Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie*
#1
*Ustaziya ko yar'duniya???‍♀??‍♀??‍♀*

 *Written by Anty Mamie*

1

Damko gashin kanta yayi yayinda ya Kara gwara shida bangon bayin a karo na biyu cikin wahalalliyar murya take ihu hawaye masu zafi nabin fuskarta, kazamar banza yar'iska ragowan Gayu Dan ubanki  maina gaya miki kafun inbar gidan nan? Juyo da fuskarta yayi yayinda ya daga habarta matse bakinta yayi cikin masifa ya hankado ta wajen bayin saida ta buga kanta da kujerar dressing mirror take kan nata ya shiga zubda jini, kasa jurewa tayi jin azaban take har cikin kwakwalwarta hakan yasa ta Saki ihu tareda tsugunnawa tana murza hannayanta biyu Alamar hakuri, 'Dan girman Allah AK kayi hakuri na tuba nabi Allah nakuma bika mijina ka yafe mun, takowa yayi har inda take yayinda take matsawa baya saboda gudun azabar dazai Kara manna mata, damko gashin kanta yakara yi tareda janta a kasa har bakin gadon dake dakin ya zauna yana ware kafafuwan shi duka biyu, fuskarta datayi jaga jaga da jini da majina yakara dagowa hadeda kai fuskar shi saitin bakinta cikin magana kamar rada "fadi Laifin ki da bakinki ina jinki, hannu yasa yana dangwalo jinin dake bakinta, " yinwa nakeji, 'tafadi dukda sanin yasan da hakan saboda kulle kitchen dinda yakeyi idan ya shirya mata babban azaba.
shiyasa gakuma zazzabin Dana kwana dashi tun shekarun jiya rabona da Abinci....'shiiiiii ya katse ta yana lumshe ido tareda jefa mata banzan kallo cikin kyama, shiyasa kika samu damar kwanciya harda bcci bayan baki gama wanke mun motocina Dana Saki ba??   Shegiya mayya duk uban abincin Danake kawowa gidan nan bakida aikin yi saici kamar jaka, ooh jakar cema na tuna, yafadi yana jijjiga kanshi, jakar titi, jakar maza, u fat for front u fat for back  Bakida wani amfani rashin Asali baiyi ba wlh saidai kici kiyi katon kashi kita cika mun Masai da wari koh? Dama abunda yasa kika Aure ni kenan, nikuma baiwa na Auro banga mata anan ba, ya nuna ta da yatsa harda dungure kanta Toh dole ki rage shegiyar kibar nan bazan Gina ma wani kato jikin kiba Danni kozaki kwana kina yawo tsirara baki burgeni so dole kifara rage tsoka Hahahaa yayi dariyar da bata wuce kalma Uku ba, "kinyi karya wlh tunda kika hanani farincikin rayuwata a haka zamuyita Rayuwa a gidan nan babu Wanda zai samu abunda yakeso nida ke sai karyan ustazanci Allah a baki fir'auna a zuciya, yafadi tareda tureta kasa, mayya mai nacin maza mai fuskoki dayawa ugly pig kawai, barin dakin yayi tanajin fitar motarsa daga gidan hakan yasa ta zube a kasan tels din dakin hawaye masu dumi  nabin kumatun ta,  'Ashe laifi ne a duniyar mu yin biyyar Aure? Laifi ne tsarkake zuciya tareda Soyyah mai tsafta? Yazama laifi tona asirin zuciyarta?  
Cike da nadamar rayuwar Tata ta Mike tana Jan kafarta dayayi mata tsami bayi ta shiga ta sakarma kanta ruwan zafi hadede gasa jikin nata kodata fito man zafi ta nema ta malka ma jikinta bata daddara ba takara bin lafiyar gado a karona biyu dukda tasan kotayi aikin daya sata ko batayi ba saiya samu dalilinda zai Kara jibgarta anjima garata kwanta saiya jibgeta da tushe. 

Azabar yinwa neya tashe ta misalin biyar da Rabi na yamma gashi ko sallar la'asar batayi ba dakyar ta rarrafa tayi salla cikin zullumi tareda Addu'ar Allah yasa ya bude mata kitchen din jinta takeyi kamar zata mutu saboda azabar yinwa jiri na dibanta ta dakyar take iya bude idonta daya kumbura fuskar nan tayi suntum  tareda dafa bango ta karasa kitchen tunkafun ta karasa ta ganshi a bude wani dadine ya ziyarce ta lokaci daya ta tattaro ragowar karfin jikinta kai tsaye fridge ta nufa tasan bazata rasa abunda zata faraci ba

Ur comment is needed saboda samun kuzarin typing.

 *Ustaziya ko yar'duniya???‍♀??‍♀??‍♀*

 *Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah, my sister yar'amana Amaryar gobe?ina yinki kanwata irin totally dinnan?*

2

Tana budewa tayi ido biyu da ragowar biredi bata damuda sanyin shiba ta barka ledan lodawa takeyi hannu baka hannu kwarya hartana shakewa wurin fanfo ta nufa dukda akwai ruwa burjik a cikin fridge din budewa tayi tareda kafa kanta kamar mahaukaciya ta dinga kwankwadar ruwan Rabi nabin jikinta tana kara tura buredin dukta jika jikinta, saida tafara dawowa natsuwar ta sannan ta dauko Karamar tukunya ta dora ruwan shayi saboda tana bukatar Abu mai dumi a cikin nata, kamar ance ta kalli gefen dirowan kitchen din tayi ido biyu da manya manyan ledoji har guda Uku da farar takarda a kansu, sauri sauri ta karasa wurin
 *sakwara da miyar Egusi, ferfesun kaji Dana kan Sa, dankali a soya da kwai, fresh coconut juice da Fruth salad kunun gyada na shinkafa is needed at 8pm.* wani murdawa cikinta yayi kafun kace kwabo ta yarda takardan bayi ta nufa tadunga kwarara amai saida ta amayo duk abunda ta loda tasan dadewa datayi ba abinci shiya jawo mata aman gashi kuma batayi cin hankali ba, cikin hanzari tagama ta gyara wurin kitchen ta nufa tana salati da kwallar tausayin kanta  Dora hannuwanta duka tayi akai tareda tarin danasanin komawa bccin datayi, dabata komaba da yanzu taci karfin aikin tunda karfe biyu yabar gidan, da gudu tafito da kansa Wanda yayi kankara dauraye shi tayi dayake ta wanke tsaf sanda aka kawo prejar pot ta dauko nanda nan ta markada kayan miyan dazatai amfani dashi harda na kajin hada komai tayi tana neman agaji wurin Allah tasan yau kashe tane kawai AK bazaiyi ba, sauke ruwan shayin data Dora tayi batashi take ba yanzu yayinda ta Dora kansa din akan gas  jawo ledojin daya kawo tayi ta fito da kaji guda biyu GA dukkan Alama Abokan shi zasuzo cin abincin gidan tasan idan Dan tashi ne bayacin girkin ta sai wani ikon Allah, gyara kajin tayi ta hada komai da komai ta Dora, kallan lokaci tayi taga shida harta gota nan takara rikicewa tunowa datayi har sakwara zatayi ga firan dankali??‍♀? Ga kunun gyada dukda sunada soyyar markadadden gyada a fridge tana tanada saboda irin hakan, but aikin yamata yawa koda yake dama jakar shi ce kamar yanda yake cewa, haka taita aikin sauri sauri har tana konewa damai a hannu wurin soya dankali saboda rawan jiki bata damuda azabar dazata Shaba akan tijarar dazai mata a gaban Abokan aikin nashi, dukda ba bakon Abu bane suma a wurinsu duk Wanda mijinta ke kawowa gidan yana sane da cewa batada bambanci da banza, daza'a iya shiga kwakwalwar kanshi a shiga tunanin shi sauron? dake yawo a gidan yafita muhimmanci Kota banza zai hanashi bcci da kuka, kallon lokaci tayi taga takwas saura kwata ko magrib batayi ba salati ta saka Dan sai a lokacin zata daka sakwara dukda tagama komai miyar neya rage ta karasa  da coconut juice din, tana cikin dakawa taji dawowar shi gidan tareda hayaniyar mutane Alamar bashi kadai bane kamar yanda tayi zargi.
      Cikin mintunan da basu wuce biyar ba taji taku Alamar za'a shigo kitchen din yayinda take kulla sakwaran a Leda dukta hada zufan gajiya, 'kallon kitchen din yakeyi a wulakance yayinda zuciyar shi ke Kara suya ji yakeyi kamar ya fusge tabaryar dake gefenta ya sata a turmin yaita kirbata Kila zai huce takaicin data sakashi 
      Naa...naaaa kusan gamaawa bari infara jera abincin a Dinning, tafadi cikin rawan jiki baiko ji karshen maganar Tata ba banda ta raina shi tun yaushe yabar gidannan? Lallai rainin nata gaba gaba yakeyi shikenan bai isa da gidan shiba? Mai Aisha take nufi Dashi? Laifin shine data fara ganin gadon bccin shi shekara Uku da Auren su amma har'yau bata bin umarnin shi? Komawa yayi tafkeken parlon nasu inda yabar bakin nasa su shida,  Abincin data gama tafara jerawa akan dining table dinsu yayinda takoma kitchen domin jiran miyar Egusin yakarasa. 

