The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*DREAM GIRL* by Deejah Abdul
#1
Sukuma su mom suka juya zuwa gida kowa nata addu'a a ransa Allah ya sa qarshen wahalar kenan Allah ya bata lfy. ???INDIA??? Direct babban birnin mumbai aka saukesu, aka saka ameerah ambulance sai CITY HOSPITAL, direct ana isa suka kar6eta dama anyi process din komai kan suzo, operation room suka kaita, aka turata cikin wata na'ura ayi checking idan bata tareda ko wache matsala, luckly ba wani brain damage, sai targade da aka samu a hannunta, sauran ciwukan kuma anyi treating dinsu tin a 9ja, doctors sukayi mata abunda ya dace sukayi shifting dinta zuwa icu, khaleed da ameerah suka taso doctor ya gayamusu, there patient is ok now, there are som minor issues da ba'ayi treating ba daz y she went into comma 4 days, but yanzu zata farfado within d next 24 hours, now she is in icu za'a ajiyeta nan 4 observation, they can go nd c her now. Khaleed da kausar suka wuce dakin ameerah kausar ta zauna kusa da ita, shi ko khaleed ya juya zaifita kausar tace big bro ina zakaje, harara ya watso mata inda kika aikeni, ya juya ya ficewarsa ya barta da mamakin inda zaitafi, bayan angayamasa matarsa zata iya farkawa any moment. Direct khaleed airport ya wuce yafara neman ticket na jirgi zuwa germany, luckly ya samu coz few passengers ake nema kawai, ana gama komai khaleed ya keta hazo sai germany without any regret. Khaleed bai dade da fita ba kausar ta dora kanta a gado bacci yayi gaba da ita, chan cikin bacci taji kamar ana ta6a hannunta, cikin hanzari ta buda idonta, ameerah taga tana motsa hannunta, tashi tayi taje kusa da kanta, tafara girgiza ta sister inlaw, ameerah ta bude idonta, amma kuma sai tafara ihu tana fizge-fizge, husnah plz don't kill me, husnah plz don't kill me. [9/14, 4:27 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣5⃣ kausar tafita da gudu taje ta kira doctor, suka shigo cikin gaugawa, nurses suka riqeta tanata fizge-fizge wani doctor take ya dauko wata allura yayi mata, cikin second da baifi 20 ba ta langa6e, ta koma bacci, kausar cikin kuka take tambayar doctor what is wrong wit my sister? Doctor yace mata kar ta damu shock ne kawai da ta samu kan abun ya faru da ita, tsoron da tajine bata samu expressing dinsa ba, shiyasa ta tashi dashi amma komai zaizama normal yanzu da ta farka bacci, kausar ta musu godiya suka fice, taso ta kira khaleed ko su mum amma sim card dinta is not working, kuma bazata iya fita tabar ameerah ba kar ta sake farkawa da taje ta siyo new
new simcard zaunawa tayi ta qurawa ameerah ido, daga bisani ta fara tofa mata addu'oin da ta iya. ???GERMANY?? Khaleed yana sauka qasar germany cab ya tara, yace akaishi near by hotel, aka kaishi ya sauka, ya nufi reception ya kama single room 4 2days, sauke er qaramar jakarsa kawai yayi, ya fito da wani qaramin diary yana duba adress din skul din su salmah da ta ta6a bashi, fitowa ya sakeyi ya dauki cab ya bashi adress din, ba'a saukeshi ko'ina ba sai LUDWIG MAXIMILIAN UNIVERSITY OF MUNICH. Aka saukeshi direct admin block ya wuce ya fara bincike Salmah Usman Nasir a final year student psychology department, akayi checking akace masa babu meh wannan sunan a final year students, khaleed yace a sake dubawa still akabashi same answer, but yayi request a bashi details na othr salmah da ke skul din, matar taga kamar ya shiga damuwa ta taimaka ta bashi, khaleed ya fara yawo diffrnt departments but duk salmar da ya gani ba salmarsa bace, yaci uwar wahala, ya gaji ga yunwa ga qishi, ya samu wani seat qarqashin wata bishshiya ya zauna, wata budurwa itama er nigeria da tabi wurin kusan sau 3 tana ganinshi, ta nufi wurinshi, excuse me handsome tace masa, ya dago idonnan da suka fara ja ya kalleta, robar ruwa ta miqomasa ba gardama ya kar6a ya kwankwade yace mata thanks, tace tindazu nike wucewa tanan ina ganinka, may i help you, ya gayamata salmah usman nasir yake nema, tace y don't u call her? Yace d number is not going, tace masa let me see her photo if u have one, cikin hanzari ya zaro wayarsa yanata jin haushi me yasa tindazu baiyi tinanin nuna picture ba, ya miaqawa budurwar tana gani tace masa ohh u mean (SUN)? SUN