The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar*
#1
? *Noorul Huda*?

19.....??

Ilham ta juya ta fita xuwa parlor tana kallonsa tace "Ya Abuu na bata hakurin" yace "And promise you two will be frnds daga yanxu" ta langwabar da kai tace "that's a promise, we re frnds now" yace "Good!" Murmushi tayi tace "Bye xamu tafi islamiyya" daga haka ta juya ta fita, bedroom ya shiga ya sameta tsaye har lkcn, ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kai tayi xata fita ya jawo ta yace "Ina xa ki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Gida xan koma" kallonta yayi daga sama har kasa murya can ciki yace "I love ur dressing...." Kwace kanta tayi ta fita da sauri, ya bi ta da ido, sai da ya ji fitar ta sannan ya fito parlor ya xauna ya bude abincin da ta kawo masa, pounded yam ya gani da vegetable soup yayi murmushi ya rufe warmer din hade da lumshe ido. Bayan kwana biyu yana xaune gaban gate da yamma yana danna waya sai dai da biyu yake xaune gun don for the past 3 dayz bai ga Samantha ba, duk ya koma kamar mara lafiya sai dai har kusan magrib bbu alamar ta. Washegari friday yana xaune office yana danne dannen laptop, tun xuwan sa hospital bbu patient din da yayi attending ma, aka kwankwasa kofarsa  ya bada izinin shigowa wata nurse ta shigo rike da file ta ajiye gabansa tace "Xaka duba patient sir" yace "Ohk" ba tare da ya dago ba, ta juya ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tare da wani mutumi da baxai wuce shekaru arba'in da bakwai ba, fari ne dogo da ganinsa ka ga bafulatani sbda kyansa, kallon mutumin Abuturrab yake har ya karaso ya xauna, suka gaisa Abuturrab ya bude file dinsa ya duba sunansa ya ga Mr David, kallonsa ya kuma yi sannan ya fara masa tambayoyi yana rubuce rubuce a white sheet dake cikin file din, sai da ya gama yayi gwaje gwajensa sannan ya koma ya zauna yace "Sir kana bukatan hutu sosai sbda bp dinka...." Mutumin yace "Toh xa a kiyaye, magunguna kawai nake so doctor" Abuturrab yayi murmushi yace "Da dai ka bari a hada da allura...." mutumin yace "No xan yi tafiya ne in 3 dayz" Abuturrab yace "Why not ka bari sai ka gama karban medication dinka, u need rest sir" mutumin ya girgixa kai yace "Tafiyar is urgent" Abutuurab yace "Ohk ba Abuja kake ba?" Mutumin yace "Nan nake" Abuturrab na son tambayarsa anguwar da yake amma ya rasa ta ya, bell ya danna don alerting din nurse, Mutumin yace "yanxun ma don family doc dina bai garin ne shi yasa na taho asibiti" Abuturrab ya dake yace "Ohk, wani anguwar kake?" Mutumin ya kallesa ya fada masa, Abuturrab yace "Ohk, nima anguwar nake kuwa, if you don't mind idan na dawo ltr sai in karasa in baka injections din, xan ma iya dinga xuwa can gidan ina baka medication din har ya kare, but that is if you are okay by that" mutumin yace "Alryt, am greatful Dr, ga digit dina sai ka kira ni" karban complimentary card dinsa yayi, ya kalli nurse din dake tsaye ya mika mata file din yace "Drugs only" daga haka Mr David ya mike yayi masa godiya ya fita, Abuturrab ya lumshe ido hade da murmushi murya can kasa yace "Samha's father!" 
Abuturrab na dawowa daga mosque da magrib ya dau mota ya tafi pharmacy ya siya drugs da allurai, ya jima xaune a motarsa bayan yayi parking a kofar gidansu Samantha, can ya dau wayarsa ya ciro complimentary card din da Mr David ya basa ya kwashe numbers din yayi dialing, sai da ya kusa katsewa ya dauka, mancewa Abuturrab yayi yace "Assalamu alaikum" daga daya bangaren Mr David yace "Yes, who's on the line?" Abuturrab ya ce "Ohh sorry, it's Doctor Aliyu... You remember?" Mr david yayi shiru, can yace "Ohh Doctor how you?" Abutturab yace "Am fine, am at ur premises, at the gate" Mr David yace "Ohk, you can come in...." Abuturrab yace "Alryt!" Daga haka ya katse wayar ya bude motar ya fito ya nufi gate ya bude ya shiga, gaisawa suka yi da mai gadi, mai gadin ya tambayesa wanda yake nema yace mai gidan ya kuma sanar da shi he's a doctor, har kofar da xai sada shi da main parlor din gidan mai gadin ya kai sa, mai aikin gidan ce ta bude kofar, ta gaida Abuturrab ya amsa ya shiga parlon yace "Ki yi ma mai gidan magana, you tell him his doctor is around" sama ta nufa ta bar sa nn tsaye yana kare ma makeken parlon da ya tsaru da kayan alatu, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Yace ka tafi dakinsa" yace "ohk" kitchen ta wuce shi kuma ya wuce sama da sauri ya juyo tunawa da yayi bai san bedroom din ba ya ga har ta shige kitchen, kamar me tsoron staircases din haka ya dinga taka su har ya isa sama ya tsaya yana bin corridor din rooms din da kallo, bude wani kofa aka yi samantha ta fito sanye da mini skirt fari sai vest hannunta rike da system, still tayi inda take tana kallonsa da mamaki kuma a tsorace, ya wara mata manyan idanuwansa yana murmushin sa mai kyau yace "Sweetheart!" Bude kofa aka yi Dad dinta ya fito, da sauri ta juya ta koma cikin daki, Abuturrab yace "Good evening sir" Murmushi dauke fuskarsa yace "Welcome Doctor, shigo" bin bayansa Abuturrab yayi suka shiga dakinsa, bbu 6ata lkci cikin minti sha biyar Abuturrab yayi abinda ya kawo sa, Mr David ya dauko dubu ashirin a take ya basa, yana shafa kai yace "No sir, sae na gama treatment din" Mr David yace "Alryt, na gode kwarai, a ina kake a nan anguwar?" Abuturrab yace "Just few houses away bbu nisa" hannu Mr David ya basa ya kuma yi masa godiya yace "Yaushe xa ka xo gobe don xan fita" Abuturrab yace "May be da yamma idan na dawo daga gun aiki" Mr David yace "Alryt, xaka taho ma Daughter na da Malaria drugs" Abuturrab yace "How old is she? Tayi test ne?" Girgixa kai yayi yace "No, ba ayi test ba, but i guess it's malaria, she's 19...." Abuturrab yace "Ohk, tana kusa ne?" Mr David yace "Yes, bari in kirata" daga haka ya fita, bayan yan mintuna ya dawo dakin, bai jima da shigowa ba Samantha ta shigo, wannan karan sanye take da doguwar riga, bata bari sun hada ido da Abuturrab dake ta kallonta ba, Mr David yace "Gata" Abuturrab yace "Sannu...." Satan kallonsa tayi tace "Ina yini" yace "Lafiya, how are you feeling, i mean ina ke maki ciwo?" Ba tare da ta kallesa ba still tana fidgeting fingers dinta tace "Ciwon kai!" Yace "Just ciwon kai?" Shiru tayi sai kuma tace "Ina amai kuma" yace "Amma kina cin abinci?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa suka yi ido hudu, kasa daina kallonta yayi ganin yanda ta rame, ta sunkuyar da kanta da sauri, shima ya dauke kai yace "Me yasa ba ku je asibiti ba sir?" Mr David yace "Ta ki yarda babu yanda uwarta bata yi su je ba ta ki" Abuturrab yace "Ohk xan kawo mata magani gobe, but still ya kamata ayi test" Mr David yace "Alryt thank you doctor ko gobe sai ayi test din...." Sallama Abuturrab yayi masa ya ya kuma kallonta ita ma kallonsa take ya nufi kofa ya fita, Blessing na parlor har ya kai kofar fita ya juyo ya ciro biro aljihinsa da takarda yayi rubutu ya ciro kudi ya hada snn ya karasa kusa da ita yace "Hello, plss ki ba Samantha, plss" kallonsa tayi ta kalli kudin sannan ta karba tace "Toh xan bata" fita yayi yana tunanin anya hakan da yayi ya kamata don bai ma san halin yarinyar ba, yana isa gida ya xauna parlor ya jinginar da kai jikin kujera ya lumshe ido. Samantha na xaune daki tayi shiru tana tunanin yanda Abbanta yasan Abuturrab blessing ta shigo tace "Sister Rebecca, the doctor gave me this to give you, ya hada har da kudi ya ban" da sauri Samantha ta karba tace "Ohk ohk, don't say anything about it blessing" kudin ta mika mata Samantha tace "A'a tafi da shi" tana fita Samantha ta bude takardar ta karanta content din "Plss plss ki xo gida yanxu am waiting, don't ignore dear" 

*Haske writers asso*?✍?

