Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Noorul Huda* by Khaleesat haiydar
#1
[7/29, 22:26] SHS: All thanks to Allah S.W.T for giving me the chance, priviledge and ability to write this Novel, i Dedicate this to my sweet siblings  and our mum,  Allah ya bar mun ku ameen.
 
? *Noorul Huda* ?

1......

A hankali ta karashe rufe windows din dakin ta juya tana kallon makeken agogon dake manne bango dakin, karasawa gefen gado tayi ta xauna murya can kasa tace "Rain? Not today pls..." Bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri Mahaifiyarta dake tsaye bakin kofar tace "Ki tabbatar kin sa sweatern ki, kiyi addu'a ki kwanta haka kuma sai da safe!" Bata ce komai ba uwar ta juya ta fita, sake kallon agogo tayi taga bakwae da kusan rabi, Wayarta dake ajiye kan gado ya shiga ring ta mike ta dauka ganin me kiran ta daga ta kai kunne tace "Hello!" Daga daya bangaren aka ce "Kar ki ce min baxa ki xo ba sbda ruwa?" Ajiyar xuciya ta sauke tace "Kema kin san mumy...." Katse ta tayi tace "A'a gaskiya baki min adalci ba, it's already dark just sneak out ki fito yanxu bbu wanda xai sani ae kince Abba baya gari fahhh" D'an langwabar da kai tayi tace "Alryt bari inyi kokarin yin hakan, gani tahowa" daga haka ta ajiye wayar, cikin kankanin lokaci ta gama shirinta ta dau jakarta ta saka waya da kudi snn ta dau rain coat ta saka, ta kashe fitilar dakin, cikin sanda ta fito daga dakinta, ta dinga bin corridor da kallo dim haske ta hango daga bedroom din Mum dinta ta sauke ajiyar xuciya a hankali don tasan me take yi, tana gamawa kuma xata kwanta sai kuma gobe, da sauri ta sauka downstairs taga duk an kashe fitilun parlon ta nufi kitchen tana lalube lalube ta bi ta kofar kitchen din ta fita ta tura a hankali ba tare da ta rufe ba, ko da ta isa gate mai gadi bai ce mata komai ba ta bude gate ta fita, da sauri take tafiya don anguwar tsit bbu kowa sai haske, a haka ta isa babban titi ta samu d'an sahu ta fadi masa inda xata ta shiga, haka kawai gabanta ke faduwa don tunda take bata taba abinda ta yi ba yanxu, gashi dai yau kawa ta sa ta, kawar ma warce basu jima da sanin juna ba, basu kuma wani saba ba, takwas saura ta isa wani babban gidan duk da ruwan da ake tsulawa hakan baxai hanaka jin sautin kidan dake tashi a gidan ba, ta shiga gate jiki a sanyaye ta karasa kofar da xai kai ta babban parlon da ake birthday din, mata ne da maxa a cakude ana ta rawa abun ba tsari, k'awartata wato celebrant din ta hango ta ta karaso da sauri cikin flowing gown dinta ta rungumeta tace "Ohh babe am happy you came to ki cire rain coat din mana, you are already missing" sauke hulan tayi tace "But i never knew the birthday will be like dis, it's just disorganized...." Katse ta tayi tace "Nothing is disorganized a nn idan xaki karaso ayi bidiri da ke ki karaso" tabe baki tayi ta cire rigar ruwan jikinta, doguwar gown na kanti ne jikinta me kyau ta saki dogon gashin kanta kawarta ta kashe mata ido tace "Waow besty kinyi kyau ina ma Boo dinki ya gan ki yanxu" murmushi tayi tace "Uhm" hannunta ta ja suka karasa inda ake ta shagalin birthday din, waje ta samu ta xauna ta dau maltina ta bude tana sha tana kallon yanda mata da maza ke ta watsewar su ga hayaki ko ta ina, duk bata saki jiki ba a gun abun ka da wanda bai saba ba, a xuciyarta kuwa tunani ta dinga yi anya xata iya ci gaba da tarayya da Clara kuwa, she's rough, bata yi minti goma da xama ba wani guy ya dawo inda take ya xauna yace "Hi babe how you doing?" Ta d'an kallesa tace "Good" yace "Pls may I know you futher?" Girgixa kai tayi tace "Noo" yafito ta da Clara ke yi yasa ta mike ta nufeta, ya bi ta da kallo, can ya kalli drink din da take sha, cikin seconds din da basu wuce 7 ba ya fiddo wasu kwayoyi ya jefa a gwangwanin malt din snn ya fiddo wayarsa da sauri yana dannawa, ba a dau lkci ba ta dawo  ta xauna ta ajiye sticks din meat dake hannunta da cake ta dau gwangwanin malt din ta ci gaba da sha, ya cije lebe yana d'an murmushi bai ce mata ba ita ma bata ce masa ba, bayan kusan minti goma taji ta fara jin bacci sosai, mikewa tayi da kyar tace "Excuse me" ya mike shi ma yace "Ohh no probs, gida xa ki ne?" Ta d'an kallesa sai kuma tace "Ehh" yace "Toh mu je kiyi ma kawar ki sallama sai inyi dropping din ki that's my duty here" bata ce masa komai ba suka karasa gun Clara, da mamaki tace "Haba babe da wuri haka" a takaice tace "Ehh am feeling sleepy" kallon guy din tayi sai kuma tayi murmushi tace "Toh shknn take her home directly plss Sam" Yace "Alryt" da sauri ta nufi kofa jin kamar kanta na juya mata, suna fita ya kama hannunta suka nufi gun motarsa, xuwa lkcn ruwan ya d'an tsagaita sai yayyafi, ya bude gaba ya sa ta snn ya shiga ya ja motar suka fita, basu yi nisa ba yyi parking yace "Baby ina ne gidan naku" ta kallesa da sexy eyez dinta tace "Tarauni...." Ya kamo hannunta yace "Ohh that's very farrr" bata ce komai ba ya fara shafa hannun a hankali yana jan long fingers dinta, ta lumshe ido tace "Take me home...." Jawota yyi jikinsa yana shafa fuskarta lkci daya ya shiga tura hannunsa rigar ta ya kwantar da kujeran motar cikin tsawa  tace "Stop itt...." Sosai idonsa ya kada cikin lallami yace "baby...." Wani mari ta sauke masa ta bude motar ta fice ya xaro ido hannunsa dafe a kuncinsa, fitowa yyi da sauri shi ma tana ganin haka tafara gudu duk da juya mata da kanta yake, iya karfinta take gudun yana biye da ita, suka yi nisa sosai, taji ta kasa ci gaba da gudun, a gaban wani gida ta hango wani mutum tsaye yyi backing flowers waya na kare a kunnensa, tana haki ta karasa kusa da shi jikinta na rawa tace "Help plsss...." Tsit tayi ganin taban dake dayan hannunsa ta juya da sauri xata bar wajen ya yarda taban ya fincikota, ihu ta fasa dai dai lkcn da Sam ya karaso gun, kallo daya biyu yyi ma mutumin sai kuma ya juya ya koma inda ya baro motarsa, sai ta gwammace da ma a hannun sam din take akan wnn mutum kkrin kwace hannunta take ko ina na jikinta na rawa amma ta kasa,  wani kallo yake mata daga sama har kasa da manyan idonsa, ta fashe da kuka a tsorace tace "Don Allah kayi hakuri ka kyaleni" fixgota yyi dai dai fuskarsa yace "Me ya fito da ke da?" Turarensa mai dadin kamshi da ya hade da warin taba duk ya isheta, ganin jiran amsa yake bakinta na rawa tace "Birthday din k'awata na fito" daga sama har kasa yake kallonta yace "Shine aka biyo ki xa ayi maki fyade knn?" Hawaye ne ya shiga bin kuncinta ta kasa cewa komai yace "Da na san daga inda kika fito knn da na bari yayi fata fata da rayuwar ki...." Daga haka ya tura ta ta bar gun da sauri tana gudu, bin ta yyi da kallo har ta kusan shan kwana sai ya ga ta tsaya, wasu samari biyu ya hango tsaye gabanta duk da ba wani haske gun, ta juya xata canxa direction wani ya sha gabanta, jan ta yaga suna yi xuwa gun wani mota da alama tasu ce ya xaro ido kafin ya ankare har sun isa gun motar yana kuma iya jiyo ihunta daga inda yake duk da uban nisan wajen, wani mahaukacin gudu ya saka kamar xai tashi sama kafin yaje har sun tada motar sun ja, yace "Shit!" juyawa yayi ya koma gun motarsa da sauri ya shige ya kwasa a dari da sittin ya bi bayansu, da kyar ya kamosu a dai dai wani round about ya kusa cin karo da su ya bude motar ya fito daya daga samarin ma ya fito da shirin masa bala'in ya buge masa mota bai ko sauraresa ba ya bude backseat din motar yaga bakinta suka rufe da wani kyalle, fixgota yyi daga motar duk suka tsaya kmr sokaye suna kallonsa ya bude tasa motarsa ya jefata a baya ya koma driver seat ya shiga ya ja motar, tafiya yayi me nisa kafin yayi parking gefen titi ya juya yana kallonta kife kanta ya ga tayi a bayan motar, yace "Keeeh" ya ji shiru, wani tsawan ya sake mata nn ma bata dago ba, ya bude motar ya fito da sauri ya bude backseat din ya dago kanta yaga ta dawo, xaro ido yayi ya shiga motar da sauri ya rufe ya dago kanta, komawa baya yyi jin warin abinda ya bugesa, yayi saurin cire kyallen ya wurgar waje, gashin kanta ya mayar baya yana kallon fuskarta, idonta a lumshe ga lashes kamar an dasa su ne, hancinta dogo kamar an xana mata, a hankali ya sauke idonsa kan karamin bakinta me kala biyu pink nd black, dauke kansa yayi sai kuma ya kwantar da ita ya bude motar ya fita ya rufe ya jingina jikin motar yana tunanin yanda xai yi da ita, d'an bude ido yayi sai kuma ya bude motar da sauri ya shiga ya dagota ya kai hannunsa dai dai hancinta, tsaki yayi ya saketa ya dafe kansa, can ya kwanto a hankali ya kai bakinsa dai dai nata, ya sa hannu ya bude bakin nata ya daura nasa kai ya shiga hura mata iska, ya kusa minti bakwae yana haka tayi wani uban atishawa ya dagata ya koma baya da sauri ya ciro handki aljihunsa yana goge bakinsa da fuska, a hankali ta bude ido sai kuma ta mike xaune ta rike kanta, shi dai kallonta kawae yake, sauka yaga take son yi daga kan kujera ya rike ta yace "ke malama stay still...." Ta fashe da kuka tana jujjuya kanta tace "Where is this please take me home my head is aching" wani uban harara yayi mata kamar tana kallonsa yace "Wani ya fito da ke yawon birthday?" Da kyar ta bude idonta da yayi jajur tana kallonsa muryarta na rawa tace "Take me home pls kaina na ciwo...." Tsaki yaja ya jefar da handki din hannunsa ya fito ya koma front seat ya tada motar ya hau titi, a fusace yace "Ina ne gidan naku?" Cikin muryar kuka ta gaya masa, waka ya kure yana bi don ma ya daina jin sautin kukan nata, parking yyi kamar wanda aka umarta yyi hakan, sai kuma ya fara reverse har ya iso wani babban pharmacy da ya wuce, ya bude motar ya fito ya shiga ciki bude motar tayi xata fita ta kasa don ji tayi kmr duniyar aka aza mata a kai ga wani jiri da take gani, ta fashe da kuka ta koma ta xauna, ba a dau lkci ba ya dawo rike da ledan Magani ya bude inda take ya jefar mata snn ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, tana masa kwatance har suka iso gidansu, ya juya yana kallonta da d'an mamaki bayan ya gama kare ma makeken gidan kallo, ta bude motar da kyar xata fita ya daure fuska yace "Ga Magani nn for the sake of Allah and Islam!" Kallonsa tayi da rinannun idonta sai kuma ta dau ledan ta fita daga motar saura kiris ta fadi amma hakan bai sa yace komai ba, tana layi ta nufi gate, yayi tsaki yayi reverse ya kwasa da gudu ya bar wajen, a daddafe ta isa bedroom dinta ba tare da ta yrda tayi ko wani kara da xai ja attention din mum dinta ba, ta jefar da ledan drugs din hannunta ta fada kan gado ta shiga juye juye hawaye na sakko mata.

