Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER*
#1
*Y'AR SARKI CE!!!..*?

{It's All About Royal,Destiny,Betrayal and A Romantic Love Story}?

*NA*

 *UMMU BASHEER*

 *HASKE WRITERS ASSOCIATION*?
 (Home of Experts & perfect Writers)


 *^°IN DEVOTION To BILLY'N ABDUL ^°*

*Page 11~12*

     A kishin gid'e take saman kilasta cikin k'asaitar ta, sai bayi hud'u dake zageye da ita, kowacce da aikin datakeyi. d'aya namata fifita, sai buyu dake matsa mata k'afafu (tausa), d'ayar na dirk'ushe gabanta tana yanka mata fruits.
  
Yanda take shan k'amshi da basarwa saika d'auka itace SARKIN ba matar sarkiba, cikin isarta takai tuffa bakinta ta gutsura, tacigaba da taunawa a hankali, gefen zuciyarta namata tunanin ina Sa'ade tadad'e haka?. (Amintacciyar baiwarta kenan, datake taimaka mata bisaga dukkan k'ulle-k'ullenta, musamman Na bin bokaye da Malam tsubbu Wanda ita batada damar yinsu, tunda matan Sarki kowa yasan basa fita saida kwakwkwaran dalili).

Wata cikin bayinta ne tayi sallama daga k'ofar d'aki, sauran bayin suka amsa mata, Fulani kam ko d'ago kai tama kalli k'ofan batayiba, cin fruits d'inta takeyi hankali kwance. Hannu tad'aga musu, alamar tabama mai sallamar izinin shigowa. wadda kemata fifita tace, "kishigo da izinin gimbiya".

Sallama sa'ade tak'arayi, kafin tashigo. Ganinta yasa Fulani kallonsu suduka, batareda tace komai kowa ya ajiye aikin da yakeyi ya fice. a gaban ta sa'ade tazube tana zabgo mata kirari irinna matar Sarki mai iko. Saida tagaji Dan kanta tayi shiru kafin tabud'e kod'ad'd'iyar jakkar hannunta tafiddo tulin k'ullin magunguna, ta zubesu a gaban Fulani tana 'Yar dariya.

"Ya uwar gijiyata, aikinki dolene agareni, cika umarninki biyyayace agareni, Na isar da sak'onki ga boka gogaji, wad'annan sune maganin daya bada. ta d'auki wani bak'in kulli ta ajiye gefe, wannan Na mai martabane kamar yanda aka saba, saikuma wannan kwan yace a soya wannan maganin dashi, wannan kuma adafa abinci dashi, shine za'a bama yarima Shaheed. ya tabbatar da zaran yaci wannan had'in, to tabbas bazai k'ara koda minti gomaba a wannan fadar dama yankin nan baki d'aya."

Cikin isarta tatashi daga kishin gid'ar datayi, ta d'auki kwan tana jujjuyawa, Dan anzaneshine da rubu, ajiyewa tayi, takoma ta kishin gid'a tana guntun murmushi, tace, "ai yanzuma Na canja shawara, su duk nakeso subarmin gidan har shuraim, dan haka kije ki huta, zuwa magriba inason ganin laminde mai musu girki agabana".

" angama uwar gijiyata, hutawarki lafiya uwargidan sarki, s........

'Daga mata hannu Fulani tayi alamar batason kirari, taimata alamar taje. da Sauri sa'ade tatashi tafice, hartana tuntu6e zata fad'i, ta daiyi nasarar dafe bango sannan ta fice.

************

Jiddah ce ke faman ba wata kawar Ramla hakuri akan taci mata bashin gulisuwa amma tak'i biya. Ramla na gefe sai auna hararra take. Naira dari Jiddah ta Ciro ta Mik'a ma kawar. Haka taja hannun Ramla suka bar islamiyyar.

A hanya Ramla sai turo baki take wai akan me Jiddah zata biya kud'in ai dama bata tayi ta siya wani alawar. 

Jiddah rangwashin ta tayi. Cikin zafi ta Sosa gurin kamar za tayi kuka.

Jiddah tace"wannan ya zama na karshe Idan ba haka ba duk abinda kikeyi zan dinga fad'a ma Mama kuma kin San abinda za tayi miki ai"

Marairaice fuska tayi kamar za tayi kuka"Allah sarki ya Jiddah nice fa K'anwar ki dan Allah kiyi hakuri kinji Idan nayi kud'i zan siya miki wata katuwar mota"

Tsaki kawai jiddah tayi suka wuce.

