The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan*
#1
*??NIDA YAH SAYYADINMU*??


_By_
*Ummu Hanan*



<<1>>


***Wai humaira saurin me kikeyi haka kike abu kamar wadda zata tashi sama?,umma dake kofar kicin tana yanka latas ta fada. humaira dake alwala cikin sauri tace "umma na makara ne fa.baki umma ta ta6e tace ai kinsan da zuwa makarantar kikaje kika kwanta kina barchi sai kuma ynx kizo kina wani saurin banza da wofi,,,umma nima fa bansan barcin ya daukeni ba ta fada yayin data ajiye butar hannunta ta shige dakinta...a gaggauce ta sanya kayan islamiyyar tasu milk color da farin hijab,ko mai bata tsaya shafawa ba ta dauki jakar ta ta fito tare da yiwa umma dake bakin famfo tana wanke latas din data yanka sallama ta fice..

Tafe take tamkar wadda zata tashi sama ,Allah yasa wnn jarababben yah sayyadi *_ABDALLAH_* n baizo ba ta fada a fili tana dan turo baki gaba..,

Ai kuwa addu'arta sam bata ci ba dan kuwa tana shan kwanar makarantar ta hangoshi zaune kan farar kujera kanshi a qasa yana duba wani littafi.


Farine sosae daya hada da sirkin ja kyakkyawane na buga misali kuma ingarman namiji da kowacce mace maiji da kanta zataso ya zamo miji gareta,,ma'abocin tsafta da kamshi yanda duk inda zaije kafin yakai daddadan kamshinshi ne zai fara yin sallama.nutsatstse mai kamala kallo daya zakayi masa ka fahimci ilmin addinin islama ya gama ratsashi.

Sanye yake cikin wani jallabiyya brown color mai kyau sai kyalli take ya dora hular zanna bukar mai zanen fari da brown kwantacciyar sumarshi baqa sidik ta sauko har dokin wuyanshi.


Duk taku daya datayi sai gabanta ya fadi dan kowa a makarantar yana shakkar yah sayyadi abdallah ,dan sam baya daukan wasa abinda yake kaishi shi yake zuwa yayi.


A hankali tayi sallama tare da tsugunawa a gefenshi motsin da jajjayen lips dinshi sukayi ta gane ya amsa sallamar datayi,,yah sayyadi ina yini?,banza yayi mata tamkar ba dashi take ba.ganin bazai yi magana ba yasa tace yah sayyadi umma ce ta sakani aiki shiyasa na makara..still dae bai d'ago kaiba haka nan kuma bai kulata ba,baki ta ta6e cikin ranta tace karkayi maganar mana..dama ai nasan hali,,haka ta cigaba da tsugunno sai faman mutsu2 take saboda kafafunta da suka fara sagewa.

*saida suka dau kusan 40mins a haka iya gajiya humaira tayi cikin nutsuwa ya rufe littafin bulugul maram din da yake karantawa ya dago kansa tare da zuba mata shanyayyun idanunsa dake tafiya da imanin daukacin "yanmata tuni tayi qasa da nata kan.saida yadan ja numfashi kafin yace cikin husky voice nasa wato ke bakijin mgn ko? kusan kullum a makare kike zuwa makaranta to ki maida hankalinki kinsan halina sarai basai an fada maki ba yau dai nayi maki afuwa but next tym ki qara ki gani haduwarmu ba zatayi kyau ba,, oya 6ace min da gani..

Da kyar ta miqe saboda kafafunta da sukayi tsami,ganin tayi nisa dashi yasa ta fara kunkunin cewa " kaji yah sayyadi abdallahn nan wai yayi min afuwa bayan irin tsugunon daya sani gashi kafafuna sai ciwo suke.ta karasa fada tare da murguda baki hadi da yin wani irin fari da fararen manyan idanunta..niko nace ashe rashin kunyar taki ta bayan fage ce da kiyi agabanshi mana idan ba tsoro ba,lolx.

A class din ta tarar da yah sayyadi nura mai musu akhdhari kusa da aminiyarta fatima ta zauna suka cigaba da karatun.

             'Yana fita fatima ta juyo ta dubeta tana murmushi tace uhm sarkin "yan makara zuwa ynx ya kamata a nadaki sarauniyar makararru na makarantar nan,tsaki taja tana harararta tace ni ki kyaleni da abinda ya dameni,kafata nan banda xogi ba abinda take.meya faru?, wnn yah sayyadi abdallahn mana wajen 40mins ina tsugune bai kulani ba wai kuma har da cewa yayi min afuwa.....shigowar shi ajin ne yasa ta maida maganar da tayi niyyar fada., tuni class din yayi tsiit saboda tsoronshi da akeji sassanyan turarenshi mai dadin qamshi ya cika ajin ,zama yayi ya fara biya musu karatun qur'ani dan shi yake daukansu.bakajin komi sai daddadar muryarshi dake karatu cike da gwanancewa tare da bawa ko wani harafi haqqinsa..


*qarfe shidda aka tashesu,suna tafe kan hanyar komawa gida ita da fatima suna hira har suka iso gidansu fatima sukayi sallama ta shige gida ita kuma ta cigaba da tafiya dan tsakaninsu akwai " yar tazara...

*_Mrs salees mu'az_*

*??NIDA YAH SAYYADINMU??*


_By_

*Ummu Hanan*


<<2>>


***Abba Hussain da baba kabeer abokanan juna ne sosai suna zaune cikin garin kano,kowanne da iyalanshi,unguwarsu daya suna da rufin asirinsu dai2 gwargwado kowanne yana da babban shago cikin kasuwar kwari.

          '''Abba Husain da matarshi halima wadda ake cewa ammi suna da "ya" ya biyar,,naseer,shine babba sai basheer, Yusuf, Zainab sai auta ABDALLAH.  sun bawa "ya" yansu nagartaccen ilmin addini dana zamani suma duk "yan kasuwane sai Yusuf da yake aikin gomnati,shi kuma abdallah yana kasuwancinsa sannan yana koyarwa a wata islamiyya a cikin unguwar.



Baba kabeer kuwa shi Allah bai bashi d'a namiji ba " ya"yanshi shidda duk mata asiya ce babba sai "yan biyu hassana da hussaina sai ramla da Asma'u sai kuma auta humaira,,duk sunyi aure dan daga secondary basu cigaba Asma'u da humaira sune kawai basuyi aure ba kasancewar Asma'u tana hannun kanin baba kabeer din da bai ta6a haihuwa ba yasa humaira ce kawai a gidan.


           "" shekarunta sha shidda kalar ta irin black American ne kyakkyawace sosae amma ba lallai kana kallonta ka fahimci hakan ba wato dai kananan kyau gareta.yayin da shi kuma abdallah ke da manyan kyau.

Sosa

 *??NIDA YAH SAYYADINMU??*


_By_

*Ummu hanan*


<<3>>



Sosae gidaje biyun ke sadar da zumunchi tsakaninsu,kuma kowanne cikinsu biyun yana da ikon zartar da hukunci kan iyalan dayan yana nan ko baya nan.


