The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie*
#1
11

Tunda Aisha tazama cikakkiyar budurwa a lokacin tanada ilimin Addini Daidai gwargwado, Boko kuma tana SS1 Makarantar gwamnati, nanfa samari suka yo mata chara, yawancin marasa jin unguwan ne duk Wanda yasan unguwan shanu yasan ba laifi akwai marasa ji saidai Allah ya shirya kawai, hakan yasa bata kula kowa ganin duk babu na kwarai koma akwai babu hurumin shi a gefen zuciyarta, nanfa suka Kara samata ido wasu harda zagi idan tafito, tana diyar mai shayi da rake amma tana girman kai, wasu suce rufa mata Asiri zasuyi danta samu ana Santa diyar Dan kwaya, hakan yasa tasa katon audiga tareda toshe kunnan ta, Ramata kuwa Kullum cikin hannunka mai sanda take mata yayinda yayanta garbati abun yafi damun shi fiyeda kowa amma ya zaiyi? Wasu yan'iskan ma cewa sukeyi darajar shi takeci mai akai da diyar mashayi dan cha-cha? 
Ya'u kuwa ko'a kwalar rigarsa hidimarsa yakeyi.
Cikin masu takura mata akwai wani Saurayin dake zaune a cikin gidan su Wanda yake dan'sara suka ne yayi suna a unguwar wurin rashin ji, duk inda ka ambaci *Virus* tohfa harta yaro yasan da zaman shi a unguwar, maguwar Sha'awar Aisha yakeyi tunda ya kyalla ido yaga surarta, hakan yasa yaita mata tayin soyyar Sa babu yanda baiyi ba  ko darajar magana baya samu dukda yana aiko mata da kananan kyauta kozata kula shi saidai ta kori Dan sakon tareda sakon, Wata rana da yamma tadawo daga islamiyya Virus na zaune a kofar gida ganinta yasa yatare karamin kofar shiga cikin gidan, tsayawa tayi dataga bayida niyyar matsa mata kallan shi tayi, 'zan wuce, 'kallon ta yakeyi sama da kasa tareda lashe baki kamar tsohon maye, 'ki wuce mana, tareda Dan bude mata hanya kadan, rabawa tayi ta gefen shi cikin natsuwa ta manne da bango gudun kada jikinsu yataba juna Virus kuwa dayake bahaka yaso ba yaso yadan ji dumin ta koda Dan gogarshi ne tayi hakan yasa kafun takarasa wucewa taji PA's ya bugan mata gefen duwawu har yana Danna hannun shi, wooooooooo   kafun yarufe baki aiko Yaji saukan Mari a gefen fuskarshi, karamai wani tayi tana huci Ranta yayi mugun baci ta kudiri aniyar duk abunda zai faru saidai yafaru tagaji da rainin wayaun su, hannun ta aka kama daga baya, 'zoki wuce, inji Ramata wacce tafito duba sanwar data Dora a zaure, babu musu tabi bayanta sukabar Virus na  hucin ganin babu namijin daya isa yayi mishi haka amma yau saboda ya latsa duwawun mace yasamu mari biyu abun takaici kuma a gaban yaransa dake zaune a gefe, aikuwa masu dariya damai kirari nayi masu bashi hakuri nayi nan yakara kulewa tareda Alkawarin daukar fansa.

Kuka takeyi da takaicin rayuwar data tsinci kanta a ciki bakowa yakara jamusu abun gori ba I'lla baban su daya kasance mutumin kwarai babu Wanda zai watsa musu shara, nan tayi mai isarta yayinda Ramata batabi ta kanta ba itama dazata samu mai lallashin nata so takeyi, Aisha kukan fili takeyi itako tadade tanayin na zuci,  batada yancin shiga cikin mata sa'an ninta iyaye koda kuwa sha'ani ne na cikin unguwan inko taje an dinga ya'da mata habaici kenan saikace itace keyin cha-cha ko shaye shayen??‍♀ gidansu AK ne kawai basu chanza mata ba.

Bayan an kwana biyu, zaune suke a'dan tsukukun dakin su cikeda jimamin rashin dawowar ya'u gida kusan kwana biyu kenan babu shi babu labari, shiba wayaba bare a kira duk inda akesa ran ganinshi bayanan hakan yasa suka dangana tareda zubama sarautan Allah ido, garbati ne ke zaune gefen mamar tasu da Aisha  yana cin tuwon masara miyar kuka Auta kuwa tana gefe daya tazuba uban tagumi sai tausar su yakeyi akan baban nasu zai bayyana gobe da sassafe zai Kara dubashi ko za'a Dace, dakyar ya lallaba sukaci tuwon suma tareda musu sallama zuwa makwancin shi a lokacin yabar dakin su ganin rashin dacewar hakan shiyasa yakoma dakin abokinshi dake unguwan yana kwana, sallama yayi musu yayinda yawuce a lokacin sunada matsalar wuta gashi lokacin zafi ne babu halin kulle kofa dukda sunsan akwai hatsari barin kofar a bude tohya zasuyi? Gashi kofar gidan nasu dan kwano ne akeja ake kullewa.

Wurin sha'dayan Dare dukansu sukayi bcci ga azabar sauro da zafi hakan yasa Ramata ke daure da zani a kirji Auta ma haka, Aisha kuwa vest ce sai underwear a cewarsu zafi bazai kashe suba.

Kafarta yake shafawa a hankali, nan yafara kokarin tube mata Riga,cikin bcci taji ana shirin cire mata kaya gashi ana shafa mata jikin ta, aikuwa kwanciya yayi sosai a jikinta jin nauyin shi yasata sakin ihun da Ramata ta farka, nanta dinga zuba ihu daduk karfin ta aikuwa kafun kace kwabo muryarta ta karade ko'ina, magana yafara cikin maye, meeeeyeee......ha.ka, Raaaa..  a'a 
Mikewa tayi ganin ana shirin keta ma diyarta haddi akan idonta Kwanan samiran dake gefenta ta kwada masa akai, sannan ta tuna da tuchlight dinda ke gefen katifar su, ihu Ramata keyi akan akawo musu dauki kwarto ya shigo aikuwa tana kunna tuchlight din idonta ya sauka akan Ya'u dake shirin cirema Aisha underware harya fara yaga mata vest din jikinta, bin bango tayi tana salati tareda dafe kirji tuchlight din hannun ta yafadi kasa hakan yayi daidai da karasowar virus da ihunsu ya tashi kowa na gida, ihu yasaka jama'a uba kecin diyarsa shiyasa aka hanamu dandane ashe cikin zafin nama ta tattaro duka karfin jikin ta tahau buga mai duk wani Abu dake kusa da ita, virus kuwa ihu kawai yakeyi yana shela a unguwa ya gansu turmi da tabarya, diyata? Duk karuwan gari sai diyata? Wlh kashe ka zanyi Ya'u Allah ya la'ance ka Allah ya hanaka farinciki Aisha sumewa tayi ganin ubanta neya yaga mata suturar jikinta yayinda Auta bilki tayi mutuwar tsaye numfashi na sama da kasa.........

