The following warnings occurred: | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
|
MATA UKU GOBARA (Last Part) - Printable Version +- Forums (http://contripeople.com) +-- Forum: Retired Forums (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=78) +--- Forum: Retired Forums. Please Make Your Post Within The 3 Forums In General Discussion (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=49) +---- Forum: Hausa Language Forum (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=40) +---- Thread: MATA UKU GOBARA (Last Part) (/showthread.php?tid=10202) |
MATA UKU GOBARA (Last Part) - Gimbiya - 09-28-2018 MATA UKU GOBARA 46-60 Kallon juna sukeyi na k’urilla kamar yau suka fara haduwa, a lokaci guda suka fashe da kuka kamar hadin baki, saida sukayi mai isarsu, ba mai lallashin daya. sannan suka ja jiki kowacce ta shige dakinta da kyar. Bayan kamar minti talatin zuhra rarrafu ta dawo palo, akwatinan ta Shiga budewa tana kallon kayan da kyar kamar wadda akayewa dole, jin motsinta ya fito da humaida, itama ta bude nata tana kallo. Can zuhra ta sauke ajiyar zuciya, tace ” nikam ba zan daura wadan nan zannuwa ba” duk wulakancin da mahmoud yayi min, ya nuna min k’arshena, humaida ta chafe ” kinsan me? kawu kunnenki kiji….!” Ta rada mata wasu kalamai a kunne, tuni fuskarta ta dau annuri, suka tafe tare da dariya. A wurin mahmoud yana fita gidansa, ya wuce family meeting dinsu, bayan ya biya ya dauki hajiyarsa, a mota yayi mata bayanin komai, tace yanzu ai idan muka karasa wurin meeting za’ayi zancen komai. Saida aka dauke ba dadi kafin families su yarda ayewa yarsu kishiya, acewarsu duka-duka yaushe ne auren nasa da zuhra, ba’ayi shekara ba yanxu zaizo ya k’ara wani, can dai wani uncle din Mahmoud yace “kafada mana gaskiya mahmoud ko dai haihuwa kake so, shine kake ta wannan aure-auren?” Kowa palon yadauka sai dai haka kam. “Toh ai indai haihuwace Allah ke badawa mahmoud, kayi hakuri ka jira lokaci mana.” Cewar wani baffansa. Cikin jin kunya mahmoud ya dukar dakansa kasa yace ” ba haka bane, nidai gaskiya matana duk sunada matsala, shine nake son k’ari ko zan dace. K’anin kakansa yace ” duk tsiyar aure-aurenka idan ka cika hudun ai ka tsaya nan.” Nan take palon ya dauke da dariya, haka dai da kyar suka amince bayan goggo tayi dogon sharhi, gobe za’aje sa rana, ya sanarda yarinya ta fadawa gidansu. Da haka taron ya watse, Mahmoud murna fal ransa. Direct gidansu JALILA ya wuce, ya same Ahmad yayi masa bayani, daga baya gimbiyar ta fito sanye da atamfa take yau, dark purple da milk, dinkin gown “A” sharp tayi rolling da veil milk, hill ne a k’afarta purple, tayi kyau sosai abinka da farar mace cikin purple, gogan naku sai smiling ake watsawa, ta gaidasi cikin siririyar murya tana wani nokewa alamar kunya, ga wani murmushi datake jefa masa duk ya rikice. Bai San lokacinda bakinsa ya subuce yace ” ranki ya dadi sannu da fitowa da rawar jiki,” dariya tayi kadan tana lumshe idanu, tuni Mahmoud ya neme inda yake ya manta, can yayi karfin Hali ” ledar Dana baki jiya fa waya CE aciki, nakira naji baki hada ba, me yasa?” Lah! Ta fada cikin shagwaba “ban duba bane, bari nadauku yanxu” daga masa hannu tayi alamar ya jira, yabi yatsunta da kallo sunsha rani jajir dasu, bakinsa yau kam har ya gaji da wangala, sai gata ta dawo tana takawa d’ai-d’ai kamar tana tsoron kada takalmin su yadata, ta mik’a masa ” ka hadamin toh baby” Saida ya k’ara kallonta saboda sunan data kirashi, Ta bata rai kamar ba ita ta fada ba. murmushi yayi ya fara hada wayar, ya hada mata komai harda watsapps, ya bata, haka dai sukayi ta hirarsu ya fada mata komai ake ciki, harda kukanta na shagwaba wai yayi wuri nan da 2weeks ta zama matar aure. Mahmoud dariya yake mata, yana k’ara zugata, “gaki yar karamar yarinya kuwa,” Ai kuwa ta fashi da kuka sai cikin gida. Haka yabar gidan ya wuce kasuwa ransa kal. Wayoyinsu kawai suka zare cikin akwatinansu irin na JALILA, mahmoud akwai adalci, wayar da yasiyawa Jalila shine suma ya siya masu, sun hada watsapps dinsu suma wai su samu k’awaye su basu shawara yadda zaci uban mahmoud, sunga yanxu watsapps yana damawa son ransa. suna jin shigowar mahmoud, ya bude palon ya shigo, suna dakunnansu, ya shige nasa, shigarsa keda wuya ya fara jin k’auri da gudu ya fito yayi wajen Palo inda hayaki ke fitowa turus yayi ganin aikinda matansa sukeyi…….!!! Mrs Jabo. MATA UKU GOBARA 61-65 Ganin aikinda sukeyi yayi matukar girgizashi, kayan daya kashe kuddi ya kawu masu, domin kwatanta adalci, sune suka zubawa fetur suka k’ona, sai ci sukeyi da wuta bal-bal, ransa yayi matuk’ar baci, amma ya daure, ya danni zuciyarsa a matsayinsa na d’a namiji Wanda yafi mata hangin nesa, kuma idan yace kullum yayi ta jibgarsu sun zama jakuna kenan. Tunda dai su kishi ke cin zuciyarsu bal-bal, ya juya yayi shigewarsa ciki, ganin ya koma cikin Palo suka sa ihun murna tare da rungume juna, bukatarsu ta biya, tunda sun bata masa rai. Humaida taja zuhra “zo mutafi ai burinmu ya cika, tunda mun k’untata masa yadda shima ya k’untata mana.” Hmmmmm ” Anty humaida yanxu ya fara ganin b’acin rai, damu yakeyi.” Cikin gidan suka shige cike da murna. Baba Abu mai gadi da yake kallon duk abinda yake faruwa, ya girgiza kai yace ” Allah ka yiwa wannan bawanka naka sauyi da mace ta gari, yanxu wadannan kayan da suka k’ona mai makon su kyautar, a’a sai su k’ona alhalin wasu na nema.” Yau dai mahmoud ya matsu abinka da d’an Adam Wanda ba icce ba, rabonsa da matansa har ya manta, yayi wanka yasha tirare yayi dakin uwar gida sarauta mata, har tafara bacci taji shigowarsa, tak’i motsi saida ya hau gadonta, ta mik’e “karka suma mahmoud, ka jira matarka