Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER*
#1
*Y'AR SARKI CE!!!..*?

{It's All About Royalty,Destiny,Betrayal and A Romantic Love Story}?


*NA*

 *UMMU BASHEER*


 *HASKE WRITERS ASSOCIATION*?
 (Home of Experts & perfect Writers)


 *^°IN DEVOTION To BILLY'N ABDUL ^°*
*Page 7~8*


 *Gaba* d'aya SHURAIM bai ji dad'in abinda ya faru ba sai dai bai San meyasa d'an uwan nashi yayi hakan ba. Sarki murmushi kawai yayi nan suka cigaba da tataunawa. Bayan sun gama SHURAIM Straight side d'in SHAHEED ya nufa.

Zaro ido yayi lokacin da yaga SHAHEED ya d'aga kwalbar giya zai sha. Da sauri ya K'arasa ya k'wace kwalbar.

A fusace yace"SHAHEED meyasa baka jin magana ne wai har sau nawa zan hana ka shan wannan abin ga tarin zunubi sannan illa ce ga lafiyar ka meke damun ka ne"

 "Ka bani kawai in sha ko na samu sukuni. Babu wanda ya damu dani ko da wani abin zai same ni"ya fad'a yana son Karb'a.

Ture shi SHURAIM yayi"mai kake nufi? Kullum ina hana ka saboda mene? Saboda kai k'anni nane d'an uwa na na jini meyasa zan bar ka har ka fad'a wani halin?"


 "Dan Allah ka fita ina buk'atar kad'aicewa ni kad'ai"

 "Kora na kake yi? Akan me? Akan na fad'a maka gaskiya ko. Ko kuma akan ina son ka na damu da halin da zaka Shiga" ya fad'a cikin wani irin yanayi tare da juya baya zai fita.

Da sauri SHAHEED ya rik'o hannun shi. Juyowa SHURAIM yayi. SHAHEED ne ya had'a hannun shi biyu alamar sorry tare da rik'e kunnuwan shi biyu.


Sosai tausayin d'an uwan nashi da son shi ya cika make zuciya nan suka rungume juna.

 "Kayi hakuri frustration ne yayi min yawa ji nake kamar zan mutu shiyasa na D'auko wannan dan in sha ko zanji sanyi a zuciya ta"

 
 "A'a kar ka sake yin hakan dan babu abinda take haifarwa sai cuta. Fad'a min meke damun ka?"


  "No just forget it"

 "Why?"

  "Babu wani abu yanzu kawai barci nake son yi"

 "Are you sure?"

   "Yeah thanks for the care"

 "Na barka lafiya ka huta da kyau domin akwai stress tare da kai later zan kawo ma drugs"

 Fita yayi cikin jin tausayin d'an uwan nashi yana addu'ar ko mene ne ke damun shi Allah ya yaye mai.


SHAHEED murmushi mai ciwo yayi yana son d'an uwan shi amma ya lura shaid'an na son had'a su. Yasan SHURAIM na son shi

Wata budurwa ce black tana da d'an kyaun ta sanye take da riga da skirt sunyi fitting d'in ta sai veil da ta dauro shi a wuyar ta. mota ta fito tana tafiya kamar baza ta taka kasa ba. Sai yatsina fuska take.

SHAHEED ne zai Shiga mota da sauri yaga ta K'araso gurin shi tana zuwa tace"Ya SHAHEED ya kake"

 "I'm fine ya kike"

 "Qalau zaka fita kenan?"

 "Yeah"

   "Ko inzo in raka ka ne?"

 "No thanks *ALIYAH*  keda kika zo yanzu ko gida baki Shiga kinga Mami ba. Don't worry bara na wuce" ya fad'a yana Shiga mota.

B'ata fuska tayi tare da barin gurin cikin gida ta Shiga  parlour'n Mami ta Shiga tana zuwa ta gan ta Zaune tana shan fruits jikin ta taje ta fad'a.

