The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*DREAM GIRL* by Deejah Abdul
#1
kwana 3 kuma wai fake ne, who are u decieving? Kar ka sake ka qara nemana, i hate you ta kashe wayarta, khaleed a rude yake kiranta amma salmah tama kashe wayarta, ya tura txt har ya gaji shiru, cikin mintuna da basu wuce ashirin ba khaleed ya fita hayyacinsa, saeed kuwa sai kallon ikon Allah yake, baita6a tinanin abokinsa zaiso mace haka ba, haquri yake bashi ys bari ta sauko tayi fushine idan har tana sonshi zata fahimceshi, khaleed kuwa kuka kamar mace, waishi ya fasa auren Allah, haushi ne ya ishi saeed ya tashi ya rafi ya barshi. [9/14, 1:44 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/22, 6:53 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣0⃣ gefen mom kuwa events kusan kala 5 suka shirya kuma ko wanne da ankonsa, kuma ko wanne na kece raini, designers aka nemo dan kawai su tsara kayan da ango da amarya zasu saka a kowane event, sun kashe nera kamar su ke qerata amma mom gani take kamar batayi komai ba. Ameerah kuwa tare suke da kausar kullum da yake sunzama best frnds, kai bakace matar yayan kausar bace, yauma tare suke sunje skul sun dauko khadijah nasir barau qawar ameerah, domin su qarasa rabon invitation cards duk da ameerah tace bazatayi ba, amma kausar da khadijah saunce dole ne, dan baza'ayi biki ba qawayen amarya ba, bayan sundawo ne kausar ta tsaya da mota bakin titi, tafita ta tsallaka ta kar6o kayan dinkinta a wani shago, qishin ruwa ta dami ameerah tace khady bari na tsallaka shagon chan na kar6o ruwa wlh qishi ke damuna, khadijah tace bari na kar6o miki kar amaryarmu tasha wahala, ameerah tace bakomai jira kawai yanzu zandawo dama inason in miqa qafa ta fita ta tsallaka titin. Bayan ameerah ta kar6o ruwan tasha ta juyo da roba daya zata kauwa khadijah da ke mota, hakan yayi daidai da fitowar kausar shago, mota taga tayo kan ameerah da gudu, kiranta ta dingayi amma ina, kafin kausar ta iso, motar ta riga ta qaraso, da qarfi ta kwashe ameerah sai da tayi sama-sama ta fado, sai ga ameerah kwance a jini bata ko motsi. Wata qara kausar tayi wadda duk mutanen da ke wurin hankalinsu ya dawo gunta, iya qarfinta take gudu, ta tunkare motar da ta kade ammeerah, husnah ta hango a mota tana murmishin cin nasara, a ranta tana fadan ai dama ba wanda ya isa ya rabani da abunda nakeso duniya, kuma ya zauna lfy, yanda kika rabani da khaleed nima na rabaki da duniya. Kausar taga tayo kanta gadan-gadan taja mota da gudu tabar gun, kankace kwabo wuri ya cika da jama'a, da qyar kausar ta kutsa girgiza ameerah take ta tashi amma ina, bata ko motsi tayi facha-facha cikin jini, jama'a ne sukecewa akaita asibiti kausar tace su taimaka mata plz ga mota chan, a saka ameerah, haka akayi kuwa suka nufi mota inda khadijah ta dasqare wuri daya tama kasa motsi da taga abunda ya faru, saida aka bude qofa aka saka ameerah sannan ta motsa, kuka take gwanin tausayi tana jijjiga ameerah, its my fault duk laifina ne da naje na soyomiki ruwan, kausar kuwa kasa driving tayi coz hannunta qyarma yake, wani da ke taron ya kar6i key yaja motar, sai asibitin USMAN DANFODIO TEACHING HOSPITAL dake sokoto, emergency aka wuce da ita direct, da yake asibitin sunsan kausar da kuma waye ubanta shiyasa ba'a sha wahala ba aka kar6eta. [11/22, 8:58 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣1⃣ Kausar ta kira mom cikin tsananin tashin hankali, mom kizo asibiti husnah ta kashe ameerah, wlh mom bata motsi, mom da tashiga rudani cikin 'yan mintuna takasa ta6uka komai, sai yawo take a tsakiyar parlour, alhj ne ya sauko, Aisha lfy kike kuwa, mom sai fadin take shikenan ta kashemin ita, alhj ya rude ya kasa fahimtarta, girgizata yayi wai aisha meh yake damunki, kuka tafara mai tsuma zuciya, alhj husnah ta kade ameerah da mota suna asibiti, kuma wlh tace ameerah bata motsi, alhj yace dauko mayafinki mutafi asibitin, ki nitsu ba abunda zai sameta inshaAllah, kasa daukowan tayi alhj da kansa ya sakawa mom hijabinta yaja hannunta kamar qaramar yarinya suka fita, daidai nan khaleed ya fito waje, alhj yace son kazo muje asibiti cikin rashin fahimta khaleed yace meh zamuyi a asibiti? Dad yace muje kaga ko mene, suka shiga mota, kausar dad ya kira, ya tambiyeta suna ina? Cikin tamasa bayani, khaleed dama tin fadansu da salmah ya riga ya fita hayyacinsa duk ya birkice, tsananin tashin hankalin da mom ke ciki yasa bata lura da yanayinsa ba. Ameerah kuwa likitoci biyar suka duqufa kanta, suna qoqarin ceto ranta, isowar su khaleed keda wuya, doctors na fitowa, suka nufi gunsu, wani doctor ke musu bayani, sunyi iya qoqarin su, sun tsayarda bleeding din da ameerah keyi, amma kuma tana buqatar qarin jini na gaggawa if not zata iya rasa ranta, haj ta rusa kuka da su kausar duka, khaleed kuwa tsaye yake kamar hoto dan baigama fahimtar meh ke faruwa ba, gun kausar ya nufa kausar rungumeshi tayi, yaya husnah ta kashemana ameeranmu, khaleed hannu ya dora akai, inalillahi wa inna ilaihi raji'un yaketa fada, mom its all my fault da ban amince zan auri ameerah ba da haka bata faru ba, m so sorry ameerah, mom taje ta rungumeshi son karka damu ba abunda zai faru da ita, wata nurse ce ta fito cikin masifa take magana angayamuku patient dinku tana buqatar jini cikin gaggawa, kun tsaya kuna kuka, zaku iya rasata in d next 30 minute idan kukayi wasa, alhj ne