         Sam humaira bata cika kunya ba ga tsiwa dan ma umma na taka mata birki.



    ''Yau din ma a makare ta tafi makarantar bataji worning din yah sayyadin nasu ba,,murmushi ta saki lokacin da taga ba kowa a wajen makarantar musamman wannan dan sa idon,. sauri ta qara dan shiga class din su.
      "Turus tayi ganin wanda ke cikin ajin ,wani mugun kallo yake watsa mata.
'Kafarta ta daga da niyyar shiga ta tsinkayi muryarshi na cewa 'karki sake ki shigomin aji kiyimin kneeling a nan.baki ta tura gaba tana kunkuni ta koma gefe tayi kneeling.

...saida ya da'de kafin ya fito duk tabi ta gaji kamar tayi kuka.

Cikin takunshi na qasaita mai cike da nutsuwa ya karaso gabanta,jikin bango ya jingina ya tokare kafarshi da'ya tare da harde hannayensa a faffadan kirjinshi ido qura mata yana mamakin rashin jin mgn irin na yarinyar.

"Ita kam kanta na qa'sa ta tsurawa zara2 fararen yatsunshi na kafarshi dake qasa....ya mukayi dake jiya??. ta tsinkayi muryarshi na fada,shiru tayi ta rasa abin fada ba dake nake ba?, ya qara tambayarta..am...uhm..yah sayyadi umman muce....shut up ur mouth stupid din yarinya kawai ya katseta cikin hasala,kullum daga kice umma ta aikeki sai kice ta sanyaki aiki alhalin kuma karya kike mata.

"Da gas...yimin shiru ya kara katseta.ajin ya leqa ya kirawo umar monitor din ajinsu yace yaje ajin malam Suleiman ya karbo masa bulala..na shiga uku badai dukana zaiyi ba?, ta fada cikin ranta gabanta na faduwa don akwaita da masifar tsoron duka nan da nan aka kawo masa bulalar,,bani hannunki yace yana daga bulalar sama tuni idanunta suka kawo kwalla,,yah sayyadin dan Allah kayi haquri bazan qara ba ta fada muryarta na shaking.ki bani hannu nace ko ya fada yana zare mata manyan idanunshi dake tsoratata,jikinta gabadaya rawa yake ta miq'a masa hannun tuni kwallar data tarar mata ta fara sauka bisa kuncinta yana shirin sauke mata bulalar tai hanzarin janye hannunta tana kuka wae ni sa'an wasanki ne ?. Girgiza kai ta shiga yi tana yayyarfe hannayenta cikin kuka tace " yah sayyadinmu dan Allah kayi haq.....maganar tace ta katse coz jin saukar bulalar a bayanta da sauri ta gantsare tare da sakin wata siririyar qara hannu takai da nufin ta sosa wajen yace
           ''Idan kika sosa ta zube.

"Tana ji tana gani saida yayi mata bulala biyar lafiyayyu sannan ya kyaleta sai faman kuka take ajin kusa dasu yayi shigewarsa ya barta awajen bayansa tabi da kallo tana jifansa da harara.

Tana shiga " yan ajin suka zubo mata idanu harara ta balla musu tare da jan wani mugun tsaki sannan ta nemi kusa da fatima ta zauna.


'Dan Allah humaira ki daina jan abinda zai dinga hadaku da yah sayyadi abdallah kinsan halinshi fa sarai tunda kamar "yan uwanku suke.
        " banza tayi mata ta cigaba da goge hawayen idonta da hijab dinta.


**Ana tashi aranar ko fatima bata tsaya jira ba ta tafi.

Tana cikin tafiya yazo ya wuceta a machine dinshi harara ta bishi da ita tamkar idanunta zasu fado afili ta furta mutum simi2 a haka amma sai mugunta fal ciki nidai sai Allah y sakamin wlh.ahaka tana ta faman kunkuni da zumbure2n baki ta shiga gida.

A tsakar gida ta samu umma tana fere dankalin turawa zata yiwa baba fatenshi da yace yana sha'awa,a kusa da ita ta zauna tana kara tura baki gaba,da kallo umma  ta bita kafin tace ke kuma fa lpy ke dawa??, ba yah abdallah bane. yayi miki me?? ba dukana yayi ba.haka nan dai nasan bazai dakeki ba da abinda kikayi masa umma tace  tana mikewa gami da daukar robar da dankalin ke ciki ta shige kitchen.

Tashi tayi ta zari Jakarta tayi dakinta tana mitar umma ta fi son abdallah akanta.



***********
"Washegari alhamis ba islamiyya suna zaune bayan sallar asr tana mammatsawa umma kafafunta. Umma tace " ya kamata fa yau kije ki gaida amminki,indai muka hadu sai tayi min korafin rashin zuwanki gidan.., nan da nan ta tur6une fuska dan sam bata son zuwa gidan saboda abdallah.., umma a bari sai wani satin dan Allah,, a'ah ki tashi ynx kije ki gaisheta bana son musu turo baki tayi tace "Allah umma in mutum yaje yah abdallahn nan yai ta wani hararar mutane..,kai umma ta girgiza tace ya salam! humaira wai me abdullahi ya tsare miki hakane?uhm?...Allah umma gaskiya nake fada,, toh naji koma me yake yi sai kince maxa2 ki tashi ki shirya...ba don ranta ya soba ta miqe ta shiga dakinta ta shirya cikin riga da skirt na atampa green color da touch din orange. tasa orange din hijab mai hannu plat shoes ta saka ta fito tare da yiwa umma sallama tayi mata Allah y kiyaye tare da saqon gaisuwa gurin ammin.



^^^Cikin natsuwa tayi sallama dan madaidaicin gidan mai kyawun fasali abinda bataso gani ba shi ta ganin abdallah ne zaune kan wata katuwar darduma gefenshi tulin littafai ne na addini da alamu karatu zaiyi ko kuma y gama sai daya gefen nashi cikin plate yankakkun fruit's ne a ciki idanuwansu ne suka sarqe cikin na juna kowa yayi hanzarin janye idonsa a dakile ya amsa sallamar tata ammi dake kitchen ta fito tana fadin a'ah muryar wa nakeji kamar ta ummyna(sunan mahaifiyarta ne shisa bata fadar sunanta).

