Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER*
#1
*Y'AR SARKI CE!!!..*?

{It's All About Royalty,Destiny,Betrayal and A Romantic Love Story}?*NA*

 *UMMU BASHEER* *HASKE WRITERS ASSOCIATION*?

 (Home of Experts & perfect Writers)


   
 *IN DEVOTION TO BILLY'N ABDUL*??


*Page 1~2**Wata* Kyawawar mata ce Zaune tana daka tare da tunanin ina yaran ta suka tsaya har lokacin basu dawo aiken da tayi musu ba. 


Wasu Kyakyawan y'an mata guda biyu ne suka shigo gidan cikin sallama.

Sallamar su ce ta katse mata tunanin ta amsawa tayi tana mai cewa"shin mene ne ya tsayar daku haka tun d'azu?"


Babbar ciki ce ta cire hijab cikin sanyin murya tace"Mama kiyi ma *RAMLA* magana"

Wacce aka kira RAMLA zama tayi tana huci.

"Mene ya faru kuma yimin bayani *JIDDAH*"cewar Maman


"Fad'a ta tsaya yi da y'ar gidan Malam Mudi..." 

Kafin ta gama magana RAMLA tayi saurin katse ta da cewa"Ya JIDDAH Kinsan fa yarinyar nan bata da kunya Allah ni da kin bar ni da ita na koya mata hankali"

Mama ce ta mik'e tana cewa"Wato har kullum dai baza ki daina jawo ma mutane magana ba ko. Sau nawa ina fad'a miki ki daina Shiga harkar mutane. Ina son wannan ya zama na karshe" tayi shigewar ta kitchen tana fad'in hakan.


 JIDDAH ce ta cigaba da yin dakan. RAMLA kuma ta d'aura kafa d'aya kan d'aya tana cizan yatsa. Bai cin JIDDAH ta raba ta da y'ar gidan malam mudi da ta koya ma shegiyar hankali.
Bayan sunyi sallar magriba suna Zaune a plate d'aya suke cin abinci dukan su ukun. Sallama Akayi tare da shigowa, Babban mutum ne amma bai tsufa ba ya shigo rik'e da sanda a hannun shi yana cewa"Mu kwana lafiya Malam Ya'u"

Daga zaure Malam Ya'u ya ansa mai.

JIDDAH ce ta mik'e da sauri ta rik'e sandan shi har zuwa kan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan.

Mama tashi tayi tana mai Sannu da zuwa. JIDDAH da RAMLA ma sukayi mai ya ansa yana sa musu albarka.


JIDDAH da RAMLA suna gamawa suka kwashe kwanukan sannan suka Shiga d'aki suna Shiga RAMLA tayi fuskar tausayi tace" Ya JIDDAH ban iya hadda Na ba gashi gobe zamu biya"

Murmushi JIDDAH tayi"D'auko Qur'an muyi haddar, Amma dan Allah K'anwa ta ki daina tsokanar fad'a kinji kinga Mama bata jin dad'in hakan"

 Mik'ewa tayi tana cewa"to bazan sake ba"
Washegari da safe


JIDDAH ce ta isa kusa da gado tare da yaye bargon da RAMLA ta rufa dashi. Da sauri RAMLA taja bargon yayin da JIDDAH ke cewa"Dan Allah ki tashi zamu makara hadda fa"

 Yamutsa fuska tayi"nidai ki barni inyi barci"


 "Haba y'ar K'anwa ta Kinsan fa Malam Haruna Idan aka makara duka yake"

Tashi tayi tana b'ata rai bata so tashi ba .

"RAMLA sarkin son jiki"cewar JIDDAH tana murmushin ta Mai sanyi.Sallama sukayi ma iyayen su. Baba sukayi musu addua sannan suka kama hanyar Hadda kasancewar asabar da lahadi suna zuwa hadda k'arfe 8:00am su tashi 3:00pm. Saboda zuwa islamiyya.

Suna cikin tafiya sai RAMLA ta hango wata y'ar islamiyyar su da basa shiri ai ko nan tace"b'akutus mai tusa a aji"?


JIDDAH cikin tsoro ta juya tana cewa"wa kike tsokana?"?

Kafin ta bata ansa har budurwan ta iso tana da jiki sosai tana zuwa ta cakume wuyan RAMLA"Uban waye kike cema haka"

Durk'usawa JIDDAH tayi tana cewa"Hanne dan Allah kiyi hakuri baza ta sake ba"

RAMLA ko cikin tsiwa tace"Ance b'akutu uban me kika isa kiyi min"?


Ai nan ta d'aga hannu zata mare ta. JIDDAH ta rik'e hannun tana cewa"kiyi hakuri Hanne dan Allah" 

Hanne da idon ta yayi ja ta kalla JIDDAH sai ta saki RAMLA tace"shegiya kinci sa'an yayar ki dan ina ganin ta da mutunci yau da sai na Zaune ki har sai kinyi fitsari" tana fad'in haka ta wuce JIDDAH na mata godiya.


Dariya RAMLA tayi sai da taga JIDDAH ta b'ata rai sai tayi shiru suka wuce suna hanya RAMLA ke ba JIDDAH labari ai Hanne saboda kibar ta sai tayi ta tusa mai wari a aji. Idan mutum yayi mata laifi ko zama takeyi a kan mutum haka tayi ma wata y'ar ajin su har sai da tayi fitsarin wahala.

Murmushi kawai JIDDAH tayi tana addu'ar Allah yasa ba'a tare lati ba. Ai ko suna zuwa suka ga ana dukan makara.

Suna zuwa yace su kawo hannun su JIDDAH ce ta bada hannu aka mata bulala uku. Za'a bugi RAMLA tace kar a buge ta ayi mata nata. Nan malamin yayi mata bulala uku sannan yace su wuce aji gobe ma su makara.

RAMLA sosai taji tausayin yayar ta. Haka kowa ta Shiga ajin su.


A hanyar dawowan su gida suna tafiya RAMLA taga wani shagon kayan kwalliya ai nan fa ta rud'e tace"wayyo Allah Ya JIDDAH kalle shagon nan ina ma ina da kud'i dana siye su kai amma wancan ribbon d'in yana da kyau"

Shiru JIDDAH tayi tare da kallon gurin"RAMLA ki rage son kyale kyale ni ko sha'awa basu bani ba"

"Kai Ya JIDDAH wallahi suna da kyau. Zance Mama ta bani kud'i ko ribbon d'in can in siya"

 "A'a kar kiyi mata magana kinga fa bata da kud'i"

B'ata rai tayi wai kullum sai ace ba kudi' mtsss taja karamin tsaki. Suka wuce gida.Bayan sunci abinci sai sukayi shirin islamiyya. RAMLA ce tazo ta rik'e hannun JIDDAH ta D'auko wani magani tana shafa mata daidai shaidan dukan da Akayi mata.