yace ku kira famlynta cikin sauri, haj tasa kiran mama ta daga amma mom takasa magana, alhj ne ya kar6a yace kuzo asibiti uduth yanzu cikin gaggawa, ameerah ta hadu da accident. [9/14, 1:46 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/22, 9:04 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣2⃣ mama tayi lu qasa jiri ya kwasheta, mutanen da suke daki tareda ita ne sukayi kanta lfy maryama? Kuka ta fara ku kiramin aliyu yazo mutafi asibiti, ameerah tayi hadari, take dakin kowa jikinsa yayi la'asar, suhaila ce tayi waje da gudu, ta kira aliyu tanata faman kuka, yaya aliyu ameerah tayi accident zumbur suka miqe da mustafa da yake taredashi, dan tinda aka saka bikin ameerah yaya mustf ya shiga tashin hankali, aliyu ne ke kwantar masa da hankali har ya fara dangana, mota mustf ya jawo suka shiga, mama ta fito ana riqe da ita kan jirin da ke dibarta, suka shiga mota sai asibiti. A asibiti kuwa khaleed ne yabi nurse din yace, jininsa blood group type O+ ne zai iya bawa kowa jini, a dibi nasa a sakamata, nurse din tajashi lab aje a gwada lafiyarsa, bayan anyi test anga lfyrsa qalau, ta wuce dashi gado aka bashi daidai na ameerah, direct connection akayi da ameerah ba'a tsaya dibar jinin ba, daga jikin khaleed direct jikin ameerah yake shiga. Su aliyu ne suka iso wurin da ka gansu kasan suna cikin tashin hankali, da isowarsu direct alhj lab yace su nufa ayi test, nurse din ce tafito tace ae already anfara sakawa patient din jini, saidai kuma zasu iya zuwa suyi test din, incase idan jinin da aka samu bai isa ba, alhj yace wai ina aka samu jinine? kausar tace yaya khaleed dad kasan O+ yakeda zai iya ba kowa jini, mom taji dadi har a ranta, sai mama take ba haquri da take darzar kuka, Aliyu da mustf kuwa suntafi ayi test din jininsu a lab. Dad ne ya sulale yaje ya samu nurse din, wai ta cire jinin yaronsa kar ta kashe masa yaro, nurse tace ae sunsan adadin jinin da zasu diba yanda bazai cutarda khaleed din ba, dad yace atafau shi sai ancire ko yayi qararsu, tinda ga en uwan patient din sunzo sa bata jinin, nurse tace toh ya bari taje ta duba results din blood test din su aliyu idan yayi match tazo ta cire na khaleed din, alhj ya dake yanzu zata je ta cire, shi sam bazai yarda ba, kafin taje ta dawo jinin dansa zai qare, dole nurse din taje ta cire tranfusion din daga jikin khaleed, khaleed yana mamaki har jinin ya isa ne bayan sunce ta rasa jini da yawa? Nurse tace masa anason patient din ta dan huta kadan kan acigaba da saka jinin, khaleed yace shikenan ya fita waje. Blood test dinda akayi jinin Aliyu daya suke da na ameerah duk A+ ne, aka fara diban nashi, na yaya musty ma O+ ne kamar na khaleed shima za'a dibi nashi gora daya a ajiye incase. Ameerah ce ta fara fisge-fisge bayan ancire mata qarin jinin, doctors sukayo kanta masifa suka dingayi meh ake jira ba'a fara saka mata jinin ba? Khaleed ya gayamusu abunda nurse ta gaya masa, take wani doctor ya kwasheta da mari tana wasa da rayuwar patient, dole su dauki mataki kanta, ita kuwa tasan za'a iya korarta, take ta fadamusu abunda ya faru itada dad, yaya mustf ne ya daka masu tsawa enof, ameerah is fighting 4 her life kuntsays kuna rigima, yace a fara zuba nashi kawai, ya basu result din test dinda akayi, doctr ya duba yaga lfyrsa qalau take yace mustf ya kwanta ya jona jinin, daga jikin yaya musty zuwa na ameerah. [11/22, 6:10 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣3⃣ khaleed da hajiya suka yiwa alhj kallon tuhuma, yace son na damu dakaine banason wani abun ya sameka, mom tace amma alhj banta6a sanin bakada tausayi ba sai a yau, da kausar ce a kwance nan zaka hana khaleed ya bata jini ne? Ko zaka hana mijinta ya bata jini? Mama tace haj kidaina 6ata ranki, ameerah ta riga tasamu jini, kuma ko na mustf bai isa ba ga na aliyu nan, ba wani abu wlh tinda ba'a daura auren ba ma haryanzu alhakin kula da ameerah yana kanmu, kuma haj bazanta6a dana sanin baki ameerah ba, dan nasan son da kike mata ko ni iya abunda zan nunamata kenan, mom ta share qwalla amma mune sanadin faruwar hakan gun ameerah, dan da alhj bai maqalawa khaleed wannan jarababbiyar yarinyar ba, da duk hakan bata faru ba, mama tace haj qaddara ce kawai ayi haquri kawai. Kausar ce ta matso amma mom bazamu qyale husnah ba dole muyi maganinta, mom tace sosai kuwa alhj ko bakayi wani abun ba ni wlh bazan qyaleta ba, doctor ne yazo yace patient dinku ta samu isashshen jini, kuma she is stable now, saidai kuma sanadiyar buguwar da kanta yayi tayi dogon suma, she is in comma right now, amma muna tunanin is temporary ko da nan da 3 days ne zata farfado, yanzu zamuyi shifting dinta zuwa ICU, u can all see her there, hamdala kowa yayi tareda ajiyar zuciya, da fatar Allah ya ba ameerah lfy. Saleem ne ya kira kausar yana azo a tafi dashi, shine kausar ta gayawa mom, mum tace shi saleem bai tashi dawowa ba sai yanzu, tun kwana baya muke especting dawowarsa, sai yanzu ana crises zai dawo? Alhj yace ai kuma yariga ya dawo, ina kausar tazo suje da khaleed su daukoshi airport din, amma aka nemi khaleed aka rasa. [9/14, 1:50 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/22, 8:41 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣4⃣ khaleed kuwa yana fita daga asibitin police station ya wuce, dama comissioner of police abokin dad dinsa ne, yau sai ya koyawa husnah hankali, bazata qara