*More comments more typing?*

 *Ustaziya ko yar'duniya???‍♀??‍♀??‍♀* 

*Written by Anty Mamie*

Masha Allah tun a page din farko naji dadin comments dinku shiyasa nayi page biyu yau nima domin faranta muku, ina yinku yan Group Dina *Anty Mamie's Novel Groups* irin sosai dinnan?

*Dedicated to sister Husnah.*

3
 
Mama na shirya zan tafi haddan, tafadi tareda daukar jakar makarantar ta, "toh Auta har'zaa tafi ooh Allah dai yaimiki Albarka diyar nan wannan San karatun nan naki har mamaki yake bani halima saikace Al'huda huda maza maza a tafi kada a makara aita kwararo hadda, tafadi tana miko mata Naira dari a dunkule, Amsa tayi hade da godiya tana gafda fita gidan taci karo da babanta ya shigo, " baban mu saina dawo, toh uwata Allah yabada Sa'a saikin dawo idan kin dawo saiki kulle kofar gidan da kwado kinji koh? Nasan kafun nan munyi bcci Yafadi tareda miko mata takardar Naira dari shima, toh 'Baba ta Amsa cikeda murna harda sunkuyar da kanta kasa.
Misalin karfe bakwai na Dare  ta fito daga gidan Budurwa ce yar'shekara sha'bakwai cikin  katotan hijab dinta dayake sharan titi tasha Safar kafa da hannu baka iya ganin komai nata sai farin kwayar idonta, tafiya take kamar mai tsoran taka kasa kallo daya zakai mata kaga tarin natsuwa da kamun kai, yarinya abun kwatance a cikin dukkan unguwan nasu duk Wata uwa da zatai ma diyarta fada tohfa da halin halima  ake kwatance kowa ya shaida halima wurin natsuwa halima ce burin kowace uwa a unguwan dattawa da iyayen unguwan kowa nama dan'shi Sha'awar Auran halima saboda yanda gidan nasu yake gidan malamai babanta ne limamin masallacin unguwan yayinda Mamarta takeda tarin ilimin Addini shiyasa yan gidan nasu suke cikeda natsuwa.

Tafiyar minti goma ne daga gidan nasu zuwa  wurin  haddar kodata karasa sainaga harta wuce makarantar tasu ta tsallake babban titin dake gaban makarantar duk a tunanina ko biro zata siya?sainaga ta bude bayan Wata shegiyar farar rangerover  2016 ta kame a ciki saikace ta tsohon ta, batare da bata lokaci ba aka cilla  motar akan titi cikin kwarewa koda na leka motukin motar macece mai tukin, Yammata biyu ne a gaban motar  cikin Wata shegiyar shiga kamar wadanda suka zo daga America a cikin Daren saika rantse da Allah musulunci baije musu ba idan kayi la'akari da kayan dake jikin nasu, 'leemah kin bata mana time fa, inji Wanda ke tukin motar, 'sorry meena abun ne saida siyasa kinsan iyayen namu sai a hankali Ummi nake Dan lallabawa saboda hawan jinin ta danta dagus banda matsala yaci lokacin shi, tafadi tana zame hijab dinta tareda Jan tsaki, bari in cire wannan buhun dukya dumama mun jikina mtseww, vest ce Mara hannu iya Mara tareda guntun wando a jikinta, "yah club din zamu wuce direct koh? Wacce take gefen Direver ta tambaya, noo nooooo feenah r u kidding me? Take a luk at me please saina watsa ruwa sai zufa nakeyi and I need to change my clothe.

 Unguwa ne na masu hannu da shuni motar ta dumfara horn naga tayi a wani katotan gida madaidaici, bude gate din gidan wani buzun mai'gadi yayi, wuri ta naima tareda ajiye motar suka furfuto cikin takun kasaita leema kuwa tuni ta nunke hijab dinta ta Danna cikin jakar islamiyar da babu komai ciki sai kayan maye da kayan kwalliya, a mota tabar jakar sanin tanada duk abunda take bukata cikin gidan, wow cikin gidan yafi wajen gidan haduwa nesa ba kusa ba saidai wani abun mamaki gidan babu kowa sai Yammata Uku da suka shigo yanzu, cikin gaggawa ta fada hadaddan bayi tareda sakar ma kanta ruwa tanayi tana waka fitowa tayi zigidir haihuwar uwarta dukda towel dinda ke bayi I'lla Dan karami data rike a hannun nata tana goge jikinta tana wakan  "cilindion mai taken Am Alive"  kawarta meena ceta buga mata duwawu nan suka hau wasan banza babu kunya a haka harta gama shiryawa nan take ta rikice daga diyar musulmai takoma leemah sak, Yar'malam taki halin Malam, kawayan nata suka furta cikin shewa suna jinjina mata ganin yanda take karairaya a gaban madubi, "da karatu gwanda rawan disko  tabasu amsa tareda Juyowa tana girgiza kirjinta Wanda babu abunda ba'a gani ko bra batasa ba.

More comments more typing.

4
 
Koda suka isa club din suna shigowa aka fara bude musu hanya anga dakin hutu sun shigo Wanda hakan ne taken nasu, wani baki dogon saurayin dake zaune kallo daya zakai mai kasan babban yaro ne  kusan minti talatin da shigowar shi wurin barasa yake sha batareda kula kowa a wurin ba da alamar jiran zuwansu yakeyi ganin ya Mike lokaci daya ya dumfare inda suke batareda bata lokaci ba cikin kwarewa ya ruko kugun leemah tsaf ta lafe a kirjin nashi tana shafawa da hannun hagu basu ko damuda yawan mutanan dake wurin ba, saitin kunnanta yakai bakinsa tareda furta mata *Ustaziya koh Yar'duniya*?
Lumshe ido tayi cike da duniyanci ta chapko lips dinshi na kasa ta shiga tsotsa harda Dan cizon shi Sannan takai bakinta saitin kunnan shi yanda zaiji abunda zatace *Duniya gidan kashe ahu tun kuruci bai wucemu ba* tureshi tayi tana juya kugu ta nufa wurin da aka killace saboda shan hayaki tahau busawa cikin kwarewa da wayewa ta hanci ta baki kamar yanda sauran frnds din nata keyi su a ganinsu kananan chicks neke rawa a club sudai kawai suji sun hau saman gajimare sujisu a duniyar sama yauwa shine magana Alhaji.