12

Kafun kace kwabo mutane sun yanyame zauran gidan, nan aka damki ya'u dukanshi sukeyi Kota ina matasan unguwan, suna cewa duk iskancin su bazasu taba naiman jinin suba karshan iskanci yakare uba ya nema yarsa ya'u tuni yadan dawo hankalin Sa saboda bugun daya kesha jini ta hanci ta baki babu kyan gani kanshi a fashe duk jikin shi ciwo, 'wlh na dauka Ramata ce, Allah na tuba shegiya, shegiyyaaa giya  giya Allah ya tsine miki  yar iska ta kassarani Allah ka dauki raina Dan girman Allah ku kashe ni banda Amfani nadauka Mamarta ce taya zan naima abunda na Haifa? Bantaba zina ba ya za'ai infara akan diyar cikina? Allah ka shiga tsakanina da giya kaimana hisabi Kin gama dani kinji dadi giyaaaaaaaa, Babu Wanda ya saurare shi, Ramata kuwa kirjinta ta dafe nanta sulale kasa sharaf, matan makota  ne suka suturta ma Aisha jiki dukda ba'a tsirara take ba nan aka Kara rikicewa a tunanin su mutuwa Aishar tayi danko motsi batayi, ruwa aka shiga watsa musu yayinda Ramata taja Ajiyar zuciya mai karfi Aisha kuwa ko Alamar motsi batayi ba, Auta bilki kuwa tana manne da bango kamar mutum mutumi itama ruwan sanyin aka shiga yayyafa mata domin batada banbanci da wacce ta suma, ana haka ne Garbati ya karaso a rikice dagashi sai gajeran wando saboda rudewa, dakyar aka iya bambare ya'u daga hannun matasa, nan Abokanan garbati suka shiga lallaba su, kememe sukace sai sun kashe shi mutumin da akace an ganshi turmi da tabarya shida diyar cikin Sa ina maganar sassauci? Karku raina mana hankali mana malam, cikin dabara Abokanan garbati sukaja hankalin su da sunan bada hakuri yayinda Garbati yaja ya'u batareda sun Ankara ba saboda garin yayi duf kowa da tuchlight yake rike, ya'u kuwa babu abunda yakeyi sai tsine ma giya da cha-cha tareda yima kanshi Allah wadaran sai a lokacin yasan illar shaye shaye wato duk abunda musulunci zai Hana toh bakaramin Rahama bane a garemu muddun zaka  kusance shi kuwa sai Allah ya nunama kyakyawan jarabawa akan haka, Allah ya tsine miki giya, kabarsu su kashe ni, 'suna barin wurin Virus ya karaso da abokansa yan Sara suka harda fetur da taya wai zasu kona ya'u bakaramin takaicin rashin samun Sa sukayi ba, yayinda wasu sukace a fito musu da Aisha, nan virus yace su kyale ta batada laifi, Laifin baban ne dayake mata mugunta hartaki yin Aure Ashe shike kwasar romon tunda budurwa ce su barta kawai, a zuciyar shi kuwa wani kudiri ne na daban akan hakan dayayi tunda yaga Aisha da underwear yasa ma Ranshi koda gawarta cefa saiya dandana.

Watsewa akayi babu Wanda yabi takan Ramata da yaranta kowa ya koma gida ana ruruta abunda ya faru dama Wanda bai faru ba kowada kalar labarin Sa akan lamarin, dakyar bilki ta tattaro jarumtar ta yayinda ta dibo ruwa a Roba da tsumma taita shafama Ramata da Aisha a jiki saboda rashin mafitan abun yi shiyasa tace bari ta gwada kila a Dace, Saida gari yafara wayewa Ramata ta farfado nan akai jugum jugum Aisha kuwa babu ko Alama, saida tayi yini daya Sannan aka samu kanta, babu mai iya magana cikin su kamar kurame yayinda zaman gida yagama Auran dukansu babu mai iya leka waje, unguwa kuwa anyi gulma harta takashi? a'haka Rayuwa ta kasance musu babu labarin ya'u babu kuma Wanda yadamu yasani cikinsu bare ya tambaya ko maganar basu Kara tadowa ba, hidimar gidan garbati ne ya dauka gaba daya harta gidansu AK Ramata ta daina zuwa inda Mamie ta tako takanas tazo musu jaje rareda Alkairi mai yawa inda Alhaji muktar ma yabada kudi masu yawa akan abasu.

Aisha kuwa saida aka dade sannan tafara fita hijab dogo har kasa take sawa kamar da nan za'ai ta mata habaici da gori a unguwan, nan aka Sa mata suna *Ustaziya ko Yar'duniya* yayinda ta dauki kaddarar tada hannu biyu bata taba tankawa ba makaranta daina zuwa tayi Boko da islamiyya akan dole inda ko Kare baya naiman ta samari kuwa ko'yan iskan ma sun daina zuwa a cewarsu ita kakarsu ce a bariki dakyar da sidin goshi mai unguwa yabarsu sukara Zama tareda kashedi mai girma idan makamancin hakan yakara faruwa za'a hukunta su tareda koransu gaba daya, sanarwa yabada duk Wanda yaga ya'u a unguwar azo a gaya mai baice kowa ya dauki hukunci a hannu  ba.

13

Bayan shekara Uku da faruwan hakan ne cikin Ikon Allah da Al'ajabi tayi wani Saurayi daga sama wai yazo kuma ba wasa ya kawo shiba Aure yazoyi bayasan bata lokaci, sunan shi Musa yanada mata daya da yara Uku baida Wata Sana'a I'lla iyaka shago dayake dashi yana saida kayan masarufi harga Allah baimata ba amma hausawa sunce da babu gara ba dadi hakan yasa batareda dogon nazari ba ta amince a lokacin tanada shekara ashirin a duniya nan Ramata taita farinciki baki yaki rufuwa kashi sittin na damuwarta ya yaye domin tagama sama Ranta Aisha bazata taba samun mijin Aure ba kila Aure kuma sai a lahira idan anayi saboda bakin fentin da Ya'u ya goga musu ita kanta Aisha bata taba tunanin samun mijin Aure ba koma zata samu batasa ran anan kusa zata samu ba harga Allah tacire Auran AK a Ranta tasan kozata mutu tadawo ita dashi har abada saidai babu na biyun shi zatai Aure bana soyya ba.

Mamie ce ke kaiwa da kawowa bakinta yaki rufuwa yayinda da kanta take shigo da farantan abincin da suka gaji da haduwa domin tarban dan'lelen ta, farin saurayi sosai kakkarfa mai kwantaccan bakin gashi dake daukar ido yayinda gefen bakin shi bakin gashin ke zagaye da karamin bakin nashi Wanda Ake kirada *Quarter mullion* hancin shi siriri masha Allah idon shi basu cika girma ba yan daidai sannan basuyi fari kar ba duk inda ake naiman Handsome indai kaga Saurayin nan tohfa an Dace, fara'a ne kwance a fuskar shi Rabon shida Nigeria harya manta he feel Alive gashi cikin gidansu yayinda ya matsu yaci abinci akwai tarin tambayoyin da yake shirin yima mamin nasa, zaune suke gaba daya harda Dadyn su anata cin abinci tareda basu labarin nasarorin daya samu a tafiyar dayayi yasha Addu'a babu adadi wurin iyayan nashi cike daso da kauna nan Dadyn su yai mishi Albishir din fara Aiki a ma'aikatar su NGO tareda mukami mai girma saboda darajar  kwalinshi saidai muce masha Allah, gakuma kasuwancin shida yakeyi Abubuwa sunmai yawa yana naiman mataimaki tunda tsufa yafara kamashi ba kamar daba, duk AK ne zai amshe su a'haka firar nasu na ranar ya Kare batareda yasamu damar yima Mamie tambayar da yakeso ba.