nan da 2 weeks” Ya kwantar da murya “haba humynah ai kema matata CE…” Ta turesa tare da fadin “humaida k’azama CE fa” Mahmoud ya kwantar da murya yana lallashinta, amma fafur humaida tak’i, sai yab’a masa bak’ak’en maganganu takeyi, har ransa ya baci…..! Abinka da zuciya batada k’ashi, tuni shima ya fara mayar mata, “ance maki k’azama, k’arya nayi?” Wata dariya ta shek’e da ita ganin ransa ya baci, ” ki kalli kanki a madubi mana, kullum daurin k’irji, hammata gashi tunkus, hakama gabanki gashi ne dam sai tsami…” Ya kyara daga murya ” kinga kuwa mai irin halin nan dole akirata k’azama, idan kinyi zuciya ki gyara, ai da ba haka kike ba…” “Anji din, kuma baza’a gyara ba, idan jikinka ne sai naji…” Yafita dakin ransa abace. Hanyar dakinsa yayi, sai can yace bari naje dakin zuhra na gwadata ko zata amince, da addu’a abakinsa ya shiga dakin. tayi baccinta hani’an da kayan bacci irin na gidan iyaye, ya hau gadonta ya kwanta, jin motsin mutum yasa ta farka, tana ganinsa tafara harararsa domin tasan kan zancen…! Goganka ya kwantar da murya harda bata hakuri, aikuwa ta runtse ido tayi masa kwal! Yayi mamaki matuk’a domin gwanda humaida da ita. Haka ya janyu tsummansa yayi dakinsa, kitchen yadawo ya rasa me zai dauka yasha yaji sanyi, can ya tuna da lime ya hada ya zauna Palo yafara banka, ransa matuk’ar baci, da matansa amma Abu daya ya gagaresa. **** Dare da rana tare da wuni nata juyawa, kwanaki nata tafiya, lokaci yana wucewa, acikin haka ne lamurra nata juyawa, al’amarin gidan mahmoud sai Allah ya kyauta, domin haushi kam yana kwasarshi, inda shikuma yabawa babu ajiyarsu. Acikin haka har ansa rana an mik’a kayan akwati gidansu amaryarsa. Har takai takawu yaune za’ayi walimar JALILA tare da angonta MAHMOUD inda aka daura aure dazo bayan jumu’a. Za’ayi walima k’arfe hudu na yamma, aka amarya gidanta k’arfe takwas. Amarya tayi kwalliyarta cikin milk and golden material, dinkin gown fitted, kasa ta bude sosai da step-step, tasha alkyabba ta net milk, shoes dinta nd purse golden, fuskar nan ta sha make-up na zamani Wanda faty azland tayi mata, tayi kyau har tagaji. Motoci sun fara daukar mutane zuwa GIGINYA HOTEL inda can aka dauke hall domin gabatar da lecture akan zamantakewar aure. Saida aka kwashe kowa, motar Amarya itace last, tare da k’awayinta, amarya tana shiga hall kallo yadawo gareta irin kyau da tayi mashaa Allah. Taje wurinta ta zauna, ba bata lokaci afara lecture Wanda malama hauwa m Jabo da malama pherty suka gabatar,malaman da akeji dasu a garin sokoto. lecture ta Shiga jikin mutane sosai, lura yadda malaman suka watse formula, wasu harda kwalla ciki harda amarya, jikinta yayi lakwas. An kammala walima aka fara rabon take away da suviniours, bansan ya akayi ba sa ga yan MERMUE HOME OF NOVELLA GROUP bansan Wanda ya gayyacesu ba, suna kokawar take away, ba kamar beeba da ummin rabajau da mum sultan sai kokawa sukeyi suna karbuma saura. Haka dai taro ya watse lafiya. Misalin takwas da rabi motocin daukar Amarya sunzo, anfito da ita da kyar daga jikin yayarta, Anty aisha, sai kuka sukeyi, Amarya tasha kyau cikin atamfarta super orange and brown, tasha gyale brown, haka aka sata mota tare da rakiyar ilahirin yan uwa da abokan arziki, sai gidanta..! Ku ‘yar mutan sokoto domin jin wainar gidan Mahmoud mijin mata uku. Maryam alkali (Mermue ) MATA UKU GOBARA 66-70 Jeren gwanon motoci ne akalla ba akasara ba sun kai ashirin, manya masu tsada, hadaddu sai wutace suke fitarwa masu sha’awa, ba kalar motar da babu, sai wadda ba’a rasa ba. sun karya kwanar layin gidan mahmoud, a dai-dai get suka tsaya kowa na matsa horn, motar amaryace kawai aka budewa get ta shige ciki, sauran kam duk a waje sukayi parking mutanen da ke ciki suka fito. Dai-dai nan wata bus ta iso sai ihu ta keyi alamar ta kwana biyu, wa zan gane MERMUE NOVELLA HOME GROUP 1&2 ne, suke dirkuwa daga cikin motar, wasu kan wasu, na dauke kaina da sauri don karsu ganni, domin naga ana rikicen hada kuddin bus din. Amarya an shigo da ita cikin gidanta bayan tayi alwala a k’ofar Palo, ta shiga da kafar dama tare da addu’a a bakinta, a Palo aka zaunar da ita domin kiran yayyenta wato HUMAIDA da ZUHRA domin damk’a masu amanarta. Said dai ko da ‘yan uwanta suka je kiransu kowacce ta rufe k’ofar dakinta GAM da key, sukayi knocking din duniyar nan amma yan gidanku ko tari sunk’iyi adole sunyi bacci. Haka aka kwashe JALILA zuwa dakinta, sai kuka takeyi harda ciccika, ahaka ‘yan uwanta da abokan arziki sukayi mata sallama bayan sunyi mata doguwar nasiha, yadda zata kula da mijinta da abokan zamanta. JALILA tana ganin kowa ya wuce anbarta ita kadai kukanta ya tsananta, can taji motsin shigowar ango, hankalinta ya k’ara tashi, sai da yaje d’akunan matansa, shima ba irin knocking dinda baiyi ba, amma sukayi mus kamar matattu, ya gaje da tsayuwa, ya bude frigde yasa masu kazarsu da lemu, ya dauke na amaryarsa ya shige d’akinta. Da kyar da lallashi da komai JALILA tayi shiru, suka ci kazarsu mai kabeji da yajin daddawa da lemu (ku tayi basuyi min ba)lol Bayan nan suka yi sallar nafila, sukayi addu’o’in samun zaman lafiya mai d’orewa da zuri’a ta gari. Ango yaja Amarya saman gado, amma gabansa sai faduwa yakeyi, sai cewa yakeyi a cikin ransa “ita kuwa wannan ko meye matsalarta?? Oho” Yayi sama da kansa yana rok’on Allah ” Allah kasa daga wannan na kawo k’arshen matsalata.” Amarya kam itama ta rude tuni, haka dai abubuwa suka kankama na fitowata waje na basu wuri. Amma sai me? Ina fitowa naci karo dasu humaida, sun lab’e a bango ganin janyu k’ofar danayi ya basu damar lek’awa ta jikin key, ina kallonsu komai ya faru a cikin kunnensu, kuma suna lek’awa ta jikin