? *Noorul Huda*?

20.....

Ta koma ta kwanta a hankali, can kuma ta mike xaune tayi tagumi, to ko taje ne, tunanin da take kenan, kawai ta mike ta kashe wutan dakinta ta bude kofa a hankali ta fita, blessing na parlor ta karasa kusa da ita tace "Blessing idan Abba ya kirani kice masa nayi bacci" Blessing tace "Toh" kamar munafuka ta fita gidan ta dau hanyar gidansu Abuturrab, a hankali ta tura gate ta shiga ta karasa balcony ta bude kofar parlor ta shiga, mikewa yayi yana kallonta ya nufeta yayi murmushi yace "Thanks dear!" Ta langwabar da kai tace "What's the call about?" Hannu ya sa a goshinta yaji xafi yace "Tun yaushe ne baki da lafiya?"  A hankali tace "Since" ya kamo hannunta da damuwa yace "And you didn't tell me, wani maganin kike sha?" Janye hannunta tayi tace "How did you know my dad?" Murmushi yayi yace "Kin raina kitaba ta ne?" Bata ce komai ba, ya kama hannunta ya xaunar da ita kan kujera yace am coming, bin sa tayi da kallo ya shiga daki, can ya fito rike da stethoscope da thermometer, ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallon kirjinta murya can kasa yace "how will i get to ur chest?" Ta masa wani kallo tace "What?" Murmushi yayi yace "Yeah, i want to use my stethoscope on u!" Tace "Toh bana so!" Wani kallo ya mata ya jawo ta kusa da shi ta xaro ido xata yi magana taji hannunsa a bayanta, a hankali ya xuge xip din ya sauke doguwar rigar kasa ya rage farin vest din jikinta, wani kallo take masa xata yi magana ya daura fingers dinsa guda biyu a lips dinta yana kallon cikin oily eyes dinta, daukar stethoscope din yayi ya makala a kunne, snn ya daga vest din a hankali ya   manna daga kasan kirjinta, lumshe ido tayi, shi ko sai kallonta yake, can ya lumshe nasa idon ya cire instrument din ya ajiye ya sauke vest din, ya mayar mata da rigarta ya ja zip ya mike, sai a snn ta bude ido taga daki ya wuce, ba a dau lkci ba ya dawo da magunguna har da allura, tana ganin haka tace "Baxan karba allura ba" bai tanka taba ya xauna ya gama hada alluran snn yace "Kin shirya" bai jira tace komai ba ya mike yana kallonta yace "Am waiting" kamar xata yi kuka tace "Ni bana so nace" hade rai yayi ya dago ta, bata ankara ba sai ji tayi yana kkrin daga mata riga tace "Noooo" ya wani daure fuska yace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Doctor there's nothing inside, just..." Dariya ta basa ya dake yace "Then???" Bata ce komai ba ta marairaice tana kallonsa, yace "Ohk Alryt!" Kama hannunta yayi ya isa gun switch din wutan ya kashe, duhu ya gauraye parlon, ya daga rigar gaba daya tace "Doctorrrr..." Dafa bango tayi ta runtse ido jikinta na rawa, har ta ji ya xare alluran, bata ankara ba taji ya rungumeta ta baya ya daura kansa a shoulder dinta murya can kasa "Get well soon wife" bude ido tayi da sauri, ya juyo da ita yana kallonta cikin duhun yace "Ki bar wahalar da ni Samha, stop pretending you don't know where i am heading, i know you know....." Rungumeta yayi cikin sanyin murya yace "I love you!" Ita dai bata iya tace komai ba, ya matse ta jikinsa yace "Kice abu mana dear, talk plsss" kamar mara lafiya yayi maganan, ta lumshe ido a hankali tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa, harde hannunta yayi da na shi murya can kasa yace "Talk plss, say something Samha" ta rasa abinda xata ce, shafa bayanta ya fara yi a hankali ya kai bakinsa wuyanta, ta bude ido da sauri jin saukan numfashinsa a jikinta, lkci daya jikinta ya dau rawa da kyar tace "Doctor stop pls...." Cikin kasalalliyar murya yace "Talk! second love" Ta kuma runtse ido jin ya ki dauke lips dinsa a wuyanta, murya can kasa tace "I... I... I... Love you tooo" wara ido yayi ya saketa yace "Da gaske baby??" Ja baya ta dinga yi kawai sai gani yyi ta juya a guje ta nufi kofa ta bude ta fice. Washegari asabar da yamma Abuturrab ya iso gidan Mr David da da magungunan da xai ba Samantha jiya ta gudu, Mumy ya tarar xaune parlor tare da Mr David din bayan an masa izinin shigowa ya gaisheta ta dinga masa wani kallon mamaki, Mr David ya mike yace "Likitan da nake fadi maki kenan" daga haka yace ma Abuturrab ya taho sama, Abuturab ya bi bayansa suka wuce saman, yau ma bbu wani 6ata lkci ya gama basa medication din, ya tambayi samantha, Mr David yace ta tafi church, shiru Abuturrab yyi sai kuma yace "But da ta hakura har ta samu sauki" mika masa magungunanta yayi, yayi masa sallama ya fita, Sai da ya isa kofar fita sannan ya juya ya kalli Mahaifiyar Samantha ya ga kallonsa take yi, yace "Sae da safe Ma!" Wani kallo tayi masa ta mike fuu ta wuce sama, yayi murmushi ya fita, a bakin gate ya hadu da samantha, tana ganinsa ta koma baya da sauri, motarsa ya nufa ya tsaya ya rungume hannayensa yana kallonta har xata shiga gate sai kuma ta tsaya ta d'an saci kallonsa taga idonsa na kanta, kamar mai counting step ta nufi inda yake ta tsaya nesa da shi, tace "Good evening!" Yace "Da wucewa xa kiyi?" Kallonsa tayi suka hada ido tayi murmushi ta girgixa kai, ya lumshe ido yace "Come here" tace "Ba gani ba?" Ya harareta ya nuna mata gabansa, kamar xata yi kuka tace "Kaga daga church fa nake, am tired! Am feeling dizzy" Yace "To tafi...." Shiru tayi tana kallonsa, can ta karaso gabansa a hankali tace "Gani" dago kanta yayi yana kallon kwayar idonta yace "Me yasa kika fita baki da lafiya?" Ta sauke idonta tace "I went to church, Mumy tace in je" Wani kallo yayi mata yace "To daga yau kar ki sake xuwa har sai kin samu lafiya...." Ta xaro ido, ya gyada kai yace "yes I mean it...." Tace "to ae addu'a ake min a can ma" ya tabe baki yace "Good sai kiyi ta xuwa...." Kallonsa ta tsaya yi, ya juya ya bude motarsa ya shiga ya tada, ta lumshe ido ta bude tace "Ohk ohk, baxan je ba kuma" hararanta yayi, tayi kamar xata yi kuka tace "I mean it baxan je ba...." Yace "Better! Taho ki ji" karasawa tayi kusa da glass din motar tace "Mene?" Yace "Matso mana" matsowa tayi, dai dai kunnenta yace "Drugs dinki da