The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/showthread.php 26 require_once
Warning [2] Undefined array key "mybb" - Line: 1952 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 1952 errorHandler->error
/inc/functions_indicators.php 41 my_set_array_cookie
/showthread.php 629 mark_thread_read
Warning [2] Undefined property: MyLanguage::$ratings_update_error - Line: 5 - File: showthread.php(732) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(732) : eval()'d code 5 errorHandler->error
/showthread.php 732 eval
Warning [2] Undefined variable $postsdone - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Trying to access array offset on value of type null - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 19937 - Line: 867 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 867 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key 19937 - Line: 1576 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1576 errorHandler->error
/showthread.php 1578 buildtree
/showthread.php 879 buildtree
Warning [2] Undefined array key "additionalgroups" - Line: 7162 - File: inc/functions.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions.php 7162 errorHandler->error
/inc/functions_user.php 844 is_member
/inc/functions_post.php 406 purgespammer_show
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "profilefield" - Line: 6 - File: inc/functions_post.php(474) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php(474) : eval()'d code 6 errorHandler->error
/inc/functions_post.php 474 eval
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 741 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 741 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 746 - File: inc/functions_post.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/inc/functions_post.php 746 errorHandler->error
/showthread.php 880 build_postbit
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "threadprefix" - Line: 4 - File: showthread.php(1168) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1168) : eval()'d code 4 errorHandler->error
/showthread.php 1168 eval
Warning [2] Undefined array key "invisible" - Line: 1506 - File: showthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php 1506 errorHandler->error
Warning [2] Undefined variable $threadnotesbox - Line: 30 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 30 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 33 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 33 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $multipage - Line: 65 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 65 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $addremovesubscription - Line: 79 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 79 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval
Warning [2] Undefined variable $forumjump - Line: 86 - File: showthread.php(1533) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/showthread.php(1533) : eval()'d code 86 errorHandler->error
/showthread.php 1533 eval




Thread Rating:
  • 0 Vote(s) - 0 Average
  • 1
  • 2
  • 3
  • 4
  • 5
*KASUWANCI NA* by ASMABAFFA
#2
    KASUWANCI NA



          109-110



Official



By
AsmaBaffa


      MAMAN 2 KIDS and MOM INTEESAR wannan page nakU ne sabo da jajircewarki a Sharhi.

  HUMAIRA sarkin Sharhi ina gaisuwa me tarin yawa.


  AUTA ina kika boye tare da ASYCOOL shuru Allah yasa lfy.

Manya manya maganin kanana Jinjina nake muku
FLOWER
MARCYCOOL
ZAINAB ATIKU SALAMA
SAMEERAN GAYA
HAFSAT KHAIRAN
MAMAN MEENAT
MOM SUHAIL
MRS HAMZA
MRS UMAR
MRA FAROUQ
JANNAT
MAMAN WALEEDA
QUEEN MERMU.
  
           Ido ya lumshe tare da budesu tar a kaina,kallonsa nakeyi cike da so tare da kewa shima hakan,wani kallon so muke aikawa da juna dadi na ratsa mu, magana ya fara yi min cikin nutsuwa,Mufeeda ya furta cikin muryar tausayi da lallashi,Kallonsa nayi sunan da ya furta har kwakwalwata haka naji kamar wata na'ura ce ta ambaci sunan haka nake jin dadinsa.
   Magana yaci gaba da cewa tunanina kinyi hankali Ashe ba haka bane,an miki bayani sai ki fassara abu bai bai,kin kasa Fahimtar me ake nufi,yanzu abinda kikayi kin kyautawa Ammah kenan,mahaifiyarki guda,ta miki komai a rayuwa ance ta rasu kin damu kina kewarta ance bata rasu ba ta dawo akwai dalilin da yasa ta shirya hakan,ba wacce take so sama dake,bata da magana sai Mufeedanta,tazo har gidan mijinki da kike aure amma kika ki Kula ta ko kallo bata isheki ba,mutumin da yayiwa Mahaifiyarsa haka waye bazai masa ba,iyaye fa basa laifi wurin yaransu,Meenat su fiki hankali,mahaifiya guda kika ki kulawa,kika wulakanta,tana can da bacin ranki Allah ma na fushi dake,sannan ni ban miki komai ba ina mijinki kalli abinda kika dinga yi min kan abu kalilan kin bani kunya,yanzu gobe zamu je ki bawa Ammah hakuri ki shirya idan kin yarda idan baki yarda ba to,Da sauri nace ni bazan je ba na daina kulata tunda tayi min haka, cike da bacin rai yace to tashi kije nima ba ruwana dake.

    Kin tashi nayi tare da yin shuru sai da aka kwashe 15mnt sannan ina kunkuni nace to shike nan ai zanje amma Allah bazan gaishe ta ba tunda tace ina da son Kudi,Hararar wasa ya jefo min yasan na hakura ma tunda na yarda zanje,abincin fa baza Kaci ba? Kince baza ki gaisar da Ammah ba ta ya zan ci abincinki,baki na turo ai dai nace idan Naje kawai zance Sannu da zuwa Ammah amma Allah bazan gaisheta ba,to ruwa kawai zan sha nima,kai dan Allah Nafa sha wahala wurin girkin nan na bata lokaci nayi maka da kaina,baka ji dadinsa ba pls Kaci ko kadan ne? Bazan ci girkin wacce bata gaida Mum dinta ba,da ace kina gaisheta sai naci,shuru nayi sai da naga lallai bazai ci ba nace to zance mata Sannu Ammah ni dai bazan ce ina yini ko ina kwana ba Allah sai in kar Kaci abincin kuma ai nayi kokari ma.
  Shi kanshi yasan ma na huce gaba daya sai yace to zanci badan halinki ba,ina murna na cire Hijab dina na ajiye gefe,ya kalleni sama da kasa yaga kayan Harka iya kaya,Nayi kyau ga kayan baccin matsiyata dasu komai ana gani, ina sane nake kara girgiza jikina ko ina rawa yakeyi na zuba masa komai kawai na dauki Hijab dina zan mayar jikina yace noooo pls ki barshi haka zo ki tsaya a gabana,haka ya tsayar dani kamar wata soja yana cin abinci yana kallona na kasa tsayawa waje daya sabo da na tafi da Imaninsa ina sani nake girgiza jikina wai irin na gaji da tsaiwa sai kukan shagwaba nake masa ina dire diren kafafu shi kuwa karfin Hali kawai yake yi tuni hankalinsa baya jikinsa idonsa ya canja da kyar ma yake kokarin cin abincin hankalinsa yana kaina.