gigin qoqarin kashe ko waye ba a duniya, koma waye ubanta a qasarnan sai ya daureta. Kiran saeed ya shigo wayarsa, buddy where are u? Yace ina asibiti kai kana ina? Yace ina police station yanzu gidan deputy governor zai wuce, he'll teach dat stupid girl a lesson, mota saeed ya shiga da sauri, mom, dad da kausar suka bishi, ya kama hanyar gidan deputy governor yasan halin abokinsa idan yayi fushi ba sauqi, khaleed kuwa da yayiwa comissioner bayani motar en sanda 3 aka hadashi dasu direct sai gidan deputy governor. Deputy na zaune da matarsa suna shaqatawa yafara ganin police na diro masa gida kamar daga sama, cikin tashin hankali ya tashi, ya daka musu tsawa wannan wanne irin rashin hankali ne, zasu fado masa gida kamar police head quater, khaleed ya shigo yace alhj kafito da husnah batareda 6ata lokaci ba dan she must pay 4 her crime, deputy cikin rashin fahimta yake tambayar what crime, meh 'yata tayi? Inspector yace ana zarginta da qoqarin kisa, ta kade matar da khaleed zai aura da mota dazu, kuma ta gudu wanda ya tabbatar da cewa tayishi ne da gan-gan, haj ra miqe dis is rubbish, husnah bata qasar nan tin jiya taje america ta ya zata kashe mutum yau? Inspector ya bada umarni afara searching gidan lungu da saqo kar abar ko ina. Bayan sun duba ko'ina sun tabbatar bata gidan, khaleed ne yaje ya chakumi wuyan deputy governor ya shaqeshi, wlh duk inda husnah take ka fito da ita kafin kaima na qarasaka, daidai nan su saeed suka shigo, tsawa dad ya sakawa khaleed akan ya saki deputy governor, amma ina daqyar saeed da wasu police suka qwaceshi, idon nan sunyi turu-turu sunyi ja, cewa yake alhj khalipha ka fitarmin da mahaukacin yaronka a gida, nagodewa Allah da 'yata bata auri mahaukaci ba. Daidai nan wayar matar deputy governor tayi ringing, cewa tayi ga ma husnah din nan ta kira dan ta lura number america ce, Inspector yace tasa wayar a hands free, ta daga muryar husnah ce kuwa, haj tace husnah ki fadamin gaskia, ke kikayi qoqarin kashe matar da khaleed zai aura? Husnah tace common mom ai kinsan ni idan bansamu abu ba ba wanda zai samu, kawai na nunamuku na haqura ne dan kawai ku dena damuna, but d truth is haryanzu ina son khaleed, dad yace amma husnah jiya kikabar qasar nan, taya akayi hakan ta faru? Dariya tayi dad kai kamar ba dan 9ja ba? Ae visa ta yau ne da yamma i just landed, kawai na cemuku jiya ne karku 6atamin plan, mom just tel me wannan ameerah din ta mutu nafara celebration ta fashe da dariya, mom tace amma Allah ya tsinemiki albarka husnah, deputy governor yace daina tsinema 'yata, ga tsinannen yaron da zaki tsinewa nan duk laifinsa ne, now i lost my daughter, haj zubewa tayi qasa tans kuka gwanin tausayi, Allah ya isa tsakanina dakai alhj duk kai ka lalatamin ' ya ka nunamata, duk abunda takeso zata samu shiyasa batasan tayi tawakkali ba, gashi ka juyen mahaifa bare na qara haihuwa, ni wlh alhj ka cuceni, mom ce ta tasheta tafara bata haquri. Deputy governor tsawa ya saka a fice masa daga gida, Inspector yace your excellency inaso kasa a ranka ko yaushe 'yarka ta dawo qasar nan sai mun hukuntata sannan suka fice. A mota kuwa kowa shiru yana jimami, dad ke nasawa a zuciyarsa yaso ya tafka babban kuskure a rayuwarsa amma ya gode Allah da ya ganar dashi da wuri, kudi ba su ke sa yaro ya samu kyakkyawar tarbiya ba, dan ga husnah duk gatanta da kudin mahaufinta takasa samun tarbiyya, shi ya godewa Allah nashi yaran Allah ya shurya su amma dan sunyi dacen uwa ta gari ne, shima daga yau bazai qara shiga rayuwar yaransa fa zaimusu fatan samun abokan rayuwa na gari, ga alama kuwa khaleed yayi dace dan yarinyar ya lura tanada kamun kai da nutsuwa, tsanar da yayiwa talaka yasa yaqi yarda da hakan, amma not anymore da haka suka isa gida kowa yayi side dinsa. [11/23, 12:02 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣5⃣ da safe dad ya samu mom tana shirye-shiryen zuwa asibiti, yace aisha magana nazo muyi, haj ta zauna, dad yace a ganina dan yarinyar na batada lfy bai kamata a janye daurin auren nan ba, haj mamaki tayi dan batayi tsammanin wannan maganar tafito daga bakinshi ba, amma tayi matuqar farin ciki, hakane alhj a daura auren kawai idan yaso daga baya ayi bikin, tace bari na kira son namasa bayani, dada yace niko na lura yaron nan kamar ba natsuwa a tare da shi, ki kira wannan abokin nasa shi ya shirya komai, mutanen da sukaji labarin accident din ya gayamusu still akwai zancen daura aure, wanda baijiba ma shikenan. Hakan akayi kuwa mom takira saeed ta masa bayani, sannan tace shikenan idan sunje asibiti tayiwa maman ameera bayani ta sanar a gefenta. Saeed da ya tashi dakin khaleed ya nufa, ya sameshi yayi wani zugum duk ya wani kode yayi rama, saeed ya ta6ashi aboki wai meh ke faruwa ne? Khaleed yace aboki kafi kowa sanin abunda ke faruwa salmah taqi saurare na, yanzu kuma ga abunda ya faru ga ameerah, kuma duk ni naja mata, amma is not too late da Allah ya tashi kafadunta zan warware wannan auren da muka shirya, saeed yace lallai kuwa ni zantafi, zanje asibiti na duba ameerah, khaleed yace ka jirani mutafi a tare yafito suka wuche. A mota kuwa shiru sukayi kowa da bikin zuciyarsa, saeed na nasawa a ransa ba sai ya gayawa khaleed zancen daurin aure gobe ba, yaji yana qudurin janye auren, idan ya gayawa su mom gaskia, abun bazaiyi dadi ba, gwanda ya barshi kawai, beside ma salmar da