khaleed yace? Yace daz what we call her here, ae tayi graduating tin last year she is working now, tace tindazu da ka nuna picture dinta da baka sha wahala ba, coz kowa ya santa she is popular............Wata figigiyar yarinya ce ta katseta, ke virus who are u currupting there, tace SNACKS dis handsome is looking 4 Your SUN, kallon sama da qasa ta masa mal lfy kake neman sun? Wadda aka kira da virus tace jst help him out tindazu yake nemanta, ta6e baki tayi aike kinsan SUN bata komai da da namiji, ba namijin da ya isheta kallo, tace malm ko kaje zaka 6ata time dinka ne, yace ni brother dinta ne ki taimakeni plz, tace shikenan address din hotel dinda take zama ta bashi, cikin jin dadi yayi godiya ya wuce da sauri, a ransa ko yana gode Allah da yasa salmarsa ta riqe masa alqawari bata kula ko wanne namiji, cab kawai ya shiga ya nufi hotel dinda akabashi address. [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣6⃣ Direct THE CHARLES HOTEL MUNICH, Aka kaishi, ya sauka ya nufi reception, ya gayawa matar he is here to visit salmah usman nasir, receptionist tafara bincike, tace masa they don't have anybody wit dat name here, take ya ciro wayarsa ya nuna mata photo, tace oh you mean SUN? Is she especting ur visit now? Khaleed yace no, matar tace yayi haquri tayi masu gargadi, idan ba ta gayamusu tana especting baqo ba, kada ma su saurareshi, khaleed yace just help me plz, i came from Nigeria just to meet her, matar taga ya damu ta daga waya ta kira dakinta, tana cemata tanada baqo kafin ta qarasa zancenta, tace mata batason ganin kowa yau ta kashe wayar, khaleed yayita insisting matar tace sam she already gave her orders su hotel dinsu baya violeting order na customers dinsu, khaleed ya gaji da tsayuwa matar tace masa ya dawo gobe, ya rubuta details dinsa yace taba salmah din plz, tace zata bata, sannan ya fice jiki ba qwari, ga yunwa ga gajiya, cab ya tara yace akaishi restsurant, CHOPAN SCHWABING RESTSURANT aka kaishi, most of there food there Are italian cuisine, haka yayi order yaci ba dan dadi ba, saidai dan kar yunwa ta illatashi, ya koma hotel dinsa HOTEL METROPOL, ramuwar salloli yayi, ya watsa ruwa ya kwanta yana jiran call daga salmah, shiru-shiru har baccin wahala ya kwasheshi. ???INDIA??? Kausar na zaune kan sallaya ta idar da sallar isha'i, Abun duniya ya isheta, mamaki da takaicin yaya khaleed ya addabeta, tun da suka iso india fa ya kama gabansa, ita batasan inda yayi ba, gashi har dare yayi, tayi zugum taji alamun ameerah ta motsa, tashi tayi cikin hanzari ta isa wurinta, da kadan-kadan ta fara bude idonta, idonta qyam sai akan kausar, ta dade tana kallonta tareda tunano abunda kausar murmushi ta sakar mata welcome bak sister inlaw kin tsoratamu ba, ameerah murmushin itama tayi mata, tace ina su mom? Kausar ta rungumeta, ameerah tafara waige-waige, tace inane nan kausar? Tafara yunqurin tashi zaune, kausar ta kwantar da ita, tace bari ta kira doctor first, doctor na zuwa cikin fara'a yace welcome bak my beutufil patient, ameerah tayimasa murmushi, zuwa yayi ya cire mata, na'urorin da ke jikinta da suke monitoring dinta, tayi yunqurin tashi doctor yace kausar taxo ta taimaka mata, wata allura doctor yayi mata, dafa hannunta tayi, tayi qara, doctor ya sangale mata hannu, a wata hand holder, da suke sakawa wa enda suka samu rauni a hannu, yace mata kar ta damu, in 2days time hannunta zai zama normal, yafita tareda cewa zasu aiko abincinta yazo, tarda magani a nurse wil help her take d medcine, ya fita ameerah tace kausar ta taimaka mata ta shiga toilet her body is weak, tazo ta kamata tace sis almost kinkusa 1week a kwance ba dole jiki yayi tsami ba? Takaita toilet tayi mata brush, ta barta tayi abunda zatayi sannan ta kamota suka fito, koda suka fito nurse na jiransu, tea mai kauri akaba ameerah tasha, da wani potatoe porridge, sannan nurse ta bata magunguna ta fita. [9/14, 4:30 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣7⃣ kausar dawowa tayi kusa dani ta zauna, ta quramin ido, na hure mata ido nace miye haka? kamar kinga wata sabuwar halitta, tace ae itace, sister inlaw munshiga tashin hankali, Allah we thought u ar going to leave us, nace kausar