    Bai ma gama ci ba naga yace kwashe na koshi,na kwashe komai na mayar kitchen sannan na koma dakina na kwanta a bed tare da yin dai dai wai irin Jan aji nasan dole zai biyo ni,Brush da shiri ya sake ya fito yaga bana Bedroom din,Wayata ya kira yaga ban daga ba,ya kara kira shuru ina kallo kuma,Da kansa ya Mike ya nufi inda yasan zai ganni,hango ni yayi na baje ina baccin karya amma tunaninsa baccin gaske ne,wani juyi nayi me Jan hankali,light ya kashe tare da haurowa Saman Bed din,yanda naga yana abu a rude shi ya bani dariya har na kasa rikewa na saki abata,cakulkuli ya fara min muna dariya yace dama kina kallona ko? Nace Oya let's go,ai Bazan iya matsawa nan da can ba kawai mu kwanta a nan, yau ban bari ya fara min komai ba,ni na fara Sabo da nayi Missing din mijina da yawa,kamar zan cinye masa lips tare da tongue haka nake tsotsesu da zafi zafi, dadi ya gama rufe shi kawai wani nishi mukeyi,Bana iya cewa komai sai dai nace Miss u Baby,Shima haka can kasa naji yace yau Dan Ficici za a bani,Lokacin ina jin dadina ya min yawa bana hayyacina nace a'a yau kamfatowa zakayi,yace Allah? Nace ai Kwaso kawai, yace an gama,ba karya kuwa ya kamfanta dan yau nafi ko yaushe jin jiki a hannunsa,ba karamar wahala nasha ba,tun ina kuka dadi sai da na koma na wahala,sabo da ban wani saba ba,kadan na saba Bazan iya dauke yanda yake so ba ba tare da na dan sha wahala ba yanzu sai nan gaba,har yau sabon nawa ba wani me yawa bane sai kuri idan anzo kuma na fara kuka ido ya raina fata,shi kanshi Aayan ya san iya limit din da nake kaiwa ban gajiba,shine yake so dole na saba sai yazo wanda lokacin na gaji sai ya dinga Dragging dina,Kuma ko yaushe yana ganin ci gaba tunda kullum ina kara samun ci gaba.

    Sai da ya samu nutsuwa muka yi wanka na gasa kaina sosai mun kwanta again yana Sa min Albarka yana jin dadi yace lallai yan matana yanzu ana ta girma kullum, tnx alot My Queen,jikinsa na shige nace ni ba wani sabawa karka kala min ina yar yarinyata.dariya yayi tare da kara kankameni yana shafa min gashina zuwa gadon baya na yace muyi bacci sai gobe kuma zanga wanne salon za a nuna min naji na yau ya hadu kin ba da style,dukan wasa na masa ina jin kunya na kara boye fuskata a kirjinsa ina dariya kasa kasa,wata Kalma na rada masa a kunne wacce saura kadan ayi second round da kyar na lallasheshi yace to ki daina kunna ni,nace kyis na kasheka to,Dariya mukayi gaba daya hannayensa suna saman Mazaunai na yana shafasu cikin Salo iri iri wanda ni kaina hakan yana min dadi.

     Abbi ne kwance saman gadonsa  yana nazarin duniya tare da mamakin canjawar komai da ya samesu a rayuwa,gashi har sun lalace suna ramewa sunyi duhu sosai kamar basu ba,dama ance duk wanda ya saba da rike kudi yana shan wahala idan karayar arziki ta sameshi,kuma dama can taimakon su akayi talakawane gaba da baya, duk gashi har sun zama abin tausayi duniya ta juya musu baya,wai sune a wannan matsayi, Hajja ce ta shigo dakin Abbi tana fada mene amfanin kwanciyarka a gida da tsakar rana haka baza ku fita neman na kanku ba,kudin hannuna sun kare saura Naira dari kamata yayi ko yar dubu biyu ina rikewa a hannuna ni bana iya rayuwa ba kudi,Abbi shuru yayi bai ce mata komai ba Sabo da bakin ciki da me zasu ji, Hajja tace au dan Iskanci kana jina ina magana kamar kaga Kashi eyee,ni na daura muku talaucin idan kudin banza ne me yasa baku yi zuciya kunyi ba, Haba Hajja me nace miki kuma,ya kike so muyi kina gani karatun su Sabeer ma nema yake ya tsaya,ba komai bamu da komai sai bashi ma da muke ci ki dinga tausayinmu mana,idan ba sata kike so muyi ba me zamuyi miki? Hajja Hawaye ta share wai an ci mata mutunci,ta fice fuuuu ta bar Abbi yana bakin ciki.
    Haneefa ce ta fito ta cikin yan uwanta Maza da mata tace to Jama'a ku kalli atamfar jikina ta gaji da wanki har ta kode tana neman jemewa,dama kayan namu kadan muka ebo,Meenal ce ta fado da gudu tace Bazan ji kunya ba bayin Allah nasan masu hankali ne gaba daya dan Allah me Pad always ta san min ko a min karo karo na kudi na siyo,Sajeeda tace ai duk dan kwalayen Ka kayana sun kare a kunzugu rannan,sai dai kiyi amfani da dankwali, Mujaheed da Khaleel suna dariya suka ce kadan kuka gani Yara tun yaushe muke cewa kuyi aure tun da gatanku samari na rubibinku kuka ki gashi na pad ma ya gagareku.

Meenal ta kalli Khaleel tace dan Allah bani gajeren wandon nan naka da naji zaka jefar naga cotton ne sosai zai sha ruwa a jikinsa,Khaleel yace ko kunya bakwa ji wai a gabanmu kuke irin wannan kalamai ba tarbiya ba komai sai kije yana cikin bakar jakar nan ki dauka,Meenal da Sauri taje ta dauki gajeren wandon Khaleel wani me nauyi cotton tasa reza tare da yankashi kashi Kashi ta linka kamar dai Pad haka ta dinga sawa tana kunzugu dashi.
   
   Matayen su Abbi talauci ne ya ishesu gaba daya suka ga gwara su tafi gida tunda yanzu ko sabulun wanka da wanki Rasawa akeyi a gidan,Nan suka tayar da rigima sai an sakesu,Umman Ameer tace ita dama tana jin Haushi an rabata da Danta Ameer ta gaji,Hajja tace ba shegiyar da za a saki kamar yanda akaci daula dasu dole Asha wahala dasu dama in sun koma dangin nasu ma dai talaucin zasu tarar Sabo da duk kanwar ja ce.

   Yaji sukayi wai sun tafi gida sai sun huta zasu dawo,Yaran gida suka ce sama dawo idan sunji Wahala kar wanda ya hanasu,suna shiryawa suka ce mu munyi gaba,Su Mujaheed suka ce a dawo lfy Allah ya kiyaye Hanya,tuna ninsu yaran zasu damu sai suka ga kowa harkar gabansa yake,Sabeer yace mu ai Aayan da Daddy kadai ne zasu ce zasu yi yaji zuwa turai mu damu Amma kawai ba abinda ake tsinana mana ace za a damemu,common toothpaste mu muke siya,sabulun wanka da wanki ba a san a bamu ba,Abbi yace Kai rufe mana baki marasa kunya,Sajeeda tace ai wlh sai daí a godewa Allah Amma ya dace ace a cikinmu akwai Karuwai,akwai yan shaye shaye tare da kasurguman barayi sabo da Halin da muke ciki a gidan nan,kowa kansa ya sani kowa ta kansa yakeyi,Hajja tace ai duniya ce yanzu ma kofa a bude take zaku iya komawa Karuwanci da shaye shaye,sace sace kuwa na wanda kuka gani shi zaku dauka dan ni nawa yafi karfinku?, Abbi Sani yace Haba Hajja addua ai zaki yi musu ba kice suje suyi ba ai yarane yanzu idan  mune zaki so yaranki su dawo haka?.
     Kai Sani ka rufe min baki shegen kunne kamar malafar Kwadi,Dariya aka dauka gaba daya har yaran Sabo da kunnen Abbi Sani kamar Malafa haka suke kuwa,Abbi Mustapha ne ya buga musu tsawa,shima Abbi babba yace zaku bar palon nan yan Bantan uban Yara.

