The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*DREAM GIRL* by Deejah Abdul
#1
 1⃣ ??: Dream girl na deejah Abdul
Tsaye nake bakin titi amma hankalina gabadaya baya jikina, tinanina kachokan ya dunguma a tunanin dream man dina, inata tsara irin rayuwar da zamu tsara a gidan aurenmu, amma abinda zai baka haushi shine kwata-kwata wanda nake tinanin bai masan abunda nakeyi ba, hasalima ko sunansa bansani ba, qarar wata babbar motace da ta doso wurin ta dawo dani hayyacina, da gudu na tsalakka titin tareda haushin kaina da nikeji, watarana sai na halakka kaina akan tinanin abunda bazan ta6a samu ba. A haka na doshi gidanmu, na tura dan qyauren gidanmu na shiga gida, na kama hanyar wucewa dan akurkin dakina naje na dasa aya a inda na tsaya na tinanin abunda bazai fishsheni ba, tsawar da mama ta dakamin ita ta katsemin hanzari, wai ke meh yake damunki zaki shigomin gida ba ko sallama, sannan maimakon ki gayamin saqon da na aikeki, kin wani wuce soqoqo zaki wuce daki, ki kwanta kina tinane tinanen iskancin da kika saba, dan narasa meh yake damun qwaqwalwarki, juyawa nayi da niyar inkoma inyi sallamar da banyi ba, mama ta katseminb hanxari hanyar tambayata saqon da ta aikeni. Nace mama wlh hajiya abu tace wai ita batada kudin da zata ranta miki, ko wanda ta baki kwanan baya sai daqyar kika........ Mama ta dagamun hannu ya isa haka, badai biyan buqata karki isheni da surutun banza wuce ki ban wuri, na wuce dan dakina ina qunquni, toh ni miye laifina daga zanfadi abunda aka gayamin, mama cikin tsawa tacemin ni kike zagi? Na wace dai ban tanka mata ba. mama kenan mutum ce mai fada da saurin fushi, amma kuma akwai saurin sauka, ni har na saba da halinta shiyasa ma idan tana masifarta bana tankamata.

Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 2⃣ daki na fada na kwanta bisa lotsatstsiyar katifata da tasha jiki, da wani kodadden bed sheet dina, da wani pillow na kamar an latse bread, ina jimami, duk da mahaifiyata masifaffiyace amma ina tausayinta, tin bayan rasuwar mahaifinmu itace taketa dawainiya damu danida qannena guda 4, nice first born khadijah amma anfi kirana da ameerah, sai qanena mai bimun Aliyu, sai suhaila, fatima da kuma autanmu umar but muna kiransa da khair. Mahaifinmu shi kadai ne a wurin mahaifiyarsa, but yanada step brothers guda biyu, mahaifiyata ma haka ita kadaice a wurin mahaifiyarta, amma tanada alots of step brothers and sisters, kuma mahaifiyarta er dangi ce sunada yawa a famly dinsu, but duk da wannan en uwa na mahaifiyata ba mai taimakamana da qwandala, idan ba wata er yayar mahaifiyarta ba da ta tashi a wurinta, itama din ba wani qarfi ne da ita ba, dan haka mama ce ke fadi tashi na ganin munsamu rayuwa mai kyau tareda ingantaccen ilimi. Inada burin na tallafawa mahaifiyata tareda qannena amma ba dama, dan yanzu nake 200level a jami'ar usmanu danfodio da ke sokoto, inda nake karanta biology, wanda ada burina baya wuce inzama likita amma kuma nayita nema bansamu ba, mahaifina ne ya qaramin qarfin guiwa na kar6i abunda na samu arzikin mutum baya wuceshi, a haka na haqura nake karanta biology. Ina 100 level ne Allah yayiwa mahaifina rasuwa, wanda mutuwar sa taso ta zautani coz my father is my best friend, da taimakon addu'oi da mama tasa akemin aka samu nadawo hayyacina.

3⃣ qwallamin kiran da mama tayi ya dawo dani daga duniyar tunanin da na tafi, na tashi da sauri na fito dan inji kiran da mama kemin, nera hamsin ta miqomin kar6i wannan kije wurin isuhu ki samo kayan miya ki dora ko jolop rice ce kafin qannenki su dawo su isko ba abinci a gidan, na koma daki na zunbulo qaton hijabina na fita siyen kayan miya, Tafiya nake kaina a qasa, kamar ance dago kanki, idona karaf akan kyakkyawar fuskarsa mai cike da annuri, tsaye nayi na zama statue a wurin na saki baki da ido ina kallonsa bana ko qyaftawa, tamkar wata mayya ina ayyanawa a zuciyata wannan hadadden guy din idan yazama nawa zan shana, dan na huce takaicin da namiji a duniya, karaf najini ta ti6is a qasa, na qwalla qara, ashe wasu shanu ne sukazo wucewa nikuma na tafi dream land, banma lura ba, shine har wata ta tureni nasha qasa? tashi nayi na kakka6e jikina ina qwalla gashi na goge a qafa, Allah dai yasa ban karye ba?, mai kiwon shanun ne yayo kaina yana fadar enmata shannu, inji bakaji ciwo ba, naji kamar in falla masa mari, nace cikin tsawa eh malam wuce kabani wuri kabarni naji da daya, da qasar da nasha zanji ko da asarar ganin dream man dina da kamin zanji, shidai bai fahimce mai nike nufi ba ya miqomin ledar nono wai ga wannan, har da zanqi kar6a sai naga da inyi 2-0 gwanda na kar6i kindirmon, na qwata da qarfi nace angode nayi gaba abina [11/9, 12:30 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdu

4⃣ agurguje na wuce ina jefa qafata, naje na siyo kayan miya, da sauri - sauri na dawo gida dukda naji ciwo a qafata, koda nashigo gida su khairi sun dawo, mama ce takemin kallon tuhuma, meh ya tsaidake, nafara inda-inda, wlh mama shanuwa ce ta tureni a hanya shiyasa na makara ina qwalla? jibi qafata duk na goge, su suhaila ne suka kwashe da dariya, na tashi nayi kansu, mamace ta tsaidani karki illatamin yara, ai indai baki daina wannan yawan tunanin da kike ba to wlh watarana ma sai ansaceki a hanya baki saniba, bani kayan miyar nan, ta zabce leda tabarni anan tsuru-tsuru kamar anturke 6arawo, ina wani rau-rau da idona alamar zanyi kuka, mamace tace 6acemin dagani sakarya kina girma kina chin qasa. Da gudu na wuce dakina ina fadan nidai gidannan duk antsaneni ba mai sona, sudai su suhaila sunsamu abun dariya, niko duk na qule, na shige daki na rufo qofar, mama tace ku qyaleta idan yunwa ta isheta a fito dan kanta. Haka akayi kuwa ina daki ina sana'a dan nashiga duniyar tunanin dream man dina, nama manta da abunda ya faru, yunwa ce ta tasani gaba, nafito waje ina neman abinci na, haka nasamu kitchen wayam, nafara zare ido, naje nasamu mama ina wani 6ata fuska, mama banga abinci na ba, ta kalleni ta watsar kije tunanin da kike ya baki abinci. Haushi da takaici ne ya kamani, na koma akurkina na kwanta ga azabar yunwa inaji, chan na tuna da kindirmo na, haka na tashi jikina har rawa yake na dauko leda na kafa kai, nonon ko suger babu amma haka na shanyeshi tas, sannan najini nadawo normal, na godewa Allah sannan na godewa dan fillo da yau yunwa ta illatani. [11/9, 3:29 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

5⃣Suhaila ce ta bankado qofa ta shigo, mama tace ga abincin nan idan kinga dama kici, nayi kamar banjita ba, ta gaji da tsayuwa toh bari naje na gayamata kince bazakici ba ta kama hanyar fita, miqewa nayi cikin hanzari na kar6o kwanon, marar kunya bani nan kuma ki fice kibani wuri, tafita tana dariya ashe kowa yace duhu baiji zawo ba, duk da yanzu banajin yunwa nasan kindirmon da nasha ba wani riqeni zaiyi ba, inhar nabari ta tafi da abincin na kade dan mama bazata saurareni ba. Komawa nayi na kwanta ina aikin da nasaba, Aliyu ne ya banko qofar ya shigo, miye haka zaka fadowa mutane a daki ba ko sallamah, tsaki nayi najuya mishi baya, haba sweet sis daga nazo na ganki naga kindaina zama a waje duk sanda na shigo bana ganinki wai meh ke damunki ne sweet sis, bakomai nace masa banajin dadi ne. Hmm sis kenan ai kinsan in zaki 6oyewa kowa damuwarki alinki bai dace ki 6oye masa ba, miqewa nayi zaune na nisa sannan nace my sweet bro bakomai wlh wani guy ne yake chazamin qwaqwalwa, ya hanani sakat tunanin sa nake day and night, Aliyu ne ya sake baki yana kallona, sannan ya kwashe da dariya saida yakai qasa, sis kece kike gayamin wani guy yana chazamiki brain. Cow face nayi nace kaga idan dariya zakamin gwanda tun muna mu 2 ka kama gabanka [9/14, 12:55 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/9, 3:43 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

6⃣ Aliyu yace sorry sis abunne da mamaki keda kikewa maza kallon banza bakya kula kowa yau kece da fadan haka, Aliyu baku fahimceni bane, ina mace baikamata na riqa kula kowanne namiji ba, idan har banaji ina ra'ayinsa ba shiyasa kaga bana kula kowa dan banaso na 6ata time dina a banza, kuma ma samarin yanzu majority duk en iska ne aliyu. ....... Toh sis yanzu dai ba wannan ba ma who is dis lucky guy, ya sunansa kuma a ina yake, rau nayi da ido sai hawaye Allah nima bansani ba bro, kamarya dai bakisani ba sis, joke apart plz nace wallahi bansani ba aliyu, lura da yayi yaga hawaye a idona yasa yayi shiru na dan wani time, anya sis ba gamo kikayi ba kuwa, Aliyu ba wani gamo, mutum ne kamar kai, miqewa yayi lallai sis abun naki azimun ne, toh ki dage da addu'a Allah ya za6amiki abunda yafi zama alkhairi, nima kuma zan tayaki, nace daz my lil bro daz y i love you alot, yace i love u too sweet sis nidai nafita, nace adawo lfy ina murmushi. Aliyu kenan yaro mai tunanin manya qanena ne amma munshaqu sosai rigimar nan ta mabiyi da mabiyi duk bamayinta, indai kaji ina fada a gida toh da su suhaila ne. [11/9, 4:08 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