key. Bakin ciki ya turnik’esu jin zantukan mahmoud Wanda bai masu ba. ai tuni suka fara tsaki suka bar wurin. Misalin karfe bakwai na safe, Amarya ta fito ta fara gyaran palon gidan, bayan ta gama ta shige kitchen ta hada break fast ta jere a dinning, ta kuma dakinta ta shirya cikin super koriya mai yarfin golden riga da skirt, tayi kyau sosai, ta kafa dauren nan na zamani, face dinta ma tayi kwalliyar zamani, ta saka saka Sark’a da dankunne da awarwaru da rings.amma fa komai takeyi cikin k’arfin Hali ne, domin ita kad’ai tasan yadda takeji. ta fito amaryarta sak! K’amshinta ne ya tayarda mahmoud, mamaki ya kasheshi, shida yasan amarya indai virgin CE da safe langab’ewa takeyi komai sai an mata, amma banda JALILArsa, yadda yaga ta taku tana yi masa murmushi tare da tambayarsa har ya tashi, yagane taji jiki k’arfin Hali ne kawai takeyi. Mik’ewa yayi zaune fuskarshi ciki da murmushi, cikin shagwaba tace “na hada maka ruwan wanka a toilet” tafada tanayi tana rausaya eyes, gogan naku tuni ya rude, k’ok’arin hugging dinta yayi ta kauce, a dole ya shige toilet zuwa wanka. Ko da yashiga ruwan wanka wani irin k’amshi sukeyi ga toilet din shima yana bada nasa kalar k’amshi, mahmoud ba abinda yakeyi sai godiya ga Allah, yana fatar Abu ya dore. Yana fitowa ya Tarar da kayansa a gado ta fitar masa, amma tabar dakin, murmushi dai har yanxu shine a face dinsa. Ya shirya tsaf cikin three quarter white da black shirt, yayi kyau sosai sai k’amshi yake badawa ya fita zuwa Palo. Mamaki ya k’arayi break fast dinda yaga ta hada, dinning ciki mak’il, yaje ya zauna tazo tayi serving dinsa, taje ta kwankwasa su humy kowacce ta fada mata tazo suyi break. Sannan ta dawo ta zauna a dinning tana yiwa mahmoud yar hira, irin ta dariya din nan, shikuwa sai kwasar dariya yakeyi yana loda abinci a tunbensa. Sai ga hajiyoyinku sun fito, suna ya tsina, suka zo suka zauna, JALILA ta mik’e ta gaidasu, suka k’arba a dak’ile, ta tambayesu me suke so ta zuba masu, bayan ta zayyanu abinda ta girka, cikin wulak’antawa suka ci tabari su zuba abinda suke so ai kayan abincin na mijinsu ne, don haka suna da iko dasu. Batayi mamaki ba, akan abinda sukayi domin halinsu ba Wanda bata sani ba, shidai mahmoud basu CE masa ba, bai CE masu ba, ya gama lodawa ya tashi, JALILA ma ta mik’e tabi bayansa. A Palo suka zube Mahmoud sai kallonta yakeyi yana wani kashe mata ido, fuskarsa murmushi yak’i b’acewa, nan Ahmad ya kirasa a waya yana masa tsiya, yace zai zo anjima suje gaida baffan JALILA, sukayi sallama ya kashe wayarsa. Ya kalle jalila da tadan kishingida saboda ta kasa jin dadin zaman, yace ” my zumah muje ki zaga kiga fasalin gidan, kinje wannan yayanki yace zamu fita anjima gaisuwar surikai.” tsaki yayi “don ni ya kwafsa min, yau get banyi niyyar lek’awa ba” Yar dariya tayi cike da salon yaudara ta mik’e tare da cewa “muje” Yabi bayanta suka fita yana nuna mata ko’ina na gidan. Su kuwa su humaida ture abincinsu sukayi suma suka mik’e tare da shigewa d’akin humaida. Bayan sun dawo daga zagaya gida, suka zube a palo, jalila tana mayarda numfashi, domin fa a wahale take, k’arfin Hali kawai takeyi, shima mahmoud yana kule da ita, sai sannu yake zuba mata, ya dauku ruwa a frigde ya bata. Misalin sha biyu na rana zai fita, jalila ta biyosa har k’ofar Palo tana masa rakiya, tace ” Allah ya tsari my adawo lafiya” cikin jin dadi mahmoud ya k’arba har yana rafka tintibe wurin waiwayenta. A daki ta zube saman gado, ta fada tinanin abinda ya faru jiya tsakaninta da Mahmoud ne yake dawo mata, kai tasha albarka jiya ba sunan da ba’a kirata dashi ba. My zumah My tea cup My fried rice My stew My jallop rice Kai ita kam wasu kunya ma suka bata, tayi yar dariya ta jin dadi, Ashe haka aure yake, kai Allah dai ya basu zaman lafiya. Dai-Dai nan taga su humaida a gabanta sai huci sukeyi, cikin daga murya humaida tace ” munafukar banza munafukar wofi, yau k’aryarki ya k’ari ai” Zuhra ta cafe “ni abinda yabani mamaki irin yadda ya mahmoud keyi mata a Daren jiya, yau sai kin yabawa aya zak’inta.” Ba bata lokaci suka ciru SUPER GLUE daga jikinsu, “inda ya shiga har ya rude nan zamu toshe yau” cewar humaida. Cikin zare ido jalila ta mik’e zata gudu jikinta ko’ina rawa yakeyi, k’afa suka sa suka tadeta, tafadi kasan dakin, zuhra ta hayeta ta dafe, humaida na k’ok’arin bude kafafuwanta……..!!!!! Maryam alk’ali { Mermue } MATA UKU GOBARA 71-75 Innalillahi wa’ina ilaihi rahi’un ita JALILA ta fara maimatawa cikin wani irin yanayi, inda ita kowa humaida sai k’ok’arin bude mata k’afafuwa takeyi, ita kuwa zuhra sai faman danneta takeyi, ta cigaba da maimaita addu’ar da idan fitina ta sameka musulunci yayi mana nuni da yinta. “Me zan gani….???” Mahmoud ne yafada haka da k’arfi cikin daga murya, tuni zuhra da humaida sun saki jalila cikin tsammani da rashin sanin inda zasuyi, ganin Mahmoud datayi tuni ta mik’e da gudunta ta shige jikinsa, ta saki wani irin kuka, ko’ina ilahirin jikinta rawa yakeyi. Mahmoud kallon mamaki yake masu, cikin tsawa yace “menene kukayi mata??” Humaida ta rik’e k’ugu sai girgiza takeyi, ta manna masa wata uwar harara, “abinda kaga munayi mana” Kallon zuhra yayi wadda tayi turu-turu da ido sai mazurai takeyi yace “ke! Gayamin me kuka yiwa MY SUGAR…!! Cikin inda-inda tace ” ba Anty humaida bace ta samu SUPER GLUE wai zamu tosheta.” A firgice yake k’are masu kallo masu, “lalle kun nuna min yau baku da mutunci,kashin kai zakuyi kenan, toh ba agidana ba..!” Da sauri yaje kan bed side drawer ya dauku wayarsa, wadda dama itace ya manta yadawo d’auka ya tarar da wannan aika-aikar. Har yanxu yana rungume da ita, yana lallashinta tare da jijjigata kamar baby, ita kuma