Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
GAMSARDA MIJINKI TAHANYAR JIMA'I
#1
Gamsar da namiji a jima’ince yafi sauki wajen gamsar da mace, duk kuwa

da cewa dukkannin halittan da aka yiwa mace a jima’ince suma maza suna
da irinsa. Kamar yadda ake samun harijin namiji haka nan ma
ake samu harijan mace, yadda ake samu mazan da suke jimawa babu gajiya
a lokacin jima’i hakama matan. Ana samun maza da mata ragwaye a wajen
jima’i da kuma wadanda sam jima’in ma bata damesu ba a dukkannin
jinsunan biyu.
Da akwai wasu mazan da basu cika son doguwar wasannin motsa sha’awa
ba, wasu kuwa suna bukatan lokaci maitsawo ana masu wasa duk kuwa da
macen tafi namiji bukatar wasan motsa sha’awa mai tsawo.
Abu na farko daya kamata mace ta fahimta a tattare da mijinta shine
abunda yafi bukata a yayi wasannin motsa sha’awa da kuma lokacin
kwanciya irin na jima’i, domin da akwai inda da zaran mace ta tabawa
mijinta maimakon ta motsa mishi sha’awarsa sai kawai sha’awar tashi ya
gushe. Hakama a kwanciyar jima’i, yana da kyau ki fahimci irin yanayin
kwanciyar da mijinki yake so. Shi yasa malamai na jima’i sukecewa
sadarwa a jima’i yanada matukar alfanu ga ma’aurata domin ta hanyarce
zasu iya fihimtar abubuwan da suke bukata a yi musu kamin, lokaci da
kuma bayan jima’i.
Da akwai mazan da zaran mace ta fara wasa dasu nan da nan suke gamsuwa
ba tareda sun shegetaba, da akwai wadanda da zaran azzakarinsu ya
shiga shikenen kuma sunyi zuwan kai kenan. A akwai mazan da sukan
dauki lokacin mai tsawo suna jima’i da mace kamin suyi zuwan kai, wasu
mazan kuwa a lokacin da suke kawowa a lokacin ne gabansu ke kara yin
karfi har sai sun kawo sama da biyu koma biyar kamin suke gamsuwa da
mace. Ke naki mijin yaya yake, domin dole sai kin fahimci yadda yake
kamin ki iya gamsar dashi. Sai dai maza masu wuyan sha’ani a jerin mazan da na ambata sune masu saurin 

zuwan kai da kuma masu daukan lokaci mai tsawo suna gurza mace basu gamsu ba, sai dai kuma da zaran mace ta samun illimin sarrafa
irin wadannan maza ta gama dasu. Maza masu saurin zuwan kai sune mazan da sukafi cutar da matansu, domin wata matan sai ta gurzu
take gamsuwa, don haka matsalar irrin wannan mazan yana tattare ne da
kodai suna da cuta da suke bukatar ganin likita, ko kuma sabbin shiga ne wato mazan da suka yi aure sabo-sabo ko suka jima basu yi jima’i ba
hakan na faruwa da su.
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA
08080678100
MENENE BUDURCI???
????????????????????????wata fata ce
dakecikin farjin mace mata shi kuma
fatar ba mai kwari bace sannan tana
yagewa ne da zarar ta samu takura
MACE TANA RASA BUDURCINTA NE
TA WADANNAN HANYOYIN:
-saduwa da namiji
-daukar kaya mai nauyi
-guje-guje
-hawan keke
-hawan doki ko jakki
-mummunar faduwa
-sanya dan yatsa a farji :wannan
kuma ya janyo mutuwar aure da yawa
saboda wannan aiki yana faruwa ga
yan'mata sosai
HAIHUWA: wasu matan ko an sadu
dasu fatar budurcinsu bata yagewa
harsai sun zo wajen haihuwa anan ne
zata yage
BUDURCIN YA'MACE NA DA
MATUKAR MUHIMMACI:
ta fuskar zaman takewa da kuma
al'ada: hakan ya sa wasu yan'matan
kan ke a yi musu tiyata domin maido
musu da budurcinsu kafin ranar aure:
 MURFIN BUDURCI murfin budurci
wani murfine da yake tsurowa a
saman farjin mace daidai kan kofar
farjinta yadda ya toshe dakkanin
yankin farji.