Washe gari Allah Allah yakeyi a hadu cin abinci cike yakeda da zumudin dahar mamakin kanshi yake, wanka yayi cikin kananan kaya misalin karfe Tara ya sauko breakfast lokacin Daddy ya Dade da tafiya office, tsakurar abincin yayi sama sama yayinda yake Jan Mamie da fira har akazo inda yakeso, 'wai Mamie ina mai muku wanke wanke ne Ramata Kota daina zuwa dawuri ne Yanzu? Aisha fa nasan tazama budurwa yanzu, 'hmmmm bari kawai son abun ne saidai muce Allah shi kyauta rabona da Ramata kusan shekara Uku kenan baiwar Allah oooh Duniya, tafadi cikin jimami, nanta bashi labarin Abunda yafaru bakaramin tashin hankali ya shiga ba sai zufa yakeyi of all people why Aisha? Eye Mamie Anya ba sharri akayi musu ba kinsan fa mutane? AK kabar mutum kawai Allah kadai yasan abunda yafaru nidai bazance yar'iska bace kamar yanda ake fadi a unguwa saboda ban gani da idona ba, inadai musu aike jefi jefi saboda samun lada, Allah yasa ta Auru shine kawai wlh na tabbata babu mai Auran yarinyar nan, why mum? Meye Laifin ta? How sure are u bazata auru ba? Yafadi tareda mikewa a fusace yabar wurin, ikon Allah konice Ya'u kokuma nice yan'unguwa dasuke kiranta yar iska? Ihu fa kakemun AK, ita kadai take maganar ta AK kuwa ya Dade da barin gidan cikin tashin hankalin da baisan dalili ba.

Saida yayi kwana biyu babu inda yaje sai tarin wasiwasi da yakeyi taya ma za'a cemai Aisha yar'iska ce? Dukda ya Dade bai ganta ba amma ya tabbata ko cikin duhu zai iya gane ta, why?  Toh kodai gskia ne kamar yanda aka Kara bashi labarin abun a unguwa dukda masu bada labarin suma sun Kara gishiri da Maggi a ciki.

Ramata keba Aisha labarin dawowar AK yi tayi kamar bataji taba saboda rashin abun cewa zuciyarta kuwa idan banda bugu babu abunda takeyi inda har Ramata ta farga da hakan taja bakinta ta tsuke,
Hijab ne kamar koda Yaushe katoto a jikin ta bayan sallar Isha'e Ramata ceta aiketa bayan Layin su kai kayan wankin da taima wasu gida kusan kwana biyu kenan basu aiko sun Amsa ba gashi ya cika mata daki gashi suna bukatar kudi basuda ko abunda zasuyi Karin safen gobe, bilkisu ta aika Aisha tace zata bataso ana aikan bilki sannan tafisan fitan Dare yanzu babu maisa mata ido kamar rana dukda Yanzu anfara sakar mata Mara ba kamar daba dadan dama dama, ta bayan layinsu tabi inda tunda Vairus yaga fitowarta da inda ta dosa Yaji kamar anmai bushara da Aljannah yayinda takai sakon tareda amso kudin wankin Naira dari Uku da hamsin, siririyar hanya yar karama ce  ba'a cika wucewa ba kasancewar ba'a gama ginin gidajan dake wurin ba koda rana hanyar shiru zaka jita bare da Dare dukda haka mutane nabin ta sosai saboda shortcuts ne mai sauki indai zaka zagaya bayan Layin kana bulla ka huta dogon tafiya, touch light ne hannun ta tana tafiya sauri sauri Addu'a dauke a bakinta bata San maiyasa ba gabanta ke matukar faduwa sosai, ji tayi an buga mata wani Abu akai yayinda aka toshe mata hanci da farin kyalle nan tafara ganin jiri, daukar ta sukayi har cikin wani gini da ba'a karasa ba dukda tana ganin duk abunda yake faruwa amma takasa komai jikinta ya mutu ko hannu bata iya dagawa, 'mai naaaay..yi muku? K..uyi hakuri Dan darajar Allah kada ku tona mun Asiri tana fadi idonta na lumshewa, "matsiyaciya asirin ki ya Dade da bankarewa ai kinada wani asirin da za'a iya rufewa ne inji virus daya kwashe tada kyawawàn Mari har guda Biyu ya jefata kasa a cewarshi ya Rama Marin datai masa shekaru Uku da suka wuce, kuji tsoran Allah da ranar hisabi ku kashe ni kawai kiyi hakuri kada ku zalumci rayuwata da Addinina, kafarsa yasa yaita hambarin ta a ciki, ko kiyimun shiru kokuma ina gama farkaki in farke cikin ki, yafadi da karkausan murya

Sha'awar zagaye unguwar nasu yakeyi dukda bawani chanji da aka samu amma ya tsinci kanshi yana Sha'awar zagayawa koba komai ya motsa kafa tunda yadawo yana zaune a gida gashi baida Abokai a layin iyakar Sa kofar gida nanzai samu mutane biyu suyita firar duniya, yagaji da zama wuri daya tafiya yakeyi jefi jefi yana danne danne a waya iska mai dadi yana hura shi cike yakeda nishadi ya kwasa a kalla minti shabiyar yana shiga lungu lungu batareda wani tsoro ba, a hankali yake jin nishi tun baya jiyo abunda ake cewa harya fara jin hayaniyar samari suna ihu da shewa nan kuma Yaji siririyar muryar mace, ana  wyyoo Allah wash kaina zai fashe, dukda zuciyarshi nabashi shawarar komawa amma idon shi nasan ganin Abunda Akema nishi da shewa, cikin dakiya ya tunkari wurin yayinda yake haskawa da wayarsa, samari ne su Uku kowa na rige rigen tube kaya yayinda Ga mace kwance a kasa idonta na lumshewa, barin abunda sukeyi sukayi kowanne da gajeran wando Aisha kuwa tuni sun cire mata katon hijab dinta sanye takeda Riga da Skart kanta da dankwali, wani irin sarawa kanta keyi kamar zai fashe, 'mai kuka bani? Kaina bana gani sosai ta furta tana shirin mikewa dakyar a karo da dama, Malam lafiya? Suka furta babu Alamar wasa cikeda takaicin tsaidasu daga garar da suka kosa su kwasa, baibi takansu ba harya juya zai tafi saikuma yadawo Kara kunna hasken wayarsa yayi tareda rissinawa daidai fuskar macen bakaramin tashin hankali ya shiga ba jikin shi har rawa yakeyi nan danan yafara hada zufa gashin jikin shi a Mike cikin tashin hankali, kulle fuskarta takeyi Dan yagama kashe mata ido da hasken wayarsa bata gani, Dan girman Allah ku Taimake ni zasu kashe ni a taimaka, aaaa.....isha ya furta tareda mikewa da sauri har yana dafa bango, muryarsa dataji ne tadan Mike zaune cikin maye dakyar dukda bata gane komai Amma taga gefen fuskar shi, Yaya, kaine? Yaya ka tafi dani daganan yaya bana gani sosai kaina zai cire.. Virus kuwa ikon Allah suke gani sai a lokacin suka gane AK cikin takaici ya kalleta, yaya? Ina yayan yayan ubanwa? Kin sanni ne? In taimake ki?  Uban waya kawo kinan? Kwartayan da suka fito dake lokacin nan su maidaki Dan ubanki ni kikaba Goran gayyatar Dana gayyato miki su nan? Zare mata ido yakeyi kwalla na zuba a idon shida yagama rinewa, harya juya zai tafi ya waigo tareda kallon su virus, kuyi hakuri da katse ku danayi ku cigaba da abunda kukeyi, juyawa yayi baiko waigo ba, Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, AK kada ka tafi ka rufamin Asiri AK! AK!!  Zasu keta mun haddi AK!!! Aaaaaaaaaaa