sai kuka takeyi k’asa-k’asa, inda su humaida suke tsayi kamar mutum-mutumi. Ya kara wayarsa a kunne ” Assalamu Alaikum alhaji barka da wuni.” Ya dan rusuna kamar yana gabansa, dayan gefen aka karba masa, cikin tashin hankali Mahmoud ya zayyanewa uban humaida abinda ya tarar suna aikatawa, tuni alhaji ya fara sallalame yace gaya nan. K’ara kara wayar yayi cikin murya kamar yasaki kuka ya gayawa hajiyarshi abinda su zuhra ya tarar dasu zasu aikata, itama hajiya ta kad’u ainun, tace gata nan, yanxu zata zo tare da family. Tuni idonsu humaida ya raina fata, kamar su saki fitsari a wando, inda shikuwa mahmoud sai lallashin JALILA yakeyi tana k’ara barkewa da kuka idan ta tuna abinda kishiyoyinta suka tashi yi mata, k’ila da yanxu ta mutu, ko tana shure- shurenta. Cikin kuka ta lalubu wayarta, tana zayyanewa antynta abinda ya faru, da sauri mahmoud ya k’wace wayar tare da cema antynta su kwantar da hankalinsu za’a dauke hukuncin da ya dace. Palonsu ya cika dam, kowa sai mamakin iskancinsu humaida sukayi, wasu sunce su kam basu tab’a jin wannan salon ba, abban humaida kamar yayi mata duka, sai kumfar baki yakeyi, ya cewa humaida “duk ta sake Mahmoud ya sawwak’e mata to ba gidansa.!” Jin hakan jikin humaida yayi matuk’ar kad’uwa. Inda ita kam yan uwan zuhra sai hakuri suke bawa Mahmoud suna cewa “hannunka baya rub’ewa kayanke kayar” mahmoud cikin ransa yace “kaji tsiyar auren zumunci, ba’a tab’a bari kadau mataki.” Sai yan uwan jalila an basu hakuri tare da d’aukar alkwari ba abinda zai samu yarsu in shaa Allah, domin su humaida anja masu kunne sosai, cewar duk abinda yasamu jalila toh sune. Ahaka taron ya watse. BAYAN SATI DAYA Mahmoud ya samu kwanciyar hankali wanda har ya cire ran samu a rayuwarshi, duk buk’atunsa kaf JALILARSA ta dauke. Yau tafita girki Mahmoud kamar maraya yake jin kansa. Ita kam yar dariyarta takeyi tana k’ara bashi k’arfin gwuiwa, domin tana son mijinta ya zamu adali. Amma itama tana jin jiki, daurewa kawai takeyi, wani irin kishi ke turnok’uta amma daure takeyi tana korar shaidan. humaida ta karb’e girki sun sha jagalgalu a zuwan wai girki ne, su humaida manya, dare nayi aka kwashi jiki zuwa dakin miji, daga ita dai sai d’auren k’irjinta, ba laifi yau tayi wanka, amma fa ba turare balle kayan bacci, haka aka tafi…..!!! Ko ya za’a kwashe oho Maryam alkali ( Mermue ) MATA UKU GOBARA 76-80 Tura dakin tayi da k’arfi ta shiga ba sallama, Mahmoud sai da ya zabura irin yanayin yadda ta bude k’ofar, bai ce da ita komai ba, ta haye saman gado ta shige bargon da yake, batace masa ba, ganin ta k’yalesa shima ya k’yaleta. Wata zuciyar ke tunatar dashi, cewar ya kwatanta adalci, yanxu yasan da jalilarsa CE ba zai kyalleta ba, kuma yana son yayi adalci a tsakanin matansa. Ai kam humaida tanajin salo ya canja ta mik’e ” nawa zaka biyani, domin ni ba banza bace, hehehehe wai ina amaryar taka ne?, ance dai da tsohuwar Zuma ake magani.” Da mamaki yace “wani irin biya humaida sai kace na dauku karuwa, alhalin ke halalina CE, kuma matata da kike kira ai duk inada hak’k’i akanku, kuma kunada akaina…!” “Oho dai! ni dai ba baiwa bace, hala kamanta duk wulakancin da kayi mana a baya, ai nayi maka sauk’i Mah.” Ransa ya bace ya kyaleta, yayi kwanciyarsa, ita bata san don yana son yin adalci ne shiyasa ya nemeta, ita kuwa har da saka dogon buri. Can tsakar dare taji ba sauk’i dole ta neme sa, ta bada kai bori ya hau. Amma sai me?? Wani irin d’oye ya cika dakin, mahmoud ya kunna wuta, ya kira sunanta ” humaida! Kinga abinda kika janyuwa kanki wurin bak’ar k’azantarki??” Tana yatsina tace “me fa?” “Kinji yadda dakin nan ya canja, alhalin da ba haka kike ba?? ” “OK, kana nufin gabana d’oye yake fitarwa??” Ya daga mata kai ahankali. Da k’arfi ta mik’e “Allah ya isa, tunda kaci moriyar ganga ai dole ka yada gaurunta.” ” tunda kayi Amarya ba sharri da bazaka yi mana ba.” Ta dirku daga saman gado, ta bar dakin tare da doko k’ofa. Da kuka ta shiga dakinta, itama fa taji wannan canjen, amma ai wannan wulakanci ne mahmoud yayi mata, don yayi Amarya, dama namiji ba dan goyo bane, tayi kwafa, tare da yin kwanciyarta, Wankan ma nafasa saida safe zanyi. Dan rainin hankali kawai. ( kun ji fa masu karatu, ana so Ku baki samu yin wanka ba, toh ki wanke gabanki da ruwa masu dumi, kiyi alwala, domin samun kariya.) Da safe haka tak’i fitowa tayi abin karin kumallu, mahmoud haka yafita bai karya ba, jalila da zUhra sun fito sun samuwa Kansu abinda zasu ci… Zuhra tuni tafada dakin humaida, ba b’ata lokaci humaida ta kora mata zancen jiya tsakaninta da mahmoud. Zuhra ta rik’e baki “ki barni dashi yau ai nice dashi, zan gyara masa zama. “Hmmmmm, da zaki bi shawarata kar ma kije” “kibari kawai naje Anty humaida” “Allah ya kaimu.” *************** Zuhra CE ke fitowa daga dakinta, cikin Riga da zani na atamfa red, ta kashe d’auri, sai k’amshi takeyi, teburin cin abinci an cikashi dam! Da cima kala-kala, mahmoud kawai ake jira ya dawo massalaci, JaLila kam yar dariyarta takeyi tana waya da antynta tana k’ara mata shawarwari, ita kuwa zuhra sai aika sak’on harara take mata. Mahmoud ya shigo aka hau table, sai satar kallon jalila yakeyi, domin kayan datake sanye dasu bai tab’a ganin an saka irinsu agidansa ba, wando skinny black da yar top iya cinya orange mai adon black gabanta sune jikinta, ta tufkec kanta da yasha k’ananu kalaba, ta watsu wasu a fuska, sai cin abincinta takeyi cike da yanga, tanayi tana kora lemu a glass cup kamar bata so,tana yanje silalan kalabanta da suke rufe mata fuska, mahmoud yaji kamar yaje ya rungumeta tayi masa kyau ainun. Lura da haka da zuhra tayi ta fara tsaki, ta mik’e tabar wurin, haka ma humaida ta mik’e