Mami tace"kai ALIYAH wai yaushe zakiyi hankali ne ni d'aga ni kar ki karya ni"

Dariya tayi"kai Mami nah yaushe zan iya karya ki"

 Mami ne ta d'aure fuska ta kalla bayin dake parlour'n"kai Baku ganin y'a ta tazo ne baza Ku kawo mata drinks ba"

Jiki na rawa ta bada hakuri tayi saurin fita dan kawowa.

Mami tace duk su fita za tayi hira da y'ar ta.


Suna fita ALIYAH tace"Mami Nazo miki hutu ne fa dan ba yanzu zan koma ba"

 "Kai amma da naji dad'i Allah yasa Baban ki dai ya amince"

 "Ai ya amince yanzu gani ga ki"

Dariya duk sukayi sannan suka cigaba da hira. D'akin da take sauka Idan tazo nan ta Shiga tasa aka shirya mata kayan ta a drawer dama Idan tazo haka takeyi sai tayi ta mulki da nuna isa.

Fad'awa tayi kan gado tana murmushi domin babban dalilin ta na zuwa Hutu saboda SHAHEED ne. Allah ya jarabce ta da kaunar shi. Tun ranar da suka dawo UK Akayi had'a musu walima ya sace zuciyar ta sosai take mutuwar son shi.SHAHEED ko yana mamakin ALIYAH  yanda take wani mai shishigi .shifa baya son mace mai rawar kai da surutu ga iyayi.


 *K'AUYE*


JIDDAH ce ke yin ma Mama kitso. Wata budurwa ce ta shigo bayan ta gaishe da Mama ta fad'a mata tana neman RAMLA ne. JIDDAH ce tace taje gidan kawar ta.

Mama tace"mene ne kike neman ta lafia dai ko"

 "A'a dama ta ara kud'i ne guri na shine tace zata bani tun wancan satin naji shiru ne nace zan zo in Karb'a"

 Mama sosai taji ba dad'i tace"nawa ne kud'in"


 "Dubu biyar ne"

Dukan su da mamaki suke kallon ta.

 "Mai RAMLA za tayi da kud'i har dubu biyar" cewar JIDDAH

 Mama tace"shikenan kije ki dawo zan baki"

Godiya tayima Mama ta tafi.

Mama wani hawayen bakin ciki ne ya zubo mata da sauri JIDDAH ta fara share mata ita ma cikin damuwa tace" Mama dan Allah ki daina zubar da hawaye. Ni kaina ban San meye RAMLA za tayi da kud'i haka ba bayan tasan bamu dashi"


"RAMLA bansan wata irin yarinya bace wacce bata sa komai a gaban ta ba sai kud'i mai zai sa ko yaushe take da dogon buri. Damuwa ta yanzu me tayi da kud'in meyasa ta Karb'a bashi ba tare da sani na ba"

"Mama addua zamu cigaba da mata komai nada lokaci zata bar hakan insha Allah. Dan Allah ki daina damuwa kar wani ciwo ya same ki. Duk duniya ke kad'ai kika rage mana" ta kare kamar za tayi kuka.


Wasu hawaye ne suka zubo ma Mama d'aki ta Shiga abinda ya bani mamaki shine wannan akwatin naga ta Ciro wani zobe na gold da d'an awarwaro ta rungume a kirjin ta tana kuka kamar ran ta zai fita amma tana yi ne a hankali dan kar JIDDAH taji.


Gab da magriba RAMLA ta shigo tana y'an wakokin ta. Mama wani mugun kallo ta jefe ta dashi sai da tasha jinin jikin ta.

Cikin d'an tsoro ta gaishe da Mama.

"Zo nan "

Jikin ta na rawa ta K'arasa.

  "Meyasa kika ci bashin mutane bayan kin San ba wai muna dashi bane kuma har dubu biyar"

 Cikin in ina tace"Mama dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan sake ba"

 "Tukuna ma tsaya mai za kiyi da kud'in?"

 "Am..dama....kawai... Ina.. Ina..."

Mama ce ta daka mata tsawa"kiyi min magana bana son shirme"

 "Mama Kawa tace ba lafiya shine naji bashin kud'in dan zasu asibiti kuma basu da komai"

 Mama dai bata yarda ba ta kyale ta ne kawai amma tayi mata fad'a sosai.


