The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
MATA UKU GOBARA (Last Part)
#1
MATA UKU GOBARA
46-60
Kallon juna sukeyi na k’urilla kamar yau suka fara
haduwa, a lokaci guda suka fashe da kuka kamar
hadin baki, saida sukayi mai isarsu, ba mai
lallashin daya.
sannan suka ja jiki kowacce ta shige dakinta da
kyar.
Bayan kamar minti talatin zuhra rarrafu ta dawo
palo, akwatinan ta Shiga budewa tana kallon
kayan da kyar kamar wadda akayewa dole, jin
motsinta ya fito da humaida, itama ta bude nata
tana kallo.
Can zuhra ta sauke ajiyar zuciya, tace ” nikam ba
zan daura wadan nan zannuwa ba” duk
wulakancin da mahmoud yayi min, ya nuna min
k’arshena, humaida ta chafe ” kinsan me? kawu
kunnenki kiji….!”
Ta rada mata wasu kalamai a kunne, tuni fuskarta
ta dau annuri, suka tafe tare da dariya.
A wurin mahmoud yana fita gidansa, ya wuce
family meeting dinsu, bayan ya biya ya dauki
hajiyarsa, a mota yayi mata bayanin komai, tace
yanzu ai idan muka karasa wurin meeting za’ayi
zancen komai.
Saida aka dauke ba dadi kafin families su yarda
ayewa yarsu kishiya, acewarsu duka-duka yaushe
ne auren nasa da zuhra, ba’ayi shekara ba yanxu
zaizo ya k’ara wani, can dai wani uncle din
Mahmoud yace “kafada mana gaskiya mahmoud
ko dai haihuwa kake so, shine kake ta wannan
aure-auren?” Kowa palon yadauka sai dai haka
kam.
“Toh ai indai haihuwace Allah ke badawa
mahmoud, kayi hakuri ka jira lokaci mana.” Cewar
wani baffansa.
Cikin jin kunya mahmoud ya dukar dakansa kasa
yace ” ba haka bane, nidai gaskiya matana duk
sunada matsala, shine nake son k’ari ko zan
dace.
K’anin kakansa yace ” duk tsiyar aure-aurenka
idan ka cika hudun ai ka tsaya nan.”
Nan take palon ya dauke da dariya, haka dai da
kyar suka amince bayan goggo tayi dogon sharhi,
gobe za’aje sa rana, ya sanarda yarinya ta fadawa
gidansu.
Da haka taron ya watse, Mahmoud murna fal
ransa.
Direct gidansu JALILA ya wuce, ya same Ahmad
yayi masa bayani, daga baya gimbiyar ta fito
sanye da atamfa take yau, dark purple da milk,
dinkin gown “A” sharp tayi rolling da veil milk, hill
ne a k’afarta purple, tayi kyau sosai abinka da
farar mace cikin purple, gogan naku sai smiling
ake watsawa, ta gaidasi cikin siririyar murya tana
wani nokewa alamar kunya, ga wani murmushi
datake jefa masa duk ya rikice.
Bai San lokacinda bakinsa ya subuce yace ” ranki
ya dadi sannu da fitowa da rawar jiki,” dariya tayi
kadan tana lumshe idanu, tuni Mahmoud ya neme
inda yake ya manta, can yayi karfin Hali ” ledar
Dana baki jiya fa waya CE aciki, nakira naji baki
hada ba, me yasa?”
Lah! Ta fada cikin shagwaba “ban duba bane, bari
nadauku yanxu” daga masa hannu tayi alamar ya
jira, yabi yatsunta da kallo sunsha rani jajir dasu,
bakinsa yau kam har ya gaji da wangala, sai gata
ta dawo tana takawa d’ai-d’ai kamar tana tsoron
kada takalmin su yadata, ta mik’a masa ” ka
hadamin toh baby”
Saida ya k’ara kallonta saboda sunan data kirashi,
Ta bata rai kamar ba ita ta fada ba.
murmushi yayi ya fara hada wayar, ya hada mata
komai harda watsapps, ya bata, haka dai sukayi
ta hirarsu ya fada mata komai ake ciki, harda
kukanta na shagwaba wai yayi wuri nan da
2weeks ta zama matar aure.
Mahmoud dariya yake mata, yana k’ara zugata,
“gaki yar karamar yarinya kuwa,”
Ai kuwa ta fashi da kuka sai cikin gida.
Haka yabar gidan ya wuce kasuwa ransa kal.
Wayoyinsu kawai suka zare cikin akwatinansu irin
na JALILA, mahmoud akwai adalci, wayar da
yasiyawa Jalila shine suma ya siya masu, sun
hada watsapps dinsu suma wai su samu k’awaye
su basu shawara yadda zaci uban mahmoud,
sunga yanxu watsapps yana damawa son ransa.
suna jin shigowar mahmoud, ya bude palon ya
shigo, suna dakunnansu, ya shige nasa, shigarsa
keda wuya ya fara jin k’auri da gudu ya fito yayi
wajen Palo inda hayaki ke fitowa turus yayi ganin
aikinda matansa sukeyi…….!!!
Mrs Jabo.

MATA UKU GOBARA
61-65
Ganin aikinda sukeyi yayi matukar girgizashi,
kayan daya kashe kuddi ya kawu masu, domin
kwatanta adalci, sune suka zubawa fetur suka
k’ona, sai ci sukeyi da wuta bal-bal, ransa yayi
matuk’ar baci, amma ya daure, ya danni zuciyarsa
a matsayinsa na d’a namiji Wanda yafi mata
hangin nesa, kuma idan yace kullum yayi ta
jibgarsu sun zama jakuna kenan.
Tunda dai su kishi ke cin zuciyarsu bal-bal, ya
juya yayi shigewarsa ciki, ganin ya koma cikin
Palo suka sa ihun murna tare da rungume juna,
bukatarsu ta biya, tunda sun bata masa rai.
Humaida taja zuhra “zo mutafi ai burinmu ya cika,
tunda mun k’untata masa yadda shima ya
k’untata mana.”
Hmmmmm ” Anty humaida yanxu ya fara ganin
b’acin rai, damu yakeyi.”
Cikin gidan suka shige cike da murna.
Baba Abu mai gadi da yake kallon duk abinda
yake faruwa, ya girgiza kai yace ” Allah ka yiwa
wannan bawanka naka sauyi da mace ta gari,
yanxu wadannan kayan da suka k’ona mai makon
su kyautar, a’a sai su k’ona alhalin wasu na
nema.”
Yau dai mahmoud ya matsu abinka da d’an Adam
Wanda ba icce ba, rabonsa da matansa har ya
manta, yayi wanka yasha tirare yayi dakin uwar
gida sarauta mata, har tafara bacci taji
shigowarsa, tak’i motsi saida ya hau gadonta, ta
mik’e “karka suma mahmoud, ka jira matarka nan
da 2 weeks”
Ya kwantar da murya “haba humynah ai kema
matata CE…”
Ta turesa tare da fadin “humaida k’azama CE fa”
Mahmoud ya kwantar da murya yana lallashinta,
amma fafur humaida tak’i, sai yab’a masa
bak’ak’en maganganu takeyi, har ransa ya
baci…..!
Abinka da zuciya batada k’ashi, tuni shima ya fara
mayar mata, “ance maki k’azama, k’arya nayi?”
Wata dariya ta shek’e da ita ganin ransa ya baci, ”
ki kalli kanki a madubi mana, kullum daurin k’irji,
hammata gashi tunkus, hakama gabanki gashi ne
dam sai tsami…”
Ya kyara daga murya ” kinga kuwa mai irin halin
nan dole akirata k’azama, idan kinyi zuciya ki
gyara, ai da ba haka kike ba…”
“Anji din, kuma baza’a gyara ba, idan jikinka ne
sai naji…”
Yafita dakin ransa abace.