?✍?
[7/29, 22:26] SHS: ? *Noorul Huda*?

2......

Yana gama parking a space din da aka tanadar don yin hakan a gidan ya bude mota ya fito, kalle kalle ya dinga yi kafin ya xaga xuwa gun shan iskan dake gidan ya ciro kwalin cigarette a aljihunsa da lighter ya ciro stick daya ya kunna mata wuta ya hau zuka, stick biyu ya gama da cikin d'an kankanin lkci ya mayar da sauran aljihu snn ya mike ya koma gun motarsa ya bude ya fito da wani abu kamar turare ya feshe bakinsa da shi ya mayar ya kulle motar snn ya shiga gida cike da tafiyarsa ta kasaita, a hankali ya murda kofar parlor ya shiga ya rufe a nutse yanda baxa a ji ba yana kallon agogon dake manne parlon yaga har karfe daya, xaro ido yyi da mamaki, how time flies, yaushe ya ajiye yarinya snn yaje gidan frnds dinsa suka tafi club amma har lkci ya wuce haka bai sani ba, stairs ya nufa yana tafiya a hankali kada ma aji footstep dinsa, yana isa corridor din rooms aka bude wani kofa, wata dattijuwa da baxata wuce 50 da wani abu ba ta fito tana kallonsa, wara ido yayi yace "Mamiiii!" Ta karaso inda yake bbu yabo bbu fallasa tace "Daga ina kake Abuturrab?" Ya shiga sosa kai yace "Am Mami daga clinic nake ban gama aiki da wuri...." Ta girgixa kai tace "Karya kake!" Shiru yayi bai ce komai ba, Cike da damuwa Mami tace "Yanxu Aliyu baxa ka ma kanka fada ba, it's high time fa kasan inda ke maka ciwo, banda bin mutanen banxa bbu abinda ka iya a rayuwa, what's the use of this, me yasa baxa ka bar ni in huta bane a rayuwar nan, idan kanninka suka yi kuma kace me?" Shiru yayi ya sinnar da kai bai ce komai ba, ta karasa gabansa kamar me son gano abu, ya rike breathe dinsa da sauri, ta kamo hannunsa ta kai hancinta ta girgixa kai tace "Ae shknn, continue destroying ur life, ur being an only son does not mean u are an only child...." Ya marairaice yace "Plss Mami am sorry...." Tsawa tayi masa tace "Shut ur mouth!" Yayi shiru yana kallonta ta juya ta shige bedroom dinta ta rufe kofar, ajiyar xuciya ya sauke ya shiga dakinsa, bathroom ya fada yayi wanka ya saka sleeping robe dinsa ya kwanta, ji yyi cikinsa na kugi, sai a snn ya tuna ashe fa bai yi dinner ba, hamma yayi ya mike xaune, tunanin abinda xai ci ya shiga yi, can ya mike ya nufi kofa ya bude a hankali ya nufi dakin sisters dinsa, a hankali ya tura kofar ya shiga ya rufe, ya lalubi switch din room din ya kunna, suna kwance su uku gaba daya sun yi bacci, ya karasa gadon ya xauna yana kallonsu, Ramlah ya shiga tashi a cikinsu ta bude ido da kyar tana kallonsa ya marairaice yace "Lil sis I've not eaten...." Hade rai tayi tace "Ohh yaya bacci fa nake xaka tashe ni.... Ga Leesah ka tashe ta mana" daga haka ta juya masa baya, kallon Khaleesat yayi ya shiga tashinta, ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "What again ya Abuu?" Ya marairaice murya yace "Ban ci abinci ba fa" tsuke fuska tayi tace "Toh ni ba ni na raba abinci ba Mami ce, but you can ask Ilham" daga haka tayi kwanciyarta ita ma ta juya masa baya, ji yyi kamar ya kwada masu mari don dai dare ne kuma kada Mami ta juyo su, ya kalli Ilham ya shiga tada ta, ta juyo tana kallonsa yace "Pretty ban ci abinci ba fa" hade rai tayi ta mike xaune tace "Toh ba kai ne baka dawo da wuri ba, ni dai ya Turab ka daina tashi na idan ina bacci ba ga Anty Ramlah da Leesah ba...." Turo baki tayi ta sauko daga kan gadon tana gunguni ta fice daga dakin, duka ya d'ada masu su biyun suka mike a firgice ya hade rai yace "Duk xan yi maganin ku" daga haka ya mike ya fice daga dakin ya sauka downstairs, yana tsaye bakin kofar kitchen Ilham ta gama hada masa abincin nasa a tray ta fito ya bi bayanta suka koma sama, a dakinsa ta ajiye masa ya xauna gaban abinci ta nufi kofa xata fita sai kuma ta juyo tace "Baxa ma kace thank you ba ko" wani kallo ya jefa mata yace "Baxa ace ba" murguda baki tayi ta fice daga dakin.  Washegari da safe da ya kasance Lahadi Abuturrab da wasu frnds na xaune gaban gidan daya daga abokin nasu Ayman street na uku away from gidansu Abuturrab din, Abuturrab ya kalli direction din da Saleem ke kallo ya hango wasu mata su uku suna tahowa, gaba daya abokan suka maida hankali gun matan, Abuturrab ya d'an yi tsaki ya dauke kai, har suka iso dai dai inda suke, Ayman yace "Cute!" Sai a snn Abuturrab ya juya yana kallonsu, ido hudu suka yi da ita, ya kasa daina kallonta ita ma haka kuma lkci daya ya ganeta, da alamar ita ma ta ganesa ganin kallon da take masa, da sauri ta dauke kai ta ci gaba da tafiya, Ita kadai ce me doguwar riga har kasa cikinsu amma sauran duk halve gown ne jikinsu, Basu wani yi nisa ba ta kalli kawayen nata tace "Kunsan me, shine guy din da nake gaya maku daxu, he rescued me..." Ta gefenta tace "Really? And you walked passed him baki masa magana ba" kamo hannunta dayar tayi tace "Gaskiya bai kamata ba ki koma ki masa godiya you don't have to pretend shi ma nasan ya gane ki" without a second taught ta juya da sauri ta nufe inda suke xaune, da sauri Abuturrab ya dauke kai, Salman yace "She's coming toward us fah" Salim dake ta kallonta da Ayman suka yi shiru har ta karaso, doguwa ce sosai kuma fara amma ba wani can ba, tana tafe ne kamar iska xae kade ta, yeah she's so beautiful kyau me daukar hankali kuwa, daga nisa ma kana iya ganin girman idonta da haskensa, tana isa inda suke ta tsaya tana kallon Abuturrab da alamar ta ma rasa abinda xata ce, sai fidgeting fingers dinta take cikin in ina tace "I I.... Came to thank you!" Kallonta kawai yake, ya kasa dauke kai, a hankali idonsa ya sauka kan abinda ke rataye a wuyarta wanda hakan sai da yasa gabansa ya fadi ba kadan ba, Salim ya take kafarsa yayi saurin dauke kai, sai kuma ya kalleta yace "Ki gode ma Allah!" Juyawa tayi ta bar wajen da sauri, abokansa suka bi ta da kallo har ta isa gun kawayen ta suka ci gaba da tafiya, Salim yace "Where did you know her?" Bai ce komai ba ya xaro kwalin cigarette ya ciro daya da lighter ya kunna ya kai baki. Tana isa gida ta tadda Mum dinta na tare da baki a parlor ta gaida su da ladabi snn ta wuce sama xuwa dakinta ta jefa jakar hannunta ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta fiddo kananun kaya ta saka ta kwanta, lkci daya ya fado mata, sai a snn taji haushin kanta da taki barin wajen bayan ya shareta, tayi tsaki ta rufe fuskarta da pillow, har ta fara bacci taji muryar mum na kiranta, ta mike xaune da sauri tana mitsike idonta, Uwar tace "Samantha ki fito ga abinci can a dinning, baxa ki Catechism bane?" Tace "Mumy da rana fa yau" hade rai Mumy tayi tace "Kina da hankali kuwa, ranan ne xai hanaki xuwa? C'mon my frnd tashi ki shirya and get out of this house, mates dinki a karkashin wata suke tafiya ba ranan ba?" Daga haka ta fice daga dakin, Mikewa Samantha tayi ta sauka parlor a sanyaye, xaune ta ga dad dinta a d'an study area yana sanye da medicated glasses dinsa, Holy Bible ne gabansa yana karanta wa, karasawa tayi inda yake ta masa side hug bai ce komai ba gaba daya attention dinsa na kan Bible din, murya can kasa tace "ina yini Abbana" kai kawai ya gyada mata ta nufi dinning ta debi abincinta ta xauna nan ta ci, sannan ta koma sama ta shirya cikin wani gown din tayi rolling kanta ta fito rike da bible dinta da Hymn book, dakin Mumy ta shiga ta ganta tana ta shirin fita fellowship ita ma, ta karasa tace "Mumy sai na dawo!" Mumy tace "Alryt dear, kila baxan dawo yau ba sbda vigil da xa muyi, you take of yourself, ga transport din ki a gaban mirror na aiki driver" Samantha ta d'an bata fuska tace "Har da Abba?" Mumy tace "Nooo shi yana gida bbu inda xa shi, xae yi bak'i anjima" juyawa Samantha tayi tace "Ohk bye!" Daga haka ta fita bayan ta dau kudin, da kafa take tafiya har tayi nisa sosai tayi deciding ta bi layin gidansu class mate dinta Esther su tafi church din tare, tafiya take tana d'an wake wakenta, tayi nisa sosai don bai wuce gida hudu xata wuce snn ta sha kwanan gidansu Esther ba, gabanta ya fadi ganin wanda ta gani tsaye jikin motarsa a gaban wani gida ga wata yarinya na tsaye daga kusa da shi, kamar ance ya daga ido suka yi ido hudu, da kyar ta bude baki tace "Ina...ina yini!" Yace "Lafiya lau" daga haka ta wucesa, yarinyar ta bi ta da kallo snn ta kallesa tace "Waye ita Aliyu?" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "A frnd!" Ta tabe baki tace "A Christian frnd?" Bude motarsa yayi ya shige ta koma baya da mamaki tana kallonsa tace "Abuturrab?" Ta glass yake kallonta yace "Even if she's a pagan (Mara addini) it's non of ur business!" Tada motar yayi ya ja ya bar ta nan tsaye ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya da sauri taga har Samantha ta bace, a fusace ta shige gida. Abuturrab na isa gida misalin sha biyu na dare yayi parking ya fito ko ba a gaya masa ba yasan Abba ya dawo ganin Prado dinsa, bae ko kalli sojojin dake tsaye ta ko ina a compound din ba ya shiga parlor Ramlah ta leko daga kitchen murya can ciki tace "Ya Abu Abba yana neman ka..." Yayi mamakin ganinta a kitchen a wnn lkcn gashi bai ji mai take cewa ba ma, xai karasa inda take suka ji muryar Mami tace "Kina da hankali kuwa Ramlah" juyawa tayi da sauri ta koma kitchen, hade rai yayi ya gaisheta shi kenan kullum cikin laifi kuma sai yayi ta xaman gida kamar mace, infact mayar da duty dinsa na clinic xuwa dare ma xai yi kawae, Mami ta amsa gaisuwarsa ba tare da ta kallesa ba xai haura sama sai ga Abba ya fito daga parlonsa, tsaye yayi gabansa na faduwa ya d'an risina ya gaishesa Abba yace "Daga ina kake Aliyu?" Sunkuyar da kai yyi ya ma rasa abinda xai ce, can dae yace "Abba taimako na tsaya yi a....." Abba ya girgixa kai yace "No! You can't just be coming into my house when ever you wish at any time, don haka ka tattara inaka inaka ka koma boys quatr snn ka bude gate din can kaga idan yaso ko da yaushe ka ga dama xaka iya shiga ka fita bbu wanda ya sani, bbu wanda kuma xai hanaka, do what I say immediately now, stupid you!" kansa a kasa yace "Toh Abba, Allah ya huci xuciyar ka" Ramlah ta karaso parlon kamar xata yi kuka tace "Abba pls forgive him for the last..." Wani kallo ya mata ta juya da sauri ta koma kitchen, Abuturrab ya haura sama ba a dau lkci ba ya fito da jakunkunan kayansa da komai nasa da xai bukata, har lkcn Abba na tsaye parlor haka ma Mami da bata ji dadin hukuncin ba, Fita Abuturrab yyi ya kira mai gadi ya taya sa daukan kayan, tsakanin main gidan da boys quatr ba wani tafiya bane can, sai dai ba lallai ka ma san me ke faruwa can ba barin ma da Abba yace ya bude gate din can, cikin yan minutes ya gama mayar da kayansa can snn ya koma yayi ma parent din nasa sai da safe ya dawo, dariya ya dinga yi shi kadai a parlor yana tafa hannu ya fada kan kujera yace "Waow waoww enough privacy!" ya mike yana murmushi ya shiga inda dakuna suke ya xabi wanda yake so ya shigar da kayansa, ya dau lkci sosai yana gyaran dakin sbda kura don ba a fiye amfani da wajen ba sai dai a sauke baki, Abuturrab ba dai tsafta ba cikin few hours ya tsaftace dakin da bathroom ya kure Ac ko ina ya dawo yana kamshi ya shimfida bedsheet, snn yayi kwanciyarsa don ya ci abinci a waje, nan da nan bacci ya daukesa, washegari Monday yana shirin fita office aka danna bell daga waje ya karasa ya bude, Cook ne rike da tray din breakfast dinsa ya d'an bude ido yace "Ohh I thought girkin ma nan xa a dawo yi min" cook din dai bai ce komai ba ya gaishesa Abuturrab ya karbi tray din yace "Thanks" har ya tafi ya kirasa ya basa spare key din parlon yace "Gashi ko bana nn idan ka kawo min abinci ka shigo kawai ka ajiye" Cook din ya karba da ladabi yace "Ohk sir" daga haka ya juya ya wuce shi kuma ya koma ya ci gaba da shirinsa snn ya yi breakfast ya dau makullin motarsa ya fita, main house ya nufa ya gaida Mami ta amsa tana kallonsa tace "Hope you are now satisfied with the punishment?" Murmushi yayi yana shafa kai Mami tace "Ka canxa halin ka Abuu, you are grown up fa yanxu, soon xa ka ji Abba ya fara maka maganan aure idan kuma kaki fidda mata na tabbata fiddo maka ita ba wahala xai masa ba, you are 30 yanxu amma kaki nutsuwa ka san inda ke maka ciwo koh" murmushi yayi yace "Mami ni fa ba dauko maku magana nake ba, ba sata nake ba, ba kisa nake ba, kuma... Um Mami ni bana neman mata kin sani fa!" Bude baki tayi da mamaki tace "Ehh lallai Aliyu ashe baka da kunya..." Dariya yayi yace "Allah Mami, naga wa ennan sune rashin jin, kuma duk bana yi" harara ta 6alla masa tace "toh shaye shayen fa da bin abokan banxa" xaro ido yayi ya dawo kusa da ita yace "Ohh Mami wllh ni na bar wannan abun da dadewa bana shan komai yanxu" wani kallo tayi masa tace "Cigarette din fah?" Ya sosa kai yace "Uhm Mami shi ma ina kkrin in ga na daina wllh, just continue praying for me" ta shafa kansa tace "Toh Allah yasa haka son. Be a good man plss, sannan ka canxa abokan ka" mikewa yayi yana murmushi yace "Toh Mamina na tafi aiki...." Daga haka ya fita da sauri ya nufi parking lot, yana shiga motarsa ya bar gidan, dai dai traffic kamar ance ta juya ya ga Samantha a bayan mota sanye da uniform alamar sch xata, mamaki ya cikasa, why yake haduwa da ita frequently now, bayan ko taba ganinta bai yi ba kuma daga layinsu xuwa nasu gidan bbu wani nisa can amma bai taba lura da ita ba, ita ko ganin yanda yake kallonta ta daga masa hannu hade da yin murmushi, murmushin ya mayar mata ya gyada mata kai snn ya ja motarsa don an basu hannu ya dau hanyar gun aikinsa.

?✍?
[7/31, 09:51] SHS: ? *Noorul Huda*?