7⃣ ranar dai ahaka na wuni a daki na kwana sallah ce kawai ke tadani, gari na wayewa bayan na tashi na taya mama ayyukan gida, na gama na kwaso kayana nafara wankewa, mamace ta kwasomin kayan su suhaila ta zubomin gashinan ki wanke, dan naga yanzu tinda kina hutu ba aikin da kike sai zama a daki, na rasa meh kike qullawa a ciki, baki na turo alamun zanyi kuka, haba mama ni gaskia bazanyiwa marar kunyar yarannan wanki ba da girmansu, ni kayan khairi kawai zan wanke, saidai idan naki zaki kwaso, mama tasan halina indai banyi niyyar abu ba ko ta tilastani yinsa bazanyi mai kyau ba. Kamar tasan meh ke raina ta kwashe kayan su suhailan ta qaromin na khairi, nayi murmushin mugunta nace wlh da tsundumasu a ruwa kawai zanyi in tsame in shanya, mama dai juyawa tayi Allah ya shiryeki nace ameen ina dariya. Koda nagama wankin duk nagaji zuwa kawai nayi na kwanta sai bacci, ban farka ba sai 3.pm da sauri na miqe nayi alwala na bada azahar sannan na shige wanka koda na qare shiryawa ankira la'asar nayi sallah naci abinci Ji nayi kawai zaman gidan ya isheni, nafita waje nacewa mama zanje gidansu saudah, batayimun gaddama ba tace adawo lfy. [11/9, 6:03 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

8⃣ saudat qawa tace da muka taso tun muna yara muna qawance, saidai ita daga secondry school muka rabu dan ita bata cigaba ba, duk da tanada ra'ayin hakan amma gidansu daga ankammala secondry sai aure, saidai idan mijinki ya amince kicigaba a gidansa. Tafe nake ina saqar zuci ai gwanda nayi keeping kaina busy ko nasamu sarari a zuciyata, nashiga gidan tareda sallamah ta, mamar saudat ce ta kar6a a'ah yau su ameerah ne a gidan ai na dauka ko ba kya gari ne, murmushi na saki na sunkuyar da kai a qasa, a'ah mama wlh inanan, mutuniyar fa tacemin tana daki, hakan yasa na wuce da saurina na fada dakin, na tarar da ita tana linke kaya, kallona tayi ta watsar, na 6ata fuska haba qawas nasan banida kirki amma amin afuwa please. Tayi murmushi ai kedince wlh sai a slow bakidamu da wanda ya damu dake ba, sai faman zuwa nike gidanku amma ke shiru ba kya leqoni, haba mutuniyar bansanki da yawan fushi ba ki yafewa qawarki mana, kinsanfa banida watche tafiki, muka tafe muna dariya. Nafara tayata linke kayan ta kalleni, amma qawas meh ke damunki u are looking so pale, kuma duk kin rame, nace kedai bari qawas wlh soyayyah ce ke dawainiya dani. Jawoni tayi muka koma gefe tana dariya kai qawas ashe kinshiga system shine baki gayamin ba, who is dis lucky guy da yake wahalarmin da qawata, amma zanso ganinsa in jinjina masa, a ina kuka hadu dan wanne garine, ya sunanshi? Tagumi nayi na zuba mata ido tana jeromin tambayoyin da nikaina banda amsarsu, girgizani tayi wai ya hakane inata tambaya kin shareni, nayi ajiyar zuciya nace how i wish inada amsar tambayoyinki qawas [11/9, 6:26 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

9⃣ kallona sauda keyi irin kallon ban gane meh kike nufi ba, na nisa nace saudah wlh dakon so nake fama dashi, saudah tace kinqara sani a duhu, ban fahimceki ba, hawaye taga na fara ita ai duk jikinta sai yayi sanyi, qawans ya haka kinfara tadamin hankali, nace saudat wanda nikeso baimasan da zamana a duniya ba, hasalima ko sunansa bansani ba, bansan a ina yake ba, nidai nasan ina ganinsa a hanya idan zani school, ko idan mama ta aikeni, amma wlh saudah Allah ya jarrabeni da sonsa day nd my night aikin tinaninsa nake, sai nafashe da kuka. Saudah kan mamaki ne ya hanata magana, tadai jawoni tayi hugging tana rarrashi, qawata take heart Allah yana tareda ke tinda har son gaskia kike masa inshaAllah zai zama naki zan tayaki da addu'a. Bansan sanda na saki wata dariya ba da saida fararen haqorana suka bayyanah, nace amin qawata daz y nikeji dake. Cikin tsokana qawas kecewa ai inaga dai alhakin misbahu ne ke bibiyarki, bawan Allah har tausayi yake bani yanda yake sonki amma ke ko oho, take fara'ar fuskata ta gushe, nace qawas ya isheki kindai san halina idan banason mutum bana iya kulashi, tin ranarda ya aikoki wurina nagayamiki kice masa yayi haquri, amma shine da nacin tsiya yaqi haqura. Toh aikema gashina kina nachin abinda baimasan kinayi ba, zumbur na miqe ni kinga tafiyata tunda abun naki ya zama wulaqanci, dariya take ta biyoni haba qawas tsokanace fa kawai kiyi haquri, kizo akwai labari ko waiwayenta banyi ba na wuce gaba abina, nace mama natafi sai anjima, a'ah amirah har anfito to kigaida mamanki, kice mata sai na shigo. [11/9, 7:29 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