Hanyar dakinsa yayi, sai can yace bari naje dakin
zuhra na gwadata ko zata amince, da addu’a
abakinsa ya shiga dakin. tayi baccinta hani’an da
kayan bacci irin na gidan iyaye, ya hau gadonta ya
kwanta, jin motsin mutum yasa ta farka, tana
ganinsa tafara harararsa domin tasan kan
zancen…!
Goganka ya kwantar da murya harda bata hakuri,
aikuwa ta runtse ido tayi masa kwal!
Yayi mamaki matuk’a domin gwanda humaida da
ita.
Haka ya janyu tsummansa yayi dakinsa, kitchen
yadawo ya rasa me zai dauka yasha yaji sanyi,
can ya tuna da lime ya hada ya zauna Palo yafara
banka, ransa matuk’ar baci, da matansa amma
Abu daya ya gagaresa.
****
Dare da rana tare da wuni nata juyawa, kwanaki
nata tafiya, lokaci yana wucewa, acikin haka ne
lamurra nata juyawa, al’amarin gidan mahmoud
sai Allah ya kyauta, domin haushi kam yana
kwasarshi, inda shikuma yabawa babu ajiyarsu.
Acikin haka har ansa rana an mik’a kayan akwati
gidansu amaryarsa.
Har takai takawu yaune za’ayi walimar JALILA tare
da angonta MAHMOUD inda aka daura aure dazo
bayan jumu’a.
Za’ayi walima k’arfe hudu na yamma, aka amarya
gidanta k’arfe takwas.
Amarya tayi kwalliyarta cikin milk and golden
material, dinkin gown fitted, kasa ta bude sosai
da step-step, tasha alkyabba ta net milk, shoes
dinta nd purse golden, fuskar nan ta sha make-up
na zamani Wanda faty azland tayi mata, tayi kyau
har tagaji.
Motoci sun fara daukar mutane zuwa GIGINYA
HOTEL inda can aka dauke hall domin gabatar da
lecture akan zamantakewar aure.
Saida aka kwashe kowa, motar Amarya itace last,
tare da k’awayinta, amarya tana shiga hall kallo
yadawo gareta irin kyau da tayi mashaa Allah.
Taje wurinta ta zauna, ba bata lokaci afara lecture
Wanda malama hauwa m Jabo da malama pherty
suka gabatar,malaman da akeji dasu a garin
sokoto.
 lecture ta Shiga jikin mutane sosai, lura yadda
malaman suka watse formula, wasu harda kwalla
ciki harda amarya, jikinta yayi lakwas.
An kammala walima aka fara rabon take away da
suviniours, bansan ya akayi ba sa ga yan
MERMUE HOME OF NOVELLA GROUP bansan
Wanda ya gayyacesu ba, suna kokawar take away,
ba kamar beeba da ummin rabajau da mum
sultan sai kokawa sukeyi suna karbuma saura.
Haka dai taro ya watse lafiya.
Misalin takwas da rabi motocin daukar Amarya
sunzo, anfito da ita da kyar daga jikin yayarta,
Anty aisha, sai kuka sukeyi, Amarya tasha kyau
cikin atamfarta super orange and brown, tasha
gyale brown, haka aka sata mota tare da rakiyar
ilahirin yan uwa da abokan arziki, sai gidanta..!
Ku ‘yar mutan sokoto domin jin wainar gidan
Mahmoud mijin mata uku.
Maryam alkali (Mermue )

MATA UKU GOBARA
66-70
Jeren gwanon motoci ne akalla ba akasara ba
sun kai ashirin, manya masu tsada, hadaddu sai
wutace suke fitarwa masu sha’awa, ba kalar
motar da babu, sai wadda ba’a rasa ba.
sun karya kwanar layin gidan mahmoud, a dai-dai
get suka tsaya kowa na matsa horn, motar
amaryace kawai aka budewa get ta shige ciki,
sauran kam duk a waje sukayi parking mutanen
da ke ciki suka fito.
Dai-dai nan wata bus ta iso sai ihu ta keyi alamar
ta kwana biyu, wa zan gane MERMUE NOVELLA
HOME GROUP 1&2 ne, suke dirkuwa daga cikin
motar, wasu kan wasu, na dauke kaina da sauri
don karsu ganni, domin naga ana rikicen hada
kuddin bus din.
Amarya an shigo da ita cikin gidanta bayan tayi
alwala a k’ofar Palo, ta shiga da kafar dama tare
da addu’a a bakinta, a Palo aka zaunar da ita
domin kiran yayyenta wato HUMAIDA da ZUHRA
domin damk’a masu amanarta.
Said dai ko da ‘yan uwanta suka je kiransu
kowacce ta rufe k’ofar dakinta GAM da key,
sukayi knocking din duniyar nan amma yan
gidanku ko tari sunk’iyi adole sunyi bacci.
Haka aka kwashe JALILA zuwa dakinta, sai kuka
takeyi harda ciccika, ahaka ‘yan uwanta da
abokan arziki sukayi mata sallama bayan sunyi
mata doguwar nasiha, yadda zata kula da mijinta
da abokan zamanta.
JALILA tana ganin kowa ya wuce anbarta ita kadai
kukanta ya tsananta, can taji motsin shigowar
ango, hankalinta ya k’ara tashi, sai da yaje
d’akunan matansa, shima ba irin knocking dinda
baiyi ba, amma sukayi mus kamar matattu, ya
gaje da tsayuwa, ya bude frigde yasa masu
kazarsu da lemu, ya dauke na amaryarsa ya shige
d’akinta.
Da kyar da lallashi da komai JALILA tayi shiru,
suka ci kazarsu mai kabeji da yajin daddawa da
lemu (ku tayi basuyi min ba)lol
Bayan nan suka yi sallar nafila, sukayi addu’o’in
samun zaman lafiya mai d’orewa da zuri’a ta gari.
Ango yaja Amarya saman gado, amma gabansa
sai faduwa yakeyi, sai cewa yakeyi a cikin ransa
“ita kuwa wannan ko meye matsalarta?? Oho”
Yayi sama da kansa yana rok’on Allah ” Allah
kasa daga wannan na kawo k’arshen matsalata.”
Amarya kam itama ta rude tuni, haka dai abubuwa
suka kankama na fitowata waje na basu wuri.
Amma sai me? Ina fitowa naci karo dasu
humaida, sun lab’e a bango ganin janyu k’ofar
danayi ya basu damar lek’awa ta jikin key, ina
kallonsu komai ya faru a cikin kunnensu, kuma
suna lek’awa ta jikin key.
Bakin ciki ya turnik’esu jin zantukan mahmoud
Wanda bai masu ba. ai tuni suka fara tsaki suka
bar wurin.
Misalin karfe bakwai na safe, Amarya ta fito ta
fara gyaran palon gidan, bayan ta gama ta shige
kitchen ta hada break fast ta jere a dinning, ta
kuma dakinta ta shirya cikin super koriya mai
yarfin golden riga da skirt, tayi kyau sosai, ta kafa
dauren nan na zamani, face dinta ma tayi
kwalliyar zamani, ta saka saka Sark’a da
dankunne da awarwaru da rings.amma fa komai
takeyi cikin k’arfin Hali ne, domin ita kad’ai tasan
yadda takeji.
ta fito amaryarta sak!