Lokacin da zasu kwanta barci. RAMLA ta kalla JIDDAH tace"Allah ya so ni da Mama ta gano ni"

 "Kamar ya" JIDDAH ta tambaya.

 "Hmm baki San wani abu ba. Ai k'arya na shirya ma mama dan ko na fad'a mata gaskiya ba barina za tayi ba. Kawa tace za'a  birthday party d'in ta Kinsan baban ta nada d'an kud'i to duk sauran kawayen mu za suyi anko da gudunwa da za'a bata shine naci bashin nan na siya anko da takalmi da gyale. Ina son ince zaki Asibiti ne gaida marar lafiya kinga Idan Mama ta bar ni sai inje party d'in"


 D'an zaro ido JIDDAH tayi jin abinda RAMLA ke cewa"kina da hankali kuwa. Mama ce ta koma sa'ar ki da har kike mata k'arya ko. Wai ma yaushe kika fara irin Rayuwar nan wai partyn qawa zaki. Anya RAMLA baki dau duniyar nan da zafi ba. Yanzu baki tsoron Allah kika yi ma Maman namu wannan k'aryar ko"


 "Kai JIDDAH to meye dan nayi haka. Nasan fa Maman nan ba wani bari na za tayi ba"

 "Zan baki zab'i biyu kuma dole ki d'auki daya a ciki. Ko ki fasa zuwa Party'n nan ko kuma in fad'a ma Mama gaskiya"

 Wani bakin ciki ne yazo ma RAMLA wuya lalai JIDDAH y'ar rainin wayau ce Wato zafi biyu ta had'a mata tasan Idan tace sai taje partyn Mama ta sani to baza ta bar ta taje ba anyi biyu babu kenan gashi ta sani kuma ta hana ta zuwa. Yanzu dai ya zama dole ta hakura da zuwa partyn.

 "Bazan je partyn ba na hakura dan Allah kar ki fad'a mata"


 "Bazan fad'a mata ba amma Kinsan bazan sa ido d'an Mama bata San komai ba sai nima in kyale ki ki fad'a halaka ba"

 Haka dai tayi mata nasiha wanda jin ta kawai RAMLA keyi.


A zuciyar ta kuwa tace sai ta rama hana ta zuwa party da tayi sai tayi Mata wani abin ita ma...


Share & comments??


   *Y'AR SARKI CE!!!*??


 *UMMU BASHEER CE*?
[6/9, 13:11] +234 802 797 9297: *Y'AR SARKI CE!!!..*?

{It's All About Royalty,Destiny,Betrayal and A Romantic Love Story}?


*NA*

 *UMMU BASHEER*


 *HASKE WRITERS ASSOCIATION*?
 (Home of Experts & perfect Writers)


 *^°IN DEVOTION To BILLY'N ABDUL ^°*


*Page 9~10*

 *Sanye* yake da  suit milk colour sai medical glass wanda ya k'ara mai kyau sosai ya d'aura lap court akai Hankalin shi na kan system wata nurse tayi knocking ta shigo.

 Sanar dashi tayi an kawo wasu sunyi accident gasu nan a emergency. Da sauri ya mik'e suka fita wani doctor ne yabi bayan su tare da nurse.

Bayan kamar wasu hours Dr SHURAIM ne na gani ya fito daga theatre room.

Office d'in shi ya nufa yana Shiga sai yaji phone d'in shi na ringing. Dubawa yayi yaga five missed call da sauri ya duba sai yaga SHAHEED ne d'auka yayi.

Cikin mawuyacin hali SHAHEED ke ce mai gashi nan zuwa hospital d'in driver zai kawo shi wani irin ciwon Mara yakeyi kamar zai mutu haka yake ji.


Ok kawai yace cikin minutes Kad'an sai gashi.

Yana zuwa already yasan damuwar shi dan haka drugs ya rubuta yasa aka kawo mai.