prescription na gun Abba, you make sure you take all before going to bed, since you ran away yesterday....." Bata jira ya karasa ba ta juya da sauri don gaba daya ta mance da incident din jiya, ya rikota da sauri ya jawota yayi planting mata kiss a cute lips dinta, ta kwace kanta da gudu ta shiga gida. Ranan litinin Samantha ta kare exams dinta na Waec, karfe uku driver ya je dauko ta a sch, kamar ko da yaushe a bakin layi ya ajiyeta ta karasa wai xai je kasuwa Mumy ta aikesa, tana isa dai dai gidansu Abuturrab ta ga motarsa a waje, ta tsaya tana kallon gate din ko me ta tuna kuma ta fasa shiga xata wuce aka bude gate, sai ga shi ya fito, wara ido yayi ganinta yace "Ina kuma xa ki?" Tace "Wucewa nake yi ai" yace "Uhm, i see yaushe xa ku gama waec din?" Tace "Mun gama" yace "Waow da gaske baby, but shine baki fada min ba?" Ta langwabar da kai tace "Gashi na gaya ma!" Yace "Alryt... Plss ki xo anjima da yamma i have a surprise for you, yanxu xan tafi gun aiki ne i forgot my office key...." Tace "Baxa a bar ni in fito ba...." Xai yi magana aka bude gate sai ga Mami ta fito, gaba daya ya mance tace xai ajiyeta a hanya, kallo daya Mami tayi ma Samantha tace "Aliyu da ban fito ba wucewar ka xaka yi knn?" Ya shafa kai yace "Ohh Mami wllh mancewa nayi...." Samantha da ko ba a gaya mata ba ta gane mum dinsa ce ganin kamar da suka yi da Hajiya Mariya ta risina tace "Ina kwana..." Mami ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Lafiya lau yan mata ya makaranta" murmushi kawai samantha tayi kanta a kasa tace "Sai anjima...." Daga haka ta juya ta wuce, Mami ta bude bayan mota ta shiga Abuturrab ya shiga motar shi ma ya tada, sai da yayi reverse Mami tace "Ina ka samo wnn kuma?" Ta madubi ya kalleta yace "A anguwar take, she's.... A frnd!" Mami tace "Amma ba musulma bace?" Shiru yayi na kusan minti hudu, cikin sanyin murya yace "Me kika ga Mami?" Mami dake danna waya tace "Me na gani a ina?" Yace "Da kika ce ba musulma bace" Mami da har ta mance xancen da suke tace "Ae musulinci ba boyayyen addini bne, duk inda kaga musulmi xaka gane....." Yace "But Mami uniform ne fa jikinta with Beret!" Tace "So? 'Ya mace musulma dai da ta taso gidan tarbiya baxata bar gida xuwa makaranta ba hijab ba, ko da kuwa makarantar ba a saka hijab xata sa d'an karami idan ta isa gate ta cire..." Abuturrab da idonsa ke kan titi murya can kasa yace "But mami ae lullubi ba shine abinda xai sa ka gane mutum me addini ba, a xuci....." Tunda ya fara Mami ke masa wani kallo bata bari ya kai aya ba a tsawace tace "Meye hadin ka da yarinyar nan Aliyu, who is she?" Shiru yayi har sai da tace "Baka ji na ne?" A hankali yace "She's just a frnd Mami...." Tsaki tayi ta ci gaba da danna wayarta, bai sake cewa komai ba har ya isa inda xai ajiyeta, yayi parking ya juya yana kallonta yace "Mun kawo Mami" bude motar tayi ta fita tana kallonsa tace "Yaushe xaka koma gida?" Yace "Zan bar clinic karfe hudu" tace "Ohk...." Yace "Xan biyo in dauke ki ne?" Tace "No, kafin lkcn ni na koma gida..." Daga haka tace "Allah ya tsare" sannan ta shiga gidan, ya kusa minti uku kafin ya ja motar jiki a sanyaye ya bar wajen. Karfe biyar da wani abu yana xaune kofar gida yana danna waya blessing ta xo wucewa, mikewa yayi da sauri ganinta yace "Hello!" Ta juya tana kallonsa sannan tace "Ina yini?" Yace "lafiya lau, plss wait in baki sako ki ba Samantha!" Da sauri ya shiga gida ba a dau lkci ba ya fito rike da takarda a linke ya mika mata tare da dubu daya yace "Ki bata pls" karba tayi tace "xan bata, nagode" daga haka ta wuce, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya xauna. Samantha ta fito daga wanka bayan magrib blessing ta bude kofar dakinta ta karasa da sauri tace "Sister Rebecca wannan Doctor din yace in baki takardan nan..." Da sauri Samantha ta karba Blessing ta juya ta fice kafin Mumy ta fara nemanta, xaunawa tayi gaban mirror tana goge jikinta tana gamawa ta dauko lotion ta fara shafawa sannan ta dau turarruka fiye da kala biyar ta feshe jikinta da su, sai da ta gama ta dau takardan ta bude, rubutu ta gani kamar haka "ki taho don Allah am waiting for you love...." Ajiye takardar tayi hade da tabe baki ta mike ta dauko kayan baccinta ta saka snn ta tusa gashinta a net, ta kusa minti talatin xaune, can ta mike a hankali ta bude closet dinta ta dauko daya daga hijabs din da take sawa lkcn sanyi ta saka shi har kasa, ta kashe wutan dakinta ta fita, tana waige waige kamar munafuka har ta fita daga gidan. Ta jima tsaye bakin gate din gidan kafin ta tura a  hankali ta shiga ta rufe, bbu kowa parlon ta tsaya bakin kofa tana kare ma ko ina kallo, fitowa yayi daga bedroom, yayi murmushi yana kallonta ya karaso yace "Woaw she came!" Rufe kofar yayi yasa key yace "Welcm love" ta hade rae tace "me yasa kace in xo?" Yace "I just want to see you" turo baki tayi tace "Bude min kofa in wuce...." Wara ido yayi yace "Noo, not until you repeat what you said yesterday...." Juyawa tayi da sauri tace "Noo, plss ka bar ni in wuce..." Murmushi yayi yace "Then ashe xa ki kwana a nan" kamar xata yi kuka tace "Plsss..." Ya daga kafada yace "Ohk let see" daga haka ya tafi three seater yayi kwanciyarsa, ji tayi kamar ta fashe da kuka, wayarsa ya dauka ya jona earpiece ya makala a kunne hade da lumshe ido, ta kusa minti talatin tsaye parlon ganin ya ki cewa komai ta juyo a hankali ta ga har lkcin idonsa a lumshe suke, can ta karasa kusa da shi ta duka tana kallonsa sae ta ga kamar bacci yake, kasa dauke idonta a fuskarsa tayi, can ta cire earpiece daya a hankali ta kai kunne taji karatun Qur'ani yake ji, mayar masa tayi, ta matsa kusa da shi har lkci tana kallonsa, a hankali tace "I... I said i... Love you!" Kallon fingers dinsa tayi ta kai hannunta tana kallon Ring din azurfan dake hannunsa har biyu, lumshe ido tayi ta daura lips dinta a hankali, rike hannunta yayi ta sake sa da sauri duk ta daburce xata mike ya ki saketa ya mike xaune.