     Khaleel ne yake ta masifa a tsakar gida an sace masa sabulun wanki wanda da kyar ya hada kudin ya siyo na wanki dan Naira Hamsim wani kato zai dinga cancanawa yana wanka dashi,daga ajiyewa ya juya baya zai dauko bokiti kafin ya dawo har an dauke sabulun yan mintuna kadan,Nan ya fara fakon wanda ya dauka duk wanda ya shiga wanka ko me wanki sai ya duba sabulunsa mata da Maza,Meenal tana fitowa daga wanka ya ganshi a hannunta ashe ita ta sace ta wanke panties dinta tunda period take dole sai da wanka da wanki,Kamar zai cinyeta haka ya kwace abinsa,dan ya bar mata tace kazanta ta na wanke dashi fa period ne duk na shafa masa na wanke da kyar ake gane kalar sabulun dazu wlh dan baka gani ba yanda ya rine kamar jar color aka Sa,abin kyankyami har wari yakeyi, Khaleel ya gano so take ya bar mata shi du, yace ai ko a Abbatuwa mayankan dabbobi aka jefa shi cikin kogin jini bani abina dan Uwarki mayya wlh idan na kara ajiye abina kika dauka sai kin gane kurenki,Meenal tace jaraba akan sabulun wankin?Yace ae din,to yi hakuri dan Allah ka bani na karasa wanke daya pant din nawa yanzu na tuna ban gama ba kaima kasan sanda muna daula bakwa sanin ma time din da muke period yanzun ma babu ce tasa ba yanda zamuyi dole muke yage yar kunyar.
    Khaleel yace ungo badan halinki ba dan dai kawai kina san min Vaseline dinki ne Allah gashi nan saura ki karar dashi,Na gode cewar Meenal ta koma toilet ta gama ta fito ta bashi sabulunsa,Mujaheed ma da shi yayi wanka haka mata da mazan kaf ba yanda Khaleel ya iya haka kowa ke zuwa yana rokarsa dashi sukayi wanka,Abbi ma yace kai Khaleel bani sabulun sodar nan naka zan cude jikina dashi ina so na fita neman Ameer ruwa a jallo dan ubansa ya zai manta da iyayensa,Khaleel yace kune fa kuka koreshi ai ni ya birgeni wlh,gashi sabulun dan Allah nasan wankanka dadewa kakeyi karka silleshi Abbi.

Harara Abbi ya zuba masa ya wuce yayi wanka sannan ya kwalawa Meenal kira tana zuwa yace Bani Toothpaste naji ance kece me shi a gidan nan,Meenal tace Vaseline gareni  ni Katon gaske wlh ko wanka zaka yi dashi ina dashi kamar tulu yake Sabo da girma saurayina nasa ya kawo min shi maganin gidan yawa,Meenal Me Vaseline kenan,Abbi yace dauko min shi na shafa,wace to me abin goge baki?Haneefa ce me su manya manya ita take matsowa kowa da kanta duk yanda kuke da ita sai daí ta Matsa ma da kanta kar ya kare da wuri,Abbi yace kirawota ta bani,Tunanin Abbi ai shi Babbane Haneefa zata bashi ya matsa da kansa yanda yake so sai kuwa yaga tace kawo Brush din,da mamaki ya kalleta ta kuwa bude ta dan difara masa kadan tare da cewa kar ka raina Abbi rayuwar sai da tattali,Hajja ma tazo tace Haneefa ashe kece me makilin matso min a nan na goge bakina,Haneefa tace  rayuwa sai Imani Hajja ku tsofaffi har wani goge hakora kukeyi idan ba iyayi ba da ganin arahar Sa me zaki goge hakora kamar Tsinken tsire duk sun zube saura dai daiku kici goronki shima yana wanke muku baki tayi tafiyarta,Hajja tace ni me na tare musu da aka rainani,ta fara kiran Khaleel sai da yazo jikinsa ba riga, tace wai kai kullum baza ka Sa riga ba kai kenan daga dogon wando sai gajere,Khaleel yace Am too sexy ne Hajja wlh shi yasa nake nuna muku baiwa ya fada yana dariya,Hajja tace ina wata baiwa a nan Da Ameer dina ne ya fada sai na yarda dalla bani sabulu na wanke jikina, Khaleel yace Rayuwa sai Imani Hajja wa zaki wa wanka ke ba miji ba,yo ko miji gareki me zai ci da ke ki sha zamanki haka da Allah wannan Asarar sabulu zaki mana,Hajja ta balbale shi da masifa ko wanne dan iska bani da iko nayi magana sai yace wani Rayuwa sai Imani wata sara kuka samo kuma ko kuwa ni kuka raina.

    Khaleel dai yayi tafiyarsa,Mujaheed ne yazo ya wuce Hajja shima ba Riga sai 3qtr ya tattaro hantsar Wando ya rike gaba daya yana tattalewa yana tafiyar yan gayun samari ga uwar suma duk ta cukurkude,Hajja tace haka dai aka iya yan iskan Yara ayi aure tun tuni kuka ki yi sai aikin rike hantsar Wando Sabo da jarabarbu ne ku mayun mata,Hajja bata san gayu bane ta dauka sha'awa ce ko Iskanci ne ke damunsu,Mujaheed yana Jinta yace Hajja sai Imani ai ko Ya kika ce,Tsaki ta ja tare da tauna 
Goronta,Sabeer da Aliyu ne wanda sun kai 24yrs yanzu su kuma boxers ne dan karami suka Sa da yar Singlet ga abar tasu nan a Wando ana gani duk ta mike da wata yar kwarababbiyar waya karama a hannusu suna dannawa suna kallon pics din yan matan turawa kusan tsirara suke,Hajja nan ma ta rasa uwar da suke sai kus kus suke suna dariya suna kallon waya,ta kalli wandonsu a ranta tace na shigesu ni Hajja kar fa a fara cikin shege a gidan nan ayi yar gida tunda ga yan mata nan kuma ba muhararram juna bane wasu to matan ma ya suke bare Maza,Ganin Hajja na Sa musu Ido Sabeer yace Allah wadaran karamin gida sanda muna gidanmu babba wa yasan me wani yakeyi Amma yanzu komai kayi akan idon wani,Aliyu yace muyi maganinta suka samu Hajja tare da cewa Hajja kinga wasu dan Allah sun hadu? Nan Hajja ta kalli waya ai sai taga Mata kusan tsirara,Sabeer yace wannan zan aura Hajja tayi? Duka Hajja ta rufeshi dashi tare da cewa wlh in dai ina raye baka Isa ka auri wannan ba,Aliyu yace musulma ce sunanta Rasheeda,Hajja ta dauka da gaske ne ta dinga tsine tsine ba a Isa ba,kuma tace sai ta fadawa su Abbi,Sabeer yace Hajja masu kudi ne fa yar gidan shugaban kasar Ethiopia ce fa kinga mun washe,sabo da son kudi Hajja sai tace ya sunanta kace? Yace Rasheeda,Hajja tace ayyo yanzu naji zance ai tun daga sunan ma kasan musulma ce,a ina kuka hadu a Internet din naku?Sabeer yace ae tace kwanan zata zo ma kuma zata Aiko min da yar million goma na sha ruwa,kirji Hajja ta dafe tare da cewa kace ina gaisheta kakarka Hajja sunana,yaro kayi dabara wlh kafi su Khaleel hankali ina kallonku yara ashe kune manyan,Aliyu yace Hajja kinji tana kira ma a waya kash Amma bamu da kudin Sa kati kuma dole sai da kati so muke mu tura mata accnt Number tace Sauri take zata turo kudin gashi bamu da sisi,Hajja da Sauri tace zan baku rance ina jin kamar Ina da dubu biyu a hannuna nawa ne Katin da zai isa? Sabeer yace tab ai sai dubu biyar yanzu kuma babu sai daí ayi asarar milliyan goma kenan Hajja ki taimaka idan ta turo zamu baki milliyan Uku a ciki kyauta,Hajja dadi ya rufeta tsohuwa da son kudi nan tace to  dama dubu shida ce ta ragemin a duniya ga biyar sai na rike daya ni kuma,Nan Hajja ta zaro dubu shida a jikinta wanda da haka kawai ne sai daí a mutu a gidan baza ta iya siyan ko sabulu ba.