14

Kai meye haku kukeyi? Inji virus yayinda yaga sauran yaranshi na zura wando, baibi takan suba ya dumfare ta babu komai a jikin shi, hankade shi daya daga cikin su yayi, oga Ashe baka gane ba, wani shegen ne zai ganmu a haka yace mu cigaba? Eye? Tarko nefa kagane mana eyeh haba baba, kasan yanda yarinyar nan suke da gidan su yaron nan AK harfa hawaye nagani a idonshi, Na Ukun ma ya amasa, 'Alkur'an nima na ankare kai, kwalawa zai kwaso mana yayinda yagama Tara mana jama'a kawai eh yanee, dakyar suka iya lallaba shi tareda  janye virus da takaici ya kusa kashe shi badan yaso ba amma tabbas AK tarko ya hada musu, nifa yasin yasin tsaf dazata Aure ni zan yarda yarinyar akwai maiko yasin yafadi yana zura wandon shi,  kaga Karamar kasa da Arzikin man fetur yasin kirarin irin matan nan kenan, Allah yabamu kudi muci babbar Giwa, Suna Allah ya isa suka watse a wurin yayinda suka dauki dari Uku da hamsin dinda tayar a kasa a cewarsu ko sigari Sa sha su rage zafi.
   Aisha kuwa wani bcci mai karfi yayi awon gaba da ita, inda su Ramata ganin shirun bana karewa bane tace bari tabi sahu taga ko lafiya, gidan wankin tayi inda suka shaida mata Aisha tabar gidan tuni harta Amsa kudin wankin, cikin mugun tashin hankali taita duba lungu lungu sako sako babu ko tsoro, "hmmm wani Abun sai mama" cikin ikon Allah hartazo inda Aishar take yashe a kasa bcci takeyi harda munshari dalilin abunda ta shaka, salati tasaki babu halin ihu yanzun nan Sai akara fassara su da gagarumar sharri, kan Aisha ta Dora akan cinyarta tana kuka mai fitarda karamin sauti, jikin ta tashiga dubawa saida ta duba komai tsaf sannan tasaki Ajiyar zuciya, barin wurin tayi gudu gudu tareda amso pure water awani shago mai sanyi aiko ta dinga bulbula mata dakyar Aisha ta iya bude ido cikin maye a'haka ta tallabo ta suka Mike tana layi Kamata sosai Ramata tayi a jikinta a haka sukayi har gida cikin ikon Allah layin babu kowa babu Wanda ya farga, ba'a samu kan Aisha ba sai washe gari  inda taita sujadar godema Allah da bata wulakanta ba, babu abun takaici GA diya mace irin zubarda budurci a titi  koda Ramata tasamu labarin abunda yafaru saidai bata gaya musu zuwan AK wurin ba, mikewa tayi tareda rantsuwar za'ayi ta takare rashin gata ba hauka bane saidai subar unguwan, dakyar Aisha da Bilkisu suka lallashe ta ko garbati bai sani ba ganin ba karamin tashin hankali za'a kwasa ba, tunda Allah na Tareda mai gskia bawa bazai taba gujema jarabawar shiba idan sunbar nan suje ina? Inda zasu wayasan gobe? Wayasan abunda zai faru??
Ta hakura tareda sharadin babu inda Aishar zata Kara zuwa Abu daya zai fitar da ita daga gidan nan shine Aure insha Allah gashi kuma yana matsowa.

Musa yazo batareda boye boye yayinda Ramata ta turashi wurin mai unguwa a cewarta shine mai bada Auran Aisha, baiko nuna damuwa da hakan ba yayinda yace bai damuda sanin komai game dasu ba sun tsaida magana akan zai mata kayan fitar biki ne kawai banda lefe a cewarshi tunda ba kayan daki zata zoda shiba zaisa abunda baza'a rasa ba a dakin amma kada su cika buri, Basu damuda hakan ba sudai burin su ace Aisha na dakin mijinta dukda yace tareda iyalin Sa zai hadata, ita kanta Aishar bata damuba ganinta babu abunda zaikara sata farinciki a duniyar ta tun dataga AK dukda bawani ganinshi tayi ba gaba daya takasa sukuni ko kadan bataga Laifin shiba I'lla haushin kanta dataji daya risketa a haka shine takaicin ta, wani maganadisun soyyar shice ke fusgarta zuwa Gare shi a karo da dama tasha yunkurin kodai ta bishi gida taimai bayani ne? Sanin Ramata bazata taba barin ta fita ba hakan yasa ta rame sosai kullum tana cikin kwalla da tunanin kada yaimata fassara Allah yasa baya fushi da ita 'inda a barayin AK kuwa baida damuwa harkokin shi kawai yakeyi ya tattara ta gefe guda ya watsar komai suna Aisha ya tsana a halin yanzu.

Angama komai na Auran Aisha Ramata da garbati sun danyi bajinta ba laifi inda Ramata tasiya zanin gado guda biyu masu saukin kudi tareda risho da kula biyu masu kyau da samiru su cups da jugs da plates harda ledan tsakar daki, da kujeran tsugune, kaya dai ba laifi na fitar kunyar uwa a cewarsu basa mika ta haka gaya ba saikace daga sama ta diru, ya'u kuwa shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu.

