The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 1070 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval

Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval

Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
MATA UKU GOBARA
#1
MATA UKU GOBARA

1
Na Mermue & Hauwa M. Jabo
“please Dan bani wanchan ribbon din” ta nuna ma mai shagon da yatsa, ya miqo mata, ta kalla ta Dan jujjuyashi, xai mata kyau sosai, zaiyi acucu yanda ya kamata..!
 ta matsa daga cikin shagon  ta kwaso kayan make up sosai, duk wani kalar kayan kwalliya saida ta xaba, daga kan foundation,primer,concealer, contour, highlighter, setting powder,blush, bronze, eye liner, maskara, lipstick, eyebrown pencil…..kai gasu nan dai kaya ta kwasa bana wasa ba.
Ta qare ta biya kudin, ta koma gefen shagon ta zauna ta fito da kayan data siya da nata ta qara rangada kwalliya, fuskar nan ta qara jin foundation yanda ya kamata.! ta gama fente fenten ta, ta fesa turaruka kala har uku, duk a gefen shagon take bidirinta,
Ta gama  ta fito tana rausaya…
Ba laaifi tanada kyau, Amma kuma kamar kwalliya ta qara mata wannan kyau din, doguwace sosai, normal macece wacce xa’a iya lissafata a chikin jerin mata masu kyau, bawai kyau na fitar hankaliba. Normal shez beauty.!!.
Wayartace tayi qara ta dauko ta kara a kunnenta, tana tafe tana surutu a waya, daga idonda xatayi tayi karaf da wani guy, namijine har namiji, duk mace mai lafiya xatayi fatar samun miji irinsa.. saida ta rude da ganinsa, ta ma rasa abinda xatace a wayar, sai Eh Aah, takeyi, shi kuma Mahmoud ya hangota, ta burgeshi, a rayuwarshi yanason yaga Mace yar gayu mai kwalliya, lokaci daya mace mai kwalliya xata wuce da imaminsa,
Ya matso kusa da ita, tamai wani rau rau da idonta, sai kuma tayi qasa da idon ta qara  budewa, eye-shadow dinta ya fito Sosai, ta basar kamar batasan tayiba. tsayawa yayi gefenta yana jiran ta qare waya, tana qarewa tayi kamar bata ganshi ba, yayi sauri yazo gaban ta ya mata sallama, kwarjinin da ya mata ya hanata kasa masa magana.!
Ta amsa adan sake,
Ya mata murmushi,
I am Mahmoud Abbas, yadan gabatar da kanshi, gurin ta Hajiyar tamu dagyar ta iya fada masa sunan ta, Dukda itama ya mata,
Ya maimaita sunanta  HUMAIDA.  Ya samu number ta shima dagyar, sukayi sallama…..
Har ga Allah Mahmoud ya mata saidai ta tsaya Dan Jan ajine Dan kada ya rainata.
HUMAIDA kenan yarinya ce Yar kimanin shekara 20, yar gayuce harna  fitar hankali, ba abinda bata saniba na gayu, tanada samarinta kala kala amma dai ba na aure duk cikinsu….
[11:19AM] MATA UKU GOBARA
2
Na Mermue & Hauwa M. Jabo
Mahmoud bai tsaya bata lokaciba ya fara zuwa gidan su Humaida tadi, tana burgeshi yanda take qamshi kullum, kuma kullum qamshi daban daban yakeji a gurinta, ga baiwar kwalliya, tsab tsab da ita kamar Hauwa Jabo.!!
Sun fahimci juna chikin qanqanin lokaci, suna xuba luv har na fitar hankali, Humaida na matuqar son Mahmoud dinta, ta shagwabashi, Dukda cewa Mahmoud Bai wani iya love ba, itama Humaida Dan Bai iya luv bane yake ganin kamar tana shagwabashi, “amma Mrs Jabo tace wannan ba luv sukeba” nan danan iyaye suka shigo aka fara xancen aure….
Mahmoud ya kai Humaida gidansu, iyayensa sun gani Kowa ya yaba da ita, sunata santinta, wata cousin sister din Mahmoud, tace ” wallahi yaya kayi dace, kasan kusan sati daya amma still kujerar data xauna qamshinta takeyi. Gaskiya Humaida tayi” yanata jin dadi ana yaba choice dinsa….
Humaida tayi sa’ar miji haka Mahmoud ma haka yake tunani yayi sa’ar mata yar gayu…….
*******         ******* *******
Mahmud da humaida sun kasance yan garin birnin sokoto ne, hakama mahaifansu, iyayensu dattawan kwarai ne masu mutunci, sun fahimce haka ne bayan kai kuddin auren yayansu.
Ranar friday 20/5 itace ranar da aka daura auren Humaida da Mahmoud, Humaida tayi bidi’ kala kala a auren ta,…
Gidan Mahmoud babban gidane,dake unguwar mabera, gidan mahaifinsa ne da ya sami gado, gidan yanada part hudu, kuma haddaden gidane naji da fada, ya gyara part daya ya saka amaryarsa humaida…
An kai amarya gidan mijinta,
Bayan Dan ciye ciye da sukayi, yasa tayi alwula suka gabatar da sallah ta godiya Ga Allah, Mahmoud ya mata addu’ar da duk ango na gari yakan yiwa Matarshi, sabanin wasu angwayen da zumudi yake hanasu aikata addu’ar samun dace da zuri’a ta gari a Daren farkonsu…
Mahmoud baisha wahalar Humaida ba, a ranar ya mayar da  ita cikakkiyar Mace, normal taji jiki kamar yanda duk mace wacce batasan namiji ba xataji jiki…
Yadan taimaka mata ta gyara jikinta, da safee ya hada masu breakfast suka karya amarya kuwa sai sinne kai akeyi qasa, an shigo social change, amarya ta ango…
*********
BAYAN SATI DAYA…
Mahmoud ne ya shigo gidan, riqe da kaya niqi niqi a hannu, yayi tafiya ta kwana biyu, wurin kasuwancisa, domin kuwa Mahmoud Dan kasuwa ne babba Wanda ake ji dashi a garin sokoto yau ya dawo, Ya shigo gidan yana saka qafarsa ya taka qashi, anchi nama an wurgar da qashi a wurin tsaki yaja, ya daga kai ya kalli palon jefa qafar da zaiyi sai chikin  plate din abinci, anchi an rage an ijiye a gurin, kuma da gani bana yau bane, haushi ya kamashi yasa qafa ya shure plate din abincin.