   Sabeer suka karbe dubu biyar da Sauri suka dauki dubu daya daya,dubu Uku kuma suka siyowa kowa na gidan sabulun wanka da wanki,suka bawa matan kudin kitso,mazan kuma na aski,har pad aka siyawa matan kowacce biyu biyu Sabeer yace gashi naga Alama boxers dinmu an fara sace mana ana kunzugu dasu, har da Sauran dan abinda ba a rasa ba duk sun dan siya me araha,karshe dai Sabeer dari biyu biyu ce ta rage musu,Duk yaran gidan sunji wayon dasu Sabeer suka hadawa Hajja sai dariya akeyi a boye kowa ya washe yau a gidan har kifi soyayye suka Dora a saman shinkafa da wake kowa daya,su Abbi da Hajja basu san me akeyi ba,dama matayen su Abbi sunyi yaji su Haneefa ke girki duk da basu wani iya ba wahala tasa har sun saba.
    Kwana biyu Hajja taga su Aliyu shuru ba 5k dinta ba milliyan Uku sai nemansu take Amma sunki yarda ma su hadu wasan buya sukeyi.Idan taje dakinsu sai su Khaleel su boyesu kowa yace basa nan sun fita,Hajja ta koma me gadin dole a Palo take kwana wai zata ga wucewar Aliyu ko Sabeer amma sai su wuce ma bata ganesu ba.

   Washe gari da Safe ma sai da Aayan ya kwashi Harka ba daga kafa kamar ma baya tausayina, kamar yanda su Meenat suka saba haka sukayi komai girki da gyaran gidan su ma yan aiki suna nasu,sai 11am muka fito bayan Aayan ya shirya ni yayi min komai,ba su Meenat gidan shuru sai guntuwar paper na gani sun ajiye min,.......wai mun tafi gidan Ammah tare da Ameer sai dare.
     Aayan yace ina suka je? Gidan Ammah na bashi amsa a takaice, da kansa yayi Feeding dina muna hira sama sama yana tsokanata wai jiya naji dadi na fara sabawa,na fara Kukan shagwaba ina Ni ba wani dadi,yana mun dariya har muka gama,yace je ki shirya muje gidan Ammah sauri ya furta ba alamar wasa,da Sauri na tashi na je sama nasha wata dakakkiyar shadda yar Senegal tasha aiki Dark purple aikin kuma da light blue and pink na fito kamar wata Hajiya,Shi kuma shadda Light blue kamar munyi ango sosai muka yi kyau.

    Jerawa mukayi wow yau abin kallo ne mu, nace muje wajen Daddy mu gaisa,Daddy ba karamin farin ciki yayi ba da ya ganmu haka sai albarka yake sa mana sannan yace mu gaishe da Ammah, yau ba Driver bane zai tuka mu kuma ba escourt mu biyu kawai,da kansa ya zagaya tare da bude min gaban motar yace ranki ya dade Allah ya taimakeki shiga,Kafadarsa na dan buga kadan ina dariya na shiga ya rufe sannan shima ya zaga ya shiga yaja motar cike da nutsuwa muka bar gidan,Ba wani nisa me yawa bane sai gamu a wani gida dan babba me kyau sosai yayi kyau gaskiya,me gadi ne ya bude mana gate ya Cinna hancin motar Sa cikin gidan,gidan yasha tiles da flowers yayi kyau sosai,jikin wata katuwar Bishiya muka hango su Meenat tare da Ammah zaune a katuwar tabarma suna hutawa,Ameer da Yarima suna gefe suma,Hajja da Katon tire a gabanta tana kwada musu zogale da Kuli yaji hadi sai nishadi sukeyi abinsu.

    Aayan ya kalleni yaga ina murmushi ni kadai ina ta kallon Ammah muryarsa naji yace muje ko? Da sauri na dawo hayyacina na daure fuska irin ba dadi naji ba,murmushi yayi yace kinfi kyau a haka muje dama naji jiya Ammah tace duk tafi so taga kina fushi dariya kike bata,da Sauri na washe bakina nace na fasa fushin tunda tana so,na fito ina ta fara'a ina murmushi wai Ammah ta gani kar taji dadi ma,Aayan yana ta dariya a ransa,a hanya yace Ammah tace tana so taga kina fushi kinki gaisheta,nace aiko sai na gaisheta din,Aayan yace ke duk abinda bata so shi zakiyi ko? To ki daure dan Allah ki nutsu tana son ta ganki a nutse cib dake,Nace haka tace?Yace ae,na girgiza kai nace za a gani wlh Bazan nutsu ba sai na koma kamar bera wasa zan tayi ba nutsuwa.Aayan yana ta dariya mugunta yake hada min.
    Muna karasawa mukayi sallama kowa Murna yake yi nazo na huce,a kunne ya rada min tace ita bata son a durkusa mata da Sauri na durkusa nace ina yini Ammah kuna lfy ya gida ya aiki?irin na bata haushi bata so a gaisheta,sai naga tana ta murna ta Amsa da fara'a harda Sa min Albarka,ni kuma sai yashe baki nake ina fara'a wai ance tana son nayi fushi shine bazanyi ba ni fara'a zanyi,har hannu nake sawa ina kara bude bakina sosai,Aayan yana ta dariya a boye,shima cike da ladabi ya gaishe da Ammah ta amsa da sakin fuska suna hira sama sama,tunowa nayi ance tana son ta ganni a nutse to Bazan nutsu ba,Sai mutsu mutsu nakeyi muna hira da Ameer tare dasu Ma'eesha duk nafi kowa surutu,dan karma ace na nutsu nace Ma'eesha jibi akwai schl kema kin sani ki tabbatar kin mana wanki da guga na furta da masifa kuma da sauri irin ba nutsuwa,Ammah hirarsu sukeyi tare da Aayan da Yarima,Na dauko wayata ina dannawa,na mike na dauko wata kujera fara naki Zama waje daya naki yin shuru kar wai ace ma ina da nutsuwa, ita kuwa Ammah dadi take ta ta ji tana kallona irin na saki jikina a gidanta sai harkata nake yi,Meenat ma da sauran haka suna ta kin dadi.
   Aayan ya zo gefena ya rada min Ammah fa bata so a shigar mata Palo da Bedroom shi yasa tunda taji na mata waya zamu zo sai ta zauna a nan wajen sabo da kar ki je mata dakinta.
   Da gaske kake?yace ina miki karya ne ki kiyaye abinda zai bata mata rai zamu fita da Yarima zan dawo anjima mu tafi, Yarima tashi muje,Yarima yace Madam yau an manta damu? Sai lokacin na tuna bamu gaisa ba da sauri na gaishe shi ina bashi hakuri suka fice daga gidan a motar Yarima.