Wannan murfi ba nau'i daya bane,
yana da nau'o da yawa. Amma nau'in
da yafi yawa, shine wani murfi mai
huda-huda kewyayya a tsakiyarsa
mata
shi wannan murfi a lokacin da zai
yage wani digo digon jini yana
zubowa,kuma zai zama amarya zataji
zafi, amma zafin ba wani zafi bane na
azo a gani, ya kamata amarya ta jure
wannan dan zafi da zata ji. Amma
akwai wasu mata da nasu murfin ya
banbanta wanda shi lokacin fashewar
baya jini domin yana jawuwa kamar
roba ta yadda zakarin namiji zai iya
wucewa ba tare da ya yaye ba.kuma
baya digar jini bare radadi
akwai wani murfi da yake da ragaraga
kamar rariya, wanda yake fashewa
cikin sauki ba tare da wani zafi ko
radadi ba
takan yiwu,a haifi yariya ba tare da
kofa ko huji ba, a tsakiyar murfin
budurcin taba. Yariya mai irin
wannan murfin budurci, idan ta
balaga ta zo haila sai anyi mata aiki
domin jinin haila ya samu kofar
fitowa
shi murfin budurci bashi da wani
mahimmanci a wajen masana ilimin
halittar dan adam, muhimmancinsa
ya tsaya ne leawai wurin tantanece
yarinya budurci wani tuni ya kau da
budurcin
da fatan samari da yan'mata su gane
ADO: wani abu ne da yake girmama
matsayin dan dama duk lokacin daya
baiyana domin haka kasancewar sa
ga miji ko mace ya zama wajibi
musamman ga ma'aurata da suke
son su girmama zaman rayuwar
auransu cikin sha'awa da kauna
mace ya dace duk lokacin da aka ce
gari ya waye tayi iya kokarin ta bayan
ta kammala aikin gida ta yi wanka ta
shafa mai sannan ta sami kayanta
masu kyau tasa yin hakan shine ya
ke kiyaye mutuncita da kara mata
matsayi a wurin mijinta kuma hakan
na sanya miji ya rika sha'awar
kasancewa da ita ako yaushe. Hakika
ado baya bambanta tsakanin yariya
da matsakaiciyar mace matukar dai
bata haura shekarun kuruciyarta ba
domin ado yana mai da tsuhuwa
yariya haka kuma rashinsa ko kuma
rashin iya shi yana maida yariya
tsohuwa mara kyau a gani sannan
ado yana daya daga cikin abubuwan
da suke motsar da sha'awar jima'i in
na miji
     TUSHEN SAMUWAR JIMA'I
tushen samuwar jima'i shine aure
duk wani jima'i da mace da namiji
zasu yi in dai bata hanyar aure bana
ya zama haramun.
Aure shine ginshikin ginin iyali kuma
shine tubalin al'umma aure na da
tasiri babba wajen cigaban al'umma
kuma rashin sa yana kawo faduwar
al'umma da rashin cigabansu
aure a musulunci wani rukuni ne mai
tsarki wanda ake kulla shido min
samuwar ingantaccen zumuci
tsakanin ma'aurata
a cikin aure akwai hakkoki da
wajibobi wanda suke wajabta lada ko
azaba a gurin ubangiji (Sw) wannan
kulli mai tsarki lokacin da aka kulla
shi a karka shin dokoki da tsari
             ABIN LURA: 
a wasu lokuta murfin
budurci na tsagewa ko fashewa, ba
tare da zakari ya shiga farji mace ba,
hakan na faruwa ne idan budurwa ta
sami tsautsayi musamman garin
hawa keke ko fadawa kan wani abu
kuma murfin budurci na fashe wa ta
sanadin yarintar yariya ta hanyar
wasa kamar ta rika sanya dan ya
tsanta cikin farjin ta sannan yana
fashewa ta hanyar daga wani abu
mai nauyi. Kamar yadda al'ada tazo
dashi tun fil'azal shi murfin budurci
ke bai yanar tsarkin budurwa da
kuma nunar da cikar budurci

1. Rashin isasshiyar lema a ‘yan matanci: Idan ya kasance babu isasshiyar lema a ‘yan matanci, to uwargida za ta rika jin zafi lokacin ibadar aure.Ruwan maziyyin da kan zubo lokacin da aka fara jin motsuwar sha’awa, amfaninsa kamar amfanin man ‘grease’ ne a injina. Wasu cututtuka masu addabar jikin dan Adam, kamar su bushewar jiki, rashin isasshiyar lema a jiki, wani ciwo da ya shafi koda ko mahaifa, da gabatowar tsufa duk suna iya sa rashin isasshiyar lema a ‘yan matancin mace. Sannan rashin cin lafiyayyen abinci musamman ‘ya’yan itace da kayan lambu na iya haifar da karancin lema. Sannan tsoron jin zafin ma kansa, ko kin da uwargida ke yi wa ibadar aure na iya hana sarrafuwar ruwan da ke kawo lema. Hanyar kawar da wadannan ita ce, uwargida ta dage da cin kayan lambu da ‘ya’yan itace, ta kuma rika yawan shan ruwa, sannan ta cire duk wani tsoro ko fargabar jin zafi daga zuciyarta. Idan kuma da wani ciwo mai dangane da ma’aikata da injinan sha’awarta, to sai ta yi kokarin warkar da shi tukuna. Uwargida na iya amfani da man shafawa na basilin lokacin ibadar aure har kafin wannan matsalar ta kau daga gare ta cikin yardar Allah SWT.