Hayaniya ke tashi a parlon Abokanan keta zuba fira AK kuwa sai kumbura yakeyi ganin har 8:30 babu miya ba Alamar Sa dukda komai da komai na wurin kowa nacin abunda yake Sha'awa sunata zuba santi,bakinta rike da sallama shigowa tayi da kular miyar  cikin natsuwa kanta da katon mayafi ta yafa, Amsa sallamar dukansu sukayi banda oga  gaishe su tayi  cikin sakin fuska suka amsa yayinda take Allah Allah ta ajiye tabar wurin "madam sannu da kokari wannan girki haka shiyasa AK kewani kiba yayi fresh abunshi gskia Abokina kayi sa'ar mace zan turo madam dita a Kara hora mun ita gurin girki inji Abokin shi Musa Wanda dama yasaba zolayar ta, murmushin dabai wuce bakinta ba tayi ganin yanda gogan yakara hade Ranshi kamar hadari saika rantse baya wurin, hannun shi rikeda da kofin mug dinda yakeshan kunun gyada sai girgizawa yakeyi kamar baisan da halittar ta a wurin ba dayake kusa dashi take tsaye ta juya kenan zata bar wurin ya Saki kofin cikin rashin Sa'a tayi saurin matsar da kafarta aiko ya tarwatse a kasa yayinda takaici yakara cika shi domin a kafarta yaso ya tarwatse duk Wanda ke wurin sunga abunda yafaru kowa yayi shiru yana kallon shi ba halin magana yahau ruwan masifa, barin wurin tayi cikin hanzari ta dauko tsintsiya ta kwashe tareda goge wurin kamar yana jira tabar wurin yabita kitchen din ta zauna kenan tanacin abincin ta akan kujerar kitchen din, a kanta ya tsaya yana Kare mata kallo, " miyar Egusi dinda ke gabanta ya dauka yana jujjuyawa a hannun shi aikuwa yafara juye mata a jikinta a Hankali harya gama Tass,  ferfesun kan Sa ya dauka Wanda tadan zuba zata sha, batareda bata lokaci ba ya daga shi harda murmushin mugunta jin yanada zafi sosai a kanta yafara zubawa da gudu ta tashi daga zaunen ta matsa gefe jin azabar da kanta ke mata rokon shi ta shigayi yayi hakuri karya Kara tozartata ta gwammace yaimata su kadai a gidan, "wannan ne kike kira miyar Egusi? Eye? Dan mugunta saikace kashin jariri? Babu abunda kika iya sai jawo hankalin yan iskan kwartayan ki nothing baki iya komai ba sai tarin iskanci da munafunci mai fuska biyu bakar munafuka, Please! please!! Am sorry I did my best, " oooh this is what u called ur best swt wiffy? Kureta yayi a jikin bangon miyar dake jikinta ya lakuto yayinda ya murza mata akan ciwon dayaji mata a baki kafun ya fita, well make sure kin cinye komai kin kuma gyara wurin nan cox niba kazami bane kamarki bazan dauki Albazaranci ba,  yafadi yana cusa mata katon sakwaran daya yanzo a hannun shi, 'hannu ya wanke a fanfo sannan ya wuce parlor kamar Wanda akaima bushara da gidan Aljannah, saikace bashi ke cika yana batsewa ba nan ya zage sukaita fira da frnds dinshi daya cikasu da mamaki bakaramin Abu kesa AK dariya ba sai washe hakora yakeyi harda zuba sakwara da Egusi tunda yaga tanaci a kitchen kanshin ya dame shi sai hadiye miyau yakeyi nan ya zage ya kwasa girki yana buga santi da shewa, Aisha kuwa bakinta ta toshe hawaye nabin kumatun ta maiyasa take kuka? Abunda muguntar shi yagama bin jininta ta rigada tasaba Duk abunda yake mata bata taba jin tsanar shiba ko kadan takaicin ta kenan, "shegiya zuciyata maiyasa zakimun haka??
Laifin maina miki kike gasani tareda horo mai tsanani? Duk cikin azabar dazaki gana min maiyasa zaki samun soyyar maso wani? Soyyar abunda baida makiyi bayan ni?

5

Maiyasa? Bakimun Adalci ba duk kece kika jamin maiyasa kika zabi Sani cikin rayuwar kunci? Maiyasa kika zaban min bauta fiyeda yancin kaina? Kuka takeyi tana cusa sakwaran dayasa mata a baki jijiyoyi dukya fito rado rado a goshin ta, tabbas babu abunda batayi ba domin yakice AK a zuciyarta kodan ta kwato ma kanta yanci ya zatayi? Cikin soyyar shi ta girma a cikinta take Rayuwa tun bata mallaki hankalin taba kuma shine sanadin komai shine mugun daya cusa mata soyyar shi cikin mugunta, shiya sata tafara sanshi cikin ruwan sanyi Abun dake Kara mata takaici bafa shi bane Autan maza but why?? Why him? Da mutum Nada yancin ganin zuciyar shi babu abunda zai hanata hukunta Tata zuciyar a karo da dama, inama zata iya damko zuciyarta data nakada mata duka Kota samu sanyin takaicin data sata, tarasa dalilin maiyasa zaiga Laifin ta maiyasa? Maiyasa shi kadai ke tuno mata da ciwon datake burnewa a zuciyarta? Wai har yaushe? Har yaushe zai manta abunda yafaru? Nanda shekara biyu? Ko biyar? Kokuma goma? Kosai bayan yazama Ajalin ta? kirjinta take bugawa saitin zuciyarta hakan yasa ta zauna sosai tanacin sauran abincin nata koba komai ya kamata ta rayu domin AK tasan bazata taba daina sanshi ba but tasan Allah bazai barshi ba tanaso taga sakayyar azabar dayake gana mata tanaso taga yana kukan jini, but ta yaya? Dazata iya ramuwar gayya da tanada yanda zatayi ta cusa mishi Santa kona Wata Daya ne tabbas babu abunda zai hanata daukan fansa,  kila nauyin da takeji a kirjin ta ya ragu tanaso ta koyama kanta kinsa tanaso tayi fito na fito da zuciyarta ta shirya damarar kwatan yancin kanta tun kafun ya kashe ta da kanta, idan banda bakar talauci da tuni ta bar gidanshi koda gari babu suger ne takoma gaban ummin ta saidai kuma wani nauyin zata daura musu ganin da ita suka dogara koba komai idan zaiyi tafiya yanadan barin mata kudi masu tsoka shi take aika ma iyayan ta suna Kara chefane kai koma ta koma Mayyar bazata barta cikin kwanciyar hankali ba"zuciyarta" Dan itace weakness dinta but komai lokaci ne tana kuma Addu'ar sauki wurin Allah. Tanajin bakin nashi  sunbar gidan da alamar yaje rakasu ta Mike da hanzari ta nufa dinning din as expected kuwa taga Envelop jiki na rawa ta dauka kamar yanda take tsammani kudi ne shake a cikin Wanda a rubuce yake duk Randa Tai musu girki haka saisun bar mata gudin kuma AK baitaba hanata ba dukda tasan baida abunda zaiyi dasu, har so takeyi suzo saboda kudin ba karamin taimaka mata da iyayan ta yakeyi ba haka ta tattara komai a gurguje ta gyara ko'ina gudun kada mugun ta yadawo ya sameta, kamar yanda take cemasa Farin muguna, 
Daki ta shiga ta garkame mukulli dukda a banza Wata rana idan ya daka mata tsawa da kanta take bude mai ya jibga na jibga, wanka tayi  tareda gasa jikinta tayi salloli da doguwar Addu'a tabi lafiyar gado dukda taso tashi takai ma Allah kukanta cikin dare amma gaba daya jikinta tsami yakeyi wurin 11 yashigo gidan baibi ta kanta ba ya shiga dakin shida AC yagama jikawa yahau lallausan gadon shi nan danan bcci yayi awon gaba dashi.
Ajiyar zuciya ta Saki jin rufe kofar shi Addu'a tayi ta shafa nan bcci yayi awon gaba da ita ko motsi batayi saikace gawa 