*Haske writers asso*?✍?

? *Noorul Huda*?

21.....

Kin bari su hada ido tayi tana girgixa kai tace "Doctor plss ka sake ni..." Yace "Noo..." Kwankwasa kofa aka yi suka kalli kofar a tare, ta xaro ido tace "Wayyo ka sake ni..."  Saketa yyi ya mike yana kallon kofar, ta tashi da sauri tayi hanyar bedroom, karasawa gun kofar yayi yace "Waye?" Muryar Ramla ya ji tace "Ni ce!" Yace "What?" Tace "Abba yana kiran ka wai..." Yace "Alryt ga ni nan xuwa" tace "Toh baxa ka bude ba yaya?" Yace "Yess" tabe baki tayi ta juya ta wuce, juyawa yayi ya shiga bedroom din ya ganta tsaye bakin kofa, tana ganinsa ta juya, ya rungume hannayensa yace "Ashe kina sa Hijab?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ina wayar da na baki?" A hankali tace "Yana gida!" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta yace "ki ajiye shi kusa da ke yau, i will cal you" ta sunkuyar da kanta tace "Toh" yayi murmushi yace "Mu je in raka ki" hanya ya bata ta fita sannan ya fita shi ma, har kusa da gidansu ya rakata yana kallonta yace "Kar kiyi bacci fa, i will call you..." Daga haka ya juya ya wuce ta bi sa da kallo, snn ta nufi gate kamar mara laka ta shiga. Abuturrab na isa gida ya wuce parlor din Abbansa, Abba dake waya tun shigowarsa ya ajiye bayan ya gama yace "Aliyu!" Abuturrab yace "Na'am..." "Kadai san in ka raina ni to yakumbo ta wuce raini a gun ka koh?" Cewar Abba kenan yana kallonsa, Abuturrab ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, Abba yace "Tashi ka je...." Ba musu ya mike murya can kasa yace "Kayi hakuri Abba dama..." Kofa Abba ya nuna masa, hakan yasa ya fita kawai, sha biyu saura ya gama abinda xai yi ya rufe laptop snn ya dau wayarsa yayi dialing  layinsa dake wayar da ya ba Samantha, tana kwance hannunta rike da hymn book tana dubawa kiran ya shigo wayar dake gefenta, langwabar da kai tayi ta dauka ta yi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Hope baki yi hacci ba?" Tace "Yanxu xan yi..." Yace "Tafi ki wanke idon..." Murmushi tayi ta make kafada kamar yana ganinta, yace "Ina son in maki wani tambaya samha..." Tace "Samantha not samha..." Yace "Noo samha not Samantha.." Tace "Uhm to ina jin ka..." Shirun kusan second ashirin yayi kafin yace "Za ki iya aurena?" Kasa cewa komai tayi sbda mamaki da ya cika ta, yace "I know you re there!" A hankali tace "Aure kuma?" Yace "Yeah.." Ta girgixa kai tace "But ae bbu aure tsakaninmu da kai, our religion differs, am a Christian, you re a muslim..." Yace "Akwai aure tsakaninmu...." Da mamaki tace "How?" Ya shafa kai yace "Sai kiyi addinin ki in yi nawa!" Wani shirun ta kuma yi words dinsa na mata yawo a kai, murya can ciki yace "Samha!" Kasa amsawa tayi, cikin sanyin murya yace "Baki so na kenan..."  Jikinta yayi sanyi still ta rasa abun cewa, kiranta ya kuma yi kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me xan ce ba..." Yace "Ki ce za ki aure ni" tace "you know that's very impossible, taya hakan xai yiwu bayan addininmu daban daban...." Lumshe ido yayi yace "Nace maki kowa addininsa xai yi, i see nothing wrong with that...." Rasa ma wani tunani xata yi a lkcn tayi, xata iya auren Abuturrab kuwa? Did she even love him? She know she so care about him.. Tunanin hakan sai da yasa gabanta faduwa sosai, to in ta yarda xata aure sa Mumy da Abba fa? Ya relative dinsu xa su dau xancen... Muryarsa taji yace "Samha!" Hawaye ne ya cika idonta ta kasa amsawa, da dadewa tasan she had alwayz like him, amma bata taba tunanin har xae shigo da xancen aure tsakaninsu ba, a hankali taji yace "Shikenan sai da safe" lkci daya hawayen idonta ya xubo cikin rawar murya tace "Doctor kasan baxai yiwu ba, My parent... My relatives, my...." Kuka ta fara masa, duk ya rikice yace "Kuka kuma... Pls stop it now" kasa daina kukan tayi, yace "OMG don nace xan aure ki shi yasa ki kuka, ok am sorry baxan sake ba..." Daga haka ya katse wayar, ya jefar gefensa ya kashe wuta yayi kwanciyarsa, hade kai tayi da gwiwa ta fara kuka, daga karshe ta gaji ta kwanta, kasa bacci tayi daren ranan, maganganun Abuturrab kadai ke mata yawo a ka, sae kusan karfe uku ta samu bacci ya dauketa, Mumy ce ta tasheta karfe takwas da minti sha biyar, ta mike xaune, Mumy tace "Baki tashi kinyi morning devotion din ki ba wnn wani irin bacci kika yi" Kallon idonta Mumy tayi tace "Me ya samu idon ki, kuka kika yi ne?" Samantha ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "kai na ke min ciwo..." Mumy tace "Kai kuma? Toh tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani," daga haka ta fita, da kyar Samantha ta mike tsaye don ji tayi gaba daya kanta ya mata nauyi, bathroom ta shiga ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, tana goge jiki Abuturrab ya fado mata wanda hakan sai da yasa gabanta ya fadi sosai, hawaye ya cika idonta, jiki a mace ta karasa shiryawa, Blessing ta shigo da tray dake dauke da breakfast ta ajiye mata ta gaisheta snn ta fita, da kyar ta iya shan tea xata kwanta sai ga Mumy ta shigo da magunguna ta bata ta sha, mumy tace "Thank God sai da ku ka gama jarabawa ciwon kan ya same ki, ki kwanta xuwa anjima mu ga" daga haka ta fita, Samantha ta kwanta hade da lumshe ido, ta kasa daina tunanin Abuturrab ta kuma rasa dalili, a da tasan yana yawan fado mata barin idan suka dade basu hadu ba, amma tun daga jiya da daddare xuwa yau sae ta ga ya fi na ko da yaushe, to fushi yayi ne yasa ya kashe wayarsa amma ai gaskiya take fada, runtse ido tayi ko bacci xae dauketa amma shiru, sae a lkcn tasan ashe fa ta damu da shi haka. Har washegari Abuturrab bai sake kiranta ba, ita dai tasan bbu wani ciwon kai but da Mumy ta tambayeta me ke damunta sai tace ciwon kai, tun da take abu bai taba tsaya mata a rai kamar yanda wannan ya tsaya mata ba, ta kasa dauke tunanin a ranta, Mumy ta kira Abba dake Lagos ta fadi masa bata da lafiya xa su je asibiti, Abba yace ba sai anje ba xae turo likita, Abuturrab na xaune office yana aikin gabansa, baka taba cewa abu na damunsa sai dai da xaka shiga xuciyarsa ka ga tulin damuwar dake tattare da gun sae ka tausaya masa, babban damuwarsa bai san yanda xae yi da Yakumbo ba don yasan shi ake ta jira, gashi ya kasa daina tunanin Samantha, yasan ba fault dinta bane that's just the fact but kawai ya shareta ya kuma dau ma kansa alkawarin ko ba yanxu ba sai ya aureta ko da kuwa threatening din kisa xa ayi masa, Tun a daren yake raya ma kansa to ko ya koma ga saudat, yana jin kuma xuciyarsa ta aminta da hakan coz he gat no option. Daren ranan ya shirya ya tafi gidansu Saudat, tun da yayi parking a kofar gidansu yake kallon motar dake parke gaba da nasa ganin kamar akwai mutane a ciki, ae ko sai ga shi an bude motar saudat ta fito, tabe baki yayi ya tada motarsa kawai yayi reverse ya bar gun, bai bar layin ba kiranta ya shigo wayarsa, ya ci gaba da tukinsa ba tare da ya sake kallon wayar ba. Washegari Wednesday yana xaune office ya hade kai da table Mujaheed ya shigo, har ya karasa gun table din Abuturrab bai dago ba, mujaheed ya bugi table din yace "Bacci kake a bakin aiki doctor?" Dagowa Abuturrab yayi yana kallonsa yace "Daga ina haka?" Mujaheed yace "Asibiti na xo bani da lafiya mana" murmushi Abuturrab yayi yace "Ohh i see" mujaheed yace "Ya na ganka haka kamar kana tare da damuwa" Abuturrab yayi yake yace "Damuwa kuma, am just tired ne, ya aiki?" Mujaheed yace "Alhmdllh"

*Haske writers asso*?✍?

? *Noorul Huda*?

22......