“Humaida Humaida.!! ”
Na’am, ta fito  daki da sauri tana gyara zaninta da ya kwance, daurin qirjine a jikinta ba Riga bare braaa,
Ta fito kamar wata mai yaya Tara..
Ya kalleta,
” mi kikeyi a daki kika bar Palo kacha khaca haka.? ”
Ta ya tsina fuska,
“wallahi bacci yayi awon gaba dani, naso tun da na gyara tunda ka mini waya kace xaka dawo bacci nake har yanxu” ta qaraso tana qoqarin karbar kayan hannun sa, ta na karba tayi xaune dirshan tsakiyar Palo ta fara bude ledodin, ko sannu da zuwa Bai samuba, fruit ce a ciki da sauransu, dayar kuma tufafi ne da sauran tarkacen mata, ta washe baki, tace ” honey kana birgine wllhy, shiyasa nake sonka kullum ” ta hura mai kiss, ta dauko Apple din ta gutsura sau biyu ta ijiye ta dauko banana daya ta bare tanaci, ta cika bakinta da ayaba tace, ” wato honey a Duniya inason ayaba, wani laushi yakeda a baki, ita ba ruwanta da shaqe mutum” baice mata komai ba sai kallon ta yake, taci wannan taci wannan, bata ma yi tunanin ta wanke fruit din ba, bare ta kawo masa suci tare……
[11:27AM] MATA UKU GOBARA
3
Na Mermue &  Hauwa M. Jabo
Ta miqe tsaye ta wurgarda fatan ayaba anan gurin da sauran abubuwan datachi,”Honey bari na kwada kayan Muga yanda zasu mini”  ta tashi da sauri ta dauki ledar kayan ta wuce daki ta kwada kayan ko bra bata sakaba abubuwan nan sun yo qasa kamar tiyo, dama bra ce take Dan dagasu, honey ” wannan kayan basu min kyauba wallhy ni gaskiya bana sonsu, please idan xaka siyo min kaya ka riqa daukata ina xabowa da kaina, nasan wayanchan ma baxasu min kyauba dama wayannan ne masu dama dama a cikinsu” Mahmoud kam gaskiya ta mishi yawa, ya kalleta ita ko ruwa batasan ta kawo ma mutumin da yayi tafiyaba, “ina abinci na!? ” ya fada yana wata busashiyar hamma, wacce da gani kasan yunwa da gajiya suna tare dashi,
Tazo kusa dashi tayi miqa, wani qarni hammatanta sukeyi da sauri ya kawar da kansa, kwana biyu yaji tana Wannan qarnin amma Bai kai na yauba, miqewa yabar gun, kitchen ya nufa, yaqa wayam ba abinci, wai mi yake damun Humaida ne,!? wannan Abu haka, ya dawo koda yazo tana shan lemu, ta kalleshi da idonta ” wallahi honey bacci yayi awon gaba dani, rai a bace yace ” ko shekaranjiya haka kikace kinyi baqi sun cinye, idan sauran kwanakin na amarcine bakya girki yanxu yaka mata ki fara girki gaskiya, dan bazab juri  chin abinci a wajeba…”
“Sorry honey xanyi Anjima,” ya buda ledar ya dauko abinda yake iyachi yaje kitchen ya wanke ya dawo ya xauna ya fara chi, da taimakon fruit din cikinsa tayi nauyi, ya wuce dakinsa yanda yabar dakin tun tafiyarshi haka ya tarar dashi ba wani gyara, tsaki yaja ya shiga wanka ya fito ya saka kayan shi yadan kwanta sai bacci….
*****************        *******
Haka rayuwar Mahmoud ta dawo gashi nan dai, shima ya fara zama qaxamin qarfi da yaji ba wani tattali bare gyara, ba gayaran daki, shidai kullum da safe yatashi yayi wanka ya fita kasuwa. Dama mace Tanada matuqar tasiri gurin tsabtar  mijinta, da yawa mata suke gyara maxansu, su mayar dasu yanda sukeso,
Humaida ba wanka bare make up, ba gyaran gida, idan kikaga tayi kwalliya to xata unguwane, kullum da daurin qirji,
Hakan yasa Mahmoud ko sha’awarta bayayi, idan ma ya nemeta idan bataso ba yarda zatayiba…..
Muje zuwa muji ya rayuwar Mahmoud da Humaida xata kasance.
Naku
M. Jabo & Mrs Jabo.
[8/7, 6:07 PM] Mamu : MATA UKU GOBARA
5
Na MERMUE
Misalin 10:0clock na safiyar litinin Mahmoud yafito dakinsa cikin shirinsa na fita kasuwa, hula CE qube rike a hannunsa yana karyawa, har dakinta ya leka yana kiranta amma shiru ya leka bayinta babu ta, sai wari ke tashi a toilet din alamar anyi kashi ba’ayi flushing ba, yadawo palo nan ma bata, har kitchen ya shiga babuta, kitchen din sai qudaje kibin plates da ba’a wanke ba,
Gaba daya gidan ko’ina ya karade babuta babu alamarta.
Wayarsa ya dauku ya kira no. dinta amma wayar akashe, fitowa yayi harabar gidan yana kwalawa mai gadi kira, Baba Abu! Baba Abu!! Baba abu!!! A guje ya qarasu wurinsa, mai gida antashi lafiya?? Mahmoud bai wani yatsayawa karba gaisuwar ba yace ko kaga madam tafita a gidan nan??? Mai gadi yace “eh naganta ranka ya dade ta fice da sassafe nan” kai kawai ya gyada yace zaka iya komawa bakin aikinka, afito lafiya yallabai.
Kai tsaye motarshi ya shige yayi mata key, ko slow bai tsaya tayi ba ya fisgeta yabar gidan, mai gadi yana Allah ya tsare alhaji.
