The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KASUWANCI NA* by ASMABAFFA
#1
????
????

   KASUWANCI NA
              1

Official

By
AsmaBaffa

BISMILLAH

Alhmdllh fans Allah ya kara kawo mu sabon Novel dina KASUWANCI NA da fatan zaku bibiyeni muji yadda zai kasance,Fatana Allah yasa mu karu da juna,Allah yasa masa Albarka ya fadakar ya kuma nishadantar daku.ina matukar Godiya masoyana,masoya novels dina,masu sharhi musamman AsmaBaffa fans club,Taskar fiddausi sodangi,da kuma House of Hausa Novels ina miko dubun gaisuwa ta gareku na gode da Sharhi.
       
   Da fatan zaku ci gaba da Sharhi a kai Kai sabo da shine yake guiding writer ta rubuta muku me dadi da ma'ana,idan ba Sharhi baya tafiya dai dai,Dan Allah a dinga Sharhi fans ana nishadi musamman yan gp na.
    Akwai gps da dama da basa Sharhi ko tnx baza suyi ma ba,zaka ta musu posting shuru,sai ranar da ba ayi posting ba sai a fara neman novel ci gaba.duk gp din da basa cewa ko Hi zan daina musu posting wlh,da nayi daya biyu naji duf to shike nan sai suji duf nima??

 Wannan page na farko na Sadaukar dashi gareki sweet frnd FLOWER.

Kudin cinikin awarata nake irgawa duk da ba kudin arziki bane amma dukkansu daga yan goma sai yan biyar sai ko ashirin,kanwata na shiga kwalawa kira MEENAT wai baza ki fito ba sai na shigo na mareki,Maganar AMMA naji tana daga gefena a kwance saman yar tabarma tace Haba MUFEEDA ta wannan wacce masifa ce haka dan Allah ki dinga dagawa yaran nan kafa kannenki ne fa,Amma kina dai jin tun dazu nake jiransu su fito su tafi Islamiyya amma sai nauyi sukeyi kuma sun San cewar anjima zan soya Awara,gashi gobe zasu zo suna takura mana a basu kudin Break, to ai sai bisu a hankali dan Allah kinga ni ba lafiya ce dani ba kece komai nasu kece uwarsu kece Ubansu Mufeeda kece komai dinmu,Zuciyata ce tayi rauni nace to Amma ba komai na Dena kiyi hakuri Allah zai baki lafiya kinji,ga kudin nan Amman mu bari na gyara gidan na daura mana tuwo naga muna da ragowar garin masara,Murmushi Amma tayi tare da kallona tace Mufeeda Allah ya miki albarka Allah ya baku miji na gari,ya baku yara su rama muku abinda kukayi mana na alkhairi,Mufeeda yau shekarar babanku Sha uku da   bacewa,har yau ina Sa ran watarana zai bayyana da Zanfi kowa murna ya ganku Ku uku kun Zama yan mata gaku kyawawan gaske kamar indiyawa,musamman ke Mufeeda kunfi kama da Shuwa sosai mahaifinku kika biyo domin shine fari kamar balarabe haka yake har kin fishi Hasken fata ma,su kuma su Meenat sune masu kalata wato su ba farare ba su kuma ba wanda zai kira su bakake duk gaku Allah ya bani Ku kyawawa farare daku amma duk kyan nan sabo da talauci ko Sallama ban taba ji ance ana sanku ba,wanda na tabbata da masu kudi ne komai muni auruwa sukeyi,musamman ke Mufeeda kin kai har 16yrs amma nafi so na aurar dake tunda ba makaranta kike zuwa ba,Baki na turo gaba tare da sakin shagwaba ina shure shure kamar yarinya ina kukan sangarta Allah Nidai Amma bana son aure kuma ma nawa nake,hmmm Mufeena Mufee tawa ai gashi nan kin fara girma har da Irgan dangi,Ammah mene Irgan dangi? tace gasu nan a kirjinki Kin fara Nono Mufeeda akwai maganar da za muyi anjima idan yaran nan sunyi bacci,kunya ce ta kamani nace to Ammah Allah ya kaimu bari na gama aikin ko kina da bukatar shiga bayi na taimaka miki? Ae rikeni muje Mufeedata Allah ya miki albarka,

kama Ammah nayi da kyar tana rike da sandar karfe wacce a asibiti aka bata ita na kaita har bayi ta tsuguna tare da Dafe jikin bango,sai na fito bayan ta gama abinda zatayi ta kwala min kira na koma nace Ammah ko na goyaki? Dariya tayi tare da cewa na gode Yata baki ji me Doctor yace ba?na dan dinga takawa,murmushi nayi wanda yasa hakorana kanana farare suka bayyana,dimple dina ya lotsa riketa nayi muka fito tare,sai Lokacin kannena MEENAT da MA'EESHAH suka fito cikin shirin makarantar Islamiyya,na kallesu cikin tsafta kayansu yasha guga,sun bani sha'awa naji inama nima haka nake zuwa kullum amma ina bazan samu dama ba,amma Alhmdllh tunda kannena suna zuwa ba matsala.Amma ce ta kalleni cike da tausayawa tace Mufeedata? Da sauri na dawo daga tunanin dana lula na kakalo Murmushin dole nace Ammah ki huta bari na gama aikin naje na siyo kayan alewar madara,kinga gobe kuma da safe Kosai yana jira shima,amma ni naga awarar tafi riba ma,Ammah tace Mufeeda wannan satinfa naji zuku yi Allurar polio vaccine da kukewa yara,Mufeeda tace wlh Ammah ba sauki abin ni haushi na ma gidan masu kudi kantama kantama na GRA Ammah ayi ta wulakanta mu da kyar mukeyi muna Shan wahala,wani gidan ma kafin ka shiga tashin hankali ne ko ina securities ne,aikina naci gaba da yi muna hira da Ammah mahaifiyarmu,saida na gyara gidan tas na kunna turaren Wutar kamshi duk da gidan ba wani me kyau bane amma ita tsafta bata buya,Allah ya haliccemu da tsananin Tsafta wanda duk Bala'in mutum bazai ce gidanmu akwai digon wani abu na kazanta ba haka muke gaba dayanmu,miyar Kubewa busashiya na kada,na tuka tuwon masara na kwashe cikin wata tsohuwar Cooler dunmu,nayi wanke wanke da wanka na shirya cikin kayan gwanjo na Riga blue me layi layi na fari,tare da skert shima ruwan goro,farar Powder na shafa da Vaseline a lebena,Hijab me hannu nasa wanda ya wuce gwiwata nace Ammah bari na siyo kayan nan nazo na fara soya Awarar dare kinga magriba ta gabato,Fadada murmushinta Ammah tayi tace a dawo lfy Allah kiyaye hanya.