Runtse ido tayi sai RAMLA tace"akwai zafi ko"

Girgiza kai tayi"babu zafi ni akan ki bana jin zafin komai y'ar K'anwa ta" ta shafa mata kai.

Murmushi ita ma tayi.
Zaune suke tare da iyayen su bayan isha'i ga farin wata. Hira sukeyi cike da ban sha'awa. 

Kasancewa Baban su Makaho ne baya gani sai dai ya rik'e hannun yaran shi ya sa musu albarka tunda bai San kamanin su ba.

Rik'e hannun JIDDAH yayi yace"Allah yayi miki albarka ki dinga kula da kanki sosai. Nasan ki da rik'e addini dan haka ki dage"

Murmushi tayi cikin jin dad'in maganar Mahaifin nasu.

Hannun RAMLA ya rik'e"y'ar auta nasan ki da tsokana to ki daina kinji. Ki dage da karatu duk inda baki sani ba ga y'ar uwar ki sai ta koya miki kinji ko y'ar albarka"

D'aga kai tayi tana d'aure fuska Wato komai dai sai a dinga cewa yayar ta ta fita ko. Hmm

Albarka yasa musu dukan su Mama tayi masu addua suka Shiga daki domin kwanciya.Wata rana suna Zaune suna aiki Mama na kitchen sai RAMLA tace"nidai burina a duniya shine in zama babbar Mai kud'i. In canza gidan nan inyi ginin birni sannan in siya motoci. Kaya masu kyau da gold"

JIDDAH murmushi tayi domin tasan ko yaushe burin y'ar uwar ta kenan,

 "Hmmm burin ki kenan?"

"Eh Ya JIDDAH sai ma na fito mota body guards suna take min baya"

"Nidai Burina kullum shine mu sami kud'in da za'ayi ma Baba aiki na k'oda. Dan Kinsan likita yace dole sai anyi mai aiki. Sannan kuma ina son inga ko yaushe Mama na cikin farin ciki dan nasan ciwon Baba yana sata cikin damuwa"


Tab'e baki RAMLA tayi kawai bata ce komai ba.


Ranar Monday da la'asar JIDDAH na d'aki sai ga RAMLA ta shigo da alama daga gidan kawar ta take. Zama tayi kusa da JIDDAH tana cewa"dan Allah ki taimake ni kiyi min wani abu"

 "Mene ne RAMLA?"

 "Dama naji y'an HAUSA film su Hadiza Gabon da Aisha Aliyu Tsamiya sunzo shooting film a bayan k'auyen nan shine nake son dan Allah ki raka ni koda ga nesa ne in gansu wallahi su biyun nan ina bala'in son su kinji"

Shiru tayi tana kallon ta da sauri RAMLA tace"Yaya ta kar kice A'a kinji"

Sauke ajiyar zuciya tayi"Kinsan dai Mama ta hana mu fita haka kawai ko Idan ba wai aiken mu tayi ba ko zuwa makaranta. Gashi yanzu yamma tayi babu lokaci kuma ran Mama zai b'aci baza ta bar mu ba ma"


 "Insha Allah babu komai nidai kiyi min wannan taimakon dan Allah zamu dawo da sauri dana gansu"

 "Gaskiya RAMLA kina da matsala Idan wani abin ya faru fa"

 "Babu abinda zai faru Allah ya JIDDAH ki rage tsoro" tw fad'i tana dariya.

D'an duka JIDDAH ta kai mata ta kauce suna dariya.


Mama na kitchen sukayi dubarar fita gidan.


Tafiya sukayi mai dan nisa kafin suka iso wani gurin wanda yake kamar bayan k'auyen ne mutane ne suka gani dayawa wanda suka zo ganin y'an film.


Cikin cunkoson mutanen suka kutsa daga nesa nesa suke iya hango su.

JIDDAH dai tana gefe dan ita ba wai sun dame ta bane.

RAMLA ko duk ta rud'e da ganin irin shigar su ta alfarma ga hadad'an motoci ai nan ta fara day dreaming d'in nata. Sosai ta shagala da kallon su.Har Magriba tayi JIDDAH na fama da ita akan su tafi ta dage ita wai Sai tayi musu magana ko zasu yarda su sata a film d'in. Ran JIDDAH ya b'aci sosai da k'yar RAMLA ta yarda suka nufo gida lokacin har an fara sallar magriba. Tana tafe tana cewa ina ma itace. Tana ta maganar motoci da kyaun da sukayi da Shigar su. JIDDAH taji haushi Wato Daren da sukayi ita bai dame ta ba kenan.Tun bayan tafiyar su Mama ta kira su taji shiru ta Shiga d'akin su babu su hankalin ta ya tashi nan fa taji wai y'an film ne ke shooting kila can suka je. Ai ko har magriba taji su shiru tana jiran su dawo.


Shigowa sukayi yayin da suka ci karo da Mama dake tsaye a tsakar gida.

Gaba d'aya sun tsorata da yanayin ta baran ma RAMLA da bata da gaskiya.

Mama tambayar su tayi daga ina suke.

Da sauri RAMLA tace"Mama ya JIDDAH ce na raka wani guri"

 Da sauri ita ma JIDDAH ta kalle ta jin k'aryar data shararo.

 "Ina ne kika raka ta?" Ta tambaya fuska a d'aure

"Gurin kallon shooting na y'an film wallahi Mama ni ba ruwa na" ta fad'a 

JIDDAH za tayi magana Mama ta dakatar da ita.

 "A matsayin Ku na y'aya mata me zai kai Ku gurin inda maza da mata ke taruwa ban hana Ku bin duk abinda ya shafi birni ba meye ruwan Ku. Sannan sai magriba zaku dawo ko. Kafin raina ya k'ara b'aci Ku bud'e min kafar Ku"


 Wata bulala ta D'auko ni ko nace duka da girman su.


Babu abinda RAMLA ta tsana irin duka har ta fara hawaye tana bada hakuri. Ai ko Mama bata saurare ta ba ta zuzuga mata a kafar yawon sannan tayi ma JIDDAH wacce daurewa kawai tayi sai hawaye.Daidai Baba ya shigo yake jin wannan k'arar dukan tabbas yasan yaran nashi sunyi laifi kenan.

D'akin su suka Shiga kowa fuskar ta yayi jaa.

Mama ko y'ar da bulalar tayi tana share kwalla domin tasan JIDDAH baza ta aikata haka ba hasalima ita bata ma kallon wani film RAMLA ce mai so. Tasan dai y'ar tata tana da hakuri ne da juriya ita kuma bata son tana nuna masu banbanci tafi son ko meye tayi musu hukunci tare.