2. Tsukewar ‘yan matanci: Wannan yanayi na iya haifar da jin zafin ibadar aure ga uwargida, watau ya kasance jijiyoyin dake kofar ‘yan mantancinta sun cika tsukewa sosai ko kuma sun cika tsauri don haka ba su ja su buda lokacin ibadar aure. Idan an fahimci hakan ne ke haifar da matsalar jin zafin, to sai a je a ga likita. Akwai ‘yar karamar tiyatar da za a iya yi don tafiyar da matsalar in Allah ya so.Haka kuma samfurin motsa jijiyoyin ‘yan matanci na kejel shi ma yana maganin tsaurin jijiyoyin al’aura ya kara masu laudi.
3. Salewar mafitsara: Saboda kusancin mafitsara da kofar ‘yan matanci, salewar wajen fitar fitsari, ko ya kumbura yana zafi, na iya haifar da jin zafin ibadar aure ga uwargida. Akwai magunguna da za su warkar da wannan nan da nan in an ziyarci likita.
4. Bankarewar jijiyoyin kofar ‘yan matanci: Wannan bankarewar jijiyoyi lokacin ibadar aure na haifar da tsananin zafi maras misaltuwa ga uwargida, wanda dole ta ji kwata-kwata ba ta kaunar ibadar auren.Sannan ga shi ba wai wata kwayar cuta ce take haifar da wannan ba illa dai wani kala kalar tunanin da ya yi karfi a zuciyarta game da ibadar auren, musamman idan akwai wani abu da take tsananin ki a ciki, kuma kin yayi karfi har zai sa jijiyoyin ‘yan matancinta, maimakon su yi lum-lum su kwanta yadda har za ta iya jin sha’awa, sai su bankare su haifar da tsananin zafi a gareta, da rashin samun isasshiyar gamsuwa ga maigidanta. Hanyar magance irin wannan matsalar ita ce, uwargida ta daure ta kawar da duk wata kyama, wani tsoro da duk wani karkatacce da birkitaccen tunanin da ta rike a zuciyarta game da ibadar aure, game da mijinta ko game da yanayin dangantakar da ke tsakaninsu.Sannan ta daure ta rika sakin jikinta lokacin ibadar aure; ta natsu ta kwantar da hankalinta, ta saita dukkan na’urorin kwakwalwarta a kan ibadar auren. Yau da gobe, in Allah ya yarda za ta ga ta yi nasara; ta daina jin irin wannan zafin.
Haka kuma wani babban maganin wannan matsalar shi ne, a dage, a rika motsa su wadannan jijiyoyin da samfurin motsa su na ‘kegel’, sai a nemi ‘yar karamar na’urar ‘kegel-master’ a rika yi a-kai-a-kai. Da fatan Allah ya sa a dace, amin.
5. Kumburi da salewar kwada na iya zama sanadin jin zafin ibadar aure ga uwargida, kuma da an warkar da wannan ciwo in sha Allahu za a daina jin zafin.
6. Fitowar yadin shimfidar mahaifa: Wannan shi ma yana haifar da jin zafin ibadar aure, kuma da an magance shi a asibiti, jin zafin zai tafi in sha Allah.
7. Salewar da kumburin labban ‘yan matanci na haifar da tsananin jin zafi lokacin ibadar aure.Wani lokacin har yakan zama ciwo mai tsanani sosai.Gwajin likita ne kadai zai tabbatar da irin kwayar cutar da ta haifar da ciwon, don magance ta da irin maganin da ya dace. Sannan rashin isasshiya da kuma cikakkiyar tsabtar wajen na daga cikin abubuwan da ke haifar da irin wannan ciwo. Haka wasu kayan zamanin da ake amfani da su kamar su sinadarin musamman don wanke ‘yan matanci ‘baginal douche’ yana iya haifar da wannan ciwo, domin yanayin halittar ‘yan matanci iri daya ne dana kwayar idon dan Adam, an halicce su da ruwan da ke wanke su ya fitar da datti ya turo waje.Kamar yadda muka san ba a sanya sabulu a wanko cikin kwayar ido, to haka ma bai dace ba wanko cikin ‘yammatanci da ‘baginal douche’ da ire-irensa.
8. Mannewar yadin cikin kugu guda biyu waje daya:Shi ma na iya haifar da jin zafin ibadar aure, amma da an yi tiyata an raba su shi ke nan ciwon zai warke in sha Allah.
9. Haka ma wasu cututtuka masu dangane da mahaifa; irin su ciwon kaba na mahaifa, watau ‘fibroid’ da kaluluwar cikin mahaifa ‘cysts’ duk suna iya sa jin zafi lokacin ibadar aure.Hanya mafi dacewa sai a je asibiti don a tabbatar da ainihin abin da ke haifar da hakan, da fatan Allah ya sa a dace, amin.
Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.                               
Reply
Users browsing this thread: 1 Guest(s)