Tunaninsa daya toh ina humaida ta tafi??? Shin tana nufin tayi yaji ne yanxu fa cikin sati na biyu suke da aure ko meye ai bai kamata afara jin kansu yanzu ba, yana tsakanin tuki ya rasa ina zai dosa karar wayarsa ne ya katse masa tinani, dubawar da zaiyi yaga anty din humaida CE tayi kiransa, da sauri yayi parking gefen hanya ya dau wayar, “Assalamu Alaikum” yafada, a dayan gefen aka karba masa, cikin girmamawa ya gayyarda auntyn ta karba masa a gaugace, tareda cewa Dan Allah mahmoud idan baka komai kazo yanxu domin ga wannan shashar tazo tun dazo tasakamu a gaba da kuka, yace gaya nan xuwa yanxu, key ya kara yewa motarsa yabata wuta sai Runjin sambo unguwarsu humaida.
************************
Da sallamarsa aka shigo dashi acikin palon gidan, kansa a qasa cikin jin nauyi da kunyar mutanen palon ya gayar dasu, suka amsa masa fuska a sake, ya neme wuri ya zauna a qasa da kyar yadawo a kujera bayan sun matsa masa.
Abban humaida ne yake tambayar Mahmoud meke faruwa tsakaninsa da iyalinsa alhalin ko 2 weeks Baku cika ba da aure??? Mahmoud yayi shiru shidai a iya saninsa shine ma yakamata yakawo qararta ba ita ba, can ya nesa yace Abba katambayeta tunda dai itace takawu qarana, nifa ban ma san zuwanta ba, sai ynxu nafito zan fita kasuwa na duba ko’ina ban ganta a gidan ba.
Kallon kuwa a palon ya kuma ga humaida Abba yace me mijinki yayi maki kika kwasu qafa kika zo bada izninsa ba, jiki a sanyaye ta fara “Abba shine fa ya canjamin” toh muna jinki wani irin canji kenan, Baya cin abincina, baya zama a gida, harta kai ta kawo kyankyamena yakeyi anan tafashi da wani irin kuka mai cin rai, kallonsu yadawo ga mahmoud, jiki a sanyaye abba yace hakane mahmoud???? Kunya duk ta rufe Mahmoud yace Abba ai ita bata fadi abinda takeyi har na canja mata ba, “toh muna jinka mahmoud cewar Anty step mum din humaida, ita dai ummar hummaida tunda aka fara batace komai ba ,Mahmoud yace Dan Allah alhaji idan babu damuwa kuzo muje kuga abin da idanuwanku, wlh kazantar da humaida keyi bantaba tinanin zatayi ba, cikin zare ido suka kazanta fa Mahmoud, Anty har dafe gaba, idan akayi la’akari yadda humaida take yar gayu a baya zaiyi wuya yanxu mutum ya yadda cewar tanayin kazanta a gidan aurenta.
Mamaki ne qarara a fuskarsu alhaji ya yewa Anty umurni taje itada humaidar driver ya kaisu ko meye a gidan idan tadawo ta gaya masu, Mahmoud yayi masu godiya hade da sallama ya bar palon. Compound din gidan ya tsaya yana jiran su humaida su kammala kimtsawa su fito.
Acikin gida kowa Abba ya rufe humaida da fada idan aka dawo aka gaya masa Cewar tanayin kazantar da gaske sai yayi matukar saba mata, itadai kuka kawai takeyi, Anty tace yabari dai tadawo amma ita kam tana mamaki wai humaida da kazanta, hakama Abba yace nasan Mahmoud bazaiyi mata qarya ba, fitowa sukayi suka zo suka samu Mahmoud a compound driver ya jasu shikuma yabi bayansu a motarsa.
Mrs jabo.
[8/7, 6:11 PM] Mamu : MATA UKU GOBARA
4
Na  Mermue
Misalin 6:00 na yamma Mahmoud ya shigo gidansa,parking yayi a motor pack,yafito ya shige cikin gidansa, turu kofar palon yayi tare da sallama, ba kowa yabi palon da kallo yayi kaca-kaca ko’ina ba kyaun gani, bude murya yayi yana kwala mata kira Humaida! Humaida!! Humaida!!!
Fitowa tayi daga daki ta karasu wurinsa, wata uwar mika tayi tuni wurin ya canja wani irin doye ke fitowa ta hammatarta sakamakon mikar datayi, Mahmoud yayi saurin dauki fuskarsa domin warin yana Neman sakashi amai, juyuwa yayi ya kara kallonta da kyau, ganin yana kallonta ta wangame baki, wani warin baki ne ya daki hancinsa saida ya ratsasa, ba shiri yabi ta gabanta yafada dakinsa da sauri ya maidu kofa, jinginawa yayi jikin qaure yana mayarda numfashi.
Daurewa yayi ya shiga toilet, ruwa ya watsa yayi brush tareda alwala, ya fito zuwa massalaci, taradda humaida yayi zaune a Palo rashe-rashe saman tile tana tsifar kai, “massalaci zakaje honey” tace masa *eh” kawai yace mata bai kalle side dinta ba, yayi ficewarsa, ta daga murya ” toh dear kan kadawo na qarasa girki”
       *********************************
Saida yayi sallar isha sannan ya shigo gidan, wannan karon tana zaune a kujera tana cin tuwu, sai kukan sharbar miya kake ji, kan nan ba dankwali ga tsifar datayi bata karasa ba, rabi a kitse rabi a banye, ya karasu ya zauna kusanta, tace “honey miyar nan yayi dadi” wata Jan majina datayi saida yaji amai, kallonta yayi “lafiya???” Ya neme sani, wlh honey miyar CE tayi yaji kuma ga dadi,ta kara jan majinarta, Mahmoud kallonta kawai yakeyi shikam idan abaya akace masa humaida zatayi wannan kazantar ba zai yadda ba, ferrrrrrrrrrrrrr yaji alamar ana fyace majina, juyuwa yayi da karfi ido ya zaru gani abinda tayi, bakin zanin tasa ta cire majina ta saka hannu ta kara sharewa ta cigaba da cin abincinta.
Baki ciki da tuwu tace honey ga fa abincinka can a kitchen ka dauku, tana wani tauna abinci baki a bude yana ganin yadda take tauna abincin, kamar Mahmoud yayi amai yatashi ya shige
dakinsa.kallo yabi dakinsa dashi yadda ya haukace, wani karfi yazo mashi ba shiri ya hau gyaran dakin.