3......
Karfe biyar saura Samantha ta dawo sch, duk da driver ne yaje daukota amma a titin anguwar tasu ya ajiyeta wai xai je dauko Mumy daga church, yawanci a nan take yawan sauka sai dai ta karasa da kafa, tafe take jakarta a bayanta da ganinta kasan a gajiye take, wani mota that look familiar ne ya xo ya wuce a guje ta bi motar da kallo, bai yi wani nisa ba taga kuma ya tsaya, ita dai tafiyarta kawai take, a hankali ya dinga dawowa baya har ya iso inda take ya sauke glass, d'an bude ido tayi ganin wanda ke cikin motar, kafin yace komai tace "Good evening," yace "Evening, let me drop you" kai ta gyada masa ta karasa ta bude front seat ta shiga ta rufe sannan ya ja motar, bai ce mata ba ita ma haka sai dai ynxu kam ba gudu yake ba, ji tayi yace "Ur name?" Ta kallesa tace "Samantha!" Ya d'an kalleta snn yace "Samantha?" Tayi murmushi tace "Samantha David!" Ya gyada kai yace "Nyc!" Tace "Urs?" Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Aliyu Ahmad!" Murmushi tayi tace "Nyc name," kallon Stethoscope din dake sakale gaban motar tayi tace "You are a doctor?" A takaice yace "Yes" bata kuma cewa komai ba har ya iso gaban gate din gidansu ta kallesa tace "Thank you" yace "Welcm" har xata fita sai kuma ta tsaya ta kallesa tace "Every doctor can draw perfectly, will you pls help me draw the Diagram of the Mammalian heart and Human Skeleton?" Kallonta ya tsaya yi, can yyi Murmushi da ya bayyana light dimple dinsa yace "Really? To ni ban iya ba" kamar xata yi kuka tace "Allah nasan ka iya Plss ka min mana" shiru yayi yana kallon yanda karamin bakinta ke motsi sai kuma yace "Ohk," cike da murna tace "Ohk to bari in dauko materials din" dakatar da ita yayi yace "Am exhausted I can't wait, idan mun sake haduwa sai ki ban" daga haka ya daga mata hannu ya ja motar ta bi sa da kallo, cikin minti biyar ya isa nasu gidan ana bude masa gate yayi parking har xai nufi kofar main parlor ya tuna ai fa ya koma Boys quatr ynxu, dariya yayi ya nufi can, wanka kawai yayi ya dawo ya debi abincinsa dake ajiye snn ya ci ya kwanta don ya gaji sosai, shidda saura ya mike ya fita ya xaga boyz qtrs din gaba daya, ya bude gate din da Abba yace, ya fita waje da farin kujera ya xauna yana kare ma street din kallo don sai yyi shekara bai bi nn ba duk da bayan gidansu ne, baxa ka taba cewa akwai mutane unguwar ba tsabar shiru, tafe suke su biyu da alamar sun dawo daga church ne, tun daga nisa ya gano ta ta yanda take tafiya, haka ya dinga kallonsu har suka karaso, ta xaro ido ganinsa tace "Doctor!" Wara ido yayi bai ce komai ba ta karasa kusa da shi da sauri ta sauke jakar dake goye bayanta ta fito da materials din drawing din ta mika masa tace "Na kama ka" murmushi yayi ya karba yace "Nawa xa ki biya?" Ta langwabar da kai tace "Ko nawa, amma service before payment" dariya yayi wanda hakan ya fito da ainahin kyansa na d'an pillo, ya kuma bayyane fararen set din hakoransa masu daukar ido, shiru tayi tana kallonsa, yace "Ke me wayo ko?" Murmushi tayi tace "nan ma gidan frnds din ka ne?" Ya girgixa kai yace "Gidanmu ne" bin gidan tayi da kallo tace "Da gaske?" Yace "Yeah!" Tace "Hmm Ohk, to yaushe xan karbi xanen?" Yace "Ran da na gama" tace "Noo we are submitting it as test on Wednesday" yace "Ohk, xan yi anjima" tace "Yauwa na gode bye" daga haka ta nufi mai aikinsu blessing dake jiranta. A ranan da daddare Abuturrab ya xauna misalin karfe goma a gun da ya tanadar as study room, ya bude textbook din da ta basa domin Duba xanen a jiki ya kwafa, tabe baki yyi ya rufe, lumshe ido yyi na kusan minti biyar yana nazarin diagram din heart a xuciyarsa, can ya bude ido ya dau well sharpened pencil din ya shiga xana Big Mammalian heart gwanin ban sha'awa ko wani curve ya basa hakkinsa, sosai Heart din ya xanu yyi kyau kamar drawing din Artist, cikin few minutes yayi labelling ko ina snn ya ajiye pen din ya lumshe ido yana nazarin skeleton, bude idon yyi ya bude wani page ya shiga rangada babban xanen Human Skeleton, ko wani k'ashi sai da ya tabbatar ya xana, ya gama tsaf snn yayi labelling ya gama ya rufe book din yana hamma ya mike ya shige bedroom ya fada kan gado sai bacci. Washegari da xae fita aiki bae bari ya mance materials dinta ba in case ko xa su hadu, ya ajiye back seat snn ya bar gidan bayan ya shiga ya gaida Mumy, amma bai ganta ba ranan, da ya baro gun aiki ma haka ya dinga dube dube a hanya ko xai ganta amma har ya isa gida bai ganta ba. Karfe takwas na dare ya shirya ya fita hankalinsa kwance ta gate dinsa bbu wanda ya sani bare yyi querying dinsa inda xa shi, gidansu Saudat ya nufa don yyi missing dinta tsakanin jiya da yau, yana isa ya kirata, ba a dau time ba ta fito sai dai kumbure kumbure kawae take, yyi murmushi yace "Why the pouting?" Ta hararesa tace "Ka manta bari na tsaye kayi ranan ka wuce?" Kamo hannunta yayi yace "Ohk Am sorry dear, how you doing?"ta turo baki tace "Am good" ya shafa kansa yace "So what's new?" Tace "Baxa ka shiga ciki ba?" Yace "Noo, an san kin fito ne?" Tace "Just my little sis" yace "Mum fah?" Tace "She's in her room" yace "Toh rakani mu je mu dawo yanxu" tace "No the other time I escorted you ka sa ana ta min wani kallo a club ni baxan je ba" ya wara ido yace "Wa yace maki can xan je?" Ta hararesa tace "Ban san ka bane" dariya yayi yace "Plss baby we are not staying long fa kawai rakani xa ki yi Akwae abinda xan karba ne" shiru ta d'an yi, sai kuma a hankali tace "Ohk, just thirty minutes before ayi noticing bana gida" hannun ta ya kamo yace "Ohk dear" daga haka ya tada motar ya dau hanyar club din nasu, duk da bin sa da Saudat take club kaffa kaffa take da kanta kuma bata sake ma kowa fuska, don tana mugun sonsa shi yasa bata iya kin yin abinda yake so, Saudat kyakkyawa ce ta ajin karshe, irin matan da samarin xamani ke so, Abuturrab bai yi amfani da wnn advantage din son da take masa ba ya cutar da ita, iyaka kawai ya rike mata hannu sae d'an peck, coz he always keep it at the back of his mind dat shi ma yana da k'anni mata, bai kuma son komai ya samu lovely sisters dinsa, hakan yasa yake yaki da duk wani yaudara na diya mace, kafin minti talatin din kuwa ya maida ta gida bayan sun shiga eatry ya cika ta da kayan ciye ciye, ba shi ya koma gida ba sai kusan sha daya sai a snn ya kuma farin cikin basa side dinsa da Abba yyi, ynxu bbu wanda xai ma san ya dawo bare yace daga ina yake, yana parking gaban gate din ya fito xai bude don bbu mai gadi a side din kuma bai ma bukata, yana bude gate ya dawo xai shiga motar ya hango Samantha da wata mata da baxata haura 40 ba, wai! Da ganinta kaga rikakkiyar Christian, skirt ne jikinta shi bai kai kasa ba amma dogo ne sosai, sae wani bujejen riga da tasa tayi tuck in dinsa cikin rigar, kanta na sanye da irin hulan nan nasu na pastress, hannunta dauke da wani gundumemen Bible, dayan kuma na rike da hannun Samantha, da ganinsu kasan daga church suke, Samantha da ta gansa ita ma sai kallonsa take fuskarta dauke da murmushi har suka iso dai dai inda yake, satan kallon uwarta tayi taga hankalinta na gaba sai rera worship songs take, hannu ta daga masa a hankali alamar bye bye, ya sakar mata murmushi shi ma ya daga mata hannun, har