tana wak’e-wak’enta na habaici, tanayi tana gyara daurin k’irjinta. (Ahayye! Ance da karuwar gida gamma ta waje, domin dai k’azantar da baka gani ba tsafta CE…!!! ) Ba wanda ya kulata cikin so, domin basu masan tanayi ba. Kamar jira yakeyi, ya tasu yadawo wurinta, “oh MY jallop rice u look so take away” Ta kashe masa ido daya tare da yar dariyar Jan hankali, “kwalliyar ai taka CE ZUMANAH, kai nayiwa kai kadai.” Kansa ya k’ara fasuwa, sai wage baki yakeyi, ta mik’e tana kwarkwasa, mazaunan sai juyawa sukeyi ta basa sumba a kumatu tare cewa “night dear” Ta watsa yan yatsunta, ya bita da kallo kamar wawa, ko’ina jikinta rangaji yakeyi kamar bishiya. Ba mai san ta shige daki ba, sai da yaji zUhra akansa tana huci, “toh na-mamajo sarkin son mata, sai katashi mu tafi ai ta shige, kai mu dai an auru mana jaraba, yarinya kamar arniya wannan shiga ko church zata ai sai haka…!” Mahmoud murmushi kawai yakeyi, yace “yarinya ba kisan dawar garin bane, Komai kika CE bana ganin laifinki.” Yana kaiwa nan ya shige dakinsa yayi shirin kwanciya, sai gata ta shigo cikin Riga da wando na bacci, wandon har ijiyar sawu Riga har ta wuce gwuiwa, da dan hijab dinta. Ta cire hijab dinta sai k’amshi takeyi, ta kwanta kusa da mahmoud tana cika tana batsewa, mahmoud shikam abin dariya yabasa, amma ya rik’e abarsa. Can taji shiru mahmoud bai CE komai ba, kawai tasa kuka, mahmoud yayi ta lallashi amma fir tak’i fadar meye. Taga ba sarki sai Allah, dole ta fada, ta rad’a masa a kunne, ai kuwa me mahmoud zaiyi idan ba dariya ba, ai tuni ta hau sabon fushi, ba shiri ya dawo sabon lallashi, tuni harka ta canja salo, amma tunda aka fara ZUHRA ko tari batayi ba ballantana k’ok’k’aran motsi. Mahmoud yana gamawa kawai ta juya ta bashi baya ta hau baccinta. Bak’in ciki kamar ya kashe Mahmoud. Da safe ta fito ta gyara ko’ina sai ta hada break fast, mahmoud ya fito a kusan tare shida jalila, taci wanka ciki wata have fitted gown na material maroun, tayi kyau har ta gaji, tuni mahmoud ya manta da bak’inci da yake ciki… K’ak’arin amai sukaji a dakin humaida kamar ranta zai fita, da sauri sukayi dakinta…..!!! Maryam alkali (Mermue ) MATA UKU GOBARA 81-85 Amai take ta kwarawa a galabaice, amma sun ja sunyi turus! Sakamakon warin dakinta da bayinta, mahmoud yayi k’arfin Hali shiga bayinta, ya kamata ya rik’e yana tambayarta “meke damunki humy?” Tana kwara amai tana amsa masa, “wlh honey nima ban sani ba, kawai yau na tashi zuciyanah sai tashi takeyi, sai ga wannan fitinannin amai.” Tana kaiwa nan ta juyu tana b’allawa JALILA harara, mahmoud ya gyara mata jiki ya fito da ita, tayi lamo ajikinsa, cikin sakin fuska jalila ta fara magana ” HABEEBE ina ga gwanda kawai mu kaita asibiti, tanajin jiki.” Mahmoud yace “haka za’ayi HABEEBIYA.” Ya waiga gefen zuhra “ki kimtsata Ku fito muje asibitin” ta karb’a fuska ba yabo ba fallasa, sai harara suke aikawa jalila kamar sa zazzage idonsu. Ita kam murmushi kawai take sambad’a masu.har suka fice dakin ita da mahmoud, sai sannu take zubawa. Kai tsayi usmanu Dan fodio teaching hospital (uduth) suka nufa da ita, G.O.P.D kai tsayi suka nufa, bayan ta samu ganin likita an aiwatar da duk gwajen-gwajen da za’ayi aka gano tana da shigar ciki, hohoho Ku zo kuga murna wurin mahmoud kamar ya taka rawa, haka suka d’ungumu suka dawo gida cike da sharuddan da likita ya gindaya mata tare da magunguna. A hanya mahmoud sai waya yakeyi yana sanar da mutane, isarsu gida keda wuya mutane suka fara zuwa duba jikin humaida, danginta Dana mahmoud, gida ya cika sai murna akeyi, inda JALILA keta d’awainiya da mutane, itakam zuhra yak’e kawai ta keyi amma ita kam ta so itace ta samu cikin nan, yadda taga Mahmoud yana murna nan taso itace keda abin arzikin nan. A haka rayuwa tayi ta tafiya, humaida kam k’azanta ta k’aru da lalace, yanzu sai tayi sati biyu batayi wanka ba, wai bata son warin sabulun wanka da man shafawa, wari takeyi sosai, dakinta ma haka, ko’ina tsartar da yawu takeyi, duk ta b’ata fentin gidan, ranar girkinta haka take kwaba girki daga kafitar da k’aton kyankyasu sai kuwa kiyashi, wai ita kasala tayi mata yawa, kan tagama girki tana kwanciya d’ari, ko turare ta hana sawa a parlour bata son k’ashin komai. Haka su jalila ke hakuri da ita, ba abinda takeyi sai chatting dinta, shikam bata gajiya dashi, inda anan ne ta had’u da Maman abdul-shakur a wani group, jin ance mata marubuciya CE yasata tabita private, daga gaisuwa ta fara zuba mata sirrin gidanta, wai ta bata shawara. Bayan dogoyen tambayoyin da m shakur tayi mata ta ganu bakin zare, dariya kawai tayi tace mata kar tadamu zata zo itada yan uwanta TASKAR MARUBUTA idan sun tsaida rana zata gaya mata. Humy sai washe bakiyi akeyi angayar marubuta zasu zo gidanta. Yau ya kama girkin jalila ne, ta kammala komai ta gyara ko’ina, abincin mahmoud ta dauka ta kai masa dakinsa saman centre table ta Jere, domin gidan yanxu ba mai cin abinci a Palo, humaida sai tayi ta tsargin yawu ko’ina, ta rufe dakin taje dakinta ta k’ara shiryawa cikin wata arniyar top spaghetty pink colour da dan gun-short iya Rabin cinya black mai ado pink, ta raba gashinta biyu kowanne tasa masa ribbon mai Teddy pink, ta k’ara feshe jinkinta da turaren Arabians, ta dauku abayarta ta saka saman kayanta, ta yafa mayafin abayar, ta dauko dan ket dinta Wanda kayan baccin ke ciki da kayan da zata da safe, ta rufe dakinta sai na mahmoud. Tana shiga dakinsa ta yaye bed sheet dinda ke kan gadon, ta dauku wani wankakke ta shimfida, ta d’ame gadon tas,tasa turaren yayyafawa, taje a washing machine dake toilet din dakin ta wanke wancan tas taje ta shanyu ta dawo. Zare abayarta tayi tare da hayewa gadon, ta dauku