Sai after 9 ya kammala ya mayarda numfarfashi, shikam bai taba gyaran daki ba sai yau, a gida kannensa ke gyara masa kullum kan yadawo gida, yanxu da yayi aure matarsa ya kamata tayi masa, ashe yayi zaben tumun dare yabi kyale-kyalen duniya.dama annabi Muhammad (S.A.W) yace ya horemu da mu auri mata mai addini itace alkhairi a garemu.
  Wanka ya kara yuwa yazo ya haye gadonsa sai qamshi yake zubawa, haushin humaida ya hanasa ko Palo ya kara komawa,ballanta har yayi maganar cin wannan kwamacalarta wai girki ne, azkar din kwanciya bacci yayi, ya janyu blanket kenan ta shigo dakinsa, kallo yabita dashi har ta karasu ciki, riga da zani na atmafar dazu ne dai ajikinta, tana matsuwa kusa dashi kayan sai warin girkin datayi sukeyi, ga jajjagen datayi na kayan miya duk ya fallatsar mata ajiki, fuskar nan sai maiko take fitarwa,bata CE dashi kala ba ta dani gadonsa, honey tun dazo ka shanyani a falo kaki fitowa kazo kaci abincinka, nikam almajiri yayi bara nabasa. “Toh ai shekinan” haka kawai yace mata, ya juya yayi kwanciyarsa.
Itama kwanciya tayi a bayansa ta fara basa labarin series dinda tayi kallo yanxu a zee tv, yayi kamar bai jitaba, data gaji tayi shiru don kanta.
Mahmoud yaji yana bukatar matarsa ya juyu wurinta tana nan idonta biyu sai latse2 takeyi a wayarta download din screen zip unlounck take tayi a wayarta, rungumarta yayi da karfi ya sauke ajiyar zuciya, Allah yasani yana kaunar matarsa amma sauyawar datayi yana matukar bata masa rai, ita kuwa hajiyar jin datayi alhajinta yana bukatarta ai sai ta shiga turesa yakara maiduta jikinsa hannu ta xira masa, “nawa zaka bani” tafada cike gadara, kamar ya?? Mahmoud ya tambaya, wani kallo humaida ta watsa masa, qara janyuta yayi hancinsa yakai ga gashinta rabi tsefe rabi a banye wani wari mai hamami yayi masa sallama ba shiri ya tureta, mikewa yayi itama ta mike harta kai tsaye “get out” ya nuna mata hanyar kofa, a zuciye ta fice daga dakin…………………..

8/7, 6:07 PM] Mamu ?: ?MATA UKU GOBARA?
                       5
       Na MERMUE?

[8/7, 6:11 PM] Mamu ?: ?  MATA UKU GOBARA ?
                        4
         Na  Mermue?
Misalin 6:00 na yamma Mahmoud ya shigo gidansa,parking yayi a motor pack,yafito ya shige cikin gidansa, turu kofar palon yayi tare da sallama, ba kowa yabi palon da kallo yayi kaca-kaca ko’ina ba kyaun gani, bude murya yayi yana kwala mata kira Humaida! Humaida!! Humaida!!! 
Fitowa tayi daga daki ta karasu wurinsa, wata uwar mika tayi tuni wurin ya canja wani irin doye ke fitowa ta hammatarta sakamakon mikar datayi, Mahmoud yayi saurin dauki fuskarsa domin warin yana Neman sakashi amai, juyuwa yayi ya kara kallonta da kyau, ganin yana kallonta ta wangame baki, wani warin baki ne ya daki hancinsa saida ya ratsasa, ba shiri yabi ta gabanta yafada dakinsa da sauri ya maidu kofa, jinginawa yayi jikin qaure yana mayarda numfashi.
Daurewa yayi ya shiga toilet, ruwa ya watsa yayi brush tareda alwala, ya fito zuwa massalaci, taradda humaida yayi zaune a Palo rashe-rashe saman tile tana tsifar kai, “massalaci zakaje honey” tace masa *eh” kawai yace mata bai kalle side dinta ba, yayi ficewarsa, ta daga murya ” toh dear kan kadawo na qarasa girki” 
       *********************************
Saida yayi sallar isha sannan ya shigo gidan, wannan karon tana zaune a kujera tana cin tuwu, sai kukan sharbar miya kake ji, kan nan ba dankwali ga tsifar datayi bata karasa ba, rabi a kitse rabi a banye, ya karasu ya zauna kusanta, tace “honey miyar nan yayi dadi” wata Jan majina datayi saida yaji amai, kallonta yayi “lafiya???” Ya neme sani, wlh honey miyar CE tayi yaji kuma ga dadi,ta kara jan majinarta, Mahmoud kallonta kawai yakeyi shikam idan abaya akace masa humaida zatayi wannan kazantar ba zai yadda ba, ferrrrrrrrrrrrrr yaji alamar ana fyace majina, juyuwa yayi da karfi ido ya zaru gani abinda tayi, bakin zanin tasa ta cire majina ta saka hannu ta kara sharewa ta cigaba da cin abincinta.
Baki ciki da tuwu tace honey ga fa abincinka can a kitchen ka dauku, tana wani tauna abinci baki a bude yana ganin yadda take tauna abincin, kamar Mahmoud yayi amai yatashi ya shige dakinsa.kallo yabi dakinsa dashi yadda ya haukace, wani karfi yazo mashi ba shiri ya hau gyaran dakin.
Sai after 9 ya kammala ya mayarda numfarfashi, shikam bai taba gyaran daki ba sai yau, a gida kannensa ke gyara masa kullum kan yadawo gida, yanxu da yayi aure matarsa ya kamata tayi masa, ashe yayi zaben tumun dare yabi kyale-kyalen duniya.dama annabi Muhammad (S.A.W) yace ya horemu da mu auri mata mai addini itace alkhairi a garemu.
  Wanka ya kara yuwa yazo ya haye gadonsa sai qamshi yake zubawa, haushin humaida ya hanasa ko Palo ya kara komawa,ballanta har yayi maganar cin wannan kwamacalarta wai girki ne, azkar din kwanciya bacci yayi, ya janyu blanket kenan ta shigo dakinsa, kallo yabita dashi har ta karasu ciki, riga da zani na atmafar dazu ne dai ajikinta, tana matsuwa kusa dashi kayan sai warin girkin datayi sukeyi, ga jajjagen datayi na kayan miya duk ya fallatsar mata ajiki, fuskar nan sai maiko take fitarwa,bata CE dashi kala ba ta dani gadonsa, honey tun dazo ka shanyani a falo kaki fitowa kazo kaci abincinka, nikam almajiri yayi bara nabasa. “Toh ai shekinan” haka kawai yace mata, ya juya yayi kwanciyarsa.