K’amshinta ne ya tayarda mahmoud, mamaki ya
kasheshi, shida yasan amarya indai virgin CE da
safe langab’ewa takeyi komai sai an mata, amma
banda JALILArsa, yadda yaga ta taku tana yi masa
murmushi tare da tambayarsa har ya tashi, yagane
taji jiki k’arfin Hali ne kawai takeyi.
Mik’ewa yayi zaune fuskarshi ciki da murmushi,
cikin shagwaba tace “na hada maka ruwan wanka
a toilet” tafada tanayi tana rausaya eyes, gogan
naku tuni ya rude, k’ok’arin hugging dinta yayi ta
kauce, a dole ya shige toilet zuwa wanka.
Ko da yashiga ruwan wanka wani irin k’amshi
sukeyi ga toilet din shima yana bada nasa kalar
k’amshi, mahmoud ba abinda yakeyi sai godiya
ga Allah, yana fatar Abu ya dore.
Yana fitowa ya Tarar da kayansa a gado ta fitar
masa, amma tabar dakin, murmushi dai har yanxu
shine a face dinsa.
Ya shirya tsaf cikin three quarter white da black
shirt, yayi kyau sosai sai k’amshi yake badawa ya
fita zuwa Palo.
Mamaki ya k’arayi break fast dinda yaga ta hada,
dinning ciki mak’il, yaje ya zauna tazo tayi serving
dinsa, taje ta kwankwasa su humy kowacce ta
fada mata tazo suyi break.
Sannan ta dawo ta zauna a dinning tana yiwa
mahmoud yar hira, irin ta dariya din nan, shikuwa
sai kwasar dariya yakeyi yana loda abinci a
tunbensa.
Sai ga hajiyoyinku sun fito, suna ya tsina, suka zo
suka zauna, JALILA ta mik’e ta gaidasu, suka
k’arba a dak’ile, ta tambayesu me suke so ta
zuba masu, bayan ta zayyanu abinda ta girka,
cikin wulak’antawa suka ci tabari su zuba abinda
suke so ai kayan abincin na mijinsu ne, don haka
suna da iko dasu.
Batayi mamaki ba, akan abinda sukayi domin
halinsu ba Wanda bata sani ba, shidai mahmoud
basu CE masa ba, bai CE masu ba, ya gama
lodawa ya tashi, JALILA ma ta mik’e tabi bayansa.
A Palo suka zube Mahmoud sai kallonta yakeyi
yana wani kashe mata ido, fuskarsa murmushi
yak’i b’acewa, nan Ahmad ya kirasa a waya yana
masa tsiya, yace zai zo anjima suje gaida baffan
JALILA, sukayi sallama ya kashe wayarsa.
Ya kalle jalila da tadan kishingida saboda ta kasa
jin dadin zaman, yace ” my zumah muje ki zaga
kiga fasalin gidan, kinje wannan yayanki yace
zamu fita anjima gaisuwar surikai.” tsaki yayi “don
ni ya kwafsa min, yau get banyi niyyar lek’awa
ba”
Yar dariya tayi cike da salon yaudara ta mik’e tare
da cewa “muje”
Yabi bayanta suka fita yana nuna mata ko’ina na
gidan.
Su kuwa su humaida ture abincinsu sukayi suma
suka mik’e tare da shigewa d’akin humaida.
Bayan sun dawo daga zagaya gida, suka zube a
palo, jalila tana mayarda numfashi, domin fa a
wahale take, k’arfin Hali kawai takeyi, shima
mahmoud yana kule da ita, sai sannu yake zuba
mata, ya dauku ruwa a frigde ya bata.
Misalin sha biyu na rana zai fita, jalila ta biyosa
har k’ofar Palo tana masa rakiya, tace ” Allah ya
tsari my adawo lafiya” cikin jin dadi mahmoud ya
k’arba har yana rafka tintibe wurin waiwayenta.
A daki ta zube saman gado, ta fada tinanin
abinda ya faru jiya tsakaninta da Mahmoud ne
yake dawo mata, kai tasha albarka jiya ba sunan
da ba’a kirata dashi ba.
My zumah
My tea cup
My fried rice
My stew
My jallop rice
Kai ita kam wasu kunya ma suka bata, tayi yar
dariya ta jin dadi, Ashe haka aure yake, kai Allah
dai ya basu zaman lafiya.
Dai-Dai nan taga su humaida a gabanta sai huci
sukeyi, cikin daga murya humaida tace ”
munafukar banza munafukar wofi, yau k’aryarki ya
k’ari ai”
Zuhra ta cafe “ni abinda yabani mamaki irin yadda
ya mahmoud keyi mata a Daren jiya, yau sai kin
yabawa aya zak’inta.”
Ba bata lokaci suka ciru SUPER GLUE daga
jikinsu, “inda ya shiga har ya rude nan zamu toshe
yau” cewar humaida.
Cikin zare ido jalila ta mik’e zata gudu jikinta
ko’ina rawa yakeyi, k’afa suka sa suka tadeta,
tafadi kasan dakin, zuhra ta hayeta ta dafe,
humaida na k’ok’arin bude kafafuwanta……..!!!!!
Maryam alk’ali { Mermue }

MATA UKU GOBARA
71-75
Innalillahi wa’ina ilaihi rahi’un ita JALILA ta fara
maimatawa cikin wani irin yanayi, inda ita kowa
humaida sai k’ok’arin bude mata k’afafuwa takeyi,
ita kuwa zuhra sai faman danneta takeyi, ta
cigaba da maimaita addu’ar da idan fitina ta
sameka musulunci yayi mana nuni da yinta.
“Me zan gani….???” Mahmoud ne yafada haka da
k’arfi cikin daga murya, tuni zuhra da humaida
sun saki jalila cikin tsammani da rashin sanin
inda zasuyi, ganin Mahmoud datayi tuni ta mik’e
da gudunta ta shige jikinsa, ta saki wani irin kuka,
ko’ina ilahirin jikinta rawa yakeyi.
Mahmoud kallon mamaki yake masu, cikin tsawa
yace “menene kukayi mata??”
Humaida ta rik’e k’ugu sai girgiza takeyi, ta
manna masa wata uwar harara, “abinda kaga
munayi mana”
Kallon zuhra yayi wadda tayi turu-turu da ido sai
mazurai takeyi yace “ke! Gayamin me kuka yiwa
MY SUGAR…!!
Cikin inda-inda tace ” ba Anty humaida bace ta
samu SUPER GLUE wai zamu tosheta.”
A firgice yake k’are masu kallo masu, “lalle kun
nuna min yau baku da mutunci,kashin kai zakuyi
kenan, toh ba agidana ba..!”
Da sauri yaje kan bed side drawer ya dauku
wayarsa, wadda dama itace ya manta yadawo
d’auka ya tarar da wannan aika-aikar.
Har yanxu yana rungume da ita, yana lallashinta
tare da jijjigata kamar baby, ita kuma sai kuka
takeyi k’asa-k’asa, inda su humaida suke tsayi
kamar mutum-mutumi.
Ya kara wayarsa a kunne ” Assalamu Alaikum
alhaji barka da wuni.”
Ya dan rusuna kamar yana gabansa, dayan gefen
aka karba masa, cikin tashin hankali Mahmoud ya
zayyanewa uban humaida abinda ya tarar suna
aikatawa, tuni alhaji ya fara sallalame yace gaya
nan.
K’ara kara wayar yayi cikin murya kamar yasaki
kuka ya gayawa hajiyarshi abinda su zuhra ya tarar
dasu zasu aikata, itama hajiya ta kad’u ainun, tace
gata nan, yanxu zata zo tare da family.