Hira suka ta yi a asibitin har bayan la'asar suna fitowa daga masallaci ko wannensu ya dau hanyar gida, yau kam Abuturrab a main house dinsu ya sauka, Mami dake parlor ta bi sa da kallo bayan ya gaisheta har ya haura sama, wanka yayi ya fiddo jallabiyarsa a daki ya sa yayi kwanciyarsa. Ringing din wayarsa ne ya tashesa kusan magrib, dai dai shigowar mami dakin tace "Lafiyan ka Aliyu, baccin yamma ana xaune kalau?" Mikewa xaune yayi ya dau wayarsa yayi picking call din, daga daya bangaren aka ce "Hello!" Abuturrab yace "Good evening" "Evening, kana gida ne doctor" cewar mutumin kenan, sae a snn Abuturrab ya dau murya yace "Yeah ina gida sir, ya aiki?" Mr David yace "We Thank God, daughter na ne bata da lafiya, i want you to check on her if it's ohk by you and you re less busy pls" Abuturrab da hankalinsa ya tashi lkci daya yace "Ohk sir, i will do that right away!" Daga haka ya katse wayar ya kalli Mami dake tsaye har lkcn tana kallonsa yace "Mami na gaji da yawa ne yau" tace "ko abincin fa baka ci ba" mikewa yayi tsaye yace "Bari in dawo daga masallaci Mami" daga haka ya fita, ana idar da magrib ya tafi gidansu Samantha, bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga, mai aiki ce ta bude masa kofa bayan ya danna bell, ya amsa gaisuwarta ya tambayeta inda Samantha take tace tana bedroom, ita ta raka sa har sama, ya bude kofar dakin suka yi ido hudu da mahaifiyarta dake xaune dakin alamar dai likita take jira, tana ganinsa ta hade rai sosai, ya sunkuyar da kansa ya karasa dakin ya gaisheta da ladabi, da hanci ta amsa masa ta mike ta fice, Abuturrab ya durkusa kusa da gadon yana kallonta ganin yanda lips dinta yayi ja, hannu ya daura forehead dinta ya ji dumi, a hankali yace "Samha..." Bude ido tayi da sauri ta mike xaune, ya kamo hannunta yace "Ina ke maki ciwo?" Hawaye ya cika idonta ta ki cewa komai, cire bargon jikinta yayi yace "Talk plss" ta sauke idonta kasa, ya tsura ma wuyarta dake dauke da farin cross ido, a hankali ya kai hannu kai xae tsinka ta rike hannun da sauri tace "Mumy ce ta sa min" bai kulata ba ya tsinka shi ya jefar gefe daya, ta sauke hannunta tana kallonsa, kallon kwayar idonta yake shi ma, hawayen da ke makale idonta ya gangaro ta daura kanta a shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Ni fa ban ce komai ba doctor, and you re angry, kayi hakuri pls..." Ya harde hannunsa da nata ya lumshe ido yace "Noo, kin fa ce baxa ki iya aurena ba" ta fashe da kuka tace "Nooo ni bnce haka ba fa..." Shiru yayi yana jin saukar hawayenta a shoulder dinsa, ya shafa kanta a hankali yace "But nace kiyi addinin ki inyi nawa fa, still kika ce it's impossible" girgixa kai tayi tace "Bayan kana rabani da duk wani abu na addini na shine xaka ce min haka, yanxu fa ka tsinka min rosary dina...." Buda ido yayi jin abinda tace, ya dago kanta yace "Ohh you gat me wrong samha..." Da sauri tace "Noo i am right" yace "You re sick kuma rosary din nan is a burden....." Hade rai tayi tace "A tunanin ka ba, kayan jikina bai xame min burden ba sai rosary" yace "Alryt am sorry baxan sake ba..." Bude kofa aka yi ya koma baya da sauri blessing ta shigo da gani kasan mumy ce tace ta taho, Ya kalleta yace "Taimaka mana da cup of tea pls.." Tace "Toh" snn ta fita, ya kamo hannunta yace "Toh yanxu ina ke maki ciwo" kanta ta nuna masa, yayi shiru yana kallonta, can yace ohk yanxun nan xae daina, lumshe ido yayi ya manna bakinsa kan goshinta, turasa ta fara yi tace "Doctorrrr" ya rike kanta gam ya sauko da ba lips din har kan hancinta sannan bakinta, yayi mata light French kiss, turasa tayi ta hade rai, ya wara mata ido ya koma baya yace "Alryt am sorry wife...." Blessing ce ta shigo da cup din tea ya karba ya mika ma Samantha, ta6awa tayi tace "Akwai zafi ai" ya ajiye sa kan bedside drawer yace "Toh bari inje in dawo yanxu" da ido ta bi sa har ya fita, gida ya koma ya dauko mata drugs ba a dau lkci ba ya dawo, har lkcn blessing na dakin, yayi mata kallo daya ya karasa gun Samantha ya dau tea din da ya ajiye ya kai baki yayi sip dinsa snn ya mika mata yace "Toh ya huce" hannu tasa ta karba, aka bude kofa Mumy ta shigo, mikewa yayi ya bude ledan maganin ya gwada mata yanda xata sha ya ajiye ya d'an saci kallon mumy ya ganta tsaye fuskar nan a murtuke, dukawa yayi kamar xae dauki abu murya can ciki yace "I will call you ltr..." Daga haka ya juya, bai bari sun hada ido da Mumy ba yayi mata sallama ya fita. Kamar jiya yau ma sha biyu da wani abu ya kirata, tana kwance ta dau wayar tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "How you feeling now?" Tace "Da sauki..." Yace "Sai kice Alhmdllh..." Ta buda ido tace "Alhmdllh kuma?" Yace "Yess" tace "Tohm Alhmdllh" yayi murmushi yace "Good, a ina muka tsaya jiya a maganar mu?" Bata ce komai ba yace "Samha..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" yace "Baki son maganan ne?" Girgixa kai tayi kamar yana ganinta tace "A'a fah" yace "Say something now" da kyar tace "Duk yanda kace doctor" murmushi yayi yace "Ohk we'll talk about that face to face...." Cikin sanyin murya tace "Toh" "Me xa ki bani for my birthday?" Wara ido tayi tace "Woaw, it's also my birthday month, wani date ne naka?" Yace "Da gaske kema month dinki ne?" Tace "Eh mana, my birthday is on 10th june...." Da mamaki yace "Are you for real?" Tace "Yes mana" yace "Woaww what a concurrent! It's same with mine" tace "heey doctor ba wani nan..." Yace "Am serious samha, i was also born on 10th june" tace "Wow so we re birthday mates?" Yace "Yeahh and we gonna celebrate it together.... No wonder shi yasa kike da kyau kema kamar ni... Haka kuma xa mu haifi yara duk june 10" Ta xaro ido tace "Uhm?" Yace "Yess am serious baby, today is 3rd, 7 dayz to our birthday!" 