? fitowa nayi inajin haushin saudat da nasan wulaqancin da zatamun kenan wlh Allah da banzo ba, samun kaina nayi da biyar hanya ba tareda nasan inda zani ba, inata mita a zuciyata, daga kaina da zanyi sai naga wani wuri, . Mai tarin itace masu ban sha'awa, ga inuwa mai sanyi a wurin ko'ina yayi luf-luf, kaina nasamu da sha'awan zama a wurin, shiga nayi nazauna ina waige_waige, wurin nidai ya birgeni, tashi nayi ina dan zaga wurin, mutum na hango zaune sanye da fararen kaya, yana zaune ya dora qafa kan qafa, amma banga fuskarsa ba, sai nasamu kaina da son ganin waye wannan mutum, tashi nayi na tinkare wurinsa batare da nasan meh zanyi idan naje wurin ba, ina gaf da isa wurin ne wani dan matashin saurayi ya isa wurin wannan mutumen, khalid dama nasan indai na nemeka narasa bazai wuce nasameka nan wurin ba, hannu yabashi suka gaisa, khalid namaimaita a zuciyata take naji zuciyata ta buga, yunquri nayi na qarasawa inda suke domin inga waye aka kira da wannan sunan, cikin rashin sa'a kafin na isa sun daga sun tafi, haushi ne ya isheni batareda nasan dalilin hakan ba, zaunawa nayi na bisu da ido, mota naga sun bude zasu shiga, wannan saurayin ne naga ya waiwayo, wata kyakkyawar budurwa ce da tayi wata shiga ta daukar hankali naga ta doshi wurinsu tana wani murmushu na yaudara, dayan saurayin ne da na tarar a wurin naga ya juyo, zambur na miqe tsaye ganin dream man dina, magana naga yanayima budurwar watche banji meh yake fada ba, naga ya juya a fusace ya shige motar, dayan saurayin ne naga ya shiga da sauri shima, sunja motar da gudu sun wuce, sunbar budurwar nan a tsaye.. [9/14, 12:55 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/9, 7:56 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul

 1⃣1⃣ inanan tsaye a wurin kamar wacche aka dasa ina aikin murmushi kamar wata sha-sha-sha, budurwar ce ta tunkaro wurin da nike, tsawa ta dakamun wache ita tadawo dani hayyacina, malama ki jaye kin wani tarewa mutane hanya, da wani uban hijabinki kamar wata matar liman, jayewa nayi nabata hanya taja wani dogon tsaki taje ta zauna tana huci, ni abun dariya ma yabani, nace bani nakar zomonba nima..... Malama ya isheki kinji ko na wulaqantaki ana wurin, sumui-sumui naja jikina zanbar wurin, wani hankerchief na hanga daidai inda khalid ya tashi, da sauri naje wurin na dauka na qara gaba abuna, zuciyata wasai kamar wadda akayiwa bushara da aljannah, sai wane yage haqora nike, khalid kawai nike maimaitawa ina smiling, khalid khadijah, khadijat khalid, what a perfect match abunda nike ta nanatawa kenan. Sai gab da magrib na isa gida ina shiga gida ana tada sallah, makewayi kawai nashiga nafito na dora alwala na wuce daki na tada sallah, nagama nayi azkar dina tareda addu'oi tareda godewa ubangiji da ya sanar dani sunan dream man dina, tareda fatar Allah ya mallakamin shi, mama naje nagaida a dakinta itadai ta lura da chanjin yanayina dan sai wane washe haqora nike ina jan su fatima da fira, ranar dai nayi fira a dakin mama har saida na lura duk bacci sukeji sannan natashi nawuce dakina, hanky din rabin raina najawo na shaqin daddadan qamshinsa na lumshe ido, na rungumeshi a qirjina da haka bacci 6arawo yayi gaba dani. [11/10, 10:42 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