Kallon SHAHEED yayi tare da cire farin medical glass d'in shi"SHAHEED pls and pls for you health kasha drugs d'in nan it will help you and stress yayi maka yawa bayan haka nasan kana cikin damuwa. Dan Allah ka cire komai a ranka kar kasa ma kan ka ciwo"

Murmushi mai ciwo yayi"ta Yaya zan cire ma kaina damuwa bayan Kasan yanda Abba gaba d'aya yanzu yayi watsi da lamura na ko gani nafa baya son yi yanzu ya juya min baya" ya k'are cikin damuwa

Dafa kafad'an shi yayi alamar hakuri"kar wannan ya dame ka may be akwai abubuwan da sukayi mai yawa ne. Ni kaina bana jin dad'in haka"

 "Amma meyasa kai baya maka hakan sai ni. Meye laifi na"

 "SHAHEED I really don't know pls kayi hakuri yanzu dai ka fara shan maganin in gani a gaba na cause nasan ba zaka sha ba"

 "No pls kayi min injection kawai"

D'an murmushi yayi"no sai kasha drugs dinan"

Badan yaso ba dolle yasha yana b'ata fuska sai da yayi kusan 30minutes lokacin ciwon ya lafa sannan ya tafi.


*Doctor SHURAIM* kyawawan saurayi mai cike D'a kwarjini. Fari ne yana da kyau gashin shi bak'i ga santsi a kwance yake luf luf. Fuskar shi na zagaye da saje. Yana da dimples wanda Idan yayi murmushi ko dariya suke lotsawa muskili ne shi bai cika magana haka kuma baya son hayyaniya. Yana son yara sosai sau dayawa idan yaga yara sai ya d'auke su ko yayi masu wasa a lokacin ne za kuga murmushin shi. A Rayuwar shi yana son zama doctor domin taimakon al'uma. Shiyasa ya dage sosai ya karanci likitanci. Yana da son addini baya wasa da sallah ko Kad'an y'an mata basa gaban shi ko Kad'an dan yace bai ga mace mai natsuwa da kamun kai ba . ko yaushe y'an mata na kawo Kansu suce suna son shi ko kallon su baya yi. Haka kuma yana da tsafta.

Yana son d'an uwan shi SHAHEED wanda suka taso tun suna yara.

*Barrister SHAHEED* saurayi ne mai tashen y'an mata akwai son gayu kyakyawa ne. Karatun law yayi domin shi akwai shi da son bincike. Yana da fara'a da harka ga son mutane. Fari ne shi yana da manyan ido yanda Idan ya zaro ma su dole ka fad'i gaskiya dan tsoro. Yana d'an shan giya wanda wasu abokai ne da yake dasu a UK suka koya mai sai dai yak'i yarda ya kwanta da mace sai dai romancing da sauran su amma baya kusantar su. Domin ko yaushe SHURAIM cikin mai wa'azi yake. Sannan yana jin k'yamar yayi amfani da mace kuma wani ma yayi da ita ga kishi. Akwai shi da nuna isa da tak'ama ni ko nace ko dan jinin sarauta ne shida SHURAIM akwai mulki da izza.


SHURAIM da SHAHEED sunyi karatun su ne a UK tun secondary har university acan sukayi Abokin Mai martaba ne dake Zaune acan yake kula dasu domin a gidan shi suka taso. 


Alhaji ALIYU shine abokin mai martaba dasu SHURAIM suka zauna a gidan matar shi tana da kirki suna da yara uku akwai babban namiji ne sa'an su SHURAIM kuma abokin su ne *Saleem* sai macen *NOOR*  sai karamin wanda bai wuce shekaru goma ba.

Family'n nan suna son su SHURAIM haka Alhaji Aliyu yana da kirki haka suka taso a gidan suka d'auke su kamar iyayen su. Lokacin da zasu dawo ba karamin damuwa dukan su suka Shiga ba.


SHURAIM da SHAHEED sun taso tun suna yara sun shak'u da juna sosai.  Suna matuka ji da juna. Sun taso kamar y'an biyu ne. 