Baba ya kasa cewa komai dan shi kanshi yasan Idan wani abu ya faru to RAMLA ce dan JIDDAH babu ruwan ta.A d'aki JIDDAH tace"kinga abinda kika jawo ko ai sai dana fad'a miki. Meyasa zaki min k'arya yaushe nace miki ki raka ni?"

 "Allah kece kawai kika jawo ai da kin ki raka ni. Gashi yanzu Mama ta ta fasa min kafa"

 "Ke ciwon ke miki zafi. Ni ba zafin ciwon ya sani magana ba sai yanda muka tashi Hankalin mahaifiyar mu muka sata a bakin ciki shin munyi mata adalci kenan"

Mik'ewa RAMLA tayi"oho ke kika sani tunda dai naga y'an film ai shikenan"??‍♀JIDDAH shiru tayi ta kasa magana sau dayawa tana mamakin wannan halin y'ar uwar tata na rashin tausayi.

*JIDDAH* kyakyawar budurwa ce doguwa tana da d'an jiki Kad'an bata da siranta tana da shape mai kyau da daukar hankali. Idanun ta manya ne farare tass. Lips d'in ta pink karami gwanin sha'awa. Hancin ta dogo ne siriri fara ce tass da ita domin fatar ta har wani Kore Kore yakeyi akwai ta da gashi ga cika ga tsawo. Gaskiya JIDDAH kyakyawa ce.


Tana da sanyi tare da tsoro sai dai kuma akwai ta da jarumta kullum cikin shigar mutunci take. Tayi primary har secondary sai dai ba tayi Weac da Neco ba saboda talauci da suke fama dashi. Budurwa Ce y'ar kimanin shekaru ashirin 20yrs . tana da ilimin addini dana boko. Tana da tausayi da son iyayen ta. Tana son K'anwar ta. Takan sadauakar da farin cikin ta domin K'anwar ta. Tana son RAMLA tun suna yara akwai lokacin da kunama us hau k'afar RAMLA sai JIDDAH tayi saurin daukar shi da hannu ta yar ashe ko ya cije ta. Ire iren wa'inan na faruwa ko kuma Idan RAMLA tayi tsokana suna yara sai a kama JIDDAH ayi mata duka. Maman na jin dad'in yanda yaran ta ke kaunar junan su. JIDDAH bata d'auki duniya a komai ba dan iyayen tane a gaban ta tana son su tana son farin cikin su. Duk kyale kyalen nan baya gaban ta. Babu ruwan ta da kawaye kawar ta d'aya ce yarinyar aminin Baban ta Ummi Kenan suna shiri saboda halayen su yazo d'aya. JIDDAH bata da lokacin Tsayawa da samari. Gashi tana da massoya sai dai yanayin yanda fuskar ta yake a d'aure KO yaushe shiyasa suke shakar tunkarar ta da soyaya ko sunje ma cewa take bata soyaya ta shige gida. JIDDAH muskila ce ta karshe dan ko magana bai dame ta ba ko abin dariya Akayi sai dai tayi murmushi JIDDAH kenan.
*RAMLA* Kyawawar budurwa y'ar shekara sha takwas 18yrs fara ce sai dai ba irin hasken JIDDAH ba JIDDAH tafi ta Haske amma ita ma RAMLA fara ce tana da hanci dogo idanun ta masu lips d'in ta karami tana da tsawo amma ba sosai ba ita siririya ce amma ba mai munin nan ba tana da shape mai kyau. Ita ma tana da gashi dan sunyi gado ne gurin Maman su wacce kamanin ta suka D'auko.RAMLA tayi secondary a s.s two ta gama sai dai rashin kud'i ba tayi su Weac ba taji haushin rashin yin ta domin tana son karatun. Tana da ilimin addini daidai bata maida hankali ne dai. Akwai ta da surutu tun tana karama shegen wayau ne gare ta. Bata da tsoro ga tsokanar fad'a da neman rigima dan ko Babba ne Idan ya shigo harkar ta bata raga mai. Tana da son abin duniya. Da kyale kyalen rayuwa. Kullum burin ta shine tayi kud'i ta Gina katon gida ga hadad'an motoci ga kayan alfarma. Tana jin zafin kasancewar Mahaifin su makaho. Har takan zauna tace dama ba'a k'auyen nan aka haife ta ba dama ita ba y'ar makaho bane. Tana son iyayen ta amma tafi hangen nesa na burin ta dan tace talauci ne duk yasa haka dama suna da kud'i ne. Komai Idan ta gani sai tace tana so yana burge ta. Amma babu halin siya. Idan JIDDAH nada kud'i shine take siyan mata wanda bai fi k'arfin ta ba. RAMLA tana bakin cikin yanda Yayar ta tafi ta komai dan kowa na cewa JIDDAH ta fita kyau da natsuwa. Sau dayawa sai tayi laifi sai tace JIDDAH ce.  Tana son JIDDAH amma wani lokacin sai taji tana jin zafin ta baran ma yanda iyayen su ke yabon JIDDAH. 


RAMLA akwai son kwalliya da gayu sai dai babu hali. Ga samari na son ta amma ko kula su ba tayi saboda tace tafi k'arfin d'an k'auye ita sai mai kud'i. Har zagin su take suma sai basa zuwa. RAMLA tana son ace ita wata ce tana da wata kawa Hafsa. Halin su yazo d'aya dama ance sai hali yazo d'aya ake abota wannan haka yake.JIDDAH da RAMLA iyayen su sun basu tarbiyya nagari. Haka Mama tana tsaye akan yaran ta domin tarbiyyan su. A k'auyen sai cewa ake su JIDDAH sun ki aure. Su dai ko a jikin su iyayen suma sunyi shiru ba wai dan basa so ba sai dan basu San wanda zai rik'e masu yaran su tsakani da Allah ba.


JIDDAH da Mama suna aikin wankau da irin d'an siyar da su kuka. Maggi. Yaji. Dadawa da sauran su. Wacce Mama ke siyarwa.


RAMLA kuma kitso takeyi shima ba ta cika sonyi ba dan ita tana da kwiya.

Wannan kenan...Barkan mu da sake had'uwa a sabon novel na massoya. Ayi comments dai domin inji dad'in shirya muku shi??

 *UMMU BASHEER CE*?
[6/9, 13:11] +234 802 797 9297: *Y'AR SARKI CE!!!..*?