suka wucesa bin su yake da kallo, doguwar riga ce jikinta sai rolling da tayi a kai, girgixa kai yayi ya shiga motarsa ya ja xuwa ciki yyi parking snn ya dawo ya rufe gate din, wanka yayi ya jima xaune yana karatun Qur'ani daga karshe ya mike ya shiga bedroom ya d'an yi xuke xukensa snn ya kwanta. Washegari da ya kasance laraba ana idar da Sllhn Asuba a masallaci drawing din Samantha ya fado masa gashi tace ranan xata yi submitting kuma test dinsu ne, satan kallon Abbansa dake Azkar yyi, don kusan ko da yaushe tare suke fitowa daga masallaci, kuma yasan ynxu sai ya bata rabin awa yana xaune, fuskewa yyi ya mike ya fice ya nufi gida, tsaye yyi a balcony yana tunanin ko dai ya bari kila idan xai fita aiki su hadu, sai kuma ya tuna jiya ma through out basu hadun ba, ya shiga gida ya dauka makullin motarsa ya fito ya bude motar ya dauki littafin da textbook din sai math set ya bude gate ya fice, tafiyar minti goma yayi ya iso dai dai gate dinsu, rasa yanda xai yi yyi, gashi har lkcn gari bai gama washewa ba, bai ma ga alamar an bude gate din nasu ba, leken cikin gidan ya shiga yi yaji daga bayansa an daka masa tsawa "Heyyy who you be, who you find?" Juyawa yyi da sauri yana kallon mutumin ko ba a gaya masa ba yasan mai gadin gidan ne, yace "Ehm, Samantha!" Mai gadin ya masa wani kallo yace "Wetin do Samantha?" Mika masa abubuwan hannunsa yayi yace "Give her plss" daga sama har kasa mai gadin ke kallonsa, Abuturrab ya kalli kansa, jallabiya ce milk colour jikinsa, karasowa mai gadin yyi yace "Who make I say?" Abuturrab yace "Aliyu!" mai gadin ya sa hannu ya karba Abuturrab ya juya ya bar wajen, karfe bakwai da kusan rabi yana kkrin rufe kofa Ilham ta karaso, ya juya yana kallonta yace "Pretty!" Tace "Ya Abu ko shigowa ka daina yi dama nasan kafi son haka" dariya yayi yace "Eh mana, baxa ku ma dinga gani ba bare ku dinga yangan bani abinci na" tace "Yaya pls ka ba Abba hakuri ka dawo cikin gida we are missing you" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yace "Noo, I like it so much here" tace "Why?" Yace "Nothing" tabe baki tayi tace "Ae shikenan, kayi breakfast?" Yace "Yep, Peter ya kawo min" daga haka ya kama hannunta suka bar wajen yace "Za ki sani latti, ki sa kanki latti" tace "Ya turrab 5k plss" yace "I don't have cash, sai ltr" bai jima gun Mami ba ta fito ya hau motarsa xuwa gun aiki. Da ya tashi dawowa da yamma daga gun aiki da gundumemen K'arensa ya dawo da cage tare da mutumin dake rike da Karen, cikin few minutes aka hada cage din karen mutumin ya fito da karen da bakinsa ke a daure ya turasa cage ya rufe snn ya kunce mouth cuff din dake bakinsa, nan karen ya hau haushi, Abuturrab yyi murmushi yace "Yesss!" Tap ya nufa ya bude ruwa yana wanke hannunsa sannan ya dawi yana kallon mutun yace "Yanxu ya xa ayi karen ya saba da ni?" Mutumin yace "In dai kai ne xaka dinga basa abinci ko da yaushe cikin lkci kankani xai saba da kai" Abuturrab yace "Ohk nagode" nn ya  sallami mutumin ya basa kudin mota, yana tsaye yana kallon katon karen da ya fito da halshe sai hakki yake ya ji muryar Mami a bayansa, juyawa yayi da sauri da mamaki tace "Meye wnn kuma Abuturrab?" Wara ido yayi yana murmushi yace "Dog Mami!" Hade rai tayi sosai tace "Uwar me yake a gidan nan?" Ya marairaice yace "Mami gadi xai dinga min ni bana son mutum nafi son dabba!" Bude baki tayi tana kallonsa, can ta girgixa kai tace "Toh ba gidan nan ba kare xai maka gadi, sai ka jira idan ka koma gidan ka na kanka!" Yace "Nooo Plss Mami, bangarena ne nn fah!" Tace "Nace ka fitar min da wnn abun Aliyu" karasowa yyi kamar xai yi kuka ya mata side hug yace "No plss Mami, kinga fa ina jin kamar jiya barayi sun xo anguwar nn, pls ki bar min karen it will be a good watch man for me, bbu abinda masu gadin nn suka iya sai bacci...." Girgixa kai tayi ta juya ta fara tafiya tace "Ni dai bbu ruwana...." Murmushi yayi yace "Yes Mami" main gidan ta nufa ba tare da ta tanka sa ba. Yana xaune misalin biyar kan farin kujera yana danne dannen wayarsa yaji kamar motsi jikin gate, ya daga kai da sauri, sai kuma ya mike ya nufi gate din ya bude, tsaye ya ganta kamar munafuka, tana ganinsa ta koma baya a tsorace, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace "Samanth....." Sai kuma yyi shiru a hankali yace "Samha!" Wara ido tayi tana murmushi tace "Ashe kana nan, just came to say a big thank you!" Har da d'an risinawarta ta kare maganan, ya jingina jikin gate ya rungume hannayensa yana kallonsa yace "For what" turo baki tayi tace "For the beautiful drawing mana" Murmushi kawai yyi yana kallon hannunta dake dauke da Bible, mota ce ta shawo kwanan anguwar ta juya da sauri tana kallon direction din, ta xaro ido tace "Jesus! Abbana ya dawo" kallon motar yayi da sauri sai kuma ya matsa daga gun gate din bata jira yace mata komai ba ta shige cikin gidan, wara ido yayi yana kallon motar har ya xo ya wuce snn ya shiga gidan ya rufe gate din, tsaye ya ganta tayi lamo jikin flower, tana ganin ya rufe gate din ta karaso da sauri tace "Ae ya tafi ko, let me leave" kallon gate din yayi yace "I don't think ya tafi fa, tare yake da wasu a motar kuma na ga sun tsaya" kamar xata yi kuka tace "Bbu wani hanyar doctor?" Girgixa Kai yayi yace "Only this.... Ga kujera ki xauna ki jira su wuce sai ki tafi," Da damuwa tace "Church fa xan tafi, I don't want to miss" shiru yyi yana kallonta, can ya juya ya dau wani kujerar yayi xamansa, bin bayansa tayi tana bin gidan da kallo ta xauna kujerar da ya nuna mata tace "Are you the only one leaving here?" Girgixa kai yayi ya nuna mata hanyar da main house din yake yace "My family members are there, my Mum, Dad and sweet siblings" mikewa tayi ta nufi inda ya nuna mata bata wani yi nisa ba ta hango kantamemen gidan daga nisa, dawowa tayi da sauri tace "Uhn! Toh me yasa kai kake boys quatrs?" Murmushi yayi yace "Because I am a boy, an I prefer here" 'yar dariya tayi tace "Ohk that's true, xan wuce church yanxu" mikewa yayi yace "Bari in duba maki ko ya tafi" daga haka ya tafi gun gate ya bude ya leka, rufewa yyi da sauri ya dawo yace "Noo they are still there ki xauna kawai su wuce" bata fuska tayi tace "Lokacin Church na wucewa" bai tanka ta ba hakan yasa ta xauna, haushin k'are taji ta mike a firgice tana kallon direction din, ihu tayi suna ido hudu da katon karen ta juya xata gudu a rikice yyi saurin rikota da sauri, ta fashe da kuka tace "Noo bana son kare pls" xaunar da ita yyi kan kujera ya durkusa gabanta yana kallonta yace "But it's caged" Har lkcn jikinta rawa yake ta kasa cewa komai, dagota yyi ya shiga balcony da ita ya sa ta xauna ya duka gabanta yace "Ohk sorry Plss...." Hawaye ya sakko idonta tace "Ni xan tafi" mikewa yayi ita ma ta tashi, yace "Karen baya komai, it's very frndly" bata ko kalli inda karen yake ba ta nufi gate da saurinta, ya bi bayanta amma tuni ta fice, tsaye yyi bakin gate dinya rungume hannunsa  ya bi ta da kallo ganin yanda take sauri, sai da ta tabbatar tayi nisa snn ta juya ta kallesa, d'aga masa hannu tayi, ya juya ya shige gate din yayi banging dinsa, kasa ci gaba da tafiya tayi sai kallon gate din take, can ta juya jiki ba kwari ta ci gaba da tafiya.

