Forums
Yadda na taba yin soyayya da kanwata Maryam a fim - Printable Version

+- Forums (http://contripeople.com)
+-- Forum: Retired Forums (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=78)
+--- Forum: Retired Forums. Please Make Your Post Within The 3 Forums In General Discussion (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=49)
+---- Forum: Hausa Language Forum (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=40)
+---- Thread: Yadda na taba yin soyayya da kanwata Maryam a fim (/showthread.php?tid=978)Yadda na taba yin soyayya da kanwata Maryam a fim - Gimbiya - 11-16-2017

Yadda na taba yin soyayya da kanwata Maryam a fim'
Jarumin fina-finan Hausa, Ramadan Booth, ya bayyana wa BBC abin da ya sa ya yi soyayya da kanwarsa Maryam a wani sabon fim dinsa mai suna Gwarzon Shekara.
Ramadan ya ce shi bai "dauki hakan a matsayin wani abu ba."
"Babu abin da na ji yayin da na fito a fim, ina soyayya tare da kanwata Maryam. Kuma na yi amfani ne da abin da darakta ya ba ni umarnin na yi."
Ya bayyana hakan ne yayin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan tare da rakiyar fitaccen dan wasan Hausa, Ali Nuhu, ranar Juma'a.
[Image: _98612729_both.jpg]
Dan wasan ya je birnin Landan ne don ya karbi kyautar gwarzon shekara ta bana wanda mujallar African Voice ta shirya.
Har ila yau Ramadan ya ce abin da ya sa duka 'yan gidansu suke fitowa a fina-finan Hausa shi ne don a kawar da zargin da ake yi wa 'yan fim cewa suna bata tarbiyya.
Ya ce suna fitowa ne a fim don a kawar da wannan zargin.

http://www.bbc.com/hausa/labarai-41870606