Itama kwanciya tayi a bayansa ta fara basa labarin series dinda tayi kallo yanxu a zee tv, yayi kamar bai jitaba, data gaji tayi shiru don kanta.
Mahmoud yaji yana bukatar matarsa ya juyu wurinta tana nan idonta biyu sai latse2 takeyi a wayarta download din screen zip unlounck take tayi a wayarta, rungumarta yayi da karfi ya sauke ajiyar zuciya, Allah yasani yana kaunar matarsa amma sauyawar datayi yana matukar bata masa rai, ita kuwa hajiyar jin datayi alhajinta yana bukatarta ai sai ta shiga turesa yakara maiduta jikinsa hannu ta xira masa, “nawa zaka bani” tafada cike gadara, kamar ya?? Mahmoud ya tambaya, wani kallo humaida ta watsa masa, qara janyuta yayi hancinsa yakai ga gashinta rabi tsefe rabi a banye wani wari mai hamami yayi masa sallama ba shiri ya tureta, mikewa yayi itama ta mike harta kai tsaye “get out” ya nuna mata hanyar kofa, a zuciye ta fice daga dakin…………………..

8/7, 6:07 PM] Mamu ?: ?MATA UKU GOBARA?
                      6
Na Maryam alkali { MERMUE}
Tafiya sukeyi ahankali har suka qarasu gidan, parking akayi duk suka fito waje, Mahmoud ya bude kofar palon yace da Anty bismillah, kanta ta kutsa acikin palo tayi turus tana kare masa kallo, ko’ina yayi kaca2, ta juyu tana yiwa humaida kallon tuhuma, tayi saurin sadda kanta qasa ganin irin kallon da Anty ke mata, kofar kitchen Anty ta bude wasu qudaje suka karba mata sallama, dayake humaida tabar window din kitchen a bude wannan dalilin qudajen suka samu wurin party, fitowa tayi daga kitchen taje dakinta tashin hankali qarara bayyane a fuskarta, ita kam tana mamaki yadda humaida ta mayar da kanta qazama, ko don tasaba agida bata aikin komai masu aiki keyi, iyakacinta tayi kwalliyarta kullum.
Mahmoud yana ganin tayi hanyar bedroom ya qarasa wurinta durkusawa yayi ya mata sallama xai fita kasuwa, Anty tayi masa adawo lfy  muryarta cikin yanayin damuwa, yana fita gidan ta fisgu humaida, turata tayi cikin dakin “duba yadda gadonki yake humaida” ke bakisan kullum ki gyara gadonki akalla sau 3 a rana ba, dubi yadda bedsheet din duk ya zame, wai wannan doyi daga ina yake fitowa? cewar Anty humaida tayi rau-rau da ido cikin murya qasa2 tace toilet dina ne, dafe gaba Anty tayi badai harda wanke toilet din bakyayi ba, zaki kuwa janyu ma kanki infection “ina wankewa Anty” kina wankewa yakeyin wannan zarnin, lekawa tayi toilet din warin kashi da fitsari ba’a magana, ta juyu ga humaida bakisan toilet mai tile yafi fitarda wari ba, aqalla kullum sau 2 a wuni ki wanke toilet dinki tas kisaka tirare, zai ta fitarda qamshi mai dadi, Dan Allah ni fito na tayaki ki gyara gidan kuma komai a kunnen alhaji shasha wadda bata san ciwon kanta ba.
Haka Anty tayi ta gayawa humaida dabarun gyaran gida da tsafta, tareda da bata tsoron cewa mijinta zai iya qaru aure ta daina ganin basu jima da aure ba, domin shi aure anayinsa domin samun kwanciyar hankali.amma idan mutum bai samu ba to lallai namiji zai iya qarawa, ai tuni humaida ta rude taji zancen kishiya cewa takeyi to Anty yasamu min aiki kinga zata tayani kula da gidan, tsaye Anty tayi tana kallonta ke humaida kazama CE kuda kuwa kinada mai aiki, yanxu ina kwalliyarda kike cancadawa a baya? ai kin daina yanxu ko kuwa mai aikince zata rika maki wanka da kwalliya?? Kedai idan zaki gyara ki gyara. Idan kuwa so kawai kike kiji anshigo da wata gidan nan mudai ba ruwanmu.
Yau namiji ko kina masa komai zai iya karu wata matar ballantana keda komai ma baki tsare masa ba, wlh humaida kishiga hankalinki, ina laifin da safe da kun gama sallar asuba kiyi addu’o’inki kije kitchen dinki ki gyara, parlour, bedrooms, kizo kiyi ma angonki breakfast kije ki cancara adonki, kitashishi shima yayi wanka yazo yayi break ya fita, a lokacin zaki samu tym kiyi baccinki enough, kitashi ki dora girkinki kan yadawo kin kammala komai gida yana tashin qamshi, amma ke kinxo kinxama wata kucaka kamar ba humaidata ba, mai tsananin kwalliya da qamshi. 
Haka dai anty ta taya humaida gyara gidan, tana yimata nasiha akan zaman aure, kuma ta jaddada mata ba dole sai mace tanada mai aiki zatayi tsafta ba, idan dai ta tsara aikinta bata biyewa son jiki tas zata rika gyaran gidanta kuma ba tareda tasha wuya ba, kan ta tafi saida tasata ta idar da tsife kitson kanta, ta wanke gashin da shampoo & conditioner tayi wanka tayi kwalliyarta cas irin ta baya, fuskar nan tafito radau yau taji foundation irin Wanda ta kwana biyu bataji ba.sallama Anty tayi mata, humaida har mota ta rakata tareda godiya sannan ta juya cikin gidanta.