15

Mai unguwa yayi farinciki sosai tun bare yanda aka Dora shi akan komai hakan yasa aka yanke ma Musa sadaki dubu talatin bayan an kwana biyu suka kawo kayan Sa rana nan akasa sati biyu masu zuwa tunda babu wani shirin da za'ai, kati aka buga mai saukin kudi akaita rabawa duk Wanda yagani saiya tofa Albarkacin bakinsa wasu na tayata murna wasu na mamakin Wanda Ze aureta a cewarsu munafuntar shi akayi wasu na ko sadaka basa so kowadai da abunda yake fadi, Ramata ta kaima mamie kati mai yawa da alewa nata Dana Alhaji aikuwa ba karamin murna mamie tayi ba baki yaki rufuwa nan taita Kara kwantar mada Ramata hankali tareda Alkawarin suma zasu bada gudunmawa mai yawa a Auran ita da Alhajin, ana haka AK ya shigo gidan daga wurin business dinshi yadawo tunda yayi sallama yaga Ramata dauke kai yayi harda juyawa, Kiranshi mamie tayi badan yaso hakan ba fuska a daure yaje, 'baka gane Ramata ba mamar Aisha wacce ka tambaya kwanaki? 'Ina wuni ban gane taba yafadi yana shirin juyawa, 'katin Auran Aisha aka kawo Aishar ka zoka gani nanda sati biyu....... Aishar babanta dai yafadi yayinda yadawo ba kunya yasa hannu ya dauki katin, kallon shi sukeyi daga Mamie har Ramata dataji wani iri a Ranta, 'Allah sarki bawan Allah, Virus zata Aura koh? Koda yake banga Alama ba su kansu maza yan iska suna neman ma yaransu uwa tagari lallai wannan ya dauko kaikayi ina fatan dai sunje Asibiti anyi gwajin kanjamau dukda maganin shi kyauta ne, 'AK wani irin iskanci ne wannan? Inji Mamie ko kadan bataji dadin Abunda yayi ba, mai nayi Mamie daga fadin gaskiya? Konayi karya ne? Yafadi yana ware hannuwa, Aisha fa nace wacce ka raina kafun tafiyar ka.....au Karuwa zaki cemun zanfi ganewa  wannan Yar'iskan? Tsawa Yaji an daka mai ta bayanshi Alhaji muktar neya dawo, subhanallah Abdulkareem musulmi kake kira da munanan suna haka? Mai akai maka daga dawowa kasar? Ashe bakada hankali ban Sani ba? Mikewa Ramata tayi ido cikeda kwalla dakyar ta iya Jan kafarta  batako bi takan Mamie dake bata hakuri ba tabar wurin cikin kunar zuci tareda tunanin Laifin da sukai ma duniya Tai musu daurin talala, AK kuwa daki ya shiga yayinda wani sabon tsanar Aisha ya shige shi ji yake kaf duniya baida na biyun ta a makiyi a dalilinta Mamie da Daddy kemai ihu a dalilin mai fuska biyu Yar'duniya yafadi 'gaban madubin dake manne a dakin ya tsaya yana kallon kanshi kamar zai hango Aishar a ciki.

Ramata kuwa babu Wanda taba labarin Abunda yafaru tabarma zuciyarta a ganinta fadin shi baida wani Amfani.

*Rana bata karya*

*Kai kubani kidan Amarya da Ango a sama kowa ya shirya kwaso shoki gobe nefaaaa??‍♀??*

Sorry for d short page am occupied yau shiyasa

16




Daddy ne zaune a parlor shida AK misalin karfe Tara da Rabi na Dare bayan sungama fira, Dadyn ya gyara Zama Alamar akwai magana a bakin shi yayinda ya kalla AK din, 'Abdulkareem , ya kirashi tareda kallon shi, 'naam dady ya Amsa hankalin shi gaba daya nakan baban nashi  sanin  daddy baya kiran sunan shi saida kwakwaran dalili, 'shawara ce nakeso inbaka inda hali, idan yama toh saidai muce Alhmdlh domin zanfi kowa jin dadin hakan, 'ina jinka dady yafadi tareda gyara zaman shi sosai hankalin shi akan daddyn, 'gyaran murya Alhaji muktar yayi sannan yafara magana, 'akwai yarinyar aminina business partner Dina duk Wanda ya sanni toh yasan Alhaji dan'juma  mutumin kirki ne kuma mai Amana hakan yasa tuntuni na Dade dama Sha'awar baban diyarsa  saboda yarda da tarbiyyan gidan danayi idan Allah ya kaimu kaje ka dubata idan tamaka harna masa magana akan zakazo kuga juna domin Kara dankon zumunci da kasuwancin  namu kuma harma yafini farinciki da hakan.......'Daddy, AK ya katse shi daga maganar da yakeyi, 'ina jinka
Inji Alhaji muktar dukda baiji dadin katse shin dayayi yana magana, 'Kaimun gafara Daddy wlh tallahi batayi mun ba bana Santa Dan Allah a hadata dawani, yafadi kai tsaye bako kunya dajin nauyin mahaifin nashi 'kasan tane? Alhaji muktar yafadi cikin mamakin AK, kaje ko ganinta kayi mana, 'ban Santa ba daddy basai na ganta ba amma bata yimun ba koda naje zan Amince ne bada San zuciyata ba, 
'Toh!
Toh!!
Toh!!! 
Hakan yayi kyau, inji Alhaji muktar cikin rashin jin dadin Abunda AK yaimai, kanada wacce kakeso ne? Saika kawota da gaggawa niba mutumin banza bane ace shekaru nata jamaka sa'annin ka sai haihuwa suke tunda kadawo muke maka maganar Aure mai kake cemana? Lokaci kake jira koh? Toh mun gaji da Zama cikin lokacin ka, wacece wacce kakeso??
'Cikin rikicewa ganin yanda Alhaji muktar yadau maganar da zafi ba kamar yanda yayi tsammani ba sai zufa yake hadawa a zaune.....'dakai nakeyi fa inane gidansu suwaye iyayanta cikin satin nan nakeso aje gidan nasu, 'damaaaa damaa Wata ce bamu gama daidaitawa ba tukunna, yafadi cikin rawar murya, 'mttsssew Abdulkareem tashi kabani guri, naga Alama nazama Abokin wasanka ance kakawo mata kaki anbaka mata a gidan mutunci kace bakaso shin auren ne bakaso koko isa dakai ne bamuyi ba? Zakasha mamaki jeka jeka shikenan, mikewa yayi jikin shi a sanyaye yabar wurin dukya rasa maike damun shi wai ina matan suke ne? Ance akwaisu a gari sosai shi yar yanzu bai gansu bafa ya akeso yayi??

Alhaji muktar neke shirin zuwa Office dukda baicika zuwa ranan juma'a  ba ko zaije baya zuwa dawuri amma tun safiyar ranar ya tashi ya shirya dawuri Mamie ceta shigo dakin cikeda mamaki, Daddyn su Abdul badai fita zakayi ba? 'Kaji mai idonki yagani idan ba fita zanyi ba mainene amfanin babbar rigar Dana Sa? Bafa nasan tambayar rainin wayau, 'Allah yabaka hakuri gani nayi yau juma'a ai sai bayan an sauko masallaci kake Fita gashi yaune daurin Auren diyar Ramata na dauka zakaje, 'auu kinga ko shaf na manta wlh Wasu baki mukeda su zasu zo daga Lagos zamuyi meeting dasu tuntuni Nike jiran kiransu saboda  yau zasu toso  da sassafe, karan kiran wayar shine ya tsaida shi yayinda ya dauki wayar dake kan kago cikin hanzari ya juya harshan turanci, yayi minti Uku a wayar ya katse cikin takaici sai masifa yake, 'ina amfanin rashin cika Alkawari kun tsaida mutane Dan iskanci kuce kun daga sai ranan Monday? Kaji fa, akin banza, 'ya akayi kuma mai gidana wake tabo munkai yaune inji Mamie datake shirin samai hula akan shi, 'maida ai nama Fasa fitan anyi canceling meeting din sai Monday insha Allah, yafadi tareda cire babban rigar shi, Anjima naje wurin daurin Auran ko lada na samu.