    Ameen nace tare da fita waje ina dan wasa da kudin dake hannuna cikin unguwarmu layinmu na bari nayi tafiya me Nisan gaske Allah yasa ma ba rana sai da na gaji sosai kafin na karasa wata yar kasuwa karama da ake saida kayan abinci da fruits etc, inda na saba siyen waken kosai da sauran kayan Sana'a ta na karasa da fara'a dukkanmu munyi sabo da juna sabo da yau da kullum,kudin na mika ina bi ko wanne layi duk na hada abinda nake bukata kaf aka hado min a wani katon buhun bacco na fito da kyar nake dagawa ina nishi haka nake tafiya a hankali, wani dattijo ne yace yarinya kawo a daura miki a kai ai zaifi ko? Murmushi nayi masa ya amsa ya daura min na masa godiya naci gaba da tafiyata da kyar,sai da nayi nisa na shiga wani layi wanda manyan gidajen masu kudi ne na gani na fada,GRA ce ta masu kudi nabi ta ciki sabo da kullum ta hanyar nake wucewa ko sabo da nasha kallon hadaddun gidaje tare da Lambu masu kayatarwa duk kuwa da cewa na saba shiga sabo da rigakafin polio na nake aikin dole muna neman Izni mu shiga sabo da tare da masu Unguwanni muke yin rigakafin dole su yarda a shiga ko Police su kama me gidan haka aikin yake.

    Wasu motocine a kalla sun kai guda takwas a jere dankara dankara ban taba ganin irinsu ba sai yau da suka shararo da uban gudu kamar zasu tashi sama cikin layin,dai dai wani gida suka Parker wanda gidan yafi kowanne kyau a layin da gudu na matsa tare da rakubewa a jikin ginin gidan ina kallon ikon Allah, 

da sauri naga sojoji sun fito daga sauran motocin tare da zagaye wata uwar shahararriyar mota me kyau da tsada na fitar hankali,wani dattijo ne ya fito fari kar dashi yana sheki da Alama kudi sun ratsashi a matukar hasale ya fito daya bangaren ma wani wani mashahurin matashi ne ya fito da sauri a matukar hasale cike da isa hade da Izza Saurayin kamar balarabe ko Bature haka yake duk Haske da kyau na da ake fada sai naga wannan ya wuce nawa ya zartani a komai nan take na raina kaina musamman yanda na kalli shigata babu maraba da Almajira mara gata.

    Saurayin bazai wuce 35years ba ya kai karshe a haduwa gashinsa abin kallo kansa style din askinsa abin kallo ne abin birgewa da sha'awa,idonsa ya bude,ban San sanda nace wow a raina ba idonsa kamar madara yana wani lumshewa gasu Dara Dara,girarsa har kamar zata hade,ga wani dan saje da gemu masu matukar kyau da suka kawata fuskarsa,hancinsa me matukar kyau kuma baiyi tsini da yawa ba,dan bakinsa wow masha Allah ga wasu pink lips duk da cewa nima bakina kamar cokali bazai shiga ciki ba gashi lips dina jajir dasu amma sai naga wannan kam nasa sunfi nawa komai,kuma sai na tashi me duhu a kansa ko dan shi Hutu da Naira sun ratsashi ne oho, Kana nan kayane a jikinsa wandon pencil Jean brown color,rigarsa fara tas da top Brown ya daura sama takalminsa fari half cover flat shoe,shi ba gajere ba shi ba dogo da yawa ba,haka ba ramamme ba kuma bame kiba ba,kai masha'Allah da a mafarki na ganshi ba shakka Aljani zance.

     Dattijon cikin farar shadda kar cike da Fada yake magana da alama da Saurayin yake,AAYAN  will u hear me out pls,da sauri Saurayin ya bata rai cike da fushi yana shagwaba kamar dan yaro cikin muryarsa da ta girgiza ni sabo da dadinta yace pls Abbi I knew it just leave me alone For God sake,Hajja she is ur mother not mine so Abbi kaine ya dace kabi Umarninta ba ni ba,taya zata dinga takura min ni kadai ne jikanta gasu nan da yawa maza da mata,ko kawai dan ni bani da Mahaifiya bata raye,sannan mahaifina bashi da lafiya bakwa kaunata shi yasa ni kadai ake ma haka yanzu ina Abuja kace dole sai na dawo Kano da Zama kusa da Ku,ban taba wani rayuwa a kano ba ka sani sabo da kana matsayin mahaifina nake maka biyayya,sabo da gudun saba maka na bar muku gidanku,bana amfani da sisin kudinka,Allah ya bani nawa Abbi har na fika ma maybe kudin,But why me,why are u doing this to me,kowa a Family kaf maza da mata nine ba a so me nayi musu?idan sabo da Umma ne bata raye sai na huta,Abbi ban shirya aure ba kunsa nayi ba muguntar da ba ayi min ba,haka mun rabu,kun kara aura min wata itama mun rabu sabo da matsalar dake damuna na rashin lafiyar haihuwa Abbi kun San bani da lfy bazan iya Rayuwar aure da mace ba akan me zaku ce na kara auro wata so kuke mata su kasheni bazan iya musu amfanin komai ba,dalilin bacin rannan da nake Sha kasan yanzu Hawan jini gareni me karfin gaske ko wanne lokaci zan iya rasa raina,sannan kasan Ina da diabetes dalilin Hawan jini yasa ya kamani tawakali da addua nakeyi,Abbi why not bakwa tausaya min,bakwa tausayin rayuwata tun tasowata a wahala na tashi a duniya,wannan yasa na tsani mata wlh Bana kaunar duk wata budurwa komai kyau da hankalinta,dalilin haka bana Hulda da kowa family da frnds etc ni kadai nake rayuwata sabo da bakin ciki da halin da nake ciki shi yasa nayi nesa da kowa,gwiwoyinsa ya  dire a kasa hawaye na kwarara a idonsa kamar ruwa tare da rike kafar dattijon yace Abbi ka fadawa Hajja zan zauna daku amma pls kar ayi min aure again ko me kuke so wlh zanyi amma yanzu banda aure,Abbi ka tuna kusan mutuwa nayi yanda mata suka ci min mutunci.

    Kallonsa Dattijon yayi tare da cewa tashi Aayan,zan yi shawara da yan uwana, muyi deal duk abinda mukace zakayi ka yarda? Ba tare da yayi tunanin komai ba Yace ae Abbi na yarda indai bazanyi aure ba shike nan,Abbi yace an gama ko ka samu Lfy kana haihuwa sai na yarda zakayi aure ka tabbatar?Kuma ko kaga wacce kake so baza ka aureta ba har sai in mune muka yarda?cike da murna yana murmushi ya daga kai alamar yes ya Amince,Abbi yace Good for u,kar kaga bani na haifeka ba kace zaka min butulci zan iya yi maka abinda baka tunani,ka dinga tunawa da halina kasanni sarai zan iya yi maka ko mene ne ba ruwana,Shi dai Bayan murna yake yace ya yarda,Tashi muje daga yau ka dawo Kano gida daya zamu zauna sai dai jefi jefi kaje Abuja harkokin business dinka shima sai idan da yardata idan kuma kaki zan iya haram tama Business dinka gaba daya kasan nasan komai akan hanyoyin da zan lalata duk dukiyar daka mallaka,

Aayan ne yayi murmushi tare da cewa Abbi matukar baza kuyi min aure na zauna da mace ba zan iya mallaka muku komai nawa,na tsani mace a duniya ni bana son Zama dasu wlh ko yan uwana banso,kallon tsana Abbi yayiwa Aayan tare da cewa dan kawai baka da lafiya ne Man amma wa yaki mata?ai mata sune jin dadin duniya,kaga duk son kudina?Saurayin ya daga kai yana murmushin takaici,Abbi yace to duk kudin da nake nema sabo da mata nake nemansu,mata mutanenmu in ba su mene amfanin kudi.
   Kai Aayan baka da amfani a duniya fa da kai da gawa daya kuke Banga Amfaninka ba sam,to kai baka haihuwa,baka iya Yiwa mace komai me kakeyi kake wahalar da kanka wajen neman kudi,gaka a haka kamar Namiji Amma na tabbata in dai ba mune muka zaba maka mace ba irin almajira ko talakawa sune suke neman kudi sune yan wahala sune wahalallu wanda basu san kansu ba,basu san me duniya ke ciki ba,basu da wani amfani da irinsu ya dace a nema a aura maka sune watakil ka samu me son kudi tayi kasuwanci da kai ta samu kudi ta zauna da kai da hakuri.