Mahmoud yau yadawo gidan komai tsaf har aransa yaji dadi yadda yaga komai tsaf, sai kallon palon yakeyi amma bata cikinsa, direct bedroom dinta yayi yasameta tana sana’ar tata wato bacci, da kyar yatasheta ta mike tana zumbure2 wai yatayar da ita daga bacci alhalin yau tasha aiki, binta kawai yayi da kallo daga bisani yayi kwafa ya bar dakin.
Dakinsa ya shige ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, jallabiyarsa ya xira fara kal ya fito zuwa massalaci domin yin sallar magrib, bai dawo ba sai after isha, ya shigo falon da sallama tana nan zaune tana kallo da remote a hannunta, “lah honey har anyi sallar isha’i” eh yace mata kitashi kije kiyi idan bakiyiba, tace toh bara akarasa wannan,Dan karamin tsaki yaja, yace wannan ba zai kaiki ko’ina ba kedai kullum kallon zee TV dramers din banxa bazasu amfaneki ba duniya da lahira.nidai bani abincina yunwa nakeji, “ido ta zaru haba honey bakaga wahalarda dana sha ba” gyaran gidan nan ko’ina jikina ciwo yakeyi, nidai kawai muje “prince restaurant” muce abincinmu mudawo..
Wani qulolon bakin ciki ya turneki mahmoud ba abinda ya tsana irin cin abincin kasuwa, ganin yabata rai tace toh Ku muje “Sa’a mai Sa’a” banxa yayi mata ya wuce dinning ya hada tea dinsa yasha ya shige dakinsa tareda sanya key yayi kwanciyarshi.
                 Mrs Jabo.
  
? MATA UKU GOBARA?
                      7
 Na maryam alkali {MERMUE}
Haka rayuwarsu ya kasance har tsawon wata biyar da aure, kazantar humaida da son jiki sai abinda ya karu, kwata kwata shima mahmoud yana nema ya zama kazamin, gidansu mahmoud duk sun gani humaida qazamace, while gidansu anyi2 da ita tadaina taki sun kawo nagani sun Dora mata.
Yau humaida tana zaune a falonta aqasa saman centre carpet dinta tayi rashe2 tana shan mango kudaje sai binta suke, dayake lokacin mango ne ynxu ya nuna ga ruwa, ruwan nata tarara a hannun humaida har sun kawo mata ijiyar hannu, shan abunta takeyi hankali kwance ruwan na dirara a centre carpet dinta, daga ita sai daurin qirji wai ita adole zafi akeyi, hammatarta tanata yoyon zufa ga gashi cunkus da ita, duk fa wannan bidirin da akeyi Abdul yana kwance  a 2seater baya jin dadi shine yau bai fita kasuwa ba, remote a hannunsa yana kallon news a aljezeera, sallama aka rafka aqofar Palon, shine ma ya karba sallamar don bakin humaida ciki yake da mangurunta qudagun gaba daya ta tura abaki, wadda Abdul yaga tashigo palon saida gabansa yafadi.
Goggonsa CE qaunace a wurin mahaifinsa marigayi mai rasuwa, uwa daya uba daya, Sam bata daukar wargi kuma bata shiri da kazame, mace CE mai matukar tsafta da kyankyame, da sauri Abdul ya mike yana yimata sannu da zuwa, turus tayi ganin humaida da iren kazantar datakeyi, ta nunata wannan fa mahmoud??? Yana Susa keya yace goggo humaida CE baki ganeta ba? 
Zauna mana yace da ita…..
Ita kuwa humaida sai yanxu ta ciru qudagun mangarun acikin bakinta ta mike tana gyara daurin kirjinta, sannu goggo kice ke tafi ynxu cikin zafin nan….! Goggo binta kawai takeyi da kallo tabdi tafada aranta, Mahmoud ya qara maimaitawa “ki zauna 
mana goggo” ta karewa palon kallo tsaf tace mahmoud banga wurin zama a palon nan ba, idan akwai wurida yafi nan dan kimtsuwa kaini.
 Ta nuna humaida pls kije ki kimtsa kanki kizo kisamemu, kada kai kawai humaida tayi ta juya ta shige dakinta, “itafa tafara quluwa da matar nan” bata son cin fuska.
Mahmoud kai goggo yayi dakinsa ta zauna a resting chair dake dakin tace mahmoud dama Ashe kucaka ka auru? Toh wlh bata sabuba bindiga a ruwa, aure zaka qara!!!! Aure???? Mahmoud ya tambaya kwarai kuwa bari matarka tazo, dai2 nan humaida ta shigo hijab kawai ta Santa saman daurin kirjinta, ta neme guri a gefen gado tazauna tana cika tana batsewa ita a dole an wulakantata.
Goggo tace humaida kalloni nan mahmoud aure zai qara domin bazaki kashe mana da ba, muna ji muna gani, wannan kazantar har ina ai saike bashi kulara yasha ciwon ciki ya aikasa lahira. Kibude kunnuwanki da kyau nayanke shawara yanxun nan zamu hadashi aure da yar uwarsa zuhra yarinya wadda ta iya tsaftace gida kai da kula da kowacce bukatarsa.
Humaida tuni ta kedeme kishiya????? Wayyo hannu da dora aka ta zunduma ihu tuni tafice dakin, dakinta tafada tana kuka birgima tafara saman gadonta har tafadu qasa.
Goggo mikewa tayi tana karkade zaninta tace kaga tafiyata, yanxu xanje can gidanku na same haj Talatu muyanki magana, shidai Mahmud rike kansa yayi dayaji yafara juya masa, baya yayi yafada sama gadonsa yana mayarda numfarfashi.
Search ANTIE MERMUE NOVELS facebook group.tnx ol my fans 
          Mrs jabo.
[8/7, 6:09 PM] Mamu ?: ? MATA UKU GOBARA?
                    8
   Na Maryam alkali (Mamu)
Humaida da taga kukan ba amfaninta zaiyi ba, mikewa tayi kamar an mitsilita, ta jawo box tafara loda kayanta dake cikin Sif, da wankakku da goggagu da masu datti duk tahade wuri daya acikin box dinta, dakyar tayi zipping, ta janyu box dinta tafito Palo, Mahmoud da sauri ya fito daga dakinsa yasha gabanta, ina zaki????….