Hmm!!!
?✍?
[7/31, 09:51] SHS: ? *Noorul Huda*?

4......

Washegari da yamma misalin biyar da rabi Abuturrab na xaune karkashin artificial bishiyar dake dauke da fararen kujeru a karkashi hannunsa rike da Cigarette, dawowarsa kenan daga aiki yayi wanka ya d'an tsakuri abincinsa da ke ajiye a parlor snn ya fito ya xauna ya fara aikin xuke xukensa idonsa na kan k'aren dake ta fama da gundumemen  naman da ya siyo masa a hanya, murmushi yayi ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da babban drawing board da materials din drawing dinsa, bude board din yyi ya tsayar ya dawo da farin kujera kusa da board din ya xauna dai dai yanda xai dinga ganin karen da kyau, ya fi minti biyar yana kallon karen hannunsa rike da well sharpened drawing pencil din hannunsa, daura hannun nasa yyi kan board din, a nutse ya shiga xana k'aren, ya kusa minti goma yana xana kai snn ya dawo jiki, yyi rabi yaji an tura gate a hankali ya juya da sauri, ido hudu suka yi da ita, ta wara ido kamar mara gaskiya ta k'asa tsaye gu daya tana jujjuya Bible din hannunta tace "Am... Ina yini!" Murmushi yayi ya maida dubansa kan board din gabansa yace "Come in....." Kin shigowa tayi tana yi tana lekan karen dake cage tace "No, am going for service!" Ya kalleta yace "Ohk baxa a gaisa ba knn yau?" Murmushi tayi tace "Gashi na gaishe ka, and I can see you are busy drawing what I can't see from here!" Mikewa yayi ya karasa gabanta, tayi tsuru tsuru tana kallonsa, kallonta yayi daga sama har kasa, yau ma doguwar riga ce sea green jikinta, sai jan veil da ta daura a kanta, cikin idonta dake kyalli kmr ta tara hawaye ya kalla, ta juya da sauri xata bar gate din ya riko hannunta, juyowa tayi tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace "Yea, baxa ki ga abinda nake zanawa daga nan ba sai kin shigo" kallon karen tayi a tsorace tace "Noo, ni ina jin tsoron...." Jawota yayi xuwa cikin gidan ya rufe gate din, tace "Noo Plss...." Janta yyi har xuwa gun drawing board din sai buya take bayansa, ya dawo da ita gaba idonta ya sauka kan xanen, shiru tayi tana kallo ko kiftawa bbu, a hankali ta furta "Waoww....." Kallon karen dake cage tayi snn ta kalli na drawing din ta juya da sauri tana kallonsa tace "Doctor wa ya koya ma drawing haka, you are.... " Rungume hannayensa yayi yace "In koya maki ne ke ma?" Da sauri ta gyada kai, ya ja kujeran ya xauna ya dau pencil din ya ci gaba da xanen, durkusawa tayi a hankali kusa da shi ta dafa kafarsa tana kallon yanda yake xanen cike da kwarewa, muryar Khaleesat ya ji, ya juya da sauri sai kuma ya mike ya xaga ae ko ya hango ta ita da Ilham suna tahowa, dawowa yayi da sauri yana kallon Samantha tun kan yace komai ta mike a rikice tace "Your sister I guess?" Bai ce komai ba ya kama hannunta ya nufi kofar parlor ya bude ya sa ta shiga snn ya rufe ya dawo gun drawing din ya xauna ya ci gaba, Khaleesat da Ilham suka karaso, Ilham ta wara ido tace "Waow ya Abuu.... It's sooo beautiful!" Ta gefen ido ya kalleta yace "Thanks" Khaleesat ta durkusa kusa da shi tace "Yaya wai Anty Ramla tace kace xaka kawo wani karen main house, da gaske ne" ya hade rai yace "You two can see am busy...." Khaleesat tace "Don ma mun taho taya ka hira tunda bbu islamiyya yau?" Bai tanka ta ba, Ilham tace "Toh shknn since he's busy let go inside and....." Mikewa yayi da sauri kmr wanda aka mintsila yace "Go where? Kar warce ta shigar min parlor....." Ilham ta bude ido da mamaki tace "Why?" Wani kallo ya watsa mata ya nuna mata hanyar inda suka fito, ganin bbu wasa tattare da shi yasa duk suka juya suka bar gun, ya bi su da kallo har suka bace, ya ajiye pencil din hannunsa, Samantha dake ta kallonsu ta window ta bude kofa ta fito, murmushi ta masa tace "Ur siblings are cute, they re fine...." Rungume hannuwansa yayi ya daga kafada, tace "Bye na tafi church!" Daga haka ta nufi gate ya bi ta da sauri yace "Wait! Baxa ki jira in gama ki gani ba" tace "Lkci na wucewa xan je church ne fa" yace "Ohk I will be very fast sai ki wuce" shiru tayi ya wara mata ido yace "C'mon" karasowa tayi ya xauna ya ci gaba da drawing din ita kuma ta durkusa kusa da shi, sai da aka yi wani minti talatin kafin ya gama xanen, ta xuba ma board din ido tana kallon katon karen dake ta dambe da k'ashi, can ta lumshe ido a hankali tace "Waow, you are so talented" murmushi yayi yana nodding kai yace "Thank you.... Samanth.. Uhm Samha!" Xaro ido tayi tace "Am not Samha but Samantha!" Ya daga kafada yace "Ohk all same...." Hamma yayi yana stretching din hannunsa yace "Am exhausted, No am hungry rather" tace "Baka ci abinci ba?" Langwabar da kai yayi yace "It's finished...." Shiru tayi sai kuma tace "toh me xaka ci?" Ya juya manyan Eye balls dinsa yace "May be black tea, da yaji kayan kamshi" ta tallabi kuncinta tace "Toh wa xai ma, ko xaka shiga gida ka gaya ma Mumy" ya d'an marairaice yace "She won't, yanxu dinner take yi na sani" a hankali tace "Toh ni in maka?" Yayi shiru sai kuma yace "Yess Plss" mikewa tayi tace "Toh xo ka nuna min kitchen din da komai...." Mikewa yayi yace "Yauwa thanks frnd, shiga ki jira inje can cikin gida in dauko lipton din da scent ingredients" dariya tayi tace "Ohk ohk" yayi murmushi ya juya ya nufi can cikin gida ita kuma ta shiga parlonsa, ba a dau lkci ba ya dawo rike da su a wani bowl, ta mike daga xaunen da take ta karba ya rakata kitchen din, yana tsaye daga bakin kofa ta gama dafa ruwan lipton din da ya dume gidan da kamshi, ta juye masa a flask din da ya nuna mata ya karaso kitchen din yana murmushi yace "Waow thanks frnd!" Murmushin ita ma tayi yayi mata stretching din long fair hand dinsa me dauke da kwantancen bakin gashi, a hankali tayi stretching din nata ya karba yayi shaking dinta, yana kallon kwayar idonta. Fitowa yyi da flask din parlor da cup, ta dau Bible dinta tana kallon agogo taga shidda har ya wuce kmr xata yi kuka tace "Ka ga har lkci ya wuce koh?" Da damuwa yace "Ayya, am sorry...." turo baki tayi tace "Yanxu I've missed church sai gobe kuma" yace "Toh ae nace am sorry, ki xauna in sha lipton din kad'an sai in raka ki har kofar gidan ku" xaro ido tayi tace "Dare xai yi" ya hade gira yace "Ba fa pounded yam nace xanci ba" murmushi tayi tace "Ohk ohk, I will wait" daga haka ta xauna ya dau cup ya bude flask ya debi lipton din ya kai lips dinsa, xaro ido tayi tace "Xai kona ka fa" dariya yayi yace "Na fi ki sanin haka" turo baki tayi ta dau Bible dinta ta bude tana kallo, da ta daga kai sai su hada ido, sun yi hakan ya kusa sau uku, yayi murmushi yace "Why you staring at me?" Kafin ta ce komai yayi saurin karawa da cewa "What are you reading" tace "Uhm! Holy Bible" shiru yyi yana kallonta can yace "Toh karanta min nima in ji" ta wara ido tace "Da gaske?" Ya gyada kai ta mike ta dawo kusa da shi da sauri ta xauna a kasa tace "Ohk I will, give me ur attention" kai ya gyada mata yana kallonta, verse din da chapter ta fado masa snn cikin sanyayyan muryarta ta fara karanto masa content din chaptern tana masa explain, kallonta kawai yake cike da tausayi, can ya lumshe ido ya ci gaba da shan lipton dinsa yana saurarenta, haka ta dinga karatun har ya ji kiran sallah, da sauri ya bude ido yana kallonta yace "Alryt, let stop there for today!" Tayi murmushi tace "Ohk!" Mikewa tayi tace "It's almost dark, xan wuce" yace "But nace xan raka ki ai, ki jira in dawo Masallaci" kamar xata yi kuka take kallonsa, can a hankali tace "Ohk!" Ya mike ya mika mata empty cup din hannunsa yace "Ke ma ki xuba ki sha" ba musu ta karba, ya nufi toilet din parlon ya dauro alwala ya fito yace "will be ryt back! You can lock the door kafin in dawo" Bin sa tayi da kallo har ya fita snn ta mike ta kulle kofar ta dawo ta xauna ta debi lipton din kadan ta sha, snn ta kai sauran kitchen, bin kitchen din ta dinga yi da kallo ganinsa fes kamar da mace a part din, fitowa tayi parlor shi ma ta dinga bin da da kallo can ta juya ta koma kitchen ta dauko sweeper da mopper ta dawo, tattare parlon tayi cikin yan mintuna don ba wani dirt bane a ciki snn ta hada ruwa ta sa freshener din da ta gani ta shiga mopping din parlon, tana gamawa ta goge kayan wutan gaba daya cikin mintunan da basu wuce talatin ba ta gama komai ta mayar inda suke snn ta dawo parlor ta xauna tana kallon agogo taga har bakwae da sha biyar, ji tayi kmr ta saka kuka, yanxu ina xata ce ma Mumy ta je, haka tayi ta xama har bakwae da rabi, can ta mike ta dau Bible din ta, taji an kwankwasa kofa, still tayi gabanta na faduwa, kaddai yan gidan ne, karasawa tayi a hankali tana leka window ta ga shi ne tsaye, takalminta ta sa ta bude kofar hade da hade rai ta fito xata wuce ya riko hannunta ya wara ido yace "Wait in raka ki mana, Abbana ne muka hadu a mosque ya aikeni fa" ta kallesa kamar xata yi kuka tace "Toh yanxu ina xan ce ma Mumy naje bayan tun six thirty ya kamata in dawo gida" ya langwabar da kai yace "tell her you went to visit a sick frnd" shiru tayi tana kallonsa can ta girgixa kai a hankali tace "My religion is against lies, we don't tell lies" kasa ce mata komai yayi ya kuma kasa daina kallonta duk sai bai ji ddin amsar ba, can yace "And my religion also! Lying is one of the greatest sin in islam" Wani kallo tayi masa sae kuma tayi dariya tace "amma karya kace inyi a gida yanxu fah!" Kallonta kawai yake duk sai yaji ya tsani kansa hakan da yace mata, "I was only joking, idan nace ki shiga wuta sai ki shiga, religion din ki ya hana karya amma bai hana fita night birthday ba koh?" A bit annoyed yayi maganar hakan yasa tayi shiru tana kallonsa bai kuma kallonta ba ya karasa cikin parlon yayi xamansa ta bi sa da kallo, can ta juya cikin sanyin murya tace "Ohk, good nyt" a takaice yace "Nyt!" Ta fita daga parlon, ta kusa minti biyar da fita sai kuma ya mike shi ma ya fita, ko alamar ta bai gani a layin ba, yayi jam din gate dinsa ya bi ta da sauri, yana shan kwana ya hango ta tsaye ta rakube jikin wani flower ya daga k'afa ya karasa gun da sauri, k'arnuka biyu ya gani a gun suna xaune shine yasa ta kasa wucewa, dafata yayi ta fasa wani ihu a tsorace ya juyo da ita da sauri ta fado kansa ya rungumeta, lamo tayi jikinsa yana jin yanda kirjinta ke bugawa kamar xai fito, a hankali tace "Doctor!" Yace "Yes matsoraciya" janyeta yayi jikinsa ya rike hannunta suka ci gaba da tafiya har suka wuce gun karnukan  tana shishshige masa, bbu wanda yace komai cikinsu har suka iso bakin gate din gidan nasu ya sake hannunta ta kallesa cikin sanyin murya tace "Thank you" murmushi yayi ya rungume hannayensa yana gyada mata kai, ta mayar masa da murmushin ta bude gate dinsu ta shiga ta daga masa hannu snn ta rufe gate din, lumshe ido yyi ya bude sannan ya juya ya bar wajen. Samantha na shiga gida suka kusa cin karo da Mum dinta bakin kofa, uwar ta hade rai tace "Where are you coming?" Shiru Samantha tayi tana kallonta a tsorace, "Baxa ki bude baki ki min magana ba kina kallona, karfe shidda aka tashi church, daga ina kike yanxu?" Sauke kanta tayi kasa, ta mata wani tsawa tace "Ba kya ji na ne?" Kamar xata yi kuka tace "Am sorry Mum, baxan kara ba" Mum din ta daure fuska tace "Wato ba daga church din ma kike ba ko....." Dad din Samantha ne ya karaso bakin kofar Samantha ta kamo hannunsa hawaye cike idonta tace "Abba kace ma Mumy tayi hakuri baxan kara ba, am so sorry" patting din shoulders dinta Abban yayi yace "It's ohk love kar ki sake dadewa church da an tashi ki dawo gida" kai ta gyada masa, ya ja hannunta suka bar wajen. Karfe tara Samantha na shirin kwanciya Mumy ta shigo tace "Oya tashi ki shirya mu je vigil tunda gobe friday da wuri xaki dawo sch sai kiyi bacci" Samantha tace "Mumy but karatu nake son xan....." "C'mon my frnd tashi kiyi abinda nace, karatu ya fi addinin ki ne" mikewa Samantha tayi bata kuma cewa komai ba ta fara shiri uwar ta juya ta fita, sai da suka yi ma Dad sallama snn driver ya fita da su xuwa church a mota, suna kusa kai wa dai dai gidansu Abuturrab Samantha ta hango gate din a bude sai gashi ya fito da mota, dai dai tsakar titin ya bude motar ya fita ya shiga gida don kulle gate din, masifa Mumy ta shiga yi Driver na taya ta don ya tare masu hanyar wucewa, Abuturrab ya fito da niyar xai basu hakuri Mumy ta sauke glass cike da masifa tace "Kai halan titin nan na Ubanka ne?" shiru yayi yana kallonta don sarai ya ganeta, Samantha sai kallonsa take, can ta kamo hannun Mumy tace "Mumy kiyi hakuri kila bai san...." Turata uwar tayi tace "Uwarki, shi makaho ne bai hango motar mu ba?" Abuturrab ya dauke kai ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya gyara parking ya basu hanya, har suka wuce idonsa na kan motar. Ranan Juma'ah yana isa main road xai je masallaci ya hangota tana saukowa daga motar gidansu, tana sauka kuma motar ya wuce, xata wuce motarsa yace "Hello!" Juyowa tayi da sauri tana ganinsa tayi murmushi ta d'aga masa hannu.