Sai wurin karfe uku na Dare unguwan tayi tsit bakajin motsin komai saboda Dare daya tsala Ustaziya aka ajiye a Wata bakar mota tasha tint baki sidik bakin Saurayin ta datake jida shi mai suna mahuta shiya dawo da ita dukda tanada su dayawa but ajin mahuta daban ne shiyasa duk Wanda ya Santa a harkan yake mata kirari da suna *Ajin hutu*  ita kuma ta amsa *Sai hutu* cikin zumbulelan hijab dinta Saurayin ya maidata bayan sun raba Daren nasu cikin kazantacciyar hanya kudi ya cika mata taf a Jakarta Wanda bata wani Abun Arziki sai gyaran jiki da magungunan mata mahaukata masu shegen  tsada da kudin halal ne tabbas data ajiye kadarori masu tarin yawa dukda account dinta shake yake da kudi Dan bata Karamar harka, amma dayake abun sai a hankali a banza suke karewa, saitin kunnan shi takai bakin ta tareda cizon shi kadan a kunnan tana lasa, *"ka goge mun hadda ta tayau mahuta* mai kakeso incema su malam idan suka Sani tilawa? Kice musu ajin hutu kikaje, yafadi yana Kara jawota, ture shi tayi sanin idan ta biye mishi wasan zai Kara chanza salo, rufe kofar motar tayi tareda lekowa ta window motar ta furta, *sai hutu* gida ta shiga ta Danna musu sakata a hankali inda Allah kadai ke tsare iyayan nata daga barayi da masu yankan kai Dan wani zubin gafda asuba ake direta kuma basa taba Sanin tadawo bata dawo ba sudai sunsan tatafi hadda, wuce dakin iyayen tayi sai zuba munshari sukeyi hankali kwance dakinta ta shiga tana Dan rangaji Dan bata gama matsewa ba, karamin bayin ta dake dakin  ta shiga ta  watsa ruwa ita kanta tasan tashi takeyi saboda tsaro, tafito tabi lafiyar gado babu sallah bare salati dama sallar ta ganin ido takeyi tafi ganewa ta jerosu lokaci daya direct kamar na kwana biyu haka.

*More comments more pages*

*Ina matukar jin dadin comments dinku na Sani nishadi tareda karamun karfin Typing  ashe haka AK keda bakin jini? Dan Allah ayi mishi A hankali babu ruwana idan kuka hadu da fushin Aisha. Anty Mamie's Novel Group 1and 2 ina yinku sosai sosai? godiya mai tarin yawa  fans Dina Wanda na Sani dama Wanda ban Sani ba ana tare.???*

*Dedicated to Sister husnah*

6

Washe gari yakama ranar     Wednesday hakan yasa halima ta tashi dakyar wurin 6:30 domin shirin zuwa makarantar Boko a lokacin SS3 take suna shirin jarabawar karshe kuma tana gama secondary school tabbas Aure babansu zai mata kassncewar basa karatu mai zurfi na Boko.
  
    A' gurguje?
*Wacece halima?*

Isma'el Wanda akafi Sani da Malam liman shine mahaifin halima tareda Ma'haifiyarta Raliya wacce suke kira Mama, dukkan su yan Asalin kauyan Rano ne dake jahar kano Auren zumunci ne tsakanin iyayan nasu Wanda a tarihin gidan nasu tun kaka da kakanni masana Addini ne gaba da baya Allah yabasu ilimin Addini sosai abun saiya Zama kamar gado hakan yasa suke Auratayya tsakanin su, Malam liman na zaune a unguwan sabon gari cikin garin Kaduna ne tareda iyalan shi cikin rufin asirin Allah dukda bawata sana'a yakeyi ba  I'lla iyaka duk juma'a manyan masu kudi dayan kasuwa suna daukar karatun Dare a wurinshi anan babban  masallacin unguwan nasu bayan sallar isha'e kuma yana samun Alheri sosai daga wurin nasu sannan shine limamin unguwan duk Wata matsala inta taso a sabon gari tohfa shawarar Malam liman ake dauka kaf unguwan ana ganin mutuncin shi fiyeda kima, Allah ya azurta shida yara hudu rak a duniya maza biyu mata biyu, Aliyu shine Babba Wanda Dan kasuwa ne yana Aure da iyalan shi a Kano kuma yana taimaka ma iyayan nashi sosai da sosai, sai  tasi'u shine na biyu Wanda yake zaune a Kano tareda Dan'uwan nashi yana taimaka mishi a kasuwancin nashi, sai Rumaisa'u itace ta Uku tana Aure anan garin Kaduna yaron ta daya rak malamin islamiyyar su ta aura, sai Auta halima wacce burin iyayanta kaf yakare a kanta yayinda suke mata soyyar da batada adadi kasancewar tun tashin ta takeda kwakwalwa sosai Ga natsuwa batada Abokin fada ko kadan ga hakuri kamar damo uwa uba sunan mahaifiyar Malam liman gareta kaf unguwan babu yarinya Abun kwatance irin halima hakan yasa dayawa ma basusan ainihin sunan taba saidai *USTAZIYA* saboda natsuwa da kamun kanta Wani abun Al'ajabi kaf unguwan babu wacce za'a nuna ace wai kawar halima ce batada kawa ko daya a unguwan saidai Abokan karatun ta a makaranta, idan akwai matsala daya a rayuwar gidan nasu toh bai wuce yanda basa lura da rayuwar halima ba dukda ita kadai ce a gabansu suna ganin tunda Allah yabata natsuwa har kwatance akeyi da ita tohfa basuda sauran tarbiyyar dazasu bata shiyasa duk abunda tayi daidai ne babu maice mata komai tun tana shekara goma a duniya ta sauke Alkur'ani mai girma yayinda tasha lashe manyan gasa tareda kyaututtuka masu yawan gske a fannin Addini dukda haka tana zuwa makarantar domin Karo karatu akan manya manyan littatafan Addini amma saida Dare kasancewar da rana batada lokaci saboda makarantar Boko daganan kuma zata tsaya lesion, tun halima Nada shekara sha'uku ta rikice tafara harka da kawayen banza yan karya data hadu dasu a makarantar boko dukda babu abunda take Sha'awa kamar rayuwar yanci da wayewa amma ganin gidan data fito shiyasa bata fito da kudirin nata a fili ba tanaso tasan duniya duniya ma tasanta, halima Nada shekara sha'hudu a duniya tafara  kananan shaye shaye harda zuwa club makarantar ma ta rage zuwa sai jefi jefi Kota fito saidai ta biya gidan kawayan nata yan'club suyita shaye shaye tareda baccin asara, Mahuta shine saurayin daya kara budema halima ido sosai, sun hadu a sanadiyyar yawan ganinta dayakeyi a club nan danan yakasa danne maitarsa a fili ganin yasamu swt 14 yaita bibiyarta ganin bata Dade a harkar ba yakara samun kuzarin bude mata ido yanaso ya Raine ta tahada komai dayake bukata shine Wanda yafara kawarma da halima budurcin ta tun tana shekara sha hudu a duniya inda bata damu ba ganin ya mallaka mata duk wani jin dadin Rayuwa har gida yabata itada kawayen ta Wanda yake a GRA madaidaicin gida ne inda shida Abokan shi ke zuwa suna holewar su a gidan kawayan nata dayake korarru ne a gidan iyayan nasu, feenah da meenah, shiyasa suka tare a gidan din'din'din   yayinda leema kuwa bcci kawai ke dawoda ita gidan iyayan ta, dukda haka babu Wanda ya farga da kazantar da takeyi harta iyayan nata saboda komai da taku takeyin sa.