{It's All About Royalty,Destiny,Betrayal and A Romantic Love Story}?*NA*

 *UMMU BASHEER* *HASKE WRITERS ASSOCIATION*?
 (Home of Experts & perfect Writers)


*IN DEVOTION TO BILLY'N ABDUL CE*??
*Page 3~4*
 *Sak'on gaisuwa na mussaman gare Ku massoya nah. Ina muku fatan Alkhairi*?*Da Yamma* suna Zaune JIDDAH nama RAMLA kitso sai ga Malam AHMAD Mahaifin su ya shigo gidan wani yaro ne ya rik'e mai sanda yayi mai jagora. 

Da sauri su biyun suka isa gare shi ganin yana tari. JIDDAH ce ta rik'e sandan tare da hannun shi RAMLA kuma ta Karb'a ledar hannun shi suka zaunar dashi kan tabarma.

 Sannu sukayi mai. Ya tambaye su ina maman su.

 "Taje makwafta yin barka anyi haihuwa"cewar RAMLA

 "Toh kune a gidan kenan"

 "Eh Baba kitso mukeyi. Bara na kawo ma ruwa" cewar JIDDAH.

"Baba meke damun ka ne" inji RAMLA

 "Babu komai y'ar nan Allah dai yayi muku Albarka ya kare Ku daga sharin duniya"

 "Ameen Baba babu inda ke maka ciwo ko?" JIDDAH ta fad'i lokacin data iso da ruwan hannun ta.

 Yana cije lebe ya ansa da ba komai dan baya son ya d'aga musu hankali dan ba karamin ciwo yake ji ba.


 Mama ce ta shigo tana mai barka da dawowa sai dai tana ganin yanayin shi tasan ba lafiya. Gaban ta ne ya fad'i nan tasa yaran aiki ta zauna kusa dashi tana tambayar shi meke damun shi.

 "KHADIJA a duniya babu abinda zance miki sai Allah ya baki gidan aljanna. Domin ke mace ta gari ce. Dan Allah ki cigaba da kula da yaran nan kina sa musu ido ko bayan rai na"

Hawaye ta share tana kallon shi"Meyasa kake fad'a min irin wannan maganar kamar ka cire rai da Rayuwa"

 "Saboda nasan bani da wani sauran rayuwa. Ni nasan mutuwa zanyi..."

"A'a ka daina fad'in haka insha Allah babu abinda zai same ka. Idan ka tafi ya kake son inyi da nida yaran nan kai ne gata na. Bani da kowa nida yaran nan a duniya kamar kai. AHMAD ka zamo wani babban b'angare Na Rayuwar mu dan Allah ka daina fad'in irin wa'inan maganganun" ta kare cikin kuka.


JIDDAH data fito daga kitchen ta hanga iyayen nasu sai jikin ta yayi sanyi da ganin yanayin su hannun RAMLA ta rik'e suka isa har gaban su.

Zama sukayi cikin damuwa Ganin Mama na share hawaye.

"Dukan tsanani yana tare da sauk'i. Addu'a shine maganin duk wani matsala ta rayuwa" cewar JIDDAH cikin hawaye.

Baban ne ya lalubo hannun ta ya rik'e"wannan haka yake JIDDAH ta. Kar kusa damuwa a ran Ku. Likita yace Idan akayi min aikin nan zan samu sauk'i bana son Ku Shiga damuwa Ku dinga kula da mahaifiyar Ku shine abinda nake so da Ku"

RAMLA kamar za tayi kuka"Wai meyasa duk hakan ke faruwa damu ne saboda talauci.."

Mama ce ta buge bakin ta"yimin shiru kina magana kamar wacce bata San k'addara ba ko addini. Allah shine mai bayarwa ba d'an Adam ba"

"Mama kiyi mata hakuri har yanzu bata da wayau ne"

RAMLA b'ata rai tayi ita dai tana bakin cikin kasancewar ta y'ar makaho da kuma talaucin da suke fama dashi.

 JIDDAH tace"Mama yanzu ina zamu samu kud'in aikin kafin lokacin da Doctor ya bamu ya cika"

 "Gadon d'akin Ku da namu za'a siyar akwai wasu kud'i a hannuna muga ko zasu isa. Sai Ku duba wasu daga cikin kayan Ku a siyar "ta k'are tana share hawaye.

 "A'a kar ki siyar da komai nasu..." 

 "A'a Baba a siyar domin lafiyar muke nema"JIDDAH ce ta katse shi da fad'in hakan.


RAMLA haushi kamar ya kashe ta wai har kayan sawan su za'a siyar bayan ma kayan tsofafi ne.


Ranar dai gidan shiru haka suka kwana cike da tunanin rashin Lafiyar Malam AHMAD.
Tun daga lokacin Mama bata tsaya ba ta fara harhada kud'in sai dai bai kai ba.


Wata rana Malam AHMAD ya tashi da ciwo sosai kamar ba zaiyi rai ba gadan gadan aka kai shi hospital.

Doctor yace sai anyi mai aiki. Mama tace kud'i basu kai ba a ataimake su haka nan. Doctor d'in yace shi hospital ba nashi bane da zai taimaka musu. JIDDAH taji zafin abinda yayi musu har tayi tunanin ina ma ace ita doctor ne data taimaki Mahaifin su. Da sauran talakawa wanda basu dashi Idan sunzo hospital kuma ayi ta musu wulak'anci.


Haka aka basu gado Mama dai taje ta samu aminin Malam AHMAD Wato malam Ya'u ta fad'a mai halin da ake ciki har ta fad'a mai ta yanke hukuncin siyar da gidan da suke ciki. Shi kan shi baiji dad'i ba amma ya zaiyi shima yana fama da talauci bare ya taimake su. 


RAMLA da JIDDAH suke hospital suna kula dashi. Ciwon yayi tsanani yanzu gashi har yanzu Mama bata samu wanda zai siya gidan nasu ba.

Cikin dare k'arfe takwas Allah yayi ma Malam AHMAD rasuwa a hospital d'in. Ba karamin tashin hankali suka Shiga ba sunyi kuka sosai baran ma JIDDAH saboda ta shak'u dashi ba kamar RAMLA ba. Mama tayi kuka sosai ita ma Malam Ya'u ya Shiga tashin hankali dauriya kawai yayi irin na maza ya samo mota aka sa gawar shi zuwa gida.Mutane tun Daren mutane suka ji haka sukayi ta shigowa makwafta kowa na nuna yanda yaji mutuwar. Su Mama ba karamin tashin hankali suka gani ba a Daren haka dai sukayi ta mai addu'oi suna kuka.


Washegari aka gaishe gidan shi na gaskiya. Su JIDDAH kuka sosai sukayi. Mama ko kusan suma tayi gaskiya kowa ya tausaya masu.

Mutuwa kenan mai yankan kauna. 