kenan ae mutuwa na kan kowa, da lokacina ne yayi dole zantafi, kausar tace sai gashi kindawo, mukayi dariya, tace ba inda zakije sai kin haifawa broda na kyawawan yara kamar ke, nace yo ni har wani kyau ne dani? Tace sis ae ke kyaunki qyalqyali ne kawai bazai gani ba, natural beuty, beuty without makeup, nace kausar da ke namiji ce sai kinyi tsari, nace baki gayamin inane nan ba, tace mumbai india kike sis, na dan fito da ido india fa? Ta gyadamun kai nace duk ina ina akazo india? Tace kishiga comma ne sis, toh mu biyu kawai mukazo nan? . ta dan ta6e baki tareda yaya khaleed mukazo, nace mata yana ina? Oho tace tinda mukazo ya fita banqara ganinsa ba, cikin rudani nace sis shine kikazo nan kika zauna, dariya tayi tace jst relax ni naji ajikina lfyarsa qalau, shiyasa ban wani tada hankalina ba, shi bai damu ya gayamin inda zai tafi ba, meh zaisa na damu kaina? shiru nayi ina addu'a a raina Allah ka tsaremun shi a duk inda yake, nace sis kwanana nawa ne a comma? Tace aikinsan 3 days to your wedding abun ya faru, jiya aka daura aure, yau mukazo nan, daura aure nace? Dariya tayi kindauka anfasa daureki ne? Ai ke matarmu ce yanzun sai yanda mukace, ni nama rasa meh nakeji dadi ne ko damuwa, nace yau kusan 5days kenan ko? Tace eh nayi yunqurin tashi, tace ina zaki kuma? Nace ina naga zama sallar kwana biyar a kaina, tace ki bari ki qara samun sauqi mana, miqewa nayi ae na warke weakness ne kawai, ta taimakamin nayo alwala, sallaya ta shinfidamin na zauna na fara ramuwar sallah. Tun kausar na jirana har tagaji ta tashi ta fita waje neman sim card, da tambaya aka nunamata wani wurin ta siye tayi register, ta juyo, wani shop tagani na snacks da drinks ta shiga ta siyo ta dawo, har ta shigo inata rafka sallah, layi tasa ta zauna jirana, sallamawa nayi, tayi sauri tace sis bari na kira su mum, cemata nayi kinsan fa 5hours ne tsakanin india da nigeria, yanzu nan 8pm chan kuma fa? Tace kusan 1.am kenan nace toh kingani ki bari har da safe kawai karki tashesu bacci, tace ok bari na kira miki su aliyu, nace ae suma sunyi baccin, tace sis Aliyu fa na egypt da salim, baki na washe kai haba when? Tace suma yau suka wuce, nace Allah sarki danuwa, i'm so happy 4u, kausar tasa kiran salim, take ya daga yanajij muryar kausar yafara murna, bayan sungaisa yace ina sister inlaw? Tace ta farka gata ku gaisa ta miqomin waya, muka gaisa yamin ya jiki, sannan nace ina aliyu, yace bari na kaimasa yama kasa sakewa sai zancenki yake, Aliyu aka kaima waya cikin hanzari ya chafke wayar, ya fara sweet sis, nace na'am sweet bro, sai kuma ya fashe da kuka, nace danuwa miye na kuka kuma? M ok now, yace kukan farinciki ne sis, ni badan mama ba Allah da bazanzo na barki ba, nace toh meh zakamin idan ka zauna ali? Naji dadi da mama ta hanaka zama, nasihohi na masa akan ya kula da karatunsa mukayi sallamah. Sallolina na koma na cigaba, tin kausar na jirana har tayi bacci, sai around 2.am nagama nayi nafiloli nayiwa kaina da khaleed addu'a, Allah yasa aurenmu ya zama alkhairi, nasa alarm a wayar kausar na dan kwanta, around 5.30 a.m alarm ya tashemu na tada kausar mukayi sallah, bayan mungama azkar munkaranta alqur'an, muka fara fira, kausar na gayamin abunda ya faru ina comma, lura tayi ita kadai ke zuba ni namayi bacci, itama ta kwanta takoma bacci. [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 8⃣8⃣ ???GERMANY?? Khaleed bai farka ba sai da gari ya waye, cikin hanzari ya miqe, yaje yayo alwala ya kabbara sallah, yana kammalawa ko addu'a baiyiba ya dauko wayarsa ya duba ko zaiga missed call or txt din salmah, amma ba ko daya, tsaki yaja ya jefar da wayar, ya koma yayi addu'a yana roqon Allah yasa yaga salma yau, ya koma india kan su mom suzo su samu bayanan, telphone ya kira yayi ordering breakfast aka kawo masa yaci ya qara kwantawa ko zuwa qarfe goma ya koma hotel din idan bata kirashi ba. Salmah ce tafito daga room dinta ta sauko, tazo gun receptionist ta kar6i saqo, har zata wuce ta tuna da saqon khaleed, ta miqa mata dubawa tayi, tayi tsaki shi wannan ma dan jaraba biyota yayi a germany, itafa batada time din yin wani aure a yanzu, yaga takardar tayi idan ya sake zuwa let me know plz ta wuce wanta. Around