The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KANO TO JIDDAH* by Zahra Muhammad Mahmud
#1
????????
*KANO TO JIDDAH*


????????

Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION(MAKI GANI YA KAUDA IDONSA)
BISSMILLAHIRRAHMANIR RAHIM.
*KIYIWA ALLAH KIDENA KARANTA LITTAFINA IDAN KINSAN ZAGINA ZAKIYI PLS?*
*Fans am sorry to say,rama alkhairi game sharri ba illah bane,wlh har cikin zuciyata nake nufin haka,bada wata manufaba*
*WANNAN LITTAFIN GABADAYANSHI SADAUKARWANE,AGAREKI ZAHRA BUKAR,ALLAH YA DAUKAKAKI DAUKAKA MAFI GIRMAN DARAJA,ALLAH YAKAREKI DAGA SHARRIN DUK ABUN KI,DUK ABINDA ZE ZAMA DAMUWA AGAREKI ALLAH YAMIKI TSARI DASHI,GABANKI SALAMUN BAYANKI SALAMU,ZAUNA DA SUNAN ALLAH KITASHI DA IKON ALLAH,TAFI CIKIN AMINCI YAR TORON GIWA MAKI GANI YAKAUDA IDONSA, SUNJA KINSAKI SUN FADI,DAMA WAYA FADA MUSU ZASU IYA,KAINUWA DASHEN LILLAHI,HANJIN JIMINA KOWA YACI SE LALACE,ALLAH YAKARAWA MAHAIFANKI ARZIKI DA WADATACCIYAR LAFIYA,ALLAH KUMA YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA,SURBAJO KE NEMAN ALBARKA AUNTY*
*1-2*
Ƙauyen *Laminkwai* wani ƙaramin kauyene a ƙauyan *Daurawa* dake garin *Yako* aƙaramar hukumar *Kiru* ta jihar Kano.
Malam Hashimu yana ɗaya daga cikin mazaunan garin.
matarshi ɗaya da ƴa guda ɗaya,sunan matarshi laminde,amman yarsu na kiranta da inna.
sunan yartasu *Suhaima* yarinyace yar kimanin shekaru goma da haihuwa,bayan Suhaima anhaifi kannanta maza guda hudu amman dukansu adaren suna suke mutuwa.
Malam hashimu ba abinda yakeso irin yaga yanada ƴaƴa maza,shiyasa,ya ɗauki tsanar duniya ya ɗorawa suhaima, acewarshi ita annobace a rayuwarshi,sabida tunda aka haifeta,amfanin gonarshi yadena albarka,talauci ya kunno masa gida,abinda zeci yafi ƙarfinshi,kuma aganinshi tunda aka haifetane take cinyemasa duk ƴaƴanshi maza sabida maitarta,ko kadan malam hashimu baya ƙaunar suhaima.
mahaifiyarta tayi kuka tayi roƙo akan yadena abinda yakewa yartasu amman yaƙi ji kullum abun se ƙaruwa yakeyi.
Mutanan garin kowa yasan hashimu baya kaunar yarsa.
Wasu har zugashi sukeyi akan yaci gaba da azabtar da ita.
Malam hashimu bafulatanine,na asali haka itama matarshi,yar tasu suhaima kyakkyawace ajin farko sabida tayo gadon kyau uwa da uba.
Makarantar allo kawai take zuwa,itama ba kullumba,dan in aka korota kuɗin laraba setafi sati agida bataje ba,sabida babanta baze biya ba.
Yauma kamar kullum,zaune suhaima take tana wanke allonta,sabida zatayi sabon rubutun da aka bata.
A fusace mahaifinta yashigo gidan,ko sallama beyiba.
Suhaima na ganinshi tamiƙe agigice tana neman hanyar guduwa,sabida,inde ta tsaya to ko batayi laifin komaiba ze fara dukanta.
ganin ya tsare hanyar da zata gudunne yasa ta tsuguna a inda take tana kuka,tana fadin.
"Don Allah Baffa kataimakeni kayi haƙuri,karka dakeni,wlh bani nakashema ƴaƴa ba,Aradu ni ba mayya bace,don Allah kayi haƙuri,kar ka dakeni"ta ƙarasa maganar cikin matsananci kuka,jikinta se bari yake.
maganganun nata ne suka kara fusata malam hashimu,dan haka afusace yayi kanta,yafara duka kamar yasamu kato.