?✍?
[7/31, 09:52] SHS: ? *Noorul Huda*?

5.....

Ganin yaki tafiya ta karasa kusa da motar tace "Ina yini?" Yace "Lafiya ya schl?" Kai kawae ta gyada masa yace "baki yi bacci bane see ur eyes!" Langwabar da kai tayi tace "We went for vigil" ya kalli wrist watch din hannunsa yace "Come in let me drop you" ta xaro ido tace "Ba masallaci xaka je ba?" Yace "There is still time" xagawa tayi ta bude front seat ta shiga, yayi reverse ya juya, a hankali tace "Sorry for what happened yesterday night" murmushi yayi yace "Yeah am at fault, gaskiya mama ta fadi" bata kuma cewa komai ba har suka iso bakin gate dinsu yayi parking ta bude motar ta fita ta rufe snn ta jingina jiki tace "Thank you" gyada mata kai yayi tace "Don't forget to pray for me fa" murmushi yayi yace "Alryt," daga haka ta nufi gate shi kuma ya tada motar ya bar layin. Washegari da ya kasance asabar Abuturrab na dawowa daga masallaci ya shiga main house don gaida Abba kasanacewar yana gari, Abba ya amsa gaisuwarsa idonsa dake dauke da glass a kan laptop din dake gabansa, can Abuturrab ya mike da nufin wucewa Abba yace "Ina fa da magana da kai Ali" komawa yayi ya xauna yace "Toh gani Abba" Abba bai ce komai ba har na kusan minti biyar sai kuma yace "How about planing of settling down Aliyu!" Shiru Abuturrab yayi don sai da gabansa ya fadi, Abba yace "Yes it's high time you do that, you will be thirty one soon...." Abuturrab ya sauke kansa kasa kana yace "Abba komai fa lokaci...." Abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Don't tell me that, Sai yaushe lokacin xai xo?" Shiru yyi bai ce komai ba, Abba yace "Go and think about it pls" a hankali yace "Toh Abba nagode" daga haka ya mike yyi masa sallama ya fita, bedroom din Maminsa ya nufa ya sameta xaune har lkcn kan darduma, Khaleesat kuma na kwance kan gado tana bacci, ya xauna bakin gadon, can ya gaji da xaman yayi kwanciyarsa kawae, sai kusan bakwae Mami ta gama Azkar dinta ta mike ta dauke darduman tana kallonsa don idonsa a lumshe yake tace "Abuu are you sleeping?" Bude idon yayi ya mike xaune sannan ya sauko kasa ya gaisheta ta amsa tace "Ka tashi lafiya?" Yace "Yea, but Abba spoilt everything" Mami ta d'an bude ido tace "Me kuma ya faru" ya marairaice yace "Mami wai maganan aure fa Abba ke min, yaushe ma na girman" Mami tayi murmushi tace "Mancewa kayi, jiya ka girma" yace "Allah Mami kije kiyi masa magana kice ur son is not grown up yet, yaushe ma kika daina ban madara da daddare?" Dariya Mami tayi ta xauna gefen gado tace "Silly you! c'mon tashi ka ban waje, it's better kaje ka xauna ka yi tunani da kyau kaga what's good for you, kilan idan kayi aure zaka nutsu" mikewa yayi yace "Am not ready for marriage Mami, toh waye xai xama mijin ma idan aka yi auren... Ita ko ni" Bai jira cewarta ba ya fice ta bi sa da kallo tana murmushi, jallabiyar jikinsa ya cire ya dau kayan sport dinsa ya sa ya dau chill Coke a fridge snn ya fito ya nufi gun da yasa aka tula masa kayan gym, ya kusa awa daya gun yaji kamar an bude gate, xagayowa yayi da sauri, tsaye tayi bakin kofar tana kallonsa hannunta rike da littattafai tana sanye da bakar abaya tayi rolling kanta, ganin kallon da yake mata yasa ta kasa tsaye gu daya, can tace "Um Good morning" sai kuma ta juya da sauri xata wuce, yace "Frnd!" Juyowa tayi, ya mata murmushi ya karasa kusa da ita ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kai tayi, yace "Ina xa ki this early morning?" Dago kai tayi ta kallesa tace "Lesson, waec lesson!" Yace "Ohh that's nyc, how was ur nyt?" Ta wara ido tace "Splendid! Xaka min assignment plss sir" langwabar da kai yayi yace "Assignment kuma, which?" Tana kkrin bude littafin tace "Physics and Biology" mika masa tayi ya karba yana kallo snn yace "Uhm!" Tace "You are busy koh?" Ya kalleta yace "Sai yamma zan fita aiki, am around now" cike da shagwaba tace "Toh ka min plss" kallonta kawai yake, can yayi murmushi yace "Ohk, but I will only show you how to solve it, and you do the rest by ur self" ta xaro ido tace "But am going to lesson...." Yace "Wannan ma ai lesson ne" shiru tayi tana kallonsa, ya mika mata littafin yace "Shiga ki ajiye a ciki, tare xa muyi" a hankali ta sa hannu ta karba littafin ta nufi cikin parlon amma da gani ranta bai so ba, ya sauke hannunsa ya bi ta da kallo sai kuma ya juya ya koma gun gym din ya dau sauran coke dinsa ya shiga parlor, tsaye ya ganta ya karashe shanye coke din ya wurga can din yace "Why standing like a soldier?" Murmushi tayi ta d'an dosana kugunta jikin kujera, ya karasa parlon yace "Let me freshen up sai mu fara" kai ta gyada masa kawai ya dau hanyar bedroom dai dai lkcn da aka danna bell, dawowa yayi da sauri ita kuma ta mike tana kallonsa da damuwa tace "ur sisters koh" bai tanka ta ba ya nufi kofar ya leka ya ga peter ne dauke da breakfast, bude kofar yayi ya karba ba tare da ya amsa gaisuwar da yake masa ba yace "Thank you" sannan ya rufe kofar ya karasa parlon ya ajiye, har lkcn tana tsaye tace "Kar sisters dinka su xo fa" yace "Bbu kowa gidan fa, duk sun tafi islamiyya" a hankali ta koma ta xauna, ya wara mata ido snn ya wuce, ya kusa minti talatin kafin ya fito sanye da farin polo da 3qtr baki ya shigo parlon yace "Sorry for keeping you waiting" murmushi kawai tayi ya xauna kan rug ya matso da tray din breakfast din da aka kawo mai, ya kalleta yace "Je kitchen ki kawo wani cup plss" ba musu ta mike ta wuce kitchen din sai ga ta ta dawo da cup ta samesa yana hada tea me kauri, ta ajiye masa cup din ta koma ta xauna, ya hada wani snn ya kalleta yace "Taho muyi breakfast" ta xaro ido tace "Noo, ni fa na k'arya" gyada kai yayi yace "Ashe ko baxa ayi assignment din ba yarinya" ta marairaice tace "Da gaske fa doctor na ci abinci" ya hade rai sosai yace "Toh ai shknn" shiru tayi tana kallonsa sai kuma ta mike ta karaso kamar xata yi kuka ta xauna, yace "Allah ya taimake ki da bbu abinda xan maki" murmushi tayi ta sunkuyar da kai, ya ajiye mata cup din tea a gabanta, snn ya debi potatoe, yam, egg, plantain a plate daya ya ajiye mata sai pepper soup din naman ram ya ajiye mata, ta marairaice tace "baxan iya cinye su ba Dr" yace "Ohk to mu ci tare" dawowa yayi gefenta ya xauna ta kallesa ta gefen ido, ya dau fork daya ya ajiye mata daya snn ya soma ci, da kyar ta iya daukar fork din don duk a takure take ta dauki potatoe ta kai baki a hankali tana satan kallonsa, sai cin abunsa yake, ganin yanda take tsakuran abincin ya ajiye fork din hannunsa yana facing dinta yace "Kinsan Allah idan baki ci abincin nn ba bbu abinda xan maki" ta xaro ido tace "Kaga ina ci fahhh" hararanta yayi ya ci gaba cin abunsa, haka yasa ta bude ciki ta ci abincin sosai don sai da suka cinye wanda ya diba snn ya shanye tea dinsa ya mike yace "Fast ki shanye tea din mu fara" kai kawai ta gyada masa kamar xata yi kuka don ta koshi. Yana kallo ta dawo kusa da shi daga kasa