Da yamma sai ga Jiddah ta shigo gidan ta samu Ramla na d'aki tana kwance. Zama tayi kusa da ita ta bud'e  ledar awarar ta tura Mata gaban ta.

Har lashe baki Ramla take taga kwad'ayi har ta sa hannu zata d'auka Jiddah ta rik'e hannun ta ai nan ta marairaice fuska.

D'auka jiddah tayi tasa mata a baki tana mai jin tausayin K'anwar tata.

Wasu hawaye ne suka zubo ma Ramla da sauri jiddah ta share mata tana girgiza kai alamar kar tayi kuka.

Rungume juna sukayi cike da tausayin Rayuwar su.

************

  Da magriba sa'ade tacika umarnin uwar gijiyarta, jikin lamunde har rawa yakeyi saboda kiran data samu sarauniya namata. tunda suka shigo tazube a gaban ta, tayi wani gurfane tamkar mai Neman gafara. maganin Fulani ta mik'a mata tana yatsine fuska.

"K! Kinutsu da k'yau aiki zan sakaki, inhar kuskure ko sa6a yin yanda nace yabiyo baya to kikira kanki gawa kawai, inason kiyi amfani dashi a karin kumallon safe nasu yarima".

A d'an firgice laminde tad'ago, Fulani ta zabga mata harara dawata uwar tsawa, "shin bazakiyi bane?".

" a'a, ALLAH ya huci zuciyarki, cika  umarninki dolene agareni aii".

Kwafa Fulani tayi, kafin ta kalli sa'ade tace, "yimata bayani". Tiryan-tiryan sa'ade taima laminde bayanin yanda zatayi, sannan tace dasafen zasu saka Wanda zaisaka mata ido, inma batayiba zasu gane. " insha ALLAH ma zanyi yanda kikeso ai, ALLAH ya huci zuciyarki, a gafarceni".

Hannu Fulani ta d'aga mata alamar tatashi taje.
........

Shuraim haryayi shirin barci zai kwanta kira yasameshi Sarki Na nemansa. jallabiya yasaka, yad'an fesa turare sannan yasa silifas yafita. Bayin dasuke tsaron k'ofarsu suka rissina suna masa barka da fitowa, hannu kawai yad'aga musu yacigaba da tafiya. 

Saida jakadiya tamasa iso sannan yashiga, Sarki Na kishin gid'e a makeken falon nasa, Wanda aka k'awata da adon tambarin sarauta, ga kayan fruits da'aka yanka agabansa, da alama koma ci bai faraba.

Shuraim ya yay durk'uson girmamawa agabansa, kansa Na ak'asa yace, "barka da dare takawa".

Jin jina kai Sarki yayi batareda ya amsaba, har shuraim yafara tunanin kobaima jishiba, yad'an d'ago ido yasaci kallonsa, saiga shima sarkin shi yake kalli. yay saurin maida kansa k'asa.

Sarki ya gyara kishin gid'ar dayayi, kafin yace, " Shuraim wata tambaya nakeson maka?".

Kan shuraim a k'asa yace, "to takawa, ALLAH yasa nasani".

A hankali Sarki yafara shan fruits d'insa, tamkar bazai sake cewa komaiba, saikuma yad'ago kai ya kalli shuraim dake durk'ushe har anzun, sannan kansa a k'asa tana kallon zanene lallausan carpet d'in dake malale a falon.  kamar daga sama yaji Sarki nafad'in " dama kasan d'an uwanka na shaye-shaye?".

Wani hautsinawa cikin shuraim yayi, saida yahad'a da addu'a sannan yasamu daidaita, cikin girgiza kai yace, "a'a takawa, Shaheed baya shan komai".  

Sosai mai martaba ke kallonsa, yanda yay maganar kawai yagane bashida gaskiya, baisake cemasa komaiba yace, " shikenan, tashi kaje, amma inason ganinka kaidashi gobe I war haka idan ALLAH ya kaimu".

A marairaice Shuraim yad'ago ya kalli Sarki, saiyaga babu alamar wasa a fuskarsa, Dan yama d'auke kansa yamaida ga TV. jiki a sanyaye shuraim  ya tashi yafita, Sarki yabishi da kallo kawai yana girgiza kansa.