Tuni idonsu humaida ya raina fata, kamar su saki
fitsari a wando, inda shikuwa mahmoud sai
lallashin JALILA yakeyi tana k’ara barkewa da
kuka idan ta tuna abinda kishiyoyinta suka tashi yi
mata, k’ila da yanxu ta mutu, ko tana shure-
shurenta.
Cikin kuka ta lalubu wayarta, tana zayyanewa
antynta abinda ya faru, da sauri mahmoud ya
k’wace wayar tare da cema antynta su kwantar da
hankalinsu za’a dauke hukuncin da ya dace.
Palonsu ya cika dam, kowa sai mamakin
iskancinsu humaida sukayi, wasu sunce su kam
basu tab’a jin wannan salon ba, abban humaida
kamar yayi mata duka, sai kumfar baki yakeyi, ya
cewa humaida “duk ta sake Mahmoud ya
sawwak’e mata to ba gidansa.!”
Jin hakan jikin humaida yayi matuk’ar kad’uwa.
Inda ita kam yan uwan zuhra sai hakuri suke
bawa Mahmoud suna cewa “hannunka baya
rub’ewa kayanke kayar” mahmoud cikin ransa
yace “kaji tsiyar auren zumunci, ba’a tab’a bari
kadau mataki.”
Sai yan uwan jalila an basu hakuri tare da d’aukar
alkwari ba abinda zai samu yarsu in shaa Allah,
domin su
humaida anja masu kunne sosai, cewar duk
abinda yasamu jalila toh sune.
Ahaka taron ya watse.
BAYAN SATI DAYA
Mahmoud ya samu kwanciyar hankali wanda har
ya cire ran samu a rayuwarshi, duk buk’atunsa kaf
JALILARSA ta dauke.
Yau tafita girki Mahmoud kamar maraya yake jin
kansa.
Ita kam yar dariyarta takeyi tana k’ara bashi
k’arfin gwuiwa, domin tana son mijinta ya zamu
adali.
Amma itama tana jin jiki, daurewa kawai takeyi,
wani irin kishi ke turnok’uta amma daure takeyi
tana korar shaidan.
humaida ta karb’e girki
sun sha jagalgalu a zuwan wai girki ne, su
humaida manya, dare nayi aka kwashi jiki zuwa
dakin miji, daga ita dai sai d’auren k’irjinta, ba
laifi yau tayi wanka, amma fa ba turare balle
kayan bacci, haka aka tafi…..!!!
Ko ya za’a kwashe oho
Maryam alkali ( Mermue )

MATA UKU GOBARA
76-80
Tura dakin tayi da k’arfi ta shiga ba sallama,
Mahmoud sai da ya zabura irin yanayin yadda ta
bude k’ofar, bai ce da ita komai ba, ta haye
saman gado ta shige bargon da yake, batace
masa ba, ganin ta k’yalesa shima ya k’yaleta.
Wata zuciyar ke tunatar dashi, cewar ya kwatanta
adalci, yanxu yasan da jalilarsa CE ba zai kyalleta
ba, kuma yana son yayi adalci a tsakanin
matansa.
Ai kam humaida tanajin salo ya canja ta mik’e ”
nawa zaka biyani, domin ni ba banza bace,
hehehehe wai ina amaryar taka ne?, ance dai da
tsohuwar Zuma ake magani.”
Da mamaki yace “wani irin biya humaida sai kace
na dauku karuwa, alhalin ke halalina CE, kuma
matata da kike kira ai duk inada hak’k’i akanku,
kuma kunada akaina…!”
“Oho dai! ni dai ba baiwa bace, hala kamanta duk
wulakancin da kayi mana a baya, ai nayi maka
sauk’i Mah.”
Ransa ya bace ya kyaleta, yayi kwanciyarsa, ita
bata san don yana son yin adalci ne shiyasa ya
nemeta, ita kuwa har da saka dogon buri.
Can tsakar dare taji ba sauk’i dole ta neme sa, ta
bada kai bori ya hau.
Amma sai me??
Wani irin d’oye ya cika dakin, mahmoud ya kunna
wuta, ya kira sunanta ” humaida! Kinga abinda
kika janyuwa kanki wurin bak’ar k’azantarki??”
Tana yatsina tace “me fa?”
“Kinji yadda dakin nan ya canja, alhalin da ba
haka kike ba?? ”
“OK, kana nufin gabana d’oye yake fitarwa??”
Ya daga mata kai ahankali.
Da k’arfi ta mik’e “Allah ya isa, tunda kaci moriyar
ganga ai dole ka yada gaurunta.”
” tunda kayi Amarya ba sharri da bazaka yi mana
ba.”
Ta dirku daga saman gado, ta bar dakin tare da
doko k’ofa.
Da kuka ta shiga dakinta, itama fa taji wannan
canjen, amma ai wannan wulakanci ne mahmoud
yayi mata, don yayi Amarya, dama namiji ba dan
goyo bane, tayi kwafa, tare da yin kwanciyarta,
Wankan ma nafasa saida safe zanyi. Dan rainin
hankali kawai. ( kun ji fa masu karatu, ana so Ku
baki samu yin wanka ba, toh ki wanke gabanki da
ruwa masu dumi, kiyi alwala, domin samun
kariya.)
Da safe haka tak’i fitowa tayi abin karin kumallu,
mahmoud haka yafita bai karya ba, jalila da zUhra
sun fito sun samuwa Kansu abinda zasu ci…
Zuhra tuni tafada dakin humaida, ba b’ata lokaci
humaida ta kora mata zancen jiya tsakaninta da
mahmoud.
Zuhra ta rik’e baki “ki barni dashi yau ai nice
dashi, zan gyara masa zama.
“Hmmmmm, da zaki bi shawarata kar ma kije”
“kibari kawai naje Anty humaida”
“Allah ya kaimu.”
***************
Zuhra CE ke fitowa daga dakinta, cikin Riga da
zani na atamfa red, ta kashe d’auri, sai k’amshi
takeyi, teburin cin abinci an cikashi dam! Da cima
kala-kala, mahmoud kawai ake jira ya dawo
massalaci, JaLila kam yar dariyarta takeyi tana
waya da antynta tana k’ara mata shawarwari, ita
kuwa zuhra sai aika sak’on harara take mata.
Mahmoud ya shigo aka hau table, sai satar kallon
jalila yakeyi, domin kayan datake sanye dasu bai
tab’a ganin an saka irinsu agidansa ba, wando
skinny black da yar top iya cinya orange mai adon
black gabanta sune jikinta, ta tufkec kanta da
yasha k’ananu kalaba, ta watsu wasu a fuska, sai
cin abincinta takeyi cike da yanga, tanayi tana
kora lemu a glass cup kamar bata so,tana yanje
silalan kalabanta da suke rufe mata fuska,
mahmoud yaji kamar yaje ya rungumeta tayi
masa kyau ainun.
Lura da haka da zuhra tayi ta fara tsaki, ta mik’e
tabar wurin, haka ma humaida ta mik’e tana
wak’e-wak’enta na habaici, tanayi tana gyara
daurin k’irjinta.
(Ahayye! Ance da karuwar gida gamma ta waje,
domin dai k’azantar da baka gani ba tsafta
CE…!!! )
Ba wanda ya kulata cikin so, domin basu masan
tanayi ba.
Kamar jira yakeyi, ya tasu yadawo wurinta, “oh
MY jallop rice u look so take away”
Ta kashe masa ido daya tare da yar dariyar Jan
hankali, “kwalliyar ai taka CE ZUMANAH, kai
nayiwa kai kadai.”