yakewa fighting ya lura, ba wani damuwa tayi dashi ba, tun farko da tana sonshi bazatace yayi keeping r. Ship dinsu secret ba, duk da yake iyayenta da na khaleed aminaine, akan wani uzurin karatu, gwanda khaleed ya auri ameerah kawai, dan yana zargin ameerah son khaleed take, da bazata iya yimasa haka ba, duk da yake bai tabbatar da zarginsa ba, amma yana fatar haka ta kasance. Saeed ya katse shirun yace khaleed meyasa ba'a nemeni ba jiya da aka kawo ameerah asibiti? Duk da kasan ina asibitin, khaleed yace aboki nikaina bansani ba mom da dad kawai suka jani asibiti, daz where i found out everything, beside ma kaida kake likitan mata meh zaka iyayi? Saeed yayi dariya wa ya gayamaka gynocologists basu iya komai ba sai aikin mata? Dariya sukayi da haka suka isa asibitin. [9/14, 1:54 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/23, 3:24 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣6⃣ koda suka shiga gun da ameerah take, mamace da aliyu da su suhaila kowa yayi zugum ba mai magana, suka duqa suka gaida mama ta kar6a da dan sakin fuska, sukace ya mai jikin? Mama tace to alhamdulillah za'ace amma bawani chanji har yanzu, saeed yace doctor ya dubata? Mama tace eh yace qalau take kuma anasa ran ta farka a kowanne time. Mama tace khaleed dafatar ba wannan abun kasa ranka ba naga duk yanda ka yamutse jiya kawai? Shidai ya sadda kai a qasa a ransa kuwa cewa yake dama damuwar da ke damuna akan hatsarin ameerah ne kawai, saeed kuwa sai kallonsa yake, sai yanzu ya qara ganin yanda abokin nasa, yayi rama yayi duhu, girgiza kai kawai yayi, a ransa yace dole na fito dakai daga wannan jarababbiyar soyayya, bari ma na tashi na qarasa rabon katin aure, mama tace saeed ka riqa bawa abokinka baki kar damuwa tamasa illah, daidai nan su mom suka shigo da kayan breakfast, mom tace son ka kwantar da hankalinka ba abunda zai samu ameerah, kacigaba da addu'a kawai ka saki ranka, kada kai kawai yayi suka miqe, saeed yace mom mu zamu tafi, sai munshigo anjima, bandir din kudi khaleed ya ajiye koda ana buqatar wani abun suka fice. Mom tace salim ga ameerah how i wish kadawo kunsan juna kan haka ta faru, gashi kace jibi zaka koma, murmushi yayi mom she is preety, dukda hakan take i know zata kula da yaya khaleed sosai, kuma mom kinsan daurin auren broda kawai yasa na dawo if not sai next session, salim yace ina yaron da kikace zamu tafi tare? Mom tace kaga ni nama sha'afa wannan tashin hankali banma gayawa aliyun ya shirya, angama masa komai ba, tafiya kawai ta rage, mama ta ta6o aliyu da ya shiga wani yanayi, firgigit ya motsa, tace aliyu ga salim ku gaisa shine zaku tafi egypt din tare, hannu ya bashi suka gaisa, salim yace i'm happy nima zansamu danuwa a chan, sai kafara shiri dan jibi zamu wuce bayan andaura aure gobe. Aliyu ya kalli mama har suna hada baki daurin aure kuma, mom tace eh maman ameerah, ae dan yarinya ta samu hatsari bazaisa ace za'a fasa daura aure ba, za'a daura auren a gobe idan yaso biki a daga har ta samu sauki, mama tace haj kina ganin haka zaiyi kuwa? Mom tace ba wata matsala wlh, ko da abunda kike tunani ne? Mama tace ba komai amma dole a sanarwa da kawunta mom tace bakomai alhj zaimasa bayani da kansa, mama tace toh Allah yasa hakan shine alkhairi akace amin. Salim ne ya miqe toh toh ni zanwuce mom sai na dawo, hannu ya bawa aliyu danuwa kagama shiri fa kan jibin tayi, Aliyu ne yace nifa ba inda zani, salim dawowa yayi ya zauna, meyasa dan uwa? Komai fa angama karkamin haka mana, aliyu yace taya za'ayi natafi nabar er uwata a haka? Yasa kuka, mama tace cikin fada, da yake zaman da zakiyi shi zai hanata mutuwa idan Allah ya tashi kar6ar ranta, ko kuma shi zaisa ta warke, mom tace kima daina fadan haka ba abunda zai samu 'yata, kubarshi kawai idan bai amince ba, yaje next session, mama tace zuwa kam yagama zuwa saidai idan bana raye, baza' ayi kashe kudin banza ba, kuma itama er uwar tashi bazataso yafasa karatu saboda ita ba, dan haka katashi ka fice kafara shiri, Aliyu ya fita a fusace salim ya bishi ya lallasheshi hakan yayi daidai da shigowar kawu da iyalansa. [11/23, 4:33 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣7⃣ Bayan su kawu sun zauna ne, angama gaisawa budar bakin saratu mom nikuma anya wannan ba gawa muke tareda ita ba? hjy asabe tace nima fa haka nagani, mutum kwance haka baya ko numfashi ace yana raye, da ma suncire mata wanna qarafunan a binneta kawai. Kausar da ka zaune raku6e gefe tinda suka zo batace kanzil ba abun duniya ya isheta, ta miqe a fusace ke ki iya bakinki fa, ni er uwata da ranta ba abunda ya sameta, kunfi likitocin iya aikine da basusan ko tanada rai ko ta mutu ba? Mom tace kausar ya isa, amma hjy bai kamata ku furta haka ba, hjy asabe tace Allah ya baku haquri. Mom tace alhj gwanda da kukazo dan koma baka zoba alhj zai sameka a gida, zancen aure ne nikeson gayamaka, hjy asabe tayi saurin katseta ai munsan dole kuce kun fasa, mutum a haka munsan ko bata mutu ba dole ta nakasa, toh meh za'ayi da nakasashshe dama? Mom cikin 6acin rai tace wai ke wace irin macece ne? Bakinki bazai fadi alkhairi ba ne kam? Toh ni ameerah ko ta nakasa ba qafa ba hannu bazaisa mu gujeta ba, bare kuma doctor ya tabbatar mana ba wani nakasa a jikinta, akai ne ta bugu shiyasa har yanzu bata farko ba, saratu tace hauka zatayi kenan? Kawu ya daka mata tsawa, saratu kifita kibar