*K'AUYE*


"JIDDAH kinga wallahi kije fa mutumin nan yana son ki Allah"

 "RAMLA kar ki dame ni pls"

 "Kai ya JIDDAH ke ko kije mana kinga mutumin nan yana da hali kinga motar shima tana da kyau"

 Dafe kai JIDDAH tayi"wallahi bansan ranar da za kiyi hankali ba. Yo ni ina ruwana da motar shi. Kinga ni maza basa gaba na yanzu"

Murgud'a baki tayi tare da jin haushin JIDDAH d'in taso taje ko mutumin zai d'an basu kud'i. Cikin haushi ta fita tana zuwa d'akin Mama ta Shiga ta fara gaya mata k'arya da gaskiya wai JIDDAH tana ma wani wulak'anci har da cewa mutumin yana da kirki. Ai ko Mama nan ta fito ta rufe JIDDAH da fad'a tace kuma dole ta fita. JIDDAH na kuka tasa hijab ta fita RAMLA d'aki ta shige tana dariya har da rik'e ciki.

Wani mutum ne bak'i gashi da jiki. Yana jingine da mota sai kada key yake.

K'arasawa tayi ta gaishe shi. Nan ya washe mata hakorin shi wanda sai da JIDDAH ta kawar da kai domin yana fara magana taji saukar yawo a fuskar ta yana magana yana fesar da yawo. JIDDAH kamar za tayi kuka haka yayi ta surutu ita dai kan ta na kasa har ya gama yayi Mata sallama ya tafi.

Haka ta shigo gidan jikin ta duk a sanyaye bata San meyasa Mama ke mata hakan ba ita fa bata son Tsayawa da kowa ni namiji ne.

Mama tana ganin ta sai ita ma bata ji dad'in fad'an da tayi mata ba. Bayan sallar isha'i ta zaunar dasu dukan su su biyun tayi masu nasiha sosai jikin JIDDAH yayi sanyi sosai dan koda is suyi barci sai da tayi kuka ta tuno da mutuwar Mahaifin su. RAMLA ma jikin ta yayin sanyi.


Cikin ikon Allah Mama ta samu ta biya masu kud'in zana jarabawa. Sosai suka ji dad'i baran ma RAMLA sarkin rawar kai. Sosai sukayi ma Mama godiya da addu'a. 

Sosai suka dage da karatu dan har basa son fad'i kodan su faranta ran Mama yaci ace sun dage sunci. 


Cikin nasara suka fara jarabawar Mama tana bin su da addu'oi. Har suka kamala lafiya sai jiran result.


Bayan yan watani  results d'in su ya fito kuma sunyi nasarar ci. Sai murna sukeyi. Results yayi kyau Malam Ya'u yayi masu nasiha sosai dan ya d'auke su kamar yaran shine. Suma suna mutunta shi.


 KINGDOM

nasan masu karatu suna son Sanin mene ainihin labarin MASARAUTAR Abdul-Azeez Bina?


*waiwaye adon Tafiya*


MASARAUTAR  ABDALLAH BINA


SARKI ABDALLAH BINA sarki ne mai gaskiya da adalci da taimakon talakawa yana da mata biyu Uwargida  HAFSA mace ce mai kirki da Sanin ya kamata auren soyaya ne sukayi da sarki Suna da yara biyu  *Abdul-Kareem da Abdul-Azeez* yaran su sun taso cikin tarbiyya nagari a gidan sarauta yaran su biyu sun shak'u da juna sosai yanda d'aya baya iya kwana d'aya ba tare da d'aya ba. Komai nasu iri d'aya ne kamar y'an biyu har kayan sarautar such iri d'aya ce.Suna da shekaru goma sarki ya k'ara aure sai dai ita matar ba y'ar sarauta bace HABIBA sunan ta. Makirar mace ce bata da kirki ko Kad'an tunda taga ta auri sarki sai take Zuba Issa yanda take so. Bayin gidan sun tsane ta ko Kad'an bata da kirki. Tunda ta shigo gidan take bala'in kishi da Sarauniya Hafsat wacce babu ruwan ta da ita amma ita ta tsane ta tana bakin cikin yanda take da yara biyu maza gashi tunda sarki ya aure ta ko b'ari bata tab'a yi ba ai ko ana ta gulmar bata haihuwa. An d'auke shekaru masu tsawon har hospital taje aka tabattar mata baza ta tab'a haihuwa ba sai dai bata yarda ba tace haihuwa na Allah ne. A haka har su Abdul-kareem suka girma.


