Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar
#1
? *Noorul Huda*?

6.....
Fitowa yyi ya bude kofar parlon ya ganta tsaye rike da basket din abinci, wara ido yayi yana kallonta, tace "Um na kawo maka abincin" rungume hannayensa yayi yana murmushi yace "Da gaske?" Ta gyada masa kai ya bata hanya ta shiga parlon ya juya ya bi bayanta, tsakar parlon ta ajiye abincin ta kallesa ya sakar mata murmushi yace "Thanks Samha!" Mikewa tayi ta dau jakarta tace "Uhm am going to church!" Shiru yayi yana kallonta, ta wara masa ido tace "Bye" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo, can ya bi bayanta da sauri yace "Church kuma?" Ta kallesa tace "Eh Catechism xan je" rasa abinda zai ce mata yyi, ganin har ta fita ya bi ta yace "Which means baxa ki rakani ba knn, ke fa nake jira....." Ta juya tace "Ina xan rakaka?" Ya langwabar da kai yace "Clinic xan je duba patients dina" tayi shiru tana kallonsa, can tace "Toh church din fa, it's being a long time bn je church ba fa" yace "Ehh to daga can sai inyi dropping din ki a church din" bai jira cewarta ba ya juya ya dau car key a daki ya dawo yace "Mu je" yana gaba tana biye da shi suka isa gun motarsa ya bude mata snn ya tafi ya bude gate yana fita da motar ya fito ya rufe gate din snn ya shiga ya dau hanyar Clinic din da yake aiki, Ba tare da ya kalleta ba yace "Tell me about ur self!" Ta d'an kallesa sai kuma tayi murmushi tace "Ohk" jinginar da kanta tayi jikin kujera a hankali tace "Sunana Samantha David, but my baptism name is Rebecca, I am an only child, ni kadai parent dina suka haifa, I was born and brought up into a devoted Christian home, My maternal grandfather is a pastor, and my Mum Rachael took over  him my mum is a Ghanian....." Shiru tayi tana kallonsa, duk da ba kallonta yake ba idonsa na kan titi amma gaba daya hankalinsa na kan abinda take cewa, still ba tare da ya kalleta ba yace "Ur Dad?" Ta wara ido tace "Sunan Abbana Aliyu Umar, but he's baptism name is David, my paternal grandfather is a Muslim, a Fulani from Adamawa, he married my paternal grand mum that was a Christian after he converted her to Islam, my father was the 1st child daga shi sai kanninsa mata biyu, duk suna kanana babansu ya rasu, shine Mum dinsu ta daukesu ta koma Ghana sbda akwai yayanta Christian a can, and that was where she re- converted to Christianity, then Abbana was still practicing the Islamic religion but when he met my mum at Sikkim Manipal University SMU sai ya koma Christian shi ma, buy he's younger sis Khadija is still a muslim she's in kaduna....." Driving kawae Abuturrab yake amma da ganin yanayinsa kasan takaici ne karara a tattare da shi, Ta langwabar da kai tace "My dad is a politician, he's a true devoted Christian also like my Mum...." Gyada kai yayi don bai ma son ci gaban labarin yace "That's nyc...." ta kallesa tace "Toh ni baka fadi min about ur self ba" shiru yayi na d'an lkcin kafin yace "Am Aliyu Ahmad, an only son with three siblings, My mum was a lecturer then, My dad a soldier.... I think that's all" Kallonsa kawai take ya kure wakar da ke tashi a motar don bai son magana kuma, har ya isa asibiti bbu wanda yace komai, yana gama parking ya kalleta ya bude motar ya fito ita ma ta fito tana kare ma asibitin kallo, tana biye da shi a baya suka shige reception, nurses din sai gaishesa suke sai dai ya gyada masu kai, ita kuma su bi ta da kallo har suka haura sama ya bude office dinsa, sai da yasa ta fara shiga snn shi ma ya shiga ya bude curtains ya kunna A.c ya xauna, tana kallonsa a hankali tace "I will like to be a doctor like you also" d'an murmushi yayi ya mike ya nufi fridge ya fiddo coke biyu ya mika mata daya ta karba ya bude dayan ya fara sha, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu, ji tayi komai yayi burgeta yake, bai ajiye can din ba sai da ya shanye ya juya yana kallonta yace "If you study hard you will be a medical doctor also" wara ido tayi tace "Ohk I will by the grace of God" Wani d'an wardrobe ya nufa ya bude ya fito da pure white laboratory Coat dinsa ya saka ya dau stethoscope ya nufi kofa yace "taso mu je mu duba patients dina" mikewa tayi ta bi bayansa suka fita, haka ya dinga bin ward ward tana biye da shi duk jikinta a sanyaye ganin marasu lafiya abun tausayi a kwance, second to the last ward din da ya shiga ya juya bayan ya gama duba patients din ciki ya ga bbu ita, juyawa yyi da sauri ya fita ya ganta durkushe jikin bango hawaye a idonta, da mamaki yace "What happened?" Ta fashe da kuka ta mike tace "Doctor bana son gani kuma....." Rungume hannayensa yayi ya bude ido yace "is that why you are crying?" Bata ce komai ba sai hawaye, yyi murmushi yace "Alryt, tafi office ki jira ni" ba musu ta dau hanyar office din ya bi ta da kallo. Ko da ya koma office xaune ya ganta ta kife kanta da table, ya karasa yana kallonta ya duka gabanta, bak'in gashin kanta dake kyalli yake kallo ta dalilin xamewa da dankwalin kanta yyi, a hankali ya sa hannu ya karasa xame dankwalin don a rayuwar sa bbu abinda yake so kamar yaga gashin kan mace da tsayi, sai da ya rike breathe ganin gashinta din dogo ne ba na wasa ba ga tsantsi ga baki, kana ganinta kasan ta hada jini da Fulani, hannu ya daura a Hankali kan gashin yaji uban laushinsa, bude ido tayi ya koma baya da sauri ta mike xaune tana kallonsa tace "Doctor" wara ido yayi ya fara kame kame yace "Oh! you've... You've got a beautiful hair..... It's... It's very fine" mayar da dankwalin kanta tayi bata ce komai ba ya mike yana shafa kansa yace "har na gama duba patients din...." tace "Toh xan wuce church" kallon agogo yayi yaga biyar ya gota yace "Ohk...." Bude kofar office din aka yi, wani guy da baxai wuce Abuturrab ba ya shigo yace "Kai fa dan rainin wayo ne Aliyu, ina ta jiran....." Shiru yayi ganin Samantha, barin da ya ganta xaune kan office chair, Abuturrab yace "Yanxu fa da xan kira ka, to muje in ji urgent call din...." Daga haka ya nufi kofa, Jaheed dake ta kallon Samantha yace "Bakuwa kayi ne?" Abuturrab yace "Yea!" Snn ya fita, Mujaheed ya kalleta kafin yace komai tace "Ina yini" yyi murmushi yace "Lafiya lau, ykk" ta sunkuyar da kai tace "Lafiya lau" juyawa yyi ya fita, ba a wani dau lkci ba Abuturrab ya dawo yace "Ohk let get going" ta mike daga zaunen da take suka fita. Hanyar da yasan xa su hadu da traffic sosai ya bi da su, duk ta damu ita church, ko kallonta bai yi ba har sai da yaga shidda yayi yace "Wai karfe nawa ake tashi daga church din naku ne?" Kamar xata yi kuka tace "Six mana" ya dauke kai yace "Ashe ma an tashi kenan...." Bata kuma kulasa ba amma da gani xaka gane ranta ya baci, bai damu ba har ya isa kofar gidansu yyi parking xata fita ya riko hannunta, juyawa tayi tana kallonsa ya ga hawaye idonta, da mamaki yace "Kuka kuma?" Share idon tayi bata ce komai ba, yace "Toh Allah baki hakuri, but you can still go the church...." bata ce komai ba ta bude motar ta fita bai yi wata wata ba ya ja motarsa yyi reverse ya nufi gida ta bi motar da kallo, a sanyaye ta bude gate dinsu ta shiga. Abuturrab na dawowa daga masallaci ya bude abincin da ta kawo masa, Shinkafa ce da miya sai fried cow meat a wani gun daban da kayan vegetables da aka yanka, kallon abincin kawai yake duk da ya burgesa a ido amma bai jin xai iya ci, ya tabe baki ya mike ya dau naman ya kai ma karensa da ya fara sabawa da ya ajiye masa a cage, abincin kuma ya dauka ya kai ma masu gadi ya dawo ya xuba abincin da Ramla ta kawo masa ya ci kadan ya tafi masallaci, yana dawowa ya ganta da Mum dinta suna tahowa da kafa ko ina xa su, ido hudu suka yi da Mum din tata, tayi masa wani matsiyacin kallo da alamar ta tuno tare masu titi da yyi ranan ne, haka kawai yaji gabansa ya fadi, ya dauke kai ya ci gaba da tafiyarsa, Samantha sai kallonsa take har ya shiga gate. Washegari Sunday throughout bai ganta ba har yamma, duk sai yaji bbu dadi ganin har karfe shidda bai ganta ba, mikewa yyi daga karshe ya fita ya dau hanyar gidansu kamar me strolling har ya gama tafiyarsa bai ganta ba ya juya kawai ya dawo gida, har ranan laraba Abuturrab bai hadu da Samantha ba duk yaji sa bbu ddi har abun ya dinga basa mamaki, wai d'an sabon nn da suka yi har xai damu don bai ganta ba, yana xaune parlor tare da su Mami da yammacin ranan alhamis, Mami tace "Abuu!" D'agowa yyi da Sauri yana kallonta, tace "What's wrong with you?" Buda ido yyi yace "Nothing Mami...." Ta girgixa kai tace "Noo, ni fa na haifeka daga jiya xuwa yau naga you are not ur self....." Khaleesat tace "Mami baki yi noticing da kyau ba, for the past two weeks yanxu ya Turab ya canxa, he no longer talk to us, idan ma muka je part dinsa koran mu yake, he no longer treat us well...." Ilham tace "And he's alwayz closing his door don ma kar mu shiga" Ramlah tace "I think his dog is now his everything...." Abuturrab dai sai bin su da kallo yake, Khaleesat tace "or may be yana jin haushin Abba ya maida sa BQ ne, but it's not too late ya Abuu you can still beg him ya bar ka ka dawo nan" Abuturrab ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, Mami tace "Aliyu!" Kallonta yayi tace "Meye matsalar ka?" Ya girgixa kai yace "Bbu komai Mami, am just occupied with work ne yanxu" Mami tace "Toh shknn Allah ya mana jagora..." Mikewa yyi yana kallon khaleesat yace "Ke kuma kika sake ce min Turab sai na gurje bakin ki" daga haka ya kalli wayarsa dake ring yace "Jaheed ya xo Mami... Later xa mu shigo" Mami tace "Ohk Allah ya kai mu" daga haka ya fita xuwa bangaren sa Khaleesat ta bi sa da harara, Xaune ya ga Mujaheed yana ta kallon k'aren dake xaune cage, Abuturrab yace "Welcome!" Mujaheed ya mike yace "Yanxu pls meye ma'anar Dog din nn maimakon mai gadi" Abuturrab ya wara ido yace "Ya fi su iya gadi...." Mujaheed yayi dariya daga haka suka shiga parlor, Abuturrab ya dauko masu can coke a fridge, Jaheed yace "Kaga maganan serious nake son muyi Man kada kuma ka raina min hankali" Abuturrab bai ce komai ba sai da ya ajiye empty can din coke din hannunsa snn yace "Ina jin ka" Jaheed yace "Old man dina ne ya takura ni maganan aure this dayz wllh, am just confused donno what to do..." Abuturrab ya buda ido sai kuma yyi murmushi yace "Salima fah?" Harara Jaheed ya watsa masa yace "Salima har macen aure ce?" Abuturrab ya d'aga kafada yace "Ohk, nima of recent Dad dina ke min xancen aure...." Jaheed yace "Ae gwara kai kana da Saudat" Shiru Abuturrab yayi, Jaheed ya shafa kai yace "Gaskiya ka sama min solution, just few months ya ban if not ya hada ni da koma wacece ta  xo masa a kai" Abuturrab yyi yar dariya yace "Amma kuma duk yan matan ka Mujaheed" Jaheed yayi tsaki yace "Kaga if you don't have anything good to say in tashi in kara ma motata mai" Abuturrab yayi murmushi yace "Kawai ka fara neman mata yanxu...." Jaheed yace "Wacece wnn yarinyar da ka taho office da ita ranan" wani kallo Abuturrab ke yi masa, wanda hakan Mujaheed yace "Ohk sorry ban san budurwar ka bace" Abuturrab yace "Ba budurwa ta bace" Jaheed yace "Then why the frowning of face?" Abuturrab ya tabe baki, sai kuma yyi murmushi yace "She's a Christian" xato ido Jaheed yyi yace "Christian kuma?" Abuturrab ya gyada Kai, shiru jaheed yyi yana kallonsa, can ya girgixa kai yace "That's sad, amma a ina ka san ta?" Abuturrab yace "Ga gidansu can few houses from ours" Jaheed yace "Lallai, babban magana kenan" Mikewa Abuturrab yayi jin kamar motsi a gate ya fita da sauri jaheed ya bi sa da kallo, bai ga kowa gate din ba da kuma alamar iska ce don a bude Jaheed ya bar sa, juyowa yyi ya koma parlon. Washegari friday Abuturrab na dawowa daga masallaci misalin biyu da rabi ya dau faran kujerar roba ta xauna waje jikin flower yana dannar wayarsa kunnensa sakale da earpiece, tun daga nesa ya hangota tana tahowa, ya kasa dauke idonsa a kanta ko kiftawan kirki bai yi har ta iso inda yake, ga mamakinsa sai ya ga taki kallon gun har ta wuce sa, bai san lkcn da yace frnd ba, ta juyo tana kallonsa.