ten ya farka, miqewa kawai yayi ya watsa ruwa, ya chanja kaya ya fita, cab ya tara sai charles hotel, yana isa yayi reception, yace taganeshi? Tace eh ba shi yazo jiya ba? Yace bataba salmah saqonshi bane? Tace tabata tace idan ya qara zuwa a sanar da ita, take wani farinciki ya ziyarci zuciyarsa, ta daga waya ta kirata, bayan ta saukene tace, tace ya jirata a CHOPAN SCHWABING RESTAURANT nan da 1 hour, khaleed bai ko damu ba ya kama hanyar restsurant din, dama jiya chan yaci abinci, ko da yaje ya kama table coffee kawai yasa aka kawo masa, tin yana kallon agogo har ya daina, gashi jirgin qarfe 2 zaibi ya koma india, wayan kausar ya kira not available, yayi tsaki har ya gaji, sai wata zuciya tace masa ya tafi, wata tace karka tafi tazo ta qara fushi, dama kasan kai kamata laifi sai ya dawo ya zauna, har qarfe daya khaleed na zaune, waiters sai zuwa suke suna tambayarsa idan da abunda yakeso, khaleed sai coffee yake order yana kwankwada dan jiya yaci abincin wurin bai gane komai ba. Qarfe daya salmah ta fito hotel dinta zata fita, taje reception ta bincika idan tanada saqo, sai lokacin matar ta tunamata da wanda tace ya jirata, tsaki tayi sannan ta fito ta nufi wurin. Khaleed ya miqe haka ya tashi ya koma hotel din, ya ganta tsaye gabanshi, wani murmushi ta sakar masa tace babyna m sorry, na zana jarabawa ne, murmushi yayi ya nuna mata wuri ta zauna, aransa yace ko mehyasa batason nasan ta gama karatu sai kuma ya basar, haquri nazo na baki salmah, kinsanj rudani na kasa sukuni, na rasa nutsuwata a kanki, kinqi ki saurari uzurina, katseshi tayi wanne uzurin ai ka riga kayi auren kuma, u break our promise, so ni bazan ta6a iya sharing dinka da wata mace ba, indai abunda ya kawoka kenan u better go, ta miqe zata tafi, sai ga khaleed a qasa ya riqe qafan salmah, ni Deejah haushi kamar na mutu baisan wahalar da nasha kan na biyo shi germany ba, amma abun takaicin da zangani kenan ? ba'anan ya tsaya ba khaleed harda kuka salmah ta saurareshi, ni DEEJAH kamar na rufeshi da duka, ga ameerah chan zata mutu ma kansa yazo yana kuka kan wannan mai kama da aljanun, leqawa nayi na qaremata kallo gajera ce fara tas kyakkyawa ce ainun da wasu ido, idan ta budesu sai ka firgita kan girmansu????. Dawowa tayi tazauna jikinta yayi sanyi a raina nace er qwal uba? gwanda ma karki haqura, ta marmada qattan idonta, toh ina jinka, shiko gautan yafara fede mata biri har wutsiya yanda akayi ya auri ameerah, amma shi ko kadan baya sonta, nace zaka sota dan malfar uba? waigowa sukayi na duqe qasan table basu ganni ba, sai cewa tayi toh shikenan naji na haqura i'll get bak 2u soon, ni zantafi miqewa yayi kamar jela ya bita yana mata kalaman soyayyah ni Deejah tsabar haushi kasa rubutawa nayi, motar ta taja ta tafi ya bita da ido kamar maye saida ta 6acemasa. [9/14, 4:37 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah Abdul 8⃣9⃣ Ajiyar zuciya khaleed yayi, Allah na godema da kasa ameerah ta sauraren, sai a lokacin ya duba tima 20 minutes to 2 cikin hanzari ya tari cab, ya koma hotel dinda ya sauka shiga kawai yayi ya dauki jakarsa ya wuce airport, koda ya isa jirgi kadan ya tashi, anyita qwalla kiran sunansa baya kusa, daqyar ya samu aka barshi ya shiga, suka daga sai india. ???INDIA??? ameerah da kausar sai around ten suka farka, kausar ta taimaka mata tayi brush sannan ta barta tayi wanka, ta dawo ta kwanta itama kausar ta shiga, koda ta fito nurse ta kawo breakfast dansu asibitin su kebawa patient abunda zasuci amma duk a kudinka, kausar ta taimaka mata tayi breakfast itadai ameerah taste din abincin india yayi mata, taci tasha magani, kausar kuwa snacks dinta ta diba taci da drinks. Kausar ta lura ameerah tayi wani zugum tace bari na kira su mom, tasa call dinsu take mom ta dauka, tanajin muryar kausar tace hope good news zaki bamu, kausar tace yes mom ta farka tin jiya ma now she is alright, murna suka fara, mom tace toh meh yasa baki gayamana tin jiyan ba? Kausar tace mom bansamu simcard da wuri ba sai cikin dare, nasan kunyi bacci, sis ameerah tace nabari har da safe, mom tace toh kibamu ita mana, ta miqomin wayar, waya mukayitayi dasu, mom, mama, suhaila, fatima, siyama da khairi