."Matsiyaciya har kina da bakin magana,ki kashemin ƴaƴa,ki ɗoran talauci,sannan kizo kina bani hakuri?,muguwa azzaluma kawai,wlh sena nakasa rayuwarki
Haka yay ta dukanta tana kuka,tana kiran.
"inna kizo ki ceceni,don Allah Baffa ze kasheni,don Allah ki fada masa niba mayya bace,kinji inna,kitaimakamin,inna ke kinsan wanda yakashe miki ƴaƴa don Allah kicewa Baffa bani bace"
Inna kuka take tana zaune agefe,tana kallon yadda malam ke fitarwa da suhaima jini,amman bazata iya hanashiba,sabida yace duk randa yake dukan suhaima tazo ta ceceta abakin auranta.
kuma abun ya hadu biyu inna macece me matukar hakuri har bada kwatancenta akeyi game da hakurin nata.
Malam seda yaga suhaima bata numfashi sannan ta kyaleta yasa kafa yafice,
Da gudu inna ta debo ruwa ta sheƙawa suhaima,wacce ta sume sabida azabar duka.
Bayan ta farfado inna wanka taimata takaita daki,tana gasa mata inda yaji mata ciwo,gaba dayansu kukan sukeyi,cikin dashashshiyar murya suhaima ta kalli mahaifiyarta tace.
"Inna don Allah ki kaini gurin Baffa na na aynihi,wannan ba Baffana bane"
kuka inna tasa,ta rungumota jikinta tace.
"suhaima baki da wani uba aduniya se wannan,shine mahaifinki,ki dunga yimada adduar shiriya,amman tabbas shine mahaifinki,kidena neman wani uba bayan shi"
Haka inna taita kwantarwa da suhaima hankali,harta haƙura ta dena kuka,sede ajiyar zuciya da take tayi.
Haka rayuwar suhaima ke tafiya agidan mahaifinta,wanda take da ja game da zamtowarsa mahaifinta.
muje zuwa.
????????
*KANO TO JIDDAH*
????????
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*ANAYIN ZAZZABIN WATA,ANAYIN KUSUFIN RANA,AMMAN BANTABA JIN ANYI NA TAURARI BA,ZAHRA DA ZAHRA,ALLAH DE YA HADA YANZU,MASU ZUGATA DON ALLAH YA KUKAJI?NIDE NASAN KUNJI KUNYA,TO KU NEMO HIJABAI DA NIKABI,DOMIN RUFE FUSKARKU YAYIN HAWA ONLINE,DAN WATA KUNYAR SEMA RANAR,DA ZAHRA DA ZAHRA,SUKA KAWO MUKU LITTAFINSU DAZASU RUBUTA ATARE,ME SUNA WACECE ZAHRA????LOL,NICE KO ITACE,BARI INBARKU HAKA,DANNASAN KUNYA TAGAMA KAREWA MUNAFUKI,AUNTY ZAHRA BUKAR,KOWANNE BUGU NA ZUCIYAR SURBAJO YANA FARUWANE DA SONKI,AUTAR HAJIYA MUNGODE,MAKI GANI YA KAUDA IDONSA*
*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR*
*3-4*
Haka mahaifin suhaima yaci gaba da ganamata azaba,tun inyana dukanra tana kuka har yanzu dukan yabi jikinta ko kuka batayi.
Yau an sake koro suhaima kudin laraba,jiki asanyaye tashiga dakin mahaifiyarta,tazauna tayi tagumi,
Lokacin innan ta tashiga toilet,tana fitowa taga cinyayyan silifas din suhaima abakin ƙofar dakinta.
Ajiye butar tayi tanufi dakin,koda ta shiga suhaima bataji motsinta ba sabida nisan da tayi acikin tunani
Tausayintane yakama inna,jitayi hawaye nabin fuskarta,jawo suhaima tayi jikinta,se alokacin suhaima ta dawo daga duniyar data tafi.
"suhaima lafiya kike kuwa,meya sameki kikazo kika zauna anan kina tunani,,ina makarantar"
Cikin kuka suhaima tace.
"inna kuɗin laraba aka koroni,kuma nasan ke baki dashi baffa ne kawai zan tambaya,kuma kinsan inde naje dukana zeyi"takarasa maganar tana kuka.
Sharemata hawaye innah tayi sannan tace.