*Haske writers Asso*?✍?

? *Noorul Huda*?

7......

Sunkuyar da kanta tayi ta dawowa cikin sarkewar murya tace "Ina yini" kallonta kawai yake ganin yanayinta yace "Baki da lafiya ne?" Kin cewa komai tayi kuma taki d'agowa ya mike yace "Talk to me mana, what's wrong?" hawaye ya cika idonta ta gyada masa kai, kalle kallen anguwar yayi, kawai ya kama hannunta suka shiga gida ya kulle gate din, parlor ya nufa da ita bayan yasa ta shiga da takalmanta ya rufe kofar yana kallonta yace "Since when?"  xaunawa tayi kan kujera ta kwantar da kanta jiki ya durkusa gabanta yace "ina ke maki ciwo?" Xamowa kasa tayi ta hade kanta da gwiwa ta fashe da kuka bata ce komai ba, jin kukan nata ya dinga yi har xuciyarsa ya dago kanta ya dafa shoulders dinta da damuwa yace "Talk to me mana, ina ke maki ciwo" kalle kalle ta shiga yi can ta mike da sauri ya rikota xai yi magana ta toshe bakinta tana kkrin kwace hannunta, da sauri ya saketa ya mike ya kama hannunta suka nufi toilet dake parlon da ita, amai ta dinga kwararawa yana kallonta har ta gama tana mayar da numfashi ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya gyara wajen ya fito da ita, kwanciya tayi nan tsakiyar parlon tana juye juye, sai kuma ta fashe da kuka, ya hade rai yace "Kinga idan baxa ki min magana ba ki tashi kiyi tafiyar ki, leave now" mikewa tayi da kyar xata fita ba tare da ta kallesa ba ya bi bayanta da sauri ya jawota ta fado jikinsa, rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, sun kusa minti uku a haka ya dago kanta a hankali yana kallonta yace "You are on ur period?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba sai hawaye, komar da ita yayi ya xaunar kan kujera ya shiga bedroom dinsa, da yake baya rasa magunguna da allurori na Dysmenorrhea sbda kanninsa daukowa kawai yayi ya fito parlor, kwance ya ganta kasa, ya fara hada alluran yana gamawa ya dawo kusa da ita yace "Kin ci abinci koh?" Cikin kuka tace "Na sha tea" yace "Ohk, let me inject you, xa ki samu relief kin ji" bai jira cewarta ba ya fara daga doguwar gown din jikinta, ta rike da sauri don dama ita ba gwanar sa dogon wando bace, muryarta na rawa tace "Doctor ban sa komai ba...." shiru yayi yana kallonta sai kuma ya mike ya shiga daki ya dauko towel dinsa ya fito ya bata yace "to tashi ki daura," ta mike ta karba ya dauke kai ta daga gown din ta daura, kujera ta tafi tayi rub da ciki ta runtse ido ya bi bayanta, a hankali ya sauke towel din yayi mata alluran, yana gamawa ta fashe da kuka ya dagota xuwa jikinsa yace "It's okay xae daina maki yanxu" Kai kawai take gyada masa, sai da yaga ta nutsu snn ya saketa, ta xamo k'asa ta kwanta ta rufe ido, durkusawa yyi yana kallonta, ba a wani dau lkci ba bacci ya dauketa, ya mike yayi disposing syringe da kwalban alluran ya dawo parlon ya taimaka mata ta koma kan kujera. Yana bedroom aka danna bell ya fito da sauri ya nufi kofar, ganin Ramla ce yace "What again?" Tace "Ohh ya Abuu Mami ce fa ta aiko ni ka bude kofar plss...." ya hade rai yace "Pls go am busy yanxu, or you say it out there" murguda baki tayi don bata san yana kallonta ba tace "Ni fa....." Yace "Leave immediately idan ba haka ba xan sa ki kuka if I shud open this door" juyawa tayi fuu ta wuce. Sai kusan karfe shidda Samantha ta tashi daga baccin, yana parlor har lkcn yana danna laptop, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo tace "Wayyo my mum is at home...." ya kalleta snn ya kalli agogo ta mike da sauri xata sauke gown dinta ta cire towel dinsa taga towel din yyi stain, still tayi tana kallon wajen, ya mike yace "What" girgixa masa kai tayi ta nufi toilet dake parlon da sauri, ya bi ta da kallo, cire towel din tayi xata wanke taji yace "Don't worry xan wanke....." Kasa juyowa tayi ta girgixa kai tace "No, xan wanke" juyo da ita yyi yace "Nace xan wanke" ta sauke idonta kasa bata ce komai ba, murmushi yayi yace "Yess" ajiye masa tayi ta nufi kofa ta fice daga toilet din sannan ta bar gidan gaba daya, tana isa gida gabanta ya fara faduwa, daga taje chemist a bata Magani tun uku saura sai after six take dawowa, mai aikinsu Blessing ce ke ta goge goge parlor, Samantha tayi kasa da murya tace "Mumy fah Blessing?" Blessing tace "Ta fita church tun daxun" Samantha ta sauke ajiyar xuciya tace "Bata tambaye ni ba" Blessing tace "No, tayi tunanin kin sha Magani kin kwanta a daki ne" Samantha bata ce komai ba sai dai tausayin kanta kawai take don kwata kwata Mumynta bata da wani lkcnta sai na church, duk ciwon da xata yi bbu abinda xae sa Mumy tayi fashin church in ma bata tilasta ta a hakan sun je church din tare ba, ga Abbanta ba wani xama yake ba ta dalilin aikinsa. Washegari asabar da safe Mumy ta shirya xa su Kaduna da tawagar pastoci kamar ta, Samantha na bacci ta tada ta tace "Rebecca you take care of ur self plss xan tafi yanxu, idan baxa ki xauna tare da Blessing ba ki tafi gidansu Stella, by the grace of God ran Monday ko Tuesday xa mu dawo, ki tabbatar kina shan maganin ki...." Samantha dake ta murxa ido tace "Toh Mumy Abba yaushe zai dawo?" Mumy tace "I don't know, just take care of ur self and make sure kin je church anjima da yamma da gobe da safe even if you cannot go to lesson" Samantha tace "Ohk, amma ni gidansu Stella xanje, Blessing ta tafi gida kawai" Mumy tace "Ohk better, ki kuma tabbatar kin tafi da wayar ki ni ban ga amfanin wayar nn naki da kike yasarwa a daki ba" Samantha tace "Toh xan je da shi Mumy, ki taho min da abu me ddi kin ji" Mumy ta nufi kofa tace "Ohk, tashi ki yi wanka ki ci abinci ki sha magani" daga haka ta fita, Samantha ta kalli agogo taga karfe takwas yayi, hamma tayi ta mike ta shiga bathroom, wanke baki tayi, tayi wanka snn ta fito ta kimtsa jikinta ta shirya cikin doguwar rigarta 'yar kanti pink colour da flowers din blue, ta fito da plain veil dinta blue colour ta daura a kai, bata wani yi make up ba sai eye pencil da tasa a ido snn ta sauko, tea kawai ta iya sha dan idan tana period bata iya cin abinci, tana xaune parlor tana ta kallo har Blessing ta gama aikinta tace "Blessing xa ki iya tafiya gida sai Monday nima gidansu Stella xan je ynxu" ba a wani dau lkci ba Blessing ta wuce. Samantha ta kashe kayan wutan gidan gaba daya misalin karfe tara ta hada kayanta kala uku ta dau bible dinta da textbooks na karatu da yake saura sati uku su fara Waec, a hannu ta rike wayarta ta fito ta kulle main gidan tayi ma mai gadi sallama ta wuce, tafiya take kamar mai tausayin kasa har ta iso gate din gidansu Abuturrab, har ta wuce ta dawo ganin kamar gate din a bude yake ta leka, ai ko ta gansa xaune yana sanye da singlet da short hannunsa rike da lighted cigarette, ido hudu suka yi ta juya da sauri xata bar wajen ya mike yace "Frnd" bata ko juyo ba, ya wurga taban hannunsa ya fita gate din, Sauri ya ga tana xubawa yace "Uhm not even a good morning frnd?" Tsayawa tayi bata juyo ba, ya rungume hannayensa yace "Hmm ae shikenan...." Juyowa tayi ta masa murmushi tace "Good morning" yafito ta yyi, ta make kafada, yayi shiru yana kallonta, ta langwabar da kai tace "lesson xan je" yace "Ohk" daga haka ya juya ya koma cikin gate, bin sa da kallo tayi a sanyaye can ta bi bayansa, tsaye tayi bakin gate din tana kallonsa tace "Are you angry" ba tare da ya kalleta ba yana tsaye kusa da karensa yace "No!" Shiga gate din tayi ta rufe ta karasa kusa da shi kamar xata yi kuka tace "You are" ya juya yana kallonta yace "Am not" murmushi tayi tace "Am sorry Dr, um naga baka shirya bane" rungume hannayensa yayi yace "Uhm ban shirya ba kamar ya?" Sunkuyar da kai tayi tana murmushi tace "Kila fa baka yi wanka ba...." Murmushin yayi yace "Toh mu je ki min" xaro ido tayi sai kuma ta juya da sauri xata bar wajen ya rikota yace "Ae sai kin min" boye fuskarta tayi a kirjinsa tace "Nooo Doctor lesson xan....." Rufe bakinta yayi ya ja ta suka shiga parlor ya rufe kofar da makulli.