Misalin karfe daya babban  masallacin unguwan ya cika makil babu masaka tsinke yayinda aka idar da sallar juma'a ana shirin daurin Aura saidai mai? Babu ango babu Alamar shi babu waliyan Ango nanfa akaita kananan surutu, a gefe daya ya'u ke zaune jikinshi manne Dana mai unguwa kassncewar tunda bikin ya matso yaita tura garbati wurin mai anguwa naiman Alfarman halartar daurin Auran diyarshi tareda Alkawarin ana daurawa baza'a Kara ganin shiba, dakyar da sudin goshi mai unguwa ya lallashi matasan unguwan akan subashi damar shigowa yau daya rak koba komai Auran diyarsa ake, yasha fararan kaya harda babban Riga sai washe baki yakeyi cikeda farinciki saikace shine angon, tunda akaga babu wani dangin ango bare angon aiko ya'u yaita hada zufa harda cire hular kanshi yana fifita dukya jike babban Riga, 'Musa ne ya shigo masallacin cikin hadin gambiza sanye da wandon farin shadda tasha guga sai Wata bakar  kodaddiyar T-shirt  baza ido yakeyi sai zage zage yakeyi aikuwa charaf idon shiya sauka kan ya'u daya kara makure jikin mai'anguwa, 'munafukin Allah ta'ala wato ni zaka Aurama diyarka daka gama kwakule ta saida ka tande ta tsaf zaka kawo mun tallar Auran ta? Macucu mazinaci tir duk iskancin ka ace sai kayi da diyar cikinka? Billahillazi ko balarabiya ce sai andawo da kudina tundaga kan taro zuwa sisi na bazaiyi ciwon kaiba yafadi yayinda yake nade kafar wandon shi kafun a Ankara harya shako wuyan babbar rigar ya'u ya hadashi da bango yakai masa naushi a baki, 'banda rainin hankali karuwar zaka aura mun duk mazan unguwan nan sungama saninta akace, mutane ke bashi hakuri yaki sakin ya'u a cewarsa sai an maido mai da komai saikace Wanda ya kashe kudin Arziki babu yanda baayi dashi ba kememe yaki sakin wuyan ya'u daya Kara makurewa, ya'u kuwa kunyar duniya tagama rufe shi ji yakeyi kamar kasa ta bude ya shiga kokuma Allah ya dauki Ranshi a lokacin wannan abun kunyar damai yayi kama? Dawani ido zai Kara kallan iyalin Sa a karo na biyu yakara tarwatse musu Rayuwa a dalilin gyaran dayake tunanin yayi, 'Alhaji muktar neya Mike yayinda ya tunkari wurin rike hannun Musa dake wuyan ya'u yayi, bawan Allah kaima Allah ka sake shi, wannan ai tozarci ne, fisabilillah saboda masifa ya fadar Ma yarinya ko'ince jarabawa saikuma taki auruwa? Haba jama'a ku tayani ganin lamarin nan idan ba'a Aurarda da ita ba karuwa barnar zatayi kadauki hakan akan zakayi sadakatul jari'a hakan ya kamata aima irinsu bawai Asa musu karan tsana ba da tsinuwar dake Kara dulmiyar da doran kasa bawai a dinga gudun suba Allah kadai yasan yawan ladan dazaka Sa.......''dakata dalla Malam gafara kafun in hadaku duka in tumurmusa rainin wayau kana nufin in Aure ta dukda ubanta ke cinta komai kake nufi? Toh billahillazi babu Dan iskan daya isa ya cuceni da dadin baki waikai zakai mun wa'azin bogi uban waya hanaka yin sadakatul jari'ar kai? Komu matsiyata akeso mu dinga yinta muna Auran yara karuwai idan kanaso ka burge ba haka zakayi ba saika Mike kawai a daura dakai ko mai gadin gidan ka ka Kara masa yakarasa ragowar ubanta dawata wa'azin ka Mara ma'ana sannu limamin madina kabar ganin ana kaunarka kanaso ka Kara siyan soyyar mutane da dadin baki, dalla kauce bani wuri ba maganan matsayi akeyi anan ba, 'Alhaji muktar Ranshi yayi mutukar baci ganin yanda Musa ya kwance mai zani a tsakiyar kasuwa duk girman shida daraja shida mutane keyi, abun takaici wasu burgesu Musa yayi yayinda dayawa ke dariya da ganin wautan Alhajin, cikin sanyin jiki yaje yaja hannun liman tareda makwabtan dake jikin gidan shi mutum biyu gefe suka koma cikin minti kadan liman yafara magana a lasifika,toh jama'a Alhmdlh ina cikeda farinciki tareda Kara ma Allah godiya akan lamarin daya faru yanzu wani baya taba Auran matar wani, duk a gyara Zama Dan Allah a kimtsa za'a daura Aure....'da uban wa? Inji musa, badai dani ba? Babu Wanda yabashi Amsa I'lla iyaka sadakin shida aka mika mishi dubu talatin chif, nan yaita washe baki yayinda ya zauna bako kunya harda lankwashe kafa cikin yan kallo shima yanaso ya kashe kwarkwatar idonsa, ya'u kuwa da garbati sakin baki da hanci sukayi, nanda nan jama'ar wurin suka shaida Auran *Abdulkareem muktar tareda Aisha Ya'u*   akan sadaki Naira dubu hamsin nan take Alhaji muktar ya kirgo su tsaf makwabtan shi sune waliyan Ango sumai unguwa kuma waliyan Amarya duk Wanda ke cikin masallacin ba karamin mamaki yayi ba, ya'u kuwa hawaye kebin idon shi wani nabin wani yatashi jiki na rawa har inda Alhaji muktar yake zaune zubewa yayi hade da rike kafafun shi duka biyun sai bude baki yakeyi amma yakasa magana sai hawaye kawai, damke kafan Alhajin yayi sosai sai nishi da numfashi yakeyi idon shiya kafe a sama, dif ya zube a wurin zuciyar shi ta buga lokaci daya baiko motsa ba nan akayi kanshi ana salati, 'Vairus kuwa baiso haka ba domin kadan yake jira yace a daura Auran dashi dama Addu'ar shi daya Aisha tayi kwantai yaga samu yaga rashi.

