The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
⚡Heedayah⚡By Khaleesat Haiydar
#1
⚡ _Heedayah_ ⚡

_By Khaleesat Haiydar_✍?

All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book.... My special greetings to my lovely Mum Hajiya Hajarah, and all my small mums? my siblings and cousins ain't left behind too, ina son ku gaba daya.... My Isiaka Safia I greet u too, and my lovely fans that have waited so long for Khaleesat Haiydar... ina maku barka da sllh, Allah ya amshi ibadunmu baki daya, ga *Heedayah* I know u all will love it, coz I Khaleesat is already in love with it ?
No disappoinment In sha Allah ?

1.....

Wani d'an matsakaicin daki ne da aka xagaye da tsadaddun labulaye, dakin na dauke da katifa babba, sai kayan kallo daga gefe, sai cushion tsadadde guda daya, Dattijuwar da baxata haura hamsin da biyar ba dake xaune dakin tayi tagumi tace "Toh mu dai baxa mu gaji da addu'a ba, Allah ubangiji ya bata lafiya, watan gobe kenan dai ake sa ran komai xai yi dai dai koh?" Matashiyar matar dake gefenta ta d'an yi murmushi tace "Haka dai likitocin suka ce in sha Allah, sai dai kinsan kana naka ne Allah na nasa, amma wnn aikin shine na karshe da xa ayi mata idan Allah ya yrda, sai kuma fatan Allah ya sa a dace" Yakumbo tace "In sha Allahu xa a dace, abinda kullum gaya ma Allah muke, kaf dangi bbu mai irin laluran nan balle ace ko gado ne, sam bbu shi a danginmu gaba daya, ko ke akwai a naku??" Dariya matar tayi tace "A'a Yakumbo" Yakumbo tace "Atoh, Allah dai ya raba bawa da wahala ke ma kuma Allah ya sauke ki lafiya, Indiyan xa a kara komawa kenan ayi aikin?" Matar tace "Ameen, ehh can xa mu je" Yakumbo tace "Toh in sha Allahu karshen wahalan kenan" Matar tace "Allah ya sa"  agogo Yakumbo ta kalla tace "Anya tafiyar nan taku na nan yau kuwa Amina, shiru shiru har yanxu Umar din bai xo ba" Amina ta kalli agogon ita ma tace "Kuma na kirasa daxu ban samesa ba, ina jin meeting suka shiga, kila sai gobe dama na cire rai yau" Yakumbo tace "Atoh, ku bari kawai sai gobe yamma yayi, sai kace wa inda ake kora, ga hanyar nan da ba kyau gari ya xama abinda ya xama mucuta ta ko ina...." Amina tace "Haka ne" Yakumbo tace "Naji wai matar Salihu na ta neman ki da fada ko? Kar ki kuskura ki kulata gayyar mayu ne, har ita Asama'un ma ki bar kulawa duk haushin ki suke ji suna ganin kin fi su walawa gidan miji, ba su san Allah ne ya baki ba" Amina tayi murmushi bata ce komai ba, Yakumbo ta kara da cewa "Kuma wai sai kiyi ta boye yarinya kar su gani, wai haka?" Amina ta kalleta tace "Aa ba gaskiya bane, ke kanki shaida ce Yakumbo tun tana yar yarinya ba a fiye fito da ita cikin jama'ah ba, a ko da yaushe tana daki tare da ni ko mai kula da ita, ko malamarta, har yau 'yan anguwa basu wani san kalan Heedayah ba, da kyar ki xo gidan ki ganta a parlor, to sau tari idan anyi baki har su tafi ma baxa su ganta ba shine ake ganin kamar boye ta muke kar a ganta" Yakumbo tace "Toh ai gwara haka, haka kawai baka san bakin wani ba, ayi ta sa ma yarinya baki, gaskiya kun yi dubara, ki rabu da su suce duk abinda xa su ce, lafiyan yarinya shine gaba kan komai" Amina dai bata ce komai ba, Yakumbo tace "Har bokon ma a gida ake mata kenan?" Amina tace "Ehh har islamiyya" Yakumbo tace "To madalla, ae gwara hakan, Ke leko yar mutane naji shirun yyi yawa, Allah ya sa dai gantalallun yaran makotan nan nawa ba shigowa suka yi suka yi waje da ita ba" Da sauri Amina ta mike tana leka tsakar gidan tace "Heedayah??" Jin shiru ta fito tsakar gidan, Katon Babyn robanta da take combing gashinta kadai ne kan tabarma da comb din sai hularta amma babu ita, Yakumbo ta mike tace "Ni da nasan sai sun shigo sun ja ta, Amma wa ennan yara iyayensu sun haifi jaraba kawai, yara kauyawa bbu kamun kai kawai malam..." Dawowa Amina tayi dakin ta dau Hijab dinta sannan ta fita waje, Yakumbo na biye da ita tana cewa "Ni dai Allah ka rufa min asiri ba rafi suka ja ta suka kai ta ba in shiga uku, yarinya dai ba ido ba, daga kawo min ziyara shaidan ya fake ta nan yayi abinda ya ga dama tawa ta sameni ina xaman xamana...." Tun Mahaifiyar Heedayah na daurewa ana shiga bukkokin makota duba Heedayah a kauyen har taji hankalinta ya fara tashi sosai ganin babu alamar yar tata.... Yakumbo dai sai salati take xabgawa a rikice tana yafa gyalen da ya ki xama tana cewa "Toh me xance ma kanina Umaru jama'ah?? Ina xan ce yar sa ta shiga?" Wata mata ce tace "Daxu fa naga sun yi hanyar kasuwa da su Hinde da Bibalo, har da fatu, kusan dai su shidda suna rike da hannun ita yarinyar" Yakumbo ta saki salati tace "Toh kuwa wllh Ubanta a Habuja yake kuma duk iyayensu xae sa a daure idan abu ya samu yar sa, ita fa kadai garesa sae ynxu da uwar ke da sabon ciki, shekararta goma sha biyu, kuma ba idanuwa gareta ba, to a kan me gantalallun yara xasu ja ta su tafi da ita kasuwa, uwayensu xa su siya mata a kasuwar? Tun shekaranjiya da suka xo kauyen nn nake ja ma ja'iran yaran nan kunne ganin ynda suke makale mata har da masu wasa da gashin kanta nake ce masu su fita harkarta, ita dai ba fuskarsu take gani ba balle ace, to wannan wani irin bala'i ne, hanyar kasuwan nan da babu kyau sace sace yyi yawa, haba jama'ah??" Tuni duk aka watse aka dau hanyar kasuwa aka bar Yakumbo tsaye ita kadai tana kumfar baki, can dai ta bi su da sauri ganin sun yi nisa. Yara ne duk mata kusan su biyar karkashin bishiyar mangwaro sai mata biyu dake saman bishiyar suna tsinkar nunannun mango suna jefowa kasa matan dake kasa suna kwasa suna xubawa a karamin buhu, wata yarinya ce warce duk baxata wuce sa'aninsu ba tana durkushe hannunta rike da mango tana sha, daya hannunta kuma na rike da rigar fatuu don ita ke mata jagora, fara ce sosai, kana ganinta kasan jinin Fulani ce don gashinta dake bude ko hula babu ma ya shaida haka, idanuwanta farare ne kal kamar Madara tana kifta su a hankali kai kace ras take ganin kowa a wajen, sai dai babu abinda take gani banda duhu, wajen duk ya kauraye da surutun yaran dake tsinkar mangwaro xa su kai kasuwa su siyar, wata bakar mota ce ta ja tayi parking a wajen, duk suka juya yaran, lkci daya kattin maxaje biyu suka fito motar da sauri, gudu yaran suka yi har da Fatuu da ta warce rigarta daga hannun Heedayah, na saman bishiyar ma duk suka diro suka ruga aguje, Heedayah ta saki mango din hannunta ta dinga waige waige a tsorace, maxan suka bi bayan yaran suka samu kamo uku daga cikinsu, Heedayah ta mike ita ma suka daga ta suka saka cikin motar, kan kace me driver ya ja motar da gudu suka bar wajen. Gaba daya ihu yaran ke yi cikin motar har da Heedayah dake ta kwala ma Mahaifiyarta kira tana cewa "Ammina...." Wanda ke xaune a baya ya ciro bindiga yana nuna masu da jajayen idonsa fuskarsa a murtuke ya daura hannu a lebbansa alamar su yi shiru, lkci daya su ladi duk suka yi shiru sai rawa jikinsu yake, Zulai har da sakin fitsari a gun, Heedayah ce kadai bata fasa ihun da take ba, Mutumin ya shake wuyarta yana nuna mata bindigar yace "Ohh ke baxa ki rufe mana baki ba koh?" Jikin Ladi na 6ari tace "Bata gani" Mutumin ya shiga kare mata kallo sannan ya gyada kai yace "Kuma duk yanxu xaku daina gani" yana fadin haka duk ya rufe ma sauran ido da kyalle, Heedayah da ta ki yin shiru kuma ya dinga buge mata baki yana marinta, hakan kuma bai hanata ci gaba da ihu ba tana lalube laluben inda xata fita, daga karshe jin taki shiru wanda ke xaune gaba ya miko masa wani leda yace "Bada mata a fuska" hakan kuwa aka yi, nan da nan kuwa ko ina yyi tsit a motar, a hankali Heedayah ta fada jikinsu Ladi. A hanya mutan kauyen suka hadu da su Hinde da sauran matan da suka samu guduwa, Nan su Hinde na kuka da ihu suka fada masu abinda ya faru, da hanxari wasu mata biyu suka rike Ammin Heedayah dake neman sulalewa nan kasa, ta fada jikinsu a sume. Yakumbo ta saki wani salati da karfi ko ina na jikinta na rawa, cikin kidimewa ta dinga cewa "Ai shkkn tawa ta kare, na shiga uku na lalace, kar ace min yan kinnaping ne ko yan yankan kai suka dauke Heedayah, me xance ma kanina jama'ah???" Ta fashe da matsananin kuka xata fadi kasa ita ma aka rikota, ana ta salati iyayen sauran yaran da aka dauke ma suka dinga kuka suka bi bayan maxan da suka nufi gun da abun ya faru. Tafiyar kusan awa daya mutanen suka yi da su Heedayah a mota kafin su fita hanyar kauyen gaba daya kasancewar hanyar bbu kyau, sannan suka yi parking gefen jaji don tafiyar minti ashirin kawai xasu kara su isa wani checking point a gaba, wasu mutane ne suka fito daga dajin bbu kyan gani kana ganinsu kaga axxalumai, Mutumin dake bayan mota ya sakko da sauri ya fiddo su Ladi aka tasa keyansu cikin dajin bayan an kunce kyallen idonsu, daya daga busassun mutanen da suka fito daga dajin na kallon Heedayah yace "Wannan fa" Mutumin na kokarin fiddota yace "Daukarta xa ku yi, xata daga mana hankali muka badata da powder" busasshen Mutumin yace "Ai baxai yiwu bane, wnn uban tafiya xaka ce a dauketa, ku kashe ta kawai a jefar a nan, mu yi wucewar mu" A fusace Mutumin yace "Mu kasheta bayan yara goma muka yi alkawari yau, duk bbu sa'a sannan mun samu yara hudu kace mu kashe daya.... Kuma dole dai ku dauketa don makauniya ce wai" Yana fadin haka ya direta kasa ya shige motar driver ya ja suka bar gun a guje" tsaki Mutumin yyi ya dau Heedayah kai kace dabba ce irin daukan da yyi mata suka shige dajin dake da manyan torns, ga duhu don Magrib ya gabato......