kowa saida akaba mukayi magana, mom tace su suna airport ma yanzu zasu taso, nace mum ku duka? Tace a'ah itada mama dai su suhaila a gida zasu zauna har adawo, tace ina khaleed? Na daburce nace mata ya fita siyo magani kausar ta dago kai da sauri ta kallonj, nayi mata alama da hannu tayi shiru, daga bisani mukayi sallamah, akan sai sun iso. Bayan mungama sai ga kiran su salim da aliyu haka mukasha fira suma saida kausar ta kar6e wayan ta kashe, nace ya haka sis? Tace magana zamuyi kafin su mom su iso. Kallon tuhuma tayimin, meyasa kika hana na fadi gaskia akan yaya khaleed? Nace toh meh zakice? Tinda aka sauka india ya gudu? Kinsan meh yajeyi ne? Ta6e baki tayi, amma koma mene ae baikamata ya kwana achan ba, sister inlaw ki gayamin gaskia tsakani da Allah, wai miye tsakaninki da yaya khaleed? Qirjina ya buga nace mata kamar ya? Ni bangane ba, tace ni Allah na lura banga wani chemistry a tsakaninku ba, kwata-kwata wanda ya zauna tareda ku baxaiga alamun soyayya a tareda ku ba, duk da nasan yayana daban ne, amma ni nasan sanda yayi soyayya da wata er abokin dad ba haka yakeyi ba, take zuciyata ta buga nace mata kinsan salmah ne? Tace farin sani kuwa? Amma ke ya akayi kika santa? Take qwalla ta cikon ido na share, zuwa tayi ta dafani, dama ni nasan da wata a qasa, titsiyeni kausar tayi saida na kwashe komai na gayamata. Ajiyar zuciya tayi, gaskia kinyi wauta sister inlaw, amma kuma banga laifinki ba so ne yaja miki, kuma da kingayawa broda gaskia bazai kalleki ba, amma yanzu kinada hope kuma ni zan taimaka miki to fulfill your DREAMS, hugging dinta nayi ina kukana inamata godiya ita kuma tana bubbugamin bayana alamun rarrashi. Sakinta nayi nace mata salmah fa? Tace diyar abokin dady ce, senior ta ce a secondry skul, tin alokacin nasan tana soyayya da broda, har lokacin da ta gama aka turata germany karatu, amma daga time din banqara jin zancenta ba ko a gida broda bai fadi ba, so mundauka ma sun dade da rabuwa, i was suprised ma da kika gayamin har yanzu ita yake so, toh ko meyasa sukaqi fada a gida oho, amma ni sis inaganin Allah shi yasan abunda ya tsara shiyasa haka ta faru, ni yarinyar tuntuni batayimun, tafiye jinkai da yiwa mutane kallon banza, itama bata qaunar talaka ya ra6eta shiyasa bama jituwa tin a skul, kuma mudai yanzu kece choice dinmu, zan tayaki fighting till d end, hugging dinta nayi cikin farinciki, araina nace samu dafa, Allah ya nunamin cikar burina. Kausar tace now dat i think may b bro germany yaje, nayi rau da ido, tace jelous ko sis nayi murmushi tace karki damu, my broda iz not dat bad bazaiwuce limit ba, doctor ne yashigo yana tambayar meh nikeji now nacemasa jst a weakness yace it normal zandaina ji, allura yamin zaifita, nacemasa zanfita nagaji da zama wuri daya, dariya yayi yace lallai sauqi yazo, kausar ta taimakamin muje garden gatachan ya nuna mana, tashi tayi ta kamani muka nufi gun. [9/14, 4:41 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah Abdul 9⃣0⃣ Garden din muka shiga muka zauna ko'ina luf-luf gwanin sha'awa sai kukan tsuntsaye kakeji, shiru mukayi 4 sometime kausar tace sis amma kinsan ya kamata mom tasani ko? Da sauri na dago na kalleta, nace dan Allah sis karki fada, inajin kunyar mom da wanne idon zan kalleta, idan tasan plan dinda muka shirya, zataga kaman mun renamusu da hankali ne, kinga mom ta yarda dani sosai, kausar tace nima dalilin da yasa nace na gayamata kenan, dan nasan tana sonki sosai kuma ta yarda dake, so zata fahimce dalilin qaryarki kuma m sure mom zata taimakeki. Nidai na girgiza kai sister inlaw just promised me bazaki gayawa mom ba, dis is my battle i need to fight it alone, tinda ni nasaka kaina, a ranta tace zanyi shiru 4 now, amma duk naga abund zai baki wahala dole mom ta shigo ciki dan broda baya tsallake maganarta, a zahiri kuma tacemin shikenan sis bazan fada ba, and remember this is our fight, not yours alone, hugging dinta nayi ina qara godewa Allah ashe dama za'a samu dangin miji haka? Nidai nayi dacen dangin miji, saura mijin shima Allah ya dorani akansa. Su mom an iso birnin mumbai india, direct mota suka shiga sai FOUR SEASONS HOTEL MUMBAI, suka kama kowa daki, suka sauke kayansu sannan