Kansa ya k’ara fasuwa, sai wage baki yakeyi, ta
mik’e tana kwarkwasa, mazaunan sai juyawa
sukeyi ta basa sumba a kumatu tare cewa “night
dear”
Ta watsa yan yatsunta, ya bita da kallo kamar
wawa, ko’ina jikinta rangaji yakeyi kamar bishiya.
Ba mai san ta shige daki ba, sai da yaji zUhra
akansa tana huci, “toh na-mamajo sarkin son
mata, sai katashi mu tafi ai ta shige, kai mu dai
an auru mana jaraba, yarinya kamar arniya wannan
shiga ko church zata ai sai haka…!”
Mahmoud murmushi kawai yakeyi, yace “yarinya
ba kisan dawar garin bane, Komai kika CE bana
ganin laifinki.”
Yana kaiwa nan ya shige dakinsa yayi shirin
kwanciya, sai gata ta shigo cikin Riga da wando
na bacci, wandon har ijiyar sawu Riga har ta
wuce gwuiwa, da dan hijab dinta.
Ta cire hijab dinta sai k’amshi takeyi, ta kwanta
kusa da mahmoud tana cika tana batsewa,
mahmoud shikam abin dariya yabasa, amma ya
rik’e abarsa.
Can taji shiru mahmoud bai CE komai ba, kawai
tasa kuka, mahmoud yayi ta lallashi amma fir
tak’i fadar meye.
Taga ba sarki sai Allah, dole ta fada, ta rad’a
masa a kunne, ai kuwa me mahmoud zaiyi idan
ba dariya ba, ai tuni ta hau sabon fushi, ba shiri
ya dawo sabon lallashi, tuni harka ta canja salo,
amma tunda aka fara ZUHRA ko tari batayi ba
ballantana k’ok’k’aran motsi.
Mahmoud yana gamawa kawai ta juya ta bashi
baya ta hau baccinta.
Bak’in ciki kamar ya kashe Mahmoud.
Da safe ta fito ta gyara ko’ina sai ta hada break
fast, mahmoud ya fito a kusan tare shida jalila,
taci wanka ciki wata have fitted gown na material
maroun, tayi kyau har ta gaji, tuni mahmoud ya
manta da bak’inci da yake ciki…
K’ak’arin amai sukaji a dakin humaida kamar
ranta zai fita, da sauri sukayi dakinta…..!!!
Maryam alkali (Mermue )

MATA UKU GOBARA
81-85
Amai take ta kwarawa a galabaice, amma sun ja
sunyi turus! Sakamakon warin dakinta da bayinta,
mahmoud yayi k’arfin Hali shiga bayinta, ya
kamata ya rik’e yana tambayarta “meke damunki
humy?”
Tana kwara amai tana amsa masa, “wlh honey
nima ban sani ba, kawai yau na tashi zuciyanah
sai tashi takeyi, sai ga wannan fitinannin amai.”
Tana kaiwa nan ta juyu tana b’allawa JALILA
harara, mahmoud ya gyara mata jiki ya fito da ita,
tayi lamo ajikinsa, cikin sakin fuska jalila ta fara
magana ” HABEEBE ina ga gwanda kawai mu
kaita asibiti, tanajin jiki.”
Mahmoud yace “haka za’ayi HABEEBIYA.”
Ya waiga gefen zuhra “ki kimtsata Ku fito muje
asibitin” ta karb’a fuska ba yabo ba fallasa, sai
harara suke aikawa jalila kamar sa zazzage
idonsu.
Ita kam murmushi kawai take sambad’a
masu.har suka fice dakin ita da mahmoud, sai
sannu take zubawa.
Kai tsayi usmanu Dan fodio teaching hospital
(uduth) suka nufa da ita, G.O.P.D kai tsayi suka
nufa, bayan ta samu ganin likita an aiwatar da
duk gwajen-gwajen da za’ayi aka gano tana da
shigar ciki, hohoho Ku zo kuga murna wurin
mahmoud kamar ya taka rawa, haka suka
d’ungumu suka dawo gida cike da sharuddan da
likita ya gindaya mata tare da magunguna.
A hanya mahmoud sai waya yakeyi yana sanar da
mutane, isarsu gida keda wuya mutane suka fara
zuwa duba jikin humaida, danginta Dana
mahmoud, gida ya cika sai murna akeyi, inda
JALILA keta d’awainiya da mutane, itakam zuhra
yak’e kawai ta keyi amma ita kam ta so itace ta
samu cikin nan, yadda taga Mahmoud yana murna
nan taso itace keda abin arzikin nan.
A haka rayuwa tayi ta tafiya, humaida kam
k’azanta ta k’aru da lalace, yanzu sai tayi sati biyu
batayi wanka ba, wai bata son warin sabulun
wanka da man shafawa, wari takeyi sosai, dakinta
ma haka, ko’ina tsartar da yawu takeyi, duk ta
b’ata fentin gidan, ranar girkinta haka take kwaba
girki daga kafitar da k’aton kyankyasu sai kuwa
kiyashi, wai ita kasala tayi mata yawa, kan
tagama girki tana kwanciya d’ari, ko turare ta hana
sawa a parlour bata son k’ashin komai.
Haka su jalila ke hakuri da ita, ba abinda takeyi
sai chatting dinta, shikam bata gajiya dashi, inda
anan ne ta had’u da Maman abdul-shakur a wani
group, jin ance mata marubuciya CE yasata tabita
private, daga gaisuwa ta fara zuba mata sirrin
gidanta, wai ta bata shawara.
Bayan dogoyen tambayoyin da m shakur tayi mata
ta ganu bakin zare, dariya kawai tayi tace mata
kar tadamu zata zo itada yan uwanta TASKAR
MARUBUTA idan sun tsaida rana zata gaya mata.
Humy sai washe bakiyi akeyi angayar marubuta
zasu zo gidanta.
Yau ya kama girkin jalila ne, ta kammala komai ta
gyara ko’ina, abincin mahmoud ta dauka ta kai
masa dakinsa saman centre table ta Jere, domin
gidan yanxu ba mai cin abinci a Palo, humaida sai
tayi ta tsargin yawu ko’ina, ta rufe dakin taje
dakinta ta k’ara shiryawa cikin wata arniyar top
spaghetty pink colour da dan gun-short iya Rabin
cinya black mai ado pink, ta raba gashinta biyu
kowanne tasa masa ribbon mai Teddy pink, ta
k’ara feshe jinkinta da turaren Arabians, ta dauku
abayarta ta saka saman kayanta, ta yafa mayafin
abayar, ta dauko dan ket dinta Wanda kayan
baccin ke ciki da kayan da zata da safe, ta rufe
dakinta sai na mahmoud.
Tana shiga dakinsa ta yaye bed sheet dinda ke
kan gadon, ta dauku wani wankakke ta shimfida,
ta d’ame gadon tas,tasa turaren yayyafawa, taje a
washing machine dake toilet din dakin ta wanke
wancan tas taje ta shanyu ta dawo.
Zare abayarta tayi tare da hayewa gadon, ta dauku
cup dinta cike da zogalenta da tayi blending
d’azo tasa madara da Zuma, ta hau kurba a
hankali dadinta na ratsata.
Dai-dai nan mahmoud ya shigo, tsaye yayi yana
kallonta, ta kuma masa kamar wata baturiya ko
yar Nigerian film, kai idan ka ganta bazakace tana
jin zo ba, hannuwa sama ya daga yana godewa
Allah.
Daga bisani ya k’arasa cikin dakin, tana ganinsa ta
ajiye cup din ta daka tsalle tazo ta mak’alk’aleshi,
tana welcoming dinsa tare da wani hot kiss, yana
dariya ya k’arasa bakin gadonsa da ita.