Bayan kwana uku da rasuwar Malam Ahmad sun d'auki hakuri tare da mai addu'a domin mamaci addua yake buk'ata ba koke koke ba haka suka d'auki wannan jarabawar tare da yarda da k'addara wanda haka Allah ya nufa.
Bayan anyi bakwai kowa duk sun watse sai mutuwar ya dawo musu sabo. Mama na Zaune ta rik'e carbi tana hawaye. JIDDAH da RAMLA ne suka zauna kusa da ita. 

Share hawaye tayi ta kalle su tunowa da tayi yanzu sun zama marayu kawai sai ta fashe da kuka. Rungume ta sukayi suma suna kuka. Sun Dade suna kuka kafin JIDDAH tayi dauriyar cewa"Mama Idan ke kina kuka mu kuma ya kike so muyi. Yanzu ke kad'ai kika rage mana a duniya. Dan Allah ki rage damuwa kar wani ciwon ya same ki"

 Share hawaye tayi"baza kusan yanda nake ji ba. Mahaifin Ku mutum ne da Samun irin su a duniya sai an tona. Ni kad'ai nasan yanda nake ji. Gata da kulawar da yake nuna muku yanzu bashi. Kun zama marayu hakan na Sani kuka. Mahaifin Ku mutumin kirki wanda mutane sun shede shi. Ku cigaba da mai Addua Allah ya gafarta mai"


 "Ameen" suka ce cikin share hawaye dan kam ya samu kyakyawar shaida a gurin mutane.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨
 *MASARAUTAR SARKI ABDUL-AZEEZ ABDALLAH BINA*?


Masarautar nan tana cike da farin ciki domin yau ne Y'ayan Sarki Abdul-Azeez zasu dawo daga UK bayan sun d'auki shekaru mai yawa acan suna karatu. Gashi yanzu sun kammala zasu dawo. Yau kowa na cikin farin ciki. Shiri sosai ake yi ko'ina na gidan an bishi da flowers gurin ya k'ayatu. Abinci kala-kala aka shirya. Kowa yaga sarki Abdul-Azeez Bina yasan yana cikin farin ciki.  
    

Motoci ne na alfarma aka tura Airport domin taro y'ayan sarkin. *AIRPORT*Sannu a hankali suke tafiya mai cike da kasaita kyawawa ne na karshe. Farare tass d'aya na sanye da black jeans. White and blue d'in Riga sai wani rigar sanyi black mai kyau wanda ya tsaya har gwiwa sai farin space daya sa. Dayan kuma yana sanye cikin coffee brown d'in jeans sai Riga white tare da coffee brown d'in jacket sunglasses ne yasa ga Rolex wristwatches a hannun su tare da zoben azurfa wanda kowanen su yake d'auke da Kalmar *S* . tafiya ce sukeyi kamar baza su taka kasa ba.   Fadawa na ganin su sukayi saurin taro su suna faman gaishe su dayan ne ke ansawa dayan kuma hannu ya daga musu nan sukayi saurin bud'e musu k'ofar mota cikin mulki da kasaita suka Shiga.
Kayan su kuma aka sa a d'ayan motar.


Straight gidan sarki motar ta wuce. Tunda suka isa k'ofar gidan sai busa da kid'e kid'e ya tashi mutane na farin cikin dawowan su marok'a na nasu aikin. Har cikin gidan sarki gurin Parking lot motocin sukayi parking.

Sarki ne tare da waziri da fadawa da sauran mutanen shi suke take mai baya.


Fitowa motar sukayi suna ganin sarki suka K'arasa. Hugging nashi sukayi shima ya rungume su cikin farin cikin dawowa. Murmushi duk sukayi mai shima yana murmushin ai nan mutane suka fara gaishe su da musu barka da dawowa kasar haihuwar su. Amsawa sukeyi sama sama cikin nuna isa.


Nan aka Shiga wani babban parlour'n gidan wanda na sarki ke zama da mutanen shi.


Zama Akayi aka k'ara gaisawa da kyau sannan sarki yace Jakadiya tasa a jagorance su zuwa part d'in su.Flats ne guda biyu masu shegen kyau komai iri d'aya ne suna kallon juna nan fa kowa ya shige nashi part d'in. Babban parlour ne ds two bedrooms with toilets har da kitchen gashi ta baya anyi masu gurin shakatawa. Komai iri d'aya.Wanka sukayi tare da shiryawa . suka huta sannan fa suka fito.

Dayan na fitowa shima dayan ya fito suka had'u suka Shiga ainihin cikin babban gidan dan nan sarki yace ace suzo.


Wani parlour'n suka Shiga mai shegen kyau komai na parlour'n royals ne brown and milk colour. Sarki Abdul-Azeez na Zaune a kujera yayin da wata mata bak'a ke Zaune a kusa dashi cikin kayan ta na alfarma na sarauta. Mik'ewa sukayi da suka shigo matar cewa take"Barkan Ku da dawowa yara na. Nayi matukar farin cikin dawowan Ku"

 D'ayan ya tab'e baki yace"shiyasa baki fito kin taro mu ba duk a cikin murnar ne"

Murmushi tayi cikin basar da maganar tace"Ina nan na tsaya sai naga an shirya muku abincin da kuke so ne *SHAHEED* mu K'arasa dining room d'in" ta fad'i tana yin gaba.

Bin ta sukayi har table d'in wasu masu aiki suka ja musu kujera suka zauna. Nan Akayi serving nasu suka fara cin abinci.

SHAHEED ne ya gyara zama"gaskiya girkin nan yayi sosai Mami"

Dariya tayi ita da sarki sai ta kalla dayan tace"Banji kayi magana ba *SHURAIM* ko abincin baiyi maka bane?"

Murmushi yayi kawai SHAHEED yace"wannan ai ko abinci yayi ma ba zai ce yayi ba za dai mu baki award domin yanda kika kula Akayi mana abincin nan mai dad'i ko Abba?" Ya kalla sarki

"Kwarai ta cancanci tukwici" cewar sarki.

Bayan sun gama cin abincin ne suka koma parlour'n nan suka fara hira Sarki na jin dad'in yanda yaran shi suka dawo. Suna fara hira Mami ta fita parlour'n. 


Tana fita ta cije yatsa da sauri jakadiyarta ta tare ta nan suna Shiga bangaren Mami jakadiyar tace"Uwar gida sarautar mata takawar ki lafiya mace d'aya tal a gurin sarki mai gaskiya da adalci.."

D'aga mata hannu tayi alamar ya isa. Tafiya d'aya tayi zuwa biyu tace"ina hango matsala a dawowan wa'inan yaran. Naji a jikina dawowan su ba alkhairi bane a gare ni. Domin tun yanzu na fara ganowa"

"Allah ya huci zuciyar ki ranki shi dad'e mata a gidan sarki"

 "Ku bani guri ina buk'atar hutawa"nan duk aka fita har da jakadiya.