   Na tuna Ammah bata so a shigar mata Palo da dakinta kawai na tafi na shige can ciki ina ganin haduwar gidan da furniture din gaba daya,Ina haka naji Muryar Ammah a bayana tace Mufeeda ta wai kamar ba ke ba? Tausayi ta bani kawai naje na rungumeta harda hawayen farin ciki,nace kiyi hakuri Ammah kece nan kika yi mana haka me yasa haka? Kin samu kuka da damuwa,kuyi hakuri haka Allah ya tsara da ace banyi hakan ba baza ki taba yarda da auren nan ba,yanzu gashi kina zamanki da mijinki,nasan halinki Mufeeda kamar yunwar cikina,ko kin yarda anyi auren baza ki zauna ba matukar kin San inda zaki ganni,kuma cewa zakiyi sai kin kula dani,zaki dinga dorawa mijinki nauyi yayi tunanin baki da tarbiya,kuma ai gaskiya ce har fa auren kasuwanci kikayi da ina raye yana hanaki kudin zaki barshi,haka kuma akan kudi nasanki ba mutunci,har auren Kasuwanci kika yarda kika yi,shi yasa yana fada min kin yarda da auren kasuwanci nasan kawai son kudin naki yayi yawa shi yasa kawai nace ace miki na rasu naga yanda kudin zasu amfaneki,nayi tunanin tun daga Ranar zakiyi nadama Ashe sai kika ci gaba da son kudin ki dole sai kin ci kudinsa,yanzu ba gashi Mufeeda na ta Zama Babba ba,ta girma,tayi hankali,da mijinta,tana zamanta lfy,tana karatu,ba ruwanta da harkar son kudi rayuwarki ta gyaru Alhmdllh.

   Tafiyar da nayi nace ace muku na rasu nan ma ba iya akan kanki bane akwai wani abu a kasa amma zan fada muku sai lokaci yayi zaku sani insha'allah,Yanzu Aayan ya sanar dani rashin lafiyar babansa akwai wani me maganin gargajiya can kauyenmu Insha'allah wani satin zamuje a kaishi ko za a dace,Allah ya kaimu nace Ammah wai Allah yanzu kece? Na furta ina shafa jikin Ammah,tana dariya tace nice ko kin tuna sanda kike kaini toilet ki dauko ni? Sannu Ammah kinji kinga yanda kika kara kyau da haske Ashe kema fara ce Ammah amma da kinyi duhu, bedroom muka kule da Ammah ta bani labari kaf tun daga yanda Aayan da Yarima sukayi ta dawainiya da ita a turai,Aayan ya kashe mata kudi,yanda ya dauketa kamar Uwarsa yake kula da ita kullum sai sunyi waya ba fashi,gashi komai akan lokaci,abinda Aayan yayiwa Ammah ko uwarsa ce abinda zai mata kenan,Ammah ta fada min irin jin dadin rayuwar da ta shiga a turai,tunda naji haka Aayan ya kara shiga raina,na kara bashi wani matsayi na daban,sonsa da kaunarsa ya kara mamayeni,nan take na fara kukan dadi nace Ammah Allah ya taimakeni ban taba wulakanta mijina ba,shi yasa ake son ko yaushe kayi me kyau,da yanzu kunyarsa zanji,Murmushi Ammah tayi na manya tace abinda naji irin son da kike masa har muna waya ina jiyo muryarki wai wace? Macece?kyakyawa ce? Dariya nayi tare da rufe Idona da tafukan hannuna,Mufeeda an girma,nima na zauna na bata labarin kaf bayan rabuwarmu wanda su Meenat basu bata ba na sanar mata,tace Allah ne yake tsare min Ku Allah yaga halin da muke ciki kuma yaga zuciyar kowa,sai mu kara dagewa da addua,yini mukayi muna ta hira da Ammah ba ji ba gani ina kwance a cinyarta muna labari,tana kara koya min yanda zan kula da mijina da gyaran jiki,Wasu magungunan tsumi data hada min ta bani katuwar leda guda da yanda zanyi amfani dasu,tace ga akwatunan lefanki can ki tambayi Meenat suna dakinsu guda goma sha biyar mijinki yayi miki a wajena ya hadasu can turai ni na hana a baki wancan lokacin sabo da baki hankali ba,yanzu kuma ya hada komai ya barsu wajena,akwati biyu kuma tsarabarki ce ni na siyo miki,Sauran kuma guda hudu nasu Meenat ne nayi musu baya min komai na nuna musu,Ammah to kayanki na gani cikin Sip na sawa ga wasu a akwatuna yaushe kika dinka? Aikin Mijinki ne gaba daya tare da Yarima.
   Ammah Yarima fa Ma'eesha yake so,ae na sani ai ya fada min rannan ma babarshi tazo wajena mun dade da ita mutanen kirki ne ai,yanzu Ammah Meenat ce kadai ta rage,dariya tayi tace tun yaushe Mijinki yace min yayi mata miji wai shi ya samo mata ban san dai waye ba,Nace ni gaskiya a'a wlh Ameer zan bawa ita sun dace kuma baki ga taimakon da yake mana ba,to Aayan ya rigaki zabin Aayan zata aura Insha'allah cewar Ammah,kamata yayi ma su dawo gida wajena Mufeeda kinga an takurawa mijinki bazai sake ba,kai Ammah ni ki bar min su dan Allah,Bakya gane me nake nufi Mufeeda sabo dake fa nake komai da bakya min musu duk abinda nace shi kike yi me yasa kike haka yanzu?kiyi hakuri su dawo zaki gane me nake nufi,to shike nan Yaushe kike so? Yanzu suje su kwaso kayansu idan nace gobe kuka zakiyi in zasuyi miki Sallama gwara kina nan gidan,Nan take kuwa suka tafi da Ameer suka kwaso nasu ya nasu tas har akwatunan da Ammah ta ciko musu da kaya,na gani kaya masu kyau da tsada duk gasu nan iri iri,nawa kuma an bar min su a gidana.

    Aayan ne ya basu Driver guda da mota dalleliya ta gaske za a dinga kai su Meenat schl da kuma unguwa har Ammah.
   Su Meenat ne sukayi Dinner Ameer yace dama shima a barshi a gidan Ammah da yafiye masa,nace ai kuwa baka isa ba sai dai ka dinga zuwa kullum,Bayan munyi sallar Isha Ammah tace bana son shaye shayen maganin matan nan barkatai,wanda na baki sun isa ni na hada da kaina da yayan itatuwa,zan koya miki wasu ki kiyaye kinji,nace to,Dauko ki fara shan wasu yanzu ko period kikeyi cike da kunya nace a'a,ta bani wasu nasha tace nayi matsi da wasu duk nayi ina zaune muka ci abinci da komai,ba na so ma na koma gida nafi so na kwana wurin Ammah muyi ta hira ina jin dadi,nace Ammah Abbanmu fa?, Nan take Ammah ta bata rai karki kara yi min zancensa,gidan nan kuma da kike gani na sa an siyar dashi na kai kudin wajen danginsa dama shike nan abinda ya mallaka tare da yan uwansa mukayi shawara,Ammah idan ya mutu fa ya Zama gado fa? Nan gaba zan muku baya ni karku damu,nace to ba damuwa.

    8:30pm sai ga Aayan ya shigo da Sallama idonsa na kaina, yace Ammah Yarima yace bazai samu Damar shigowa ba sai gobe zai zo,ba damuwa ai yana kokari ma kullum sai yazo,Aayan ya kalleni yaga ina jikin  Ammah a kwance nayi rashe rashe ina danna waya,tashi mu tafi gida,Baki na turo gaba ina shagwaba nace anan zan kwana ni sai nayi kwana uku zan dawo,Su Ma'eesha duk sakin baki sukayi suna kallon irin yanda nake kashe murya,Ammah tace tashi ke ku tafi bana son shashanci shi yasa nasan da ina kasar nan zaman auren ma gagararki zaiyi gashi daga dawo wata zaki fara,Ameer kuwa shima tuni ya tafi gida yace sai gobe.