    Aayan yaji matukar zafin kalaman Abbi wanda gaba daya ji yayi kamar ya mutu Sabo da bacin rai,haka ya hakura ya danne bakin cikinsa Amma idonsa ya kada yayi jajir,sai da Abbi ya gama gasa masa bakaken maganganu masu zafi sannan yace tashi muje ciki kasa a kawo ma motocinka kasan ko aron nawa ko na gida babu me baka kamar yanda kace kowa yayi amfani da kudinsa,Aayan yace ai duk new nayi Order an siyar da wancen saban yayi za a kawo min  gobe,dariyar mugunta Abbi yayi tare da cewa kana kokari fa wlh ni da kai da gawa haka nake kallonka baka da amfani a duniya me zaka amfanawa wani?ko mace baka amfana mata komai ba sai wa? Bakin ciki ya tokare zuciyar Saurayin yana tsaye a gate har Abbi ya bawa Sojojin da suke can gefe dasu Umarnin su shigo da motocin gida,nan suka bar Aayan wanda ya dafe saitin zuciyarsa da hannunsa,har suka shige da motocin gidan,suna rufe gate din ya fadi a wajen ya sankame kamar ya mutu,gashi unguwar shuru ba kowa bare a taimaka masa.

    Ni da nake Rabe ina jin komai da Sauri na jefar da kayan dake kaina nayi kan wannan Saurayi cike da tausayawa,tunani na sumewa yayi,na rasa ya zanyi na tasheshi robar ruwa dake hannunsa na Eva na fisgo da Sauri hannuna na rawa na bude tare da kwara masa a fuska Amma shuru bai tashi ba,hannayena biyu na daura saman kirjinsa ina dannawa kamar yanda nake gani likitoci nayi,yi kawai nakeyi ba ji ba gani danna kirjinsa nakeyi sosai ina nishi,a rude na kara kwara masa ragowar ruwan na sunkuya a kansa kamar zan shige masa ciki,kamshin turarensa yasa kamar na sume Sabo da dadi,fatarsa laushi kamar auduga lumis,wukil naga ya bude ido mun hada ido dashi kafin na kifta ido naji an sharara min uban Mari sai da na daina gani na wasu yan lokuta,kafin na dawo hayyacina yasa kafa ya harbar dani da mugun karfin da sai da nayi uwar Sufa na tuntsira naci ta ka na kife can gefe yaraf,nan take lebena ya fashe fuska ta ta kumbura,sabo da rashin Imani bai kyaleni ba takowa yayi har inda nake ya kara Sa kafa yayi ball dani sai da kaina ya bugu da wata yar bishiya,kafa yasa ya take hannuna dake yashe kasa ya murza,idonsa yayi ja da hannu daya ya damki wuyana ya shake tare da rabani da kasa ina kakari,Mari ya shiga yarfa min ban san iyakacinsu ba sannan ya jefar dani kasa kamar wani kayan wanki,Kuka me karfi na saki duk dauriyata ban san inda kaina yake ba,tunani na mahaukacine dama ashe,ina ta kuka a wajen Fuskata ta kumbura sosai jikina duk wani wajen ya farfashe Sabo da ball da ya dinga yi dani,tsorinsa ya shigeni ina nan wajen har ya shige cikin gidan da motoci suka shiga,Allah ne ya taimakeni wani dattijon kirki yazo wucewa a motarsa yace yarinya motace ta bigeki?Ban san me zance ba kawai sai nace kare ne ya biyoni shine na dinga faduwa,mutumin bai yarda ba Amma ya Kira Driver dinsa yace ka dakko mota ka kai yarinyar nan asibitina ka samu Sajeeda tayi mata dressing ka maidata gidansu kayi Sauri dare ya fara,godiya nayi masa ina kwance a kasa ina tunanin zalincin da Saurayin nan ya gwada min tare da rashin Imani daga taimako sai naci Dukan tsiya,
haushinsa naji sosai a raina ga tsoronsa da ya dasu a Cikin raina bana fatan sake ko kallonsa Sabo da tsoronsa nake ji yanzu.

   Ina tunani a kwance Dattijon Driver ya karaso tare da bude min mota da kyar na iya shiga motar,Driver ya saka min kayana a Cikin motar wanda na siyo a kasuwa,wani hadadden asibitin kudi ya kaini nan take akayi min komai da ya dace aka bani magunguna da Alama asibitin dattijon mutumin ne da ya Bada motarsa a kaini gida,Driver na gwadawa gidanmu ya kaini har kofar gida sannan ya miko min dubu biyu yace na sha Maltina inji Alhaji me gidansa,da kyar na yarda na karba,shima sai da Driver ya nuna baiji dadi ba sannan na karba tare da zuba godiya na dauki kayana na shige gidanmu shi kuma yaja mota ya tafi,ina shiga gida Kannena Meenat da Ma'eeshah har sun yanka awarar suna jirana da gudu suka taso suna Sister Mufee me ya sameki?lfy?hatsari kikayi ko motace ta kadeki,kinga yanda kika koma kuwa,Da Sauri Ammah ta fito da Rarrafe kamar zata kifa Sabo da rudewa tana Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un shine Abinda Ammah ke furtawa tana Hawaye tare da cewa me ya samu Mufeedata?Me ya samu katangarmu? Kuka na fashe dashi me karfi tare da Rungume Ammah ina cewa ba komai Ammah a wani layi ne kare ya biyoni na dinga gudu na fada cikin kwalabati da kyar wani ya taimakeni ya kaini asibitinsa kinga an bani magani harda kudi dubu biyu na shan Madara da Maltina,Ammah tace wannan waye me kirki haka?Wlh Ammah wani  ne Doctor ne Babban mutum ya sa Driver dinsa,to ku dai kiyaye da mazan zamani a tsare mutunci,Alhmdllh tunda komai yazo da sauki,Meenat ki dafa mata ruwan zafi ta gasa jikinta taci abinci tasha maganin ta kwanta,ke Ma'eeshah jeki kofar gida ki fara soya awarar kafin yan siya su fara taruwa, mikewa mukayi tare da aikata abinda Ammah ta ce.