Mahuta Dan gata ne gaba da baya irin sangartattun yaran yan siyasa Wanda babu kwaba babu tsangwama kusan duk abunda yakeyi wurin babanshi ya gada  barewa bazatai gudu danta yayi rarrafe ba baban shi babban mazinaci ne hakan yasa shima ya haifi magaji a zina babu abunda basu mallaka maiba najin dadin Rayuwa dukda baban nashi yana samun labarin ta'asar da yaronsa keyi jefi jefi amma bai damu ba ganin hakan shine wayewa, mahuta bakaramin manemin mata bane kuma Dan kwaya domin baya kananan shaye shaye har cocaine sha yakeyi.

7

Bakaramin San halima mahuta keyi ba inda ya kudira a Ranshi idan lokacin auren shi yayi zai iya Rayuwa da ita dukda yakai munzulin auren amma a cewarshi bayaso ya tsufa abunda ya lura Aure na saurin tsufar da mutum tun bare idan yafara Tara yara gara nanda kamar shekara 45 ya daure yayi, suko iyayan shi ko'a kwalar rigar su Dan suma American style sukeyi basa takura ma yaro a cewar su rayuwar shice yanada yancin yin komai, duk cikin bebs dinshi bai hada leemah da kowa ba a cewarshi saboda tana nishadantar dashi yanda ya kamata, kullum jinta yakeyi zamzam ko kadan bata sakaci da maganin mata hakan yasa yake mata duk abunda takeso gudun kada ta naima a waje abunda baisani ba Yammata irin halima basuda Alkawarin rike saurayi daya tunda zata iyama iyayanta basaja shi awa? yanda cikin takun ta take kula Gayu sosai tareda basu kanta jinta takeyi bazata taba Rayuwa da namiji guda daya a rayuwar taba saboda karfin Sha'awar da takeda shi hakan yasa kullum saita samu mai debe mata kewa inda take abunta cikin kwarewa tareda taimakon maganin Hana daukar ciki, tunda tataba yin ciki kusan sau biyu dakyar tasha inda a lokacin Mamarta keta zuzuta yanda tayi haske dakara cika aiko nan ta sanarda mahuta sukaje asibiti aka burge shi bakaramin wahala tasha ba hakan yasa aka daure mata bakin mahaifa, dayake Allah ba'a mai wayau saiga wani Alamar cikin a jikinta a lokacin su meenah ne suka farga cikeda tashin hankali suka koma Asibiti Ashe mahaifar budewa tayi ba karamin wahala tasha ba inda har jinya saida tayi a gida amma ankasa ganewa mama tadage da dafa mata huntu da ararrabi a cewarsu shawara ce taimata mugun kamu hakan yasa duk Wata saitaje an duba lafiyarta a Asibiti saboda ba kowani maganin planning ke amsarta ba shiyasa yakara cika ta dam dam harta fara losing shape ba tareda ta farga ba.
Halima tana cikin jerin mata masu matsaikacin tsawo itaba gajera ba bakuma doguwa ba, tanada haske farace amma ba Sol dinnan ba dirin jikinta ma babu laifi saidai batada cikar kirji sannan basuyi Kanana sosai ba, yar madaidaiciya  yayinda hancin ta Dan daidai yadan bude kadan baiyi tsini sosai ba saidan karamin bakin ta tareda ido masu Dan girma, baza'a kirata mummuna ba tanada kyau mai sanyi, tareda zubin halitta mai kyau saidai kan nan nata ne toh masha Allah kamar kwallon goriba?a takaice dai irin gashin sister Husnah gareta?? amma tareda taimakon karin gashi wanda dorawa kawai takeyi akai bata yarda aimata kitson shi saboda tsaro shima tana gama abunda zatayi take tunbuke shi saidai kan nata dukda bawani gashi a tsaftace yake zaka ganshi Ras da kitso maiban Sha'awa kwarjinin ta  shike Sa manyan Gayu ke mutukar kaunarta duk kankantar ka indai zaka zube mata kudi toh babu abunda zai hanata budema kafa a takaice dai *The definition of halima is fake*

*Cigaban labari*

 Shiryawa  tayi cikin kayan makarantar nata doguwar Riga wacce tadan haura kugun ta da dogon wandon har kasa sky blue sai hijab dinta iya guiwa fari tas takalmin gida tasa flat a cewarta tunda karatun WAEC sukeyi ba'a takura musu daka ganta kaga student fuskarta babu kwalliya I'lla pawder da man baki Mara kala dukda haka tayi kyau ba laifi, wurin 7:30 tafito dauke da Karamar jaka Wanda katon littafi guda dayane a ciki shima dandai daukan nashi yazama dole ne, iyayan ta tasamu zaune a matsaikacin parlor dinsu Wanda babu komai a ciki sai ledar tsakar daki a gefe daya kuma katon dirowa ne shake da littattafai kala kala na Addini ko'ina tsaf gwanin ban Sha'awa suna zaune akan tabarma da Alama Karin safe sukeyi, dukawa tayi ta gaishe da iyayan nata cikin faraa suka Amsa mata, 'uwata ya karatu? Yakuma haddar taki? Duk inda kike da matsala wurin rashin fahimta ki gayamun sai inkara doraki akai, inji Malam liman, Toh Abba insha Allah bama Wata Matsala, "toh toh yayi haka akeso aita dagewa shi ilimi da kike gani kogi ne sai gaba zakiga amfanin shi maza zauna ki karya ki hanzarta kada ki makara ya fadi yayinda da kanshi ya tsiyaya mata koko cikin kofin dake hannun shi da Alama ko gama sha baiyi ba tura mata yayi gabanta harda ledan kosan daya siyo musu na Kari, mamanta ce ta turo mata wani kwanon Samira ta ajiye gabanta, dumamen tuwon dawa ne miyar kubewa danya sai tururi yakeyi, 'maza ki hada da wannan saboda kiji nauyi nauyi tunda keda dawowa sai shida na yamma, 'a'a mama kosan maya isheni tafadi tana shan koko cikin natsuwa, dari biyu babanta ya mika mata dari Na abun hawa dari  kuma kozata siya wani Abu darana saboda yinwa gashi zata tsaya lesson din WAEC, 'baba kabarshi Wanda kabani jiya da daddare ma yananan tafadi , a'a uwata hada duka aikin chanchanci komai gurina babu abunda bazan iya miki ba dakyar ta Amsa Naira dari wacce tace kudin mota zatayi dashi, 'mikewa tayi cikin natsuwa tabar gidan a'daidaita ta nema drop ta dauka basu zame ko'ina ba sai gidansu na isa kaita Wanda yake a U/rimi GRA  rabonta dawata shegiyar Boko harta manta a cewarta babu abunda kudi bazai siyan mata ba kuma tana dasu, hakan yasa harta biya ansamu Wanda zaimata komai da komai da sunanta batareda ciwon kai ba. tana isa  mai'gadin su dayake zaune kofar gidan sanin cewa daidai lokacin take zuwa, gaishe ta yahau yi Kota kanshi batabi ba  'kada abar kowa ya shigo batareda ambaka izinin yin hakan Ba, tafadi yayinda tashiga cikin gidan, batajin zata iya tarban baki da safe saita huta domin bccine sosai a idon nata.