"karki dami yata,kije kimasa magana,inya dokeki yau watarana goyaki,zeyi,ba yauba suhaima,ba yanzu ba ni nasani komai nisan jifa kasa ze sauko,kuma duk girman gona akwai kunyar karshe,ke da mahaifinki beso insha Allahu se ya shiga karkashin inuwarki,kijure duk wahala,bayanta daɗi nanan zuwa,kinji ko dan haka tashi kije ki tambaye shi insha Allahu ze baki"
jiki asanyaye suhaima tanufi dakin mahaifinnata.
Daga bakin ƙofa ta tsuguna tayi sallama.
Be amsaba yanufota afusace,tun kan yaji abinda ya kawota,yakifeta da mari har guda biyu,sannan yace.
"Aradu suhaima da badan kurwata tafi taki ƙarfiba da tuni nima kin cinyeni,meyasa bakida fshimta,nifa sonki ne banayi,meyasa dole se kinzo gurina,ki nisants kanki dani dan gudun kada wata rana awayi gari na kasheki,sabida kiyayyar danake miki"
"Baffa uba baya kin dansa,haka shima ɗa baya kin iyayenshi,wlh baffa koda ka kasheni nayafe maka fansar raina,don Allah baffa kataimakeni kabani kudin laraba mslam ne ya koroni"ta karasa maganar tana kuka.
hannu yasa a aljihu ya ɗauko wata tsohuwar naira ashirin yabata,da murnarta,ta amsa ta juya zata tafi,dakatar da ita yayo,sannan yace.
"Wlh har abada bana kaunarki,ina roƙon Allah da yayi gaggawar kasheki kamin bakin cikin ganinki yasa ni na mutu,suhaima wlh na tsani ganinki"yana kaiwa nan yajuya yashige cikin ɗakin.
inda sabo suhaima tasaba da irin wainnan kalaman na mahaifinta,dakin inna taje ta nuna mata kudin tana murna ta juya ta koma makarantar ta biya kuɗin.
Rayuwa taci gaba da tafiya ahaka,kullum ba sauki sena Allah.
yau counsilor din garin yayi rabon kudi inda yaba malam hashimu dubu goma.
Ay Baffa jinshi yayi kamar ansashi a aljanna,kasuwa yaje yasiyo balangu na dari biyu,me daɗi sannan ya wuce gida.
da sallamarshi yashigo gidan,wacce rabonshi dayinta har ya mance.
Da faraa inna tafito tana amsa sallamar.
ganin faraa a fuskarshine yasa ta ɗauko masa tabarma ta shimfiɗa masa suka zauna sannan yace cikin faraa
"Laminde ay yau take sallah agidannan,dan har balangu na siya miki na jaka guda dan kici kiji daɗi,Nura kansila ne yayi rabon kudi shine nima yabani dubu goma"
"Alhamdulillahi,natayaka murna Allah ya amfana"
kunshin naman yaciro a aljihunshi yabata yace taci.
Nan inna tafara cin naman suna hira,sallamar suhaimace ta dakatar dasu,dawowarta daga makaranta kenan.
Tana shigowa annurin fuskar Baffa ya ɓace yakoma kamar anmasa mutuwa.
daga gefe ta tsuguna tana musu sannu da gida.
inna ce kawai ta amsa amman banda baffa.
Suhaima ganin inna nacin namane yasa hankalinta komawa gurin,dan rabonsu da nama shekara guda kenan.
mikoma suhaima sauran naman inna tayi,jiki na ɓari tamika hannu zata amsa dan dama tuni yawun bakinta ya tsinke.
wani azababben mari baffa ya ɗauketa dashi,sannsn yarufets ds duka,seda yamata,dukan daya janyo mata targaɗe akafa.
inna bakinciki ne yasa tamiƙe tashige ɗakinta,tana jiyoshi yana fadin.
"wlh baki isa kici namannan ba bakar matsiyaciya,"
hakade yayta balainshi,yawuce yabarta sgurin jiki afashe
inna dayake ta iya gyaran targade ita ta gyarawa suhaima sannan ta koya mata yadda akeyi.
koda dare yayi baffa ƙasan shimfiɗarshi ya adana sauran kuɗinshi,cikin dare yana bacci bera yaja kuɗin zuwa bakin raminsa.
koda gari yawaye,baffa yakasa fita sallar asuba sabida neman kuɗinshi dabe ganiba,koda yaga begansuba,cikin fushi yafito tsakar gidan beyi wata wata ba yarufe suhaima da duka wacce ke tsugune tana ƙoƙarin haɗa murhu dukanta yake yana faɗin.