*Haske writers asso* ?✍?

? *Noorul Huda*?

_Happy Belated born day Asmy B Aliyu, age with grace dear sis, Allah ya karo shekaru masu albarka ya nuna mana auren ki mu xo mu sha biki_?

8.....

Kwace hannunta tayi kamar xata yi kuka tace "Doctor...." Yace "Toh in ruwan ki da rashin wanka na?" a hankali tace "Toh yi hakuri...." Murmushi yayi ya juya ya nufi daki ta bi sa da kallo, can ta ajiye jakar hannunta ta xauna tana kallon program din da ake a tv, bayan minti kusan ashirin taji an danna bell, mikewa tayi da sauri tana kallon kofar, ji tayi ance "Ohh ya Abuu me yasa kake kulle kofa ne yanxu, ni dai ka bude min Mami ce ta aiko ni wllh...." Da sauri Samantha ta mike ta shige bedroom dinsa ta tura kofar tayi lamo jiki, kwata kwata bata ji fitowarsa ba sai gyaran muryarsa da taji a bayanta ta juyo da sauri, daure yake da towel a waist, bakin gashin kirjinsa ya kwanta luf luf don ko goge jiki bai yi ba, a rikice ta juya xata bude kofar dakin ya riko hannunta  kamar xata yi kuka tace "Doctor ur sister is outside.... Shi yasa na shigo" key ta ga yasa ma kofar ta juyo da sauri tana kallonsa a tsorace, ya wara ido yace "Tell me what you are afraid of?" Girgixa kai tayi da sauri tace "Noo... Nothing" yayi 'yar dariya yace "Why is it that girls always have this negative thought?" Juyawa tayi bata ce komai ba, yayi murmushi ya kamo hannunta yace "Am not a bad person, erase that thought off ur mind immediately" a hankali tace "Ohk!" Ya kama hannunta ya nufi gado da ita ya xaunar da ita gefen gadon, snn ya dau kayansa ya shiga bathroom, ba a dau lkci ba ya fito sanye da kananun kaya ya dau turaren gaban mirror ya feshe jikinsa da shi ya karasa kusa da ita ya feshe ta ita ma, boye fuskarta tayi jikin gado tana murmushi, can ta dago a hankali taga bbu shi a dakin, mikewa tayi tana kare ma dakin kallo, ko ina fes except from the bed that's untidy, murmushi tayi ta bude curtains din room din ta fara gyara gadon, cikin yan mintuna ta gama ta fita xuwa parlor, xaune ta gansa cup din coffee a hannunsa, ta wuce kitchen ta dauko sweeper da mop ta dawo ya bi ta da kallo har ta shiga bedroom, tana fitowa yace "Well done, thank you" tayi murmushi ta kai abubuwan hannunta kitchen ta fito, yace "Come and make a tea for ur self" tace "Nayi breakfast" yace "Nasan kin yi ae, karawa xa kiyi" tace "Noo na koshi sosai" kan kujera ta nufa ta dau jakarta yace "Ina xa ki?" Tace "Lesson!" Yace "Lesson da jakar kaya?" Ta kallesa tace "Aa xan ajiye gidan wasu family frnds dinmu ne, Mumy ta tafi Kaduna, Abba baya nan, ni kadai baxan iya zama a gida ba shine xan je gidansu" Abuturrab ya ajiye Mug din hannunsa yace "Sbda kina tsoron abu xai cinye ki?" Dariya tayi tace "A'a ni bana tsoro kawai bana son in xauna ni kadai ne" yace "Ohk...." Xaunawa tayi kan kujera ta dalilin ciwo da taji cikinta ya fara mata, kamar ko ya sani yace "Kin samu lafiya Yanxu?" Kai kawai ta gyada masa ta jinginar da kanta jikin kujera, ya bude warmer din dake dauke da wainar shinkafa ya debi biyu ya kalleta ya ga kallonsa take, yace "Taho mu ci" a hankali tace "Masa?" Ya gyada mata kai, tace "Sa min guda daya" yace "Sauko mu ci dai" ba musu ta sauko ta dawo kusa da shi ya kara masu guda biyu, ya debi rich vegetable soup din dake wani warmer a waje daban ya fara ci da spoon, dauka tayi ita ma ta fara ci, ganin yanda take ci kamar ana tilastata yace "Bai maki dadi ba ne" girgixa masa kai tayi da sauri tace "Yayi dadi...." Yace "Then me yasa kike haka da fuska" kamar xata yi kuka ta ajiye Masan hannunta ta kwanta gefensa tace "My tummy" sai kuma ta mike ta koma kan kujera ta kwanta, bin ta yayi da kallo ya ajiye spoon din hannunsa yace "Ya fara maki ciwo" kai ta gyada masa lkci daya hawaye ya cika idonta, a hankali yace "Sorry" mikewa yayi ya shiga bedroom sai ga shi ya fito da allura da Magani ya dawo kusa da ita ya shiga hada alluran, yana gamawa ya kalleta yace "Toh juyo in maki sai ki sha Magani" ba musu ta juyo har xata daga gown din sai ta tsaya kuma, kallonsa tayi hawayen da ke makale idonta ya silalo ta juya masa baya tace "Bude min zip din pls" bude zip din yyi a hankali, ta cire hannun gown din don akwai ves jikinta, ta sauke gown din kasa yanda xai iya yi mata alluran snn ta juya masa baya ta kwanta, daukar syringe din yayi ya mata alluran ta juyo tana kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "Sorry!" Ya mike ya dauko table wata ya bata maganin ta sha snn ta koma ta kwanta, bayan awa daya ya kalleta ya ga idonta biyu, yace "Ya daina" ta gyada masa kai, har bayan azahar tana gidan a kwance, yana dawowa daga masallaci bayan anyi la'asar ya durkusa kusa da ita yace "Baki ci abincin ba har ynxu" ta girgixa kai tace "Baxan ci ba" mikewa yayi ya shiga daki ya shirya ya fito da makullin mota yana kallonta yace "Xan je clinic in dawo yanxun..." Mikewa tayi tace "Gida nima xan je" ya hade rai yace "Noo kiyi kwanciyar ki kina tashi cikin xae fara, don't worry i will lock the door" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita, har shidda bai dawo ba, ta sauko da kyar jin cikin xae fara mata ciwo ta xuba abincin da aka kawo masa daxu ta ci kadan ta dau sauran magungunan da ya bata ta sha ts koma ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa..
A hankali ya durkusa kusa da ita yana kallonta ganin tun da ya dawo take bacci, can ya kalli agogo ya dafata yace "Frnd!" Da gani kasan bacci me nauyi take da kyar ta bude idonta, yace "Cikin ya daina" ta gyada masa kai a hankali hade da lumshe ido, dagota yayi yace "Taso ki kwanta a ciki, there might be mosquitoes here" girgixa kai tayi cikin sanyin murya irin ta mai bacci tace "A'a gida xan tafi" bai kulata ba ya dagata ta rike sa ta dalilin jiri da taji, ya ja ta xuwa bedroom dinsa, tace "Noo Doctor I want to go home...." Kwantar da ita yyi kan gadonsa ya dau lallausan duvet ya rufa mata ya kai bakinsa kunnenta yace "Go to sleep" rufe ido tayi ya gyara mata gashin kanta a hankali yace "Sleep tight Sam~ha" mikewa yayi ya kashe mata fitilan dakin ya bar na bed side snn ya dau wani duvet din ya fita parlor don idan yace xai shiga wani dakin ma tare da k'ura xa su kwana, kashe wutan parlon yyi ya kwanta kan 3 seater ya lulluba da duvet hade da lumshe ido, ya dade bacci bai daukesa ba, daga karshe dai baccin yayi awon gaba da shi bai tashi farkawa ba sai ana kiran assalatu, mikewa xaune yyi bayan yyi adduar tashi daga bacci ya kusa minti ashirin a haka kafin ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala, raka'atainul fajr yyi yana ta xaune kan darduma har yaji xa a tada sllh a masallaci snn ya mike ya fita ya kullo kofar ta waje, ko da ya dawo durkushe ya ganta kusa da gado idonta lumshe ta hade tafin hannunta alamar addu'a take, ya jingina jikin kofa yana kallonta cike da tausayi har dai ta gama, tana ganinsa tayi murmushi cikin sanyin murya tace "Good morning Doctor" ya mayar mata da murmushin yace "Morning how's ur health?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki yanxu" mikewa tayi ta fara gyaran gado, ya shiga bathroom sai ga shi ya fito da toothpaste da new toothbrush ya ajiye mata gaban mirror ta kallesa tace "Thank you" murmushi kawai yyi ya fita, main house ya nufa don xuwa gaida Mami, a kitchen ya sameta tana hada ma Abba breakfast ya gaisheta ta amsa tace "How was ur nyt!" Yace "Alhmdllh,  mene yasa su Ramla ba su yi girkin ba" tace "Na ma gama, he's travelling ne shi yasa...." Abuturrab yace "To where?" Tace "Shiga ka tambaye shi mana" juyawa yayi ya fita ya wuce part din Abbansa, yana kkrin rufe briefcase dinsa ya shigo, Abba yace "How you?" Xaunawa yyi kasa yace "Alhmdllh tafiya xa kayi Abba?" Abba yace "In shaa Allah, ya maganar da muka yi da kai ranan?" Shiru Abuturrab yyi, lkci daya jikinsa yayi sanyi, Abba yace "This is not a matter of u looking at me that way, Yakumbo tace hada bikin da na Yusuf xa ayi..." Kamar xai yi kuka yace "Abba ni fa bani da kowa" Abba yace "That's not a problem, sai ka fara nema yanxu don ina jin nn da watanni biyar ne bikin Yusuf din, idan kuma ka amince mu yi maka xabi it's okay my Stubborn!" Abuturrab bai ce komai ba, Mami ta shigo da sallama rike da tray din breakfast, mikewa Abuturrab yyi ya sallami Abban nasa ya fice, ji yyi ransa ya baci, bai ko kalli Khaleesat dake gaishesa a parlor ba ya fice ya koma bangaren sa ya kusa minti ashirin xaune a waje kafin ya shiga ciki, shara ya sameta take a parlor, ya xauna kan kujera yace "Wel done" murmushi tayi bata ce komai ba, har ta gama ta shiga kitchen ma ta gyara, ya mike ya shiga bedroom yana fitowa ya kalleta yace "Na hada maki ruwan wanka a bathroom...." Xata yi magana wayarta ya dau ring a jaka, karasawa tayi da sauri ta ciro wayar taga Mumy ce ke kiranta, kallonsa tayi sai kuma ta xauna ta daga ta kai kunnenta, daga daya bangaren Mumy tace "Samantha kin shirya tafiya church kuwa?" Turo baki tayi tace "Mumy baki ko tambaye ni ya ciki na ba..." Mumy tace "Ohk ya cikin" kamar xata yi kuka tace "Yana sauki..." Mumy tace "Ohk toh ki shirya kar fa kiyi latti, and make sure yau ma ki tafi gidansu Stellq kar ki kwana ke kadai" Samantha ta kalli Abuturrab dake ta kallonta a hankali tace "Ohk mum" daga haka uwar ta katse wayar, Ta mike tana kallonsa tace "Xan je gida in shirya" yace "Cinye ki xa ayi a nn idan kika shirya," murmushi tayi tace "A'a xan dauko abu ne" yace "Pad?" Xaro ido tayi tace "A'a fah!" Yace "Toh me?" Ta langwabar da kai tayi shiru, yace "Toh tafi kiyi Wankan ki" a hankali tace "Toh" snn ta nufi bedroom din, ko kafin ta fito har ya kai mata jakar kayanta dakin, tana fitowa ta shirya da sauri da sauri tana tsaye gaban mirror xata daura dankwali aka bude kofar dakin, juyawa tayi da sauri, tayi still a gun ganin Ilham, ita kanta ilham kasa motsi tayi bakin kofar, can ta juya da sauri ta fita daga dakin, Abuturrab dake baya gun Gym dinsa ya zagayo don daukan Coke ya ga takalman Sister tasa a bakin kofa, kasa shiga yyi sai gata ta fito, bata ko kallesa ba xata wuce sa ya rikota da sauri yace "me kike nema nn Ilham" fixge hannunta tayi tace "Yaya wacece ita?" Jawota yyi jikinsa yace "listen she's just a frnd lil sis....." Kamar xata yi kuka tace "Noo yaya me yasa kake haka...." Dago kanta yayi yace "Wllh frnd dita ce ilham, trust me.... You've got a decent brother" tace "Amma ae bai kamata ta shigo maka gida har bedroom ba sae kace ba musulma ba" yace "No but she's a Christian, an innocent Christian" shiru Ilham tayi Tana kallonsa, yace "Trust me sis" tabe baki tayi bata ce komai ba, yace "Promise you won't say anything... Even to Khaleesat and Ramlah" turo baki tayi tace "Naji" yayi murmushi ya ja hancinta yace "That's my sis, taho inyi maki introducing dinta, she's a nyc gal" girgixa kai tayi a takaice tace "Noo I hate Christians" daga haka ta wuce ta bar sa gun a tsaye ya bi ta da kallo, can ya shiga parlon yaga Samantha na hada kayanta tana ganinsa kamar xata yi kuka tace "Am sorry doctor...." Yace "For what?" Hawaye ya cika idonta tace "Ur sis...." Murmushi yayi yace "Ae bbu ruwanta ita...." Bata kuma cewa komai ba ta dau jakarta tace "Xan tafi" ya mata wani kallo yace "Sai kin yi breakfast" tace "Noo nayi late for church" yace "toh baxa ki fita ba sai kin yi breakfast ki sha Magani" shiru tayi tana kallonsa, yace "Yes!" Daga haka ya wuce bedroom, xaunawa tayi parlor tayi tagumi, bata ji shigowar Ilham ba sai ganinta tayi parlon rike da tray din abinci, ko kallonta ilham bata yi ba ta ajiye xata fita sai kuma ta nufi bedroom dinsa, Samantha ta bi ta da kallo duk jikinta yyi sanyi, Abuturrab na ganin Ilham yace "Sis kin rufe kofar...." Ta hade rai tace "Breakfast na kawo maka gashi can a parlor" mikewa yayi ya kama hannunta suka fito parlor yana kallon Samantha yace "Meet my Lil sis Rabi'ah but we do call her ilham!" Samantha ta kalleta tana kirkiran murmushi tace "it's nyc meeting you ilham" Bbu yabo bbu fallasa Ilham tace "Same" ta kwace hannunta tayi hanyar kofa, ko kadan Abuturrab bai ji ddin yanda ta amsa ba, ya bi bayanta suka fita a tare, sai da suka yi nisa ya fixgota yace "Why did you answer her that way?" Bluntly tace "Because I don't like her" hade rai yayi yace "Then you don't like me also" da mamaki tace "Toh meye hadin ka da ita ma yaya, ni I hate her...." Wani tsawa yayi mata tayi tsit, strictly yace "Idan kika sake cewa you hate her I won't take it likely with you, me tayi maki?"

*Haske writers association*?✍?

? *Noorul Huda*?

9.....