suka nufi adibiti. Khaleed ma yayi landing saidai traffic hold up ya tsayar dashi a hanya. Muna zaune a garden muna hutawa dan ni wurin yayimin, wata nurse tazo tace its time 4 my medcine, natashi muka koma dakin da aka maidani, dan tinda na farfado anyi shifting dina daga ICU, Mom suka iso sukayi inquiry aka basu number dakina suka nufi dakin. Ina zaune ina cin lunch sai ganin su mom nayi, da saurina na miqe har ina qoqarin faduwa, dan haryanzu jikina ba qwari na nufi wurinsu, kausar dariya tayi sister inlaw wlh kiyi a hankali kar jinya ta dawo sabuwa akayi dariya, mum ta riqoni ta rungumeni m so happy to see u my daughter nace me too mom, mundade a tsaye a haka sannan ta sakeni naje na fadawa mama, janyeni tayi kinga ni karki karyani, lura nayi tana share qwalla, na tayata mama kukan dadi kike ko? Karki damu bazan mutu da wuri na barki ba, kema sai kinga jikokinki, nayi sauri na rufe baki alamun jin kunya, dan qaramin duka ta kaimin nasa qara, tace mara kunya ashe har yanzu wannan bakin bai mutu ba, dariya akayi mom ta jawoni ta zaunar dani, nidai karki jimata ciwo daga zuwanki, mama tayi dariya ae kunfi kusa yanzu ni gwanda ma da kika ma da kika daukemun ita, nace mama idan na tafi sai kinyi missing dina fa, Mom tace ina mijin naki na buda baki zanyi magana sai gashi ya fado kamar daga sama, sallamah yayi aka amsa jikinsa duk yayi sanyi ganin su mom da yayi, mom tasha mur daga ina kake, yarasa meh zaice mata, tunaninsa mun gayamata tin jiya bayanan, sosa qeya yayi mom neman wani doctor na tafi a germany, kausar ta kallan na kalleta, mama tace germany dannan wato duk likitocin da ke india basuyi maka bane? Mom tace toh ina likitan yake? Yace bayan na tafi ne kausar ta kirani ta gayamin ameerah ta farfado kuma ta samu sauqi shiyasa Ban daukoshi ba, kausar ta koma kallona nayi mata inkiya tayi shiru, harara ta watsomin ta kauda kanta, mom tace kenan ko hotel baku sauka ba? Tinda kai tin jiya bakanan kausar kuwa nasan a asibiti ta kwana, to kuzo muje hotel dinda muka sauka ku samu daki. Cewa nayi mom plz kice doctor ya sallameni nima karku barni anan, Allah na warke, doctor ne ya shigo, ya duba hannuna yamin allura, mom tace doctor za'a iya sallamarta kuwa? Yace no saidai zuwa gobe idan sun kwance hannun idan aikin yayi, zasu iya tafiya dani zan iya dinga zuwa kullum na kar6i allura 4 3days. Mom tace toh mu mungaji munso mu huta, ameerah ki haqura sai goben kawai, suka juya zasu tafi, kausar ma ta dau jakarta, mom tace ina kuma zaki? Tace mom nima inaso na huta ga mijinta nan ya tsaya da ita 4 tonight, mama tace gaskiyarki fa zo muje, haushi harda hawayena, kausar ta kalloni tayimin gwalo, suka hada ido da khaleed ta watsa mai harara ta fita. Mom ta radawa khaleed a kunne son is your chance today to spent time wit your wife, dan idan ankoma biki zamu shiga so bazaka samu chance irin wannan kusa ba, ta fice ta barshi a sandare kamar photo, niko sai share hawaye nake. [9/14, 4:43 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 9⃣1⃣ khaleed ya dade anan tsaye sannan ya shigo dakin waige-waige ya fara, ya hango ledar snacks da drinks dinda kausar ta bari yazo ya diba, ya fara turawa kamar mayunwaci, nidai kallonsa kawai nike, a raina nace ita salmar ta kasa baka abinci ne ko kuma ba abinci a germany? Yanda yake tura bread yana kora lemo ni har abun dariya ya bani, na rufe bakina kar ya lura dariya nike masa, karaf muka hada ido yace abincin germany ba dadine, murmushi nayi ae kuwa naga ka kwaso yunwa na india da dadi kuwa, ya jikin yace min nace da sauqi, sai kuma shiru ne ya biyo baya, sai chan nace masa ya salmah din? Ya wani washe haqora dariyar da baita6amin ba, lafiyanta qalau wlh, i missed dat girl da inada chance da nayi ko 2weeks a germany, bamu wani samu time sosai ba, idan kika ganta yanzu ta samu hutu ta qara kyau, kamar na daukota na taho da ita, haushi ya kamani wai dama wannan ya iya surutu? Meyasa ma na tambiyeshj ita? Cewa nayi cikin fushi a raina, toh meh yahana ka sakota jaka kazo da ita? Ashe maganata ta fito fili, dariya naga yanayi na qura masa ido, kinga ni banyi tinanin haka ba fa, amma da na sakota bag din kuwa, da yanzu sai na cire abata na riqa