"Au dan jiya na hanaki cin nama shine kina sacemin kuɗina?to wlh kinyi ƙarya,dole sekin fitomin da kuɗina,bakar muguwa,azzaluma,mayya,barauniya,bakincikin ki baze kasheniba,kifitomin da kuɗina duk inda kika kaisu"
"wlh baffa ni bansan kanada kuɗi bama bare in ɗaukar maka,kayi haƙuri don Allah"
inna ko inbanda kuka ba abinda takeyi.
Shiko baffa dayaga ya caje suhaima bega kuɗin ba buɗar bakinshi se cewa yayi.
"Aradu awa biyu na baki,kije kwanar dangora kiyi karuwanci kizo kibiyani kuɗina in bs hakaba abakin auran uwarki"
jin furucinshine yasa tari sarƙe inna,tun tanayi atsaye harta kai ga tafaɗi jini nabiyo bakinta,dakyar tace
"suhaima matuƙar ba fyaɗe aka miki ba,duk ranar da son zuciya ko wahalar rayuwa tasa kika zubar da mutuncinki awaje ba a gidan auranki ba banyafe mikiba"
da gudu suhaima tayi gurin innarta tana kiran sunanta.
shiko baffa ɗakinshi yakoma daniyyar ɗauko magani ya jikawa innar,abinda yaganine yabashi mamaki,kuɗinsa sbakin ramin ɓers,ds sauri ya ɗauka yaga ba abinda yasamesu a aljihu yasaka sannan ya ɗauko maganin yafito.
koda yazo gurin innar numfashinta na sama tace.
"Hashimu na yafe maka,Allah yadawo dakai kan hanyar gaskiya,suhaima kiyi haƙuri da duniya da mutanan cikinta,Allah ya albarkaceki,insha Allahu bazaki taɓe ba"dakyar tagama furta maganar,daga ƙarshe tayi kalmar shahada tace ga garinku nan.
Tunda baffa ya fahimci inna ta mutu yazube agurin yana faɗin.
"Tur dake suhaima,yanzu mahaifiyar takima seda kika kasheta me nayimiki kike kashemin iyali?,Allah ya isa tsakanina dake"yasake rushewa da kuka.
itako suhaima jin inna ta rasu ne yasa ta yanke jiki ta faɗi kasa sumammiya
muje zuwa.
surbajo for life.
????????
*KANO TO JIDDAH*
????????
Zahra Muhammad Mahmud
*maki gani ya kauda idonsa*
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR*
*5-6*
Ihun baffa ne yajanyo hankalin maƙwabta,dayake asubace shiyasa suka jiyoshi.
Nanfa mutane sukai ta shigowa,bakin baffa yaki rufuwa kowa yazo se yace mishi suhaimace ta kashe uwarta.
Wata ce ta dibi ruwa ta watsawa suhaima ta farfaɗo,kuka takeyi gwanin tausayi,haka tanaji tana gani aka haɗa mahaifiyarta aka mata sallah akaje aka birne ta.
Duk me imani yaga suhaima seya tausaya mata,lokaci guda tafita hayyacinta,in banda kuka ba abinda takeyi.
Shiko baffa memakon yayiwa matarshi addua se lantar suhaima yake,wai takashe mishi mata.
Haka akaita zaman makoki har akayi arbain din innah suhaima bata koma daidai ba.
***************
Bayan wata uku da rasuwar inna,baffa ya haɗu da wata bazawara me suna,Lantana ya aureta.
Lantana,irin tsofaffin karuwan nanne,dan haka tana shiga gidan baffa,balai ya karu akan na da agurin suhaima.
Komai na gidan ita takeyinshi,dan har cikin dare turata dam din daurawa takeyi ta ɗebo ruwa,gashi da nisa atsakaninsu,haka zata kwana ahanya,dan ko amashin ne zaka seka biya naira dari koma fin haka,bare suhaima ga jarkunan ruwa har guda uku haka take turata.
Baffa be taɓa kallon hakan amatsayin cutarwa ga rayuwar yartashi ba,sema daɗi dayake ji.