⚡ _Heedayah_ ⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍?

2......

Bayan tafiya that seems endless da kafa suka bullo ta wani titi inda wata mota ke jiransu, nan suka shiga aka ci gaba da tafiya, gaba daya yaran kana ganinsu kasan sun gaji sosai, Heedayah dai har lkcn dabata farka ba, sai kusan goma suka iso wani karamin Uncompleted building, mata da maza ne sun kusa 6 yashe a wani daki da bbu hasken kirki sbda karamin window ne a dakin daga can sama, Nan aka tura su ladi da Heedayah da ta fadi kasa ko motsi bata yi, Wani wanda da alamar shine babba cikin yan bindigan dake wajen yana rike da bindigarsa ya kalli wanda ke gadin mutanen shi ma da bindigarsa a hannu yace "Ya ku ka yi da mutanan wancan Mutumin a waya?" Ya kalli wanda yake nuna masa yace "Ae kawai bbu alamar xasu bada kudaden nan, sun ma daina daga kiran" Bai rufe baki ba ogan nasu ya harbe Mutumin da ake magana a kai, hakan ya kidimar da mutanen da ke xaxxaune gun, barin matan, sound din harbin ya farkar da Heedayah ta fasa wani ihu tana kokarin mikewa tsaye wata mace dake xaune kusa da ita ta jawota da sauri ta rufe bakinta a jikinta, Ogan ya dinga ma Heedayah wani kallo sannan ya kalli Mutumin gefensa yace "Is she among the kidnapped?" Mutumin ya girgixa kai da sauri yace "Aa yan kauye ne, su hudu muka dauko a kauyen jiya, ba kace ana son body parts ba" Mutumin ya karasa gun Heedayah ya dagota daga jikin matar yana kare mata kallo da kyau, ya girgixa kai yace "Yar wani babba ce wnn, it will have been good she's kidnapped, but anyway, ana bukatan parts din ma" Yana fadin haka ya turata ta fadi kasa, janye gawar Mutumin ogan yasa aka yi aka fitar waje,   sannan duk Yan bindigan suka fita aka garkame kofar. Ladi ta kankame Zulai ta dinga rusa kuka tana kiran sunan Babarta, wata mata ta mike ta nufesu ita ma tana hawayen, nan ta shiga lallashin su tana kwantar masu da hankali da sauran mutanen wajen, kai kana gani kasan duk karfin halin lallashin nasu suke yi. Matar dake kusa da Heedayah sai kokarin daga Heedayah take ganin kamar suma tayi..... Sai kusan asuba Heedayah ta kuma farkawa, ta mike xaune da kyar tana laluban inda take tace "Ammi??" Jin shiru bbu muryar Mahaifiyarta kamar ko da yaushe sai mutane a kwance tana ta6a su ta janye hannunta da sauri, muryar Zulai taji a hankali tace "Kiyi shiru yar birni yan yankan kai ne suka sace mu, kiyi shiru kar su shigo" Tsit Heedayah tayi da farko, sai kuma ta fasa ihu tana kwala kiran Ammi, wani da ke sallah ya sallame ya taho kusa da ita da sauri gudun kar mutanen su shigo don babu abinda suka tsana irin a dinga masu ihu, karamin aikinsu ne su kasheta in har suka shigo, lallashinta ya dinga yi yana ce mata xata koma gida in sha Allah, ita kuwa sai cewa take "Aa ni a kai ni gun Ammina da Abbana yanxu...." Nan dai ta tada wa enda suka samu bacci aka dinga hiaikin lallashinta a d'an dakin, Cikin kuka take ce masu xata yi fitsari, aka nuna mata wani karamin kofa dake cikin dakin, Ladi tace "Yo ai bata gani" furucin Ladi ya sa duk aka tsaya kallon Heedayah, wata mata ta mike a sanyaye ta kama hannunta ta kai ta bayin. Har aka yi asuba gari ya waye Heedayah shesshekar kuka take a hankali, can ya ta6a matar dake kusa da ita cikin kuka tace "Aunty yunwa nake ji" Matar ta kuma jawota jikinta cikin sanyin murya tace "Yanxu xa a kawo abincin idan Allah ya yrda" sai karfe goma aka bude kofar dakin, duk kowa yyi tsuru tsuru ana addu'a a xuciya, Mutane uku suka shigo ko wanne ya saita bindiga, kamar ko da yaushe facemask na fuskarsu, sai wani mutum da shi ma fuskar tasa ke a rufe dake rike da babban leda me dauke da kananun bread, daga inda yake tsaye ya dinga jefa ma kowa da ledan pure wata daya, ya jefa ma Heedayah dake ta bin duk inda ta ji sound din faduwar bread da ido, Zulai ta mike xata dauka ta bata ya mata wani mugun kallo ta cikin mask din fuskarsa da ke nuna idonsa kadai, jiki na rawa tace "Yo ai bata gani ne" kallon Heedayah ya sake yi, gashi dai fararen idanuwanta a kansa kuma ace bata gani, wani tsawa ya mata yace "Sa hannunki ki dauka da kanki" Heedayah da tayi mugun tsorata ta fara laluben inda xata ga bread din amma bata gani ba don bayanta yake, karasowa yyi cikin dakin bindigar sa a hannu, duk occupant din dakin suka rike numfashi ganin ya nufo Heedayah da ta hakura da laluben inda bread yake ta sunkuyar da kai, dukawa yyi ya dau bread din ya mika mata yace amsa, tana laluban inda yake, ya kamo hannunta ya sa mata bread din, tana kallon direction din da ta ji hannunsa idanuwanta cike da kwalla a hankali tace "Thank you" ajiye mata ledan ruwa daya yyi ya bar sauran bread din  ya mike ya fice daga dakin sauran yan uwansa suka bi sa sannan suka garkame kofar, matar dake kusa da Heedayah ta rungumota hawaye na zuba idonta ita ma, ta amshi bread din ta kunce mata ledan ta mika mata. Zulai da Ladi dai tuni suka handame bread din suna zare ido. Ammi ce kwance gadon asibiti da drip a hannunta, da ido kawai take bin mutanen dake cikin ward din, she looks so sick, Yakumbo na can wani gefe xaune