Juyawa tayi, tayi wucewarta ta bar sa gun a tsaye, ya bi ta da wani mugun kallo, can yyi kwafa ya juya ya koma parlor, wayam yaga parlon ya kalli gun da takalmanta suke  ya ga ba su wato ta wuce, da sauri ya fita ya bi bayanta, can ya hango ta xata main road sai tafiya take da sauri da sauri, bata san yana bin ta ba har sai da ya isa dab da ita ya fixgo hannunta, ta juyo a tsorace tana kallonsa, kamar xata yi kuka tace "Doctor church xan wuce am almost late" ya mata wani kallo yace "Toh baxa ki ba, uwar me ake k'ara ki da shi a church din?" Shiru tayi tana masa kallo irin ta mamaki, ya ja hannunta ta dinga bin sa har suka iso gida ya kulle kofarsa, breakfast ya nuna mata ya wuce daki, a hankali ta xauna kasa hawaye cike idonta sai kuma ta fara kuka a hankali, sai kusan Karfe goma ya fito shirye cikin kananun kaya as usual, bai ko kalleta ba ya nufi gun breakfast din dake ajiye har lkcn ya xauna ya shiga hada tea, ya debi potatoe da egg kawai ya fara ci, kin dago kanta tayi don har lkcn hawaye take, ya gama cin abinda xai ci ya mike yyi kwanciyarsa kan dogon kujera, ko kukan jini xaki yi baxa ki Church din nn yau ba, ya fadi hakan a xuciyarsa tare da jan tsaki a fili, Har sha biyu da rabi tana wajen a xaune shi ko yyi bacci abun sa hankali kwance, kiran sllh ya sa shi tashi ya mike xaune yana kallon agogo, ga mamakinsa har lkcn tana nan a yanda yake, ya mike bai ko kalleta ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito ya jima bedroom kafin ya fito don tafiya masallaci, bin sa da kallo tayi har ya fita sai kuma ta fashe da kuka. yana fita ya kulle kofar ta waje yayi tafiyarsa, ana idar da sllh main house ya shiga ya tadda Mumy a bedroom da sistern ta Mariya, ya xauna murmushi dauke fuskarsa yace "Mumy yaushe kika xo?" Tace "Tun daxu, nayi xaton baka ma gidan ne, baka je aiki yau ba knn?" Ya shafa kansa yace "Sae da yamma nake tafiya da week end" tace "Toh Allah ya taimaka, kwana biyu ka guje ni Aliyu" yar dariya yayi yace "Mumy aiki ne ya sha min kai wllh...." Hajiya Mariya tace "Toh Allah rufa asiri...." Mikewa yayi yace "Amma sai da dare xaki wuce koh?" Tace "Anything for me?" Dariya yayi yace "in dai da nyt xaki tafi nasan na dawo daga aiki then sai in maida ki gida" tace "Toh shknn xan jira har ka dawo" daga haka yayi masu sallama ya fita, dakin sisters dinsa ya leka ya gansu suna kallo a system, tsaye yyi bakin kofa ya rungume hannayensa yace "Ba islamiyya yau?" Ramlah tace "Sae anjima" kallon ilham da taki kallonsa yake, ganin yanda ta hade rai tana kallon ya karasa dakin ya dagota, kwace kanta take son yi tana tura hannunsa ya dauketa cak suka fita daga dakin, Khaleesat ta kalli Ramlah suka tabe baki a tare, a downstairs ya direta xata gudu ya fixgota yace "Haba my Lil sis baki son abinda nake so kenan?" Kallon mamaki take masa sai kuma tace "Son ta kake yaya?" Da sauri ya girgixa kai yace "Noo ba haka nake nufi ba, I thought you will also buy the idea of  being her frnd too, bata da matsala ko kadan, assignment take kawo min in mata, her home is just few houses away from ours, she's nyc....." Tabe baki ilham tayi tace "Ni dai bana son tana xuwa har cikin parlor da bedroom din ka, baka san shaidan is real ba koh?" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya danne dariyarsa yace "Na sani mana lil sis.... Amma kinsan ur brother is decent, he can't do anything silly...." Tabe baki tayi tace "Ni dai ina gaya maka" ya ja hancinta yace "Ohk naji my sis, but ki daina daure mata fuska plss kin ji" tace "Na ji" daga haka ya saketa yace "Good of u, kar kuma kice ma su Ramla komai, more especially that stupid Leesat" bai jira cewarta ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. Yana isa part dinsa ya ganta xaune har time din tana hawaye, da kamar baxae ce komai ba ya nufi bedroom sae kuma ya dawo yana kallonta ya rungume hannu yace "When ake tashi a church din" kallonsa tayi bata ce komai ba tana share hawayen ta, yace "Answer me!" A hankali tace "Karfe daya" kallon agogo yayi yaga dayan ya wuce, ya koma kofa ya bude yana kallonta yace "Ohk tashi ki tafi, a gaida mutan church!!" Mikewa tayi ta dau jakarta da books ta nufi kofar ta fita snn ta juya tana kallonsa, rufe kofarsa yayi, ta juya a sanyaye ta tafi xuwa gate ta bude a hankali ta fita, gida ta nufa don ta san an tashi a church din, tana isa ta shiga kitchen don yunwa ba kadan ba take ji, doya ta fere ta soya da kwai ta hada tea rabin cup ta dawo parlor ta ci, tana gama ci ta kwanta sai bacci. Hadari ne ya tada ta, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo ganin yanda garin yyi duhu, taga karfe biyar har lkcn tafiyarta catechism ya wuce tana bacci, mikewa tsaye tayi jin iska ta hau sama ta rufe windows gaba daya, garin yyi bakikirin, tsoro ne ya kamata tunawa da tayi ita kadai ce fa yau, parlor ta dawo ta rakube jikin kujera lkci daya ruwa me karfi ya sakko, har shidda ruwa ake kamar da bakin kwarya, tsawan da ake ne ya kara rikitata don ko kadan bata son tsawa, wayarta ta dauka ta fara kiran Mumy ta kira ya kai sau biyar no answer, ta kira Abba shi ma haka, ta fashe da kuka ta kife kanta da kujera, har karfe bakwae tana nan a haka, can tayi karfin halin mikewa xata kunna wutan parlor aka yi wani tsawa ta koma da sauri ta rufe fuskarta, ganin parlon yyi bakikirin sbda duhu yasa ta mike cike da karfin hali ta karasa ta kunna sai taga bbu wutan ma, dawowa tayi ta kunna wayarta ta shiga tunanin ko ta hada kayanta ta wuce gidansu Stella kawae, bata tsaya wani tunanin ba ta wuce sama da sauri ta dauko uniform dinta da duk abinda tasan xata bukata ta xuba su jaka, ta canxa kayan jikinta snn ta dawo parlor ta shiga store don dauko umbrella, tana dauka ta fita nan taga ruwan ba na wasa bane ake yi ga iska, kin komawa parlor tayi, tayi ta tsayuwa a balcony, har takwas na dare, hawaye ne ya shiga sakko mata, can ta rufe kofar kawae ta shiga ruwan a haka da umbrella din, mai gadi ya leko daga windon dakinsa yace "Madam ina xuwa cikin ruwan nan?" Ta kallesa tace "Gidan Anty xan je...." Bata jira me xai ce ba ta fice da sauri, haka ta dinga tafiya duk a tsorace tabi ta kankame leman ganin iska na neman dauketa da shi ga walkiya dake ta haskata, ta d'an yi nisa ta ji haushin karnuka, bata kuma san ta ina ne ba, bata san lkcn da ta wurgar da lema da jakar hannunta ba, ta fasa wani ihu ta fara gudu, tun daga nesa ta hango mota na tahowa hakan bai sa ta fasa gudun da take ba, ganin an dallareta da fitila yasa ta tsaya tana rusa kuka, duk tayi jagab, ana bude motar ta ci gaba da gudunta, bin bayanta yyi da sauri har ya isketa ya fixgota, ta fasa ihu ko ina na jikinta na rawa, daga sama har kasa yake kallonta, ta rufe bakinta da hannunta, lkci daya shi ma yayi jagab, yace "Where are you coming from?" Hanyar gidansu kawai ta iya nuna masa, ya ja ta suka nufi gate ya ciro makulli ya bude yana rike da hannunta suka shiga ya bude kofar parlor ya shigar da ita snn ya bude gate ya fita ya shigo da motarsa yana gama parking ya fito ya rufe gate din ya koma parlor tana nn tsaye inda ya bar ta sai rawan sanyi take, kunna wutan parlon yyi ta sunkuyar da kanta, yace "Baki tafi church din kin tsaya can ba da kika ga hadarin kenan?" Shiru tayi bata dago kanta ba, ya tabe baki ya rufe kofarsa ya wuce bedroom ya dauko towel ya dawo ya mika mata, karba tayi ganin taki motsi yace "Go to the bathroom, take off those clothes nd stop shivering" bata ce komai ba ta nufi bedroom din nasa ta shiga bayi ta cire kayan ta daura towel din, jikin gado ta rakube don wani mugun sanyi take ji. Fita Abuturrab yayi bayan ya dauko umbrella ya nufi main house, Mami dake bedroom dinta tare da su Ramlah tace "Har ka kai ta?" Yace "Eh Mami..." Mami tace "Toh meye na yawo da jikakkun kaya kuma..." Yace "Yanxu xan tafi in cire" bai jira tace komai ba ya fita ya shiga dakinsu Ramlah, closet dinsu ya bude yana yi yana waige waige ya dauki wani riga me kauri da yayi kama da na bacci ya rufe press din dai dai lkcn da aka bude kofa, da sauri ya boye rigar a bayansa, Khaleesat ta shigo, daga sama har kasa take kallonsa tace "What are you hiding ya Abuu?" Ya hade rai yace "Nothing"

*Haske writers association*?✍?

? *Noorul Huda*?

10....