6angaren Shaheed shuraim yafara Shiga, Dan hankalinsa a matuk'ar tashe yake, sai dai tun'a k'ofa dogari ya tabbatar masa yafita babu dad'ewa. hankalin Shuraim kuma tashi yayi, yanufi nasa 6angaren, wayarsa ya d'auka yashiga kiran Shaheed, amma harta tsinke bai d'agaba, yamasa kira yafi goma bai d'agaba, tamakar shuraim zaiyi kuka haka yaji. dole ya hak'ura ya zauna tsumayen jiransa, saidai kuma kafin Shaheed yadawo barci 6arawo ya sacesa.

....

Tunda safe laminde tashiga kichin domin had'ama shuraim da shaheed Karin kumallo kamar yanda tasaba, tafara babu dad'ewa sa'ade tazo ta tsaya akanta, dole ta aiwatar dakomai yanda suka bata umarni, tagama tsaf tazubama kowanne takai 6angarensa, masu musu share-share harsun kammala, ta tarar Shaheed ma yana k'ok'arin fita, dan yasamu kiran gaggawane wajen wani abokin aikinsa, wannan yasa baima saurari Karin kumallonba yafice.

Shuraim kam bayan yagama shirinsa cikin Jan suit, yayi k'yau sosai, ya feshe jikinsa da turare sannan ta d'auki jakkar aikinsa yafito, soyake suhad'u da Shaheed yagaya masa zancen da mai martaba yamasa jiya, dakuma nemansu dayakeyi. A falo ya tadda komai need sai k'amshi ketashi Na turaren wuta da freshener, ganin breakfast yasashi zama yaci a gaggauce, dan jiya baiyi dennar ba ya kwanta, kad'an yaci soyayyen kwan da dankali, yasha farfesun naman kazar dad'an yawa, tea ma kad'an yasha yamik'e yafice. Yanzuma yataki rashin sa'a Shaheed yarigashi fita, clinic yawuce danufin idan anyi azhur zaije office yasameshi suyi magana.

Tunda Shuraim yashigo asibitin yau yaji Kansa Na juya masa, gawani k'unci dayakeji a zuciyarsa, tun yana d'aukar abin  ba serious ba harya fara fin k'arfinsa, Dan wata tsanar asibitin da garinma yakeji baki d'aya, daurewa yafara amma ina, kusan 12 yafice daga office d'in, nurses NATA gaisheshi, amma bai tanka kowaba, su mamakima yabasu, tunda yazo asibitin yau bai fitoba, ya kulle Kansa a office, gakuma marasa lafiya daketa jiransa tun d'azun.
  

Fita yayi daga hospital d'in mai gadi na tambayar shi lafiya ganin zai fita a kasa bai kula shi ba. Gaba d'aya kansa wani irin juyi yake mai shi kanshi bai San inda zashi ba duk ya fita a hayyacin shi.Shuraim baisan inda yake jefa k'afarsaba, tafiya kawai yakeyi, shidai babban burinsa yabar wannan garin, jinsa yake kamar ana masa wanka da ruwan wuta, ga kansa namasa wani mugun ciwo.

Har magriba tarufa Shuraim nata tafiya, koma gajiya bayayi, tuni yabar gari yafara shiga jeji, wani mai mashin yadawo daga cin kasuwar k'auye yagansa, ganin yana tafiya a k'asa yatsaya Dan taimaka masa, koda yaymasa tayi bai musaba ya hau suka fara tafiya, mai mashin nata zuba surutu, amma Shuraim yamasa shiru, shima ganin haka yaja bakinsa ya tsuke.

Kusan k'arfe 9 Na dare suka isa k'auyen damai mashin yake, yace, "abokina wane gida zakaje?".

Shiru Shuraim yayi dan shi kanshi bai San inda za shi ba. Massalaci yake son zuwa dan yayi sallah. Dan haka a hankali da k'yar yace"ina son yin sallah ka kai ni massalaci dan Allah"