Tuni tadena zuwa makatantar Allo,shinkafa da wake lantana take dafa mata ta turata talla.
ga suhaima me kan tallah ce tana fita yake ƙarewa,hakanne yasa lantana komawa dafa mata rabin buhu,da safe takai garin Kiru,da rana kuma takai kwanar dangora,da yamma takai yako.
ba irin wahalar da suhaima batasha,kuma duk da wannan wahala mahaifinta ko gaisheshi tayi baya amsawa,sedema yarufeta da duka,ko so ɗaya lantana bata taɓa cetonta ba.
Ana haka ne wani ƙanin lantana yazo daga garinsu,murna gurin lantana kamar me,shima baffa yayi murna da zuwan salele,ba kaɗanba.
To dama gidan ɗaki biyu neHH,ɗaya na suhaima,ɗaya kuma baffa da lantana,dan haka koda dare yayi baffa dakanshi yakai salele ɗakin suhaima wai yadunga kwana aciki,kamin yatafi.
Suhaima ido kawai take warewa ganinta kwance da shirgegen ƙato a shimfiɗa ɗaya.
Koda baffa yafita adakin,salele zuwa yayi ya kulle ƙofar,sannan yazo kusa da suhaima yakwanta.
Cikin dare suhaima ta farka taga salele yacire mata riga,se matse mata kananan nashanunta yakeyi,wainda farkon fitowarsu kenan,se zafi suke mata.
Da sauri tamike zaune tace bakinta naraw.
"meyasa kakeson zubarmin da mutunci don Allah,?"
Dariya yayi sannan yasake shafota yace .
"sabida mahaifinki be nuna ke me mutuncin bace,tunda ya iya haɗani dake mukwana guri ɗaya"
Kuka suhaima tasa mishi tana bashi hakuri amman ina salele,se kokarin rabata da duka kayanta yake,Cikin saa suhaima ta kwace a hannunshi tafita tsakar gida tana kuka,
Da gudu baffa da lantana suka fito.baffane yace.
"dan kan uwarki meya faru kike ma mutane kuka tsakar dare?"
Baki narawa suhaima tace.
"Baffa salele ne yaciremin kaya yana son yin lalata dani"
Carab lantana ta amshi maganar.
"kaji munafuka,lokacin dakike rabawa yan tasha,ubanwa kika yiwa kuka,se yanzu dan sharri irin naki zakice wai salele,ni inbanda masifa irin ta salele ubanme zeyi dake".
Baffane yakarasa inda suhaima take yarufeta da duka,seda yamata lilis,sannan ya hankaɗata ɗakin da salelen yake ciki,yace.
"Bakar munafuka,kyayi kya gama,yanzu kuma sharri kika zo dashi to wlh munfi ƙarfinki,"daga haka suka juya ɗaki shida lantana suka rufo ƙofa.
Salele murna ce takamashi dan haka yanufo inda suhaima take tsugune tana kuka,itako tana hangoshi,ta kwasa aguje,tafice ma daga gidan,.
Gudu take ba kama hannun yaro,har ta isa gidansu wata hanne ƙawarta,kuma maman hannen tana da kirki,baban hannen ya rasu,
Dayake gidan kauye bakowanne keda murfi ba dan haka shigewa gidan suhaima tayi tabaje atsakar gida,koda salele yabiyota be ganta ba dan haka yakoma gida yana huci.
A tsakar gidan suhaima ta kwana ko riga babu ajikinta,da asuba maman hanne ce tafara fitowa,koda taga mutum kwance tsakar gida abunka da mutanan karkara basu da tsoro kanta tsaye taje gurin tana tambayar waye.
Farkawa suhaima tayi,ganin innar hanne ne yasa tafashe da kuka tace.
"inna nice suhaima"daga gaka takwashe komai ta faɗawa innar.
tsananin tausayin suhaima ne yasa inna kuka,kamota tayi ta rungume race cikin kuka.
"kiyi haƙuri suhaima insha Allahu,nan gaba zakiga amfanin rayuwarki,kibarwa Allah komai,yana sane da halin da kike ciki"
Daga haka daki takaita nan hanne taita kuka na tausayin kawar tata,kaya tabata tasauya bayan tayi wanka,tayi sallah taci dumamen tuwo,sannan tanufi gidansu. A tsakar gida tasamesu duka suna karyawa,bawanda yadamu da ita bare yatambayi daga ina take.
kayan tallan ta ta ɗauka tafice,zuwa kiru,bayan ta amshi kuɗin mota ahannun lantana.