Tun daga lkcn wayarsu ya xama constant don xaman gida kawai take, duk bayan awa biyu sai ya kirata, hakan kuma yasa bai damu da rashin ganinta ba tunda suna waya, a haka har ya rage kwana daya birthday din nasu, da daddare yana daki ya kirata yace "Baby plss ki daure ki fito yau mana, i want to see you" ta kalli agogo taga har tara da rabi tace "But baka kalli agogo ba koh doctor" yace "Na kalla mana ai ba dadewa xa kiyi ba" xata yi magana yace "Plssss" kamar xata yi kuka tace "Doctor....." Yace "Plss" turo baki tayi tace "Na ji" daga haka ta katse wayar, tayi tagumi, can ta mike ta dau hijab ta sa ta kashe wutan dakinta ta fita, ko blessing dake daki bata sani ba, tana isa gidan bata gansa parlor ba, ta bata fuska tana kallon kofar daki, a bayanta taji sa a tsaye ta juyo da sauri ya wara mata ido yace "Welcome..." Tace "Toh kiran meye" kama hannunta yayi ya shiga da ita kitchen yace "Am hungry kuma potato and egg nake son ci, hope Mumy baxa ta neme ki ba" shiru tayi bata ce komai ba, can a hankali tace "Ohk... Mumy ta tafi church" Yace "Good, cire hijab din" tace "No xan yi a haka" gun da potatoes suke ta nufa ta debi wanda tasan xai yi masa ta fara ferewa da peeler, cikin kankanin lkci ta gama, duk yana tsaye yana kallonta, kafin minti goma har ta gama, ta daura ruwan Lipton ta juya tana kallonsa tace "Ko baxa ka sha ba" yana rungume da hannunsa yace "Xan sha mana" kayan kamshi ta xuba ta rufe snn ta dau dankali da kwan ta fita ta kai parlor ya bi ta da kallo, tana dawowa kitchen din tace "Toh kaje ka ci kafin ruwan shayin yayi" ya girgixa kai yace "No xan taya ki jira a nn" murmushi tayi bata ce komai ba, haka suka ta tsayuwa har ruwan ya tafasa ta juye flask snn suka fito, sai da ya tilasta ta suka ci abincin a tare, nan ya sa masu film a system tun tana cewa ita gida xata wuce har ta hakura tana kallon, kamar ance ta kalli agogo taga sha biyu saura 'yan mintuna, xaro ido tayi tace "Na shiga uku, doctor kalli agogo" mikewa take son yi ya riketa yace "But it's late Samha...." Turasa tayi tace "Let me plss, ni bana son kana min irin haka, you are just letting me betray my parent, ni ka sake ni" a fusace tayi maganar ta mike ya bi ta da kallo har ta isa kofa ta dawo don daukar takalmanta dake bakin kitchen, lkci daya aka bude kofar parlon, still tayi a gun tana kallon kofar, Ramla, Khaleesat, da Ilham ne suka shigo a tare, juyawa yayi shi ma yana kallonsu sannan ya kalli agogo da mamaki, ko kadan bai lura da abinda ke hannunsu ba da mamaki yace "Lafiya?" A tare duk suka bude murfin ruwan gora me sanyi dake hannunsu suka tuttula masa gaba daya a jiki lkci daya suka ce "Happy birthday....." Bai gama recover ba duk suka fice da gudu suna dariya, me Samantha xata yi banda dariya, ya kalli system dinsa da aka yi masu wankan tare ya mike da gani kasan ransa ya gama baci ya shige bedroom, Samantha ta langwabar da kai ta karasa parlon ta dau system din ta kashe ta ajiye kan kujera a bude, snn ta dauke lallausan rug din da ya jike ta fita da shi waje ta shanya, ta koma kitchen ta dauko mop da bucket ta share ruwan da ya malala a parlon bbu bata lkci ta gama ta wanke mop din, ta dawo parlor tayi jim, can ta kalli agogo sai kuma ta nufi bedroom din, xaune ta gansa gefen gado ya rike kai, ta xaro ido tace "Baka cire kayan ba?" Bai tanka ta ba haka yasa ta karasa ta durkusa gabansa tace "Doctor...." Ganin bai dago ba tayi shiru tana kallonsa, a hankali ta dago kan nasa suka hada ido, kamar xata yi kuka tace "Toh ka cire kayan kar sanyi ya kama ka mana" unbutton din shirt din ya fara yi, ta mike tsaye ta taimaka masa ta cire, tana kallon singlet din jikinsa tace "Toh ka cire doctor" mikewa yayi ya bude closet ya fiddo wasu inners ya shiga bayi, ba a dau lkci ba ya fito, a hankali ta juya masa baya, ya fiddo pyjamas dinsa ya saka, ita dai tana tsaye tana fidgeting din fingers dinta, kamar ance ta juyo ta ga belt hannunsa ya nufi kofa, da sauri ta bi sa ta rikosa tace "No doctor daga suna maka wasa, they just wished you happy birthday, kalli fa hana idonsu bacci suka yi har sae da sha biyu yayi, kai baka san wasa ba?" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da su ne xasu xuba min ruwan sanyi a jiki" bata fuska tayi tace "Toh meye don sun xuba ma ruwan sanyi, after all they wished you a happy birthday" karamin fridge din dake dakin ya nufa ta bisa da kallo ya bude ya ciro ruwa me sanyi ita dai kallonsa take taga ya nufota yana bude ruwan, wani k'ara tayi xata gudu ya cafkota, ta kwala wani k'aran jin ruwan sanyi, k'adan ya xuba mata ya ajiye, ta fashe da kuka ya wara mata ido yace "Happy birthday...." Kwace kanta tayi xata fita ya rungumota yana dariya yace "Ashe ba dadi" dage hijab dinta xai yi ta rike da sauri tace "Bana so...." Da karfi ya cire hijab din ya ga yar fingil rigar bacci ne jikinta, ya ja ta xuwa kan gado ya kwantar da ita ya rufa mata bargo murya can ciki yace "Go to sleep it's late" daga haka ya fita ya rufe kofar parlor ya dawo, a rufe ya ga idonta ya dau blanket ya xaga inda take ya durkusa cikin sanyin murya yace "Happy birthday wife!" K'in bude ido tayi duk da tana jinsa, xae mike yaji murya can kasa tace "Happy birthday also dear...." Murmushi yayi ya mike ya kashe wutan dakin ya fita parlor yayi kwanciyarsa.