Yana kaisa massalacin dake k'auyen yatafi gida, Shuraim kam buta ya d'auka, yabud'e randar dake gaban massalacin yad'iba ruwa, Dan zuwa yanzu yad'an sami Nutsu, amma hankalinsa duk baya jikinsa, alwala yayi yay sallolin da'ake binsa, yana idarwa yazame awajen ya kwanta, barci mai nauyi ya d'aukesa, dukda matsannciyar yunwar dayakeji. Bai farkaba saida yafarajin maganganun mutane masu zuwa sallar asubahi, sai kallonsa suke da mamaki, saboda shigar dake jikinsa, dukda a firgice yake saboda yunwa da gajiyar tafiyar k'asa dayayi. Babu Wanda ya tambayesa komai, yafita yay alwala, k'in Shiva massalin yayi, yatsaya daga waje yabi jam'i, sunayin sallama baijira anyi addu'aba yabar wajen, a hanzarce yacigaba da tafiya dukda matuk'ar ciwo da jikinsa kemasa, kokad'an bayason kowa Na k'auyen ya biyo bayansa. suna idarwa kuwa suka fara tambayar ina bak'on nan?, kowa yace bai gansaba, nanfa aka fara nemansa, amma babushi babu alamunsa. Wasu suka fara tsegumin k'ilama mugune.

Shidai Shuraim tuni yayi nisa da k'auyen. Tun yana tafiya da k'arfinsa harya koma jan k'afa, yagaji matuk'a, ga yunwa ga k'ishirwa, ga wata matsanan ciyar gajiya, tunda uwar data haifeshi baita6a makamanciyar tafiyar nanba, a matuk'ar wahalce ya iso wani k'auye mai d'an girma, yara sai kallonsa sukeyi, harma da manyan, sunga bak'on ido, daka ganshi kasan a matuk'ar gajiye yake, sai rangaji yaki yana fidda numfashi da k'yar. zaton yara mahaukacine, Dan babu takalma a k'afarsa, yabarosu k'auyen daya kwana, hakama rigar suit d'insa, sai wandon kawai da farar rigarsa long sleep, suma sunyi bud'u-bud'u da k'urar jar k'asar hanyar k'auyen, gashi duk inda yasamu zubewa yakeyi danya huta, dolene kagansa ka d'auka sabon shiga haukane. jifansa da yara suka fara suna kiran mahaukaci-mahaukaci, wuff ya afka wani gida dake kusadashi, Dan har sun fasa masa goshi da dutsin dawani yaro ya jefa masa, dafe wajen yayi sannan yashige gidan.

Mama dake daka a tsakar gida tayi saurin cewa Malam lafiya zaka shigo babuko sallama!....

Shigowar yara suna cigaba da jifansa ya dakatar da mama daga magana, matsawa tayi ta korasu waje, tarufe k'ofar gidan, sannan tajuye garesa, tuni shuraim yazube awajen yana kiran ruwa ruwa a hankali.

Sosai mama taji tausayinsa, saiya tuna mata da tata rayuwa, kusan a wannan yanayin tashigo k'auyen nan, banbancinsu kawai ita akwai taimakon Wanda tasamu yamata jagora.

Matsawa tayi wajen randansu, ta d'ebo ruwa ta kawo masa, idonsa a rufe yakafa kai, tas ya shanye ruwan kuwa, kafin yakoma ya kwanta yaraf yana sauke numfashi, saikuma yafara amai, sosai mama ta rud'e sai sannu take masa. Ana haka saiga Jiddah da Ramlah sun shigo, dama aikan da mama tamusu sukaje.

Tambayarta wanene wannan? Suka shigayi, babu wanda tabama amsa acikinsu, saima tabarma data buk'aci su shimfid'a mata a inuwa. jiddah taje da sauri ta d'auki, Ramlah kam tamkar tasamu magiji, sai k'arema shuraim kallo take.

Saida suka taimaka masa ya wanke fuskarsa da bakinsa sannan yatashi da k'yar yak'arasa kan tabarmar kamar yanda mama ta buk'ata. Mama tabama Ramlah kud'i tace, "maza ki sayomin fura a 'Yar yara, saura ki zauna shashancin dakika saba, danna sanki".

Ramlah na zum6ura baki tafita, jiddah kam tana gaban Shuraim tana masa fifita da maficin kaba.

Ramla bata b'ata lokaci ba ta dawo dan tasan ba lafiya. Tana zuwa Mama ta Karb'a tasa ludayi a ciki tana cewa"bawan Allah tashi kasha ko Kad'an ne"

Da k'yar Shuraim ya iya d'aga kanshi yasa hannu biyu yana sha har zubo mai yake tsabar yunwa da yasha. Sai daya shanye tass. Jiddah ta Karb'a rubar cike da tausayin shi.

Bayan 10 minutes duk suna Zaune suna. Shuraim na Zaune sai sauke ajiyar zuciya yake.

Mama ce ta katse shirun da cewa"bawan Allah kai wane ne daga ina kake? Meya faru har yara suka biyo ka da jifa?"ta jero mai wa'inan tambayoyin.