Murguda masa baki tayi tace ” gidan ubana” humaida ynzu akan wannan maganar da goggo tayi ne zaki kwashe qafa kije gidanku??? Kuma Allah yasa kowa yanada gidan ubansa ballantane ayi masa gori, so “u can go” Allah ya tsare hanya, har tafara tfya ya daga murya “aure kuma ba fashi” juyuwa tayi kamar ta cinyeshi danye, me kuma ta tuna ta ficewa aguje a palon janye da trolley dinta.
Acan kowa goggo taje tasami Hjy talatu mahaifiya ga Mahmoud, ta labarta mata komai tas, tace tayanke hukunci za’a hada Mahmoud da zuhra, ynxu zataje tasamu mahaifin zuhra akira family meeting atsaida rana, “hakan yayi” cewar hajiyar Allah yasa hakan yazamu alkhairi garemu gabaki daya “Amin” goggo ta cafke tareda mikewa “toh ni xantafi” komai ake ciki sai anhade a family meeting. Acan kowa gidansu humaida har napep ya sauketa a kofar gidansu kuka takeyi, ta bude murya kamar wani qaton drum, mika masa tayi kuddinsa ta shige da gudu, mai napep yana Hjy ga canji ina….!
Sai mai gadinsu yabawa yakaimata canjinta, da gudu ta shigo palon tana wani irin kuka, duk mutanen palon suka mike tsaye gabansu yana dakan tara2, kowa na gidan yana Palo kasancewar Abba yadawo duk anzo masa sannu da dawowa, saiga humaida ta fado palon kamar ancilluta, rungume Anty tayi tana fadin “nashiga uku” wai meke faruwa Abba yadaka mata tsawa, Mahmoud ne ya mutu ko accident yayi????
Gwanda haka Abba da abinda zaiyimin, ido abude Abba yace me zaiyi maki??
Nashiga uku abba goggonsa CE tazo gidanmu wai ni kazamace kar nabawa dansu kwalara yace ya mutu yar uwarsa zasu aura masa mai tsafta….!!
Wayyo Dan Allah na rokeku kuje kumasu magana ina son mijina banaso su aura masa wata, kamu qafar abba tayi ta rike “pls abba am begging u” karka bari ayi mani kishiya, wlh hauka zanyi idan akayi………bata qarasaba ya dauketa da wawan mari, “kinsan kina sonsa me yasa baki kyautata masa” tambayarki nakeyi….???
Anty CE tazo tana bada hakuri, ummar humaida kam sai qara ziga abba takeyi, wai albasa batayi halin ruwa ba, agidannan nida antynki waye qazami acikinmu Allah ya shiryaki humaida, daga fadar haka tayi shigewarta dakinta.
“Albishirinki” humaida ta dago da sauri jin cewar abbanta nayi mata albishir, ta fara shafe hawayen fuskarta, harda Dan murmushinta da bai kai ciki ba, “nayi alqawari ni xanbiyawa Mahmoud sadakin matarsa da aka basa” wani ihu da zuba saida Anty ta firgita she thoughts ko aljannu sun kama humaida, rike Anty tayi tana turmushi2 a qasan carpet din palon, ” and now get of house” abba ya nuna mata qofar palon, tsayawa tayi da abinda takeyi, ta mike ” abba kadaina sona ynxu koh…..??? Eh naji din ki ficemin agida ynxu, Anty tace alhaji…….ya katseta yimin shiru……!
             Mrs Jabo.
      ? MATA UKU GOBARA?
                    9
   Na Maryam alkali ( MAMU)
Alhaji ba don niba kasa driver yakaimu da ita, zanyi mata nasiha kuma natayata gyaran gidan, pls alhaji katausaya mata kada ka kara mata wani bakin ciki kan wani….” Wa ya janyuwa kanshi idan ba ita ba” Allah nace alhaji, toh ai shikenan tunda kince Allah sai kuje din, amma humaida idan kika sake kika qara dawowa gidana da sunan yaji…….yayi kwafa bai fadi abinda zaiyi mata ba….hmmmm zaki gane shayi ruwane and then zaki San barno gabas take……!
Wani kuka humaida ta kuma sake, Anty ta kamata muje ta duka tana janyu trolley dinta, sai ynxu suka lura tazo da ita, “au dama harda box kikazomin agida ke ga gidan ubanki koh” ai ynxu gidan nan yafi qarfinki shashasha, sususu, hoteho kawai…..! Drya kamar takwacewa Anty jin irin sunayenda yake kiran humaida dasu tace “muje” drv ne ya tasu ya karbe box din yasaka a boot, ina zamuje Hjy…!
Gidan humaida zaka kaimu, dukkansu abaya suka kame drver yajasu sai gidan mahmoud.
Shikuwa agefen Mahmoud yana ganin fitar humaida shima key din motarsa yadauka yayi ficewarsa, wurin hajiyarsa yaje, yana nan tana masa nasiha aka kirasu taron emergency na family, daukar hjyarsa yayi suka wuce, agidan kakansa dake kofar atiku akeyin family meeting dinsu, tafiyar 15minutes CE takaisu daga low cost zuwa cikin gari kofar atiku, suna xuwa aka fara meeting inda iyaye maza sukayi na’am da shawarar goggo, nan take aka yanke lokacin daura aure nan da 1month.
A gefen Amarya kuwa kamar ta taka rawa kasancewar ta dade tana son Mahmoud kwatsam taji ance ya nemo mata zaiyi aure, hakanne yasa tafitar da rai da samunsa da cigaba dayin addu’ar Allah ya bata irinsa domin mahmoud badai kyau kuma ga kyaun hali dama shi akeso.
“La’ilaha illalah muhammadu rasulullah sallalahu alaihi wasalam” ni mairo cewar Anty ” ynxu Ashe wannan yarinyar baki daina qazanta ba, ji yadda kika mayarda gidan, kamar mai ‘ya ‘ya goma, dole suce zasuyi masa aure kada ki kashe masu yaro lokacinsa baiyiba, yanxu kina nufin duk nasihar danayi maki abaya ta zama ta banxa….????
      
? MATA UKU GOBARA?
                    10
    Na maryam alkali (MAMU)
Kunnenta ta janyu ta mirde saida humaida ta saki fitsari a pant, ta saketa “wlh humaida nakusa fitarda hannuna a lamarinki” kinga alhaji da hajiya duk sunyi fushi dake Nima nakusa fitarda hannuna a lamarinki, kuma nagaya maki fushin mahaifa bazai haifar maki ‘da mai ido ba, komai naki kara lalacewa zaiyi tun wuri ki gyara nagaya maki….!