            " murmushi ta danyi tace nice ammi.lale marhabin da uwata zauna ga darduma nan mana kin tsaya kamar bakuwa ammi ta fada tana komawa kitchen din,,satar kallonshi tayi taga ya hade girar sama da ta qasa baki ta ta6e.ta samu bakin dardumar ta zauna a dofane,,yah sayyadi ina yini??,tamkar ba dashi take ba,,wae auta kana ji ana gaisheka kayi shiru nifa halin miskilancin nan naka ne yake hadani dakai muryar ammi suka jiyo tana fada...ammi na amsa fa ya fada kamar wani karamin yaro,,baki ta ta6e cikin ranta tace waishi bai yadda ba dan auta sai anje makaranta ya iya mugunta,,ammi ce ta fito daga kitchen itama ta zauna suka gaisa ,sama2 suke hira da ammin dan duk a takure take saboda abdallah dake wajen..,plate din fruit din ammi ta jawo daga gefenshi ta dawo dashi gaban humaira, ummyna ga fruit nan maza kisha..murmushi tayi tace ammi na koshi.6ata rai ammi tayi tace "a'ah ban yarda ba meyasa baki son sakewa agidan nan ne ?, maza kisha a kunyace taja plate din gabanta dai2 lokacin suka hada ido da abdallah shima ya d'ago daga duba littafin da yake harara ya watsa mata yadda ammi ba zata lura ba da sauri tayi qasa da kanta..,siririn tsaki yaja tare da miqewa ya dau key din machine dinsa,,kallo ammi ta bishi dashi kafin tace " kai kuma fa lpyr ka kake tsaki kai kadai??, kanshi ya dan sosa da key din yace ba komi ammi.., baki ta ta6e tare da juyowa gurin humaira. gurin machine dinshi ya nufa dake kafe a jikin bango yace ammi zan dan fita toh saika dawo Allah y kiyaye daga haka ya fice daga gidan.



Sai daf da Maghreb sannan ammi ta bar humaira tafiya, bayan ta hada mata kayan kwalliya godiya tayi sosai,,tana qara jin matar cikin ranta don tana sonta sosai Allah y hada jininsu tun tana karamar ta.


           ''Tana bude kofar zata fita shi kuma yazo shiga akan machine saura kadan ya bugeta,,har ledar hannunta ta fadi qasa kayan ciki suka zube,a fusace yake kallonta yana harararta yace' makauniyar ina ce ke??da kina kallon mutum bazaki bashi hanya ba?...baki ta tura gaba cikin kunkuni tace ni da kaso bigewa bance maka makaho ba sai kai??..me kikace ?,ya fada yana watsa mata wani irin kallo.tsugunawa tayi ta fara kwashe kayan tare da cewa ni ba abinda nace,,kwata yayi tare da jijjiga kanshi ya shige cikin gidan. mutum sai baqin halin tsiya sauka tayi daga kan dandamalin kofar gidan ta nufi hanyar gida.

 *??NIDA YAH SAYYADINMU??*


_By_

*Ummu Hanan*



<<<4>>>



*D* a sallama ammi ta shiga dakin abdallah dan ganin bai fito yadda ya saba fitowa ba.

"Subhanallah"!
Ta furta tare da qarasawa gurinshi da sauri ,kwance yake ya riqe cikin shi sai faman juye2 yake, lpy autana meya sameka ta fada tana riqoshi..,da kyar ya furta Kalmar ammi cikina zan mutu,sannu ta shiga jero masa tare da tofa masa adduo'e wani irin dogon salati yaja tare da mimmiqewa arude ammi ta sakeshi ta fito da gudu tana jan Kalmar

" inna lillahi wa inna ilaihi raji'un''

Dai2, lokacin yaya Yusuf ya shigo gidan yana ganin ta yasan ba lpy ba. Ammi lpy?? ya tambaya,,abdallah, abdallah haka kawai ta iya fada tana nuna dakin abdallahn,, cikin hanzari ya shiga dakin ta rufa masa baya,gabanshi ya durkusa ya dago shi yana kiran sunanshi amma ba amsa..ammi dauko mayafi mu kaishi asibiti yaya Yusuf ya fada cikin damuwa..,da sauri ta fito ta shiga dakinta ta dauko hijab ta saka ta fito.

Kamashi suka yi suka sashi a motar yaya Yusuf din ta rufe gidan suka tafi..



***Wani asibiti dake kusa dasu sukaje nan da nan aka bashi gado likitoci suka rufa kanshi dan ceto rayuwarshi".


Ammi da yaya Yusuf kuwa sun kasa tsaye sun kasa zaune gani suke kamar zasu rasashi,,yaya Yusuf ne ya kira Abba ya sanar dashi tare da fada masa asibitin da suke,.

Ba'a dau dogon lokaci ba Abba ya iso nan shima ya tsaya suna jiran fitowar likitocin yana qara kwantarwa da ammi hankali..



**Saida aka dade sannan babban likitan Dr suraj ya fito da sauri suka tareshi suna tambayar jikinshi... Hanky dinshi ya dauko daga aljihunsa ya goge gumin fuskarshi sannan yace.

"Alhamdulillah"!!

Mun samu ya farfado ynz yana barci coz allurar da mukayi masa but Ku biyoni office akwai mgnr da zanyi daku gaba yayi suka bishi jikinsu a sanyaye.


Da'ya bayan da'ya ya kallesu kafin yace.
" ga dukkan alamu yaronku bashi da aure ko??...kallon juna sukayi kafin Abba yace.

     "Eh!
" Dr bashi da aure .
Kai ya kada yace ok binciken da mukayi masa ya nuna mana danku yana tsananin buqatar mace kusa dashi urgently dan haka sai kusan abinyi.. Toh Dr mun gode sosai kuma insha Allah zamu san abinyi Abba ya fada yana miqa masa hannu sukayi musabiha.

Sai dare aka sallamesu bayan an rubuta masa magunguna,, yini da'ya amma kamar wanda yayi wata a kwance saboda ramar da yayi..har lokacin ba'a fada masa dalilin ciwon cikin nashi ba.



_After two dyz_

*Wai nikam halima akwai wadda Abdullahi yake so ne??, kayya dai abbansu ni ban ta6a jin ko ganin yace yana son wata ba.

Ajiyar numfashi yayi yace toh shikenan zan san abinyi game da al_amarin.


A kasuwa Abba yake sanar da baba kabeer rashin lpyr abdallah da kuma abinda Dr yace. ya qarasa mgnr da fadin ni ynz bansan yarinyar da zan hadashi da ita ba munyi mgn da amminsu tace bashi da budurwa.

Murmushi baba yayi yace.
"Indai dan wannan ne ta kwana gidan sauqi mai zai hana mu aura mashi humaira kawai... Baki Abba ya bude cike da jin dadin mgnr abokin nashi ,kai alhmdllh Masha Allah wlh nayi matuqar farin ciki nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunchi,, ameen ameen amma dan Allah ka daina min godiya kai ma fa kana da ikon da zaka aurar da ita ga ko waye bare kuma da'na Abdullahi fatanmu Allah ya basu zaman lpy mai dorewa ameen...daga nan suka cigaba da tattauna al'amarin.



A ranar ya fadawa ammi yadda sukayi da baba sosai tayi murna ta godewa Allah daya cika mata burinta dan dama ta dade tana addu'ar hakan sai gashi Allah y amsa addu'arta..