8

ko lekawa dakin su meenah da suketa ramokon bcci batayi ba dayan dakin tasa makulli tabude ta shiga kassncewar two bedroom flat ne sai katotan parlor a tsakiya tareda toilet Uku, kowane daki da toilet sai daya a parlon ko'ina tsaf tsaf gwanin ban Sha'awa yasha furniture's ba laifi gidan baida wani hayaniya, dakinda yake mallakinta ta shiga saboda babu mai shigar mata nan take sauke mahuta da sauran samarin ta yayinda dayan dakin kuma mallakin su meenah ne.
  Cire kayan jikinta tayi batabar komai ba saidan pant da bra ta bararraje tafara sharara munshari.Kiran sallar asuba neya farkar da Zainab duk nauyin bccin da takeyi tohfa ana fara kiran farko cikin ikon Allah saita tashi, nan ta Mike tayi salla tana zaune a wurin tana lazumi har gari yafara haske sannan tashiga bayi tayi wanka, kwalin plaster dinda ke garkame akan madubin dakin ta bude tareda daukan guda biyu, ta manna daya a goshin ta daya sace amma yabar karamin ciwo, daya kuma a gefen bakinta ta manna, blue material Mara nauyi ta dauko wacce akai mata simple dinkin doguwar Riga ba hayaniya simple make-up tayi tareda feshe jikinta da turare nan tafito Ras abunta dinkin ya amshe ta sosai dukda Zainab masha Allah kamar yanda AK yace she fat for back she fat for front tohfa haka yake a cike take taf tareda taimakon shafaffen cikinta  dake tona asirin kyawun halittarta  ya kwanta ya lafe kamar ba hanji a ciki, irin dogayan matan nanan ne amma ba fara bace bakuma baka sidik ba black beauty ce skin dinta mai tsada  tanada kyau mai tsayawa a rai  hmmmm *'nasan zakuso kuji wacece Zainab ku cigaba da  kasancewa da Yar mutan katsinawa*


Saida ta kyara ko'ina na cikin gidan dukda girman gidan amma yauda gobe tasaba bata wani ganin wahalar hakan kasancewar tun Dare ta wanke kwanukan da akai Amfani dasu tareda goge kitchen din, hakan yasa turaren wuta kawai tasa ko'ina yadau kamshi masha Allah, ragowar ferfesun jiya ta dumama tareda Juyewa a cooler sai sandwich datayi tareda dafa ruwan tea Wanda Yaji kayan kamshi kan dinning ta jera komai da komai cikin rawan jiki tafito makeken harabar gidan nasu wurin jerun motocin AK ta nufa guda Uku masu kyau, 'dattijon mai gadin gidan nasu ne ya matso wurinta tana hango shi ta gaishe shi nan ya Amsa mata cikeda fara'a da mamakin ranarda zata daina wankema AK motoci kusan shekara Uku Abu yakici yaki cinyewa ba karamin tausaya mata yakeyi ba hakan yasa har Addu'a yake mata Allah yakawo mata karshe wahala wurin uban gidan nashi, a iya sanin shi baitaba jin AK ya dagama wani murya ba kokuma ya zagi wani sai matarshi hakan yasa yake cikeda zumudin San jin tarihin rayuwar su dukansu idan da Hali, sanin babu halin shiyasa ya hakura yaja kafarshi tareda komawa bakin aikinsa, 'motocin ta shiga wankewa sauri sauri gudun fitowar shi, hakan yasa tagama dawuri ta wanke su duka tas tareda gogesu ciki da waje a gajiye take lis ko wankin motocin wani katon aiki ne sanin ko kura yagani cikin motar tohfa ta shiga Uku, tana gamawa ta dauki abun gyaran flowers ta nufi  flowers dinda ke zagaye da gidan nasu, dukda ada akwai masu aikin gyaran flowers din harda mai wanke mai motan tun farkon Auran suya sallame su duka a cewarsa kudinsa ya huta an kawo mishi jakar mai Aiki, cike da sabo da kwarewa tashiga gyarawa tagama komai nan ta hau sharar tsakar gidan nasu dakyar ta gama saboda girman gidan,  shiganta cikin gidan yayi daidai da fitowar shi daga dakin shi sanye da dakakken suite milk color yasha necktie black da zanan milk ya tsuke fuskar nan a murtuke dukda haka yayi matukar yin kyau gawani bakin gashi daya zagaye fuskar nashi hakan yakara fito da madarar kyan shi, dogon Namiji ne fari tas Tubarkallah masha Allah, shagala tayi da kallon Sa kaunarsa na Kara ruruwa a ruhinta ji take kamar tayi tsalle ta makalkale shi, ganin batada niyyar daina kallon nashi yasa shi watsa mata Wata shegiyar harara a cewarshi kada ta shafa mai bad luck da sanyin safiya, russunawa tayi tana gaishe shi, 'ina kwana ka tashi lafiya? Kamar kullum wuceta yayi kamar tana magana da dutse kallon dining yayi yaga ta jera abinci kotakan abincin baibi ba, dama baci yakeyi ba sai ranarda tayi matukar Sa'a idan kuma batayi ba wani sabon tashin hankali ne,  duk Randa tayi gigin mai tayin abinci kuwa a jikinta yake Juyewa duk zafin shi.
    Tanajin fitar shi gidan a gurguje tashiga daki Kara gyara jikinta tayi tareda chanza kaya duk sun takura ta, ta matse cikin kananan kaya gajeran wando jins  blue da farar vest, masha Allah ita kanta tasan Allah ya kawata surar ta, shiyasa ta dinga fuskantar matsaloli ada saboda hakan kan dining ta nufa nanta kwasa girkin ta yayinda ta koshi daki ta koma ta zumbula dogon hijab sauran abincin ta juye awani cooler Wanda yake mallakin mai gadi ne, mika mai tayi tadawo tareda kunna TV takamo Arewa24  kwantawa tayi akan doguwar kujera tanata kallo har wurin 11 taji tsamin jikinta ya dame ta baya mata dadi ko kadan, tashar ta chanza aikuwa ta kama Wata tashar wakan turawa sai karkada jiki sukeyi, nan danan ta Mike wai itama zata gwada kozata danji karfi karfi a jikin nata idanta jijjiga jinin jikin ta dukda maganin datasha a banza, rawan ta shigayi tana botsarewa sai bankare bankare takeyi tana juya cikin ta kamar yanda taga sunayi , tayi Akalla kusan minti 10 cikin nishadin data dade batayi ba ganin takoma saikace yarinya yar shekara sha Tara,  karan Abu taji hakan yasa ta waigo da sauri abun mamaki AK tagani tsaye kamar gunki ya sankare yana Kare mata kallo ko kyaftawa bayayi baki a bude aikuwa a 360 tabar wurin tareda garkama makulli a dakin nata, wayarshi daya Saki ya kalla a kasa domin tunda tafara rawan ya shigo da niyyar Amsa waya haryasa a kunne yanaji ana mai magana cikin wayar amma yakasa tabuka komai............yanzu abun Aisha harya kaiga haka? Tuno wani littafin sanin sirrin mata daya taba karantawa idan bai manta ba malamin cewa yayi duk macen datake yawan mika ko bankarewa toh tana cikin tsananin bukatar Namiji, *Innalillahi wa inna ilaihir raji'un* ya furta cikin sanyin jiki.