kan kujera tayi tagumi idanuwanta duk a kumbure, wani matsanancin kuka ta saki tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, Allah kai kasan yanda xaka yi da axxaluman bayin nan naka, Ya Allah ka rufa min asiri 'yar Dan uwana ta dawo cikin koshin lafiya, wllh Ita kenan garemu..." Kanwar Ammi dake Ward din ita ma ta fashe da kuka sosai, haka ma sauran mutanen ciki, Mahaifin Heedayah dai na xaune kusa da Ammi yana rike da hannunta, shi ma ko kadan tashin hankali bai boyu a fuskarsa ba, kawai ta maxa yake, Yakumbo ta mike tana hade hanya ta fice ward din kamar xata shide don kuka tana cewa "Shkkn ni dai tamu ta kare, ita kenan gare d'an uwana fa, na cikin ma anyi barinsa sbda wnn tashin hankali, wannan wani irin xalunci ne ake yi haka a duniya ni Khadijah, Allah ka tsine ma duk wanda ya raba mu da Heedayah, Allah ka isar mana, ka dawo mana da ita cikin aminci...." Kanin Abban Heedayah ya mike ya bi bayanta shi ma dai trying hard to control his tears. Kusan la'asar aka bude kofan dakin da su Heedayah ke ciki, ja baya kowa ya dinga yi a tsorace, Heedayah ta mike xaune daga kwancen da take tana kallon inda taji karan budewar kofa, su hudu suka shigo, ko wanne da bindiga, Ogansu na nuna wani matashi yace "Kai taso xaman ka ya xo karshe a nan, Yan uwanka sun yi abinda ake bukata" tashi yyi da sauri yana hamdala sauran mutanen wajen sai hawaye, haka aka fitar da shi, ogan na nuna wani a cikin sauran yace "Kai yan uwanka na raina mana hankali, xuwa gobe idan basu yi complying ba xa mu aika ka barzahu kowa ya huta...." Yana fadin haka ya kalli wanda ke gefensa yace "Cikin yaran nan ka fito da guda daya a cire abinda ake bukata, me siya na kan hanya anjima, gobe da yamma ma akwai me xuwa zai siya" yana fadin haka ya fice, sauran suka bi bayansa, Mutumin daxu da ya kawo masu bredi ne kawai bai fita ba sai wanda aka sa ya dauko yarinya daya ya dinga bin yaran da kallo, Mutumi dai mai bredi ya nufi Zulai ya dagata ya fice tana ihu tana sakar masa fitsari, d'an uwansa ya bi bayansa ya garkame kofar, bbu abinda mutanen cikin dakin ke yi banda hawayen tashin hankali, Heedayah ta dinga waige waige jin ihun Zulai, matar dake kusa da ita ta rungume ta tana kuka sosai, cikin kuka ita ma tace "Aunty ina xa su kai ta??" Matar dai bata ce mata komai ba sai kuka. Washegari har kusan yamma basu samu an kawo masu bredin ma da ake kawo masu ba, Heedayah ta fada ma matar kusa da ita tana jin yunwa ya fi a kirga tun matar na ce mata xa a kawo abinci har ta gaji ita ma tayi shiru, kusan la'asar aka bude kofar wajen, mutumin da ke basu bread ne ya shigo da buhun bread da ruwa, nan duk ya jefa ma kowa, har bread din ya kare amma bai ba Heedayah ba, matar dake kusa da ita har xata yankar mata nata, Mutumin ya karasa ya daga Heedayah cikin kaushin murya yace "Mu je ki amshi naki" cikin rawan baki matar tace "A'a ko in yankar mata a nawa ba cinyewa xan iya yi ba, baxan ma ci ba...."  Wani mugun kallo ya dinga mata hakan yasa tayi tsit jikinta na rawa, juyawwa yyi ya nufi kofa da Heedayah dake ihu tana kiran Ammi tana gatsa masa cixo a hannu, bayan ya fita ya rufe kofar, ya toshe bakinta yace "Ke xan halbe ki yanxu idan baki rufe min baki ba" Tsit tayi ko ina na jikinta na rawa tana kallonsa kamar dai tana ganin fuskarsa, xagawa yyi ya canxa hanya yanda sauran yan uwansa dake xaune a baya baxa su gansa ba, cikin hanxari ya karasa bayan wani karamin bukka da suke ajiye makamansu ya ajiyeta bayan Bukkar ya durkusa yana kallonta yace "You don't move, ki tsaya nan har in dawo idan ba haka ba, I have gun...." Kai kawai take gyada masa a tsorace tana komawa baya, ya mike da sauri ya koma inda Yan uwansa ke xaxxaune ana xuke xuke ana buga karta, Makullin mashin dake rataye jikin bishiya ya dauka yace "Xan je amso ruwa in dawo yanxu...." Wani daga cikinsu ya kallesa yace "Oga na hanya da customer fa" yace "Ehh yanxu xan dawo ai" har ya nufi gun da suke ajiye babur dinsu sai kuma ya juya da sauri ya sake komawa dakin da ya dauko Heedayah ya bude ya shiga yana masu wani kallo yace "Ko da an tambayi yarinyar nan kuce ta mutu an fitar da ita...." Tsuru tsuru suka yi suna kallonsa ya juya ya fita ya kulle kofar. Daga haka ya nufi machine ya hau ya tada, a guje ya bar wajen, dai dai inda ya ajiye Heedayah ya tsaya, sai xare ido take tana kalle kalle, ya daga ta ya daura gaban machine din yyi speed off, gudu kawai yake a dajin kamar mai race din motorcycle, tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi suka shigo cikin gari sosai, a hankali yake tafiya yana kalle kallen jama'ah dake ta kokarin rufe wajajen sana'arsu kasancewar Magrib ya gabato, sai kuma ya tsayar da machine din ya kashe, sauke Heedayah da tashin ta bacci kenan yyi, ya ajiyeta nan gefen hanya yana kallonta, laluba wajen ta shiga yi, jin ya sake kunna bike din da sauri tace "Noo, Are you leaving me??" juyar da Machine dinsa yyi ya dau hanyar da ya fito with speed, ta fashe da kuka sosai tace "Noo"

⚡ _Heedayah_ ⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍?