6angaren baba ma ya sanar da umma hukunchin da suka yanke itama din dai addu" ar tayi musu tare da fatan alkhairi a zaman nasu..
Sai dai can kasan ranta tana tunanin artabun da za'a sha da humaira sanin yadda sam basu jituwa da abdallahn.


Tsitt ajin yake kasancewar yah sayyadi abdallah ne a ajin yana zaune kan kujera sanye yake cikin wani farin yadi mai laushi ya saka farar hula data qara fito da ainahin kyawunsa,,dake daukar hankalin mutane,karatu ya gama biya musu sai ya fara musu tafseer din wasu daga ayoyin daya biya musu",humaira dake can karshen ajin jikin Bango ta sunkuyar da kanta sai surutu takewa fatima tayi banza da Ita saboda tsoron yah sayyadi abdallahn.., qasa2 yake jin surutu ya rasa daga ina yake dakatawa yayi da bayanin da yake yace.
        "Waye mai mana surutu??.. tana jin haka tayi shiru,tsayin mintina uku ya dauka sannan ya cigaba da bayaninshi tana ganin haka ta cigaba da mgnr da take..jin an cigaba da surutun ne yasa ya d'ago kai ai kuwa idanunshi suka suka kan humaira data daddage take ta faman zuba..,jijjiga kanshi yayi ya cigaba da abinda yake Ita kam bata ma san ya ganta ba,sai daya gama yana shirin fita yace humaira kabeer ta biyoshi yana fadin haka ya fice yana tunanin irin hukunchin dazai mata tunda kunnen qashi gareta,,to me nayi kuma dazai kirani?, ta fada tana wani yayyatsina fuska..surutu ya ganki kina yi fatima ta bata amsa,baki ta ta6e tace 
" ba wani surutu muguntarshi ce dai ta motsa,ta shuri takalminta ta fita,Allah ya shirya ki humaira fatima ta fada tana binta da kallo.


Can ta hangoshi kasan itaciyar dalbejiya a zaune,, sallama tayi ta durqusa tace gani.sai daya 6ata lokaci sannan yace "kije office ki dauko tsintsiya baki a dane ta tashi ta dauko ta dawo daga inda yake zuwa can nesa dasu ya nuna mata yace ta shareshi..


_*Mrs salees mu'az*_

*??NIDA YAH SAYYADINMU??*

_By_

*Ummu Hanan*


<<<5>>>


***Duban inda ya nuna mata tayi taga da nisa sosai.. tsabar mugunta ko me zan share anan gurin? ta fada cikin ranta tare da tashi ta fara sharar.

          "Da kyar ta k'arasa sharar saboda kugunta da ya ri'qe,a wahalce ta dawo ta tsuguna gabanshi tace 
       " na gama'
'Maimaita'
Haka kawai yace ba tare da ya dago kanshi ba.Allah zai sakamin wlh ta fada cikin ranta,tana shirin yi masa magiya,,hannu ya daga mata alamun bai son wata mgn.
Tashi tayi kamar tayi kuka ta fara tisawa,,,tana yi tana dafe baya gami da hararar inda yake.shikam bai ma san tana yi ba.

Da kyar da kyar ta gama ta qaraso gabanshi, na gama tana ajiye tsintsiyar dago kai yayi ya watsa mata wani kallo fuskarshi ba alamun wasa yace "dauki ki qara yi batayi ba.

Na shiga uku ta fada tana zubewa a gabanshi tuni hawaye sun cika mata ido,,dan Allah yah sayyadi kayi haquri Allah bazan kara surutu ba.ido ya tsira mata na " yan wasu mintuna kafin yace mara kunyar karya kawai 6ace min da gani,,da sauri ta tashi wata siririyar qara ta saki saboda kugunta daya amsa,binta yayi da kallo yana jin haushin rashin maida hankali da takeyi wajen karatu karamin tsaki yaja ya maida kanshi qasa.


Wash Allah na humaira ta fada tana zama tare da dafe bayanta,tuni dariyar da fatima ke 6oyewa ta fito wata katuwar harara ta jefa mata tace ,"dama ai halinku da'ya dashi,,dariyar da take ta tsagaita tace Allah humaira ke kike jan abinda yah sayyadi abdallah ke miki rashin mutunci wa kika ga yana yiwa haka in ba ke ba..,kinga ni bana son doguwar mgn Allah zai saka min ba inda yake sauke muguntarshi inba kaina ba.


Ke kuma fa lpy?? umma ta tambayi humaira ganin yadda tana shigowa ta zube bisa dardumar da umman take,, wlh umma shara yah sayyadi abdallah ya sani kuma fa wajen ko datti babu saboda tsabar zalun......hannu umma tasa ta bige mata baki tace Abdullahin ne azzalumi ko?,saboda baki da ta ido baki ta turo tace Allah umma kinfi sonshi akaina,,eh nafi sonshi din tashi ki bani guri..tashi tayi da kyar kamar zatai kuka ta nufi dakinta.

Bayan ta umma tabi da kallo tana tunanin irin zaman da zasuyi Ajiyar zuciya ta sauke Allah dai ya basu zaman lpy ameen


_Asabar 8:24pm_

"Abba ne da iyalanshi gaba da'ya Zainab ce kawai babu,zaune suke a tsakar gida kan katuwar darduma.. Bayan wasa da dariya da sukayi tsakaninsu dan abba mutum ne mai faram2 ya maida " ya"yanshi kamar wasu abokanshi.

Zaman shi ya gyara tare da yin gyaran murya yace.
       "Mgn ce kan dan uwanku Abdullahi.gabanshi ne ya fadi cikin ranshi yana tunanin wace mgn ce za'ayi akanshi?? tunanin shi ne ya katse jin mgnr abba na cewa" ciwon cikin da yayi kwanaki Dr ya mana bayanin cewa yana da buqatar mace akusa dashi hakane??.. ya tambayi abdallah da  duk kunya ta gama kamashi kai amma likitocin nan da tonon silili suke ya fada cikin ranshi yana kara yin qasa da kanshi,,ko ba haka bane ?? abba ya sake jefo masa wata tambayar..,keya ya fara sosawa yace am...uhm..abba.murmushi abba yayi yace ya isa nasan gsky Dr ya fada dan haka nida babanku muka yanke shawarar hadaka aure da kanwarka humaira.... dam gabanshi ya fadi lokaci da'ya yana maimaita sunan humaira cikin ranshi ,sukam su yaya naseer fuskarsu ta washe da farin ciki da gani sunji dadin hadin ,dan haka suka fara jero adduo'en zaman lpy garesu,,shiru yayi kanshi a qasa ya rasa abinda ke masa dadi..ya kayi shiru ne yah sayyadi?? in yaso tsokanarshi haka yake ce masa.a marairaice ya dago kanshi yace.
     "Amma abba...dakata malam.. Yaya naseer ya katseshi dan akwai shi da zafi,,sun riga da sun yanke hukunchi kuma kai baka isa ka kawo mtsl ba....ya isa haka nasiru Abba ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu,ni nasan yah sayyadi bazai bani kunya ba in kuma da wadda kake so to sai ka fada min,shiru yayi ya rasa abin fada  dan shi bai ta6a soyayya ba,akwai dai wata dalibarshi daya so tun farkon fara koyarwarshi a islamiyyar yaji tayi masa saboda nutsuwarta itama kafin ya furta yaji labarin bikinta tun daga nan bai qara jin son wata cikin ranshi ba....da kai fa ake abdallah ya tsinkayi muryar ammi.... Uhm Abba ni ba wadda nake so..kai abba ya gyada yace.
" toh kayi haquri ka auri humaira insha Allah alkhairi ce a gareka,kuma zaka sota kaji??,shikenan Abba na amince ya fada muryarshi a sanyaye,, yawwa Allah yayi maka albarka yasa alkhairi cikin aurenku kaji?? dukansu suka amsa da ameen banda abdallah da yake jin tamkar yayi ta tsala ihu ko zasu fahimci yadda yake ji.
       "Toh ynz abbansu kun tsaida lokaci ne??,ammi ta tambayi Abba. kai ya daga sama alamun tunani yace,
" eh toh duka dai ai bazai wuce wata biyu ba,to Allah y nuna mana ameen...daga nan su yaya basheer suka yi musu sallama kowanne ya nufi gidan shi.