dakinnan kan ranki ya 6aci, tafita tana kukan shagwa6a, mom tace alhj zancen daurin aure gobe yana nan bai chanjaba, alhj yayi jim sannan yace toh aini har na sanarwa mutanena anfasa, mom tace lokaci bai qure ba, kasake gayamusu daurin aure yananan, hjy asabe taja tsaki idan kuma yarinyar ta mutu bayan andaura auren fa? Mom tace wannan ba matsalarki bace, ko mutuwa ameerah tayi a gobe bayan andaura aure, zamuyi farinciki ta rasu tareda auren dana khaleed, barema da izinin Allah ba abunda zai samu ameerah, haj asabe baqinciki taga zai kasheta ta fice daga dakin. Bayan tafita ne alhj yace hjy kuyi haquri, haka nike fama dasu, zantafi yanzu na sanarwa da mutane Allah dai ya tashi kafadunki ameerah ya matse qwallan munafunci ya fice. [9/14, 1:58 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/23, 4:53 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣8⃣ Bayan fitar kawu mom tace wai wannan wace irin macece, da ita da 'yarta? Mama tayi murmushin takaici, kinsan haka Allah yake halittr bayinsa, wasu mutane basason suga alkhairi gun wasu sai kansu, mom tace Allah ya sauwaqa, sallamar da akayi ta katsesu matar deputy governor ce ta shigo, sai shigowa ake da carton carton na lemuka da ruwa, tashigo ta tambiye mai jiki, akace mata da sauqi, mama tace saidai hjy kiyi haquri ban wayeki ba, hjy ta matse qwalla ta girgiza kai, ina baqincikin da ba alkhairi ne ya hadamu ba, nice uwa marar sa'a da 'yarta tayi yunqurin kashe' yarki sai ta fashe da kuka, dan Allah hjy kuyi haquri ta sauka ta riqe qafafun mama, mama ta share qwalla bakomai qaddara ce bata wuce ranarta, saidai muce Allah ya kiyaye gaba, check ta ciro ta miqawa mama na 2 million, duk da nasan wannan bazai siyowa 'yarki lfy ba, kiyi hakuri ki kar6a dan Allah ba danni ba, mama tace kibarshi wlh bakomai, bama buqatar komai, hjy tace idan baki kar6a ba zandauka baki yafemin bane kuma wannan laifi bazai bazai ta6a barina na zauna lfy ba, idan na tuna abunda' yata tayi kuma ni banyi komai akai ba, mama ta kar6a tayi godiya sannan suka fice. Kawu kowa da suka fita masifa ya dinga yiwa haj asabe da saratu waisu bakinsu bazai iya shiru ba? Sai sun bata masa plan susa yakasa samun komai, hjy asabe kuka tasa wai ita wlh tasan asiri aka masa dan yanzu baya qaunarta da ita har 'yarta, shidai girgiza kai kawai yayi, a ransa yana danasanin auren mace mai qwaqwalwar kifi irinta, gashi ta haifa masa ' ya irinta, kansu baya ja, da haka suka isa gida. Khaleed kuwa ana wurin rabon invitation card batareda yasan nashi ake rabawa ba, dan saeed yace masa na abokin aikinsu ne, bayajin dadi shiyasa yace ya taimaka masa, duk inda sukaje saeed shikadai yake zuwa, yabar khaleed a mota, wannan kenan. [11/23, 5:39 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 7⃣9⃣ Yau takama ranar juma'a ranar da za'a daura auren khaleed da ameerah, shiga da fice a gida ana shirye-shiryen daura aure, amma khaleed baimada lbr shi ya ajiye tinda ameerah na asibiti ba wani zancen daura aure, Allah dai ya bata lfy ya warware mata wannan fake auren, shima ko zai samo natsuwarsa. Salim ne yafito yaci uban ado kamar wani dan sarki ya sauko parlour, kausar ta fara shewa wannan wankan yayi bro dole kabani poster tazo suka dauki hotona, sai ga mom da dad sun sauko suma sunci uban ado, kausar ta sheqa ta rungumosu, akayita daukar pictures, salim yace dad uban gayyarfa bai fito ba kar ya 6atamana lokaci, bari naje na fito dashi mom tace kaje ka fito dashi, ya fito ya nufi side din khaleed, qwanqwasa qofa yake, amma khaleed na kwance a daki har wata fever yakeji, masifa yafara yiwa salim ya daina qwanqwasa masa qofa, haka yayi daidai da zuwan saeed wurin, da kuma fitowar su dad, saeed yace salim kaje ku tafi da su dad kawai zanzo da khaleed din, suka shiga motocinsu suka wuce. Qofa ya fara duka buddy kazo ka bude qofar mana, khaleed haka ya taso ya bude qofar ya koma ya kwanta, saeed yaje ya ta6ashi yaji zafi gau a jikinsa, tashi yayi ya koma mota, ya bude jakaraa ta aiki allura ya dauko da wasu tabs, khaleed na kwance ba zato ba tsammani, Allura kawai yaji an soka masa, saida ya riqe gado da qarfi, ? yace aboki wlh ka cika dan iska, da kajimin ciwo fa? Saeed yayi dariya ai nasan kai jarumi ne, tadhi kasha tabs dinnan ka tashi mutafi, khaleed ya kar6a yasha yace, bt ni ba inda zani dan bakada tausayi bakaga yanayin da nike ciki ba ne? Saeed yace idan ma nabarka a haka ba sauqi zakaji ba, nasan ba aikin da zakayi sai tunanin salmah, dan haka ba wani dogon excuse ka tashi kawai ka watsa ruwa, mutafi ka rakani daurin aure, khaleed yace auren wa kuma, saeed yace mai katin da muka raba jiya, ae yaune daurin auren, buddy katafi kawai bazan iya zuwa ba, miqeshi saeed yayi ya tura toilet, na baka 15 minute kafito, ba barin da zammaka naje nadawo nasamu kayi mushe a daki. Khaleed yace ok u win, ya rufe toilet din ya fara wanka, kafin ya fito saeed ya fito masa da kayansa da ya dinka masa dan kawai daurin aurensa, yana fitowa ya goge jikinsa kawai saeed ya miqamasa kayan yafara sakawa, saida yasa saeed ya miqo masa babban riga da tasha aikin kamar sarkin musulmi, khaleed yace ar u mad? Ni ango ne da zansa wannan kayan? Saeed yace masa ai theme din daurin auren ne haka, nima bakaga ita nasaka ba, khaleed yace but naka is more simpler dan mine, ni ae za'a dauka nine angon, saeed yace ba wani duk salon kar kajene, ai