Jansa tayi har toilet ta nuna masa ruwan wankan
data hada masa, ta tayasa wankan suka fito,
boxer da singlet ta bashi yasaka, ta fesa masa
body spray da tirare, ta ciko plate dam da
girkinta, ta mik’a masa, tare da gwanda jiluice din
da yayi sanyi ga kaure kamar ice-cream, ba bata
lokaci ya fara ci, tas ya cinye ya ajiye plate,tare
da cup.
ya fara lek’on cup dinta, cikin dariya tace “zogale
ne Idan zaka sha maganin wanki Jini ne”
Ya k’arba yasha ya bata, yana dariya yace “my
STEW Kedai komai kin iya, harda magani kin iya
hadawa kuma”
Kashe masa ido tayi tare da gwalo, eyeeeee “ni,
kike tsokana” zai cafkuta ta mik’e ta fara zagaya
dakin, shima ya bita suka fara zagaye dakin suna
dariya, saida ta gaji sannan ta bari yakamata, tace
takalminta ne dayake hill sosai shiyasa ya
kamata.
gani kawai sukayi an Banko k’ofar dakin da
k’arfi…..!!!
Ko waye oho?
Maryam alkali (Mermue )

MATA UKU GOBARA
86-90
Shigowa sukayi kowacce hannunta a k’ugu suna
girgiza, kallon mamaki Mahmoud da jalila suka
bisu dashi, cikin k’arfin Hali Mahmoud ya dubisu
tare da cewa “lafiya kuka shigo min daki haka da
k’arfi kamar wani mugun Abu ya biyuku?”
Humaida ta banka masa harara tace “ai gwanda
wani mugun abun ya biyumu da wannan rashin
adalcin da ake mana”.
Zare ido Mahmoud yayi yace “wani rashin adalci
humy nayi maku?”
Sai lokacin zuhra ta karbe “au baka San ma
abinda kayi mana, lalle guy din nan ka rainamu”
Kallon mamaki yabita dashi, ita kam jalila tuni ta
hau gado abinta ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya
tana kurbar zogalenta a hankali tana murmushi,
tana k’are masu kallo.
“Yanzu dan Allah Mahmoud tunda ka auremu ka
tab’a shigewa d’aki da d’ayanmu kana wannan
wasar ana dariya” cewar humaida.
Zuhra ta cafe ” haba-haba wannan rashin adalcin
dame yayi kama? ” ta nuna jalila dake wani
lumshe idanu kamar mai jin bacci, “yanzu Dan
Allah bazakayi mata fada irin wannan shigar
datayi, irin ta fitsararrin turawa amma har ka biye
mata kuka cika gida da ihu kamar yan k’wallo.”
Dariya mahmoud yayi kamar cikinsa zai fashe,
yafara cewa ” yanzu na ganoku kuce kawai kishi
ne ke damunku, kunji haushi kunga muna irin
abinda dayarku bata tab’a yi ba, toh ahir dinku, Ku
fitar da idanku daga kanmu, idan kunji haushi
ranar girkinku kuyi Wanda yafisa.”
Ya nuna masu k’ofa, “leave!”
Cikin harguwa yayi maganar, ” I said leave my
room pls” sumi-sumi suka juya suna shirin
ficewa, domin dai sun san halin gogan nasu yanzu
ba’a kawu masa wargi.
“Shashayen banza, kunyi sakaci wata tazo ta
k’wace maku miji shine zaku zo kuna karanta min
hauka.”
Ganin ransa ya b’ace tuni jalila ta ajiye cup dinta,
ta tasu tana rangwada ta basa kyakkwar runguma
saida ya sauke ajiyar zuciya, yana rungume da ita
ya k’arasa bakin k’ofa dai-dai nan su humy suka
fice cike da k’onar rai, ya datse k’ofar tare da
saka key.
Aikuwa iya k’arfinsu suka zage suna dukan k’ofar
kamar zasu karyata, dariya mahmoud da jalila
suka saka lokaci daya.
Jin motsi kamar mahmoud zai bude k’ofa sukayi,
tuni kowacce ta gudu d’akinta suka rufe.
************
Yau Maman abudul-shakur tayiwa humaida waya
zasu zo, sai murna takeyi, ta tashi ta Shiga
kitchen ta rasa me zatayi masu, ta gaji da
tsayuwarta tana dogon tinani tace bari tayi masut
taliya kawai.
Bayan ta kammala taliyar taje ta watsa ruwa haka
nan ba sabulu don bata son warinsa, ta fito ba
Shafa mai domin shima bata son warinsa, a sif
dinta ta rasa kayan da zata saka su ganta da
haske, haka ta hakura daga k’arshe ta d’auku wata
exclusive dark blue da fari ta saka, zanin duk ya
kod’e tare da dafewa, riga da dankwali fes dasu,
haka ta sakasu duk sun cumuimuiyi kamar an
kwatosu daga bakin kura, ta dawo Palo ta zauna
tana chatting jira k’arasowarsu kawai takeyi.
Tana nan zaune bayan ta turawa m shakur address
ta fara jin dirin motoci, da Sauri ta mik’e tana
lek’o ta window, manyan-manyan motoci data
gani suna parking tuni murna ta kasheta, wata
LAND CROUSER fara sol taga manyan mata na
fitowa acikinta ahankali bayan tagama parking.
Ta k’ara kallon gefe daya taga wata black RANGE
RUBBER itama sai mata ke fitowa cike da
nutsuwa, murna ta k’ara kashe humaida ganin
cewar marubuta yau gasu a gidanta, wata motar
ta k’ara tsayuwa kirar MORANO bayanta SIENA
CE itama mata ne suke ta fitowa cikin shiga ta
mutunci, ai da gudu humaida ta fito zuwa
tarbarsu.
Maryam alkali (Mermue )

MATA UKU GOBARA
91-95
Da gudunta ta k’arasa wurinsu, tana dariya ta nuna
m-shakur dake cikin dakakkiyar shadda free gown
ash colour taji surfani pink, tace kice! Hope na
canka, dariya sauran sukayi suka CE u’re right, da
rawar jiki ta k’arasa dasu cikin palo, sai murmushi
kowa keyi, bayan su zazzauna angama gaishe-
gaishe, m shakur ta mik’e tana introducing ‘yan
uwanta marubuta.
Ta nuna wata mace da tasha lullube har saman
kai, tayi adonta das da ita, wannan itace Maman
khadija, sai Ummi asha, wannan kowa meena dan
musa, Benazir Omar, Jamila, Firdausi sodangi,
lubiee, Anty YBK, Reporter, miemie bie, Anty
aysha, Ummu samha, haneefa, kausar luv, Mrs
saif, salma atiku, aysha, Nernerh, Romaysa, sai
k’awata humaira.
Bayan sun gama cin abinda zasu iya tabawa aka
fara zanxen abinda yakaisu, Kowannensu fuskarsa
cike da murmushi suke kallon humaida, itama
bakinta kamar gonar auduga, ta karkace kai tare
da kashi murya, “pls Anty kubani shawara mijina
ya auru karuwa duk ta kwashe masa hankali.”
Ta kwashe duk labarinta ta basu.
Maman khadija ta fara “gaskiya humaida da
laifinki baki San k’azanta duk yadda mijinka ke
sonka indai kanayinta to kowa harka ta lalace.”
Humaida sai zare ido takeyi, Ummi Aisha ta cafe
” gaskiya kinga ko wurin girki kinada Matsala.”
Anty ybk tace “humaida kinsan me?
Shi namiji dan tattali ne, duk mai faranta masa zai
kuma masa kamar wawa, sai ki dauka an
magancesa ne ko karuwa CE kamar yadda kika
CE.”