   Aayan na kalla nace dan Allah fa nace sai gobe to ka dawo mu tafi,Har gida Ammah tazo yanda zaki ganta kika ki yarda sai yanzu zaki ce wani kaza kaza,tashi mu tafi kin ma san bazan iya kyaleki ba,Ammah tace ka daina bata bakinka tasar min a cinya ku tafi, gani Ammah tayi ina bata lokaci tace Meenat kuje Ku kwanta suka tashi suka wuce tare da ce min sis sai da safe zamu zo,Na Galla musu Harara nace dalla...dalla..dalla kuje can ku rufe min baki,ance muku bazan iya zama ni kadai ba ko aikin nawa bazan iya ba na gida,Dariya sukayi suka wuce suna yiwa Aayan sai da safe.
    Ammah ma tureni tayi daga jikinta ta shige dakinta sukayi Sallama da Aayan tace ka rufe mana kofar,Daukan kayan da Ammah ta bani yayi tare da mayafina ,jakata da takalmina har dankwalina,cikin mota ya kaisu ya dawo ya daukeni cancak tare da cewa zaki san kin min musu yau Allah ya kaimu gida,ina magana kina min musu ko,nace wayyo na tuba Allah ni na isa,wlh wasa nakeyi na tuba pls My Man bazan kara ba,yace ai kin jawowa kanki yau.
  Kin san dai Bana son ina magana ana min musu dan kinga Ammah na wajen ko? Da sauri nace a'a am so sorry bazan kara ba.

KASUWANCI NA





           111-112





Official





By

AsmaBaffa



    AUNTY SUMEE and NAFI ga page nakune an kara muku.



    KASUWANCI NA FANS ina godiya da Jinjina gareku,masu Sharhi kuna birgeni sosai.???



Gaban mota Aayan ya bude tare da sani a hankali ya gyara min Zama tare da rufewa,komawa yayi ya shiga shima sannan ya figi mota muka bar gidan,sai da yayi mana take Away na kayan lashe lashe sannan muka nufi gida,Allah sarki Ameer yau ba abokan hirar tasa duk gidan sai yaji ba dadi,sai yanzu ya tuno da yan uwansa Frnds dinsa Su Mujaheed,Ummansa ya tuna tare dasu Abbi amma me zai musu tunda sune suka koreshi da kansu,Muna dawowa ni na kwashi wasu kayan shima ya dauka muka shiga ciki,a Bedroom muka ajiye komai muryarsa naji yace tashi muyi wanka,kunya nakeji amma haka na dan daure muka cire kayan mu tare da daura Towel, Aayan so yake kawai ya fisge towel dina ni kuma naki yarda,sai da ya shammace ni ya fisgo dan towel din Allah yasa na rike kam ina kallonsa ta gefen Ido,Dariya nayi nace woo ai ina kallonka dai, da gudu na matsa ya biyoni dole sai ya cire min Towel dariya mukeyi gaba daya har muka shige Toilet,Wanka mukayi tare kusan ma ni nayi masa komai sannan muka fito,bayan mun shirya tsaf damu Nafeela zamu fara nace tsaya a bawa Ameer takeaway dinsa shima kar yayi bacci,kyaleshi yanzu ma maybe yayi bacci kuma yaci abinci gidan Ammah.



   A'a amma ai alhakinsa a kanmu yake tunda kai kake masa komai ko bazai ci ba a bashi shima,kawo na kai masa cewar Aayan,ko da yaje ma Ameer dama yunwa yake ji a gidan Ammah bai tsaya yaci abincin ba,tnx yace Aayan ya dawo mukayi Nafeela raka'a biyu sannan muma muka ci kadan Namu sabo da a koshe muke, nayi mamaki yau da Aayan ya kyaleni naji yace naga kin gaji ne, ganin na gaji Tausa ma ya shiga yi min ina lumshe ido kawai bacci me dadi ya kwashe ni,shima bai San sanda ya fara baccin ba, Da Asuba ni fara farkawa da sauri nayi wanka tare da brush sabo da naji na fara period,sai da na fito bayan na shirya kaina na tashi Aayan yayi shima wanka da komai ya fito yayi Sallah tare da azkhar nima duk da banyi sallar ba nayi azkhar dina,Juyowa yayi yana kallona tare da cewa Period kike kuma? Nace ae da Asuba na fara,na ma yi tunanin kin samu ciki,nace wanne ciki tun yanzu ai yayi sauri,Murmushi yayi tare da cewa ba wani sauri a rana daya ma zaki iya samu,yanzu ya zakiyi dani sai da na kyaleki jiya kika huta na gama tanadin yau da safe sai kuma ki wani fara period naji haushi ya karasa kamar wata mace tana shagwaba,dariya na shiga yi sabo da ya bani dariya maganar tasa,na kalleshi cike da so shima haka nace sai dai kazo muyi Romancing zansa kaji dadi Allah sai ma yafi wanda kake so,bazai fi wanda nake bukata ba ke kin San dadin dayan kuwa,Yana saman Sallaya a zaune na koma tare da sakalo da hannayena ta wuyansa na kwanta a bayansa,Ajiyar zuciya ya saki,fuskata tana a wuyansa ina goga masa,Saman bed ya daurani ya shiga murzani cike da kwarewa nima haka ba abinda Bana yi masa har wanda ma ban taba yi masa ba duk yau na dage nayi masa sai da na zautar dashi,Sucking na masa last a nan kuma yace yama fi komai sweet,sai Santi yakeyi ya rude gaba daya,Sai da nasa ya samu nutsuwa kwarai da gaske yana ta jin dadi yana sa min albarka tare da zafafan kalamai.

 

    Ina kwance a jikinsa muna hutawa na manna masa kiss a wuya nace na gode My Man ban ma san da me zan fara gode maka ba,ka gama min komai,abinda kayiwa Ammah,dangina,yan Uwa da duk Wanda ya shafeni bare kuma ni kaina,ban san me zance ba kafi karfin godiya a wajena, shiiiii naji yace kin wuce haka a wajena kasa ganewa kikayi lokacin ta kasuwancinki kikeyi,Dariya nayi nace Allah ba wani nan,ai kaima ba so na kakeyi ba da,ni ai ba kece bana so ba aure ne Bana so a lokacin kinji nace bana Sonki?sai dai nace bana son aure kece baki gane ba,gashi kin canja min rayuwa da tsari kin kawo min farin ciki wanda na kasa samu,kin yarda kin zauna dani duk da cewa ina bata miki amma kinyi hakuri,d angina duk abinda suke miki kin iya jurewa ai Alhmdllh

   Addua kawai zamuyi Allah ya barmu tare Babyna,nace Insha'allah kuwa,dan Allah kayi ta sona kaji ni bana son ka kula kowa,ke zaki dage ai ki hanani kula kowa ta hanyar yin abinda ya dace ace matar aure ta gari tana yiwa mijinta shike nan.

     Yau banyi dogon baccin safe ba,da wuri na Mike na shiga kitchen na shirya breakfast sannan na gyara ciki ko ina,naje nayi wanka naci kwalliya cikin material black and red nayi kyau,sai kamshi nakeyi ina kitchen ina kokarin shirya Dining,naji Kamshin Aayan kafin nayi wani motsi naji ya rungumeni ta baya yana shinshina wuyana,abinda ko kitchen baya wani shigowa sai yau Ashe sabo da su Meenat ne baya shigowa sabo da kunyar idonsu ba komai zaiyi a gabansu ba,lallai Ammah ta iya gyara Harka na furta a zuciyata Ashe a fili nayi maganar,Murmushi yayi me Sauti yace kin ganki baki da kunya fa kema,Juyowa na nayi tare da boye fuskata a kirjinsa,nace Saura Ameer ma,Baki ya tabe yace ai Ameer ba ruwansa shi har ya canja part jiya in baki sani ba yana daya part din tare da Daddy wai yace Meenat basa nan me zaiyi,Amma ya bani aiki abincinfa sai na kai har can da yar tafiya fa,ga mata nan a gidan ma'aikata nace ya zabi guda ta dinga masa,Amma yau dashi fa nayi ka kirashi a waya yaci a nan,Aayan yace zancen kike so Ameer wai danki ne ko yaro ne shi da kike damun kanki ai ni kadai zakiyiwa wannan.