17


Kan Ya'u akayi ina rai yayi halinsa tuni nan aka dauki kabbara Allah sarki ya'u ashe yanada rabon ganin Auran diyarsa Allah ya dauki Ransa a wurin daurin Auran yar'sa, jama'a nata jimamin lamarin tun bare jarumtar da Alhaji muktar yayi, liman yabada sanarwa da la'asar za'ai mai salla akai shi makwancin shi nan danan wani yaro ya ruga gida batareda bata lokaci ba Amarya taci kwalliyar ta babu laifi tayi kyau tasha lallan gargajiya inda babu wasu yan biki masu yawa sai makwaftar da gulma ce yakawo su harda masu kawo mata gudunmawar maganin mata na Ni'emah maganin matsi kuwa ankawo mata shi babu iyaka wasu saboda cin fuska kawai zasuzo suna mata bayanin yanda zatayi matsi bilki ceke tanka musu yayinda Ramata ta kwabar musu kada kowa ya tanka sunaso ayi rigima ne kuma yau ranar farinciki ne, shinkafa jaluf akayi mai kyau sai faten tsaki, Amarya kuwa kawayan ta basu wuce mutum biyu ba suma Abokanan karatunta ne suka samu labari dukda bata gayyaci kowa ba suko sunzo, 'Aisha ta Auri AK Dan gidan Alhaji muntari Naira, abunda yaron keta shela kenan harya isa gidan, Kai zonan mai naji kana cewa bafa masan iskanci, inji Wata makwafciyar suda ta damki hannun yaron tana shirin ingiza keyarsa waje, Wlh wlh yanzu aka daura Auran Aisha da AK wannan baturan daya dawo kwanaki, yasin idan nayi karya Allah tsinan, 'mikewa Aisha tayi bako kunyar Amare tareda jawo hannun yaron cikin daki, 'ummah kinji fa abunda yake cewa, tafadi tana washe baki nan kallo yakoma kanta, koda karya yakeyi yagama faranta mata ayau tunda ya danganta AK a matsayin mijin Auren ta, nan mata akaita surutu ana karyata zancen, 'yo duk matan garinga hauka yayi dazai Auri diyar unguwan nan, haba Malam banda ma haka GA yara masu komai a unguwa kai dalla wuce kada in zabga maka Mari, inji wasu matan da abun yafara kaisu bango, 'yauwaaa sannan babanku Ya'u mai shayi yafadi ana tunanin kamar Maya rasu, 'salati aka dauka gaba daya nan kowa yagama yarda ya'u ya rasu, Ramata kuwa tunda aka fara maganar kallon kowa dai'dai takeyi tarasa abun cewa koda aka fadi Rasuwar ya'u ko motsi takasa yi nan aka dinga bata baki, ana haka Garbati ya shigo tareda rokon jama'a akan subar musu dakin yanasan ganawa da Mahaifiyar Sa, 'zaure suka koma wasu kuma na zaune kofar gida a cewarsu sai sunga abunda zai ture nadin buzu, 'kallon Aisha yayi yayinda ya kalla bilki, 'ki harhada duk wani abunda Musa yakawo na Aure harda kayan fitan bikin dayayi ta cire wannan na jikinta a hada da sauran a kawomun, sannan mama........babanku ya rasu koh Garba? Ta katse shi tana kallon cikin idonsa, Allah ya gafarta masa mukuma Allah yabamu juriya da tawakkalin rashin nasa, 'jikin shi yayi sanyi yayinda tunda abun yafaru sai lokacin Yaji hawaye nabin kumatun Sa na tausayin mamar tasu da kannan shi, Wata irin mace ce ita mai dakewar zuci? Bata taba bayyana sirrin Ranta, hannunta yakamo zaiyi magana, 'tashe kuje a suturta shi akai shi gidan shina gaskiya, kukuma ku share hawayen ku Addu'a zamu cigaba dayi, 'mikewa yayi zai fita saiya waigo tareda kallon Aisha wacce ta hade kanta da guiwa tana kuka kasa kasa, 'An Daura Auranki da Abdulkareem Dan gidan Alhaji muktar akan sadaki dubu hamsin, dukda tana cikin tashin hankali saida ta dago ta kalli yayan nata idonta taf hawaye, murmushin ke neman subce mata nanta maida kanta akan cinyar ta samun kanta tayi da mika tawassali tareda godiya ga Allah Ashe AK Santa yakeyi?
 Ashe ba ita kadai take dakon soyyar shiba?
 ashe zata Kara tsintar farinciki a Rayuwar ta lokacin data cire ran samun murmushi a duniyarta sai gashe bayan lokaci mai tsawo ta manta daduk kuncin ta dukda Rasuwar mahaifin ta nanan daram a gefen zuciyarta amma murnar Mallakar AK ya shafe duk wani kunci a tattare da ita, mikewa tayi kamar mahaukaciya tareda girgiza bilki datake gabzan kuka, 'Auta Auta kinji mai yaya yake cewa? Auta Dan Allah ki mareni Auta ki jijjiga ni dukda nasan ba mafarki nakeyi ba inaso in tabbata bani kadai naji Abunda yake cewa ba, cewa fa yayi nazama matan Aure kuma AK na Aura, yaya AK na,
 Auta Ashe AK zan Aura? Ashe sona yakeyi? Ashe shine ya Hana Musa Aurena yayinda kaddara taso ta shiga tsakanina dashi, Ummah, tafadi tareda rarrafawa tana rike kafan Ramata dake binta da kallo itada bilki gani sukeyi tadan samu matsala akanta ubanta fa akace ya rasu yanzu amma tana murnan Mallakar namiji ko kunyar idonsu bataji, 'ummah kice wani Abu mana, kinji, kinji umman mu, Kuka tafara yi mai sauti inda kadan yarage Ramata tayi kanta da bugu ganin ta zube a wurin tana kuka mai taba zuciya taji tausayin diyar nata yagama mamaye ta datasan matsayin ta a wurin AK din datafi haka yin kukan babu Wanda ya lallashi wani cikin su Ramata kuwa babu koda digon hawaye a idonta.


Ankai ya'u gidanshi na gaskiya saidai muce Allah ya gafarta mashi idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani, yayinda Garbati yace baza'ai zaman makoki ba sanin babu abunda za'ai a wurin sai gulman mamacin hakan yasa kowa ya watse badan rai yaso ba, 'Mamie ceke tsaye a parlor sai zufa takeyi dankwali rike a hannun ta tunda abun yafaru yan'gulma suka gaya mata komai tareda cikama wandon su iska gudun kada Alhaji muktar yadawo ya samesu a gidan, bakaramin tashin hankali ta shiga ba inda har kukan bakin ciki saida tayi ta kudiri aniyar saidai tarasa Auranta akan Auran Aisha amma Sam danta bazai taba Auran Yar'duniya ba, shigowar Alhaji muktar neya Kara tunzura ta da hanzari ta tarbe shi bakin kofan falo inda taita ruwan Masifa tana zagin Ramata akan asiri sukayi banda aikin Asiri ina AK ina Auran Aisha? Ance kwarya tabi kwarya ko cikin kwaryar bakowace kwarya bace tadace da dangatan danta ba, Aikin banza aikin hofi wlh saiya Saki karuwan nan bazan Zama abun nunawa a gari ba yarinyar da ubanta ke neman ta, 'kallon ta Daddy yayi tunda tafara haukan ta baice mata komai ba kanshi na Sara mishi babu abunda yake bukata sai bcci a lokacin dukda ana neman karfe biyar na yamma, wucewa zaiyi ta tare mishi hanya akan saitaji dalilin tozarcin daya jamusu, 'cikeda takaici ya kalle ta sama da kasa, 'wai bilki baki San mahaifin yarinyar nan ya rasu bane yau? Karona farko tun Auran su dataga yamata irin kallon nan, 'toh sai me? Nice na kashe shi? Ina ruwana dawata Rasuwar shi? Allah na tuba ai gara daya rasu koba komai an rage mugun iri a doran kasa, bai dameni ba wlh yau yau sai an sakar musu da diyarsu, 'hankade ta yayi saida tafadi akan kujera bayasan biye mata bare yadauki mummunan hukunci cikin fushi, yanufa dakin sa yayinda yarage kayan jikin Sa, wai maiyasa mata wani zubin sukeda Karamar kwakwalwa ne? Idan tanada magana dashi aiba haka ya kamata ta tunkare shiba  yaushe bilkin ta chanza Halinta ne? Shi za'a kawoma iskanci a cikin gidanshi aiko zaiyi maganin ta daga ita har yaron nata Aure kuma zaiga ubanda ya isa ya raba shi muddin yana raye.