3.....



Heedayah ta fi minti biyar a tsaye tana Shesshekar kuka, jin bbu alamar xai dawo ta fara tafiya a hankali tana yi ma kanta jagora da hannuwanta biyu, da tayi tafiya kadan sai ta tsaya, ihun da taji aka yi wajen ya sa ta tsaya a mugun tsorace, ji tayi kamar an hankadata da katon abu ta fadi kasa, tun tana jin surutun jama'an wajen sama sama har ta daina ji kwata kwata. A hankali Heedayah ta bude ido tana laluba inda take kwance, muryar namiji taji a gefenta yana cewa "Alhamdulillah she is back (Ta farfado....)" Ya kamo hannunta yana mata sannu murmushi dauke fuskarsa, kanta da yyi mata nauyi kawai take gyadawa tana kokarin mikewa xaune, ya komar da ita ya kwantar yace "A'a bari likita ya xo ya duba ki, bari in kirasa, ina xuwa ynxu" ita dai kai kawai take gyadawa, ba a dau lkci ba sai ga mutumin ya dawo da likita, directly Heedayah ke kallon fuskar likitan, ya sakar mata lallausan murmushi wanda bata san ma yana yi ba, likitan ya xaunar da ita ya dafa goshinta yace "Ya jikin baby girl?" Kifta ido ta shiga yi tace "Where am I? (Ina ne nan?)" Yana murmurshi yace "Hospital dear, fatan dai babu inda yake maki ciwo" kanta ta nuna masa, yace "Xai daina in sha Allah, xa a baki magani yanxu" shi dai wanda ya kirawo likitan kallonsu kawai yake, A hankali tace "Xan yi fitsari" likitan ya saukar da ita kasa, yana nuna mata kofar bandaki, hannunsa ta kama, yace "Xa ki iya dear, walk gently now (Kiyi tafiya a hankali....)" kin motsawa tayi, sai kuma a hankali tace "I can't see (Bana gani)" da mamaki likitan da Mutumin da ya kawo ta asibitin ke kallonta, likitan yace "Why? is the eyes paining you? Idanuwan suna maki ciwo ne" Ta girgixa masa kai yace "Toh yi tafiyar ki da kanki" ta rike hannunsa gam kamar xata yi kuka tace "Ae ni bana ganin hanyan" sosai hankalin likitan ya tashi, haka zalika Mutumin dake Ward din da ya mike shima yana kallonta, don gaba daya tunaninsu a lkcn ta dalilin accident din ne vision dinta ya samu matsala, Banda innalillahi wa Inna ilaihi raji'un bbu abinda Mutumin ke furtawa yana kallon Heedayah. Likitoci sun fi biyar a kan Heedayah, all trying to figure out where the problem is, ko wannensu na kokarin gano inda matsalar take amma abu ya ci tura, ita dai sai bin duk inda ta ji motsi take da manyan idanuwanta, duk da ba ganinsu take ba, daga karshe dai aka ba Mutumin da ya kawota shawara kawai ya kai ta asibitin ido, ba karamin tashi hankalin wannan mutumin yyi ba, haka dai ya biya bill din asibitin ya dau Heedayah xuwa asibitin ido dake nan cikin garin kano. Dai dai lkcn da suka shiga haraban asibitin motar optician din dake duba Heedayah tun da aka haifeta har kawo lkcn da aka yi referring dinsu india kuma na fita daga asibitin. Mutumin dake rike da hannun Heedayah bayan ya sauketa daga motar ya duka dai dai fuskarta cike da damuwa yace "Daga yaushe kike daina gani Little girl? What was the last thing u saw? Meye abu na karshe da kika gani?" Tayi shiru sai kuma tace "Nima ban sani ba" Damuwa ne sosai fuskarsa, yace "Toh daga ina kike jiya da magariba kuma ina xa ki? Where are ur parents? Ina iyayen ki" Shiru tayi, staring at him kamar tana ganinsa, nan ya shiga tantaman ganin da tace bata yi, ganin yanda take masa kallon cikin ido ya kai yatsunsa har kusa da idonta yaga bata rufe ba har sai da ya taba lashes dinta, kikkifta idon ta shiga yi, yace "ki min magana, Where are ur parent? Ina iyayenki" Ta girgixa kai tace "I don't know, (Nima ban sani ba)" da mamaki yace "Baki san inda iyayenki suke ba, ina xa ki jiya?" Ta fashe da kuka tace "Nima ban sani ba, kawai an saka ni a mota aka wuce da ni, sai na ji an sake hawa da ni bicycle kuma ynxu ban san inda aka kawo ni aka ajiye ni ba" rasa abun cewa yyi yana kallonta, can dai yace "Ya sunan garin ku?" Tace "Abuja" ya xaro ido ganin dai a garin kano suke ynxu, yace "Ya sunan baban ki?" Tace "Abba" yace "Abba??? Mamarki fa?" Cikin rawar murya tace "Ammi" Innalillahi ya dinga nanatawa a ransa, sai kuma yace "Abuja ya sunan anguwan ku?" Tace "Abuja ne" mikewa yyi just as confused as she is, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna goma na safe, yana rike da hannunta yana mata jagora suka shiga asibitin, Ba su suka fito ba sai kusan Azhar after series of Diagnosis da ya tabbatar da she was born with the blindness, a haka aka haifeta, kuma tana stage din operation din karshe kenan wanda xa ayi mata idan ba ayi nasara ba she will remain blind till the end (Xata xauna a makauniyar ta har karshe...) Alhaji Ahmad na rike da hannun Heedayah xuwa gun motarsa a haraban asibitin, bai ta6a shiga rudani irin na ranan ba, to ina xai kai wannan yar baiwar Allahn, kara kallonta yyi yaga bata wuce autarsa Rabi'ah ba, yanxu ina xai samo iyayenta ko wani wanda ya santa??? Yanke shawarar kai ta police station kawai yayi, yasan su xa su san yanda xa su yi da ita, driving kawai yake absentmindedly ya ji Heedayah tace "Abba, yunwa nake ji" ya d'an kalleta yana ci gaba da tukinsa yace "Me xa ki ci?" Tace "Shayi da bredi da kwai" sake kallonta yyi sannan ya dauke kai, Mintuna kadan ya rage ya isa nearest Police station, sbda yunwan da tace tana ji ya dau wata hanyar daban xuwa wani restaurant, abinda ta ce take so ya sa a kawo mata, ya tabbatar shayin ba xafi sosai sannan ya bude mata bread din da kwai ya mika mata, ganin yanda take ta lalube lalube kar ta kwa6ar da shayin ya mike ya koma kusa da ita, feeding dinta yayi har ta ce ta koshi, Banda kallonta bbu abinda yake yi cike da tausayinta, Bai taba