Mami sai kaiwa da komawa take can taja tsaki.
Sarki Abdul-Azeez da yaran shi sai da sukayi sallar magriba da isha'i a massalacin gidan sarkin sannan sukayi mai sallama suka nufi part d'in su fadawa Na take musu baya.

Part d'in SHURAIM suka Shiga yayin da suka sa fadawan su juya.

Suna Shiga SHAHEED ya zauna a Kujera yana cewa"oh God yanzu tunda mun dawo kasar nan bani ba zuwa club kenan shit"ya d'an buga hannun shi a kujera.

Tsaki SHURAIM yaja tare da jawo wani stool ya d'aura kafa d'aya kan d'aya yana d'an girgiza su. 

 "Come on man you heard what I said. Now what I'm I gonna do"

 "Calm down SHAHEED you have to rest, and now you have to know that there is different. Nan 9ja ne not UK "


 "That's none of my business SHURAIM. Ina jin kamar bazan iya yin Rayuwar nan gidan ba I need some privacy"

 "I'm tired I'm feeling sleepy can we continue tomorrow ha" ya fad'i tare da Mik'ewa.

Tsaki SHAHEED yayi"kai baka da matsala tunda nike da matsala you don't care kai fa banza ne ni na wuce ma" zai fita SHURAIM ya rik'o shi.

 "Ina son kayi tunani kayi nazari da kyau abinda zaka yi a nan gidan"

 "No need to think ko ka manta I'm *BARRISTER SHAHEED ABDUL-AZEEZ BINA* nasan me zanyi don't worry bro"

Murmushi SHURAIM yayi"I trust you .good night" ya d'aga mai hannu shi kuma ya nufa side d'in shi.


SHURAIM wanka yayi yasa pyjamas tare da daukar lap top ya fara wasu bincike.


SHAHEED ko yana zuwa yayi shirin barci shima sai ya D'auko wata jaka ya Ciro wata karamar kwalba kamar na turare. Zaro ido nayi lokacin da naga an rubuta whiskey kawai sai gani nayi ya fara sha can ya ajiye sai kuma naga ya hau barci.Bayan dawowan su da kwana biyu sarki ya shirya musu wata walima wanda aka Tara mutane domin taya su murnan kamala karatun su tare da murnan dawowan su bayan shekaru goma sha biyar.


Taro yayi taro dan ya kayyatar da mutane har abubuwa aka raba sosai wanda Mami tayi bakin cikin hakan.


Bayan sati biyu 

Sarki ya malaka ma SHURAIM Hospital wanda ya gina mai har an fara aiki kasancewar SHURAIM babban DOCTOR ne Wato *DOCTOR SHURAIM ABDUL-AZEEZ BINA* .

SHURAIM yaji dad'i sosai mutane ma sun taya shi murna yayin da SHAHEED aka sa mai aiki a wani babban Court kasancewar shi lawyer Wato *BARRISTER SHAHEED ABDUL-AZEEZ BINA* sosai shima yaji dad'i mutane suna ta taya shi murna tare da sarki ganin ya had'a jarumai Wato ga Doctor ga kuma lawyer.


Monday d'in da ta zagayo suka fara aiki kuma sun fara cikin nasara da sa'a.*K'AUYE*
Mama ta fita takaba Wato wata hud'u da kwana goma kenan da rasuwar malam Ahmad Mahaifin su JIDDAH.

Sunyi rashi sosai gaskiya sai dai sun sa ma Kansu hakuri da juriya. Suna taimakon Mama basa barin ta cikin kadaici da damuwa.


A yau suna hanyar su ta dawowa islamiyya sai wata mota mai kyau ta wuce. RAMLA ce tace"kai ina ma ace nice a cikin motar can"

JIDDAH da haushi ya ishe ta tace"ai sai kije ki Shiga. Wai ke yaushe zaki cire wannan burin banzar ne. Nayi tunanin rasuwar Baba zai sa kisa ma kanki hakuri da yanda rayuwa tazo mana"


 "Kai JIDDAH meye laifi na a ciki yanzu. Shikenan bazan fad'i burin raina ba. Nifa yanzu burina kullum shine Idan nayi kud'i in d'auke ki keda Mama mu bar k'auyen nan mu koma gida mai kyau ga kud'i ga motoci in kai Ku Hajji sannan..."

 "Ya isa haka. Ko yaushe kina addua amma bana jin kina cewa Allah ya kawo ko insha Allah. Komai fa ki dinga sa sunan Allah a ciki dan shine mai bayarwa"

 "Tohm Insha Allah" cewar RAMLA. A haka suka kama hanyar gida.


Comments and share??

  *Y'AR SARKI CE*??
*UMMU BASHEER CE*?
[6/9, 13:12] +234 802 797 9297: *Y'AR SARKI CE!!!..*?

{It's All About Royalty,Destiny,Betrayal and A Romantic Love Story}?*NA*

 *UMMU BASHEER* *HASKE WRITERS ASSOCIATION*?
 (Home of Experts & perfect Writers)


 *^°IN DEVOTION To BILLY'N ABDUL ^°*

  
 *Godiya mai tarin yawa gare ki Sister Billyn Abdul thanks for you love and care Ummu loves you much*?

*Page 5~6*

*A gajiye* yake da k'yar yake tafiya hannun shi rik'e da brief case sai kayan shi na doctor Driver na ganin shi yayi saurin bud'e mai mota ya shiga. 


Driver na parking sai ga motar SHAHEED ya shigo. Tsayawa yayi har SHAHEED yazo suka gaisa sannan suka wuce part d'in su.

Duk sai da sukayi wanka suka huta sannan suka SHAHEED ya Shiga cikin gida. Sai SHURAIM shima ya Shiga gidan duk a Parlour'n sarki suka hallara.


Sarki Idan har weekends ne da families d'in shi yake cin abinci amma ranar saboda yana son magana dasu.

FULANI Wato Mami tana hakimce a kujera cikin Shigar alfarma. Gaishe ta sukayi ta ansa tana murmushi. Nan suka fara having dinner.


Bayan sun gama Sarki Yace yana son Magana dasu.

 "Alhamdulillah muna ma Allah ubanghiji godiya da kuka kamala karatun Ku lafiya har kuka fara aiki. Allah yasa kuyi aiki da taimakon kasa"

 Ameen duk suka ce.