   Shike nan muje to tare dashi muka shirya komai a Dining, cup din tea dinmu daya,plate na farfesu tare dasu chips duk daya ne tare muka ciyar da juna.a Binda nakeyi wajen kula da Ameer da Daddy ba karamin birge Aayan nakeyi ba,hakan yana sawa ya kara so na Sabo da yanda wasu matan ke wulakanta dangi da iyayen mijinsu,ko kuma miji yana rike wata ko wani a wajensa abinci ma idan bai ce a bashi ba baza a kula shi ba,ko a dinga takura musu ga aike komai na wahala su za a Sa,bare miji yazo dasu nama tare da kayan dadi irin su gashashiyar kaza,yogourt etc wanda ake rikewa a gidan bazai ji ko kamshi ba sai dai idan danginta ne wannan su za a basu,amma sai gashi ni dole duk abinda zamu ci sai na bawa Ameer nasa duk da cewa Saurayin matashi ne,nasan zai iya siya ma yaci a waje tunda da kudinsa,Daddy ma dan kalar abincinsa daban ne,kuma na turawa yake ci,masu dafa masa daban suke.

   Aayan ne ya kalleni tare da cewa  yau zanje Office Amma bazan dade ba da wuri zan dawo,Shagwaba na fara masa dan Allah ka tafi dani kaji,ki zauna anjima su Meenat zasu zo miki fa,Ameer zai kawo miki su munyi waya da Ammah,baki na turo nace ai ni na tsanesu yanzu,haushinsu nakeji gaba daya.

    Dariya yayi yace ke fa kika ce Ammah ta iya gyara Harka yanzu kuma kina jin haushinsu ina son ranar da zanga Mufeeda tayi hankali ta daina kuruciya,wai shekarunki nawa? 18 fa nake yanzu,dole kiyi yan mata,kai fa? Dariya yayi yace kin girmeni ai,nace lallai Ashe saurin girma kayi amma dai nasan ka girmeni dan Allah shekararka nawa? Yace 20, dariya na dinga yi nace Ashe ma kusan sa'a na ne ai da kadan ka girmeni,gaskiya kayi mugun saurin girma na shafa sajensa da gemu nace harda gemu na kyalkyale da dariya,shi kanshi dariya na bashi taya zan kalleshi na yarda 20yrs yake inba kuruciya ba.



    Nace to muyi goyo goyo dama ni ina yarinya banyi wasanni ba sabo da neman kudi kullum a business nake kaga yanzu sai nayi kara'i tunda mate ne kusan ni da kai,Wai kasuwancin nan naki me Dame kike siyarwa? Dariya nayi nace komai,nan na fara masa lissafin irin abubuwan da na siyar,da komai da komai har lokacin dana fara ganinsa na dawo daga kasuwa,da irin Algus din danayi ina zubawa kosai garrin kwaki da jar color a ganshi sutu sutu jajir sai ace yasha kayan miya?da wahalar da muka Sha har lokacin da yake yawan ganina gidajen yan siyasa,Sai ga Aayan yana hawaye wai na tausayi,ni kaina dana tuna abin sai danayi kwalla,tun daga farkon rayuwarmu na bashi labarin komai, dariyar karfin Hali nayi nace kalli kana kwalla kamar ba namiji ba,da sauri ya goge tare da cewa tausayi kuka bani,amma gaskiya an raina miki hankali ma da muke cewa kina da son kudi, jikinsa ya jawoni na kwanta yana rada min words masu sanyi da kwantar da hankali yace I love u ,love u more My Man,bana son fita ma ina da meeting ne ba yanda zanyi,nace never mind zan iya zama, yace Ok harda tsokanata wai idan na tafi ki cinye abincin nan du tunda bakya iya cin abincin a gabana,dariya nayi nace ka tuna cin abincina a gidanka farko daka sace ni? Dariya yayi shima yace ai naga yanzu kin daina wai dan Allah a lokacin nan kuma kalau kike?nace ras ma kayan dadi ne da ban saba ci ba kuma dama ni inada ci da yawa,lokacin idan naga kayan dadi ko cikina zai fashe sai na cinye,Dariya mukeyi,amma yanzu kin daina ci da yawa amma dai ba laifi akwai cin nan yana nan, ga iya cin abinci abinci a kitchen,sai azo ayi ta min yanga ashe kin gama koshi a tukunya, dariya na dingayi ina rufe fuska tare da cewa ashe ka sani? Ka kureni lallai kamar Aljani haka kake Allah,amma ai gwara naci na koshi ko? Murmushi yayi tare da tura hannunsa a rigata yana wasa da Boobs dina yace ai nafi so wannan su kara girma kullum su zauna a haka kar su rame, oya muje ki rakani zan wuce,Sai da ya kara brush tare da gyara wankansa sannan na rakashi har mota,nan ma a ciki haka muka dinga kissing din juna kamar baza mu rabu ba da kyar na kyaleshi ya tafi ina daga masa hannu.



    Ban dade da dawowa ciki ba na gyara upstair dinmu komai kamshi yake a gidan,sai ga su Meenat tare da Ameer sun shigo suna kwala min kira, fitowa nayi cike da murna nace Ina Ma'eesha kuma? Saloon zata je gobe akwai schl,Ameer ka gujeni yanzu gida daya amma su Meenat sun fini ganinka,Haba Anty ni na isa damuna tayi da waya tayi missing dinki nazo na kawota, mene a flask din nan? Ammah ce tace a kawo miki kunun gyada ne,Godiya nayi na karba tare da kaiwa kitchen,Meenat ta kalli Ameer bari na gano Dakinmu Allah sarki nayi missing dinsa,kyaji dashi cewar Ameer, abincinka fa Ameer tun safe baka nema ba,a gidan su Meenat nayi Breakfast fa Anty,nace lallai Ameer dakai ma za a hada baki a gujeni ka kyauta,dariya mukayi gaba daya, nace ban baka labari ba My Man fa ya min kayan lefe baka gansu ba sun hadu,Ameer yace ai Meenat ta bani labarinsu,munafuka har ta fesa maka? Dariya yake yace haba Anty Ba munafunci tayi ba.



   Magana nayi ba alamar wasa nace Ameer wai Aayan ya maka mata? Ameer yace ni din? Ban San zancen bama,nace to na rigashi ko yace ya baka mata kace na rigada nayi maka mata ni, Ameer dariya yayi yana tunanin wasa nake,nace wlh ba wasa nake ba,Anty wacece takin da kika Zaba to? Nace Meenat,ido ya zaro tare da cewa a'a gaskiya ai masifa zata ta yi min bakya ganin ta rainani gwara dai naji idan ta Ya Aayan tafi sai na karbeta Amma Meenat kina ganin yanda take iyayi tana ji da kanta,dariya nayi nace to ai kafi Meenat iyayi kai,i dan kuma bata sona fa? Nace a'a kai dai kace kawai Zabin Aayan kake so shine dan uwanka,Ameer yace haba dai ai wlh nafi son zabinki Anty,to ko Meenat dince baka so? Ni na Isa yanda take me kyau haka da tarbiya ai ta fiki kyau ma Anty sai yanzu na gane duk Meenat tafiku kyau,Dariya nayi nace karya kake kuma wannan a wajenka dai zaka ce amma a wajen Aayan nice gaba,haka Yarima kuma Ma'eesha ce,muna Hira sama sama sai ga Meenat ta fito tare da daukan uban wanka,da mamaki na kalleta nace dama kuna da kaya a gidan nan ne? Ina kuma kika samu gown haka? aro nayi cikin na lefenki,nace aiko baki isa ba koma ki cire tun ma kafin Mijina ya dawo ya ganta a jikinki ban masa kwalliya da ita ba,Dariya tayi tace to wasa nake da abata nazo a jaka ko Ya Ameer?yace kwarai yana daga kai da sauri kamar uwarsace na magana.



