The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 160 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 160 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 165 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 165 errorHandler->error



Forums
KO KUN SAN AMFANIN SHAN LIPTON TEA? - Printable Version

+- Forums (http://contripeople.com)
+-- Forum: Retired Forums (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=78)
+--- Forum: Retired Forums. Please Make Your Post Within The 3 Forums In General Discussion (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=49)
+---- Forum: Hausa Language Forum (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=40)
+---- Thread: KO KUN SAN AMFANIN SHAN LIPTON TEA? (/showthread.php?tid=9397)



KO KUN SAN AMFANIN SHAN LIPTON TEA? - Gimbiya - 08-18-2018

KO KUN SAN AMFANIN SHAN LIPTON TEA?

Bincike ya tabbatar da cewar Sinawa su suka kirkiro shan  shayi  (tea) kuma sarkin kasar Sin SHENG NONG shi ne ya fara shan shayi  a matsayin wani abin sha tun shekaru 2,737 kafin haihuwaar  Annabi  Isa  A.S. Wannan shi ya sa Sinawa ke da shayi iri-iri a matsayin magunguna.
Yayin da kuma shayin da ya zama ruwan dare a duniya wato LIPTON wani  mai suna  THOMAS LIPTON dan kasar Scotland  ne wanda aka haife shi a 1850 ya kirkiro wannan brand  din kuma har yau ake aamfani da sunansa LIPTON.  A shekarar 1889  ne Mr LIPTON ya soma sayar da wannan shayi bayan da ya je kasar CEYLON wato wadda ake kira Srilanka a yanzu inda ya soma noman ganyen tea dinsa. Sai a shekarar 1906 Mr Lipton ya soma fitar da shayin LIPTON zuwa kasar japan.
To menenee amfanin shan ganyen shayen LIPTON ga lafiyar jama’a?
Masana kuma masu bincike kan ganyayen shayi sun tabbatar da cewar yawan shan ganyen shayin LIPTON na taimakawa.
1. Shan LIPTON kofi datya a kullun na rage saurin kamuwa da cutaar sankara wato cancer.
2. Shan kofin Lipton daya da safe na kara inganci da kare lafiyar zuciya da hanyoyin jini saboda yana dauke da wani sinadari da ake kira (Epigallocatechin gallate) da kuma sauran sinadarin da ke hana toshewar hanyoyin jini.
3.  Lipton tea na dauke da sinadarin Flavonoids  da ke taimakawa jiki samun kuzari.
4. Yawan shan Lipton na kawar da kwayoyin cuta na baki don haka na maganin cututtukan baki da warin baki.
5. Yana taimakawa wajen narkar da kitse a jikin mutum don haka yana rage kiba da nauyin jiki sosai in aka juri shansa. Idan ana sha duk safiya da zarar an tashi a gado  ba tare da an sanya masa suga ko wani abin zaki ba yana haifar da sakamako mai kyau na rage kiba.
6. Yana rage ciwon jiki da na gabobi  domin Lipton tea na daauke da sinadaran EGCG  wato Ephigallocatechin gallate.
7. Yawan shan ganyen tea na Lipton yana sa kullun mutum ya zama kamar saurayi ko budurwa domin yana gyara lafiya da ingancin fatar jiki. Mai yawan shan Lipton tea kullun fatarsa za ta rinka sheik da laushi.
8. yana rage yawan kitse a cikin jijiyoyin jini ( cholesterol) idan aka juri shan sa a kullun
9.  Shan Lipton tea a kai a kai na rage yoyuwar kamuwa da ciwon sugar musamman ma diabetes2.domin yana kunshe da sinadaran da ke rage karuwa sugar a cikin jini.
10. Yana rage wasu kananun kumburi a jikin mutum domin yana kunshe da abinda ake kira  ANTIOXIDANT.
11. Yawan shan Lipton kan kwantar da hankali kuma ya kawo natsuwa ga wanda ke cikin wani halin tashin hankali.
12. Shan Lipton tea na kara inganta grkuwar jiki saboda yana dauke da Vitamin C mai yawa. Don haka yana rage saurin kamuwa da cututtuka musamman  cutar mura.
13.  Bincike ya tabbatar dacewar shan Lipton tea na rage yiyuwar kamuwa da PROSTATE CANCER. Na kuma sanakarar nono na mata. Bincike ya tabbatar da cewar matan da ke yawan shan Lipton tea sun fi matan da bas u shansa rashin kamuwa da sankarar mama/nono
14. Yana  rage yiyuwar kamuwa da STROKE wato katsewar bugun zuciya nan take. Domin yana kunshe da sinadarin da ke hana kaurin jijiyoyin jini.
15. Shan Lipton akai akai na maganin mantuwa kuma na sanya ka ji garau a lokuta da dama.dattijai da tsofi da ke yawan shan Lipton tea sun fi wadanda bas u sha kaifin basira da rashin mantuwa kuma yana  hana yiyuwa kamuwa da cutar ALZHEIMER
16. Shan Lipton tea na maganin  hawan jini domin na kunshe da sinadaran daa ke daidaita karfin guddun jini a jiki.
17. A cikin Lipton tea akwai sinadarin IRON wanda ke maganin karancin jini a jiki don haka yana taimakawa wajen cutar ANEMIA. Wato karancin jini a jiki.
18. Shan Lipton yana kare lafiyar koda  da hanta sosai domin yana fitar da cututtuka daga koda da hanta kuma ya inganta ayyukansu ta yadda  ba za su iya rike cututtuka ba.
19. Shayin Lipton na rage karfin tari. Idan aka sha Lipton da ruwan zafi aka sa zuma yana amfani sosai. Kuma na maganin ciwo ko zafin cikin wuya. Ana shan Lipton ne da LEMONGRASS da ruwan dumi.
MATSALOLIN DA SHAN LIPTON KA IYA SAWA.
1. Hana barci cikin dare sabode caffeine da ke cikinsa. Amma bai kai na sauran tea yaw aba.
2. Masu ciwon koda kuma  saboda shan Lipton tea na sanya yawan fitsari, zai fi kyau ku tuntubi likitanku.
Lokacin shan Lipton da ya fi dacewa shi ne da sassafe sai kuma awa daya bayan cin abinci.
Allah sa mu dace.