*Haske writers asso*?✍?

? *Noorul Huda*?

23.....

Da asuba ya rakata har gate dinsu don tace karfe bakwai Mumy xata dawo, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "dont forget karfe shidda plss love..." Ta kallesa tace "Nace maka ni ban san yanda xanyi ba fa, Mumy xata tambaye ni inda xan je, idan nace mata church nasan ita ma xata je idan bata ganni ba kuma sai in ce me" yayi shiru yana kallonta, can yace "Toh kice mata gidan kawar ki xa ki je mana" turo baki tayi tace "Allah yasa ta bar ni" daga haka ta d'aga masa hannu ta shiga gida. Har bayan la'asar Samantha tunanin me xata ce ma Mumy da xata bar ta ta fita take, can dai ta dau shawarar sa na cewa tace gidan kawarta xata je, ae ko biyar da kusan rabi ta shiga dakinta ta sameta ta xauna gefenta a hankali tace "Mumy xan je gidansu Victoria kinga ta daina xuwa nan don bana xuwa gidansu...." Tsit tayi tana mamakin kanta don ita dai tasan bata karya gashi yau Abuturrab yasa tayi, duk jikinta yayi sanyi ta fara wasa da fingers dinta, Mumy dake mata wani kallo don taga alamar karya take wanda hakan ya daure mata kai wai yau samantha ce ke kkrin hada karya, bata dai nuna ta gano ta ba tace "Tun safe kina gida baki ce xa ki ba sae da yamma tayi?" Shiru tayi bata ce komai ba, Mumy tace "Toh tafi kar ki dade amma" Samantha ta kasa cewa komai kuma ta kasa kallonta, can dai tace "Toh Mumy driver ya kai ni" Mumy ta xuba mata ido sai kuma tace "Toh kije kiyi masa magana" mikewa tayi ta fita ta koma dakinta, hawaye ya cika idonta ta rasa dalili, wayarsa dake gunta ta dauka ta kirasa, yayi mamakin ganin kiranta ya dauka yace "Wife!" Hade rai tayi tace "You made me lie to my mum, ni bana karya kasa nayi karya" sai kuma ta fashe da kuka, yace "Alryt, shknn yi xaman ki a gida kawai, it's nothing and i don't want you to lie because of me" daga haka ya katse wayar, jikinta yayi sanyi ta sake kiransa ya ki d'agawa, ta fashe da wani kukan ta xauna gefen gado, can kuma ta mike kamar mara laka ta shiga bathroom, wanka tayi ta fito ta shirya cikin abayarta tayi rolling, sosai tayi kyau duk da bata yi wani kwalliya ba, ta boye wayarta a jaka ta fito tana rike da jakar, Mumy dake shirin fita church tayi ma sallama ta fita driver ya ja ta xuwa inda tace wato gidansu Victoria, mintin ta sha biyar a gidansu Victoria ta sake kiran Abuturrab, wnn karan sai da ya kusa katsewa ya dauka, kasa cewa komai tayi amma kiris ya rage ta fashe masa da kuka, shi ma dai kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "ya aka yi samha?" Ta fashe da kukan da ke cin ta tace "Bayan kasa na fito gida shine ka ki daga kirana koh?" Da mamaki yace "kin fito da gaske? Kina ina" cikin rawar murya ta gaya masa, ya lumshe ido yace "Alryt, gani nan xuwa am sorry plss" daga haka ya katse wayar, shidda da 'yan mintuna ya iso anguwar, tun da ta fito gate yake kallonta har ta karaso ta bude gaban motar ta shigo, ya lumshe ido yace "Am sorry samha" bata ko kallesa ba ya tada motar suka bar gun, wani babban gun make up taga yayi parking, ta kallesa tace "Me xa mu yi a nan?" Ya fito daga motar ya zaga ya bude mata ta fito tace "Me xa mu yi a nan mana" Yace "Follow me ko kuma in kama hannun ki" daga haka yayi gaba ta bi bayansa kamar xata yi kuka, babba ne gun kwalliyan sosai, har kunshi ana yi da gyaran gashi, matar dake gun da alamar ita ce me gun tayi masu sannu da xuwa da fara'a ya nemi kujera ya xauna, Samantha ma ta xauna sai dai duk gabanta faduwa yake, Abuturrab yace "Madam light make up nake son ayi mata...." Samantha ta hade rai tace "Make up kuma!" Bai kalleta ba yace "Xan je in dauko kayanta yanxu...." Matar tace "Muna gyaran gashi da kunshi na amare, bari in kawo maka list ka ga bbu abinda bama yi a nan" Abuturrab yace "No ba sai an kawo ba, a gyara mata gashi kawai sai make up" daga haka ya mike yana ma Samantha wani kallo da manyan sexy eyes dinsa har ya fita, ji tayi kamar ta rusa kuka, nan matar da yaran gun suka taho don yi mata abinda yace. Sai bayan magrib ya dawo rike da leda ya mika ma matar yace "A dan yi sauri madam lkci ya wuce" babu yanda samantha ta iya haka ta bi matar. Gown ce me d'an karen kyau ja with long sleeves, mai ratsin silver daga saman wuyar kawai, dama gata fara gown din ya wani haska ta sai ka rantse amarya ce, gashi kamar an auna ta, ya fito mata da shapes dinta tun daga sama, tayi kyau iyakar kyau, ga gashinta da aka gyara mata bakikirin da shi ya xubo har kasan wuyarta, matar sai maa sha Allah take cewa tana kallonta, necklace ta sa mata da earrings suma silver sai bracelet da wristwatch, ta fiddo takalmi me ratsin ja da silver ta bata ta saka, matar da samantha ta gama tafiya da imaninta tace "Ya sunan ki 'yan mata?" Samantha ta sunkuyar da kai a karo na farko da taji wani iri tace mata sunanta Samantha, murya can kasa tace "Samha!" Matar tace "Ki gode ma Allah Samha kina da kyau, wanda ya xo da ke shine angon naki koh?" Samantha ta sunkuyar da kai kawai, matar tace "Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya da xuri'a dayyaba...." silver head tie mara nauyi matar ta daura mata, sannan ta fesheta da turare kala hudu da ya saka cikin kayan, matar takara mata da nata, snn ta kama hannunta suka fito, tun da suka fito Abuturrab ke kallon Samantha ko kiftawa babu, ita kam kasa dago kanta tayi, duk occupant din wajen kallonta suke ko wanne na fadin maa sha Allah, Har gabansa matar ta kai ta, sai a snn ya mike da kyar ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu talatin din dake ciki ba tare da yace komai ba ya mika mata, farin ciki ya lullube matar ganin tulin kudin, karfin halin kama hannunta yayi suka fita tana binsa duk jiki a sanyaye, suna shiga mota ya kamo hannunta cikin raunin murya yace "promise to be with me no matter the situation we re going to find our self samha..." Kasa cewa komai tayi hawaye ya cika idonta, harde hannayensu yyi cikin sanyin murya yace "Talk plss Samha," rungumesa tayi cikin rawan murya tace "I promise!" Kiss ya shiga yi mata a wuyarta, duk ta rikice tana turasa, da kyar ta samu ya saketa, ta hade kanta da gwiwa, jiki a mace ya tada motar ya ja suka bar wajen, sai da ya je gidan wani abokinsa don shiryawa shi ma, sai dai bai bari ta fito ba ya shiga gidan, ba a dau lkci ba ya fito sanye da suit dinsa na royal blue. Bata bari sun hada ido ba har ya ja motar. Wani lafiyayyen hall taga sun yi parking, tun daga waje kana iya ganin uban motocin dake Parke ga abokansa na hannun dama na jiran isowarsa, yana fitowa ya xaga ya bude mata ya kama hannunta ta fito, wani kallo suka dinga mata gaba dayansu shi dai yana rike da hannunta har ya iso gabansu, sai a snn suka ankare, kusan dukkansu suka sa hannu aljihu suka fiddo sabbin dari biyar biyar suka watsa masa shi da ita, lkci daya suka ce "Happy birthday Aliyu" dariyar yake yayi ya na rike da ita ya nufi hall din suka rufa masu baya. Sai ka rantse d'an sarki ko d'an shugaban kasa ke birthday tsabar cika da haduwar wajen don Aliyu akwai son life, manyan 'yan mata da samari masu ji da kai ne kuma a gun, Gaba daya kallo ya koma kan Samantha, wanda hakan yasa Abuturrab ya ji wani kishi ya rufesa, komai da aka yi design a gun red and silver ne, manyan cake har uku ne a gun, nan aka fara shagalulluka, ita dai Samantha taki sakin jiki, shi ma kuma bai takurata ba, Saudat na daya daga matan da suke gun, sai dai tun da ta kyallara ido taga Samantha hankalinta ya tashi barin da taji wai birthday mate dinsa ce kuma da dukkan alama budurwarsa ce, bbu wanda ya dauko Samantha Christian ce, Abutuurab dai na ta kallon agogo don bai son su wuce tara gun, ko da xa su wuce hakan ma yafi son ya maida Samantha gida, tunda Samantha ta xauna bata tashi ba sai da aka fara hotuna shi ma kuma tilasta ta yayi, ae ko kowa so yake suyi hoto tare, har dai aka gama sai yanka cake, Yayi ma abokinsa magana cewar ya ba ma Dj umarnin kashe wakar da ke tashi coz he wants silent, cikin kankanin lokaci gun yayi tsit, wanda hakan yasa kallo ya dawo kan Abuturrab dake facing din Samantha, kasa kallon cikin idonsa tayi, da mamakinta da kowa na gun sai gani suka yi ya durkusa a hankali on his kneel ya sa hannu a aljihu ya ciro wani box me bala'in kyau ya bude, sai ga kyallin diamond, abokansa na ganin haka suka dauko Mp xuwa inda suke ko wannensu na cewa waowww, Abuturrab ya ciro ring din ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Will you marry me plss?" Tafi hade da ihu ya kauraye ko ina, tuni aka fara video da waya, bbu wanda abun bai burge ba a wajen sai saudat da taji kamar xuciyarta xai fashe, samantha kam hawaye ne ya cika idonta, ta kasa ce masa komai ga ido da ya tsare ta da, da kyar ta gyada kai hawayen idonta ya xubo, cikin sanyin murya tace "Yyess i will!" Dai dai lkcn da ya gama xura mata xoben ya mike ya rungume abarsa, aka dinga tafi da shewa ana daukarsu photo, juyawa saudat tayi ta fice daga hall din da gudu, gift ba na wasa ba Samantha ta samu a gun don har ta fi uban gayyar samun kyauta, karfe tara kuwa ya fita da ita daga gun, duk taki yarda su hada ido, sai da ya kai ta part dinsa ta canza kaya snn ya rakata har kofar gidansu, bata yi wata wata ba ta shige ta bar sa a tsaye, yayi murmushi ya juya ya bar wajen. Xaune taga Mumy a parlor fuskar nan nata bbu alamar rahama, jikinta yayi sanyi ta karasa ta gaisheta kanta a kasa, cikin kakkausar murya Mumy tace "Daga ina kike Rebecca?" Gabanta yayi mugun faduwa tana kallon uwartata a hankali tace "Birthday Mum" Mumy ta mike tace "Birthday din wa" sunkuyar da kai tayi xuciyarta na bugawa tace "A frnd" fincikota Mumy tayi tace "ki gaya min meye hadin ki da likitan dake xuwa gidan nan?" Sosai samantha ta tsorota kafin tace komai uwar ta sauke mata mari cikin tsawa tace "Baxa ki bani amsa ba??? Uban meye tsakanin ku, a ina kika san shi? Har ya sauke ki a mota" Samantha ta fashe da kuka jikinta na rawa tace "Mumy kiyi hakuri don Allah, he's a frnd!"

*Haske writers asso*?✍?

? *Noorul Huda*?

24.....