Sunyi karatun su har sun kamala sun fara aiki anan ne sarki yace lalai sai sunyi aure. Abdul-kareem yana da wacce yake so *MALEEKA* nan aka nema mai auren ta Abdul-Azeez ko har lokacin baiga macen da tayi mai ba har yayan shi na cewa ya tsaya ruwan ido. 


Ana cikin haka Sarauniya Habiba taji ai shi bashi da wacce zai fito da ita. Nan ta had'a plan tunda ba haihuwa takeyi ba tasan ko sarki ya mutu bata da wani gado kamar wancan Sarauniya Hafsa d'in shiyasa taje ta samu K'anwar ta ta fad'a mata komai na plan d'in ta tace tana son ta had'a y'ar K'anwar ta da yarima Abdul-Azeez.


Nan suka had'a makircin su. Koda *MARYAM* Taji Wato y'ar K'anwar Sarauniya Habiba. Ba karamin farin ciki tayi ba domin Idan taje gidan tana ganin Yarima tana son shi gata da son sarauta ai nan tayi ta farin ciki. Nan suka had'a plan d'in yanda abin zai kasance.


Sarauniya Habiba cikin kissa da kisisina ta shawo kan Sarki Abdallah akan ya amince a had'a Abdul-Azeez da Maryam aure.  Nan dai ya amince domin baya son taga kamar ko bai nuna mata Su Abdul-Azeez yaran ta bane. Ai ko taji dad'i kamar me nan ta sanar da y'ar uwar ta akan a fara shirya Maryam zata zauna a masarautar ne su fahimci juna da Yarima Abdul-Azeez.

Sarauniya Hafsa duk da tasan halin Kishiyar ta amma bata nuna bata son auren ba.  Sai dai bata ji dad'i ba.

Lokacin da Abdul-Azeez yaji zai auri y'ar K'anwar Kishiyar Maman Shi ai Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba. Domin shi baya son auren had'i yafi son ya samu wacce yake so kamar yayan shi.


A haka dai ba tare da yana so ba aka sa rana. Ko yaushe Maryam itace mai makale mai a haka har ranar bikin yazo aka had'a dana Abdul-kareem.Bayan d'aurin auren kowa ce da flats d'in ta. Tun bayan auren sai ya zamana Maleeka da Maryam basa shiri domin kam halin su ya banbanta. Maleeka mace ce mai hakuri tana son mutane tana kula da mijin ta cikin soyaya. Suna zaman lafiya. Sannan tana mutunta surukar ta. Sabanin maryam da bata da kirki ko Kad'an akwai ta da son mulki ko Kad'an basa shiri bare tana ganin Maleeka anfi son ta sai ta tsane ta. Gashi taga ita suna zaman lafiya da soyaya da mijin ta. Kinsan ko yanda dai wasu Matan wa  da kani yanda dai sukeyi.Maleeka ta haihu namiji ta haifa kwana biyu tsakani Maryam ma ta Haifa namiji. Sai dai tayi bakin cikin yanda Maleeka ta Haifa namiji har bayan suna tana bakin ciki.Bayan shekaru biyar abubuwa dayawa sun faru ciki har da rasuwar sarki Abdallah wanda mutuwar ta girgiza mutane dayawa. Kowa na yabon halayen shi nagari.


Bayan rasuwar sarki mutane suka zab'a nada Abdul-kareem sarki domin shine babban d'an sarki. Lokacin da Maryam taji kamar za tayi hauka meyasa za'a ce wai maleeka ta fita ai nan tayi ta zuga Yarima Abdul-Azeez akan kar ya yarda sai dai baibi takan ta dan Mahaifiyar su a tsaye take akan su bata son abinda zai raba mata kan yara dan ta basu tarbiyya tagari da yanda zasu kaunace junan su.


Yarima Abdul-kareem ya zama sarki. Maleeka ta zama Sarauniya wannan abin ya bakan ta ran Sarauniya Habiba da Maryam kamar zasu mutu dan bakin ciki.