Benaziratu tace ” kinsan me humaida ki gwada
shawarwarin da zamu baki kiga shin harkar ta
maganice ko kowa tsabagin kyautatawa Miji CE.”
Humaida kam sai daga kai takeyi kamar
k’ad’angaruwa.
Mrs saif tace ” yiwa miji bala’i bashi zaisa ya
tsoraci kiba, ko ya k’ara sonki hasali ma sai dai
ya k’ara k’inki, dafatar yanzu zaki bude kunnenki
kiji kuma ki sauraremu tare da fahimtarmu.”
Humaida ta daga kai fuskarta kalar tausayi.
Sai sannan Maman Abdul-shakur tasa baki ” yanzu
humaida ki duba kayan jikinki shin ya akayi Riga
da dan kwali yafi haske fiye da zani?”
Humaida tayi sauri ta dube kayanta, ita fa bata
lura ba, sai yanzu, ashe shiyasa duk ta fita
unguwa aketa kallonta, ita kam sai dai tayita hura
hanci, tadauka duk ta bada kala ne, Ashe abin ba
haka yake ba…!
Ajiyar zuciya ta sauki, tace “inaga don ina daurin
k’irji da zanin ne” kamar zatayi kuka tayi
maganar, kausar luv tace ” kinga ko awurin
dressing bakya yi, saboda Allah me zai hana
mijinki ya k’ara aure”
Anty lubie tace ” ko kwalliya fa humaida kowacce
da lokacinda yadace keyita, misali idan mijinki zai
dawo da yamma kinyi wankanki kinyi light make
up kina zuba k’amshi cikin kaya masu Nuna surar
jikinki yadda zaki tak’alu masa sha’awarsa, haka
nan da dare kishige cikin kayan baccinki wadanda
suda babu duk daya! Kina zuba k’amshi ki nufi
dakin oganki.”
Ido da kunne humaida ta gwalalo tana saurarensu,
Anty aysha ta cigaba, ” idan kinji dakinsa kin
tabbatar kin gyara dakin tsaf! Sai k’amshi yake
fitarwa.”
 Reporter ta amshe ” a gado ki ajiye kunya, karki
zama irin Matan nan masu kunyar miji wadda ke
cutarsu, ko kice ajina zai zube ne, ko kice bazan
nemesa ba matuk’ar bai nemeni ba, ai idan nayi
haka na zubar da class dina.”
Maman khadija ta k’ara saka baki ” kuma akwai
matanda komai basu tab’o kawa a gado sai su
zube kamar kayan wanki, ke kya CE matattu ne,
kul! Humaida karki zamu cikinsu, ko ace miji sai
yabiyaki kuddi sannan zai kusanceki, narabaki! Ya
riga ya biya sadakinki, ko sai kinga mijinki yana
matse dake sannan ki dauku buk’atunki ki d’ora
mai kisa yin alkwalin abinda ba zai iya ba, karki
soma!”
Humaida sai ga hawaye sharrrr! M shakur tasa
tissue ta goge mata, Anty YBK tace ” duk Abinda
kika San mijinki zai faranta masa a shimfida yi
k’ok’ari kiyi masa, Allah ne zai baki lada, sannan
zuciya nason mai kyautata mata, tabbas indai kina
kyautatawa mijinki to shima zai kyautata miki.”
Benazir ta k’ara cewa” da safe kitashi kiyi
wankanki ki shirya cikin lace ko atamfa ko
shadda ko material kiyi adonki kamar zaki gidan
suna, yadda idan oga ya fita ba wata kwalliya da
zai gani ta dauke masa hankali, ki gyara gida, kiyi
break fast mai dadi, kije ki tada mijinki ki tayashi
shiryawa, kizo ki bashi break fast dinsa, idan zai
fita ki rakasa, tare da addu’a da kalaman soyayya
da yar shagwaba to ba zai manta kiba bini-bini
zai kiraki ya k’agu yadawo gida domin yasan
abinda zai tarar.
M-shakur tace “yanzu kinga akan dauren k’irjin da
kikeyi nononwanki duk sun bace, ki nemu man
kwakwa kina shafawa zasu tashi, kuma zasu
cicciko, sannan na doyin gaba ki neme magarya
tare bagaruwa ki tafasa ki sauke idan yayi dai-dai
yanda zaki iya shiga ki juye kwalbar misk fari ki
shiga, wurin zaiyi k’amshi tare tsantsi, zai tsuke
kuma zaki bani labari.”
Miemie bie tace ” tsafta fa sai an d’aure malama
humaida, komai indai zaka d’aure to zakaga kayi,
kidinga share gidanki kina gyarawa, kuma dan
Allah kid’aure ko sau biyu ne kirik’a yin wanka da
brush a wuni.”
Humaida tace “in shaa Allah zan d’aure.”
Humaira tace ” kidaina damuwa da kishiyoyinki,
kidai kiyi harkar gabanki, ki rik’e gaskiya da
adalci, kuma ki rik’e mijinki, kowaccenku
gwargwadon farantawarta ga miji haka shima zai
na rawar jiki da ita.”
Ummu husna ta cigaba “bari nabaki sirri daya ki
rik’e zogale, idan kimsamu zogalenki danya kiyi
blending ki tace, kisa Zuma da mdara idan kika
sha ni”ima da matsewa ba magana yar uwa,
sannan daffafar zogale zaki soya da man zaitun
tare da timatir da magi, kina ci kina korawa da
ruwan da kika dafa zogalen hohoho, sannan ki
tafasa minnnas da kaninfari kisa Zuma ki mayar
dashi juice dinki keda oga.”
Sai yanzu chuchu tayi magana tace “humaida
kinsan ciki yana tare da laulayi pls ko kina laulayi
ki rik’a daurewa komai ya kamata kiyi abinki
ahankali kinayi kina hutawa, karki biyewa Mata
masu lalace idan anayi ciki.”
Wannan karun humy kai tad’aga, haka kowannensu
yayi mata nasiha sannan sukayi mata sallama
zasu wuce, humy sai washe baki akeyi.
Bayan sun wuce humy ta dawo ta zauna apalo
tana tinanin abubuwan dataji yau, ai tuni ta fara
hawaye, saiga zuhra ta fito dakinta tace “Anty
humaida wai bak’i kikayi naji hayaniyar mutane,
kai ta d’aga mata alamar eh!
Humy ta mik’e ta shige dakinta.
Ku biyoni masu karatu muje humy zata canja
kowa????

 
MATA UKU GOBARA
96-100
Tsayi take tana k’arewa dakin nata kallo, kamar
na wata mahaukaciya, ko’ina shirgi ne, ta fara
waige-waige ganin ta ina zata fara?
Can ta nufi wurin drawer ta fara fitar da komai
dake cikinta, kayanta ne gasu nan kamar an kwato
bakin kura, ta ware masu Dan dama-dama da
English wears dinta ta tsarasu a drawer, sauran ta
kwasa ta saka hijab ta fita ta kaiwa baba Abu mai
gadi ya bawa matarsa.
K’ara dawowa tayi ta fara shara sai dustbin take
cikawa tana kaiwa tana k’ara dawowa ta k’ara
cikawa, canja zanin gado, bayan ta kammala
sharar,tayi goge-goge a dakin duk abinda yayi
k’ura sai da ta goge, ta zauna ta huta, kamar
minti shabiyar ta tashi tayi mopping ta feshi
dakinta da air freshener ta kunna Bonner tuni daki
ya hau k’amshi.