Gyara zama yayi irin na sarakuna yace"yanzu Aure ne ya rage tunda kun kai lokacin ya kamata ace yanzu kowanen Ku nada iyali, cikar namiji da mutuncin shi shine aure"

Fulani tayi murmushin mugunta tace"ranka ya dad'e nima naga dacewar hakan ya kamata ace sun fito da mata"

Sunkuyar da kai SHURAIM yayi SHAHEED koma ya fara Sosa keya yace"a bamu lokaci insha Allah komai lokaci ne"

Murmushi mai martaba yayi"Allah ya Baku mata nagari"

 "Ameen" suka ce suna jin kunyar mai martaba.
Suna barin bangaren mai Martaba SHAHEED yace"Bros nifa na wuce I want to get some fresh air. Tunda Nazo ban fita shakatawa ba"

 "Komai dai za kayi ka tuna akwai Allah"

 "Wai kai meyasa kake min irin haka ne wannan ai rainin sense ne"

 Dariya yayi shi dai ya wuce ya bar SHAHEED.

Shima wata mota ya Shiga. Body guards zasu bishi yace su barshi shi kad'ai yake son fita. Haka ya Shiga mota ya bar gidan.


Wani hadad'an night club naga ya Shiga yana zuwa yayi order d'in giya. Y'an mata ne suke ta kallon shi suna zuzuta yanda ya had'u. Sai daya sha barasar yaji ta d'an fara kama shi sannan ya ajiye cup d'in.

Wata budurwa ce sanye da mini skirts da top karami kirjin ta duk a waje sai taunar chewing gum take yi. Kallon ta yayi ta kashe mai ido d'aya.  Hannu ya Mik'a mata ta rik'e ya zaunar da ita a cinyar shi. Shafar shi ta fara can taja shi zuwa wani d'aki dake cikin club d'in. Suna Shiga ta cire kaya tana K'okarin cire mai. Cikin maye yake romancing d'in ta. 


Sosai suke romancing juna kamar an tsikare shi yayi saurin ture ta. Yana son dawowa hayyacin shi. Da sauri ya fara sa kayan shi. Zai fita tayi saurin rik'o hannun shi.

 cikin buk'atuwa tace"ya haka ina zaka"

 Cikin d'an maye yace"bana sex, sorry babe I just have fun that's all" ya fita har da d'aga mata hannu alamar bye.

Koda ya isa gidan 11:00pm da sand'a ya Shiga parts din su. Dan baya son SHURAIM yaga time d'in daya shigo.


Yana zuwa ya kwanta kan bed ko takalmi bai cire ba sai barci.SHURAIM ko aiki yake tayi a laptop bai kwanta ba har sai da yaji shigowar SHAHEED dan yaji k'arar bud'e kofa. Nan shima ya kwanta.

 *K'AUYE*
 An fara maganar rabon gado. Wata y'ar uwar Malam Ahmad ne tazo gidan rabon ta da gidan tun ranar uku sai yau tazo tunda tazo gidan sai fad'a take. Wai Mama ta malake komi na gidan gara ayi rabon gado ai. Ita dai Mama bata ce komai ba.


JIDDAH ma dai bata ce komai ba. RAMLA ko haushi ya ishe ta gashi Maman tace kada ta sake tayi magana dan tasan zata musu rashin kunya ne.


Matar sai yamma ta tafi washegari kuma sai ga K'anwar Baban nasu wacce take aure a wani k'auye shine tazo sai tazo gidan dan bata zo gaisuwa ba.


Tunda tazo sai ta fara da habaici wai Mama ta kashe mata d'an uwa. Kasancewa su JIDDAH na islamiyya koda suka dawo dai basu kula taba dan Mama ta hana su. Ita ko Inna Laure sai habaici take.


Cikin wannan lokacin dai Mama tana fama da y'an uwan Baba dan kullum cikin mata habaici da gori suke. Hakuri kawai takeyi ga zafin mutuwa.


Zaune Mama take rik'e da wani d'an karamin akwati mai kyau sai kuka take. Sosai take kuka tana tausaya ma yaran ta. Ga dangin Baba da suka sata a gaba massifar na yau daban na gobe daban.Yau suna Zaune sai ga Inna Laure ta shigo zama tayi ba ko sallama. Can tace"Ke RAMLA dan uwar in baki da tarbiyya ko baki San mutum yazo ki kawo mai ruwa ba ko bare gaisuwa"

 RAMLA turo baki tayi tana son mata rashin kunya. JIDDAH tayi saurin cewa"bari ni in deb'o miki" ta tashi.

 "Ke uban wa ya saki ko na sako ki a magana nane. Yarinyar da ba'a San Asalin ta ba!"

Dum gaban su ya fad'i da sauri RAMLA tace"Inna Laure mai kika ce Yayar tawa"

 "Dallah ni rufa min baki ai baki San komai ba kima bar kiran ta da Yayar ki dan ba'a San Asalin ta ba"


Mama a fusace tace"Haba Laure wani irin magana ne kikeyi haka"

 "Ai Kinsan maganar da nakeyi ko zaki musa ne"

 "Laure tashi ki tafi dan zaman lafiya nake nema ba fad'a ba baza ki zo gida na ba kina cin min mutunci nida yara na"

 Rik'e baki Laure tayi"Wato ni zaki cima mutunci kenan akan Nazo gidan d'an uwa na ko dan kinga yanzu baya raye"

 RAMLA tace"koda yake raye ma ai ba zuwa kukeyi ba sai daya rasu shine kuka zo dan kuci gado"

Mama ce ta daka mata tsawa Inna Laure ta fita tana kukan munafurci.

JIDDAH ko tun maganar Inna Laure ta girgiza shiru tayi kawai tana kallon su can dai tace"Mama mene ne Asalin Ki?meyasa Inna Laure tace bani da Asali?"


Da mamaki sosai Mama ta kalle ta"wani irin maganar banza ce wannan Ku tashi kuje kuyi haramar sallah" ta fad'a ta bar gurin.

Cikin sanyi jiki dukan su suka tashi.Tun daga wannan lokacin y'an uwan Baba suka sa Mama a gaba wai ta kori Inna Laure dan tana son cin gadon ita kad'ai. Anyi rabon gado dama dai wannan gidan ne kad'ai da suke ciki.Bayan sati biyu


JIDDAH da RAMLA sun fara Shiga damuwa domin gaskiya suna son Sanin mene ne asalin labarin Maman su. Gashi sun lura tana cikin damuwa sosai.


Tana Zaune suka same ta
 Gaba d'aya fuskar tausayi sukayi mata kamar za suyi kuka.

 "Mama tunda muka taso dangin Baba kawai muka sani. Bamu tab'a ganin wasu y'an uwan ki ba har lokacin da Baba ya rasu" JIDDAH ce ta fad'i hakan.

 RAMLA tace"eh Mama dan Allah ki fad'a mana Asalin ki. Muna son jin labarin ki"

 B'ata rai tayi"meyasa kuke son Sanin Asali na?"