Idanun shi jajazur ya kalle ta da k'yar ya bud'e baki cikin galabaita yace"...........

Nace"Ku biyo ni"?

*Godiya mai dumbin yawa sister Bilyn Abdul*??


 Don't forget to share and comments??


*UMMU BASHEER CE*?
[6/11, 17:53] +234 703 934 2613: *Y'AR SARKI CE!!!..*?

{It's All About Royal,Destiny,Betrayal and A Romantic Love Story}?


*NA*

 *UMMU BASHEER* *HASKE WRITERS ASSOCIATION*?
 (Home of Experts & perfect Writers)


 *^°IN DEVOTION To BILLY'N ABDUL ^°*

*Page 13~14*

 *Kuyi hakuri da jina shiru. Masu min magana nagode sosai wannan shafin naku ne Massoyan Y'ar Sarki Ce*?

 *Aunty Billy ina taya ki murnar fara litafin ki mai suna SIYYASA KO KABILANCI?... Allah ya bamu ikon amfani da darasin da yake ciki Ameen....*??

*Idanun* shi ya lumshe yayin da yaji kanshi na Sara mai ya bud'e baki da niyar magana sai dai ya kasa. Rik'e kanshi yayi da hannun shi biyu yana juya kan. Nan suka fahimci kanshi ke mai ciwo wani D'aki Mama tasa Jidda ta bud'e d'akin a gyare yake nan suka sa ya Shiga dan ya d'an samu Hutu.


Tunda Shuraim ya kwanta bai farka ba sai k'arfe shidda. 


Mama dai sai jajan ta halin da yake ciki suke da tausaya mai. 

Gaba d'aya wani irin kallo yake bin d'akin dashi yana mamakin a ina yake. Ganin kofa yasa ya bud'e ya fito waje suna Zaune a tabarma suna gyaran zogale. Wani irin kallo yake musu kamar ranar ne ya fara ganin halita.


Jidda ce tayi mai Sannu tare d d'aukar wani kujera ta ajiye mai dan ya zauna.

Zama yayi tare da yana rik'e da kanshi.

Mama ce tasa suka kawo mai abinci. Ai ko yaci sosai dan ji yake cikin shi ba komai bayan yaci yasha ruwa Mama ta Zauna tare da k'ara tambayar shi a karo na biyu cewa wane ne Shi kuma daga ina yake?


"Ban sani ba nima bansan wane ni ba gaba d'aya bansan meya sameni ba. Ya Akayi nazo nan duk ban sani ba" maganar da yayi kenan cikin wata irin damuwa.


Hankalin su gaba d'aya ya tashi ganin fa dagaske ya manta komai baya iya tuna komai na Rayuwar shi. Nan tayi ma Ramla magana cewa taje ta kira Malam Ya'u.


Koda Ramla taje k'ofar gidan malam Ya'u ta same shi yana alwala dan zuwa masallaci. Bayan ta gaishe shi ta fad'a mai cewa maman su na son ganin shi. Yace bayan magriba zai je nan ta koma ta fad'a ma Mama.


Ana idar da sallar magriba sai ga Malam Ya'u.

Bayan sun gaisa mama ta fad'a mai duk halin da ake ciki. Malam Ya'u ya tausaya ma Shuraim nan ya k'ara tambayar shi yace yayi K'okari yaga ko zai iya tuna wani abu a Rayuwar shi sai dai ya kasa tuna komai shi kanshi babban damuwar shi rashin Sanin wane ne shi suwaye iyayen shi da y'an uwan shi ba zai iya tunawa ba.

Malam Ya'u yace zai dawo da safe suje gurin liman domin fad'a mai halin da ake ciki.

Washegari da asubah

Malam Ya'u da Shuraim suka je massalaci nan suka samu liman Malam Ya'u ta fad'a mai komai Liman ya tausaya mai tare da mai tambayoyi sai dai shiru ba ansa nan yace Idan safe tayi su zo zasu je gurin wani babban malami.

Haka ko Akayi sunje gurin Malamin nan har Ruk'iyya Akayi ma Shuraim wai ko aljanu ne sai dai ba komai. Daga karshe suka gano sihiri ne akayi mai wanda ya mantar dashi tunanin shi da ko shi wane ne.

 Bayan dawowan su gida Malam Ya'u ya fad'a ma Mama komai nan ta k'ara jin tausayin shi. Sannan suka d'auki niyyar mai magani dan tunanin shi ya dawo.