*Shin wakesan yasan labarin ma'auratan nan masu ban Al'ajabi?* duk maiso ya daga hannu??‍♀

9

*Shin wacece Aisha? Wanene kuma AK?*

Ya'u shine Mahaifin Aisha tareda mahaifiyarta Ramata Asalin yan cirani ne daga  Damagaram dake jahar Nijar, inda suka shigo Nigeria lokacin da yaransu biyu, namiji da yar'karamar yarinya mace wacce mahaifiyarta   Ramata ke rike da ita a hannu, a lokacin bazata wuce shekara biyu a duniya ba, namijin suna kiransa da garbati, yayinda macen suke cemata shatu, Sanye suke da bakaken kayan buzaye yayinda sukasha nadi a kansu daka gansu kaga bakin haure, daga Ya'u har  Ramata irin  dogayen buzayen nanne sosai wankan tarwada  kyawawa Tubarkallah, yayinda cikin ikon Allah  suka sauka  garin Kaduna a unguwan shanu kai tsaye gidan mai unguwa sukayi inda suka gayamai kudirin suna San fara sana'a yanda zasu tallafa rayuwar su, cikin ikon Allah mai unguwn yabasu daki daya Wanda ke  zauran cikin  gidajan shina unguwan  aiko ba karamin murna suka dinga yiba tareda godiya da Addu'a a gareshi, dakin karami ne baida girma sai window kwaya daya rak, inda Allah ya taimake su zauran nada dan fadi hakan yasa Ramata keyin sanwa a lungun zauran, yayinda suka hada bayi da mutanan dake cikin gidan dukda gidan bawani Babba bane dakuna Uku ne a cikin gidan sai bayi guda daya da kitchen dinda kowa ke Amfani dashi, batareda bata lokaci ba Ya'u ya kafa Karamar teburin shayi a gaba da gidan nasu nan danan yafara Tara customer's bakaramin ciniki yakeyi ba darana kuma saiya kasa rake duk anan wurin  yayinda Garbati ke tayashi Zama a lokacin yanada shekara goma a duniya akwai tazarar shekara takwas tsakanin shida Aisha, Ramata kuwa baa barta a baya ba, wankau tafara a cikin gida, itama babu laifi tana samu hakan yasa tace barita gwada shiga cikin gidajan masu kudin unguwan kila zata Dace su dauketa wani aikin, cikin ikon Allah nan saman layin su sosai inda gidaje masu kyau suke nanta tunkara duk gidan data shiga bata dacewa harta fara gajiya ga zafin rana Ga Aisha dake bayanta sai kuka take tsalawa, ganin sauran wani gida daya Wanda yafi duk Wanda take zuwa tsaruwa  tana shirin komawa gida hakanan tace bari ta gwada sa'ar ta, tun daga kofar gidan mai gadin gidan ya dakatar da ita, 'hajiya lafiya? Yana Kare mata kallo sama da kasa, kafun takaiga bashi Amsa sukaji karan horn din mota Alamar masu gidan ne suka dawo, matsawa tayi gefe tareda rusunawa, koda suka shigo hajiyar gidan ce dayara guda biyu tareda ita, babban shekaransa goma sha biyar mai suna Abdulkareem  yayinda dayan bazai wuce  sha'daya  ba, shikuma Abdulhakeem kallo daya zakai musu kaga kallar kamarsu da mamar tasu wacce take fara kar, 'a'a lafiya? Wacece wanchan? Hajiyar ta tambaya tareda nuna Ramata daketa zuba zufa cikin tsakiyar rana, Kafun mai gadin yabata Amsa ta karaso tareda Kara dukawa gaban hajiyar tana gaishe ta, 'amsawa tayi cikin sakin fuska, 'hajiya Dan girman Allah ki taimakeni kibani aikin yi, ta furta cikin rawar murya, achan kasan layinku gidanmu yake Mijina ne mai saida shayi da rake a kasan layi, 'shigo mu shiga ciki hajiyar ta furta ganin yanda Aisha keta tsala kuka kamar zata suma, samarin kuwa tuni sukayi cikin gida hannun su rikeda Leda da Alamar siyya sukayi da mamar tasu.

A babban parlon dake kasan gidan sukai masauki kassncewar gidan gidan sama ne, parlon ya tsaru sosai, a gefen kujera Ramata ta zauna yayinda hajiyar tayi tayi ta zauna kan kujera taki, Wata dattijuwa ceta shigo parlon rikeda farantin ruwan sanyi da lemu tanama hajiya sannu da zuwa, amsawa tayi tareda mika ma Ramata ruwan aikuwa ta Amsa ta sha sosai tareda kwanto Aisha tabata tasha nan tayi shiru tana Ajiyar zuciya da Alama zafi neya dameta dama.

Basu bar gidan ba saida hajiya taimata Albishir din bata aikin wanke wanke da gyaran kitchen da tsakar gida, tunda sunada mai musu girki sannan ba abincin kowa suke ciba, cikin Ikon Allah tafara zuwa tareda samun Alheri mai tarin yawa inda kusan anan take saman musu abincin da sukeci a gida, kassncewar idan abinci ya kwana basa ci, nan hajiya taba Ramata izinin dauka tunda dama Almajirai ake dunduma ma, dukda ranar juma'a ana girki na musamman da yamma Almajirai na layi amsar sadakan abinci mai rai da lafiya, nanfa duniya tadawo masu ya'u da Ramata harma da yaransu sabuwa sunyi fes sunyi kyau sosai sun murmure Aisha kuwa sai wayo takeyi tayi bulbul da ita gwanin ban Sha'awa takawa takeyi ko'ina.

*Woooo page biyu harda Read more har biyu?dukda haka some one must complain??lemmi c*?

10

Alhaji muktar babban Dan kasuwa ne kuma ma'aikacin gwamnati inda yake aiki a NGO yayinda yake zaune a unguwan shanu, tareda matarsa hajiya Bilkisu wacce sukai Auran saurayi da budurwa cikeda soyya, Alhaji muktar Dan Asalin jahar katsina ne matar shi kuma yar Yola ce bafulatana kyakyawar mace sun hadu dalilin wani zuwa Yola dayayi cikin ikon Allah har sukai Auran soyya tareda Arzikin yara biyu duka maza, Abdulkareem shine Babba Wanda akafi Sani da AK, sai Abdulhakeem tun akansu haihuwa ta tsaya musu chak dukda a duniya babu abunda suke Sha'awa kamar Tara yara masu yawa Wanda  burin hajiya Bilkisu wacce suke kira da Mamie bai wuce ta ganta da diya mace ba, hakan yasa kullum Addu'ar ta kenan samun mace,
Alhaji muktar mutum ne mai tausayin talaka hakama matar tasa, ba karamin kyautata ma talakawan unguwan yakeyi ba hakan yasa a karo da dama yaso barin unguwan talakawa na hanashi ganin yanda suke karuwa dashi matuka dukda yanada gidaje masu dumbun yawa a garin kullum arzikinsa karuwa yakeyi saboda yanda yake wanke dukiyar shi inda yaso yakoma GRA cikin manyan  gidajan shi nachan ya koma da iyalan shi amma yan'unguwa sunyi kememe sun hanashi, babu yanda basuyi dashi ba akan yashiga harkar siyasa yaki, a cewarshi bata burge shi.
 zuwan su Ramata gidan yasa hajiyar sakewa da Aisha a cewarta yarinyar na burge ta gata kyakyawa gata yar'duma Duma bakaramin gashi Aisha keda shiba inda tayi gadon shi wurin dangin uwa harna uba, kyawawàn halin Ramata neyasa Mamie takara janta a jiki itada diyarta domin tasha gwadata ta hanyoyi da dama kuma cikin ikon Allah bata kamata dawani laifi, soyyar da Mamie kema Aisha yasa AK shiga lamarin ta indai yana gidan tohfa tana hannun shi har fita kofar gida yakeyi da ita yanai mata wasa kassncewar kullum zaka ganta fesfes an tubke mata gashi gwanin ban Sha'awa, hakan yasa  Ramata na zuwa Mamie ke amsarta taita mata wasa itama, shakuwa sosai ke tsakanin AK da Aisha, inda a yanzu a'kalla takai shekara  hudu a duniya wayau da surutu  kuwa ba'a magana komai Yaya AK, hakan yasa Mamie ke tsokanar AK Take cemishi Angon Aisha, na Aisha wasa wasa shima yafara kiranta da matarshi, inda babu Wanda yayi zargin wani Abu, shakuwar AK da Aisha ba'a magana inda hajiya har kaya siyan mata takeyi hakan yasa Alhaji ma yafara sake mata ganin iyalin Sa na kaunar yarinya shima ta shiga Ranshi, nan Ramata tasa Aisha awata islamiyya anan unguwan tana zuwa safe da yamma, A'nanan har babanta yasata awata makarantar gwamnati tafara zuwa Boko cikin lokaci kadan takara wayau sosai, a kwana a tashi saiga wani cikin ya kuma bullowa a jikin Ramata nan taita rainon abunta har Allah ya sauke ta lfy ta haifi diya mace inda a wannan karan hajiya Bilkisu akaima takwara a cewarsu basuda kamarsu a kaf unguwan bayan mai unguwa, bazasu manta Alkairin su a garesu ba, sunji dadin karan da akai musu nan suka Kara rike juna da Amana.