 "Mama dan Allah ki fad'a mana"

 "Kuyi min shiru bana son Ku k'ara tambaya na. Mene ne Asali na daga yau. Wata rana zan fad'a muku Idan lokacin daya dace in fad'i yayi daga yau kar Ku sake tambaya na"


Kamar za suyi kuka haka suka hakura dan basa musu da mahaifiyar su. Amma fa sun so jin labarin ta.


Mama d'aki ta Shiga ta bud'e wani drawer ta D'auko wani d'an karamin akwati ta rungume a kirjin ta tana kuka mai cin rai. Tayi kuka sosai kafin daga baya ta hakura ta fita d'akin.
 *Masarautar Sarki Abdul-Azeez Bina*


Rayuwa na cigaba da tafiya. Mai martaba na kula da yaran shi sai dai yafi ba SHURAIM kulawa duk wani abu da mai martaba zaiyi sai yasa an kira SHURAIM in dai bai aiki. Ko wani harkar daya shafi cikin gidan sarki ko wani abin duk Mai martaba nasa SHURAIM a ciki. SHAHEED tun baya kula da hakan har ya fara ganewa. 

Tun abin baya damun shi har ya fara damun shi dan Mai martaba baya wani bashi kulawa.

Gashi yana fita yawan shi na dare yaje club yasha giya sai dai baya neman mata amma yana romancing d'in su dan rage ma kanshi zafi. Baya tab'a yarda ya kusanci mace. 

Mai martaba ya gano cewa kullum sai SHAHEED ya fita nan yasa ayi mai bincike domin yasan ina yake zuwa. Labari yazo ma sarki cewa SHAHEED night Club yake zuwa ran sarki ya b'aci sosai. Nan yasa aka kira mai SHAHEED.


Bai nuna mai yasan komai ba cemai yayi kawai ya nemo mata aure zaiyi. Hankalin SHAHEED ya tashi dan bashi da wata budurwa duk wacce suke d'an romancing dinnan ba wai son wata yake ba har yau baiga macen da tayi mai ba. Kasancewar shi lawyer sai ya lura kamar akwai abinda Sarki ya gane da har yake son yayi aure. Sai dai yana addu'ar Allah yasa ba wai yasan yana zuwa club bane. Nan ya bashi hakuri yace a bashi lokaci haka kawai yace. 


Tun daga wannan lokacin ma mai Martaba hidima yayi mai yawa suma Kansu su SHURAIM d'in basu da lokaci.


Sai dai fa rashin kula SHAHEED da mai Martaba yakeyi yana damun shi ranar yaje yana son mai magana ya tarar yana meeting koda suka gama bai ce a kira shi ba. Abin yayi mai ciwo wai meyasa Abba yanzu baya Shiga harkar shine? Wannan tambayar kullum shine yake ma kanshi

 *K'AUYE*


JIDDAH ce ke tashin RAMLA barci tak'i tashi. Pillow ta D'auko ta buga mata. Tashi tayi tana turo baki sai ta d'auki pillow d'in ta wurga a JIDDAH ta koma barci. JIDDAH ce ta fara bubuga mata pillows. Ita ma ta tashi ta fara ramawa nan suka fara dariya suna buga ma juna pillows yayin da audingan pillows d'in ke zuba sai hakan ya bada wani irin yanayi mai dad'i. Mama ce ta tsaya daga bakin Kofa tana kallon su tana murmushi. Taji dad'in kasancewar su cikin farin ciki. Baza ta so ta fad'a musu abinda zai tada musu hankali ba. Abinda zai sasu cikin rudani ko tunani. Baza ta so su bar farin ciki ba. Kullum burin ta shine ta gansu cikin farin ciki. Zata fad'a musu wacce ita a lokacin daya dace dan tana son yaran ta da farin cikin su. Amma ba komai tasan nan gaba za suyi farin cikin daya fi hakan na har abada take masu fata.

RAMLA ce ta buya a bayan ta JIDDAH kuma tazo tana son kama ta RAMLA ko cewa take Mama ta b'oye ta JIDDAH ko cewa take ita sai ta rama haka sukayi ta juyi da Mama sosai ita ma take farin ciki sannan da k'yar suka bari suka had'u suka ci abinci su su ukun.


*KINGDOM*Mai martaba ne da SHURAIM tare da wasu. SHAHEED zai Shiga fadawa suka ce sarki suna meeting haushi suka bashi.

 "What do you mean ko kun manta ni wane ne" SHAHEED ya fad'i.

"Kayi hakuri ranka ya dad'e Yarima ba'a bamu izinin barin kowa ya Shiga ba"

 A fusace yace"Har ni *D'AN SARKI* kuke nufi?"

 Fadawa dai shiru sukayi suna kallon kasa.

A fusace ya shige ciki mutanen duk suka kalle shi cikin bakin ciki yace"Mai Martaba har ni Akayi ma iyaka da shigowa meyasa bazan gan ka a lokacin da nake so ba har wasu fadawa suke gaya min magana"
 Wasu fadawa ne suka ce" ka gyara maganar ka ko ka manta a wanda kake magana"


 Waziri ne yace ya fita. Haushi kamar zai tashi sama ya fita.

Gurin jakadiya ya wuce. Tayi mamakin zuwan shi gurin ta. Gaishe shi tayi ya kasa amsawa.

"Meyasa Mai martaba yake nuna min banbanci tsakani na da SHURAIM?"

Tambayar kamar daga sama yazo ma jakadiya. Gaba d'aya ta rasa mai zata ce mai har ya sake magana.

"Ina son ki fad'a min dalili shin mene ne gaskiya?"

 "Ranka ya dad'e ban fahimci mai kake son fad'a min ba?"

 "Jakadiya nasan Kinsan komai. Dan Allah ki fad'a min meyasa Mai martaba baya nuna min kulawa sai SHURAIM ko yaushe yana tare da SHURAIM baya son gani na yanzu. Mene ne laifi na" magana yake cikin damuwa sosai.


Jakadiya hakuri tayi ta bashi tare da tatausan kalamai ta fad'a mai babu komai hidima ce dai tayi mai yawa.


Badan ya yarda ba ya tafi yana cike da tunanin neman mafita.

Comments and share??


    *Y'AR SARKI CE!!*?? *UMMU BASHEER CE*?
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 830 06-12-2019, 12:04 AM
Last Post: Gimbiya
  *Y'AR SARKI CE by *UMMU BASHEER* Gimbiya 0 611 06-09-2019, 02:37 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 2,118 07-16-2018, 03:34 PM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 8,280 06-28-2018, 10:16 AM
Last Post: Gimbiya
  *NIDA YAH SAYYADINMU* _By_ *Ummu Hanan* Gimbiya 0 7,392 06-24-2018, 12:15 PM
Last Post: GimbiyaUsers browsing this thread: 1 Guest(s)