An d'auki kwana biyu ana mai magana sai dai babu cigaba sai godiyar Allah. 

Nan Mama ta tari Malam Ya'u da maganar inda Shuraim zai zauna tunda ita yara mata take dashi kuma yanzu bata da miji ba zai yuwu su zauna dashi haka ba. Malam Ya'u yace ta kawo magana mai kyau ko shi yana da niyar mata magana ya bari ne a gama mai magani.

Nan yace zai d'auke shi ya zauna a gidan shi shine zai d'auke shi kamar d'an shi dan dama yaran shi uku mata kuma duk sunyi aure akwai d'aki da zai sa a gyara mai sai ya koma can da zama. Sannan shi da Liman sun bashi sunan *AHMAD SALIM* tunda basu San sunan shi na gaskiya ba. Kowa kam sun yaba da sunan.

Su jiddah da Ramla basu so komawar shi gidan Malam Ya'u ba dan har sun saba dashi sun d'auke shi a matsayin Yayan su.

Bayan komawar Salim (Shuraim) gidan Malam Ya'u ya nema Sana'a ya fara yi. Yana matukar son su yanda suka damu dashi har suka yarda dashi suka d'auke shi a matsayin D'a ba tare da sun guje shi ba bare suyi tunanin ko shi mugu ne.

Ya d'auki Malam Ya'u a matsayin Mahaifin shi dan Baba yake kiran shi. Yana zuwa gaishe da Mama suyi ta hira da Jidda da Ramla.

A duk lokacin da zai zo Jidda takan samu kanta cikin wani irin farin ciki. Gashi tana yawan zuwa gidan malam Ya'u cewar taje gaishe da Umma (matar malam Ya'u) nan ko kawai dan taga Salim ne.

Har girki takeyi na mussaman ta kai gidan tace ta kawo mai. Ramla ko dariya takeyi tace wai tana ji da Yayan su ta daina ma ji da ita sai ta b'ata rai sai jiddah ta fara wayancewa.

*MASARAUTA*

Lokacin dawowan aiki yayi Shaheed ya dawo gida sai daya yi knocking side d'in Shuraim yaji shiru sai yayi tunanin ko ya kwanta ne dan shima bai dawo gida da wuri ba.

Har washegari da safe ya Shiga flat d'in Shuraim but sai yaga Kofa a bud'e koda ya Shiga baiga alamar yana nan ba. Ya Shiga gurin mai martaba ya gaishe shi amma sai yayi mamaki da mai martaba ke tambayar shi ina Shuraim dan yasan dole yazo gaida mai martaba kafin yaje aiki.

Da zai Shiga mota ne ya lura babu motar Shuraim sai yayi tunanin kawai ya wuce hospital ne may be kiran emergency ne Akayi mai kunsan likitoci.

Straight hospital d'in Shuraim ya nufa sai dai ba karamin girgiza yayi ba lokacin daya ga phone. System da motar shi va sannan aka sanar mai tun jiya basu ganshi ba sunyi tunanin ko gida ya tafi. Har gurin maigadi shaheed yaje sai dai maganar da maigadi ya fad'i ta k'ara girgiza Yarima shaheed. Fad'a mai yayi yanayin da Yarima Shuraim ya fito yayi.

Hankali a tashe a dinga nemar Shuraim duk inda yasan zai ganshi har da abokanen su sai dai babu Yarima Shuraim babu alamar shi. 

Komawa Masarauta yayi ya fad'a ma mai martaba halin da ake ciki. 

*Abu kamar wasa fa*(Na Rahmat Nalele) an rasa Yarima Shuraim har gidan radio da television an baza labarin nemar shi a gaba d'aya social media. Ai nan da nan duniya ta d'auka da batan d'an sarki Abdul-Azeez Bina Wato Yarima Shuraim Abdul-Azeez Bina.

Kamar daga sama sai ga mutanen kasar waje sun zo Wato Aminin sarki Daddy'n su Noor.

Noor dama tunda taji batan Yarima Shuraim take rusa kuka dan tana massifar kaunar Shuraim.

Bangaren Fulani kuwa sai murna take kamar ta Zuba ruwa a kasa tasha haka take ji sai dai bata nuna murnar ta ba dan sai jajantawa take ita ma tana nuna damuwar ta.

Nan tasa Baiwar ta sa'ade da taje ta kira mata laminde. Bayan baiwa sa'ade ta kira laminde ne Fulani ta rufe ta da fad'an ya Akayi bata sa ma shaheed  maganin ba sai Shuraim kad'ai.