cup dinta cike da zogalenta da tayi blending d’azo tasa madara da Zuma, ta hau kurba a hankali dadinta na ratsata. Dai-dai nan mahmoud ya shigo, tsaye yayi yana kallonta, ta kuma masa kamar wata baturiya ko yar Nigerian film, kai idan ka ganta bazakace tana jin zo ba, hannuwa sama ya daga yana godewa Allah. Daga bisani ya k’arasa cikin dakin, tana ganinsa ta ajiye cup din ta daka tsalle tazo ta mak’alk’aleshi, tana welcoming dinsa tare da wani hot kiss, yana dariya ya k’arasa bakin gadonsa da ita. Jansa tayi har toilet ta nuna masa ruwan wankan data hada masa, ta tayasa wankan suka fito, boxer da singlet ta bashi yasaka, ta fesa masa body spray da tirare, ta ciko plate dam da girkinta, ta mik’a masa, tare da gwanda jiluice din da yayi sanyi ga kaure kamar ice-cream, ba bata lokaci ya fara ci, tas ya cinye ya ajiye plate,tare da cup. ya fara lek’on cup dinta, cikin dariya tace “zogale ne Idan zaka sha maganin wanki Jini ne” Ya k’arba yasha ya bata, yana dariya yace “my STEW Kedai komai kin iya, harda magani kin iya hadawa kuma” Kashe masa ido tayi tare da gwalo, eyeeeee “ni, kike tsokana” zai cafkuta ta mik’e ta fara zagaya dakin, shima ya bita suka fara zagaye dakin suna dariya, saida ta gaji sannan ta bari yakamata, tace takalminta ne dayake hill sosai shiyasa ya kamata. gani kawai sukayi an Banko k’ofar dakin da k’arfi…..!!! Ko waye oho? Maryam alkali (Mermue ) MATA UKU GOBARA 86-90 Shigowa sukayi kowacce hannunta a k’ugu suna girgiza, kallon mamaki Mahmoud da jalila suka bisu dashi, cikin k’arfin Hali Mahmoud ya dubisu tare da cewa “lafiya kuka shigo min daki haka da k’arfi kamar wani mugun Abu ya biyuku?” Humaida ta banka masa harara tace “ai gwanda wani mugun abun ya biyumu da wannan rashin adalcin da ake mana”. Zare ido Mahmoud yayi yace “wani rashin adalci humy nayi maku?” Sai lokacin zuhra ta karbe “au baka San ma abinda kayi mana, lalle guy din nan ka rainamu” Kallon mamaki yabita dashi, ita kam jalila tuni ta hau gado abinta ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya tana kurbar zogalenta a hankali tana murmushi, tana k’are masu kallo. “Yanzu dan Allah Mahmoud tunda ka auremu ka tab’a shigewa d’aki da d’ayanmu kana wannan wasar ana dariya” cewar humaida. Zuhra ta cafe ” haba-haba wannan rashin adalcin dame yayi kama? ” ta nuna jalila dake wani lumshe idanu kamar mai jin bacci, “yanzu Dan Allah bazakayi mata fada irin wannan shigar datayi, irin ta fitsararrin turawa amma har ka biye mata kuka cika gida da ihu kamar yan k’wallo.” Dariya mahmoud yayi kamar cikinsa zai fashe, yafara cewa ” yanzu na ganoku kuce kawai kishi ne ke damunku, kunji haushi kunga muna irin abinda dayarku bata tab’a yi ba, toh ahir dinku, Ku fitar da idanku daga kanmu, idan kunji haushi ranar girkinku kuyi Wanda yafisa.” Ya nuna masu k’ofa, “leave!” Cikin harguwa yayi maganar, ” I said leave my room pls” sumi-sumi suka juya suna shirin ficewa, domin dai sun san halin gogan nasu yanzu ba’a kawu masa wargi. “Shashayen banza, kunyi sakaci wata tazo ta k’wace maku miji shine zaku zo kuna karanta min hauka.” Ganin ransa ya b’ace tuni jalila ta ajiye cup dinta, ta tasu tana rangwada ta basa kyakkwar runguma saida ya sauke ajiyar zuciya, yana rungume da ita ya k’arasa bakin k’ofa dai-dai nan su humy suka fice cike da k’onar rai, ya datse k’ofar tare da saka key. Aikuwa iya k’arfinsu suka zage suna dukan k’ofar kamar zasu karyata, dariya mahmoud da jalila suka saka lokaci daya. Jin motsi kamar mahmoud zai bude k’ofa sukayi, tuni kowacce ta gudu d’akinta suka rufe. ************ Yau Maman abudul-shakur tayiwa humaida waya zasu zo, sai murna takeyi, ta tashi ta Shiga kitchen ta rasa me zatayi masu, ta gaji da tsayuwarta tana dogon tinani tace bari tayi masut taliya kawai. Bayan ta kammala taliyar taje ta watsa ruwa haka nan ba sabulu don bata son warinsa, ta fito ba Shafa mai domin shima bata son warinsa, a sif dinta ta rasa kayan da zata saka su ganta da haske, haka ta hakura daga k’arshe ta d’auku wata exclusive dark blue da fari ta saka, zanin duk ya kod’e tare da dafewa, riga da dankwali fes dasu, haka ta sakasu duk sun cumuimuiyi kamar an kwatosu daga bakin kura, ta dawo Palo ta zauna tana chatting jira k’arasowarsu kawai takeyi. Tana nan zaune bayan ta turawa m shakur address ta fara jin dirin motoci, da Sauri ta mik’e tana lek’o ta window, manyan-manyan motoci data gani suna parking tuni murna ta kasheta, wata LAND CROUSER fara sol taga manyan mata na fitowa acikinta ahankali bayan tagama parking. Ta k’ara kallon gefe daya taga wata black RANGE RUBBER itama sai mata ke fitowa cike da nutsuwa, murna ta k’ara kashe humaida ganin cewar marubuta yau gasu a gidanta, wata motar ta k’ara tsayuwa kirar MORANO bayanta SIENA CE itama mata ne suke ta fitowa cikin shiga ta mutunci, ai da gudu humaida ta fito zuwa tarbarsu. Maryam alkali (Mermue ) MATA UKU GOBARA 91-95 Da gudunta ta k’arasa wurinsu, tana dariya ta nuna m-shakur dake cikin dakakkiyar shadda free gown ash colour taji surfani pink, tace kice! Hope na canka, dariya sauran sukayi suka CE u’re right, da rawar jiki ta k’arasa dasu cikin palo, sai murmushi kowa keyi, bayan su zazzauna angama gaishe- gaishe, m shakur ta mik’e tana introducing ‘yan uwanta marubuta. Ta nuna wata mace da tasha lullube har saman kai, tayi adonta das da ita, wannan itace Maman khadija, sai Ummi asha, wannan kowa meena dan musa, Benazir Omar, Jamila, Firdausi sodangi, lubiee, Anty YBK, Reporter, miemie bie, Anty aysha, Ummu samha, haneefa, kausar luv, Mrs saif, salma atiku, aysha, Nernerh, Romaysa, sai k’awata humaira. Bayan sun gama cin abinda zasu iya tabawa aka fara zanxen abinda