Sarauniya Habiba saboda tsananin takaici kawai an wayi gari ne ta bar MASARAUTAR. Mahaifiyar Su Abdul-kareem ko tun lokacin ta kwanta ciwo. Ko yaushe yaran ta cikin kyautata mata suke tare da Maleeka. Maryam ko zuwa gaishe tama ba tayi .Duk wani makirci da hatsabibanci irin na wasu Matan sai da Maryam tayi yanda za tayi tasa aka ba Sarauniya Maleeka maganin hana haihuwa ba tare da Sanin ta ba. Domin wacce ta aminta da ita ce aka sa wanna abin.Ana cikin haka wata rana kwatsam Abdul-Azeez ya had'u da y'ar Sarkin Adamawa Wato Gimbiya *BILKISU* mai gadon zinare. Tunda suka had'u yaji duk duniya babu macen da yake so sama da ita. Ita ma tunda ta had'u dashi take mai wani irin kauna wanda yafi k'arfin a kira shi da sunan so.


Gimbiya BILKISU kyakyawar budurwa ce kasancewar ta jinin FULANIN Adamawa y'a tali d'aya gwal a gare shi wanda aka d'aura mata tsananin so da kauna.Soyayyar Yarima Abdul-Azeez da Gimbiya Bilkisu yayi k'arfi sosai kwatsam ba zato ba tsamani aka ji zai aure ta. Maryam Hankalin ta yayi mugun tashi. Ba shiri tayi gurin boka dan a hana auren amma ya fad'a mata hakan ba zai yuwu ba.

.
Maryam tana ji tana gani Akayi mata kishiya babu yanda za tayi sai dai taci alwashin raba su ko ta halin Yaya ne. Domin tana da azababan kishi irin na haukar na

Gimbiya Bilkisu tana da matukar hakuri da juriya tare da biyayya wannan yasa tayi nasarar sace zuciyar mutanen MASARAUTAR kowa na son ta domin kyawawan halayen ta. ita da Maleeka suna shiri sosai kamar ya da K'anwa. Ana cikin haka aka wayi gari Allah yayi ma mahaifiyar su Abdul-Azeez rasuwa. 

Mutuwar ta girgiza mutane domin har ta fara Samun sauk'i sai kuma ciwo ya dawo sabo har ya rikice.

A haka har Akayi 40days da rasuwar ta yaran ta mutuwar na girgiza su. 

Shirin da Maleeka da Bilkisu sukeyi yana k'ara tunzura zuciyar Maryam tana bakin cikin hakan burin ta d'aya shine ta raba kan su. Amma hakan ya gagara.


Rashin k'ara haihuwa yana damun su Sarki Abdul-kareem da matar shi Maleeka amma sunyi hakuri sun d'auki k'addara kila dama Allah ya rubuta D'a d'aya zasu Haifa.

Rana d'aya kwatsam wani mumunan labari ya faru a masarauta Wato Yarima Abdul-Azeez ya saki Bilkisu babu wa'inda ba suyi mamakin hakan ba domin ansan tsananin soyayar dake tsakanin su tare da halayen ta nagari.

Maryam kamar ta Zuba ruwa a kasa tasha haka ta dinga shi.

Sai dai ita kanta Maryam d'in haihuwa ya tsaya mata dan bata sake Samun wani cikin ba. Kamar tayi hauka ko duk da hakan dai bata hakura ba duk wani magani Idan dai akace na haihuwa ne sai tasha shi a haka har ta kamu da Cancer na mahaifa. Sai dai bata sani ba domin lokacin data fara ciwon ba'a bari likita ya fad'a mata ba dan kar ta Shiga damuwa.

Wata rana Sarki da Maleeka sun tafi kai ma iyayen ta ziyara sukayi accident???

Hospital aka kai su rai a hannun Allah ko kafin akai Sarauniya Maleeka har ta ansa kiran mahalicin mu. Emergency aka nufa da sarki Abdul-kareem.


Hankali tashe Yarima Abdul-Azeez da wazirin sarki suka isa hospital d'in. Ganin halin da yayan shi yake ciki ba karamin tada mai da hankali yayi ba. Jini ta hanci ta baki haka yake Zuba.