Laminde tuni ta fara had'a zufa baiwa sa'ade ce ta daka mata tsawa cewa tayi masu bayani.

Jiki na rawa ta fad'a masu cewa Shaheed baici abincin bane amma tasa mai.

Wani kulin kud'i Fulani ta jefa mata cikin isa tace"Gashi nan ki d'auka ki bar masarautar nan tun kafin wani abu ya fito daga bakin ki ki b'ace bat kar in sake jin labarin ki a duniyar nan. Ki kuma dinke bakin ki Idan ba haka ba Rayuwar ki tana cikin had'ari"

Cikin tsoro ta d'auka tana godiya yayin da take ta zufa har zata fita baiwa sa'ade ts daka mata tsawa"ke gyara natsuwar ki domin kar mutane su fahimci wani abu. Sannan kiyi yanda Aka umarce ki a yanzu d'in nan ba sai anjima ba."

Daidai tawa tayi sannan ta fita. Yayin da ko minti goma bata k'ara ba a masarautar ta tafi k'auyen su bayan tayi k'aryar zata je duba maman ta s k'auye ba lafiya ta fad'a ma wanda suke tare.

An d'auki sati uku ana ta bincike da nemar Yarima Shuraim sai dai labari. Shaheed ya rame dan ko abinci baya ci. Kai in takaice muku har kwanciya a hospital sai da Shaheed yayi.

Haka mai martaba a tsaye ya fara ciwo. Gaba d'aya Masarautar Hankalin su a tashe yake na rashin Yarima Shuraim.

Aminin Sarki da iyalan shi haka suma suka koma Canada cikin rashin jin labarin Shuraim. Noor ko tayi kuka har sai da ta kwanta ciwo.


K'AUYE

Rayuwa tana cigaba da tafiya cikin ikon Allah da yardar shi.

Salim Na jin dad'in rayuwa a k'auye tare da wanda ya d'auke su a matsayin iyaye da  y'an uwa.

Rayuwa tana cigaba da tafiya yayin da Jidda Tun bata gane mai take ji game da Salim ba har ta gane cewa son shi take sai dai ranar taci kuka domin tasan ba lalai bane ace shi yana son ta. Bata bari kowa ya gane ba sai dai abinda bata sani ba shine tuni Mama ta gano ta. Ita kan ta Maman ta ta Zuba mata ido ne.

Yayin da Zuciyar Salim ke cike da kaunar Jidda tun ranar daya fara ganin ta sai dai yana tsoron fito da sirin zuciyar shi dan yasan ba lalai bane a yarda baran ma shi da bashi da Asali. Dole yayi shiru sai dai duk lokacin daya gan ta sai gaban shi yayi ta fad'i. Yana mata wani irin so wanda yafi k'arfin a kira shi da massifar so.

Salim ya kasa hakura dan har wani zazab'i yake akan kaunar ta. Nan ya yanke ma kanshi hukuncin sanar da ita sirin zuciyar shi sannan duk sallah yana rokon Allah ya malaka mai ita a matsayin matar shi  wata rana da daddare yaje gidan dan bayyana mata sirin zuciyar shi.

Jiddah suna Zaune aka ce ana sallama da ita ai nan ta b'ata rai dan abin da ta tsana kenan. Ai ko nan Mama ta sa dole sai taje hijab tasa sai murgud'a baki take dan haushi Ramla na dariya tana tsokanar ta.

Ba karamin mamaki tayi ba lokacin data fita taci karo da Salim cikin yadi boyel arsh colour yayi matukar kyau dan akwai hasken farin wata Gana lantarki.

Gaishe shi tayi cikin jin d'auyin shi tace ya shigo cikin gida sai dai ya fad'a mata yau ba yazo ya shigo bane.

Tayi mamaki amma tayi shiru. 

Baiyi kasa a gwiwa ba ya sanar mata da yanda yake kaunar ta Kusan suman tsaye Jidda tayi dan ta rasa farin ciki za tayi ki sabanin haka.

Sosai taji kunya tayi kasa da kai nan dai ya gane kunya take yace ya bata kwana biyu ta bashi ansa shi. Nan ta shige gida cikin farin ciki.

Mama da Ramla dake Zaune suka bita da kallon mamaki ganin ta shigo cikin farin ciki.