Karasowa tayi xata xaga ta bayansa ya maza ya juya ya turata kan gado ta fadi, kafin ta juyo har ya fice ta mike da sauri ta bi sa, a stairs ya kusa cin karo da Ramlah ta je hado ma Mami tea, ya boye rigar a bayansa da sauri, tace "What are you hiding...." Bai tanka ta ba ya sauka ta bi sa da kallo sai ga Khaleesat da gudu tace "Sis meye hannunsa?" Ramlah ta buda hannu alamar bata sani ba, Abuturrab na fita ya dau umbrella dinsa ya nufi part dinsa, yana shiga yasa key kofa don yasan cunning sisters din nasa na iya biyo sa, har lkcn tana durkushe kusa da gado ta takure waje daya, kashe Acn dakin yyi gaba daya ya karaso ya durkusa gabanta ya mika mata rigar yace "Wear this" ba tare da ta kallesa ba ta sa hannu ta karba, ya mike ya bude closet dinsa ya fiddo jallabiya ya fita, tashi tsaye tsyi ta sa rigar taga iyakarsa da kadan ya wuce kneel, bathroom ta karasa har lkcn rawan sanyi take, ta shanya masa towel din ta fito ta koma inda take ta xauna, bayan kusan minti talatin har bacci ya fara daukarta taji muryarsa a kanta, bude ido tayi da sauri ta gansa durkushe gabanta yana sanye da jallabiya hannunsa rike da cup din tea yace "Take!" Sunkuyar da kanta tayi tasa hannu ta karba ya mike ya fita, ba laifi ta sha tea din da yawa ta ajiye wanda ta rage, ta kalli agogo taga goma ya kusa, wayarta ta tuna yana cikin jakar da ta yar a titi, jinginar da kanta tayi jikin gado a sanyaye, sae gashi ya dawo ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Toh tashi ki kwanta sarkin yan xuwa church!" Bata ce komai ba ta mike a hankali tana kallon gadon, hawa tayi ta takure gu daya ta kwanta, yayi murmushi ya rufa mata duvet yace "Sae da safe" murya can kasa tace "Thank you" kashe mata fitila yayi bayan ya dau wani bargon ya fita ya rufo kofar, parlor ya koma ya kwanta kan 3seater. Can cikin dare tarin ta ya tada sa, ya dde xaune ganin har lkcn yi take yasa shi mikewa ya nufi bedroom din, bude kofar yyi ya kunna fitila ya karasa ya cire bargon yana kallonta, kakkarwa ya ga tana yi ga numfashinta na sama, ta bude ido tana kallonsa, hannu ya daura kan goshinta yaji xafi sosai, ta rike hannunsa a hankali yace "Are you Asthmatic?" Girgixa masa kai tayi yace "But you have pneumonia?" Bai jira tace komai ba ya mike ya bude closet ya fiddo babban sweater dinsa ya dawo ya dagota ya sa mata da kan shi ya kwantar da ita, kallonta ya tsaya yi yana tunanin taimakon da xai mata ganin yanda numfashinta ke yi, mikewa yyi ya dauko rub ya dawo ya bude zip din sweatern ya mika mata yace "Tashi ki shafa a chest din ki, it will help...." Jin bata ce komai ba ya bude ya diba sai kuma ya rasa yanda zai yi, imagine yyi da daya daga sisters dinsa ne ke shoe din nn ya xae yi, daga rigar xae yi ya shafa masu, yana wannan tunanin kawae ya daga rigar baccin jikinta ya sa hannu ya fara shafa mata rub din all over her body, hannunsa ta rike da sauri tace "Doctor..." A hankali yace "Yes am only being the doctor I am" bai kuma sauraranta ba ya shafe duk jikinta da man xafin, rufe ido tayi taki budewa, yana gama ya xuge xip din sweatern ya lulluba mata bargo murya can kasa yace "Go to sleep" bata ce komai ba bata kuma bude idon ba ya mike ya kashe fitilar ya fita, har bakwai bata tashi a bacci ba shi ma bai tasheta ba sanin jiya bata wani yi bacci ba, wanka yyi ya fito ya gama shirinsa a dakin sannan ya dawo parlor ya kunna laptop yana dube dubensa, can ya mike ya shiga kitchen don hada coffee, yana fitowa ya ga kofa a bude ya kalli kofar bedroom ya ga a bude shi ma, da sauri ya karasa bedroom din don a tunaninsa tashi tayi, tayi wucewarta, still yayi bakin kofa ganin khaleesat tsaye, ta juyo tana  masa wani irin kallo, duk ya daburce, juyawa tayi xata wuce ya rikota ya ja ta suka fita balcony yace "look leesat, she's just a frnd.... Bata da lafiya ne wllh..." Kamar xata yi kuka tace "Ni dai ba ruwana, ko nace maka wani abu ne.... Ni dai bance komai ba, ba ruwana" marairaice mata yyi yace "Baki yadda da brothern ki ba knn?" Wani kallo ta jefa masa ta warce hannunta tace "Eh ni ban yrda da kai ba kuma, dama shi yasa this days baka son muna xuwa wajen ka koh?" Hade rai yayi yace "I said she's my patient, are you daft?" Tabe baki tayi ta juya tayi wucewarta, da sauri ya bi ta ya fixgota fuskarsa daure yace "One word about what you just saw will mean you spelling dooomm" saketa yayi ya koma parlonsa, bai dade da shigowa ba peter ya kawo masa breakfast, takwas saura 'yan mintuna ya shiga bedroom bayan ya gama cin abinda xae ci na abincin da aka kawo masa, xaune ya ganta kan gado ta lulluba da bargo, tana ganinsa ta sunkuyar da kai, ya karaso bakin gadon yana kallon gashinta da yyi scatter all over, yace "Good morning" kallonsa tayi tayi murmushi bata ce komai ba, cire bargon jikinta yyi ta jawo da sauri ta rufe, buda ido yayi sai kuma ya d'an yi murmushi yace "ohk.... How's ur health?" Kai ta gyada masa ya juya ya fita, mikewa tayi bayan ta cire bargon ta nufi bathroom, ta tara ruwan xafi ta tsirka sannan ta wanke fuskarta, ta dau Listerine mouth wash/freshner dake bayin ta wanke bakinta snn ta fito, tsaye ta gansa dakin gaban mirror ta juya masa baya da sauri, karasawa yyi bayanta ya dafa shoulders dinta ya juyo da ita, ji tayi kamar ta nutse cikin sarkewar murya tace "Ina kwana...." Kallon kwayar idonta yake sai kuma yayi murmushi bai dai ce komai ba, ta sunkuyar da kanta, saketa yyi yace "xan tafi aiki yanxu....." Da sauri ta dago tana kallonsa tace "Nima xan je sch" kallon agogo yayi da sauri ita ma ta kalla, kamar xata yi kuka tace "Why did you not wake me" ya langwabar da kai yace "Coz you are sick" tace "Ni na samu lafiya.... I can still go" yace "Toh uniform din ki fa?" Xaro ido tayi tunawa da tayi ae fa ta jefar a titi, a hankali tace "Na yadda jakar a hanya doctor" shiru yyi yana kallonta snn yace "Ohk, let me get it for you" daga haka ya juya ya fita, ta koma a hankali ta xauna kamar warce ta tuno abu kuma ta mike ta shiga bathroom ta fara hada ruwan wanka, bayan kusan minti sha biyar ta fito daure da towel dinsa, xaro ido tayi ganinsa ta juya da sauri xata koma bayin ya dakatar da ita ta hanyar cewa "do I look like a monster!" kasa shiga bayin tayi ta kuma kasa juyowa, ya tsura mata ido daga sama har kasa, haka kawae yaji ya kasa tsayuwa, can ta juyo a hankali jin bai kuma cewa komai ba tana kallonsa, dauke kai yayi gabansa ya shiga faduwa, ta karaso a sanyaye tace "Am...am sorry!" Yayi karfin halin kallonta yace "Better, uniform din ki sun jike, kawai ki bari gobe ki tafi schl din" shiru tayi bata ce komai ba, ya dauke idonsa yace "Let me get you something to put on, but before then...." Gaban madubi ya nufa ya nuna mata lotions hadda na gashi yace "You manage this" sunkuyar da kanta tayi ya juya ya fita. Main House ya tafi ya ga Mami ce kadai a parlor tana kallon wani program, kanninsa duk sun tafi boko, ta kalli agogo tace "Baka tafi aikin ba har yanxu Haiydar" yace "Ehh yanxu xan tafi, wasu takaddu da na ba ilham xan karba" daga haka ya wuce sama ta bi sa da kallo, yana shiga ya kulle dakin ya bude closet dinsu, ganin tafi son saka dogayen riguna ya fiddo mata da wani bakin abaya da ya gani gogagge da veil dinsa, har da sabbin inner dinsu ya dauko mata, tunanin yanda xae fita da kayan ya fara yi, can ya leka window sai kuma ya dawo ya dau towel dinsu dake baje a kan gado yayi wrapping din kayan ya koma gun windown ya jefar ya  rufe wajen, snn ya dawo ya bude bedside drawer ya fiddo full scap sheet dinsu har uku ya linke yana rike da shi a hannu ya fita, ya sallami Mami da ta bi sa da kallo ya fita, yana xagawa ya dau kayan ya nufi part dinsa, xaune ya sameta gaban madubi har lkcn tana shafa mai, kallo daya yayi mata ya dauke kai ya ajiye mata kayan kan gado ya juya ya fita, cikin few minutes ta ga gama shiryawa ta fito ta samesa xaune a parlor, sosai kayan suka mata kyau kamar balarabiya haka ya dinga kallonta har ta karaso kanta a kasa tace "Thank you Dr!" Yace "Welcome, ga breakfast" girgixa masa kai tayi tace "A'a, gida xan tafi" d'aga kafada yyi yace "As you wish, uniform din suna balcony" tace "Toh" snn ta nufi kofa ya bi ta da ido, sae da ta bude kofar snn ta juya ta kallesa suka hada ido, dauke kai tayi da sauri ta fita, ya lumshe ido na kusan minti bakwai sai kuma ya mike ya dau makullin motarsa ya fita. Ko da ta isa gida bata damu da ta kunna wayarta ba sanin ba lallai ya kawo ba, duk da tasan kila su Mumy na ta kiranta, gabanta ya fadi tunawa da tayi Mumy xata iya kiran gidan su Stella su ce bata je ba, mikewa tayi da sauri ta fita xuwa gun mai gadi tace "Plss ka aran min wayar ka idan kana da flashing power xan kira su Mumy ne" mika mata yayi ta karba, tana flashing ba a jima ba kiran Mumy ya shigo ta daga tace "Mumy!" Daga daya bangaren Mumy tace "Samantha me ya samu phone din ki" kamar xata yi kuka tace "Ya fada ruwa" Mumy tace "How manage, me ya sa baki tafi schl ba" tace "Mumy am coughing, am not feeling fine" Mumy tace "Baki je gidansu Stella din ba kenan?" Tace "Ehh mumy am at home" Mumy tace "You are covered with the blood of Jesus my daughter, don't worry gobe ina hanya, ki dau kudi ki siyo maganin tari" a hankali tace "ohk Mumy" daga haka suka yi sallama, Samantha tayi kwanciyarta, sai can kusan sha daya ta tashi ta fara gyara ko ina na gidan kafin sha biyu ta gama, ta wanke uniform dinta ta shanya snn ta shiga kitchen nan ma ta gyara ko ina, tunanin abinda xata girka ta shiga yi, can tayi deciding tayi jollof rice da sauce din cow meat sai fried plantain anjima, kafin ta fita ta hada tea ta soya kwai ta fito ta ci ta kwanta sai bacci, ba ita ta tashi ba sai hudu, ta kunna TV tayi kallon kusan awa daya, mikewa tayi jin tana jin  yunwa ta shiga kitchen don yin girkin, da yake akwai komai a gida kafin karfe shidda da rabi ta gama tayi slicing lettuces, tomatoes, cucumbers, onions, and carrot ta ajiye su gefe, ta debi abincin da xata ci ta fita xuwa parlor, ajiyewa tayi ya huce ta tafi wanka, tana daure da towel ta dawo ta dau abincin ta, tana fara ci Abuturrab ya fado mata haka kawai taji tana son kai masa duk da ba da yawa tayi ba, kallon agogo tayi taga bakwai ya gota, tasan ya dawo aiki yanxu, bata wani ci abincin da yawa ba ta mike ta koma kitchen ta xuba masa shinkafar a warmer, ta debi sauce din a wani cooler, ta dau wani transparent breakable bowl ta xuba masa vegetables din ta rufe, ta sa su gaba daya a basket snn ta dawo parlor ta ajiye, sama ta tafi xuwa saka kaya, ta shirya cikin doguwar riga me tsantsi, ta daura veil a kai ta fita.

