaso gun, yana zuwa Abdulmajid na gaisheshi ya juya zai yi tafiyarsa.

  Hisham ganin haka yabishi da sauri tare da kiransa, tsayawa yai tare da juyowa, Hisham ya iso yace " gida zaka?"

  Abdulmajid ya kalleshi yace " eh, da wani abun ne?"

  Zaiyi magana Abu Turab ya karaso yace " Abba barka da juma'a."
A tare suka juya suka kalleshi, Hisham yace " ni?"
Turab yace " Kai Abba, zumunci akeyi shine kuka taho gefe?"

  Abdulmajid yace " a yaushe ya zama Abbanka?"
Turab ya kalli Hisham irin jin kunyar nan yace " Waziri baka sanae dashi ba?"

  Hisham ya had'e rai yace " me zan sanar dashi?"
Turab yai murmushi yace " Abdulmajid ai munkusa zama surukai."

  Kallan Hisham yai cikin mamaki, yace " me? Sirikai? Badai Khadija ba?"
Turab yai kasa dakai yace " da alama kuna bukatar keb'ewa ko kwa zanta na maganar, ko gun Khadijan zaka kaji komai?"

  Abdulmajid ya cika yai fam, yace " Kawu me kenan?"
Hisham ya kasa magana.
Turab ya kalli Abdulmajid yace " ka tambayi kanwarka."
Ya juya yai gaba, sai dai hankalinsa na kansu.

  Baisan me sukace ba sai dai yaga sun juya a tare sunyi hanyar fita.
Turab ya kalli Garzali yace " dubamin ko gida sukai."

  Yace to.

Bai dade ba ya dawo yace " ya gansu sum shiga mota a tare."
Murmushi Turab yai yace " Bari muje muga Hajiya Umma Magajiya."

  Yai gaba.

    Tanaji an sanar da ita zuwan Turab sai da gabanta ya sake fad'uwa.
Mike wa tai ta shiga cikin d'aki, gyara kanta tai sosai, sannan ta fito.
A zaune ta ganshi yana cin ayaba.

Karasowa tai ta zauna, Turab ya kalleta yace " Umma barka da rana."

Ta amsa cikin izzarta sannan tace " banyi tsammanin ganinka ba."
Yace " nima bansan zanzo ba sai dai kinsan Juma'a dole ne d'a ya kwashi gaisuwar iyaye."
Baki tad'an tabe, jujuyawa yai kamar yana neman wani abu yace " Banga Abdulmajid da Waziri ba, na d'auka nan sukazo."

  Kallansa tai tace " baka gansu ba anan kuma ka d'auka nan suka zo? Wace irim tambaya da amsa ce wannan?"
Turab yace " naga sun fita tare da aka idar da Sallah shiyasa na garzayo saboda ingaida Baban namu."

Shiru tai sun fita tare? Me kenan? Badai Hisham baiji fadanta ba?

  Turab yace " Hala sun shiga garine zumunci, abinka da d'a da mahaifi."

A hankali ya karasa maganar.
Kallansa tai tace " me kace?"
Turab yace " me nace? Nikaina na manta."

  Idanu ta kafa mai tace "kamar zance d'a da mahaifi kai...."

Dariya yasa yace " d'a da mahaifi kuma? Wa? Abdulmajid da Waziri? Ta yaya?"

  Kallansa tai tsoro ya gama kamata, duk yanda taso ta b'oye sai da Turab ya gano hakan, yace " Umma?"

  Kallansa tai tace " wani shirme kake fad'a, kai d
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KAINUWA* A Historical Fiction* by Ayusher Muhd Gimbiya 1 15,759 08-21-2019, 01:53 PM
Last Post: Ebony Lacklock
  *JALILAH* by Ayusher Mohd* Gimbiya 0 20,165 09-10-2018, 09:03 PM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 3,758 06-16-2018, 10:17 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 6,907 06-16-2018, 10:16 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 3,349 06-16-2018, 10:09 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 3,717 05-07-2018, 11:04 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* by Ayusher Mohd Gimbiya 0 4,309 05-07-2018, 10:54 AM
Last Post: Gimbiya
  *KAINUWA* A Historical Fiction* by Ayusher Muhd Gimbiya 0 4,614 03-29-2018, 11:44 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)