    Bayan nayi wanka na gasa jikina Mai na shafa sannan na Sa doguwar riga mara nauyi itama yar gwanjo ce,abinci na dauko tuwon da nayi dazu naci na koshi domin ni cuta bata hanani cin abinci,komai rashin lafiya sai naci na koshi nayi luf,bayan naci Ammah ta dinga ballo min maganin tana bani ina sha har na gama,tace kawo na shafawa na shafa miki,Ammah zan shafa ki barshi kinga ke ba lafiya gareki ba, bayan na shafa jikin Ammah na koma na kwanta ina tunanin Saurayin dazu tare da maganganun da naji sunyi nake ta faman tunani shi kuwa mene tarihinsa me mutanen nan suke nema dashi ne haka,tunowa da nayi irin rashin Imaninsa nan take na firgita tsoronsa ya kara shigata na kankame Ammah har bacci ya kwashe ni,. Washe gari da asuba da kyar na tashi na gabatar da Sallah tare da Azkhar kamar yanda muka saba gaba dayanmu,Bayan gari yayi haske naje da Sauri na hada wutar  itace na daura ruwan zafi yana tafasa na dama koko sannan na kafa daya kaskon gefe daban na fara suyar kosan siyarwa ta,ana sallama ana siya sai kuma ruwan zafi ya tafasa na kwalawa su Ma'eeshah kira suzo suyi wanka su wuce schl,da Sauri sukayi wanka suka shirya tsab cikin Uniform dinsu wanda yasha wanki da guga,Kokon dana dama musu suka eba tare da kosan suka ci suka koshi sannan suka kaiwa Ammah nata itama,Nima ina aikin Suya kosan siyarwa ta ina shan koko da kosai na ,Sister ya jikin naki gashi kumburin ya baje,murmushi nayi tare da cewa Alhmdllh kuje kar kuyi late ayi karatu da yawa banda wasa,bani da burin da ya wuce naga kunyi karatu sisters ku dage cikinku mu samu lauya da Doctor dariya suka dingayi Ammah ma tana tayasu cike da tausayawa Mufeeda,kudin Break na mika musu nace gashi yau ba ashirin za a baku ba Hamsin Hamsim zan baku kuci me dadi,murna suka dinga yi suna tsallen murna tare da godiya,Nace kuje mana Gashi karbi Meenat kece babba kuyo mana Cefane muyi miyar egusi da tuwon shinkafa ki taho da nama na dari Uku muma muci dadi ko Ammah? Murmushin farin ciki Ammah ta saki tare da kallona tace Allah ya muku albarka dai yaran nan,

bayan sun tafi na gama siyar da kosai na ya kare kaf ,ina ta faman murna na lallaba jikina na gyara gidan fes na tattaro kayanmu har na Ammah da kannena na wanke su fes na shanya,Ammah wacce ta rarrafo ta zauna saman tabarma tace Mufeeda me za a dafawa yan makarantar ne yau? Na gaji taliya zan dafa da mai da yaji kafin dare sai muyi tuwon,eh hakan ma yayi ai tunda muna samun na sawa a bakin Salati ba kamar lokacin baya ba,tashi ki kokarta ki gama ke ma ki kwanta ki huta idan sun dawo yau ba Islamiyya sai suyi girkin daren,amsawa nayi da to na mike nayi abinda ta Umarceni,na hada mata ruwa na kamata har Nayi tayi wanka fes na koma na riko ta muka dawo naa tayata shiryawa tsaf muna hira. 

ina gamawa na hada yaji me dadi yasha hadi na soya manja,na gyar dan kitchen dinmu wanda yake na karfen langa langa ne,Ammah na zubawa na kawo mata tare da ruwa,taimaka mata nayi ta zauna nima nasa hannu muka ci muka koshi muna Bada dunkulen Maggi star,Sallah muka gabatar ta Azahar,sai ko mukaji Sallamar Yan makaranta su Meenat,da gudu suka shigo suna sallama suka rungumeni,Ido na waro mene hakan? Sis wlh wani ne yace yana son Ma'eeshah mu kuwa muka zabgo da gudu,ke kin ganshi wlh in banda wari ba abinda yakeyi wai yanzu Ammah duniya ta lalace me kudi bazai Hulda da talaka ba komai kyanka indai ku talakawa ne babu me kulaka sai talaka dan uwanka,Ammah tace ai duniya haka ta koma idan da gate a gidanku to me mota ne zaizo idan babu kuwa sai dai dan uwanka talaka,Yanzu kalli irin kyawu da Allah ya zuba muku Amma babu me zuwa wajenku talakan ma ya gagara sabo da talakan ma gudun talakawa yake Allah kayi mana magani,dan baki na na turo Ammah ke komai kice aure wai shekarunmu nawa,dan gidanku gata nake nema muku yanzu ko idan da kunyi aure ai kuna da yancinku ko ba komai sai kiga kun huta shine burina,Ammah wa zai kula dake to aini aure bai taso ba a wajena Ammah wlh Bazan iya aure na barki a haka ba ko da kuwa zan dawwama ba aure ne a duniya,ki daina zancensa indai kina so hankalina ya kwanta,Maeeshah tace Sis manya bari muyi girkinmu,harararsu nayi nace kuje dai ku cire Uniform kuci abinci kuyi sallah ku huta sai kuzo ku fara aikin,ni yanzu kun san kasuwa zanje siyo kayan da nake siyarwa citta,kaninfari,barkono,wake,kanwa,Sabulu,omo,maggi kala kala,har su Aya duk siyarwa nakeyi duk wasu kana nan Abu na amfaninmu kayan girki ina siyarwa a gidanmu,haka ina saida su Aya,ridi,kantu,alewar Madara,albishir etc su Ma'eeshah nake sarowa suna Tafiya min dasu makaranta su siyar min,ina kosai na siyarwa,da rana na siyar da su Zobo kunun zaki da dare kuma nayi Awara,ina kitso da zanen lalle sosai kudi idan sunzo zanyi na karbi kudina,sannan ina cikin masu polio rigakafi,duk wani neman kudi na Sana'a kanana na gida ina yi,kusan komai ma siyarwa nakeyi,kullum bani da lokaci bana zama sam sai neman kudi dashi muke ci muke sha,muke Sutura tare da makaranta,

biyawa Ammah kudin magani,yanzu kasuwanci a duniya shine buri na wanda har ya kai ga dasa min matsiyaci son kudi tare da tattali,iya lissafi da planning,sabo da yawan Hulda da mutane yasa na kara gogewa na waye sosai,akan kudi ba mutunci ko bashi ya shiga tsakanina da mutum akan dan Kasuwanci na to fa zan iya rufe ido dole a bani ma,kamar zanyi sata haka nake matukar neman kudi.

    Yau Monday Su Meenat suna schl na gama komai na fita naje wajen saro kayan Yara na sha,ina siyowa kala kala har su tuwon madara na wuce schl na kaiwa su Ma'eeshah domin su siyar,ina zuwa na hango Malam ya sa Ma'eeshah kamun kunne ya hanata ko shiga aji wai sun makara.




    Ina matukar Jaje gareku fans da raguwar shekaru da muka samu domin ba karuwa shekarunmu suka yi ba raguwar suka yi,ana ta happy new year a daina addua ya dace muyi Allah yasa mun shigeta a Sa'a tazo lfy ta wuce lfy,Allah yasa ta Zama shekara me amfani a Rayuwar mu,ta zame mana farin ciki da samun ci gaba a cikinta,Allah ka kara mana lfy da Nisan kwana me amfani,Allah ka kara mana imani,Allah yasa muyi karshe me kyau idan tamu tazo,Allah ya azurtamu da mutuwar shahada,Allah ya rufa mana asiri duniya da lahira Ameen.