*Haske writers asso* ?✍?

? *Noorul Huda*?

11....
Tsarguwa tayi da irin kallon da mai gadinsu ke mata, ta hade rai tana rike da basket din abincin tayi ficewarta, cikin minti sha biyar ta isa gate din gidan, sai kuma ta tsaya tana tunanin kila ma bai dawo ba, karasawa gate din tayi ta tura a hankali taji a bude, ta leka compound din ta ga motarsa a space din mota biyu dake wajen, shiga tayi kamar mara gaskiya ta rufe gate din snn ta wuce parlor, a bude ta tadda kofar ta shiga da takalmanta tana kalle kalle, ta ajiye basket din hannunta ta xauna jin kamshin sabulu da ya gauraye ko Ina yasa tayi tunanin kila wanka yake, ta kusa minti bakwai xaune ta ji kamar foot step, mikewa tayi tana kallon kofa, sae kuma ta juya da sauri ta nufi bedroom dinsa ta bude kofar ta shiga ta rufe, kasa barin bakin kofar tayi kuma ta kasa juyowa, taji an bude kofar bathroom duk da haka bata juyo ba, ji tayi an juyo da ita ta daga kai tana kallonsa, daure yake da towel a waist dinsa, ta sunkuyar da kai, yayi murmushi yace "No church yau?" Kasa magana tayi, can cikin in ina tace "Dama...dama yanxu xan tafi, I brought you food... Yana parlor" kallonta kawai yake ko kiftawa bai yi, duk ta rikice ta juya da sauri, ya kuma juyo da ita taki dago kanta, murya can kasa yace "You brought me food..." Tana gyada kai kamar munafuka tace "Yess, yes I taught you will like it..." Dago kanta yayi a hankali yace "Thank soo much..." kasa kallonsa tayi, shi ko sai kallon bakinta yake, ta juya a hankali tace "Sae da safe" bata jira cewarsa ba xata bude kofa sai jinta tayi a jikinsa, ta xaro ido tace "Doc...." Bata kai karshe ba ta ji bakinsa cikin nata, a tsorace take kallon kwayar idonsa, ya lumshe ido ya jinginar da ita jikin kofa ya shiga kissing dinta a hankali, rikicewa tayi ko ina na jikinta ya dau rawa ta kuma kasa kwace bakinta, a hankali ta fara silalewa kasa ya rungumeta a bare chest dinsa har lkcn yaki cire bakinsa a nata, sun kusa minti shidda a haka aka bude kofa can parlor, wani karfi ya xo mata ta turasa xata bude kofar dakin ya jawota jikinsa ya kankameta, saukan hawayenta ya ji kirjinsa, ya sa ma kofar key jin muryar Mujaheed, xamewa tayi kasa ta hade kai da gwiwa, bubbuga kofar dakin Mujaheed yayi yana cewa "Are you there Aliyu?" Abuturrab bai tanka sa ba ya bude press ya fiddo jallabiyarsa ya sa ya cire towel din jikinsa ya kai bayi ya fito yana kallonta don har lkcn bata dago kanta ba, bude kofar yyi ya fita ya rufe, Mujaheed da har ya koma parlor yace "Meye na rufe kofa a bedroom kamar mara gaskiya?" Abuturrab na shafa kansa yace "Su Ramla ke damuna" Mujaheed yace "Ohk, Mum ce ta aiko Amira gun Mami.... Shine nayi dropping dinta, and we are leaving yanxu" Abuturrab yace "Ohk xan shigo anjima idan na fito" Mujaheed yace "kamar gaske" daga haka ya nufi gun abincin dake ajiye parlor ya bude yace "Whose food is this" Abuturrab yace "Mine" spoon Mujaheed ya dauka ya debi abincin ya kai baki yana cewa "But tuwo Mami ta xuba mana wai sai mun ci Ashe akwai wnn..." Abuturrab bai tanka sa ba, mujaheed ya xaro ido yace "Kai amma Mami da kanta tayi girkin nan koh..." kara kai wa baki yayi yana lumshe ido yace "Ae sai na koma an xuba min nawa, wnn dadi haka" daga haka ya nufi kofa Abuturrab ya dakatar da shi da sauri yace "look siya nayi ba a gida aka yi ba, kasan ni bna cin tuwo" Mujaheed ya dawo yace "Toh bari in dauko plate..." Kitchen ya tafi ya dauko plate ya dawo ya debi abincin da sauce da vegetables ya xauna ya fara ci yana ta santi, Abuturrab ya xauna ya kunna tv amma duk hankalinsa baya kai, da ya tuna incident din moment din sai gabansa ya fadi, Allah Allah yake Mujaheed ya wuce, ae ko sai bayan kusan minti sha biyar Mujaheed ya bar gidan, Abuturrab ya rakasa ya dawo, kasa shiga bedroom yayi duk jikinsa yayi sanyi, can yayi karfin halin bude kofar a hankali, ganinta yayi durkushe yanda ya fita ya bar ta har lkcn bata dago kanta ba, ya karasa kusa da ita a sanyaye ya durkusa amma ya kasa dagota, lumshe ido yayi ya dafata yace "Am..am sorry I didn't mean...." Mikewa tayi da sauri idonta ya kumbura don kuka ta juya xata fita ya tashi ya rikota kan yace komai ta fashe da kuka sosai har da shessheka, rikicewa yayi yace "Plss kiyi hakuri it's not intentional, I..." Fixge hannunta tayi ta fice da sauri, ya bi bayanta, tana ganin haka ta saka gudu ya bi ta har suka fita gate, hanyar gida ta dauka tana gudu iya karfinta shi ma kuma bai fasa bin ta ba, tana isa dai dai Inda ta saba jin haushin kare ta tsaya cak tana maida numfashi ganin karnuka har biyu, suna ganinta suka fara nufota suna haushi, juyawa tayi a rikice ta fara gudu ta nufi gunsa don tuni ya tsaya ganin karnukan tana isa gabansa ya rungumeta tayi tsit sai dai duk jikinta rawa yake, a hankali ta xame jikinta da kyar tace "Ka raka ni plss" hannunta ya kama ya nufi gate ta ce "No plss gida xan wuce" yace "Not when you are still angry at me" da sauri tace "No am not angry, ni ban yi fushi ba..." Xai yi magana fitilar mota ta dallarosu daga nisa, da sauri ta boye fuskarta a jikinsa don mutane daddaya ne basu san Mumynta anguwar ba, suna a haka har motar ya wuce ta dago da sauri tace "Doctor ka rakani plss" a hankali yace "Ke daya xa ki kwana?" bata bari sun hada ido ba tace "A'a Antyna tana nan" kama hannunta yyi ya fara tafiya xuwa gidan nasu, har suka isa bbu Wanda yace komai, shi dai duk jikinsa a sanyaye yake, bata ko kallesa ba xata shiga gate yace "Frnd..." Shigewa tayi abun ta ba tare da ta juyo ba ta rufe gate din, juyawa yayi ya bar gun ya koma gida.
Yana isa gida ya xauna parlor yana kallon abincin da ta kawo masa, can ya mike ya bude abincin ya kusa minti biyar rike da cover din warmer din yana kallon abincin, can ya dau spoon din da Mujaheed ya ci ya debi abincin ya kai baki, a hankali ya dinga taunawa, sai a snn ya gane ma'anar santin da Mujaheed ya dinga yi, wato the food was just perfect, so sweet, sosai yayi mamakin iya girkinta, plate ya dauka ya xuba abincin da vegetables sae sauce din naman, mancewa yayi da abinda ya faru bai ajiye plate din ba sai da ya cinye abincin, murmushi yayi underneath his breathe yace "Waow, she's a nyc cook" bude kofarsa aka yi ya daga kai da sauri Ilham ta shigo ta karaso kusa da shi tace "Ya Turab towel din mu muke ta nema bamu gani ba....". Kallonta ya tsaya yi kamar bai gane me take cewa ba, tace " Ya Abuu" ya ajiye plate din hannunsa yace "Toh ni ta ina xan san inda towel din ku yake...." Tace "Wa ya kawo ma abinci?" Yace "I bought it" mikewa yayi ya shiga daki ya bar ta wajen a tsaye, tabe baki tayi ta juya ta fita. Kasa sukuni Abuturrab yayi, duk ya tuna abinda ya faru sai ya ji haushin kansa, mikewa yayi daga kwancen da yake misalin tara saura ya fita, ya d'an yi xuke xukensa ya dau motarsa ya fita,  gidansu Saudat ya nufa, har ya mance rabonsa da ita, yana parking kofar gidansu ya sa mai gadi yayi masa sallama da ita, bayan kusan minti goma ta fito, ya dinga kallonta har ta karaso babu yabo bbu fallasa ta rungume hannayenta tana kallonsa, yayi murmushi yace "Kin mance ni kwana biyu" wani kallo tayi