     Gefen Ameer ta zauna tare da masa magana kasa kasa ba a jin me suke cewa sai gani nayi sun Mike wai zamuje mu dawo,nace ina? Ammah ta sani fa gidan kawata, dama ba wajena kuka zo ba ashe,yanzu fa zamu dawo am serious,sai kun dawo to,suna fita sai ga kiran Aayan ya shigo wayata.

   Dagawa nayi fuskata dauke da murmushi na rangada Sallama cikin muryar da nasan ina zuke masa numfashi,zaki sa na dawo Sweet Heart,wannan murya me zaki haka ,Ya Office to,Yace alhmdllh,good kace da wuri zaka dawo amma shuru am missing u,Wani sanyi yaji a ransa yace 2pm zan gama  just wait for me I wl be thr,Fari nayi da Ido kamar yana kallona nace Allah ya kaimu,me zaka ci? Kin san me nake so just make something delicious for me Baby,alright Insha'allah zanyi,kiss ya sakar min ta waya nima na aika masa,ina kukan shagwabata can kasa kasa nace kaga su meenat sunzo sunyi tafiyarsu yawonsu gidan kawaye dama ba wajena suka zo ba kuma tsoro nake ji Daddy yayi nisa da part dinmu da sai naje wajensa muyi hira. Laifin Ameer ne bari na kirashi sannan ya kashe kamar kar mu rabu,nan take ya kira Ameer yana ta Masifa Lallai su dawo su tayani Zama kafin ya dawo,ko Minti 10 Meenat batayi a gidan kawarta ba ta fito Ameer ya dawo dasu yana bata labarin masifar da Aayan ke yi, suna dawowa na dinga musu dariya, kitchen na shiga na fara shiryawa Mijina abincin da nasan yafi so fiye da ko wanne.



     12am cikin dare Hajja ce ta fito direct dakin Mazan gidan ta shiga sabo da wai dole sai ta kama Aliyu da Sabeer,Suna ta bacci gasu nan birjik wasu a shimfida kasa wasu saman katifa,Sabeer yana bacci sai duka yaji a gadon bayansa,yana bude ido yaga Hajja ce sai ya kara shigewa bargo,Hajja ta girgiza shi amma yaki tashi sai ma maganganu da yake wai na mafarki,kan Aliyu ta koma ta fara tashinsa,Aliyu dama ba a tashinsa a bacci magagi ne dashi idan ya farka sai ya rufe mutum da duka kuma a bacci, yana farkawa ya rufe Hajja da duka gashi Namiji hannunsa Zafi ba shiri Hajja ta kwace da kyar ta bar dakin da dan gudunta,Abbi kwana uku kenan yana fita duk inda yasan zai ga Ameer da mutanen da zai tambaya amma babu labarinsa,yauma gwiwa ba kwari ya dawo gida ana Palo a zaune kowa da abinda yakeyi Abbi ya wuce a fusace ta palon ana masa sannu da zuwa ba wanda ya saurara ya kara gaba cikin Bedroom.



    Mujaheed ya bude sabuwar Rezarsa yana yanke farcensa tun kafin ya yanke yatsa daya sai ga Meenal tace idan ka gama dan Allah ka bani na yanke wani farce da ya taso min yaki cirewa, Aliyu yace idan kin gama ki bani nima na yanke nawa,Wata uwar Harara Mujaheed ya zabga musu tare da cewa jarabar gida ko Kashi ka taba sai wani yace ka San masa zai taba shima ba tunanin ma cuta ta shige ku ko ina da ita ku kawai a baku.

   Yana gama yankewa Sajeeda ta karbe ta gama ta mikawa Aliyu,Aliyu ma ya gama ya bawa Meenal,ta gama ta dan ajiyeta a gefen kujera sai ko yar karama Juwairiya ma ta dauke harda zuwa ta kyasta Ashana ta konata wai ta kashe cutar jiki duk kan rezar ya disashe ba kaifi amma haka ta yanke da kyar.
   Khaleel kuwa wanka yakeyi ana ta jiran botiki ya fito ya bayar amma yaki fitowa yan matan duk da daura kirji suna jiran botiki, yana fitowa ya kallesu wai sabulunsa ake jira haka da botiki,sabulun ma duk ya gama narkewa Saura kadan,Ba tambaya ba komai Haneefa ta fisge tare da lakeshi a jikin sosonta,Sabeer ya faki idonta ya fisge har soson nata dama sabulun yana manne jiki bazai fita ba,haka ya shige wankansa yayi da sosonta,Khaleel baki bude yake kallonsu yace wai Ku ina sabulun da aka siya ne shekaran jiya?kowa an bashi nasa fa,sukace to ga wanka ga wankin su Inner wears ya zamuyi duk karewa sukeyi sabo da wanki kasan dai mata ba irin maza bane,kuma wlh gidan nan satar sabulu akeyi da nawa dana Meenal sacewa akayi,Aliyu yana daga Toilet yace nima wlh ina ajiye nawa jiya kafin na je Palo na dawo an dauke kuma Dan masifa ka rasa waye,Abbi ne ya fito tare da cewa wa dauki toothpaste sabo wani karami MyMy a saman gado na? Kowa yace ba shi bane,yace wlh duk Wanda bai fito dashi ba sai na kai sunansa wajen Malami ya mutu kafin safiya,Ko cikinsa ya kumbura dam cikin dare yayi ta tsaga ihu sai ya fito dashi,yan iska barayi,to wlh ban haifi barawo ba,da mu zauna da barawo gwara ya mutu,na gaji da sace sace da akeyi a gidan nan,dan Bala'i ko Guba ce a gidan nan ka ajiye sai an sata,to ko a fito dashi ko gobe wanda ya dauka ya mutu,Dama Juwairiya ce Ashe ta sace bata fi 14yrs ba bata da wayo jin ance mutum zai mutu ko cikinsa ya kumbura sai ta faki Ido ta dakko tace bari na tayaka dubawa Abbi tana shiga dakin ta daga Haukarsa ta sa a ciki,Abbi ya yarda da yarinyar ai yara b
Reply


Messages In This Thread
*KASUWANCI NA* by ASMABAFFA - by Gimbiya - 03-26-2019, 10:44 AM
RE: *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA - by Gimbiya - 03-26-2019, 10:46 AM

Possibly Related Threads...
Thread Author Replies Views Last Post
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 4 120,151 02-22-2019, 08:04 AM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 7 60,141 01-20-2019, 01:58 PM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA Gimbiya 0 7,552 01-18-2019, 09:17 AM
Last Post: Gimbiya
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA 0 2,511 Less than 1 minute ago
Last Post:
  *KASUWANCI NA* by ASMABAFFA 0 3,072 Less than 1 minute ago
Last Post:



Users browsing this thread: 1 Guest(s)