ganin irin haka shi dai ba, yar karamar yarinya da makanta, tace "Abba..." Ya shafa kanta yace "Daughter" murmushinta me kyau tayi tace "Thank you" Bai ce komai ba, Amma naxari me iri iri yake yi a ransa, bayan few seconds ya kalleta yace "Ya sunanki?" Tace "Heedayah" Ya lumshe ido ya bude yace "Heedayah baki san anguwan ku a Abuja ba? Ki tuna da kyau ki gaya min daughter" Tace "Abuja ne gidanmu" ya girgixa kai ya mike yace "Tashi" tashi tayi ya kama hannunta kasancewar ya biya bill din suka fita xuwa gun motarsa, bayan sun bar Restaurant din, ya dau hanyar police station, Yana rike da ita suka shiga ciki, Bai bata lkci ba bayan yayi report ya bar Heedayah tare da su don yana da meeting da xai shiga karfe daya kuma a ranan yake son barin garin kano, sai dai har ya isa inda xa shi hankalinsa ya ki kwanciya, gaba daya ya rasa sukuni.... Washegari karfe takwas a police station yayi ma Alhaji Ahmad to be sure an samu iyayen Heedayah duk da yasan da kyar hakan ya faru a rana daya kawai, Bayan sun gaisa da policemen dake wajen suka sanar masa an kai ta orphanage for the meantime, shiru yyi na few seconds kafin yace "Shikenan, nagode...." Wani police officer yace "We will try our best in sha Allah, an kuma riga da an fara broadcasting tun jiya, so hopefully she will get back to her parent soon, (xa mu yi bakin kokarin mu na ganin ta koma ga iyayenta)" Alhaji Ahmad yace "Allah ya sa hakan" Sallama yyi masu ya bar station din. Ammi dake xaune saman gado a dakin asibiti da take ta kai hannunta xuwa na Mahaifin Heedayah dake xaune gefenta sai dai yyi nisa tunanin da yake, juyawa yyi ya kalleta, hawayen da ke gefen idonta ya gangaro cikin sanyin murya tace "Muhammad pls let nothing happen to my daughter, plss nothing shud happen to Heedayah, (Kada wani abu ya sami Heedayah) ku dawo min da yarinya ta" Uncontrollably ta fara kuka, tun xuwansu asibiti kwana biyu kenan sai yau tayi magana, Alhaji Muhd ya na rike da hannunta trying his best to be strong yace "Nothing dear, I mean nothing will happen to our daughter, (Babu abinda xai sameta) in sha Allah, zata dawo garemu soon da izinin Allah, hukuma na bakin kokarinsu, ki kwantar da hankali don Allah" Kuka kawai take bata ce komai ba, she looks so weak, ya sake hannunta ya fita don kiran likita. Da yammacin ranan Alhaji Ahmad ya gama shirin komawa kaduna, sai da ya bar gida sannan yyi deciding kafin ya tafi ya fara xuwa orphanage da yan sandan suka ce masa an kai Heedayah, Bai yi wani wahalan shiga gidan marayun ba bayan ya nuna Identity dinsa, ya dinga bin yaran dake wasa a waje da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kan Heedayah dake rakube can gefe ita kadai staring into space, hannunta rike da ledan biscuit, kallonta ya dinga yi kafin ya nufeta ya duka kusa da ita har sannan bai daina kallonta ba hawaye ne cike manyan idanuwanta, lkci daya ya ji jikinsa yyi sanyi sosai, ya dafa goshinta yace "Heedayah" Hannunsa ta kama kamar tana jiransa a lkcn, sai ta fashe da kuka tace "Abba" Ya jawota jikinsa yace "Why are you crying? (me yasa kike kuka" Cikin rawar murya tace "Suna min dariya bana gani, wata ta karbe min biscuit guda daya, Abba ka kai ni gida gun Ammina...." Bai ce komai ba, can ya mike yana rike da ita yace "Toh daina kuka" goge idonta tayi, yana rike da ita still ya tafi office din shugaban wajen, bayan sun gaisa yace "What are  the process before adoption of a child in here? (meye matakan bi kafin daukan yaro a gidan marayu)" Tana kallonsa tace "It's a very long process mister, (Matakan suna da yawa gaskiya" yace "Alright.... I will be back in some minutes time (Xan dawo nan da wani lkci)" kuka Heedayah ta dinga yi sosai da ta gane tafiya xai kara yi ya bar ta, haka nan ya bar ta gun masu kula da marayun wajen ya wuce, police station ya koma. Asp ya ajiye pen din hannunsa yana kallon Alhaji Ahmad yace "So you mean kana son tafiya da ita har lkcn da Allah xai sa a samu iyayenta" Alhaji Ahmad yace "Yes exactly sir" Asp yace "Sai dai kasan da cewar you didn't adopt her, duk lkcn da iyayenta suka bayyana xa a mayar masu da ita" Alhaji Ahmad yace "In sha Allah, Ni ma nafi son haka, and as I have said sbda health issues dinta yasa xan tafi da ita, she won't cope in the orphanage, i will be dropping all necessary information kamar yanda ka bukata duk da ni ba bako bane a gun ka, idan ma baka san ni yanda ya kamata ba, na tabbata kasan Yayana ai" Murmushi Asp yyi yace "Sure, I am not doubting you Barrister, Allah ya taya ka riko har kafin Allah ya bayyanar da mahaifanta" Alhaji Ahmad yace "In sha Allah, nagode sosai for understanding me" Wani short note Asp din yyi a takarda yayi stamping sannan ya kira wani police officer ya koma orphanage din tare da Alhaji Ahmad don dauko Heedayah. Har sannan Heedayah na xaune inda Alhaji Ahmad ya bar ta tare da daya daga mai kula da su, sai dai mai kula da su din bata gun, ita kadai ce xaune gwanin ban tausayi, har sannan ta ki cin biscuit din, Bbu 6ata lkci aka basa ita ya bar orphanage din bayan ya sallami police officer din, he can see how happy Heedayah was bayan sun shiga mota, ganin tana ta kokarin bude biscuit din hannunta ya amsa ya bude mata ya mika mata, tace "Abba xaka maida ni gun Ammina da Abbana?" Ya shafa kanta yace "In sha Allah daughter" tayi murmushi sosai tana cin biscuit din hannunta, seat belt ya sa mata, yana kallon agogo dake nuna masa biyar saura yan Mintuna, ya gama addu'o'in da xai yi sannan ya dau hanyar fita kano xuwa garin kaduna.....