Baki uwar ta bude da mamaki tace "Rebecca yaushe kika fara karya?" Durkusawa samantha tayi cikin kuka tace "Plss Mumy kiyi hakuri am not lying frnd dina ne" Mumy tace "A ina kika san shi?" Rasa abinda zata ce  tayi hawaye na sakko mata tace "Kiyi hakuri Mumy" hankada ta tayi cikin tsananin fushi tace "Baxa ki bude baki ki min magana ba?" Jikinta na rawa tace "Watarana ne naje birthday din Suzan shine muka hadu, he helped me" tafe hannu uwar ta shiga yi cikin tashin hankali tace "Nashiga uku, Samantha dama abinda kike yi knn yanzu ban sani ba, when did you change, meye hadin ki da musulmi daga fara bin sa har ya koya maki karya," a fusace uwar ta kuma kai mata mari ta fixgota tace "Maza wuce ki hada kayan ki yanxun nan, dole ki bar gidan nan gobe gobe, baxan bari ki ja mana abun kunya ba, tunda har ya koya maki karya ban san nan gaba me xae faru ba kuma" daga haka ta ja ta xuwa daki, tana tsaye tasa ta gama hada kaya ta tabbata bbu wani abu da tasa a jakar banda kayanta don har wayarta da bata fiye amfani da ba ta karbe, wayar Abuturrab ne dae bata san da shi ba, bedroom dinta ta kai ta ta kulle ta sauko kasa tana huci tana tunanin ghana kawai xata turata gobe tunda tana da visa, Samantha ta hade kai da gwiwa ta dinga kuka, duk ta rasa me ke mata dadi, kallon fingers dinta tayi da sauri taga ring din da Abuturrab ya sa mata na nan, cirewa tayi ta wurgar ta kuma fashewa da kuka, tayi mai isarta  ta kwanta nan kasa ta lumshe ido, har ta fara bacci kamar warce aka tsikara ta mike da sauri, kalle kallen dakin ta fara yi tana neman xoben, can ta mike ta nufi ta inda ta wurgar bata gani ba, jikinta yayi sanyi wasu sabbin hawayen suka xubo mata, a hankali ta dinga bin ko ina na dakin tana dubawa, har bayan minti talatin bata gani ba, hankalinta ya tashi ta fara dage komai tana dubawa, kan kace me duk ta juya dakin upside down, da kyar ta ga xoben a wani lungu, ta karasa da sauri ta dauka, dai dai nan aka bude kofar dakin, Mumy, da aunties dinta har uku suka shigo dakin, daya kanwar mahaifinta ce, biyu kuma kannin Mumy ne, Mumy da ta hango xoben dake kyalli hannunta ta karaso da sauri tace "Meye wannan hannunki?" Kasa cewa komai samantha tayi tana kallonsu xuciyarta na bugawa, Mumy ta kare ma dakinta kallo tace "Ubanki kike nema kika rikita min daki, xoben meye wnn kamar na diamond a hannunki" sauke idonta kasa tayi hawaye ya silalo idonta, daya daga aunties din nata a fusace tace "Amma Rebecca ba kurma bace ba dai koh!" Ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Mumy shi ya bani" dafe kirji Mumy tayi cikin tashin hankali tace "Amma na shiga uku ni Rachael, na meye?" Ta sulale nan kasa ta kuma fashewa da kuka sosai tace "He said he wants to marry me" wani jiri Mumy ta dinga ji har sai da Anty Vivian ta riketa, Mumy ta fashe da kuka sosai tace "Ae ni nasan na shiga uku, amma Allah ya tsine ma mutumin nn yar tawa xae yi engaging? Wayyo Allahna kila ma asirce min ita yayi, shi yasa jinina bae taba haduwa da musulmai ba, mugaye ne, matsafa ya ma 'ya ta tsafi, ku kira min David yaji abinda yar sa ta koma, tuni Rebecca ta daina xuwa church na lura, ko taje kuwa bata dadewa take dawowa, Rosary da na bata ta saka sai ta cire, ta bar karanta Bible, ta yaye catechism da dadewa, addu'ar safe yanxu bai dameta ba, kai bata ma yi, Samantha da ko kasheta xaka yi baxata maka karya ba ita ce yanxu da masters a karya, snn ace bae asirce min 'ya ba... Babban abinda ya kuma tada min hankali nayi ta leke ina jiran in ga ta inda xata billo shine yau fa birthday dinta amma yar nn daga ni har babanta bbu wanda tace ma komae abinda bai taba faruwa ba tsawon rayuwarmu tare, ashe birthday d'an iskan ya hada mata" Tana kai wa nan ta kuma fashewa da kuka sosai ta daura hannu a ka, Wani wawan mari kanwar Abba ta dauketa da shi cikin tsananin fushi tace "Waye shi? A ina kika sansa, d'an wani anguwa ne? Me garesa da har ya burge ki kike kulasa?" Kasa cewa komai Samantha tayi sbda wani jiri da ta dinga gani tsabar shigarta da marin yayi, Anty vivian ta rike Sarah kanwar Abba ganin wani marin xata kuma kai mata tace "Haba sis sarah mu bi ta a hankali mana..." Sarah tace "Xaman ta ya kare a Nigeria, gobe gobe xata wuce Ghana, har mu xata dauko ma abun kunya, me xa ayi da musulmi? Yesu yayi mana tsari...." Samantha bata san lkcn da cikin kuka tace "Toh su musulman ba mutane bane? Ina ce Grandfather na har ya mutu musulmi ne shi, kuma dama ba Jehovah ne ya halicce mu gaba daya tare da su ba, kowa da nasabarsa gun Allah.... Kuma a Bible ae dama ance addini xai kasu....." Mumy bata jira jin karashen ba tayi kukan kura sai a kanta, tana duka Sarah na duka, ita kanta Vivian wnn karan wani wawan hauri ta kai mata tana cewa "Rebecca mu kike gaya ma haka???" Da kyar Anty Mary Ann ta ja samantha suka bar dakin, ta shiga da ita wani dakin ta rufe da makulli, Samantha ta sulale kasa ta hade kanta da tiles din dakin, Anty Mary da damuwa tace "Rebecca waye wnn mutumin, meye hadin ki da shi?" Kasa cewa komai Samantha tayi idonta a rufe, xama Anty Mary tayi gefen gado tayi tagumi, tana jin su Mumy na bubbuga kofa kamar xasu cire suna kunduma xagi, daga karshe suka gaji suka bar wajen, Samantha ta mike da kyar ta hau gado ta rufe ido, Mary da ta bi ta da ido ta girgixa kai cike da damuwa, har karfe sha daya samantha bata bude ido ba sai dai ba bacci take ba, mikewa Mary tayi ta shiga bayi, samantha ta juya a hankali taga ta rufe kofar, mikewa tayi ta sauka daga kan gadon da sauri ta bude kofa a hankali kamar kiftawan ido sai ga ta downstairs, Blessing na xaune parlon tana ganinta ta mike da damuwa tace "Sister Rebecca ina xa ki kuma, you re in trouble plss kar ki fita" Hawaye cike idonta tace "Plss don't say anything, kawai kice baki gan ni ba" daga haka ta fice da gudu jin budewar kofa a sama, Blessing ma ta shige kitchen da gudu, ko takalmi bbu kafarta ta fice gidan gaba daya, ae ko Mary na jin budewar kofa ta fito da sauri, ganin dakin wayam ta fice waje dai dai lkcn da Mumy ma ta fito da su Sarah, Mary ta fara kalle kalle hankali tashe, Mumy na ganin haka ta daura hannu a ka ta fara sauka stairs tana cewa "Ae ni shknn na shiga uku na lalace, gudu tayi...." Duk suka bi ta hankali tashe, Mumy ta dinga kwala ma Blessing kira ta fito da sauri, A tsawace tace "Ina Rebecca?" Girgixa kai tayi a tsorace tace "Madam ni a kitchen nake ai...." Kamar Mahaukaciya Mumy ta fita parlon ta dinga kwala ma inusa mai gadi kira ya fito cikin tashin hankali tace "Inusa Samantha ta fita ne?" Inusa yace "Ehh yanxun nan ta fita..." Da gudu su Anty sarah suka fice  don bin bayanta, a tsawace Mumy tace "Me yasa ka bar ta ta fita?" Mai gadi yace "Madam ae ba yau ta saba fita ba, in dai xaki kwana church yawanci bata kwana a gidan nan sae asuba take dawowa, nayi xaton yau ma kinje kwana a church ne...." Wani kara Mumy tayi ta daura hannu a ka tace "Yesu!! Ae ni nace dama na shiga uku, Rebecca bata kwanan gida, ina take kwana" kuka sosai ta fashe da, daga haka ta bi bayansu Sarah ita ma da gudu, yau kam samantha bata ji tsoron karnukan dake haushi ba, neman tsoron ma tayi ta rasa, gudu kawai take don tasan da wuya idan ba a san ta fita ba yanxu, tunanin hakan yasa jikinta ya dau rawa a xuciyarta kuwa addu'a take Allah sa Abuturrab bai rufe gate ba, don tasan idan ta tsaya bubbugawa xa a iya risketa kuma tata ta sameta knn gun su Mumy.....

*Haske writers asso*?✍?
Reply
#2
muna bukatar comment dinku.
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  ⚡Heedayah⚡By Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 14,580 07-08-2021, 05:08 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 29,503 09-10-2018, 08:20 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 11,459 08-18-2018, 01:15 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 20,044 08-10-2018, 12:48 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 24,871 08-05-2018, 11:27 AM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat haiydar Gimbiya 0 53,300 08-03-2018, 05:26 AM
Last Post: Gimbiya
  *CAPTAIN_AHMAD JUNAID* By Khaleesat Haiydar_ ✍? Gimbiya 0 40,819 11-16-2017, 12:51 PM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)