Shima din tashi yayi dan yadda yake ji yau ko hirar da suke dan ta6awa bazai iya ba.yau ba hirane??...Abba ya tambayeshi fuskarshi dauke da murmushi,, hannu yakai kan kwantaccen sajenshi yadan shafa yace "eh Abba zan danyi binciken wani hadith ne,,ok toh Allah y taimaka mu tashi lpy.... sallama yayi musu ya shige dakinsa....rijib ya zube bisa katifarshi da take a gyare tsaf tamkar ba'a kwanciya akai hannunshi duka biyun yasa ya dafe kanshi dake sara masa ya shiga tunani...da Abba yasan yadda basu jituwa da mara kunyar yarinyar nan da rashin jin mgn da bai yi tunanin hadasu aure ba wai ma ta yaya zai iya zaman aure da humaira??.... Toh ma da suke cewa sun aura masa ne saboda buqatar mace da yake yi ta ina zai iya kai lalurarshi ga humaira??, ta qara rainashi kenan kuma bayan haka ma tayi masa qanqanta dan a yadda yake jin qarfi zai iya karya ta ma,,wannan" yar tsigigiyar.,shawara da'ya ce mafita bayan auren nasu da dan wani lokaci sai ya qara wani auren duk da bashi da sha'awar aje mace fiye da da'ya amma ya zaiyi dole ya samu wadda zai dinga sauke buqatar shi amma ba dai humaira ba.

????
A 6angaren humaira kuwa ranar da aka fada mata cewar abdallah zata aura kamar tayi hauka kuka ta shiga rairawa harda shure2n kafafu saida umma ta dauko wayar redio sannan ta tashi da gudu ta shige dakinta tana rusa ihu da fadin ita wlh bazata auri wannan mugun ba..kwata umma tayi tace zakici gidan ku aure da Abdullahi ba fashi.


***Nan da nan zancen auren abdallah da humaira ya karade kunnuwan "yan uwa da abokan arziqi hakama mutanen unguwa,,shirye2 aka shiga yi ba kama hannun yaro.ta 6angaren ango da amarya kuwa abin ba dadi musamman humaira saida baba yayi mata da gsk kafin ta haqura saidai kullum cikin kunci take,,duk ta qara ramewa dama ba jikin kirki ba umma har tayi rarrashin ta gaji ta watsar da lamarinta.kullum tana daki dan sun samu hutun islamiyya da boko shi yasa ma basu haduwa da abdallahn.


Da sallama ya shiga dakin ammin tasu ya tarar Zainab tazo ,amsa masa sukayi ya qarasa shiga,, ya zauna, suka gaisa da Zainab,, ammi tace " ka dawo??"eh" ammi Allah yasa da abinci wlh yunwa nakeji,,akwai abinci Zainab zubo masa..,toh ammi ta fada tana shimfide yaronta ammar dan wata hudu kan kujera ta fita ,kallon ammi yayi kamar zaiyi mgn kuma ya fasa ta lura da hakan yasa tace 'yadai? naga bakinka na motsi koda mgn ne??...marairaicewa yayi yadda zata fi tausaya masa yace,

"Kan mgnr auren nan ce ,zaman ta ta gyara tace 'uhum ina jinka wani abune ya faru??...ammi dan Allah... Shiru yayi yana sosa kai.fadi mana...ammi dan Allah a fasa auren nan, tuni fuskar ammi ta tamke ta fara watsa masa wani irin kallo,, daurewa yayi ya cigaba, ammi tayi yarinya da yawa wlh... Kuma.. Kuma bata da...kunya,, ka gama??...nace ka gama??..ammi ta tambaya tana harararshi, kai ka kiyayeni wlh bana son sakarci da rashin hankali mgn tayi nisa shine kakeso ka maida hannun agogo baya...dai dai nan Zainab ta shigo hannun ta dauke da plate tuwon semo ne ciki sai dayan hannun wani karamin kwano ne da miyar busasshiyar ku6ewa da taji nama sai kamshin man shanu ke tashi,ta ajiye a gabanshi ta koma inda ta tashi ta zauna jin irin fadan da ammi keyi yasa ta fuskanchi kan mgnr kallon shi tayi tace " ni wlh abdallah banga aibun humaira ba kodan ka ganta baka bafa finta kyau kayi ba farar fata kawai zaka nuna mata..rabu dashi ko meye dai aure babu fashi da kake cewa wani yarinya to ko jaririyace karewar yarinta sai ka aureta wlh ka qara zuwa min da mgn makamanciyar wannan idan ranka yayi dubu sai ya 6aci,,nan ammi ta shiga caccakarsa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba har sai da yayi dana sanin furta mgnr,, miqewa yayi da shirin fita ,wa ka barwa abincin??..na qoshi ya fada kamar zaiyi kuka ,koma ka zauna ammi ta fada tana nuna masa inda ya tashi..ba musu ya koma ya zauna.., maza ka dauka kaci kafin in sa6a maka..tura abincin kawai yake yana kallon ammi dan duk yunwar daya kwaso sai yaji ya koshi.sai daya cinye tas sannan ta kyaleshi har yakai bakin kofa ta sake kiranshi ya dawo.. Anjima da daddare saika je ku gaisa da ummyna din ko?? to kawai yace ya juya ya fita yana jin kamar ya hadiyi heart ya mutu.

_*Da dare*_

Bayan sallahr Maghreb yana daki a kwance yana aikin tunani ammi ta leqo tace,
         "Wai me nace maka daangwancin ga baka da niyyar shiryawa,,kafin yayi mgn ta saki labulen ta tafi...ranshi a jagule ya tashi ya shirya cikin shadda grey color da hula kalar kayan
" Masha Allah "
Kyau dai Ba'a mgn sai kyalli yake kamar ranar angwancin sassanyan turarenshi mai dadin kamshi ya fesa ya fito yayiwa ammi sallama ya fice sai faman cewa take ya gaida mata da ummynta.