masa tace "Dole kace haka, tunda kun bata da sabuwar budurwar ka shine ka yo guna yau" yace "Haka kika ce" tace "Eh mana..." Ya tabe baki yace "Toh shknn, will you escort me" wani kallo ta kuma jefa masa tace "Ga mara mafadi ko, dama abinda ya kawo ka knn na sani, in rakaka dabar ku, to baxan je ba" yace "Seems kin fara gajiya da ni Saudat, naga alama you want breakup...." Tace "Toh meye maraban dambe da fada, da wannan sharenin da kake for months ae gwara ma breakup din....". Yace "Alryt..... Good you told me that" daga haka ya shige motarsa ya kara gaba, sosai ya ji ransa ya baci ya koma gida yayi kwanciyarsa. Washegari Tuesday throughout bai ga Samantha ba, duk da xaman da ya dinga yi waje bayan ya dawo aiki, laraba ma ta xo ta wuce bai ganta ba, wasa wasa har Friday, ya rasa dalilin da yasa ya damu haka, ko abinci sai ya tilasta kansa yake ci, he just can't say how much he missed her, misalin hudu na yamma ya kasa daurewa ya dau hanyar gidansu, can gaba da gate dinsu ya tsaya jikin flowern gidansu kamar me jiran wani, bude gate din aka yi Mum dinta ta fito suka yi ido hudu, har ta dauke kai ta kuma juyowa ta kallesa, shi ko ya fara danne dannen waya, Komawa ciki matar tayi ta fito tare da mai gadi tace "Habu wannan fa?" Mai gadin ya kallesa ya karasa Inda yake yace "Malam kana neman wani ne" Abuturrab ya kallesa yace "Ehh abokina nake jira a can gidan" ya fadi hakan yana nuna wani gida, matar tace "Toh ae ba wajen jira bane nn, jikin gidan mutane kake, ka kara gaba kadan malam" Kallonta kawae Abuturrab yake, ta hade rai tace "Ko flawan uban ka ne kke kallo na haka" bude gate aka yi duk suka juya, Samantha ta fito rike da jakar uwar tata, tana sanye da Doguwar riga amma na atamfa ta yafa yellow veil kallan atamfar a kanta, Ido hudu suka yi da shi ta kasa motsi Inda take, Cike da masifa uwar tace "Kai ni fa na fi ka hauka bani da kyau, before the count of 5 get out from this premises, it's my husband's not ur father's" Abuturrab yace "Kiyi hakuri Mama ya ma ce min ba nan bane can gaba ne" daga haka ya kalli Samantha cikin ido snn ya juya ya bar wajen, ta bi sa da kallo uwar ta fixgo hannunta tana cewa "Mahaukaci kai" 
Ilham ta warce hannunta daga rikon da Khaleesat tayi mata tace "Meye ne baxa ki iya gaya min parlor ba sai kin jawo ni nan" Khaleesat tace "It's about ya Abuu, and bana son Sis Ramla ta ji, I know she might tell Mami...." Ilham tace "What about him?" Khaleesat tace "That boys qtr he is staying is doing him more harm then good, kin san me na gani ranan?" Ilham tace "Meye kika ga" khaleesat ta bata fuska tace "I saw a lady in his bedroom...." Ilham tayi shiru sai kuma a hankali tace "I don't know what yaya Abu is turning to now" kamar xata yi kuka ta kare maganan, Khaleesat tace "Ke ma kin taba ganin ta koh?" Ilham ta gyada kai tace "Ehh, but warce kika gani ya take?" Khaleesat tace "Tall, fair, slim, sai kyan dan maciji" Ilham tace "Yess ita ce...." khaleesat ta dafe kanta tace "Toh ya xa muyi yanxu?" Ilham na gyada ksi tace "nasan maganin yar iskan, kuma fa arniya ce ba ma musulma ba" khaleesat ta xaro ido tace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Me yasa ya Abu ke haka...." Kwafa ilham tayi tace "I know what to do" daga haka ta fita Khaleesat ta bi ta tana cewa "Toh me xa mu yi"  washegari Saturday bayan azahar Abuturrab ya tafi gun aiki, su kuma su Ilham da khaleesat na ta kai komo part dinsa tun safe don ko islamiyya basu je ba duk suna jiran ganin xuwan Samantha amma har dare shiru, Ranan lahadi yana cikin bedroom su kuma suna xaune daga balcony dinsa, Khaleesat na neat din table cloth duk don kada ya xargi komai idan ya fito ya gansu, shi kam ko sanin suna gun bai yi ba, Ilham ce ta fara jin motsin gate ta mike da sauri haka ma khaleesat, a hankali ta turo gate din ta shigo sae dai bata bar kusa da gate din ba, suka labe jikin pillar suna kallonta, Abaya ce jikinta ta daura bakin dankwalin a kanta, hannunta rike da bible, jira suka dinga yi ta karaso amma bata karaso ba, sae jujjuya bible din hannunta take kamar Mara gaskiya tana kalle kalle, gani suka yi ta juya a hankali xata fita, ilham tace "Keeeee" cak ta tsaya sai kuma ta juyo da sauri tana kallonsu, duk suka fito suna mata wani matsiyacin kallo, ilham tace "In tambaye ki mana, nan kin ga yayi Kama da club?" Shiru Samantha tayi tana kallonta, khaleesat ta mata tsawa tace "Ke kurma ce xaki dinga kallonmu haka, idan baki fadi me ke kawo ki gidan nan ba sai mun yi maki shegen duka" Sauke idonta tayi bata ce masu komai ba, Ilham ta fincikota tace "Are you daft, ki fadi me ke kawo ki gidan nan kar mu maki shegen duka" hawaye ne ya cika idonta cikin rawar murya tace "Assignment yake taya ni....." Khaleesat kmr xata yi kuka ta dungureta tace "Assignment din uwarki, kina dai xuwa koya ma yayanmu iskanci koh? Ance maki prostitute ne shi kamar ki...." Xaro ido Samantha tayi tace "Ni ba prostitute bace...." Ilham tace "Karya kike, you are a prostitute...." Ta fashe da kuka tace "Am not a prostitute believe me...." Shakota khaleesat tayi a fusace tace "Wllh wllh daga yau kika sake xuwa kusa da gate din gidan nan sae mun cire maki hakora, kina xuwa kina lalata mana yaya, arniya kawai" sosai Samantha take kuka cikin raunin murya tace "Ni ba arniya bace, I have my religion, I am a Christian...." Ilham tace "Toh suwaye Christians din idan ba arnaye ba, ke katuwar arniya ce......" Bude kofa aka yi duk suka juya da sauri, kallon mamaki yake masu gaba daya, Khaleesat ta saketa da sauri, ya karaso a tsawace yace "Meye haka?" Khaleesat da ilham suka xumburo baki, ita kuwa Samantha banda kuka babu abinda take, duk ya rikice ya kuma yi masu wani mugun tsawa yace "Meye haka nace?" Ilham ta murguda baki tace "Warning muke yanka mata ta bar xuwa....." Hannu ya kai xai dalla mata mari ta bar gun a guje khaleesat ta bi bayanta, da sauri ya bi Samantha da har ta bude gate, ya rikota ta fashe da kuka tana son kwace kanta, ya ki saketa yace "No plss kiyi hakuri frnd, listen to me...." Cikin kuka tace "They called me a prostitute....." Lkci daya idonsa ya kada ya ma rasa abinda xae ce mata kawae ya jawota jikinsa yace "You are not dear....." Ganin yanda take kuka ya ja ta xuwa parlor, ya fi minti ashirin yana aikin lallashinta, ya lura tana da rauni sosai, ta maimaita an kirata prostitute ya fi sau biyar, da kyar ya samu tayi shiru yana rungume da ita, a hankali tace "And ni ba arniya bace, I have my religion, I am a Christian" shiru yayi bai ce komai ba, sun fi wani minti goma a haka snn ta xame jikinta a hankali ta mike ta kallesa tana goge fuskarta, mikewa yayi shi ma ya kamo hannunta yace "Plss am sorry on behalf of those stupid gals, I promise to teach dem a lesson" girgixa kai tayi tace "Ni basu min komai ba" daga haka tayi ficewarta a parlorn. Lumshe ido yayi ya bude shi ma ya fita, main house ya nufa fuskarsa daure, Ramlah kadai ce xaune parlor tana assignment fuskarsa daure yace "Ina su Rabi'ah?" Sama ta kalla tace "Suna sama" sama ya nufa ya bude dakinsu bbu su, ya bude na Mami ya gansu xaxxaune gefen ta.