yakaisu, Kowannensu fuskarsa cike da murmushi suke kallon humaida, itama bakinta kamar gonar auduga, ta karkace kai tare da kashi murya, “pls Anty kubani shawara mijina ya auru karuwa duk ta kwashe masa hankali.” Ta kwashe duk labarinta ta basu. Maman khadija ta fara “gaskiya humaida da laifinki baki San k’azanta duk yadda mijinka ke sonka indai kanayinta to kowa harka ta lalace.” Humaida sai zare ido takeyi, Ummi Aisha ta cafe ” gaskiya kinga ko wurin girki kinada Matsala.” Anty ybk tace “humaida kinsan me? Shi namiji dan tattali ne, duk mai faranta masa zai kuma masa kamar wawa, sai ki dauka an magancesa ne ko karuwa CE kamar yadda kika CE.” Benaziratu tace ” kinsan me humaida ki gwada shawarwarin da zamu baki kiga shin harkar ta maganice ko kowa tsabagin kyautatawa Miji CE.” Humaida kam sai daga kai takeyi kamar k’ad’angaruwa. Mrs saif tace ” yiwa miji bala’i bashi zaisa ya tsoraci kiba, ko ya k’ara sonki hasali ma sai dai ya k’ara k’inki, dafatar yanzu zaki bude kunnenki kiji kuma ki sauraremu tare da fahimtarmu.” Humaida ta daga kai fuskarta kalar tausayi. Sai sannan Maman Abdul-shakur tasa baki ” yanzu humaida ki duba kayan jikinki shin ya akayi Riga da dan kwali yafi haske fiye da zani?” Humaida tayi sauri ta dube kayanta, ita fa bata lura ba, sai yanzu, ashe shiyasa duk ta fita unguwa aketa kallonta, ita kam sai dai tayita hura hanci, tadauka duk ta bada kala ne, Ashe abin ba haka yake ba…! Ajiyar zuciya ta sauki, tace “inaga don ina daurin k’irji da zanin ne” kamar zatayi kuka tayi maganar, kausar luv tace ” kinga ko awurin dressing bakya yi, saboda Allah me zai hana mijinki ya k’ara aure” Anty lubie tace ” ko kwalliya fa humaida kowacce da lokacinda yadace keyita, misali idan mijinki zai dawo da yamma kinyi wankanki kinyi light make up kina zuba k’amshi cikin kaya masu Nuna surar jikinki yadda zaki tak’alu masa sha’awarsa, haka nan da dare kishige cikin kayan baccinki wadanda suda babu duk daya! Kina zuba k’amshi ki nufi dakin oganki.” Ido da kunne humaida ta gwalalo tana saurarensu, Anty aysha ta cigaba, ” idan kinji dakinsa kin tabbatar kin gyara dakin tsaf! Sai k’amshi yake fitarwa.” Reporter ta amshe ” a gado ki ajiye kunya, karki zama irin Matan nan masu kunyar miji wadda ke cutarsu, ko kice ajina zai zube ne, ko kice bazan nemesa ba matuk’ar bai nemeni ba, ai idan nayi haka na zubar da class dina.” Maman khadija ta k’ara saka baki ” kuma akwai matanda komai basu tab’o kawa a gado sai su zube kamar kayan wanki, ke kya CE matattu ne, kul! Humaida karki zamu cikinsu, ko ace miji sai yabiyaki kuddi sannan zai kusanceki, narabaki! Ya riga ya biya sadakinki, ko sai kinga mijinki yana matse dake sannan ki dauku buk’atunki ki d’ora mai kisa yin alkwalin abinda ba zai iya ba, karki soma!” Humaida sai ga hawaye sharrrr! M shakur tasa tissue ta goge mata, Anty YBK tace ” duk Abinda kika San mijinki zai faranta masa a shimfida yi k’ok’ari kiyi masa, Allah ne zai baki lada, sannan zuciya nason mai kyautata mata, tabbas indai kina kyautatawa mijinki to shima zai kyautata miki.” Benazir ta k’ara cewa” da safe kitashi kiyi wankanki ki shirya cikin lace ko atamfa ko shadda ko material kiyi adonki kamar zaki gidan suna, yadda idan oga ya fita ba wata kwalliya da zai gani ta dauke masa hankali, ki gyara gida, kiyi break fast mai dadi, kije ki tada mijinki ki tayashi shiryawa, kizo ki bashi break fast dinsa, idan zai fita ki rakasa, tare da addu’a da kalaman soyayya da yar shagwaba to ba zai manta kiba bini-bini zai kiraki ya k’agu yadawo gida domin yasan abinda zai tarar. M-shakur tace “yanzu kinga akan dauren k’irjin da kikeyi nononwanki duk sun bace, ki nemu man kwakwa kina shafawa zasu tashi, kuma zasu cicciko, sannan na doyin gaba ki neme magarya tare bagaruwa ki tafasa ki sauke idan yayi dai-dai yanda zaki iya shiga ki juye kwalbar misk fari ki shiga, wurin zaiyi k’amshi tare tsantsi, zai tsuke kuma zaki bani labari.” Miemie bie tace ” tsafta fa sai an d’aure malama humaida, komai indai zaka d’aure to zakaga kayi, kidinga share gidanki kina gyarawa, kuma dan Allah kid’aure ko sau biyu ne kirik’a yin wanka da brush a wuni.” Humaida tace “in shaa Allah zan d’aure.” Humaira tace ” kidaina damuwa da kishiyoyinki, kidai kiyi harkar gabanki, ki rik’e gaskiya da adalci, kuma ki rik’e mijinki, kowaccenku gwargwadon farantawarta ga miji haka shima zai na rawar jiki da ita.” Ummu husna ta cigaba “bari nabaki sirri daya ki rik’e zogale, idan kimsamu zogalenki danya kiyi blending ki tace, kisa Zuma da mdara idan kika sha ni”ima da matsewa ba magana yar uwa, sannan daffafar zogale zaki soya da man zaitun tare da timatir da magi, kina ci kina korawa da ruwan da kika dafa zogalen hohoho, sannan ki tafasa minnnas da kaninfari kisa Zuma ki mayar dashi juice dinki keda oga.” Sai yanzu chuchu tayi magana tace “humaida kinsan ciki yana tare da laulayi pls ko kina laulayi ki rik’a daurewa komai ya kamata kiyi abinki ahankali kinayi kina hutawa, karki biyewa Mata masu lalace idan anayi ciki.” Wannan karun humy kai tad’aga, haka kowannensu yayi mata nasiha sannan sukayi mata sallama zasu wuce, humy sai washe baki akeyi. Bayan sun wuce humy ta dawo ta zauna apalo tana tinanin abubuwan dataji yau, ai tuni ta fara hawaye, saiga zuhra ta fito dakinta tace “Anty humaida wai bak’i kikayi naji hayaniyar mutane, kai ta d’aga mata alamar eh! Humy ta mik’e ta shige dakinta. Ku biyoni masu karatu muje humy zata canja kowa???? MATA UKU GOBARA 96-100 Tsayi take tana k’arewa dakin nata kallo, kamar na wata mahaukaciya, ko’ina shirgi ne, ta fara waige-waige ganin ta ina zata fara? Can ta nufi wurin drawer ta fara fitar da komai dake