Da misalin ƙarfe,goma na safe bayan tafiyar suhaima talla,hajiya zaituna me makkah me dubai,ta bayyana a garin na laminkwai.
Gida gida take bi tana haɗa kan yanmata wainda iyayensu suke da shaawar akaisu saudiyya aykatau,ayko duk inda tashiga kowa yaƙi bada yarsa,ahaka harta shigo gidansu suhaima.
Da faraa lantana ta karɓeta,koda hajiya zaituna tamata bayanin abinda yakawota ba ƙaramin daɗi tajiba,suna cikin tattaunawa,suhaima ta dawo daga tallah.
Nan take lantana tace hajiya ta tafi da suhaima ta bata,lokacin mahaifin suhaima bayanan haka lantana ta yanke hukunci.
Dubu ɗari hajiya taba lantana,ay ji tayi kamar ansata a aljanna,murna da godiya har kasa.
cikin masifa lantana tasa suhaima haɗo kayanta,kuka suhaima takeyi tana ba ta hakuri amman taki sauraronta,daga ƙarshema ta rufeta da duka.
Ganin zasu bata mata lokaci ne yasa hajiya zaituna cewa tabar kayan,insunje zata saimata wasu,
haka suhaima tanaji tana gani suka sata a motar hajiya zaituna,ita kuma takulle taja suka tafi.
Koda baffa yadawo lantana tabashi dubu hamsin sannan tace.
"dayake naga harkar ƙaruwa ce shiyasa nabada ita,nan kano zaa kaita tadunga aykatau,duk bayan wani lokaci zatazo ganin gida"
baffa ko damuwa beyiba yashiga sawa lantana albarka.
Suko mutanan gari,gaba ɗaya kowa yaɗauka antafi da suhaima karuwanci.
koda labarin yazo kunnen baffa ko damuwa beyiba dan yasan hassadace.
Tun suhaima tana kuka har tadena,haka sukaci gaba da tafiya hajiya najanta da hira.
ga sanyin ac yana busata ay suhaima batasan sanda bacci ya ɗauketa ba,har suka iso kano,anguwar hotoro kwanar maggi bata sani ba.
muje zuwa.
surbajo for life.
????????
*KANO TO JIDDAH*
????????
Zahra Muhammad Mahmud
*maki gani ya kauda idonsa*
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*umeeeeeeeeeh naga sakonki nagode Allah yabar zumunci*
*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR*
*7-8*
Koda hajiya zaituna tayi parking suhaima bata saniba seda ta tasheta,a firgice ta farka.
Haka hajiya tajata zuwa cikin gidan,suhaima se kauyanci takeyi,sabida shine karon farko na shigarta birni.
Koda suka shiga falon yanmata ne ajere su tara,se wata babbar mace atsaye agabansu tana koya musu wani abu,koda suhaima ta lura dakyau ashe tafiyar jan hankali ake koyar dasu.
Ganinsu ne yasa matar zuwa gurinsu tana faraa tace.
"me makkah me dubai,ina kika samo mana,zuma farar saƙa kuma?"
Dariya hajiya zaituna tayi sannan tace.
"hmmm kede bari uwar mabukata,wlh can wani kauye na siyota afarashi dubu ɗari,gatanan na kawota,nasan zamu samu dubunsu ajikinta,sabida inkin lura yarinyar akwai kira,"
Dariya uwar mabukata,tayi sannan tasa hannu ta shafo gefen fuskar suhaima wacce tunda suka fara magana take ware ido kamar tsohuwar mayya,sannan tace.
 
 
 
 
Reply
#2
muna bukatar comment dinku akan littatafen hausa dinmu. Allah ya bada sa'a
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 2 36,320 09-14-2018, 12:13 PM
Last Post: Gimbiya
  *KANO TO JIDDAH* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 9 111,928 09-05-2018, 06:57 PM
Last Post: Gimbiya
  *Y'ar Bautar K'asa* A Youth Corper*by Zahra Surbajo Gimbiya 1 17,110 08-10-2018, 01:58 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 18,162 07-26-2018, 12:53 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 33,643 07-16-2018, 03:44 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 13,366 06-26-2018, 01:07 PM
Last Post: Gimbiya
  *KARAN BANA* by zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 15,622 06-19-2018, 01:08 PM
Last Post: Gimbiya
  *AMANA TA BARMIN* by Zahra Muhammad Mahmud Gimbiya 0 42,148 11-30-2017, 11:25 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)