AsmaBaffa

2-5

Wannan page naki ne HUMAIRA Allah ya bar kauna.

Wajen malamin naje da kyar na rokeshi ya kyaleta yace tayi Sauri ta karbi sakon ta shiga aji, nima ina mikata mata na kama hanya sai gida,washe gari kuwa da sassafe na shirya na barwa su Ma'eeshah suyar kosai da Komai nayi shirin Tafiya rigakafin Polio dama indai ina rigakafin nan to dole  Meenat ce zata zauna tayi dukkan abin da nake siyarwa har na gama Polio sannan taci gaba da zuwa,Sabo da Ammah bata yarda da talla ba shi yasa Sam bama fita talla a gida muke sana'armu,     Ma'eesha kadai ke zuwa yanzu kafin na gama Vaccine.

     Inda muke haduwa da ma'aikatan unguwar da mukeyi naje na samesu cikin Napep na sauka cike da fara'a da murna muka gaisa da juna,sannan na dauki akwatin da kwalaben Allurar suke ciki ga kuma supervisor dinmu da sauransu,sabo da box carrier ce ni ba a biyanmu da yawa dubu hudu da dari biyar muke dauka idan an gama,bani da ilmin da za bani Babban matsayi,haka mune da wahala mune muke daukan kudi kadan,a kafa muke Tafiya muna shiga gidaje ana house marking,sai 2pm muka tashi,washe gari ma bangaren unguwan da mukaje daban,a kwana na Uku kuwa da muka fara GRA din nan da na taba ganin Saurayi Aayan ya zaneni yau gidajensu zamu shiga aikin Vaccine duk da cewar ban taba shiga gidan ba,amma bana fatan shigarsa,ina ji ina gani muka zo jikin gate dinsu,

takadda aka rubuta sannan akayi knocking,Sojoji sunfi  biyar ne suka fito kamar zasu masgemu,sai da aka basu takardar cewar yan Polio ne suka zo ga me unguwa a tsaye kuma dole sai an digawa yaro dan kasa da 5years,takardar suka karba sannan suka koma ciki zasu nunawa me gidansu,tunda suka shiga muna tsaye a wajen gate har sai da suka kwashe fin hour guda sannan suka fito sukace ance mu shiga,ma'aikatan sai murna suke zasu gano haduwar gidan,ni kam cikina ya duri ruwa bana fatan shiga Amma ba yanda zanyi haka na fara binsu kamar kwai ya fashe min a ciki sanye nake da red hijab dina me hannu har kasa duk da cewa nayi kyau Amma sam na raina kaina,

   Muna shiga muka firgita domin ma'aikata da Securities ne ko ina,gidan ko ina kamshi ke ratsowa yana sheki,ga wasu motoci sunfi ashirin a gidan lafiyayyu,har round ne a gida kamar wani Babban titi tsakiyar youturn din ruwa ke tsiri sama yana shararowa a kasa kuma yana komawa kasan yana fesowa,a film ake ganin irin wannan gida jen,can gefe ga wasu sweeming pool har kala biyu,ko ina flowers ne a gidan,duniya guda ce a gidan domin wani part din ma ya dace ka hau mota sannan ka Isa in kuwa ba haka ba zaka gaji,wani soja ke mana jagora muna binsa a baya har muka zo wani garden ba abinda babu a garden din nan domin har da filin ball da Sauran wasanni iri iri,kida ne na wakokin Naija ke tashi har tsakiyar kai a manyan speakers,yan mata su Uku kyawawa yan gayu ne sanye cikin English wears Wando short da yar vest suna ta faman taka rawa ,hannunsu rike da kantama kantaman wayoyi,gefe wasu Yara ne sunkai su hudu mace daya da Maza su Uku sun sha kyau cikin kana nan kaya yan yayi suna ta faman buga ball, abin mamaki ko kallon inda muke basuyi ba kamar ma basu san mutane sun wuce ba, haka muka ci gaba da Tafiya muna yin gaba kadan sai ga wasu Maza zaratan samari suma hadaddun gaske baza su wuce 29 yrs ba su uku suna zaune a wasu kujeru masu malafa a sama game kawai suke bugawa suna dariya,ko wanne yasha kyau cikin kana nan kaya kamar a England,kaina nidai yana kasa Amma suma samarin inda muke ma basu kalla ba balle musa rai za a kula mu,tafiya dai muke muna bin Soja can wani wawakeken fili ne fetal yasha tsari da haduwa carpet dan gaske ne a kasan wajen da wasu manyan pillows ko ina yasha flowers ga wasu grass carpet wata mashahuriyar Dattijuwa tsohuwa tukuf muka hango kwance tayi kwanciyar Isa kamar sarauniya fatarta lumis fara kar duk da cewa ta tsufa Amma akwai hutu kayan marmari sun ratsata.

    Mu matan da muka shigo dama mu Uku ne,da hannu tayiwa Soja Umarni nan muka ga yace gasu nan yayi gaba abinsa,har kasa na durkusa na gaisheta cike da girmamawa,su kuwa sauran matan cewa sukayi ai ma'aikata ne wlh baza su durkusa ba duk wulakanci da akayi musu ba wanda ya musu ko sannu bare kallon arziki,gata ita wannan ta tsufa ma Amma bata saduda da duniya ba har wani jin dadi take.

   Kallonmu tayi tsohuwar ko amsa gaisuwata bata yi ba tana yatsina fuska tana kebe baki tare nuna Isa ta fara magana kuje dan Allah kun tsaya min a kai wari yana hawa min kai,da mamaki muke kallon ikon Allah,can ta jawo waya ta danna kira tana jan tsaki,sai ga wata da Alama yar aiki ce harda Uniform dinta dauke ta fito da ruwan roba tare da wani liquid soap me kamshi tace kuzo muje ku wanke hannunku sai a diga musu polio,Tsohuwar nan cike da izza tace wlh badan Hukuma da suke hadawa da ita ba baza a digawa jikokina ba sam,kazanta abinda ana kaisu asibiti ayi musu me kyau ko kasar wajene ma sai suje a diga musu Amma a dinga turo mana kazamai gidaje jasu can kuje,ina jin haka na daga kaina ina kallon sararin samaniya tare da kallon tsayi da girman building din nasu kamar baza a mutu ba katanga ma tayi tsiri sararin samaniya kai kace Mala'ikan daukan rai bazai iya tsallakawa ba,a raina nace to yaje har fadar shugaban kasa ma ya dauke Yar Adua,yau Ina sani Abacha? 
 