cikinta, kayanta ne gasu nan kamar an kwato bakin kura, ta ware masu Dan dama-dama da English wears dinta ta tsarasu a drawer, sauran ta kwasa ta saka hijab ta fita ta kaiwa baba Abu mai gadi ya bawa matarsa. K’ara dawowa tayi ta fara shara sai dustbin take cikawa tana kaiwa tana k’ara dawowa ta k’ara cikawa, canja zanin gado, bayan ta kammala sharar,tayi goge-goge a dakin duk abinda yayi k’ura sai da ta goge, ta zauna ta huta, kamar minti shabiyar ta tashi tayi mopping ta feshi dakinta da air freshener ta kunna Bonner tuni daki ya hau k’amshi. Toilet ta shige ta fara darzarshi sai da yayi tas, shima ta fesa masa tirare, sannan itama ta hada ruwan wanka, ta fara wanke gashinta da yake a tsefi, tayi ta wankewa tun bakin kumfa na fita har yadawo fari tas, sannan ta dauraye gashin. ta fara darzar jikinta da soso da sabulu, duk wani sak’o da lungu na jikinta inda ke ajiye datti har wurin ya fara wari kamar su tsakanin matse- matse da kasan nonowa da hammata duk sai da dirze iya k’arfinta, tanayi tana k’ak’arin amai amma haka ta daure tana toshe hanci, har jikinta yayi fes ta dauraye da ruwa tayi brush tare da kuskure bakinta da ruwa mai k’amshin mint, ta d’auru towel ta fito. Tuni taji iska ko’ina ya shigarta ya hudata, bayan ta tsani jikinta ta draying din gashinta da hand drayer, ta dauri ta dauku vassilene ta shafe jikinta domin bata son k’amshin lotion, wata gown yar kanti black mai hannun vest ta saka, tabi lafiyar gado tuni bacci yayi awon gaba da ita. ************** Wata had’ad’d’iyar matashiya CE ke kai komu tsakanin kitchen da dinning, cikin blue jeans pencil da yar top red,rabin cinya armless, fuskar nan tasha fenti-fenti na kwalliyar zamani, k’afanta sanyi cikin red plat shoes, gashi nan yasha gyara tayi parking tsakiyar kai da wani tafkeken rebbon blue, ta watsu wani gashi agaban fuska har yana rufe mata ido tana janyewa. Dan cikinta ya fito d’as dashi yayi mata kyau sosai, daga kitchen take fitowa zuwa dinning, tana jere abinci cikin warmers masu kyau, sai k’amshi take bad’awa, jin anyi hugging dinta ta baya ta juya da k’arfi don ganin waye???? Mahmoud cikin brown jeans da white T-shirt mai bottomgs a gaba tana da layi-layi brown, “oh my humy I really proud to have u” jin yafadi haka tuni ta hau kada ido abinda ke matuk’ar burge mahmoud, “me too my honey” ta furta a hankali, mahmoud sai washe baki yakeyi yana shafar cikin jikinta, yayinda humy sai rausaya akeyi, girke ne ta shirya masa hadadde mai rai da lafiya. Taje ta kira jalila da zuhra, jalila ta fito cikin mini skirt iya gwuiwa blue top dinta pink, sai k’amshi take zubawa, kan nan yasha kalaba ita dai tana son kalaba kuma tasan sirinta,( kuna so Ku sani masu karatu?) sai murmushi takeyi, sai ga zuhra ta fito cikin Riga da zani na atamfa an kashe d’aure, baki saki take kallon humaida da jalila ta tab’e Baki, daga bisani ta zo ta zauna. BAYAN SHEKARA 1 Competition sosai ake bugawa a gidan Mahmoud, tsakanin JALILA da HUMAIDA, kowannesu gani yakeyi gwani ne wurin iya kwalliya, sai buga game akeyi kowaccenta k’ok’arinta taga miji ita yafiso, while ita kam ZUHRA duk gani takeyi iskanci ne suke zubawa. Misalin k’arfe shida mahmoud ya shigo gidansa a gajiye, HUMY itada babynta Wanda aka sakawa sunan mahaifin mahmoud Usman Suna kiransa affan, sun sha wanka, humy cikin half gown iya gwuiwa ash and pink, ta yiwa babynta kwalliya cikin kaya farare sol, yayinda a gefe JALILA da cikinta cikin riga mai Dan fadi daga k’asa da wando skinny, tayi kyau sosai sai hajiya ZUHRA cikin leshe Riga da zani, an kafe d’aure, sai chewing gum ake tauna. Shigowa yayi gidansa kowacce da kalar kwalliyarta ya bisu da kallo, ransa k’al in bayan zuhra da tak’i canja Hali, shiyasa yake fushi da ita ko gefenta yak’i kallo, kuma ita keda girki, bayan ya rungume humy da jalila tare da sumbatarsu ya wuce dakinsa. Da gudu tayi dakinta tana kuka, bayan tayi mai isarta, ta janyu waya ta kira yayarta Maman abideen, tana kuka tana zayyane mata abinda mahmoud yayi mata, cikin fada ta fara magana “me na gaya maki zuhra rannar? Kina nufin baki dauka ba?” Cikin kuka tace “Anty wlh bazan iya wannan rashin kunya ba, ai iskanci ne da d’ibar albarka.” Ta daka mata tsawa ” yimin shiru wawiya kawai su sauran kishiyoyinki da suka yi iskancin me ya rage ajikinsu, yanzu zan k’ara turu maki text idan bakiyi ba, karki k’ara kirana.” Cikin 5 minute ta turu mata text, ba yadda ta iya haka taja jiki zuwa dakin Mahmoud yana ta cika yana batsewa, ta k’arasa wurinsa ta bashi hak’uri tare da alk’awarin zata gyara, sannan ya fito akayi dinner bayan ya dawo masallaci tare dax familynsa. K’warai mahmoud yayi makinta yadda ta ajiye kunya ta faranta masa a Daren, sai albarka yake sa mata, ita kam dad’i ya cikata, domin dai tana son mijinta kuma tana so tasakashi farin ciki a kodayaushe. ************* Lokaci yana tafiya kwanakinmu na k’arewa, a cikin haka ne gidan mahmoud ya zama “HAPPY FAMILY” matansa sun cika masa gida da yara inda HUMAIDA keda yara biyu affan da yusra, while zuhra nada daya sultan, jalila nada baby khairiyya kuma kowaccensu nayin iya bakin k’ok’arinta wurin faranta masa. Yau zai dawo daga tafiya kowaccensu ta tsoke,cikin shiga mai kyau, yaransu kuma sunyi masu kwalliya gwannin sha’awa. Ya shigo cike da zumudi, yana ta doka murmushi, matansa suka tarbesa cike da kulawa, da tsantsan soyayya, ya rungumesu yana dariya yace “ance MATA UKU GOBARA nidai ga nawa MATA UKU ZUMAH NE.” ALHAMDULILLAH !!! Anan na kawu karshen wannan buk mai suna MATA UKU GOBARA, Allah yasa mu amfana da abinda ke cike, inda nayi kuskure Allah ya yafemin. Sai mun hade a sabon littafina “WASWASI” (aikin shaidan) GODIYA |