1⃣2⃣ tun daga ranar namaida gun wurin zuwana, amma kamar khalid yasani nadaina ganinsa sam a wurin, yauma kamar kowacce rana nafitoh da yammah zuwa inda namaidah wajibi, tafe nake ina faman sauri kamar wacche tamakara tana gudun bulala, fatana kawai nasamu ko glance ne na abun qaunata, kici6is naji na yi kaura da mutum, dagowa nayi da niyyar bada haquri, wa zangani wannan masifaffiyar yarinyar nan ce ta ranar, kafin na iya bude baki sai ji kawai nayi ta daukeni da mari, shashasha sakarya jaka kawai, kina tafiya amma kamar wata dabba, bloody illeterate i dunno y i just hate u tayi tsaki ta wuce ta barni riqe da kunce, wurin da nayi achan naga itama ta nufa, binta nayi cikin hanzari dan idona ya riga ya rufe, da mari zanji ko da zagin da tamin, bana ko ganin gabana ina isa wurin ta na finciko kanta, sai ga acuci mazanta a qasa? na kwasheta da mari har guda biyu, kukan kura tayi tayo cikina, wlh yau sai na kassaraki ko waye ubanki a garinnan tinda kika mareni yau sai kin raina kanki, wanine ya taso ya shiga tsakani yana miye haka husnah kuna abu kamar illeterates, murya naji daga bayanmu wai saeed miye haka kabarsu su kashe kansu mana, yaja dogon tsaki, ya juya gurin husnah kewai wace irin mayyace, nasha gayamiki kar ki kuskura ki qara bibiyata, amma da yake ke jakace daqiqiya kinkasa fahimta, Zuwa tayi gabansa tana rausaya, tana wani marmadi da ido, haba sweathrt kayi haquri mana wlh i can't live without you, tureta yayi den go d hell and die, ni dama na huta wlh, jarababbiya kawai nd get d hell out of here nida na aureki gwanda na mutu ba aure sakarya kawai, kuka tafara tana fadin toh wlh baka isa ba indai kudi da mulki na magani dole ka aureni, miqewa yayi kamar wani zaki yayi kanta, ko ni da ke gefe ina kallo saida na tsorata, saeed ne ya shiga tsakani da sauri tareda fadar husna just leave here pls, tashi tayi da gudu-gudunta ta kama hanyar barin wurin, waiwayowa tayi ta kalloni ke kuma wlh sai na lalata rayuwarki, tafita wurin da sauri. [11/10, 11:12 AM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

1⃣3⃣ sai a lokacin ma suka lurada i'm still a wurin, saeed ne ya kalloni ke kuma miye ya hadaki da wachchen mahaukaciyar, a cikin muryata mai sanyi nike masa bayani wlh kawai colliding mukayi a hanya, na tureta without my knowledge, kafin na bata haquri shine ta wankeni da mari tana zagina, shine nikuma nakasa haquri, ko mamana da tahaifeni bata ta6a marina ba zanbar wata qatuwar banza ta shani a banza. Saeed ne yayi murmushi i like dat, inason inga wanda yasan enchin kansa, mutunen nawa na kalla sai naga baya ko kallon inda muke ya murtuqe fuska, smile nayi a raina nace wannan akwai mishkili, but i still love u nayi murmushi, saeed ne yake cemun ya naga kinata faman smile en mata, murmushin naqara yin nace bakomai, kawai whether wurinnan ne so romantic, saeed ne yace wow romantic huh just kina wishing your man is by your side ko, dariya nayi da ta bayanna fararen haqorana amma dai kai akwaika da zolaya, ni bamanida saurayi, hannu naga yasa a kunnensa yana dariya i'll just pretend i din't hear dat, dariyar nayi nima ina fadar just blif me ai ni bana qarya, jinjina kai yayi yace toh shikenan naji amma bawai yarda nayi ba, en mata baki gayamin sunanki ba fa, gashi har munzama friends, sunana khadijah amma anfi kirana da ameerah, wow toh nima dai ameerar zance dan kinada sunan mummyn mu, murmushi nayi yace lets seat mana. Mutumen ne ya miqe tsaye toh uban surutu idan kagama kasameni gida ni kaga tafiyata, juyawa yayi ya tafiyarsa baiko sake waiwayenmu ba. [11/10, 12:10 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

1⃣4⃣ saeed na kallah nace meh yake damun abokinka ne he look worried, murmushi yayi don't mind my friend he is so tense, kinga qawarki, nace qawata kuma wacheche qawata, yayi dariya abokiyar fadanki mana, nache oh kajika da wani zance, what about her? Yace er deputy governor ce fa na nan garin, zare ido nayi nace ashe na debo ruwan dafa kaina, dariya yayi harda qyalqyacewa, ashe dai mummynmu matsoraciya ce, nace haba ae dole ni ba er uban kowa ba inani ina masu government, dariya yasake yi, toh itace akeso a aurawa khalid take naji gabana ya fadi, amma shikuma baya qaunarta wacce yakeso tana germany wurin karatu, sai next year zata gama sannan suyi aure, sukuma mahaifansa sunqi su amince da haka, saidai ya kawo wacce yakeso sunbashi one week time, shikuma idan ba salmah ba he promised bazai zauna da kowacce mace ba, take hawaye suka cikamun ido na juya gefe na share kar saeed ya lura, yace so kinji matsalar abokina gashi sati dayan da aka bashi gobe ne zata cika daz y kika ganshi ba annuri, na jinjina kaina lallai yana cikin matsala, toh yanzu ya zaiyi, how i wish nasan amsar tambayarki nima da na samowa abokina solution, anyway ni zantafi en mata sai wani ganin ya juya ya tafi abunshi ya barni nan zaune bana ko motsi kamar wata statue. [9/14, 12:55 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/10, 2:39 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