By
_Khaleesat Haiydar_ hope this is enough?
*Haske writers asso*?✍?

? *Noorul Huda*?

12___13
Hade rai yayi ya xauna Mami dake kallonsa tace "Ya aka yi Aliyu?" Kin cewa komai yayi Ilham da khaleesat suka yi lamo jikinta, lkci daya duk ya jefa masu wani arnen kallo ya mike kamar wanda aka tsikara ya fice daga dakin kamar xae tashi sama, Mami ta kallesu tace "Kun nemi tsokanarsa koh?" Ilham ta turo baki tace "Ba abinda muka yi masa" har magrib su ilham basu yarda sun bar dakin Mami ba, nan ta tabbatar ba karamin laifi suka yi ma yayan nasu ba, bbu yanda bata yi da su ba su fadi me suka yi masa suka ki magana, har part dinsa Mami taje bayan Isha ta shiga har bedroom dinsa ganin baya parlor ta gansa xaune gefen gado hannunsa rike da waya, karasawa tayi tana kallon kofar bathroom jin k'aran washing machine, ya ajiye wayar hannunsa yace "Mamina...." Mami tace  "dama akwai washing machine a nan?" Yace "Ehh akwai...." Tace "Wanki kake?" Yace "No, just singlets..." Xaunawa tayi tace "Laifin me su ilham suka maka ne wai?" Ya shafa kansa yace "Ya wuce Mami...." Mami ta tabe baki tace "Toh ku kuka sani, naga tun daxu baka shigo ba" yace "Ehh Mami dama yanxu xan shigo" tace "Ohk, toh xan samu a d'an siyo min fruit?" Ya kalleta yace "Toh Mami" mikewa tayi tace "kar ka siyo lemo just app
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 12,485 09-10-2018, 08:20 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 4,996 08-18-2018, 01:15 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 14,152 08-10-2018, 01:18 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 10,655 08-10-2018, 12:48 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat haiydar Gimbiya 0 26,830 08-03-2018, 05:26 AM
Last Post: Gimbiya
  *CAPTAIN_AHMAD JUNAID* By Khaleesat Haiydar_ ✍? Gimbiya 0 20,498 11-16-2017, 12:51 PM
Last Post: GimbiyaUsers browsing this thread: 1 Guest(s)