Ku biyoni


_*Mrs salees mu'az*_

*?NIDA YAH SAYYADINMU*?


_By_

*Ummu Hanan*


<<<6>>>


_*Happy sallah 2 oll Muslims Allah yasa ibadunmu kar6a66iya ce yasa muna cikin yantattun bayinsa ameen s ameen*_


***Kamar yadda ya saba shiga kai tsaye in yazo gidan haka yauma ya shiga tare da sallama,,,umma ta fito tana amsa sallamar.murmushi tayi tace "a'ah Abdullahi ne a gidan?.. Kai ya dan sunkuyar yana shafa lallausar sumarshi yace " eh wlh umma nine.,dakin suka shiga suka gaisa suka dan ta6a hira kafin daga bisani ta miqo masa key tace,
        'Amshi nan ka bude dakin bakin babanku ka shiga bari in turo maka ita hannu biyu yasa ya amsa sannan yayi mata sallama ya fice ranshi sai suya yake ganin wai yau shine yazo zance wajen wnn yarinyar.

Tashi kije Abdullahi yazo yana jiran ki, umma ta fada tana yaye labulen dakin,,humaira dake kwance tana ta faman tunani tun bayan idar da sallahr Maghreb ta juyo ta dubi umma kamar zatayi kuka tace'umma kaina fa ke ciwo..haka nan zaki haquri kije tunda yazo kinji daure autar umma..ni wlh Allah wnn yah... Ke bana son diban albarka kinji ko dan kinga ina rarrashinki kin tashi kin wuce ko kuwa??...umma ta fada cikin 6acin rai,tuni hawaye suka cika mata idanunta.. tashi tayi ta fito ta shuri takalminta data ke sawa a tsakar gida tayi hanyar fita tana share hawaye,kai umma ta girgiza tace "Allah ya shirya min ke humaira.


**Saida ta gama hararar dakin tamkar shine mai laifin sannan ta shiga tare da yin sallama a daqile,shima din can qasan makoshi ya amsa mata kanshi na qasa yana latsa waya ,nesa dashi ta zauna kamar mai koyon zaman.. ina yini?...ta fada tana tuttura baki gaba..sai daya dan dau lokaci kafin yace lpy, daga haka ba wanda ya qara cewa wani abu.....shiru dakin ya dauka kowanne da abinda yake tunani,kuma har lokacin bai dago ya kalleta ba ita dinma juyar da kanta tayi gefe,,....sai ynz kika ga damar fitowa??...saida ta dan harari gefen da yake,nan dai ai ba islamiyya bace bare kace na makara,,ta fada cikin qunquni..sai a lokacin ya dago kanshi dan sarai yaji abinda ta fada. kai ya kada cikin zuciyarshi yace zanyi maganinki ne...numfashi ya sauke yace" am ba saina 6ata bakina wajen fada miki bana sonki ba kinsan hakan saboda haka saiki daura niyyar zama da abdallah mugu azzalumi kamar yadda kike fada baki ta ta6e cikin ranta tace to ba gaskiya bane kai ba mugun bane?,,tashi yayi ya fita ba tare da ya sake mgn ba dan a yadda take fitsararriyar nan idan ya cigaba da zama a gurin ba karamin aikinshi bane taci na jaki.
"Tsaki tayi ta fito tana mitar sai kace ce masa akayi nidin sonshi nake ,ragowar shawara dakai..a haka ta rufe dakin ta shiga gida, a tsakar gida ta samu umma... har ya tafine??,umma ta tambayeta,,
" eh"
ba dai wani abin kikayi masa ba ko??...umma ta sake jefo wata tambayar.., to ni umma dan Allah me zan masa ta fada cikin muryar shagwa6a.kai umma ta kada tace "nasan halinki ne ai"

Shirye2 suna ta kankama tsakanin gidajen biyu,sai dai amarya da ango kamar ba bikinsu za'ayi ba,,.


Humaira! Humaira!! "Na'am umma'

Sallama tayi ta shigo dakin umman tana daura dankwali kofin dake hannunta ta mika mata tace maza kafa kai ki shanye ki bani kofin,,kar6a tayi ta leqa taga an dama wani abu da madara,,umma menene wnn din??magani ne shanye ki ban kofin umma naga ni lpy ta.....ke bana son surutu maza kisha baki ta kai ta dandana da sauri ta dauke kanta daga kofin tana yamutsa fuska saboda rashin dadinshi....a takaice dai saida umma tayi mata da gsk sannan ta sha da sauri ta fita taje bakin famfo ta dinga wanke bakinta

*?NIDA YAH SAYYADINMU*?

_By_

*Ummu Hanan*

_Kyautar shafi ga "yan Ummyn Yusrah novel group gaba dayanku ina maku fatan alkhairi Allah ya bar zumunchi da kaunar juna❤❤_


<<<7>>>


Yau alhamis yinin gidan aunty asiya humaira tayi tun wuri taje gidan,,, suna zaune tsakar gida tana gyara mata alayyahu,,suna ta6a hira, mikewa aunty asiya tayi ta shiga kitchen bata jima ba ta fito hannun ta dauke da karamin kofi ta miqawa humaira,, baki ta turo dan tasan bazai wuce irin abinda umma ke banka mata ba..waini aunty asiya meye wnn dan Allah haka fa umma kusan kullum sai ta sani a gaba nasha ,rannan ma fa da aunty hassana tazo ta kara kawo mata wasu da yawa ni wlh na gaji,aunty asiya data kura mata ido tace,
" toh sarkin surutu kin kar6a kinsha ko kuwa kinsan dai bazamu baki abinda zai cutar dake ba ko??...to ai ba da'di ta fada cikin shagwa6a, tare da kar6ar kofin, hannu tasa tadan dangwalo ta dandana ji tayi ya bambamta dana wajen umma dan wnn zaki gareshi ga abin aya da dabino da mazarkwaila,ai nan da nan ta kafa kai ta shanye shi tas ,data shanye dinma bata barshi ba sai data sa hannu ta dinga kalato ragowar na kofin tana fadin "kai wlh aunty asiya naki yafi na umma da'di,akwai wani??...hararar ta aunty asiya tayi tace,
" uwar kwad'ayi kawai kedai indai gurin zaki ne shaxumamu ma haka ya barki ,dariya tayi ta ajiye kofin ta cigaba da yankan alayyahun.