1⃣5⃣ zaune nake nayi jungum hawaye sai korar juna suke, har hijabina ya fara jiqewa idona har sunyi red kamar wadda uwarta ta rasu, duhu ne naga yafara sauka wurin sannan na tashi na kama hanyar gida, tafiya nake kamar wachche qwai ya fashewa a ciki, gabadaya hankalina baya jikina, ina isa qofar gida naji ana kiran sunana, ko waiwayawa banyi ba bare mai kiran sunan yasa ran zan saurareshi, haba ameerah magana fa naketsa miki tindazu nazo nan ina jiranki akacemin ba kyanan, a fusace na juyo malam na aikamaka da invitation nace kazo ne? Ko anaso dole ne wlh mustafa kafita hanyata dan nagane take_takenka dan ka kuskura ka gayawa mama cewa wai sona kake wlh sai kayi danasani a rayuwarka, baki ya saki yana kallona dan ko a mafarki baita6a tsammani na iya tsiwa haka ba, tsaki naja na shigewata a gida, Aliyu ne yazo wurinshi ashe dama yana tsaye yana kallonmu, yace danuwa kayi haquri my sis ba haka take ba inaga dai da abunda yake damunta, jst go i'll talk to her later, sannan ya tafi. Mustafa cousin dinane dan wan mahaifiyata, yaro ne mai natsuwa kuma shima din ya hadu dai_dai misali, lura nayi da en kwanakinnan yana yawan zuwa gidanmu, kuma duk yazo sai yace a kirani mu gaisa, harda en gifts yake kawomin da mama, shiyasa nagane inda ya dosa, nasan kuwa idan har ya gayawa mama zancen yana sona na kade dan nasan tsaf yadda zatayi dan yaron yanada kirki, shiyasa nikeson intaka masa birki, dan nariga nayi nisa a son maso wani banajin kira. Fusace na fada gida nayi sa'a ba kowa a tsakar gida dakina na wuce direct na kullo qofa na fada kan katifata, da yake ina hutun sallah shiyasa banma bi ta tinanin sallah ba. [11/10, 2:55 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

1⃣6⃣ Aliyu ne ya banko qofar dagani ransa a 6ace yake, haba sis haba sis ae wannan bai kamaceki ba, yanzu miye laifin mustafa da zaki wulaqantashi, ko bakomai ai dan uwanki ne, hannu na daga masa ya isa aliyu kaga kaina kemun ciwo dan Allah kafita kabarni na huta, amma dai koma miye yaha musty bai chanchanchi hakan ba, mamace ta shigo tana kallon aliyu wanne mustafan tayiwa wulaqanci, cikin sauri nace mama wani yaro ne a chan layin ya dameni bayan ni nagayamasa bana sonsa, mama tace to wai ke ubanwa ma kikeso ni nagaji da halinnan naki duk wanda yazo gidannan da sunan yana sonki zakice ba kya sonsa, ko a haka zanta zama dake a gidannan muna gwada tsayi? Aliyu ne yace yo mama dama wa zataso bayan ta dorawa kanta........ Alamar magiya nayiwa aliyu alamun kar ya fada dan Allah, sai ya fakaice yace bayan ta dorawa kanta wani ustazanci kamar wata waliyiya, mama tace yo waya gayamata su ustazan basu son maza, dariyace taso ta su6ucemin, nace mama nidai kiyi haquri zan gyara, tace karma ki gyara yarinya kisha mamaki dan duk wanda naga dama zanbashi ke inhuta, shigowar saudah ne yasa mama da aliyu suka fita suka bar dakin. [11/10, 5:44 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 