Abdul-Azeez na kuka ya isa gare shi ya rungume shi a jikin shi yana kuka yana cewa kar ya tafi ya barshi bashi da kowa sai shi.

Sarki Abdul-kareem da k'yar yake magana cewa yake"D'ana D'ana ka kular min da D'ana na baka amanar d'ana kar yayi maraici kar ya tab'a Sanin ba kai ka haife shi ba. Dan Allah na baka amanar D'ana" wannan shine kawai Kalmar da yake fad'i domin yana son d'an shi kamar me.

A hannun Abdul-Azeez Sarki Abdul-kareem ya rasu. Wannan rasuwar ta girgiza Abdul-Azeez da sauran mutane baki d'aya.


MASARAUTAR Nan sunyi babban rashi.


Bayan wani d'an lokaci Aka nad'a Abdul-Azeez a matsayin Sarki. Maryam an zama Sarauniya duk da ko yaushe dai tana cikin ciwo ne.


Sarki Abdul-Azeez ya d'auki d'an yayan shi ya rik'e shi Amana kamar yanda yayan yace.


Ana wata ga wata Sarauniya Maryam bata d'auki tsawon lokaci ba ta kwanta ciwo. Gaba d'aya ta canza kamani a haka wata rana da daddare ta rasu.

Wannan rasuwa ya k'ara tayar da Hankalin Sarki Abdul-Azeez yana ganin yana ta rasa na kusa dashi. Yaji mutuwar ta koda bai son ta amma kunsan ance mata da miji. Sarauniya Habiba ta da da mahaifiyar Maryam sun zo. Dan ba karamin girgiza sukayi ba.


Bayan wasu shekaru


Sarki ya had'a kan yaran shi biyu ya tura su kasar waje gurin wani aminin shi dan suyi karatu a can Wato UK.Waziri ne da sauran mutane suka sashi a gaba sai yayi aure. Sarauniya Habiba mussaman tayi ta kawo mai mata amma yace shi baya ra'ayin yin wani auren domin ya fitar mai a rai tun lokacin daya rabu da Gimbiya Bilkisu.


A haka dai ya samu wata bazawara yar ta d'aya ta rabu da mijin nan ya aure ta dan ya kare mutuncin kan shi ba wai dan yana son ta ba. Koda yake ba laifi ya d'an sama mata guri a zuciyar shi ganin yanda take son shi da yaran shi dake UK.


FULANI itace wacce Sarki Abdul-Azeez ya aura. Mace ce mai nuna kyawawan halaye a waje a cikin zuciyar ta kuwa zallar mugunta da makirci ne. Ta iya siyasa. Baza ka tab'a gane ainihin ta ba. Shu'umar kenan.


Y'ar ta takan zo mata hutu lokaci zuwa lokaci Wato Aliyah. Idan tazo akwai ta da iyayi kamar itace y'ar sarkin haka take nunawa.


Sarki yakan kai je UK ganin yaran shi wani lokacin yana zuwa da Fulani. Fulani tunda taga manyan yaran sarki sai Hankalin ta ya tashi baran ma dai SHAHEED tasu bai zo d'aya ba ko Kad'an baya raga mata cikin wasa da dariya yake fad'a mata magana ta tsane shi sosai.


Sarki yaja kunnen mutane akan yaran shi biyu ne kar wanda yace akwai wanda ba nashi ba ko nan gaba to wannan sirin an b'oye shi.


Fulani bata kaunar su SHURAIM ko Kad'an. A haka ne har suka dawo kasar su ta haihuwa bayan dumbin shekarun da suka kwasa a UK.


*Wannan shine labarin MUSARAUTAR SARKI ABDUL-AZEEZ BINA a takaice*??


   Share and comments??


*Ku cigaba da Bina*


*UMMU BASHEER CE*?
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 830 06-12-2019, 12:04 AM
Last Post: Gimbiya
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 549 06-09-2019, 02:22 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 2,118 07-16-2018, 03:34 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 8,280 06-28-2018, 10:16 AM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 7,392 06-24-2018, 12:15 PM
Last Post: GimbiyaUsers browsing this thread: 1 Guest(s)