Toilet ta shige ta fara darzarshi sai da yayi tas,
shima ta fesa masa tirare, sannan itama ta hada
ruwan wanka, ta fara wanke gashinta da yake a
tsefi, tayi ta wankewa tun bakin kumfa na fita har
yadawo fari tas, sannan ta dauraye gashin.
ta fara darzar jikinta da soso da sabulu, duk wani
sak’o da lungu na jikinta inda ke ajiye datti har
wurin ya fara wari kamar su tsakanin matse-
matse da kasan nonowa da hammata duk sai da
dirze iya k’arfinta, tanayi tana k’ak’arin amai
amma haka ta daure tana toshe hanci, har jikinta
yayi fes ta dauraye da ruwa tayi brush tare da
kuskure bakinta da ruwa mai k’amshin mint, ta
d’auru towel ta fito.
Tuni taji iska ko’ina ya shigarta ya hudata, bayan
ta tsani jikinta ta draying din gashinta da hand
drayer, ta dauri ta dauku vassilene ta shafe jikinta
domin bata son k’amshin lotion, wata gown yar
kanti black mai hannun vest ta saka, tabi lafiyar
gado tuni bacci yayi awon gaba da ita.
**************
Wata had’ad’d’iyar matashiya CE ke kai komu
tsakanin kitchen da dinning, cikin blue jeans
pencil da yar top red,rabin cinya armless, fuskar
nan tasha fenti-fenti na kwalliyar zamani, k’afanta
sanyi cikin red plat shoes, gashi nan yasha gyara
tayi parking tsakiyar kai da wani tafkeken rebbon
blue, ta watsu wani gashi agaban fuska har yana
rufe mata ido tana janyewa.
Dan cikinta ya fito d’as dashi yayi mata kyau
sosai, daga kitchen take fitowa zuwa dinning, tana
jere abinci cikin warmers masu kyau, sai k’amshi
take bad’awa, jin anyi hugging dinta ta baya ta
juya da k’arfi don ganin waye????
Mahmoud cikin brown jeans da white T-shirt mai
bottomgs a gaba tana da layi-layi brown, “oh my
humy I really proud to have u” jin yafadi haka tuni
ta hau kada ido abinda ke matuk’ar burge
mahmoud, “me too my honey” ta furta a hankali,
mahmoud sai washe baki yakeyi yana shafar cikin
jikinta, yayinda humy sai rausaya akeyi, girke ne
ta shirya masa hadadde mai rai da lafiya.
Taje ta kira jalila da zuhra, jalila ta fito cikin mini
skirt iya gwuiwa blue top dinta pink, sai k’amshi
take zubawa, kan nan yasha kalaba ita dai tana
son kalaba kuma tasan sirinta,( kuna so Ku sani
masu karatu?) sai murmushi takeyi, sai ga zuhra
ta fito cikin Riga da zani na atamfa an kashe
d’aure, baki saki take kallon humaida da jalila ta
tab’e Baki, daga bisani ta zo ta zauna.
BAYAN SHEKARA 1
Competition sosai ake bugawa a gidan Mahmoud,
tsakanin JALILA da HUMAIDA, kowannesu gani
yakeyi gwani ne wurin iya kwalliya, sai buga game
akeyi kowaccenta k’ok’arinta taga miji ita yafiso,
while ita kam ZUHRA duk gani takeyi iskanci ne
suke zubawa.
Misalin k’arfe shida mahmoud ya shigo gidansa a
gajiye, HUMY itada babynta Wanda aka sakawa
sunan mahaifin mahmoud Usman Suna kiransa
affan, sun sha wanka, humy cikin half gown iya
gwuiwa ash and pink, ta yiwa babynta kwalliya
cikin kaya farare sol, yayinda a gefe JALILA da
cikinta cikin riga mai Dan fadi daga k’asa da
wando skinny, tayi kyau sosai sai hajiya ZUHRA
cikin leshe Riga da zani, an kafe d’aure, sai
chewing gum ake tauna.
Shigowa yayi gidansa kowacce da kalar
kwalliyarta ya bisu da kallo, ransa k’al in bayan
zuhra da tak’i canja Hali, shiyasa yake fushi da
ita ko gefenta yak’i kallo, kuma ita keda girki,
bayan ya rungume humy da jalila tare da
sumbatarsu ya wuce dakinsa.
Da gudu tayi dakinta tana kuka, bayan tayi mai
isarta, ta janyu waya ta kira yayarta Maman
abideen, tana kuka tana zayyane mata abinda
mahmoud yayi mata, cikin fada ta fara magana
“me na gaya maki zuhra rannar? Kina nufin baki
dauka ba?”
Cikin kuka tace “Anty wlh bazan iya wannan rashin
kunya ba, ai iskanci ne da d’ibar albarka.”
Ta daka mata tsawa ” yimin shiru wawiya kawai
su sauran kishiyoyinki da suka yi iskancin me ya
rage ajikinsu, yanzu zan k’ara turu maki text idan
bakiyi ba, karki k’ara kirana.”
Cikin 5 minute ta turu mata text, ba yadda ta iya
haka taja jiki zuwa dakin Mahmoud yana ta cika
yana batsewa, ta k’arasa wurinsa ta bashi hak’uri
tare da alk’awarin zata gyara, sannan ya fito akayi
dinner bayan ya dawo masallaci tare dax 
familynsa.
K’warai mahmoud yayi makinta yadda  ta ajiye
kunya ta faranta masa a Daren, sai albarka yake
sa mata, ita kam dad’i ya cikata, domin dai tana
son mijinta kuma tana so tasakashi farin ciki a
kodayaushe.
*************
Lokaci yana tafiya kwanakinmu na k’arewa, a cikin
haka ne gidan mahmoud ya zama “HAPPY
FAMILY” matansa sun cika masa gida da yara
inda HUMAIDA keda yara biyu affan da yusra,
while zuhra nada daya sultan, jalila nada baby
khairiyya kuma kowaccensu nayin iya bakin
k’ok’arinta wurin faranta masa.
Yau zai dawo daga tafiya kowaccensu ta
tsoke,cikin shiga mai kyau, yaransu kuma sunyi
masu kwalliya gwannin sha’awa. Ya shigo cike da
zumudi, yana ta doka murmushi, matansa suka
tarbesa cike da kulawa, da tsantsan soyayya, ya
rungumesu yana dariya yace “ance MATA UKU
GOBARA nidai ga nawa MATA UKU ZUMAH NE.”
ALHAMDULILLAH !!!
Anan na kawu karshen wannan buk mai suna
MATA UKU GOBARA, Allah yasa mu amfana da
abinda ke cike, inda nayi kuskure Allah ya
yafemin.
Sai mun hade a sabon littafina “WASWASI” (aikin
shaidan)
GODIYA
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  MATA UKU GOBARA Gimbiya 1 7,396 09-20-2018, 09:52 AM
Last Post: Gimbiya
  MATA UKU GOBARA Gimbiya 0 12,612 09-20-2018, 09:36 AM
Last Post: Gimbiya
  2019: Kwankwasiyya Ta Raba Wa Mata 100 Naira 10,000 A Yobe Edoman 2 2,534 04-23-2018, 12:44 PM
Last Post: Edoman
  PDP Za Ta Kara Wa Mata Mukamai Idan Ta Lashe Zaben 2019 –Mariya Waziri Edoman 0 1,767 04-22-2018, 12:57 PM
Last Post: Edoman
  PDP Za Ta Kara Wa Mata Mukamai Idan Ta Lashe Zaben 2019 Edoman 0 1,954 04-22-2018, 12:53 PM
Last Post: Edoman
  HANYOYIN GYARAN JIKI NA MATA DA MAZA Gimbiya 0 3,111 11-13-2017, 05:39 PM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)