1⃣7⃣ juyawa saudah baya nayi nace meh kin qara zuwa da wani sabon wulaqancin ne, dariya tayi wai ke har yanzu fushi kike? Haba qawata ki haqura mana Allah tsokanarki kawai nakeyi, ns basar toh miye labarin da kikace zaki bani, bayan kin shareni kuma wane labarin zanbaki, toh shikenan riqe abunki nayi kwanciyata na qyalete. Duka saudah ta kaimin wlh ni badan nasaba da halinki ba, da tuni mun raba hanya shegen mishkilancin tsiya kamar wata er sarkin misira, dariya nasa na kaimata duka aini namafi er sarkin misra, gimbiya ameerah kenan na dagamata gira, muka tafe muka qyalqyale da dariya, amma wannan da ake dakon son sai yayi haquri dake, nace ba wannan ne sunanshi ba sunanshi KHALEED, kwantawa saudah tayi itama, ke qawas ashe love story yaci gaba ambarni abaya, toh ya akayi kika samo sunan keda kikace bakisan sunan ba, na kwashe duk yanda akayi bayan barina gidansu har zuwa yau da nasamo wannan bad news din na gayamata. Saudah ta sauke ajiyar zuciya tace ina ke ina jayayya da er governor da er germany ai ni a ganina gwanda ki haqura kawai wannan battle yafi qarfinki, zumbur nayi natashi zaune in haqura fa kikace saudah ai kuwa wlh kiji sai inda qarfina ya qare, ni kisani wannan er deputy governor batama dameni ba dan nasan bata gabanshi, wannan salmar ce dai ta tsayamin a heart dan ita yakeso nafara hawaye, saudah tace qawas gwanda kawai ki manta da wannan khaleed din dan yafi qarfinki, hannu na dagamata qawas ya isa haka indai bazaki fadi alkhairi ba gwanda kiyi shiru kawai, in yafi qarfina baifi qarfin Allah ba, danni dakice na haqura da khaleed gwanda ki fallamin mari. Baki qawas ta riqe miyayi Allah ya ba mai rabo sa'a nace ameen. Kinga kafin ki fara fushin bari na gayamiki abunda ya kawoni, gobe za'a kawo lefena, washe baki nayi dama kinada wannan good news din kiqaki gayamin da wuri saida kika 6atamin rai? Saudah tayi dariya tace ai yanzu na gyara ran ko, dariya nayi nima nace shine baki gayamin da wuri ba ina matsayin babbar qawa, tayi dariya ina naganki bare nagayamiki kina fushi dani, gashi duk sanda nazo kinfita ashe ke gun zuwa kika samu, saudah ta miqe ni zantafi kishigo da wuri gobe akwai aiki nace toh na rakata waje, sannan nadawo na kwanta ina saqa abunda zanyi dan inga na taimaki rabin raina kuma yanda za'ayi na sameshi. [9/14, 12:55 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/12, 3:22 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 1⃣8⃣ ranar dai rabin dare haka ya qaremin ina saqa da warwarar abunda zanyi, sai kusan asubah nasamu bacci ya daukeni, asubar ma makara nayi saida mama taga ban tashi ba tazo ta tadani, ina gama sallah kuwa da qyar nayi azkar dina nakoma bacci ba, bani na farka ba sai qarfe goma, da yake weekend ne su suhaila na gida inaga shiyasa mama bata tadoni ba, nayi aiki, a gurguje na fito na dibi dumame naci na fada wanka, nafito na shirya, na saka hijabina nayo waje, mama ce tace sai ina kuma, dan na lura kwanan nan qafar kare kikaci, shiyasa kullum sai kinfita wai ina ma kike zuwa, karfa kiga na sake miki kizo kiwuce gona da iri, haba mamata ai kema kinsan er da kika haifa bazatayi shashanci ba, gidansu saudah fa nike zuwa da yake bikinta ya kusa, kuma yau za'a kawo lefe shiyasa ma zanje da wuri yau, mama ta saki fuska to ai ba laifi adawo lfy, kigaida hajiya asabe sai nazo taya murna nacd toh na zura takalmina zanfita. Khairi ne yace shishta(sister) kizo mana da alala da sho6o (zo6o) dariya muka sa nace qanen shishta don't worry zakaci alala da sho6o na fice. Gidansu saudah na nufa, nashiga sunata faman aiki na cire hijabina nima na shiga akayi dani, bayan mungama ne nace bare inje gida inyi wanka, kan masu kawo lefen suzo, mamarsu saudah ce ta debomin alale da zo6o, abinci da ma wasu kayan soye-soye da akayi na tarar baqi, nayi godiya na fice gida, da shigata khairi ne ya taso da gudu ya tareni ya kar6i wasu kayan da nazo dasu, dariya nayi nace khairi baban kwadayi ga alale da sho6o nan ayita fama, mama tace har ankawo lefen, nace a'ah nadaizo in watsa ruwane kan suzo, na debi ruwa na fada makewayi. [11/12, 3:23 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 1⃣9⃣ nafito wanka na bude akwatina na za6o sababbin kayana, na sheqa kwalliya, wata atamfa nasa mai kallar ja da black, dinki atamfar ya kar6eni gashi dama red nd black color sunamin kyau, red hijab dina na dauko nasaka saidai yau ban dauko mai kaimin har qasa ba yadai rufemun hands kawai, black shoes nasaka na riqe red nd black purse dina, ina fitowa suhaila tace su sis yau ansha kyau kamar wadda zataje beuty contest, murmushi kawai nayi nacewa mama natafi, koda na isa gidan har sunzo, lefe yayi kyau ba laifi daidai gwargwado, cikin raina sai fata nike Allah ya nunamin nima khaleed ya kawomin nawa. Daki na wuce wurin saudah da yake ita bata fito ba, tambayana take qawas ya kikaga kayan, dariya nayi nace gulmammiya ai da sai kifita kigani tinda kinkasa haquri, nace sadiq din naki gaskia bai iya za6en kaya ba ba abunda yayi kyau, qirji