Gogan kuwa yana chan yana harkokin Sa a cikin gari gaba daya gidan nasu baya mishi dadi yanzu ya  gwammace yabata lokacin Sa wurin business dinshi hakanan yau ya tsince kanshi da Muguwar faduwar gaba harsaida ya gayama wani Abokin shi inda yabashi shawarar yaita Addu'a kila Alkairi ne zai Same shi, hankalin shi gaba daya ya karkata kan gida hakan yasa shida saura ya doshi unguwan nasu tunda matasa suka hango motar shi nan akaita ihu ana daga masa hannu, Ango Angooo Angoooo kawai kakeji suna fada suna shewa, mamaki yayi toh dawa sukeyi? ango? Kodai sunyi tsammanin wanine bashi ba? Dariya yayi harda Jan tsaki yakara murza zaman hularshi a kanshi, 'oooh mutane da rigima sukeyi kaji wai Ango nida ko budurwa bantaba yiba naiman rigima kawai yawancin suma ban sansu ba, 'yafadi shi kadai, yana isa kofar gida tunda yayi horn kafun mai'gadi ya bude mai tuni wasu sun biyo motarshi a baya inda akan dole ya bude musu glass din motar cikeda mamaki, 'Ango kasha kamshi Dan Alaji yaushe za'a hada mana walimar maza tunda Auran yaxo bawai an shirya bane, 'walimar maza? Ya tambaya cikin mamaki, 'au eh mana wacce akeyi bayan an daura Aure mana, koda yake jeka huta muna nan munanan muna Sa ido Dan Allah kada a manta damu Dan Alaji, wooooo sai Ustaziya yasin Allah barku tare, 'dayaga abun yazama hauka Jan motarshi ciki yayi cikeda Al'ajabin samarin unguwar tasu, haka yafito ya rufe motar jikin shi dukyayi sanyi, mai'gadi kuwa sai kirari yake masa tareda Addu'ar Allah ya sanya Alkairi, 'wucewa yayi baiko bi takanshi ba inda yana shiga parlor ya tadda Mamie ta buga tagumi da hannu biyu biyu cikin yini guda harta Dan fada saboda tashin hankali, 'subhanallah Mamie lfy? Ya tambaya yayinda ya zauna kusada ita, kallon shi takeyi idonta ya rine yayi jajir, 'AK kasan abunda babanku yaimana? Kaji labarin tozarcin dayayi mana? Toh an daura maka Aure yau bayan sallar juma'a kasani idan baka Sani ba kabude kunne kajida kyau kazama mai mata mai iyali, tafadi tareda gyara zamanta harda buga cinyarta, 'dariya yayi har saida fararan hakoran shi suka bayyana, haba Mamie wlh kema kin iya tsokana Auran lfy saikace yaro, 'riko hannun shi tayi tareda kafa mishi ido babu Alamar wasa take kallon shi nan jikin shi yayi sanyi ganin yanayin nata, 'Abdulkareem nataba maka irin wasan nan? Wlh yau aka daura Auran kada Aisha diyar mai shayi, Mikewa yayi zumbur hadeda goge kunnansa harda Dan bugawa a tunanin shi baiji dakyau bane, 'eye? Yafadi yayinda yayi jifa da hular kanshi Mai kikace? Mikewa Mamie tayi hadeda maimaita mai abunda tace, 'chab haba wasa yakeyi duk matan duniya?jada baya baya yakeyi, Idan hukuntani yakeyi saboda naki Auran diyar Aminin Sa toh yanzu na yarda,  Mamie Yammata nawa nema a gidan? Sun kai hudu? Wlh idan dukansu yakeso in aura na yarda akan abunda kike danganta nida shi, wlh ina sansu, ko Auran kauye ne aimun na Amince, kowacece na yarda Mamie ina Dadyn? Yafadi yana waige waige waiko zaiga Dadyn a wurinda suke, *Ina Dadyn?*  yafadi cikin razanannan ihu har saida jijiyoyi suka furfuto akansa idonshi kamar zasu fado kasa sai zaro su yakeyi sunyi jazur, 'shi maiyasa bai aurota ata biyu ba? Maiyasa baiyi sadakatul jari'ar da itaba bayan yataba Aure? Tunda yataba Aure maiyasa dasai yakara da bazawara why me?? 
Why?
Why? 
Auran fari infara da bazawaran titi?
Haba!
Haba!!.
Bazawara duk mazan gari sun Santa fa, Ustaziyaar banza? Kirarinta fa kenan, wai Ustaziya saboda yanda takeda fuska biyu, Ustaziya koko yar'duniya? yafadi yana yarfa hannunsa duka biyun saikace zai Mari mamin, saidai shi Dadyn ya aureta wlh sakinta zanyi Dan bata auru ba sai zaro mata ido yakeyi itako baki da hanci tasaki tana kallon ikon Allah yayinda take girgiza kanta cikin bacin randa bata taba tsintar kanta a cikin saba, ji takeyi kamar ta rufe shida duka, Dan ubanka AK ni zakaima bakin ciki? da tsufa na kake mun fatan kishiya? Yaron nan bakada mutunci kishiya kakemun fata da tsufana diyar cikina yarinyar Dana raina da hannuna? Lallai ko kishin mamarka bakayi kakemun fatan babanku yakara Aure? Tafadi da Alamar maganar ba karamin zafi taimata ba.
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 25,099 12-17-2018, 03:07 PM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 26,656 12-17-2018, 03:06 PM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 17,920 11-28-2018, 09:33 AM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 54,886 11-26-2018, 11:37 AM
Last Post: Gimbiya
  ABUBUWA 17 MAFI BAN DARIYA A DUNIYA Gimbiya 0 3,433 11-13-2017, 04:04 PM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* 0 3,291 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* 0 4,115 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* 0 3,475 Less than 1 minute ago
Last Post:



Users browsing this thread: 1 Guest(s)