Yan Niger Khaleesat bata iya rubutun Hausa xalla bbu turanci ba, kun ban wahala a page din n

⚡ _Heedayah_ ⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍?






4......


Har suka shigo cikin garin kd wajajen karfe tara na dare bacci Heedayah take, slowly yake driving bayan ya shigo anguwar da gidansa yake, anguwar so silent ga fitilu ta ko ina da ya haska anguwar kamar da rana, bakin wani gate ya ja ya tsaya yyi horn, wanda hakan ya farkar da Heedayah, laluba motar ta shiga yi tace "Abba...." yana kallonta yace "I am here..." Bata kuma cewa komai ba dama kawai so take ta tabbatar bai bar ta bane, ya d'an yi murmushi ya ja motar xuwa cikin babban compound dake dauke da gida ginin duplex bayan Mai gadi ya bude masa gate da sauri, parking yyi a space din da aka tanadar domin parking a compound din, wani matashi ne da baxai wuce 28 ba ya fito daga cikin babban building din gidan, ya nufo parking space din, Alhaji Ahmad ya kashe motar ya bude ya fito, Matashin ya d'an risinar da kansa yace "Sannu da hanya Abba" Alhaji Ahmad yace "Yauwa sannu, but ka damu ka kirani tun jiya da kake min sannu da hanya ynxu??" Yana fadin haka ya wuce sa ya xaga daya side din motar, da ido dogon Matashin ya bi sa bai ce komai ba, Alhaji Ahmad ya bude door din side din da Heedayah take, ya kamo hannunta ya sakko da ita daga cikin motar, Matashin ya d'an koma baya yana kallonsu a bit surprised, Alhaji Ahmad yace "Ka fiddo min laptop dina bayan motar, they are some other things ma ka taho da su ciki" Yana fadin haka ya nufi entrance din shiga gidan yana rike da Heedayah, Matashin ya bude motar ya dauko abinda yace masa sannan ya bi bayansu, Alhaji Ahmad na shiga parlor Rabi'ah da Khadija suka taso da gudu don rungume sa, sai dai ganin Heedayah da yake rike da duk suka tsaya basu karasa gun nasa ba, Khadija tace "Who is she Dad?" Yana kokarin cire takalminsa yace "Sabuwar 'yar uwar ku" kallon juna Khadija suka yi da Rabi'ah, ya karasa parlon ya xaunar da Heedayah kan kujera sai dai ta ki sakin hannunsa kmr xata yi kuka tace "Abba kar ka bar ni don Allah" Yace "Noo baxan bar ki ba, we are home yanxu" Yana fadin hka ya kalli Khadijah yace "Ina Mumyn ku?" Khadijah ta d'an cinno baki tace "Upstairs" ya daga Heedayah ya wuce sama da ita, Khadija da Rabi'ah suka juya suna kallon yayansu dake tsaye bakin kofa yana kallon ikon Allah shi ma, da sauri suka nufesa a tare suka ce "Ya Shuraim who is she? Wacece ita" Ko kallonsu bai yi ba, ya nufi part din Abbansu don ajiye masa system dinsa dake hannunsa. Alhaji Ahmad ya bude kofar parlon Mai dakinsa still holding Heedayah's hand, dai dai fitowar ta daga bedroom dinta, ya xaunar da Heedayah saman kujera kafin yace komai tana kare ma Heedayah kallo daga sama har kasa tace "Waye wannan kuma Barrister?" Yace "sannu da hanya ya kamata ki fara min sannan tambayoyin ki su biyo baya" a takaice tace "Toh sannu da hanya, wacce yarinyar ce wannan ka shigo min da ita har parlor?" Sai a sannan ya daga kai ya kalli matar tasa yace "Bakuwa ce" Ta d'an yatsina fuska tace "Bakuwa kuma? Daga ina? Kuma ina xa a kai ta?" Yace "Eh bakuwa.... Daga kano, kuma nan xata xauna in sha Allahu rabbi" Da mugun mamaki tace "Yar wacece ita din?" Yace "Baiwar Allah ce..." A kufule tace "Plss be straight barrister, ina ka samo yarinya? Kowa ma bawan Allah ne ai" Barrister yace "Gashi nan na gaya maki, what else did you want to know, me kuma kike son sani" kamar jiran tambayar take ta mayar masa da amsa da sauri tace "Manufar xuwanta gidan nan, sannan mun hada wani dangantaka ne da ita??" Ya gyara xama yace "Manufar xuwanta gidan nan shine don ta xauna da mu na wani d'an lkci, dangantakar mu kuma kawai shine kasancewar ta 'yar uwar mu musulma" Kallonsa ta dinga yi, surprised, Furious, and mad at the same time.... Blankly tace "I don't get you Abban Shuraim, ban gane abinda kke nufi ba, a ina kasamo wannan yarinyar??" Ya mike yace "Her parents are missing, so we need to look after her kafin Allah ya bayyanar da iyayenta, all that aside, she is blind Hajiya Maryam, makauniya ce...." Yana fadin haka ya fita daga parlon..... Hajiya Maryam da ta bi sa da kallon mamaki lkci daya tace "Tabdijam!!! Toh sannu Humanitarian, Do-gooder.... sai kuma nace maka gidana orphanage ne (Gidan marayu) ko kuma police station?? to wllh ka saurareni da kyau, yarinyar nan dai baxa ta xauna gidan nan ba, me muka hada da ita daga ganin yarinya a titi ka kinkimota ka kawo mana gida wai iyayenta sun 6ata kamar wasu gyada, Anya ma Barrister kasan me kake yi kuwa, yanda duniyar nan bbu gaskiya kwata kwata kowa ya xama mugu ya xama abun tsoro ka dauko mana yarinya ka kawo gida?? A'a wllh ba gidana ba, ka dauketa ka kai ta police station ko kuma ka kai ta gidan marayu" tana fadin haka ta wuce dakinta rai 6ace don daukan wayar ta, Heedayah dai na xaune sai kallon direction din da masifar ke tashi take yi, gaba daya a tsorace take, lkci daya hawaye ya kawo manyan idanuwanta.... Bayan minti biyar Hajiya Maryam ta fito dakinta tana kallon Heedayah tana huci ta daka mata tsawa tace "Ke maza tashi ki fita ki ban waje kar in illata ki...." Mikewa Heedayah tayi da sauri ta fashe da kuka tana laluben hanya tace "Abba where are you" muryarsa ta ji yace "I am here...." Har ya karaso cikin parlon kallon Hajiya Maryam yake, calmly yace "Wannan ya xama na karshe a gidan nan, kar ki sake yi mata tsawa, nace a gidan nan Heedayah xata tsaya har sai an samo iyayenta, I mean my words" bude baki tayi tana kallonsa da farko, sai kuma tayi wani murmushi me sauti tana tafe hannu tace "Toh sannu Humanitarian, idan ni ban kai inyi magana ka ji ba nasan baxa a rasa wa enda xa su yi maka ka ji ba, look Ahmad it's not as if i am being wicked, ni ba muguwa bace Allah ya ga xuciyata kawai xamanta ne damu bna so don hankalina bai kwanta da hakan ba, to wai ma akan me xata xauna da mu, kai da kke lawyer ai ya ci ace ka fi ni sanin me duniya ke ciki, to idan ba akwai wani boyayyen lamari a kasa ba daga xuwa meeting kano sai ka dawo da yarinya wai ka tsince ta a titi bbu iyaye, Kar ka manta idan kai lawyer ne to ni kuma matar lawyer ce...." Ya dakatar da ita yace "Wallahil Azeem Maryam wannan yarinya a hanya na hadu da ita kamar ynda na fada maki, mota ce ta bigeta muka yi asibiti da ita, I was there har ta farfado.... Let just stop all this, Maryam put Rabi'ah or Khadijah in her shoes plss" a mugun fusace tace "Allah ya kiyaye, I can't imagine my children in her shoes, why will I? Kar ma ka gaya min haka, Ni dai abinda na sani shine hankalina bai kwanta ba kuma baxai ma ta6a kwanciya da yarinyar nan ba, wa ya sani ma ko aljana ce da gashi haka??" Bai kuma ce mata komai ba ya kama hannun Heedayah dake kuka a hankali ya fita parlon da ita xuwa downstairs.... Hajiya Maryam ta kasa zaune a parlon nata sai xagaye take, bude kofar aka yi Shuraim ya shigo da sallama can kasa, Hajiya Maryam ta kallesa da sauri tace "Shuraim kana ganin mahaifinku koh? Me yake nufi da kawo mana yarinya gida ba dangin Iya balle na Baba, ya san yar wacece ko ma shegiya ce bai sani ba kawai ya kawo mana ita gida, wllh something is fishy, kuma in dai yarinyar nan xata xauna gidan nan sai dai mu bar masa gidan shi da ita gaskiya, don mu ba gantalallu bane, wai kuma makauniya ce kai ka ji fa???" Tun fara maganar ta sai a sannan Shuraim ya kalleta da sauri jin wai makauniya ce, Tayi mitsi mitsi da ido tace "Wllh haka yace Makauniya ce bata gani, kuma naga alamar hakan, she is blind, oh innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, me ya samu Barrister ni Maryam... Anya kuwa yana right senses dinsa??" Shuraim dai bai ce komai ba ya juya xai fita, a mugun fusace tace "Toh malam ba shiru xaka yi ba ka wani juya sumui sumui xaka wuce, xuwa xaka yi ka samesa tunda yana jin maganar ka, ka lallabasa ya fitar mana da yarinyar ya kai ta police station, bbu ruwana da gayyar tsiya, yarinyar nan baxata kwana gidan nan yau ba..."  Shuraim na fita ya nufi Part din mahaifinsa, ya bude kofar parlon da sallama, Heedayah ce kawai xaune kasan carpet dake parlon ga cup din fresh milk a hannunta, jin an bude kofa ta dakatar da shan madaran da take yi tana waige waige, bai kalli direction dinta ba ya nufi dakin Abbansa, sallama yyi bayan ya amsa masa ya shiga, xaune ya samesa gefen gadonsa, ya karasa ya xauna nan kasa gabansa yana kallonsa yace "Ya hanya Abba?" Abba ya kallesa yace "Alhmdllh..." Shuraim ya d'an shafa kansa yace "Abba, akan wannan yarinyar....." Sai kuma yyi shiru, Abba yace "Yes, what about her? Ina jin ka" Shuraim yace "Is she suppose to be here?" Abba yace "Of course, ai nan din gidana ne ba na wani ba, so why won't she be here?? Me kuwa xai hana xamanta a nan tunda na amince da hakan?" Shuraim ya girgixa kai alamar ya rasa abinda xai ce, Abba yace "Yes gidana ne, ba naka ba, balle na Mahaifiyar ka" Shuraim yace "But Abba hakan ba dai dai bane, bbu abinda muka hada da ita, ba mu san ta ba, we don't even..." Dakatar da shi Abba yyi so pissed off yace "Get out my frnd, who are you to question my orders? And don't u even have human conscience? Xaka so kanwarka ta tagayyara a rayuwa?" Mikewa Shuraim yyi yace "I am sorry" daga haka ya nufi kofa ya fita, satan kallon Heedayah yyi, lkci daya ya wani hade rai ya fice daga parlon.