ango ma kalar kayansa daban mune zamusa farare, kuma ma ai kowa yasan kai babban mutum ne, khaleed ya ta6e baki, ya zura rigar saeed ya dora masa hula, sanna ya fidda kwalbar turare ya fara yimasa feshi, take ko ina ya biye da qamshi, khaleed saida ya kar6e kwalbar turaren yayi wurgi da ita, wannan ae haukace wlh Allah zance nafasa, saeed yace Allah ya baka haquri nafiso ne, da munfasa taro asan munshigo, khaleed ya hararesa to takara zamuje e yaja tsaki ya fito, saeed yace Allah aboki banta6a sanin kai maikyau bane sai yau, naji dai anata fada amma sai yau na yarda, fararen takalmi ya ajemasa ya saka, khaleed sai qyalli yake komai fari, kamar wani sarki mota ya shiga ya kame, kaxo mutafi b4 i change my mind, saeed yace sorry your excellency a farar sabuwar motar chan ta dady zamu, khaleed yace frnd motar dad fa kace, makulli ya nunamasa don't u worry, dady ya bamu aro, tsaki yayi ya fito motar saeed suka nufi motar dady suka shiga, sai qyalli suke kamar taurari dan shima saeed ba bayaba wurin kyau, saeed yaja mota suka nufi wurin daurin aure. [9/14, 1:59 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/24, 8:02 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣0⃣ Wurin daurin auren kai tsaye saeed ya nufa, da yake wani qaton wuri ne da yake bayan gidan kawu sheshu, ya kama dan kawai daurin auren dan yanada yaqinin daurin auren zai tara manyan mutane dan yasan dadyn khaleed babban mutum ne a jahar, wurin saeed ya nufa kaitsaye khaleed kuwa baisan wurin ba dan haka, baiyi zargin komai aransa ba, koda suka isa wurin dubunnan mutane sun taru, ciki kuwa harda gwamna jahar, da tawagar sarkin musulmi, jan hannunsa saeed yayi suka kutsa taron, maroqa sai biyarsu suke suna musu kirari, duk wanda ya hangosu sai tasowa suke suna miqawa khaleed hannu, anamasa congratulations, khaleed yaga tarin abokanansa a wurin sai tsiya sukemasa, shidai kansa duk ya qulle, wai meh yake shirin faruwane, saeed ya nufa da yashige taro yana musu godiya anata dariya, da niyyar ya jawoshi, yamishi bayanin abunda ke faruwa, hannunsa yaji anjawo, dad ya gani, kafin yagama mamaki, dad yaja hannunsa, son ina kajeni kanaso kasa a makara, tindazu liman ku kadai yake jira, afara daurin aure, jansa yayi sai wani qayataccen daki inda taron manyan mutane yake, duqawa khaleed yayi yafara gaidasu, suna tayashi murna tareda sa masu albarka, kafin khaleed ya ankara sai ji yayi ana tambayar waliyin ango da amarya, gwamnan jaha ne ya wakilci waliyin ango, shi kuma kawu na amarya, su kawu sai. Washe haqora ake yau shine a layin manyan mutane haka lallai haqarsa takusa cimma ruwa. Khaleed dai yaje dogon tunani shifa baigane abunda ke faruwa ba, meh dad da kawu keyi a wurin daurin auren abokin saeed? Ko dama diyar kawu ce zai aura shikuma shi ya gaygato dady? Khaleed bai ankara ba sai ji yayi ana sanarwa a loud speaker, ALHAMDULILLAHI ANDAURA AUREN KHALID DA KHADIJA AKAN SADAKI NERA DUBU DARI. Khaleed ya qara maimaitawa khaleed da khadijah kuma? Wai shin meh yake shirin faruwa idan nine khaleed khaleed toh waye kuma khadijah? Na shiga 3 wace khadijar dady ya auramin? Khaleed bai ankara ba akafara bashi hannu anamasa congratulations, shidai duk ya sandare saeed yake ta wara ido ya gani dan shikadai zaimasa bayanin abunda ya faru, bai ankara ba sai hasken camera ya fara gani daga ko'ina daukar hotunansa ake, jama'a sai tsayawa suke, ana daukar photo, chan ya hango saeed a cikin taro, cikin sauri ya wuce kamar mai son ya tashi sama, jama'a kuwa sai biyarsa suke, hannun saeed ya riqo, ya riqeshi gam danma kar ya kufcemasa, abokansa suka matso ango kasha qamshi tindazu muke nemanka, sai tsayawa suke tare dasu ana daukar hotuna, murmishin yaqe kawai yake musu, jan saeed yayi da qarfi sukayi gefe, chakumarsa yayi saeed kagayamin da wacce khadijar aka dauramin aure, saeed ya janye hannunsa daga chakumar da yamasa, just calm down my man, cikin tsawa khaleed yace how can i calm down, just explain dis, saeed ya lura zai tara musu jama'a dan duk wanda yake kusa dasu saida ya waigo Jansa saeed yayi suka nufi mota ya turashi gidan baya shima ys bude dayan side ya shiga, khaleed ya sake chakumarsa banta6a tunanin za'a hada baki dakai a lalatamin rayuwa ba, kasan yanayin da nike ciki kasan alqawarin da yake kaina, taya za'ayi ka yarda da wannan auren? Kuma da wadda banmasanta ba, yafara share hawaye. Saeed haushi kamar ya kasheshi, janye hannunsa yayi daga riqon da yayimasa, khaleed meh kake tunani? Ni zansaka hannu a lalata rayuwarka? 4 goodness sake aure aka dauramaka ba, ba life imprisonment aka maka ba, ko yanzu almakashin datse igiyar auren a hannunka take, zaka iya zuwa ka kar6i speaker kayi sanarwa, kace ka saketa dan bakason auren akwai alqawarin wata a kanka, kuma 4 your own information ameerah itace khadijah asalin sunanta kenan, bude mota yayi ya fito, malam kafito kayi sanarwa kan jama'a su watse, tinda farincikin budurwarka yafi na iyayenka muhimmanci, ya rufomasa qofar da karfi ya wucewarsa cikin 6acin rai. [11/24, 3:17 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣1⃣ khaleed zugum yayi a mota, sannan ya sauke ajiyar zuciya, tinda ameerah ce aka auramasa da sauqi, tinda akwai hanyar warware abub cikin sauqi, dan dama da yarjejeniya a tsakaninsu, itama ba so take ba, qwanqwasa masa mota yaji anayi, abokanensa ne, ya washe haqora, suko