      Ina wannan tunani sai ga wasu dattijan Maza farare suma su Uku sun fito harda Abbi wanda na taba gani zama sukayi kusa da tsohuwar suna magana,lokacin mu kuma an jamu part din yan aiki nan aka dinga dirje mana hannu sannan suka fito damu, wajen yaran dake Garden tare da yan matan nan masu rawa da Wando 3qtr muka koma,nan fa da kyar aka jawo mana yaran ana cewa Hajja ce tace ayi musu suka bude bakin su tas dasu cikin taka tsantsan na diga musu yanda akeyi sannan nace to Alhmdllh mun gama mun gode,me rubutu ta cike talley sheet din,muna jiranta tana rubutu yan matan nan dake rawa dauke da cup a hannu suna shan lemo suna rawa suna bige mu Amma ko kallon mu basayi bare mu Sa ran ko Sorry zasu ce,gefe dasu muka matsa,wata ce ta fito cikin shiga ta alfarma zata kai 40years da Alama da yaranta a ciki domin munga suna daga mata hannu bye Mum,tayi murmushi Tare da shigewa mota Driver ya jata ta daura kafa daya kan daya tana karanta Jarida,Numfashi ne ya kusa daukewa sakamakon wasu motoci da suka keto cikin gidan a kalla sun kai guda biyar suka Parker zunzurutun Securities ne suka fito tare da zagaye motar kamar wani Shugaban kasa ne zai fito,bude motar sukayi muna tsaye muna shan kallo Wani arnen takalmi ya zuro waje nan take kamshinsa ya cika gidan me dadi,ya dan jima a haka kafin daga bisani ya fito cike da takama kamar wani Sarki,cikin kana nan kaya yake yau ma farin Wando  pencil sosai rigarsa Silver color da Golden rubutu,takalminsa Silver yasha masifar kyau,duk wanda ya ganshi zai rantse ba mutum bane Sabo tsabar baiwar sura da kyau,ga iya daukan wanka yanda yake matukar kyau,yan matan nan ne muka ji sunce Hi Ya Aayan,ko kallonsu baiyi ba sai ma wani kallon Banza da muka ga ya watso musu kamar yaga kashi,sabo da nima gwanar mugunta ce a raina nace Allah ya kara shegu ga ubanku a girman kai gwara haka,

    Matar da muke aiki da ita wato Salima itace ta kalli yan matan tayi dariya wai irin ta tura musu haushi,ai kuwa ba zato muka ji karar Mari a fuskata domin suna rawa tunaninsu nice na musu dariya shine daya a ciki kawai ta daukeni da shegen mari wanda ya jawo hankalin wannan Saurayin da Sauran Ma'aikata kaina,Kuka na fashe dashi a wajen nan take na fadi a wajen na dinga shure shure,wanda muke Polio ne suke bani baki kan nayi shuru mu tafi,cikin kuka nace Wlh sai na rama mikewa nayi a hasale na cakumo daya a Cikin yan matan wanda ban san wace ta mareni ciki ba nidai na kama daya tare da makalkaleta na cisgo gashinta na murde na ja da karfi,sannan na dalla mata mari har biyu na sake ta na zura da gudu domin sunyo kaina da kwaben lemon me tsada da suke sha zasu fasa min a kai,daya ciki ta jawo Hijab dina ta baya,Securities sun taho Saurayin nan ya dakatar dasu cewar a kyalesu,suna kallo sun rike min Hijab na sunkuya tare da zare Hijab dina na bar musu a hannunsu na Arce jikin gate ina rokon a bude min,Saurayin nan yace kar wanda ya bude min,Har yan matan nan suka zo kaina na kara runtumawa da uban gudu amma saida suka kamani suka rufarmin suka dakeni sosai naji jiki sai da suka gaji dan kansu sannan suka tafi ina yashe a kasa,sai Hawaye nakeyi abokan aikina suka dagani da kyar sannan naga wannan Saurayin yace a bude mana mu bace a ganinsa ya tsani mata ko da yan uwansa ne baya kaunar ganinsu,sai da na tabbatar an bude mana nasa kafa ta daya ciki daya waje sannan nace kai yan mata?duk kuwa suka juyo suna kallona nace Allah ya Isa kuma sai na rama watarana idan kanwata ta zama Doctor ko Lauya,kallon banza suka min tare da tabe baki,nace zaku gani wlh kyaleki nayi dan ba a kan KASUWANCI NA kuka tabo ni ba,rigimar ba akan kudi bace Amma da akan kudi ne ai da sai daí a mutu a gidan nan shegu,tsinannu tambadaddu,arna,jahilai,dabbobi kuma dukkan yan gidan nan na zaga na nuna Saurayin nan dake tsaye nace harda kai da wannan tsohuwar dake zaune a carpet a sanar mata dazagina da iyayenku baki daya,sannan kuma ina tunatar muku Mala'ikan mutuwa na nan zuwa watarana,sojoji ne suka yo kaina na Arce da uban gudu tare da cewa Allah ya isa dana gaishe da tsohuwar nan kekakashashiya,na dinga zura uban gudu Allah yasa time din tashinmu yayi kawai na fada Napep ina haki sai gida tazarce kawai tun daga Cikin gidan nake gudu har nazo bakin titi na hau Napep,su kansu abokan aikin nawa dariya suke min da kyar wani cikin wanda ke jiranmu a waje ya karbi box din hannuna Sabo da uban gudun da nake kamar na fanfalaki.

     Bayan na koma gida sallah na gabatar tare da fara harkar kasuwancina har Awara nayi ta dare bayan na siyar na gyara komai tare da irga kudin na cire ribar na zuba cikin asusun da nake tarawa Ammah kudin asibiti na magani tare da ware na gida da yan abubuwa,washe gari haka muka je wata unguwar mukayi polio abokan aikina su Salima sun sani gaba suna min dariyar abinda ya faru damu a gidan masu kudin jiya,sai dariya muke muna Bada labarin,Salima tace ammafa sun hadu da yawa a gidan kowa me kyau ga iya kwalliya musamman dan Iskan da yasa aka dakeni domin ni tunanina shine yasa a Zane ni tunda shi ya hana a bude min gate,Salima tace lalle Mufeeda ashe haka kike da rashin kunya idan an tabo ki,kina da Silent falava wlh,u like too much falava,murmushi nayi kawai domin bana jin wani turanci ni kam,karatun Hausa da Arabic kawai na iya Amma Ilmin turanci sai dai kalmomi dai dai domin bani dashi,h akan ma don ina dagewa ne su Meenat suna koya min amma da ba karamar dakikiya za ayi ba ni kam.

      Yau cikin nishadi muka gama Polio na dawo gida da Sauri naci abinci na shirya sai kasuwa siyayya ina tsoron bi ta cikin GRA Kawai sai na hau Napep naje na dawo lfy, bayan mun gama suyar Awara mun siyar wanka muka kara yi tare da Sallar Isha,Su Meenat Assignment sukayi na schl tare da karatu nima na zauna suna koya min karatun turanci da rubutu haka Arabic ma duk da ina da Ilmi domin Uzu na ashirin cif haka wasu litattafan duk nayi wanda Kannena su Ma'eeshah sunyi Sauka tuni littafin da suka sani kam ko kafarsu ban kama ba danma ni gwanar jin wa'azi ce nasan duk wasu hukunce Hukunce na addini da dama Amma su suke koya min karatun,da badan haka ba da anyi kungurmar Jahila ni,

      Part of speach suke koya min common adjective sun sha fama dani kafin na iya fada Sabo da ba laifi kwakwalwata da saukin ja tunda ni dai iyakacin Jss 2 makaranta ta gagareni Allah ma yasa Makarantar Arabic da boko mukeyi a hade shi yasa muke dana addini,su Meenat kuwa ai akwai Ilmi,shi yasa da munyi fada zasu ce to Sis me kika sani ma in ba neman kudi ba musamman Meenat uwar iyayi da son kwalliya domin duk wata kwalliya ta yan Zamani ta iya ta komai nata na harkar son gayu,Maeeshah ma haka suyi ta faman iyayi ni kuwa sai dai na siya musu kayan yi suyi ta zuba kwalliya ina kallo tunda har cosmetics na talakawa ina siya musu iri iri,kayan wanke gashi na talaka ni dai barni da jarabar tsafta amma ba ruwana da wata kwalliya gani nake bata lokaci ce kawai kudi nake nema dan mi tsira da mutuncinsu,
 ni kullum sai daí na labta Hijab na fita neman kudi ba sauki wanda yanzu Unguwarmu sun samin suna Yar Kasuwa,sabo da bani da lokaci sai na neman kudi akan kudi ba daga kafa.