saudah ta dafe nashiga 3, na kece da dariya kewai har kin yarda wlh komai perfect kamar ke, duka ta kaimin na goce ni har kin tsoratani tace, fira muke da saudah amma ni duk rabin hankalina yana gun dream man dina na matsu time yayi na wuce inda ya zamemin ibada kullum, da qyar naga anyi la'asar sallah kawai na sallamah na miqe tsaye, saudah na fadin ina zuwa qawas, ban waiwayota ba nace sai na dawo qawas, murmushi tayi a ranta tace Allah ya raba rai da wahala. [11/12, 3:25 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 2⃣0⃣ tafe nake ina sauri dan naga na dan makara, kar nayi missing ganin abun qaunata, shigata wurin keda wuya nafara waige-waige ta bayana naji kamar ana magana, najuya na nufi gun sa'id ne na hango yanata zuba dukda bansan meh yake fada ba, raina yamin fes dan duk na hango sa'id nasan my dream man is there too, ina isa wurin sa'id naji yana fada, dis man u ar too stubborn ita salmar taka takasa komai akai idan har tadamu dakai she suppoz to agree ko auren ne a daura den she can continue wit her studies but no, now u are left wit no other option rather dan ka aure husnah, miqewa naga yayi what are u saying man, kasan yanda na tsani yarinyar nan nida na aureta gwanda na rasa raina beside ma, i promissed salma she'll be the only one 4me, saeed yace now m sure u gone mad, sai kagayamin meh zakayi now and today is your dead line, cikin tsawa khaleed yace i don't know man, may be zanyita roqonsu ne may be zasu haqura, saeed yace karma kasa ran faruwan haka kasan halin parent naka idan sukayi niyyar abu only God can stop it. Khaleed neh yace cikin muryar tausayi now what i'm gonna do, kasan idan aka auramin dat girl angama da rayuwata, nd dat means she won over me kenan? Sallamah nayi musu wanda yasa suka juyo wurina, saeed ne ya kar6a cikin sakin fuska, ameerah gimbiyar mata kema kinfito kenan, eh nace masa cikin sakin fuska, khaleed ne ya juya zaibar wurin, nayi sauri nace masa excuse me plz ya tsaya yanamin kallon meh zanmiki, nace can i suggest something please? Khaleed yace i don't get u, nace i over heard ur conversation and akwai abunda nakeson na fada may be dat will help you............ Daga mun hannu yayi cikin fushi daz enough who do you think yo are? Waya baki damar da zaki shigo rayuwata har kiyi tunanin zaki taimakeni? I don't need any help from anybody nd definately not from someone like you, yayi tafiyarsa, jiri naji yafara daukata take nakai zaune hawaye ne naji sunfara zubomin, saeed ne yace common big girl don't cry mana don't mind my friend yana cikin tension ne, sai sannan ma na tuna da mutum a wurin tears dina nagoge nayi murmushi wanda dagani kasan na dole ne, nace bakomai he is right i should have mind my own business. [9/14, 12:55 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/25, 2:20 PM] Deejah Abdul??: Dream girl na deejah Abdul 2⃣1⃣ saeed ne ya zauna kusa dani, now tell me wane suggestion ne zaki bawa abokina, miqewa nayi never mind kawai wanda zanbawa dinma he is not interested so what is the point of telling you, tasowa yayi shima, don't say dat if ur suggestion wil help my friend wit his problem ki fada kawai i'll be the one to convince him, kabarshi kawai sa'eed is ok, is not ok really i beg u in d name of God ki fadamun ko sai na duqa a qasa, dariya nayi no its ok komawa nayi na zauna shima ya biyoni, i'.m all ears rasa ta inda zansoma nayi. Nace do you know sa'eed yace no i don't, murmushi nayi nace nima halin da nikeciki daya ne da abokinka? yace kamar ya mumcy? Na nisa nace akwai cousin brothers dina da suke sona guda biyu , so nikuma da wanda nikeso anturashi course a england sai nan da 1 year zai dawo, so wa en nan cousins din nawa sune suka fara rigima akan ko wanne shi za'a baiwa ni, so shine mamana tace na fito da wanda nikeso kawai a raba gardama, amma da naje na sameshi shine yake gayamin inba mama haquri da zaran ya dawo daga england zai turo magabatansa ayi zancen aure, shine da nayiwa mama bayani tace batasan zancen ba dole ne na fiddo wani dan ita tagaji da maganganun da ake gaya mata a dangi, kamar ita ta hanani aure, ko dai nakawo wani ko na za6i daya daga cikinsu, ni kuma na tsane auren dangi beside ma ni da wanda nakeso banji zan iya haqura dashi ba, gashi mama tabani 1week na zo mata da zabina, ko ita tayimin na kammala zancena ina qwalla? nima dai deejah da nike gefe ina kallonsu mamaki ne ya turnuqeni naji yanda ameerah ta taqar qare tana zuba qarya??? kuma ga alama saeed qaryar ta shigeshi dan naga jikinshi 
Reply


Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 7,717 11-14-2018, 09:37 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,342 11-14-2018, 09:28 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,376 11-14-2018, 09:12 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,340 11-13-2018, 09:41 AM
Last Post: Gimbiya
  *DREAM GIRL* by Deejah Abdul Gimbiya 0 2,417 11-13-2018, 09:31 AM
Last Post: Gimbiya



Users browsing this thread: 1 Guest(s)