ta xauna tace "Doctor na gama" kallon wajen yyi ya ga wayam ta kwashe komai yace "Are you sure kin shanye shayin kuwa" ta turo baki tace "In kawo cup din ka ga?" Ya gyada kai yace "Alryt! Kwaso books din" mikewa tayi, tayi yanda yace ta ajiye su a kasa, ya sauko ya rage volume din Tv din, ya bude physics book din yana kallo, shafa beard dinsa yayi ya lumshe ido ya bude yace "Ohk, listen attentively" tace "Toh" a nutse ya shiga mata solving din questions din yana mata bayani, ya maimaita ya kai sau biyar har sai da tace ta gane, yayi forming questions uku ya bata tayi ta karba tana kallo, ya mayar da hankalinsa kan kallon da yake, tana gamawa ta kallesa tace "Am through" karba yyi yana dubawa, can ya gyada kai yace "Then do ur assignment now" tace "Toh" snn ta fara assignment din, ko da ta gama tare suke yi biology din har suka gama, ta kalli agogo taga goma ya kusa ta kallesa kafin tace komai yace "Lokaci ya riga ya wuce, just read ur note...." Xaro ido tayi tana kallonsa tace "Ohk to xan tafi gida" yace "Mum xata tambayeki why you came back early" shiru tayi bata ce komai ba, yace "So it's better ki jira time yyi sai ki wuce" ita dai bata ce komai ba, yyi kwanciyarsa kan 3 sitter ya canxa station, wani American film ake yi tayi tagumi ita ma tana kallon movie din, gajiya tayi ta bude essential bio dinta tana kallo, kmr ance ta dago kai ta kalli Tv abinda ta gani yasa ta kallesa da sauri, lumshe ya ga idonsa, bata kuma kallon Tvn ba ta mike da sauri tayi hanyar kitchen, plates din da suka yi breakfast ta shiga wankewa tana gamawa ta gyara kitchen din snn ta fito da sweeper da mop har lkcn rufe ta ga idonsa sai ta ga kamar bacci ma yake, gyaran parlon ta fara yi da yake bbu wani kura cikin few minutes ta gama gyaran ta mayar da komai inda yake ta dawo ta kalli agogo ta ga sha daya ya kusa, one sitter ta xauna ta canxa station xuwa Bollywood, bata yi minti goma tana kallon ba ta jinginar da kanta jikin kujera sai bacci, bude ido Abuturrab yayi ta dalilin wayarsa da ya ji yana ring a bedroom ya mike xaune yana kallonta ganin yanda ta takure kan kujeran tana bacci, mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya durkusa, long lashes dinta kawai yake kallo ko kiftawa bbu can ya sauka idonsa kan dogon hancinta kafin d'an karamin bakinta, hannunsa ya daura kan fingers dinta ta bude ido da sauri, ya mike yace "You are not comfortable xo ki kwanta a can" xata yi magana ya kama hannunta ta mike ya nufi kan kujeran da ya tashi daga yasa ta kwanta snn ya wuce bedroom, missed call din Abokinsa Mujaheed ya gani ya shiga kiransa back, bugu uku Jaheed ya daga, daga daya bangaren yace "Ina ka shiga man?" Abuturrab yace "Was having a Nap at the parlor, ya aka yi?" Jaheed yace "Alryt gani tahowa....." Da sauri Abuturrab ya katse sa ta hanyar cewa "Yanxu fa xan fito office ku hadu a can" Jaheed yace "It's urgent....." Abuturrab ya kalli agogo yace "Ni na ma shirya fa, fitowa kawai xan yi" Jaheed ya d'an yi tsaki ya katse wayar, Tabe baki Abuturrab yayi xai shiga toilet ya ji ana danna bell, fitowa yayi da sauri, ga mamakinsa ko motsi Samantha bata yi ba, baccinta kawai take, kofa ya nufa a leka waje yaga Mami tsaye, xaro ido yyi ya juya da sauri ya isa gun Samantha tashinta ya shiga yi ta bude ido a hankali tana kallonsa, sai kuma ta mike xaune tana kalle kalle dai dai lkcn da Mami ta kuma danne bell tace "Abuu?" Mikewa Samantha tayi a tsorace tana kallonsa da kyar tace "Ur Mum?" Bai ce komai ba ya kama hannunta ya wuce bedroom dinsa da ita tana shiga ya rufe kofar snn ya fito ya koma gun Kofar ya bude, sai ka rantse daga bacci ya tashi yanda yyi da fuska, Mami tace "Bacci kake?" Gyada Kai kawai yayi, tace "Ohk sorry, ka xo ku gaisa da Yakumbo ta xo" shiru yyi yana kallonta sai kuma ya hade rai yace "Mami maimakon kice na fita aiki?" Mami tace "Go and freshen up ka fito ku gaisa nace, bana son magana" daga haka ta juya ta bar gun tana kallon karen dake cage abinsa, girgixa kai tayi tayi gaba. Abuturrab yayi tsaki ya juya ya koma bedroom dinsa, durkushe ya ganta bakin kofa ya buda ido yace "Me kike a nan kuma?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, yayi murmushi ya nuna mata gefen gado yace "Kiyi xaman ki, or are you afraid, she's gone already?" Mikewa tsaye tayi ta girgixa kai tace "A'a xan wuce gida karfe sha biyu muke dawowa daga lesson din" kallon agogo yayi sai kuma yace "Alryt, me xaki yi a gida yanxu idan kika koma?" Tace "Idan Mumy bata nan xan yi girki, that's all, da yamma kuma in tafi catechism" ya rungume hannayensa yace "Uhn ashe kin iya girki" xaro ido tayi tace "Kai!" Sai kuma tayi murmushi ta dauke kai, yace "Ohk idan ke kika yi girkin ki xubo min xan ci" ta kallesa da sauri tace "Da gaske?" Ya gyada mata Kai, tace "Ohk xan kawo maka" daga haka ta juya tace "Bye na tafi" yace "in raka ki?" Girgixa Kai tayi tace "Noo, thank very much" daga masa hannu tayi ya bi ta da ido har ta fita daga dakin, murmushi yayi ya sauke hannayensa ya shiga toilet, wanka ya kuma yi ya fito ya shirya cikin kananun kaya ya fito xuwa main House, da sallama ya shiga parlon, Yakumbo dake xaune tare da Mami ta bi sa da ido har ya karaso parlon, xaunawa yayi a kasan lallausan carpet din dake malale tsakar parlon ya gaisheta, ta tabe baki tace "Lafiya lau, ya aiki?" Ya shafa kai yace "Alhmdllh" Tace "Wato dai har gobe baxa kayi xumunci ba ko Aliyu, nan nan yayanka ya dawo daga Germany bayan shekaru masu yawa amma ka kasa xuwa inda yake ka gaishesa" Abuturrab ya d'an hade rai yace "Umma na kirasa fa...." Tace "Rufen baki, kira nace ko xuwa can" dauke kai yyi, Mami dai bata ce komai ba, Yakumbo tace "Ba dai ka da kamarsu a duniya wllh, idan ka so ka rike su da mutunci su ne iyayenka gobe" Mikewa Abuturrab yayi ya nufi kofa, ta bude baki tace "Ohh ga shegiya na magana koh?" Ko juyowa bai yi ba har ya fice, ta kalli Mami tace "Hajarah anya tarbiyar arxiki kika ma Aliyu kuwa, yo ashe idan Ahmad na masa magana xai iya tashi ya wuce" Mami bata ce komai ba ta mike ta bi bayansa, har ya kusa part dinsa ta gansa tace "Aliyu" juyowa yayi yana kallonta ta karasa tace "Are you stupid ake maka magana xaka tashi ka wuce" yace "Haba Mami ni me yasa matar nn baxata kyaleni bane a rayuwar nn, komai nayi tace bai yi ba, ni gaskiya darajar Abba yasa nake daga mata kafa....." Tsawa Mami tayi masa tace "Koma dai meye yayar Mahaifin ka ce, and you have to respect her the way you will respect ur father...." Bai kuma cewa komai ba ya dauke Kai, tace "Maxa ka koma ka bata hakuri kar in saba maka" da kyar yace "Ohk Mami, amma sallah xanje yi masallaci yanxu" bata ce komai ba ya nufi gate, ta girgixa Kai ta juya ta koma gidan, ko da Abuturrab ya dawo daga masallaci sai da ya ga dama ya shiga gidan bbu yabo bbu fallasa ya bata hakuri ya fice daga parlon, karfe hudu yana shirin fita gun aiki aka danna bell a parlor.