   Duk inda naji wata Sana'a ko harkar samun kudi to fa yanzu zan cusa kaina ciki dole sai na samu domin mu samu na ci da sha tare da Sutura,ina da karancin wannan shekarun Amma na shaku da kudi,yanzu abinda ya dameni bai wuce kai Ammah Hospital ba domin dubu Sittin da biyar zamu je da ita za ayi mata wani aiki a Ciwon dake kugunta zuwa kafafunta shi yasa na gigice yaki Halak yaki Haram haka nake tara kudin,
    Akan wannan yanzu kam na koyi ha'inci a Sana'a ta domin Awara da ina yinta me kyau da dadi Amma yanzu dan na samu riba da yawa na daina alkintata idan na tashi tacewa Bazan matse ruwan da yawa ba,kadan nake dan matsewa kana ci zaka ji ciki lumtsum da ruwa da mai,haka yajin na daina me dadi sai na gabza uban gishiri a ciki dan yayi yawa,haka ake siye Sabo da tsaftarmu Amma sun daina karba da yajinmu,haka kosai na ma da wata taba da ha'inci ya taso min sai na siyo garin kwaki tare da jar kala bayan na dauko markaden saina zuba garrin kwaki a Cikin markaden waken kosan nawa tare da jar color yayi wani jajir sannan kosan ya kumbura yayi sutu sutu dan na samu riba na samu kudi sai kiga ana ta siye Malam kosai yasha kayan miyar color gashi har wani Danko yake Sabo da yaji garrin kwaki ciki ba a sani ba ayi ta siye ina samun riba tunanina dai dai duk kuwa da cewar nasan ba kyau sai daí nayi Istngifari domin ko Ammah da kannena basu san tabar da nake aikatawa ba gara awarar gida idan zan soya musu daban nake tace ta tas tsam ba ruwa sai su zata ma wacce ake siya haka take.

    Hattana Alewar madarata dasu kwakwimeti tare da kafi tsire in dai zanyi sai na san tabar dana yi a ciki Sabo da kawai na samu riba me yawa,gullisuwa idan zanyita sai na tankade garrin masarara me Laushi na kara a cikin Madarar Sabo da tayi yawa,haka ma Zobo na siyarwa sai na samu jar color na tafasa zobon kadan na narka uwar Color a ciki nayi hadinsa a ganshi kamar gaske ayi ta zuka ba a san rabi color ce kawai da ruwa ba,kuma bana sa sugar dan zaki wato sugarin nake dan yafa kadan sai kaji zaki cai.

     Ina zaune kusa da Ammah ina tufke mata gashinta muna sauraren Radio kawai sai muka ji cewar Gomnati zata raba tallafi ga marasa karfi Naira dubu sha biyar biyar tare buhun shinkafa da taliya sugar da man gyada tare da waken Suya a ja jari,nan take na mike zumbur naji kudi,Ammah ta kalleni tace sarkin neman kudi dan Allah ki hutawa kanki zafin nema baya kawo samu haka duk kin damu kanki Allah yana rufa mana asiri dan Allah ki rage takurawa kanki ayi amfani da abinda ya samu,baki na turo Ammah kina gani kudin maganinki har yau basu hadu ba fa,to ta wacce hanya zaki bi ki samo mana tallafin? Ammah wajen counsilor din Unguwarmu Adamu zanje na nemi Alfarma ya nemo mana hanya,ai yana da kirki Amma fa kija mutuncinki duk da nasan irin tarbiyyar da nayi muku ki kiyaye Mufeedata sannan kinga girma ya fara kamaki idan kika bari Namiji ya rike miki ko yatsa shike nan kinyi ciki an gama,da Sauri na zaro ido waje a tsorace nace Ciki Ammah?ae ai indai Namiji ya rike maka ko farcene to shike nan ciki ya shiga,da tsoro na firfito da ido waje,nace Ammah su Meenat nake tsoro bari su dawo na fada musu gaskiya kar suje su yarda da Maza su rike musu hannu.

    Su Meenat suna dawowa na taresu da Sauri tare da jansu dan Bedroom dinmu nace dan ubanku karku bari Namiji ya rike ko yatsanku,Meenat tace Sabo da me?ba kyau kuma Ammah tace ciki ake dauka,Dariya naga Meenat ta kyalkyale tare da cewa Allah ya bamu kudi Sis ki koma schl kema wlh ba haka bane ke baki da labarin abinda ake a aure ana samun ciki,ai Ammah wayo ta miki kar mu kula Maza mu lalace shi yasa ta fada haka Sabo da taga mun fara girma,shuru nayi ina Nazari Amma naki yarda da Meenat Sabo da nasan Ammah baza ta fada mana karya ba,kyalesu nayi kawai na fita abina naci gaba zuba kwakwimeti na à leda,bayan na gama na fara daura su citta dasu kanwa,kaninfari etc,kusan duk makwaftanmu a wajena suke siyen kayan miya,idan suka siya kawai sai su zauna a gidanmu suce bari su daka kayan miyar ko jajjage da sun shiga gida kawai sai daí su fara girki,sabo da son kudi na nace to daga yau na kafa doka cewar ko wacce idan zata yi daka a turmin gidanmu to sai ta bayar da Naira goma kudin turmi,ganin haka yasa Bazan basu tabarya ba sai an miko goma shike nan suka daina daka a gidanmu,Muna da wata Kura da yake gidan mu akwai rijiya idan guganmu ya fada da ita muke amfani mi Ciro gugan,mutane suna zuwa aro sosai nan ma nace kudin aron Kura Naira talatin wasu haka dole suke bayarwa suna dauko Guga,Ammah ta hanani Amma naki ji,su Meenat ma dole suyi abinda nace ko bana nan idan aka zo to fa sai an Bada kudin nan,komai nawa idan zaka taba na kudi ne.

     Haka na kama kafa naje har gidan Adam counsilor neman Alfarma a sani cikin masu tallafi,yace Mufeedata ki. Makara wlh an gama daukan sunaye amma na miki alkawari akwai na wani watan kizo Office ki sameni a secretariat zan sa sunanki a wasu da za fara bayarwa na manoma,ban kawo da wata manufa ba kawai na dinga Murna ina godiya cewar zanje in Sha Allah. 