07087865788

⚡ _Heedayah_⚡





_By Khaleesat Haiydar_✍?






5....

Jin budewar gate ya sa Alhaji Ahmad ya mike ya isa jikin tagar dakinsa yana kallon compound din gidan don ganin wanda xai fita, motar yayansa ne ya shigo compound din, ya bi motar da kallo har yyi parking, sannan ya girgixa kai ya koma ya xauna... Ba a dau lkci ba kuma wayarsa ya fara ring, ya duba ganin yayan nasa ke kiransa ya mike ya fita dakin, kwance ya ga Heedayah ta fara bacci nan kasa, ya d'aga ta ya kwantar kan kujera sannan ya fita, direct main parlor ya wuce, ya tadda wansa Alhaji Umar zaune saman kujera ga Hajiya Maryam xaune parlon ta sha kunu kai kace bata ta6a dariya ba, xaunawa yyi ya gaida Yayan nasa, Alhaji Umar ya amsa yana kallon Hajiya Maryam yace "Me ke faruwa Maryam" Ta kwantar da murya tace "kana ji Alhaji, Ko awa daya ba ayi ba da dawowan barrister daga kano, amma sai me??" Nan ta kwashe komai ta tsara masa, tana matsar kwalla tace "Saninta muka yi Alhaji? Ko me muka hada da wannan yarinyar? Mun san me yasa iyayen suka jefar da ita da har shi xai daukota, to gaskiya naga abun ba wanda hankali xai dauka bane shi sa na kira ka don kayi intervene don gaskiya I don't know what came over Barrister, ban san me ya samesa ba, kawai muna xaman xaman mu ya ja mana magana...." Alhaji Umar na kallon kanin nasa yace "Barrister wace yarinya ce wannan ka dauko ka kawo cikin gidan ka?" Alhaji Ahmad ya jinginar da kansa da kujera yace "Doctor nasan da kai ka ga yarinyar nn xaka yi fiye da abinda nayi ma... Sincerely I mean no harm to my family, taimako kawai nayi sbda Allah, and I thought they will also welcome the idea, na xata xa su so taimakon da nayi...." da sauri Hajiya Maryam ta katse sa tace "To family dinka basa son taimakon nan gaskiya, ur idea isn't welcome, kawai ka maida ta inda ka ganta, idan kuma xuciyar ka baxai yarda ka maida ta ba to ka kai ta gidan marayu..." Wani kallo ya jefa mata yace "Baki isa ki bani order a gidana ba Maryam, I did what I know is right, you are not in the place to kick away my decision, nace baki isa ba" Alhaji Umar na kallonsa yace "Hold on bawan Allah, bana son hayaniya, ka saurareni...." Alhaji Ahmad yace "Dr if you are in anyway doubting me ka kira abokin ka Asp Usman, he will explain everything to you, Babu abinda xai boye maka, shi ma ya bani go ahead din tahowa da yarinyar when I request doing so, ban taho da yarinyar nan ba sai da izini da sa hannun Asp...."  Mikewa Alhaji Umar yyi bayan shirun wani lkci yace "Ynxu ina yarinyar take?" Barrister ya mike yace "Mu je ka ganta tana sama parlona" Bin bayansu Hajiya Maryam ma tayi xuwa part din mai gidan nata da sauri, kallon Heedayah dake bacci Alhaji Umar ya dinga yi kafin yace "She so little" Alhaji Ahmad ya bude hannunsa yace "Of course she is" hannu Alhaji Umar ya kai goshinta ta bude ido da sauri ta kamo hannun tace "Abba..." Ya d'an yi jim sai kuma yace "How are you?" Shiru tayi tana kokarin mikewa ya dagata ta xauna, Hajiya Maryam sai kyabe baki take fuska a murtuke tana kauda kai, Alhaji Umar ya girgixa kai ya sauke ajiyar xuciya yace "This is serious... abinda xai faru ynxu shine ke Maryam kiyi hakuri ta kwana xuwa gobe xa a san ynda xa ayi in sha Allah, they will be a meeting tomorrow at my resident idan Allah ya kai mu" shi dai Barrister bai ce komai ba, Hajiya Maryam tace "Allah ya kai mu, amma wllh baxan rike yarinyar nan ba Kun ji rantsuwar musulmi sai dai duk abinda xai faru ya faru" daga haka ta fice daga parlon duk suka bi ta da ido. Karfe goma Barrister Ahmad ya fita parlonsa xuwa parlon Hajiya Maryam, kallo take ita da Rabi'ah da Khadijah a parlon nata, Khadijah tace "Toh Mumy me yasa bai kai ta orphanage ba??" Hajiya Maryam ta kyabe baki tace "Neman suna mana, ke ko bayan lawyer gashi Humanitarian din da ya laka ma kansa, to wllh ba dai wannan gidan ba, dai dai nake da su dukka...." Rabi'ah tace "And kuma yace makauniya ce fa" Hajiya Maryam ta dau apple din gabanta tace "Ko kurma ce sai ya fitar da ita gidan nan, ban gama wahala da nawa yaran ba baxai kwaso min wata can ba, ba dangin iya balle na baba, shi dai ya cika fitina ne kawai" Khadijah tace "Ni dai idan yace nan xata xauna gwara in koma gidan Aunty Fatima, I can't stay in the same roof with her, what if muguwa ce" Hajiya qMaryam tace "Sai dai shi da ita su bar mana gidan...." Shigowan Abban yasa tayi shiru, Yana kallonsu gaba daya yace "Bani da abinci a gidan nan yau kenan?" Hajiya Maryam tace "Ohh na xata you are full ai da naga kafi concentrating kan yar tsintuwa, ban san kana tare da yunwa ba, Rabi'ah go and serve him downstairs" kallonta kawai yake kafin ya gyada kai ya juya ya fita parlon, a hankali Khadijah tace "Abba is just acting strange, dubi fa ko kula mu bai yi ba tunda ya dawo..."  Hajiya Maryam tace "Atoh ina xai kula ku ga makauniya ya saka a gaba Khadija" Rabi'ah ta tashi ta fita don kai ma Abban nata abinci parlonsa, Yana xaune parlon yyi nisa tunanin da yake, ta ajiye abincin tace "Abba ga abincin" yace "Baxan ci ba, ki dibar ma yarinyar nan kawai ki fita da sauran" ta kalli Heedayah dake kwance fararen idonta a bude, ta d'an hade rai ta bude abincin ta diba kadan ta daura nama daya, kallonta kawai Abban nata yake yi yace "Add the meat" Ta kara daura wani naman sannan ta mike ta fita da sauran abincin. Mikewa yyi ya tafi gun Heedayah yace "kina Jin yunwa ko?" Ta gyada masa kai, ya kama hannunta ya dau plate din abincin ya fita, main parlor ya koma, ya shiga wani d'an corridor ya kwankwasa daya daga kofofi biyun dake wajen, wata matashiya da baxata haura talatin da biyar ba ta bude kofar, ganinsa ta durkusa da sauri tace "Sannu da dawowa Alhaji, ina yini" yace "Lfya lau, ga wannan yarinyar ki kula da ita, ki bata abincin nan, sannan ki taimaka mata tayi wanka ki mata shimfida ta kwanta, tana da matsalar ido" Matar ta kama hannunta da sauri tace "To in sha Allahu Alhaji" daga haka ya juya ya bar wajen bayan yyi mata sai da safe. Washegari da ya kasance