Haske writers asso?✍?
[7/31, 09:52] SHS: ? *Noorul Huda*?

6.....
Fitowa yyi ya bude kofar parlon ya ganta tsaye rike da basket din abinci, wara ido yayi yana kallonta, tace "Um na kawo maka abincin" rungume hannayensa yayi yana murmushi yace "Da gaske?" Ta gyada masa kai ya bata hanya ta shiga parlon ya juya ya bi bayanta, tsakar parlon ta ajiye abincin ta kallesa ya sakar mata murmushi yace "Thanks Samha!" Mikewa tayi ta dau jakarta tace "Uhm am going to church!" Shiru yayi yana kallonta, ta wara masa ido tace "Bye" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo, can ya bi bayanta da sauri yace "Church kuma?" Ta kallesa tace "Eh Catechism xan je" rasa abinda zai ce mata yyi, ganin har ta fita ya bi ta yace "Which means baxa ki rakani ba knn, ke fa nake jira....." Ta juya tace "Ina xan rakaka?" Ya langwabar da kai yace "Clinic xan je duba patients dina" tayi shiru tana kallonsa, can tace "Toh church din fa, it's being a long time bn je church ba fa" yace "Ehh to daga can sai inyi dropping din ki a church din" bai jira cewarta ba ya juya ya dau car key a daki ya dawo yace "Mu je" yana gaba tana biye da shi suka isa gun motarsa ya bude mata snn ya tafi ya bude gate yana fita da motar ya fito ya rufe gate din snn ya shiga ya dau hanyar Clinic din da yake aiki, Ba tare da ya kalleta ba yace "Tell me about ur self!" Ta d'an kallesa sai kuma tayi murmushi tace "Ohk" jinginar da kanta tayi jikin kujera a hankali tace "Sunana Samantha David, but my baptism name is Rebecca, I am an only child, ni kadai parent dina suka haifa, I was born and brought up into a devoted Christian home, My maternal grandfather is a pastor, and my Mum Rachael took over  him my mum i
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 16,207 09-10-2018, 08:20 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 5,998 08-18-2018, 01:15 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 1 16,370 08-10-2018, 01:18 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar* Gimbiya 0 12,618 08-10-2018, 12:48 PM
Last Post: Gimbiya
  *Noorul Huda* by Khaleesat Haiydar Gimbiya 0 15,975 08-05-2018, 11:27 AM
Last Post: Gimbiya
  *CAPTAIN_AHMAD JUNAID* By Khaleesat Haiydar_ ✍? Gimbiya 0 22,977 11-16-2017, 12:51 PM
Last Post: GimbiyaUsers browsing this thread: 1 Guest(s)