kallo, ya sake dariya, taisayin kaina nafara ji wato shi ko zancen salmah akayi masa nishadi yake shiga, wayyo ni ameerah, take qwalla take qwalla ta cikamin ido, na juya kai na share kar ya lura. Sauri nayi nace masa yaya saeed fa? Waya ya zaro ya kirashi miqomin wayar yayi, ya daga nace hello yaya saeed, cikin farinciki yace princess, Allah mungodemaka inanan inata zullumi ashe ke kin warke? Fira mukasha dashi, yabani aunty fareedah itama, tace qawata akwai special tanadi da nayimiki fa, sai kundawo Allah ya baki lfy, nace ameen mukayi sallamah na bashi wayarshi. Shuru ne ya biyo baya a dakin, har nurse ta shigo ta bani dinner da magani nasha, fita yayi ya dade a waje saida dare ya tsala sannan ya shigo, icecream naga ya miqomin na kar6a na fara sha, shikuma ya koma gefe yana shan coffee, duk sanda zan dago kai na kalleshi sai naga yana smiling, nasan kuwa duk akan salmah ne, haushi ya isheni kamar na tsala ihu amma ba dama, a haka har bacci yayi gaba dani. [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 9⃣2⃣ da assubah alarm din khaleed ne ya tadamu, tashi mukayi sallah, azkar dina nayi na shafa addu'oi, sannan na dauko qur'an da kausar ta barmin na fara karantawa, cikin er qaramar muryata da qira'a ta mai dadin saurare. Khaleed shima ya kammala tashi sallar yayi kasake yana sauraren karatun ameerah, har wata nutsuwa ta saukar masa, saida gari yayi haske, na rufe qur' an na aje, toilet na shiga da kayan da kausar ta barmin, brush nayi nayo wanka na chanja kaya, wata 3quater riga ce da pencil trouser da mayafi, samfurin kayan india ne, kayan sunmin kyau ba laifi na fito, na kwanta a gado na, khaleed kuwa ya bini da ido aransa yace itadai komai nata a nutse takeyinsa, tsaki yayi kuma y do i even care. Karaf muka hada ido dashi murmushi na mai sanyi na masa, nace good morning, ya kawar da kansa gefe sannan yace morning ya jikin nace masa da sauqi, ear piece nasa na kunna qira'a ina saurare, kwanciya nayi na rufe ido alamun bacci, yadan jima yana kallona sannan shima ya shiga toilet ko da yafito, ya chanja kaya, baqar shirt yasa da wando ya fito fes dashi sai sheqi yake, nidai satar kallonsa kawai nike duk inda yayi ina binsa da ido kamar munafuka, wanda bai lura ba zaice bacci nake, snacks din jiya naga ya sake kwasa yaci yasha lemo, da ya gama ya miqe zaifita kuma sai ya juyo ya kalleni, doso wurina yayi niko na qara rufe ido, zuciyata sai harbawa take da sauri, duqowa yayi ya ciremin ear piece dinda ke kunnena, shi a tunanin sa nayi bacci, ya aje wayar a gefen gadona ya juya ya fita, sai lokacin na bude idona ina murmushi, my khaleed you ar not dat bad na qara murmushi, na rufe ido bacci ya daukeni. Cikin bacci naji ana ta6ani buda ido nayi, kausar ce gira ta dagamun, amarya how was your first night? Naga sai wani sheqi kike, bacci kike amma kowa ya kalleki, yasan kina tareda farinciki coz u r smiling while sleeping, duka na kaimata ke bakida kunya ko? Ina ruwanki da sirrin ma'aurata mukasa dariya, mom da mama suka shigo tareda khaleed, mom tace en matana meh kukewa dariya? Kausar tace mom abun sirri ne, tace kudai kuka sani idan tayi tsami zamuji, nurse ta shigo ta kawomin breakfast da magani, kausar ta kar6a har ta fara bani, sai kuma ta aje, brother kazo ka ciyar da matarka ni nagaji da bata, kaga hannunta na dama a sangale, yi yayi kamar baijita ba, mom tace bakaji meh qanwarka tace bane? Mama tace kibarshi may b kunyarmu yake, mom tace toh wa zai cigaba da kulamasa da ita dama? Ae gwanda ya saba, muje muga doctor yazo ya duba hannun if possibl ya bata sallamah suka fita, kausar ta miqe nima zanbiku ta wuce abunta. Tsaye yayi kamar ya wuche abunshi ya juyo dai ya kalloni muka hada ido, ya dawo ya zauna, spoon ya dauka ya debo abincin ya zunguromin batareda ya kalla ba, jiyayi anqi kar6a ko da ya lura a hanci yake qoqarin turamin abincin, da sauri ya sauke spoon m sorry plz yace, na fashe da dariya, shima da ya kalli painting da yamin a hanci ya fara dariya, muka riqa dariya kamar zautacci, mom suka shigo, son lallai duniya tayi dadi kace dama, wuri kakeso mubaku da matarka ku kyakyata, nidai duqar da kai nayi alamun kunya, shikuma har yanzu bai rufe baki