    Bayan kwana goma Zaune muke gaba daya tunda anyiwa Su Meenat hutun schl muna ta Hadin Zobo nan nace suje su ebo robobi a wanke suna Tafiya na watsa Maroon color tare da makawa Zobo ruwa na hadashi da su Flavour yasha uban Barkono a ciki,sabo da aji yaji sosai sai na zuba citta da kaninfari kadan na ebi Barkono na watsa a ciki na tafasa dashi Sabo da aji yajin ya fito sai ka rantse yajin cittane da kaninfari me uban yawa,gaskiya na iya taba sosai ni kaina ina jinjinawa kaina yanda nake tabka tsiya a sana'oi na ba a magana watarana nakanji haushin kaina nima ba da son raina nakeyi ba Amma Sabo da neman rufin asiri,su Ma'eesha suna kawo robobi Meenat tace sis wannan uban zobon fa dazu fa dan kadan ne bai kai rabin botiki ba amma yanzu ya cika botiki,Maeeshah ma tace nima haka na gani kamar na Aljanu,Harara na zabga musu sannan sukayi shuru.

abin takaicin da kyar na hada dubu Sittin da Bakwai kudin Ammah na asibiti,haka nace su shirya mu tafi,har kofar gida na kira Napep muka hadu tare da daukan Ammah muka sata cikin Napep muka kulle dan gidanmu da yar kofar da ta kusa ballewa ma haka na zarge ta muka shiga Napep Sai Asibitin Murtala na cikin Kano,Munje  Dr Naseer ya duba lafiyarta ya dinga fada me yasa ba a kawota da wuri ba tuntuni yace a kawota ayi aikin to gashi ciwon nata ya kara karfi yanzu dole wasu magunguna zasu rubuta mana mu siya na dubu Hamsim da biyar sannan idan ta shanye bayan sati Uku mu dawo da ita za ayi mata aiki.

    Bakin ciki da tsoro tare da firgici suka kamamu gaba daya,nayi Zuru Zuru kamar wacce ta shekara taana zawo haka na koma nace Doctor yanzu nawa ne kudin aikin? Yace ai kudinku da yawa,likitan da zaiyi mata aikin nan baya zama a kasar nan sam Sabo da aikinta zaizo yayi mata ya koma,don haka idan yayi muku sauki ku biya dubu dari takwas da  Hamsim domin ciwon ya girma,da ace tun farko kun kawota da tuni baifi ku kashe dubu dari ba Amma yanzu danma da wannan Doctor dinne Amma wannan aikin kasar waje muke tura mutane masu irin cutar ayi musu aikin anfi dacewa,a nan kuwa sai dai mu dage da addua,kuje ku dawo lallai nan da 3wks tare da kudade in ba haka ba kuna kallo wlh zata kasa ko motsa yatsa dake gabarta nan gaba sankamewa zatayi ku daure ku dawo ayi mata aikin kunji.

   Likita na bayani Hawaye na sintiri a fuskata tunanina ina zan nemo kudin nan ko kaina zan siyar wlh bazan yi wannan kudin ba,Innalillahi nake maimatawa Doctor kuma na kwantar min da hankali yana cewa cuta jarabta ce daga Allah,idan Allah ya jarabceka sai hakuri aci gaba da addua Amma tana cikin hadari,Meenat dake kusa dani itama Hawaye takeyi,da kyar na Lallashi kaina nice babba Amma kuma nice me raguwar zuciya bana iya rike Hawaye na saurin kuka gareni ammafa a bangaren abin tausayi,ko ya naga abin tausayi yanzu zan yi kuka,kanmu da Ammah nake tausayawa kawai,Meenat karki fadawa Ammah me Doctor yace kawai kiyi shuru da bakinki Sabo da bana so hankalinta ya tashi,muce kawai aiki za ayi mata nan da 3wks sai kudin zamu fada mata,amma karki fada mata Doctor yace zata iya rasa ranta ba lallai ta tashi ba kinji,ok Sis Bazan fada ba cewar Meenat dake shesheka,hawaye na share mata nace muje kawai muk ayiwa Dr sallama muka tafi,Ma'eeshah da Ammah suna jiranmu a can waje, magunguna muka siya sauran kudin na siyo mana wasu kayan abinci da Cefane,Su Meenat kuwa tuni na hadasu tare da Ammah nace suje gida zanzo daga baya,Ina cikin Napep kawai tunani nake ta ina zan samu kudin nan,lallai Zafin nema baya kawo Samu,gashi dai na gama Ha'incina a sana'ata na cuci mutane da dama ta hanyar siyar musu da gurbataccen abun ci kuma karshe kudin anfaninsu kadan ne a wajenmu abinda nayi don shi ba a dace ba,amma duk haka ban hakura ba kuma ban damu ba matukar zan samu kudin da Zan nemawa Ammah lfy.

     Tunani nake bana ganin komai bana ji har Napep ya saukeni a gida na shiga da kaya Niki niki,Meenat ta karba ta shigar dasu ciki,tsabar bakin ciki da muke ciki yau bamu iya daura kaskon Awara a kofar gidanmu ba,duk muna zaune kowa da tunanin da yake banda Ma'eeshah da yake ita ba wani girma da hankali tayi ba sosai bacci ma takeyi,abincin da muka dafa ba wanda ya iya kai ko loma daya bakinsa,musamman ni gaba daya na rude na rikice,idan kuka ya taho min sai na shiga toilet naci uban kuka na wanke fuskata na fito haka na kwana inayi kafin Safiya tayi idona ya kumbura yayi jajir, ga addua muna tayi, mura ta kamani muryata har ta dashe Sabo da Hawaye na kawo Mura yawan kuka,da sassafe kamar me aikin Gomnati 8am nayi shiri da kumburarren idona tare da jansa na maka hijab kowa ya ganni yasan ba lfy,tunani nake ina zanje neman kudi Office din yan siyasa ko gidajen masu kudi?ko kuma kasuwa zanje wajen masu kantina,domin   banyi tunanin kaiwa gidan Radio ba ko wani waje,kaf makwaftanmu haushina sukeji Sabo da kan Sana'a ta ba mutunci idan maganar kudi ce ba kawaici don haka ba da wanda muke shiri sai daí daiku duk sunfi jin haushina,don haka babu me bamu shawara ko gidan Radio ko wani waje to idan ba business ba babu abinda ke hada mu dasu Sabo da ba a kula mu ance dan munga muna da kyau sai mu dinga yanga mu ba yayan uban kowa ba,sannan tunaninsu ma ni yar Iska ce Sabo da yawan fita da nake kullum ina gantalin neman Kudi tunaninsu ai iskanci nakeyi kullum ina titi,haka suke zagina ba abinda ba ce min.

    A fusace na fito daga gida ka Rantse  mutanen garin ne suka min abin haushi domin kowa haushinsa nakeji kamar zan make mutane haka nake tafiya fuuuuuuu fuska ba annuri,duk motar dana gani sai na harareta na harari na ciki dake tuki irin ga mutane da kudi ba taimako,common arna ko church kaje a tallafa ma amma musulmai ko a masallaci basa iya bada Sadaka me tsoka sai biyar,goma,ashirin katon me kudi kaga ya mika Hamsim,mafi akasarin Hausawa haka suke bare har wani ya dauki nauyin karatun wasu ko ci da Sha bare na magani sai dai dai ake samun masu haka,amma arna sai kaga mutum daya ya kwashi yan unguwa da yawa ya fitar dasu kasar waje karatu etc.
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 1 32,229 03-26-2019, 10:46 AM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 4 120,151 02-22-2019, 08:04 AM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 7 60,141 01-20-2019, 01:58 PM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA 0 2,511 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA 0 3,072 Less than 1 minute ago
Last Post:



Users browsing this thread: 1 Guest(s)