Abunda masu karatu basu Sani ba shine ya'u Nada wani mugun hali tun a kasarsu nijar babban mashayi ne kuma dan'chacha ko bayan daya Auri Ramata babu abunda yafasa a halinshi talaucin daya mamaye sune yasa ya ajiye shaye shayen a gefe ganin baida kudin dazai siya tareda ma Ramata Alkawarin dainawa yayi gaba daya tunda yara sun fara girma baiso yabar musu abun kunya, ganin yanda kudi ke shigo mishi yanzu gakuma matarshi kusan ta dauke mai hidimar ci Dasha na gida hakan yasa yadawo da tsohon halin shi, tun yanayi a boye har Ramata ta farga hankalinta ba karamin tashi yayi ba, inda zata tasa shi a gaba taita masa magiya tana rokon Sa tana kuka, haka zaikara mata Alkawarin daina wa, Wata rana idan ya bugu tana magana zai lakada mata duka a daki tanaji tana gani zai jibge ta haka zata hadiye kukanta a cewarta bataso kukanta ya tona asirin uban yaranta, haka yaran zasu makure a bango suna kuka  ganin yanda ake jibgar mamarsu, washe gari haka zaizo ya tsugunna yana bata hakuri da nadama, amma hakan bazata chanza zani ba. babu yanda batayi dashi akan su nema hayan gida kusa dasu koda wani daki dayan ne tunda garbati ma yafara Zama saurayi, dakin yamusu kadan ga Aisha tafara girma rai biyar dakin bazai dauke suba amma kememe ya shafa ma idon shi toka dukda yanada kudin yin hakan a yanzu ganin biyan kudin hayan  dakin da zai kama kamar barnan kudi ne gara yasha kudin shi yayi tatil haka zai shigo yana rangaji tareda zage zage tun yan unguwa basu farga ba har aka fara ganewa inda sanaar shayin ma yadaina garbati keyi yanzu shi saidai ya kwanta a gida idan Ramata tatafi aikatau yaita baccin Asara, wasa wasa abun nashi yai tsanani inda akaita kaima mai unguwa karar shi, hakan yasa ya kirashi yai masa nasiha sosai, hakuri yaita badawa, inda har cewa yakeyi asiri akai masa daga kasarsu a cewarshi wai sun sami labarin rufin asirin shine, Jama'a saidai suce Allah shi kyauta, Daya daina na kwana biyu zai dawo ruwa tsundum harma yafi Nada.

Shakuwar AK da Aisha ba'a magana, inda AK bai hadata da komai ba hidima yake mata baji ba gani a lokacin ya mallaki hankalin kanshi yazama kyakyawan saurayi sosai,  babu abunda yafi kauna kamar ka danganta shida Aisha tun bare idan kace mai mijin Aisha hmmm har kowa yagane hakan ita kanta Aisha dadin hakan takeji komai Yaya AK bakinta baitaba rabuwa da sunan shi, a lokacin yafara shirye shiryen barin  kasar zuwa Egypt yin jami'ar shi dukda baiso hakan ba a cewarsa wazai kula maida Aishar Sa, dakyar iyayan suka lallaba shiya tafi, inda Aisha ta rikice lokacin tafara Zama budurwa itama har abinci saida ta daina ci dukta rame nanfa iyayan suka fara tsoran shakuwar dake tsakanin su. A kwana a tashi babu wuya  komai na tafiya daidai banda halin ya'u dake Kara birkicewa dukya rikice yakara tsufa abun na damun iyalan Sa tun bare Aisha da a makaranta har gori ake mata haka zatai ta kuka tun bata saba ba harta saba mai unguwan yaso korarsu a karo da dama tuno Laifin wani baya taba shafar wani saboda darajar matarshi da yaran shi Wanda suka samu shaida mai kyau a unguwan shiyasa ake daga mai kafa, inda Aisha tazama Silent kasancewar batada kawaye a cewar su babu Wanda zaiyi harka da diyar mashayi, nan kewar yayanta yakara cikata saidai ta kwanta a daki taita kukan kewar AK Wanda a lokacin tagama yarda shine farin cikin ta, tagama yarda idan bada shita rayu ba toh rayuwar Tata batada wani Amfani, tagama yarda sanshi takeyi soyya Mara iyaka inda Ramata tun tana biye mata suna labarin harta fara tausaya ma diyar Tata ganin dala da gwauron dutsen data dauko ma kanta ko'a duniyar mafarki AK ba sa'an ta bane hakan yasa Ramata tadage dayimata Addu'a Allah ya yaye mata larurar data Dora ma kanta.
Ta fannin mamie kuwa komai na tafiya daidai duk sanda zasuyi waya da AK baida abun tambaya sai Aisha, tun bata damuwa abun yafara damun ta nan ta taka mai birki bataso zargin da takeyi yazama gaske, ganin yanda Ranta baisan hakan yasashi daina tambayar badan Ranshi naso ba, Mamie babu abunda suka Fasa yima Ramata da yaranta dukda sanin halin ya'u saidai mommy taita bata hakuri da tattausan kalamai.

A kwana a tashi lokaci na ta tafiya tun Aisha nasa ran dawowar AK harta dangana saidai soyyar shi nanan daram a Ranta tareda Alkawarin bazata taba mai kishiya a Ranta ba, yayinda ta bangaran shi kuwa  iyayanshi kekai mishi ziyara a cewar su gara ya zauna wuri daya saiya gama komai da komai tas na karatun  shi domin yana hada Degree gara ya karasa gaba daya   zasu dinga zuwa tareda kanin shi Abdulhakeem Wanda a yanzu shima yake shirin komawa chan karatu.

A lokacin ne makerin budurwa yagama kawata halittar Aisha fiyeda tunanin mai tunani tahada duk abunda ake bukata a wurin mace, Allah ya wadata tada zaunannan baya 'duwawu' ga tudu kamar ka Dora Kofi ya zauna daram? ga hips masha Allah ga kirjin nan ya cika yayi dam Tubarkallah, da taimakon shafaffen cikinta shape din halittar ta yakara baiyana, ko hijab tasaka idan tana tafiya komai na jikinta saiya dinga kadawa, kiban jikinta a wuri biyu yake  hakan ba karamin tsokale ma samarin unguwan ido yakeyi ba uwa uba Allah ya zuba mata natsuwa ta musamman kullum cikin dogon hijab zaka ganta hakan yasa yan iskan samari saka fara samata ido, inda Ramata ta farga Kullum cikin yimata Addu'a da nasiha takeyi hakan yasa take Kara suturta kanta kokadan bata shigan banza.

*Bakar rana........coming soon*
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 15,126 12-17-2018, 03:07 PM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 12,988 12-17-2018, 03:06 PM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 11,994 11-28-2018, 09:33 AM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* Gimbiya 0 12,890 11-26-2018, 11:44 AM
Last Post: Gimbiya
  ABUBUWA 17 MAFI BAN DARIYA A DUNIYA Gimbiya 0 2,153 11-13-2017, 04:04 PM
Last Post: Gimbiya
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* 0 2,409 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* 0 3,326 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *Ustaziya ko yar'duniya* by Anty Mamie* 0 2,360 Less than 1 minute ago
Last Post:Users browsing this thread: 1 Guest(s)