Ramla har tsokanar ta take wai da alama Mama tayi suriki kenan haharan ta tayi ta shige d'aki.

In fad'a muku tunda ga nan fa shikenan sai Salim da jiddah suke wata irin zazafan Soyayya. Kullum da daddare sai yazo har gida yakan shigo su sha hira Mama ta gano Soyayyar dake tsakanin su.

Yanzu kam koya ya gane Soyayyar dake tsakanin su kuma Malam Ya'u da Mama sun amince su had'a su aure.

Dangin Mahaifin su Jidda ko Sam suka ce basu yarda ba ya za'ayi a had'a Jidda da marar Asali. Haka y'an k'auye ma sai gulmar suke wai za'a had'a Jidda aure da wanda baasan Asalin shi ba. Nan dai aka sa ranar aure wata biyu masu zuwa.


Salim da Jiddah ko murna suke sosai domin zasu kasance ma'aurata.

MASARAUTA

Zuwa wannan lokacin Shaheed ya d'auki hakuri akan batan d'an uwan shi.

Yanzu duk wani abu da yakeyi marar kyau ya daina ko fita ba yayi sai dai Idan Zai je aiki kawai. Yanzu an dage da addu'oi Allah yasa agan shi.

Tunda Mai martaba ya gano Shaheed yanzu ya bar wa'inan halayen nashi sai yaji dad'i. Nan ya sa aka kira shi ya sanar dashi cewa ya fito da matar aure ko  a d'aura mai aure da wata ai fa yaji tsoro dan baya son auren had'i ko Kad'an.
Lokacin da aka bashi ya fito da matar aure yayi sai dai shi bai samu wacce yake so ba
Fulani tunda ta gane y'ar ta tana son shaheed sai tayi amfani da hakan dan shirya wani abu nata.
Nan take sa yar tana shishige ma shaheed. Sai ta d'auki shiri taje gurin shi da sunan taje ta ya shi hira a haka ya d'an saki jiki da ita dan yanzu bashi da wani wanda zai fad'a ma damuwar shi. To Idan suna hira sai yaji ta damu da Shuraim da halin da yake ciki sai yaji ta kwanta mai a rai.
Sannu a hankali sai suka saba shi dai ba wai yaji yana son ta bane dan shi ki Kad'an Fulani mahaifiyar ta bata kwanta mai a rai ba gani yake kamar da sa hannun ta a batan Yarima Shuraim.
Ya lura Aliya tana son shi dan haka sai shima ya amince suka fara Soyayya ai murna da farin ciki gurin Aliya ba'a cewa komai. Lokacin da Mai martaba ya k'ara tambayar shi sai ya gabatar da Aliya a matsayin wacce zai aura ba dan komai yayi hakan ba sai dan yana son gano ko FULANI ce tayi sanadiyar batan d'an uwan shi ta hanyar auren Aliya.

Ansa ranar d'aurin auren su yayin da aka fara shirye shirye domin auren D'an sarki ne.

K'AUYE

A yau dubanin mutane suka shaida d'aurin auren Salim Ya'u (Shuraim Abdul-Azeez) da Amaryar shi Jiddah Ahmad akan sadaki mafi daraja.

Ango da Amarya sai farin ciki suke anci ansha taro yayi taro an watse lafiya bayan an kai Amarya jidda d'akin ta wanda yake gidan Malam Ya'u.

A wannan Daren Ango Salim bai d'aga ma Amarya Jiddah k'afa ba dan sai daya angwance? sis Billy nayi shiru?

Amma fa Jidda taci kwakwa au?.

A MASARAUTA

A Yau aka d'aura auren Shaheed Abdul-Azeez Bina tare da Aliya Ishaq akan sadaki mafi daraja da albarka. Gaba d'aya masarutar ana cikin farin ciki sai dai Shaheed yana jin rashin d'an uwan shi sosai.

Da daddare aka kawo Amarya bangaren Shaheed inda yasha gyara an kashe dukiya. Fulani sai murna take domin burin ta ya kusan cika....

*Dan Allah kuyi comments fah Idan ba haka ba sai bayan sati biyu*?

*UMMU BASHEER CE*?
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 620 06-09-2019, 02:37 PM
Last Post: Gimbiya
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 556 06-09-2019, 02:22 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 2,121 07-16-2018, 03:34 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 8,304 06-28-2018, 10:16 AM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 7,409 06-24-2018, 12:15 PM
Last Post: GimbiyaUsers browsing this thread: 1 Guest(s)