suka fara masa tsiya, ango guduwa kakeson yi gun amaryarka? Ae dole ka haqura dan mu da kaika yau sai dare, shidai fitowa yayi yana musu dariya, wanne daren bayan amaryar tawa tana asibiti, wani daga cikinsu yace ohh no wonder muka ganka haka yau ba nishadi, sai gudun mutane kake, karka damu tinda andaura zata miqe ne, Allah ya bata lfy akace amin, jansa sukayi akachigaba da daukar hotuna, daga nan aka shiga motoci aka wuce giginya coral hotel domin chin abinci, dan wasu baqin ma nan aka musu masauki. Khaleed sai wara ido yake yana neman saeed, amma da ya hangoshi ya nufi inda yake, saeed sai ya kauce masa, yasan fushi yayi, amma shima baidace sumasa haka ba, ya dace a sanarmasa amma yasan duk plan din saeed ne, dan ya gayamasa zai warware auren da ameerah ta samu sauqi, shiyasa yamasa haka, da haka har aka gama liyafar, akayi addu'a aka watse, amma khaleed ko loma baisa a bakinsa ba, duk inda ya nufa jama'a tareshi suke, har yagaji. Wani abokinsu da ke tare da khaleed ne ya hango saeed ya qwalla masa kira yazo, cemasa yayi sunaso suje su duba matar khaleed a asibiti, saeed yace bakomai mutafi, khaleed ya jawo hannunsa ya riqe gam, yanata so ya sakeshi yaqi, cemasa yayi amma malam kasan kai ka janyoni anan, kuma kanaso ka gudu ka barni, saeed yace kai baka iya motar bane? Wani abokinsu yace kaima saeed kasan ango bazai ja mota ba, yacemasa toh ai sai kajashi kai, yayi yunqurin wucewa khaleed still ya riqeshi yace kuje ku shiga motocinku, ga motar da zamuje a chan, kowa ya juya zuwa motar da yazo a ciki, saeed yace khaleed ya haka? Ya kabari har kowa zaiwuce banji kafara sanarwa ba? Khaleed baicemasa komai ba yajashi sukaje mota, ya turashi driver sit shikuma ya zagaya ya shiga dayan side din 
saeed yaja motar. Khaleed yace saeed m sorry, amma kaima kasan abunda kukayimin baku kyauta ba, ae yakamata a sanar dani, saeed yace naga yanda mom and dad suka damu da ameerah, naga yanda mom keson ayi auren nan, sanda suka kirani sukamin bayani akan na cinye gaba da shirye-shiryen daurin auren ba dagawa za'ayi ba, amma sun lura da yanayin da kake ciki, basai na gayamaka ba dan zaka iya qin amincewa, sun dauka damuwarka da yanayin da kashiga duk akan ameerah na, niko nasan ba shi bane wannan salmar ce take wahalar dakai, har kake shirin fasa aure saboda ita, zanbarka ka ruguza farincikin iyayenka saboda wata mace da bata damu dakai bane? Shiyasa nayi maka haka dan nagane kariga kayi nisa a son wannan yarinyar, nidai shawarar da zanbaka Allah kabi a hankali da ba'a ba mace amana, ni nama rasa meh kagani a wannan salmah da ka liqe mata, idan kyaune ae akwai wa enda suka fita, kuma zasu so ka fiye da ita, hannun khaleed ya daga masa, ya isa aure dai anriga an daura kuma nace kayi haquri, amma ni bazan dauki cin zarafin salmah ba, i love her alot kuma i don't need any reason to do dat, saeed ya ta6e baki, kai kasani ayi dai mugani, idan tusa na hura wuta, da haka suka isa asibiti. [9/14, 2:02 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/25, 7:40 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣2⃣ Mama da mom ne zaune da kausar a dakin da ameerah take suna fira, mom kecewa yau wannan ranar ranace da yakamata ace kowa na farinciki, amma farincikin mu ragagge ne tinda ga halin da ameerah ke ciki, kausar tace mom wai nifa hankalina bai kwanta da zaman ameerah anan ba, gasgi suncemana nan da 3 days zata farfado amma har yanzu shiru, mom tace kamar kinshiga zuciyata kausar dadynku nike jira ya dawo anemi visa kawai a fitar da ita, daidai nan salim da aliyu suka shigo, mom tace angwaye har antashi daurin auren? Salim yace eh mom daga wurin liyafa ma muke duk an watse, yace mom nima na goyi bayan a fitarda sister ameerah waje kawai, amma kuma ina za'a kaita, Aliyu yayi sauri yace akaita egypt kawai, mama tayi murmushi wato Aliyu akaita egypt dan ka tare a gunta ka fasa karatun ko, akayi dariya, mom tace ae maman ameerah ba wani abu bane indai za'a samu visa egypt zuwa gobe ae sai sutafi gabadaya, shima dan ya damu da er uwarsa ne, yake fadn haka bawai wani abu ba, mama tace nidai ban goyi bayan akaita egypt ba dan nasan gunta zasu tare kawai, suda sukaje karatu, Aliyu ya so6are baki, toh ni mama angayamiki ko bamu tafi tareda ita ba zan iya karatun ne bayan nasan er uwata ba lfy? Mama tace kanka akeji kuma. Mom ta daga waya takira dad tamasa bayanin shawarar da suka yanke, yace perfect timing, ina tareda alhj salmanu kuwa zanmasa bayani yanzu, idan nazo sai na gayamuku abunda yace, dan zamu shigo tareda mai girma governor yanzu zai duba ita yarinyar mom tace toh shikenan sai kunzo, ta kashe wayar. Su saeed ne suka sallamah suka shigo, mum tace angwaye ne haka sukace eh, kusan su goma sha 12, suka duqa suka gaida mama da mom sannan suka tambiye mai jiki, aka gayamsu da sauqi, daga bisani suka miqe zasu tafi, duk wanda zai fita sai ya ajiye kudi kan gado suka fice kowa yana fadin Allah yaba ameerah lfy, saeed ne yafita rakasu shikuma khaleed na zaune wuri daya zurum, su dad ne suka shigo sallamah khaleed ya miqe ya basu wuri dan ganin manyan mutane, suka shigo suka duba ameerah wani malami da ke taredasu yayi ta zuba addu'a ana kar6awa daga bisani suka miqe, alhj salmanu yace hjy alhj yayimin bayani saidai zaku iya samun visa zuwa india a gobe itama ta mutum 3 kawai, kuma naga suma medical facilities dinsu suna da