Yana kwance bayan asr dan yau da wuri ya dawo daga kasuwa, tunani yake yaufa duka baifi saura sati uku bikin nan ba,da sauri yasa hannu ya dafe mararsa data wani tsira masa kwanan nan kamar kara masa wata natsananciyar sha'awa ake,,jin bata da niyyar dainawa yasa ya fito a daddafe ya shiga kitchen, cikin sa'a ya hangi lemon tsami,,bai tsaya 6ata lokaci ba ya matseshi da dan ruwa kadan ya koma daki har lokacin ammi tana daki ,,,"
Sallamar Hashim ne abokin abdallah ta fito da ita har qasa ya tsuguna ya gaisheta ta amsa cikin fara'a,kaci sa'a kuwa dan bai da'de da dawowa ba...ammi ta fada tana juyawa dakinta,,.

Salamu alaikum ango Hashim ya fada cike da tsokana yana shiga dakin,,harara ya fara jefa masa kafin ya amsa masa,. ango kasha kamshi me ake sha ne??...ya fada yana leqa kofin hannun shi,baki ya dafe tare da sakin wata shegiyar dariya, yace,,"kace jarabar ce ta motsa??...a fusace abdallah yace "dallah malam kar ka dameni waima uban me ya kawoka bayan bamu da'de da rabuwa ba??....,murmushi Hashim yayi ya zauna yace" ayya sorry abokina zuwa nayi mu tattauna game da bikin ,sai kuma na tarar abin ya tashi Allah dai ya kusa yanke maka,,,ni wlh har na fara tausayawa humaira,, wani banzan kallo yayi masa yace, "dame kake tausaya mata?, ah kaima ka sani ai duk macen daka aura ai ta kade har ganyenta wlh wnn jarabar taka,gata yarinya karama dan Allah ka dinga tausaya mata....wani dogon tsaki yaja tare da galla masa harara yace,banza ni me zanyi da wnn yarinyar?, ai ni me iya min sai mace ta isa wnn tsaf zan iya 6allata..ta6e baki Hashim yayi yace sai kace gaske lokacin da zakaje kana " yar murya waya sani haushi ne ya isheshi wai zaije yana yi mata karamar murya dan haka bai kara tanka masa ba. Ammi ce ta leqo tace,"suzo suyo mata cefane almajirin da keyi mata baizo ba, tashi sukayi suka fito ta fada musu abinda zasu siyo mata suka fita.



Ranar Asabar aka kai lefe yayi kyau sosai, yaya basheer ne ya hada masa akwati hudu da karamar jaka.

*?NIDA YAH SAYYADINMU*?


_By_


*Ummu Hanan*


<<<8>>>



Su aunty hassana ne suka za6ar mata wadanda zata dinka,,ranar saida Tasha kuka da daddare dan sam ta tsani yah abdallah jininsu bai hadu ba.


Biki yana ta matsowa baifi saura kwana goma ba,Abba ya bawa abdallah wani gidan shi tsakaninsu ba wani nisa,,karamin gida ne mai dauke da falo sai bedroom guda biyu sai kitchen da bandaki a waje da store,,"gidan yayi kyau ba laifi yasha gyara sai kamshin sabon fenti yake da sumunti,ana sati da'ya biki akaje akayi jere shima baba yayi kokari sosai yayi mata kaya masu kyau..... Falon yaci saitin kujeru,sai kayan kallo da dan karamin frige ,an shimfida center carpet a tsakiyar falon,Masha Allah komi yayi kyau, sai bedroom din guda da'ya aka jera gado da wardrobe da mirror da yake dakin da girmanshi ya cinye komi a wadace,kitchen ma da yake an buga kanta,anyi mata jerenta mai kyau komi dai yayi cikin rufin asiri saidai fatan zaman lpy ga ma'auratan,



Wae kuwa kaje kun tattauna da ummyna kan bikinnan??...ammi ta tambayi abdallah dake kwance kan doguwar kujera a dakinta yana danna waya ,shiru yayi ya rasa abinda zaice, ba da abdallah nake ba??...ta fada tana masa kallon tuhuma, eh ammi....ai zan...zanje,ya fada cikin in ina yana shafa kwantaccen sajenshi..,wai abdallah me yake samunka ne,? ynz badan nayi maka mgnr ba kilan bazaka jeba,wlh ka shiga hankalin ka tun kafin raina ya 6aci inyi maka abinda baka tsammani,zuwan farko ma saida nayi maka mgn saboda kai baka san abinda ya dace ba ko??...to yau din nan kaje kaji abinda take buqata na biki,in ba haka ba kuma wlh tamu ce dakai,kaji na fada maka,tashi tayi ta shige daki ,tana ta mita,,,,

Wayar ya ajiye kan cikin sa tare da lumshe idanu,..gaba da'ya ammin tashi ta canza masa akan wnn fitsararriyar yarinyar..mtss an kusa yin auren dai kowa ya huta kafin nima in nemo wadda nike so ya fada cikin ranshi yana miqewa tsaye,ya fice daga gidan..


Da daddare yaje gidan,ranar ma baa wanye lpy ba gurin zancen?,daya tambayeta abinda zatayi da bikin kai tsaye tace ai auren so ne akewa hidima ita ba abinda zatayi,, kudin daya bata tace bata so wurga mata yayi ya fice daga dakin yana fadin ta konasu ko ta zubar..wata muguwar harara tabi bayan shi da ita harda murguda baki ta dauki kudin ta shiga gida,,kai tsaye dakin umma ta shiga ta miqa mata kudin ,na menene?umma ta tambaya,, baki a dane ,tace,
"Bani yayi wai in da abinda zanyi, kar6a umma tayi tace to me zakuyi keda kawayenki??,nifa ba abinda zanyi umma,, ban gane ba abinda zakiyi ba??to umma ni me zanyi??... Kada Allah yasa kiyi,fice ki bani guri.



Toh duk abinda aka sawa rana to komi daren dadewa yana nan tafe ,yau ake kamun humaira gidan aunty ramla anan akayi kamun dan yafi kusa dasu sosai,, amarya humaira taci kwalliya,tayi kyau sosai saidai fuskar nan a cukule kadan take jira kamun ma saida aunty asiya taci mata dan da farko cewa tayi ba inda zataje fatima taje ta fadawa aunty asiya,, anyi lpy an tashi lpy.

Washegari akayi walima a wani kangon baba da bai dade da siyaba aka gyara shi sosai..malamai mata biyu su suka wa'azantar tare da fadakarwa kan zamantakewar aure,bayan an gama ne aka rarraba abubuwan da aka tanada na rabo....



Ana gobe daurin aure saqo yazo musu islamiyyar su ta hadawa ango da amarya wata walimar.


Cike filin makarantar yake da mutane,wajen maza daban mata ma daban,sai gefen hagu humaira ce da kawayenta sai daga gefen dama kuma abdallah ne da abokanshi,,sanye yake cikin shadda light ash color da hula kalar kayan sai farin space daya saka hakan ya kara fidda kyawunsa,ita kam sanye take cikin atampa sai akayi sa'a kalar atampar yazo da'ya da shaddarshi,,da kuma hijab din data saka fatima ce takai bakinta kusa da kunnen humaira tace,"kai kawata wlh ba karamin dacewa kukayi da yah sayyadi abdallah ba,ashe duk fadan nan da akeyi na luv ne,, tsaki taja tace a'ah na uban luv ne, dai2 nan suka hada ido dashi saqon harara ya aika mata dashi, ai kuwa batai kasa a gwiwa ba ta maida masa harda murguda baki,, kai ya kada alamun zata sani,,in ka kamani ka kasheni abinda yayi hasashen ta fada kenan.da haka taro ya tashi lpy.