Dallah ni zo natayaki ki gyara gidan, kucakar banxa kawai, daga idonta tayi suna tsiyayar hawaye “Anty nice kucaka” yuuuuu ai wata kuxaka tafiki domin kila ita idan tayi aure tadaina kucakancin, kefa saida fa kikayi aure sannan kika fara ” wlh nagaya maki duk kwalliyar da kikayi abaya baki da lada kilama idan aka bincika kinada zunubi, amma da ace saida kikayi aure ne kikayi kwalliyar ladarda zaki samu Allah ne yasan adadinta.
Anty Ta gyara zama ” murushi idan kikayi masa lada ” ido humaida ta bude da kunnuwa tana sauraren anty, Anty tacigaba, shima idan ya mayar maki lada” idan kikayi masa kwalliya yagani yaji dadi lada, ke lada shi lada, girki idan kikayi mai dadi lada, gyaran gida idan kikayi yagani yaji dadi shima lada, komai fa kikayi Wanda zai faranta ran mijinki to zaku samu lada, amma ke humaida kina wasa da aurenki, kin dau aure abin wasa ” toh wlh tun wuri ki gyara zamanki a gidan aurenki domin idan wannan matar ta Abdul ta shigo baki gyara ba, idan yasameta yanda yake son mace toh wlh kin kade har ganyenki” bude murya humaida tayi ta fashe da kuka ” ke Dallas can wawiyar banxa wayace maki haka mace ke kuka” ba shiri himaida ta hadiye kukanta….!
Yanxu haka kike bude masa murya kamar drum ai babu aji anan, ke bakisan komai na mace mai class daban ne…!!!!
Hmmmm humaida kenan tashi muyi aikin dazamuyi drv yana jirana, haka suka kammala aikin gyaran gidan Anty tana wayar ma humaida kai haka suka kammala tayi mata sallama ta tafi.
          
? MATA UKU GOBARA ?
                   11
    Na Maryam alkali (MAMU)
Anty na wucewa humaida ta xube a 3seater tafara dirkar baccinta, dai dai nan Abdul ya shigo gidan, yayi mamakin ganinta, yadai wucewarsa dakinsa, wayarsa ne yafara ringing ya dauku yaga abban humaida ne, cikin girmamawa ya gaidasa kamar yana gabansa, abba ya karba masa cikin jin dadi shidai yana son Mahmoud “wannan shashashar tazo amma nasa andawo da ita” don Allah Mahmoud acigaba da hakuri dama zaman sure haka yagada “ba komai abba” ya maganar dayar matarka??? Saida yayi jimmmmm sannan yace abba daga can nake ynxu muka tashi daga family meeting wai sun saka date nan da 1 month za’ayi biki, cikin jin kunya duk Mahmoud ke wannan jawabin ga abban humaida, toh “Alhamdulillah” yaji abba nafada Wanda za’ayiwa ‘yarsa kishiya…..!
“Mahmoud inaso kafadamin ko Nawa ne kuddin sadakinka idan anfada domin nayi alqawarin ni zan biya” eyeeeeee abba me kake cewa, dariya abba yayi yace kaji ai mahmoud sai dai kawai najika ya tsinki wayar…….!
Mahmoud rike waya yayi a hannu yana mamaki iyayen humaida sunada matukar mutunci “in shaa Allah” zai rike yarsu hannu bibbiyu yayi hkr da halinta.
            ****** ******** *******
Lokaci nata tafiya mahmoud tuni sun dai daita da zuhra, soyayyarsu sukeyi mai tsafta, cikeda girmama junansu.
Yau saura 2 weeks biki yau ne za’a kai lefe, humaida kamar ta kurma ihu takeji tabi daji, bayan lefen Amarya dana uwargida iri daya komai akayi masu kowa set 1 na akwati, colour ne kawai ya bambanta kayansu, haka adauke kaya aka kai gidansu zuhra dake wurno road, uwar gida da tawagarta sai harare-harare takeyi, anci uban kwalliya ita adole ga wise, duk yan gidansu zuhra sun ganta amma sukayi banxa da ita, dataga ba Wanda ya kulata tafara yada kananan maganganu wai zuhra tayi kwantai anlekawa mijinta ita.
Banza sukayi mata sai Anty CE ta jata gefe cewar xata sanarda alhaji rashin mutuncin datakeyi sannan fa takama bakinta tana taunar chewing gum, haka dai taro ya watse dangin Amarya sunata murna abinsu.
Saura sati 1 biki mahmoud duk ya kammala gyaran gidansa, ya canja kayan Palo yanzu son zama mallakinsa, itama humaida ya canja mata gadon dakinta domin duk tabata nata, dakinshi ma ya gyara abinsa tsaf, sai rashin mutunci humaida ke tafkawa, anata haukar ta dauka zaisa afasa ko Mahmoud yaji tsoronta, bata San duk abinda takeyi ba  tsanarta yake qara masa ba…….!!!!
Reply

Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  MATA UKU GOBARA (Last Part) Gimbiya 0 8,308 09-28-2018, 08:05 AM
Last Post: Gimbiya
  MATA UKU GOBARA Gimbiya 1 7,396 09-20-2018, 09:52 AM
Last Post: Gimbiya
  2019: Kwankwasiyya Ta Raba Wa Mata 100 Naira 10,000 A Yobe Edoman 2 2,534 04-23-2018, 12:44 PM
Last Post: Edoman
  PDP Za Ta Kara Wa Mata Mukamai Idan Ta Lashe Zaben 2019 –Mariya Waziri Edoman 0 1,767 04-22-2018, 12:57 PM
Last Post: Edoman
  PDP Za Ta Kara Wa Mata Mukamai Idan Ta Lashe Zaben 2019 Edoman 0 1,954 04-22-2018, 12:53 PM
Last Post: Edoman
  HANYOYIN GYARAN JIKI NA MATA DA MAZA Gimbiya 0 3,111 11-13-2017, 05:39 PM
Last Post: Gimbiya

Users browsing this thread: 1 Guest(s)