ba, duk ya kalle fuskata sai tabashi dariya, kamar wani cartoon na koma, tissue yasa ya gogemin hancin, doctor ya shigo ya kwance hannun, ya tura a wani machine ya cire, ya daga sama ya sauke, yace do u feel any pain? Na girgiza masa kai, hannun yaja da qarfi saida nayi er qara, yace very good ur hand is ok now, saidai karkiyi aiki mai wahala dashi ko ki dauki abu mai nauyi sai nan da 1week, na gyada masa kai, allura ya ciro zaimun ya lura banyi breakfast ba, ya ajiye eat your food first, idan kungama akirani namiki alluran den u can go. Mom ta kallemu wato abincin kuka aje kuna shan soyayya ko? Duqar da kai mukayi tace oya kabata abincin da sauri karku batawa doctor time, spoon ya dauka ya fara bani ina kar6a, saida na qoshi na nunamasa ya isa, ya gogemun baki ya bani magani ya fita kiran doctor. [9/14, 4:47 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/2, 9:14 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 9⃣5⃣ Da assubah ma bayan munfarka nayi 'yan karance-karancena da nasaba nagama, kuma nidai nagaji da kwanciya tashi nayi, na kama hanyar fita ya bini da ido kawai, dakin kausar naje na riqa buga mata qofa, tataso tana tsaki ta bude, koda ta bude na ingejeta na shige ciki, mitsitstsike ido tayi, au amaryar broda ya haka tin da safe? Sai kuma tafara dariya, harara na watsa mata, toh ni meh nayimiki kuma? Nace tambayata ma kike? Dariya ta saka toh miye laifi dan mata ta tafi gun mijinta? Nace nidai karki qaramin haka, cewa tayi sister do u want to get close to broda or not? Nace inaso mana tace toh kina nisanta kanki dashi taya zaki samu kusanci dashi? Nace sis nifa Allah tsoronsa nike somtimes, tace gwandama ki daina, danni yanxu ma nafara, duk wata wata hanya da zata sa kusamu kusanchi sai na ingizaki kinbita, cewa tayi ki tashi ki koma ni bacci zankoma, gado taga na haye na kwanta murmushi tayi ta rufe dakin ta dawo itama ta kwanta. Da safe bayan kowa ya tashi munfito, muka gaida su mom, restsurant dinda ke hotel din muka sauka, mukayi breakfast, sannan muka fito yawon buda ido. Munje amusement parks kala-kala, da ordinary parks ma irinsu, cross maiden, horniman circle gardens, joseph baptista garden da sauransu. Muna chan mom ta tuna da zuwa asibiti tace muje da khaleed, bayan anyomin allura ne, horniman garden din yace amaidamu, zuwa yayi ya samu wuri yayi zamansa, nima haka sai kallon mutane da nike, khaleed harda beach saida yasa aka kaimu, shiga ruwa yayi yanata wasa nikam ina nesa akwaini da tsoron ruwa. Bamu muka koma ba sai yamma kausar sai tsiya take mana, wai dama neman hanyar guduwa mukeyi, shine daga zuwa asibiti mukaje shaqatawa, mom tace kada ki samusu ido, mutum da matarsa, idan angama biki ma ae dole suje honeymoon, a raina nace honey wahala dai, wannan idan na yarda mukaje honeymoon guduwa germany zaiyi ya barni, ina kwance bana motsi ya tafi bare ina qalau. Mama tace ae dama ambar zancen bikinnan tinda abun yazo haka, muna komawa ta wuce gidanta kawai, tinda angama gyara komai, mom tace wai hakan yayi ameerah? Gyada kai kawai nayi, khaleed yace ae ama daina zancen wani biki. Kausar tace broda meh kake yiwa sauri ne? Ko munyi bikin ae dole akai maka matarka, harara ya watsa mata ta basar, mom nifa Allah gwanda ayi bikin komai fa munshirya, kuma kinsan kowa cemasa muke biki sai sister inlaw ta warke, mom tace nima dai haka nagani, gobema shopping zamu dan har indian night sai anyi, kausar tafara ihun murna, mama tace itadai tagaji zata shige, mom ma ta miqe, kausar ma ta tashi, jawo hannunta nayi, nace miye naki na wani dagewa sai anyi biki? Jawoni gefe tayi sis we need dis, qawayen salmah nakeso na turawa hotinan biki, nasan dole su tura mata, idan taji haushi may b tace ma ta haqura dariya mukayi muka tafe, 
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,342 11-14-2018, 09:28 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,376 11-14-2018, 09:12 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,340 11-13-2018, 09:41 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,417 11-13-2018, 09:31 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 4,651 11-13-2018, 09:24 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)