*?NIDA YAH SAYYADINMU*?


_By_


*Ummu Hanan*



<<<9>>>


_*Ina mai miqa saqon gaisuwa da fatan alkhairi ga duk wani masoyin novel din NIDA YAH SAYYADINMU, haqiqa ina matukar jin dadin yadda kuke nuna min kauna nagode sosai Allah y bar zumunchi,, ina yinku irin sosai din nan❤ humaira da yah sayyadi abdallah na miqo gaisuwa?.*_



***A ranar da daddare aunty asiya, aunty ramla da aunty hassana da hussaina suka tasa humaira a gaba danyi mata fada dan sun san halin "yar kanwar tasu...aunty asiya ce ta fara mgn da fadin Dan Allah humaira ki nutsu ki sani bauta zakije kiyi,kar kiyi abinda zai jawo matsala a zamantakewar auren ki....nifa wlh ba sonshi nake ba,yayi harkarshi inyi tawa,humaira ta katse aunty asiya daga fadan data fara yi mata tana turo dan mitsitsin bakin ta mai kama da gidan tsutsa,,,,kinga irin halin nata ko??...aunty ramla ta fada tana nuna humaira da hannun ta tare da kallon aunty asiya,, murmushi aunty asiya tayi ta ka'ra kwantar da murya tace,
"Haba mana autar umma kiyi haquri wata rana zaki ji kina sonshi sosai,, kefa kamata yayi ki godewa Allah mata nawa ne suke neman irin abdallah saboda haduwarsa ke kuwa Allah ya kashe ya baki,dan haka kar kiyi wasa da damarki kinji ko aishatul humaira?? ta karasa mgnr cike da rarrashi,kai ta da'ga tace ," to shima wlh ayi masa fada,ya daina mugunta. dariya suka sa gaba dayansu dan yadda tayi mgnr tsakaninta da Allah,eh ammi zatayi masa ai aunty hussaina ta fada tana kokarin maida dariyar ta,nan dai suka hadu suka dinga bata shawarwari wadda taji ba tayi mata ba kuwa sai tayi mgn.a haka dai suka gama... Aunty hassana ta janyo food flask din kusa da ita ta tura gaban humaira budewa tayi ta fa farfesun kaza ,sai kamshi yake...dariya tayi tace "wlh aunty hassana kamar kinsan yunwa nakeji, cinya ta dauko takai bakinta ai da sauri ta cire tana yamutsa fuska.. yana ji da'ci ta tambayesu tana maida naman cikin flask din..... da kyar suka samu taci ta shanye romon,tana faman yatsina.






" Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya inji masu karin mgn, domin kuwa yau lahadi mutane da dama suka shaida daurin auren _*abdallah*_ da _*humaira*_ akan sadaki naira dubu ashirin,can na hangi ango yana gaggaisawa da jama'a fuskar nan ba yabo ba fallasa,sanye cikin farar shadda "yar ciki da malum2 ba karamin amsarsa kayan sukayi ba,jinshi yake tamkar ba shiba wai auren shi aka daura da humaira.



A ranar gidaje biyun sukayi yini inda da daddare za'a miqa amarya gidan ta.



_*Bayan sallahr esha'e*_


Amarya na hango lullu6e da mayafi sai uban kuka take an shiga da ita dakin baba dan yayi mata nasiha,sosai baba yayi mata fada tare da sa mata albarka.daga nan gurin umma aka nufa da ita tayi mata nata nasihar tare da fatan alkhairi... Gurin fita da ita kuwa saida tasa wasu da dama kuka dan ri'qe umma tayi gam tana 6urari ita kanta umman saida tayi kwalla..da kyar aka jata aka fita da ita sai gidan *Ya sayyadi*,ko wani irin zama kuma za'a yi??.



" Yan kai amarya duk an watse daga Ita sai kawayenta fatima,sadiya,hafsat,sai kuma hauwa.har lokacin bata daina kuka ba muryar ta har ta fara dashewa,fatima ce ta gaji da jin kukan tace, "dan Allah humaira kiyi haquri kiyi shiru haka nan haba ai saiki jawa kanki ciwon kai,kiyiwa yah sayyadi abdallah asarar wnn daren ,dariya suka saki tare da tafawa...suka cigaba da hirarrakinsu dai na " yamnmatan amarya tana jinsu tayi musu banza hafsat harda cewa dan Allah banda gardama ta bada hadin kai,sai a lokacin ta yaye mayafinta cikin dashewar murya tace, "kin manta hadin baki zan bayar ko na hanci," yan iska kawai,,, dariya suka kara sheqewa da Ita hauwa tace, "suma din ai duk daya.




Durkushe abdallah yake gaban Abba da ammi nasiha suke masa mai ratsa jiki,duk jikinshi yayi sanyi.su yaya naseer ma baa barsu a baya ba kowa saida yayi masa nasiha.sannan suka sallameshi ya fita inda abokanshi ke jiranshi danyi masa rakiya,dama tuni kayan dakin shi aka kaisu gidan aka sa a dayan bedroom din,


Sallamar angwaye ce tasasu dakatawa da hirar da suke,amsawa suka yi sannan kowa ya nemi gurin zama,,, bayan an gaggaisa akayi dan barkwanci sannan abokan kowa ya tofa albarkacin bakinshi,,,,"daga nan aka sayi baki,ango dai banda ta6e baki ba abinda yake,sallama sukayi musu suka fita,nan ta kara sakin wani kukan,,"

Hashim ne yaja abdallah gefe yace,"toh ango mu zamu fece Dan Allah kabi musu yarinya a hankali kaga dai karama ce,dan nasan yadda kake a hannun nan zaka iya aika2..tsaki yaja tare da 6alla masa harara yace "banzakaine maye,,Allah ko shi yasa naga anyi maka aure ba shiri ko??,,tsaki ya kara ja yayi wa sauran sallama ya shige gida dan in ya biyewa Hashim zai 6ata masa lokaci ne shikam a gajiye yake dan Hashim akwai" yar banzar tsokana.


Yasin na gaji?



Yawan comments yawan pages dan shi ke kara karfafa mana gwiwar yin typing.


_*Mrs salees mu'az*_
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 24,277 06-12-2019, 12:04 AM
Last Post: Gimbiya
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 14,082 06-09-2019, 02:37 PM
Last Post: Gimbiya
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 39,805 06-09-2019, 02:22 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 32,473 07-16-2018, 03:34 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 79,251 06-28-2018, 10:16 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)