kyau, amma idan kunfison other countries din sai nan da zuwa kwana biyar, hjy tace a'ah wlh bazamu iya bari har kwana 5 ba, ayi visar india kawai, alhj salmanu yace toh da waye da waye za'a yiwa? Mom tace mijinta da kuma mahaifiyarta, mama atafau taqi amincewa saidai ita mom taje, ita meh zataje tayi? Ae yanzu 'ya tasu ce sukeda haqqin kula da ita, kausar da ke gefe tace mom toh ni atafi dani mana, Allah zan iya kula da ita ta marairaice, mom tace kausar ni bance bazaki iya ba amma a ganina gwanda atafi da babba kawai, kausar tafara shagwa6a har da kuka ita atafi da ita kawai ba ga yaya khaleed nan ba, mom tace kausar rigima shikenan ayi mata visa din kawai idan yaso mu daga baya sai muzo. Alhj yace toh su kawomin pssport dinsu a office yanzu, mama tace saidai fa ameerah batada pssport dan ko qasar nijer bata ta6a fita ba, alhj salmanu yace ba matsala akawomin hotunanta qanana pssport sai nayi mata yanzu da na koma, mama tace sai anje gida kenan aliyu ka tashi ka tafi, ka duba bag dinta na skul ka dauko, kausar tace there is no need inada pictures dinta, ta zuge purse dinta ta dauko ta miqa musu, alhj yace toh saura pssport dinku keda khaleed, kuma karku damu governor zai dauki nauyin komai, suka miqe akayi godiya, haka sukayita jibge bandir din kudade kamar a bank sannan suka fita. [11/25, 8:10 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣3⃣ Mama ta tsurawa tulin kudin da ke gabanta ido, tace Allah mai iko a ranta, ameerah dai ita zatw zame musu sanadin arziki a duniya, Allah dai kaba wannan yarinya lfy. Mom katse mata tunani ta hanyar cewa khaleed da kausar suje su dauki psspirt din kawai su kaiwa alhj salmanu karsu bata masa lokaci, suka miqe suka fita. Mom tace maman ameerah ya dace a kai kudinnan a bank fa, baikamata a ajiyesu anan haka ba, mama tace ba toh aimu ba mai account banki a cikinmu, mom tace bakomai salim katashi kutafi first bank gurin wannan qawar tawa bjy binta, kace nace ta budawa Aliyu account yanzu katashi ku kwashi kudin kutafi, mom tace kibasu har cheque dinda matar deputy governor ta bayar, kai salim ka cika sunanka ka chire kudin, sai ku zubasu duka a account din Aliyu, yace toh suka miqe suka kwashi kudin suka fita. Khaleed kuwa bayan sunje gida sun dauko pssport din cewa kausar yayi taje takai kawai shi bazashi ba dan bayajin dadi ya miqamata psprt din ta shiga motarta shikuma ya shige daki, tea mai kauri ya hada yasha akan yunwar da hakeji, yasha magani ya zuge babbar rigarsa ya kwanta, wannan abun da ke faruwa kamar a mafarki, wai yau shine aka daurawa aure, baqincikin shi daya bada abar qaunarshi ba, kuma ita takasa fahimtar shi, wata idea ta fado masa, tinda india zasu gobe kuma daga shi sai kausar da ameerah ba su mom, suna sauka zaije yayi visa zuwa germany kawai yaje ya sameta idan taganshi yasan dole ta saurareshi, da wannan shawarar har baccin da ya dade baiyi ba ya kwashe shi. Khaleed ba shi ya farka ba sai bayan magrib, shima salim ne ya tadashi da ya dinga bugamasa qofa, tashi yayi ya bude, salim yace mom da dady ke nemanka, yace yana zuwa, ruwa yashiga toilet ya watsa ya hado da alwala, yayi magrib, yana sallamawa aka fara kiran isha miqewa yayi kawai ya kabbara ta ya gama, yayi addu'oinsa ya shafa, ya miqe ya nufi inda ake kiransa, bayan yayi sallamah ankar6a ya duqa ya gaidasu. Dad ne ya fara magana, khaleed haquri mukeso mu baka, munsan ko wanne namiji idan aka daura masa aure burinsa ya kasance da matarsa a wannan ranar, amma kuma kai naka auren sai yazo a haka, kayi haquri haka Allah ya tsara maka, kuma ina roqonka dan Allah ka riqe yarinyar nan amana domin marainiya ce, kaima zaka samu ladar kula da ita. Mom tace kadai riga ka karanta kagani bama buqatar mu gayamaka miye aure, ko haqqin matarka a kanka, inada yaqinin wannan yarinya zata zamemaka mace ta gari, shiyasa tun farko namaka sha'awarta, Allah ya muku albarka, ya baku zama lfy da zuri'a ta gari akace amin, mom tace katashi kafara shiri jirgin qarfe goma zakubi gobe khaleed yayi godiya ya miqe ya fita, a ransa kuwa yana nazari, lallai warware wannan auren sai ya zame masa matsala ya tafka kuskure, dan iyayensa sun ba ameerah yadda da aminci 100%. [9/14, 4:21 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah Abdul 8⃣4⃣ Angama visa anyi clearance din komai, ya rage kawai suyi boarding jirgi, mom ce riqe da kausar tana jamata kunne akan ta kula da ameerah sosai, tace mom bafa sonta kika fini ba, zankula da ita fiye da yanda zankula da kaina, mama kuwa da su suhaila sai faman kuka suke, ana basu haquri, Aliyu da salim kuwa jirgin sha biyu zasubi zuwaegypt, passengers aka fara kira masu zuwa india suzo suyu boarding, ameerah aka tura ta bisa gadon marasa lfy aka wuce da ita straight sai wani special place da ake aje uncouncious patient, sukuma khaleed da kausar suka zauna a VIP side cikin sauran passengers masu kudi en uwansu jirgi ya daga sai qasar INDIA?✈✈✈. 
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 7,717 11-14-2018, 09:37 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,376 11-14-2018, 09:12 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,340 11-13-2018, 09:41 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,417 11-13-2018, 09:31 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 4,651 11-13-2018, 09:24 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)