The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 160 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 160 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 165 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 165 errorHandler->error



Forums
Katsina Ta Tsakiya: Zan Tsaya Takara Don Amsa Kiran Al’ummata –Sanata Ibrahim Ida Re - Printable Version

+- Forums (http://contripeople.com)
+-- Forum: Retired Forums (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=78)
+--- Forum: Retired Forums. Please Make Your Post Within The 3 Forums In General Discussion (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=49)
+---- Forum: Hausa Language Forum (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=40)
+---- Thread: Katsina Ta Tsakiya: Zan Tsaya Takara Don Amsa Kiran Al’ummata –Sanata Ibrahim Ida Re (/showthread.php?tid=6659)



Katsina Ta Tsakiya: Zan Tsaya Takara Don Amsa Kiran Al’ummata –Sanata Ibrahim Ida Re - Edoman - 04-30-2018

By Mubarak Umar

Tsohon Sanata mai wakitlar Katsina Ta Tsakiya, Ibrahim M. Ida, ya bayyana cewar irin abubuwan day a gudanar lokacin da wakilci al’ummar yankinsa tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011 su ne makasudin day a sa mutane suka bukaci ya sake tsayawa takara a zaben 2019. Sanatan ya bayyana haka a wata hirar musamman da ya yi da LEADERSHIP A Yau a ofishinsa da ke Abuja kwanan baya, inda ya ce, lokaci ya yi da ya kamata ya amsa kiran al’ummarsa, domin sake wakiltar Katsina Ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya. Ya ce sa’ilin da yake Majalisa, ya gudanar da abubuwa masu yawan gaske, wanda al’ummar mazabarsa har yanzu suke amfana, amma wasu tsirarun mutane a jam’iyyar day a bari (watau PDP) suka shirya kitimurmurar hana shi dawowa Majalisa, wanda hakan ya say a bar PDP, sannan ya dawo APC. Danmajen Katsina wanda ya yi takarar gwamna a Katsina a zabe day a gabata na 2015, ya tabbatar da cewar, al’ummar Katsina Ta Tsakiya su kwantar da hankalinsu, domin y agama shiri tsaf domin tsayawa takara kamar yadda suka bukata, inda ya ce, yana sane da irin kiraye-kirayen da ake yi kan ya tsaya takara, saboda haka, zai shiga jerin masu neman jam’iyyar APC ta sahale masu. “Masu iya magana kan ce, alheri madara, ba ya faduwa kasa banza. Mutanen da na wakilta ba su manta abubuwan alherin da na yi masu ba. Na tabbata suna bibiyar yadda abubuwa suke tafiya, watakila ba su jin dadin wakilcin yanzu, shi ya sa suka bukaci inda ya dawo. “Lokacin da nake Majalisa ban yi kasa a gwiwa ba wajen gabatar da kudurori wadanda za su amfani al’ummar Nijeriya, ba wa mazabar da nake wakilta kadai ba. Saboda haka na amsa wannan gayyata al’ummar mazabata, zan sake tsayawa takara a 2019 da yardarm Allah.” A cewar Sanatan. Da yake tsokaci game da takarar Shugaba Muhammadu Buhari a 2019, Sanatan ya ce, “Mulki dai na Allah ne, wanda zai yi Shugban Kasa daga nan har duniya ta tashi Allah ya riga ya tsara abinsa. Amma ya ce mu nema, illa iyaka kirana ga dukkan dan jam’iyya shi ne, eh ka nemi mulki halal ne, kuma ka yi hamayyar siyasa halal ne, abinda yake haram shi ne, ka zo ka bata ruwa, kai ka san ba sha za ka yi ba, amma ka zo ka gurbata shi, to shi ne ba shi da kyau. Muna maraba da matakin Shugaba Muhammadu Buhari na tsaya takara, domin ya ci gaba da ayyukan alherin da ya farowa al’ummar Nijeriya. “Shugaban kasa ya yi min daidai, domin kamar yadda wasu suka ce in ma da bai tsaya ba, da kotu za su kai shi, to ina daya daga cikin wadanda inda takarda ce zan sa hannu, domin na san mutum ne kamili, mutum ne mai akida ta alheri ga wannan kasa.” In ji shi.

Read More at: https://leadershipayau.com/2018/04/30/katsina-ta-tsakiya-zan-tsaya-takara-don-amsa-kiran-alummata-sanata-ibrahim-ida/