lahadi bacci yan gidan suka dinga yi har karfe takwas, Hajiya Maryam ta sakko parlor wajajen tara don ganin ko Saudat ta gama shirya breakfast, Kitchen ta sameta tana juye ruwan Lipton dake ta kamshi a flask, alamar dai ta gama komai shi kadai ya rage, Heedayah na xaune daga kusa da kofa hannunta rike da cup din shayi da Saude ta hada mata ga plate din kwai da dankali da plantain, Hajiya Maryam ta wani xaro ido tace "Saudat me xan gani haka? Wa ya saki wannan aikin, a ina kika ga yarinyar? Ko a ina kika santa?" Da sauri Saudat ta xube kasa tana gaisheta tace "Hajiya... Alhaji ne ya kawo min ita jiya da daddare yace in kula...." Tsawa tayi mata da karfi tace "Toh wllh a bakin aikin ki, da ya kawo maki ita baki iya xuwa ki sameni ba? Kawai sai ki yanke hukunci sbda ke ke ajiye da kanki? To wllh kin gama min aiki a gidan nan yau, yanxun nan xa ki kama gabanki" Hakuri Saude ta dinga bata a tsorace tana cewa "Hajiya wllh Alhaji ne ya kawo min ita kiyi hakuri ki rufa min asiri, ni ban san komai ba" Hajiya Maryam tace "Ni dai nace kinyi na aikin ki wllh, maxa tattara yanaki yanaki" daga haka ta juya ta fice daga kitchen din tana huci. Karfe goma Alhaji Ahmad ya dau Heedayah suka fita xuwa parking space, Hajiya Maryam dake xaune ta bi sa da kallon mamaki sannan ta kalli Shuraim dake operating laptop a parlon tace "Ka gani ko Shuraim, gaskiya abun nan ya fara bani tsoro, wannan abu ba na hankali bane... Something is wrong somewhere, what is wrong with your father" Shi dai kallonta kawai yake bai ce komai ba, wayarsa ya fara ring ya dauka ganin Abbansa ne ya kai kunne, Daga daya bangaren Abba yace "Ka gaya ma babarka karfe sha daya ne meeting din don Dr ya kirani xai yi tafiya" Shuraim yace "Toh Abba" Daga haka ya katse wayar, Yana kallon mahaifiyarsa yace "Abba yace Baffa xai yi tafiya, so da wuri xa ayi meeting din" mikewa Hajiya Maryam tayi tace "Toh ai a shirye nake sai ka kira kanninka duk mu duguma xuwa gidan, wato baxai iya gaya min ba sai dai ya bada sako a bani, to duk muje ayi ta ta kare yanxu" Babban gida ne sosai don har ya fi na Barrister Ahmad girma, Shuraim yyi parking a parking lot din gidan, Mumy ta fito ta nufi hanyar shiga gidan, direct dakin Hajiya Amina Uwar gidan Alhaji Umar ta nufa, bayan sun gaisa Hajiya Amina tace "Daxun nan Alhaji ke ce min akwai meeting wai kuna hanya, ni dai nace to Allah ya sa lafiya" Mumy tace "Ina fa lafiya, wllh ba lafiya...." Tsaf ta kwashe ma Hajiya Amina abinda ke faruwa ta sanar mata, Hajiya Amina ta buda ido sosai tace "Iko sai Allah, to meye ma'anar hakan da Barrister yyi??" Mumy tace "Ni nasan masa, ni dai wllh wllh kinji rantsuwar musulmi koh?? To yarinyar nan baxata xauna tare da ni ba, ba ruwana.... Haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba yanda duniyar nan ta lalace..." Hajiya Amina tace "Toh ai dama bbu wannan xancen, taya xaki rike yar da ba a san tushenta ba, kada ki kuskura wllh, Wai kuma makauniya kamar dai a wasan kwaikwayon hausa..." Mumy tace "Ke ki bari kawai, nasan karshe Dr yace a barta gidan nan...." Da sauri Hajiya Amina ta katse ta tace "Wajen wa??? Haba wannan ai labari ne, bbu wanda xai soma wannan gangancin..." Dariya Mumy tayi tace "Toh ba sai abokiyar xaman ki ta riketa ba" Hajiya Amina tayi tsaki tace "Ai sai dai ta kai ta gidansu amma wllh bbu wajen xaman yarinyar nan a gidan nan" Mumy tace "Atoh, taimakon da idan kayi ma yanxu yake xame maka jaraba" Mikewa tayi tace "Bari in je in gaida tsohuwar can..." Hajiya Amina tace "Tana can kuwa yau bbu mutunci ta tashi...." Mumy tayi dariya tace "Ni dai Allah ya dube xuciyata ya rabani alakakai..." Hajiya Amina tace "Wa?? Ai xance komawa gidan ki take yanxu" Mumy tace "Tabdi, xaman mu baxai yiwu ba, wnn karan karara xan fito inyi magana" daga haka ta fita dakin. Da sallama Mumy ta bude kofar wani daki ta shiga ciki, babba daki ne sosai bbu abinda bbu a ciki irin dai na tsoffi, Shuraim na xaune kusa da wata tsohuwa da tayi tsit lkci daya ganin shigowan Mumy, Mumy na murmushin yake ta xauna kasa tace "Sannu Kaka...." Tsohuwar na gyara daurin dankwalinta tace "Sannu..." Mumy tace "An tashi lafiya kaka" kaka tace "eh toh lafiyar kenan, amma kin gan ni nan?? Wllh tun safe bbu karen da ya leko ni a gidan nan har shi Umarun, hana rantsuwa dai ya shigo da Asuba ya gama xamansa a can na kusan minti talatin ya fita, wllh Maryam gidanki ya fiye min nan sau goma, gwara ke da yunwa kawai kike bari na...." Mumy ta hadiya abu da kyar ta sunkuyar da kanta, Kaka tace "Kinga wannan bakar matar Amina?? Ni dai ina ga da kyar ta wanye lafiya, ni dai ki tafi da ni gidanki" Da sauri Mumy tace "Ai hakuri ake yi a ko ina kaka, ko ina hakuri ake ba wai wani abu ba, kawai ayi ta hakuri tunda Doctor ya fi son yana ganinki kusa da shi, kuma ma hakan ya fi wllh, yanxu ma meeting muka xo yi bbu lafiya" Da sauri kaka tace "Me ya faru kuma?" Mumy ta gyara xama tana tabe baki, nan ta tsara ma Kaka duk yanda aka yi daga daren jiya har xuwa safiyan yanxu har da kari, Kaka da ta gwalo ido tana kallonta tace "Ba lafiya, shi Ahmadun yace bbu wanda ya isa ya saka shi ya kuma hanashi?" Mumy tace "Toh nima dai ban gane kan lamarin ba, abun dai gashi kamar almara" Kaka tace "Toh ina yar makauniyar take yanxu?" Mumy tace "Tun sassafe ya fice da ita ko bi ta kanmu bai yi ba....."
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 29,503 09-10-2018, 08:20 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 11,459 08-18-2018, 01:15 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 24,858 08-10-2018, 01:18 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 20,044 08-10-2018, 12:48 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 24,871 08-05-2018, 11:27 AM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat haiydar Gimbiya 0 53,300 08-03-2018, 05:26 AM
Last Post: Gimbiya
  *CAPTAIN_AHMAD JUNAID* By Khaleesat Haiydar_ ✍? Gimbiya 0 40,819 11-16-2017, 12:51 PM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)