The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 160 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 160 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 165 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 165 errorHandler->error



Forums
An haramta hadawa da shigar da kodin Najeriya - Printable Version

+- Forums (http://contripeople.com)
+-- Forum: Retired Forums (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=78)
+--- Forum: Retired Forums. Please Make Your Post Within The 3 Forums In General Discussion (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=49)
+---- Forum: Hausa Language Forum (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=40)
+---- Thread: An haramta hadawa da shigar da kodin Najeriya (/showthread.php?tid=6731)



An haramta hadawa da shigar da kodin Najeriya - Gimbiya - 05-02-2018

An haramta hadawa da shigar da kodin Najeriya
[Image: _101104490_doc.images.-2-15of17.jpg]
Najeriya ta haramta hadawa da sayar da maganin tari mai Kodin bayan BBC ta bankado yadda ake sayar da shi barkatai.
Ministan Lafiya na kasar Farfesa Isaac Adewole ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun Mataimakin Daraktan watsa Labara na Ma'aikatar Olajide Oshundun.
Mr Oshundun ya shaida wa BBC cewa za a ci gaba da sayar da wadanda suka rage amma kawai ga wadanda likitoci suka ce a bai wa.
A binciken da BBC ta gunadar ya gano cewar masu safarar kodin suna aiki cikin kamfanonin da ke hada maganin, kuma suna sayar da magungunan ba bisa ka'ida ba.
Miliyoyin matasa a Najeriya na shan maganin, wanda ke sa mutum ya nace masa, domin su bugu.
Maimakon amfani da kodin, ministan ya ce masu hada maganin tari su rinka amfani da Dextromethorphan wanda bai kai kodin illa ba.
Ministan ya kuma umarci Hukumar Kula da Masu Hada Magunguna ta Najeriya, (PCN) da kuma Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) da su sa ido wajen janye kodin din dake cikin kasar.
Za a yi haka ne domin tabbatar da yawansu da kuma sanya musu alama, in ji sanarwar.
Karanta cikakken binciken da BBC ta gudanar kan kodin

[Image: p065t0ww.jpg]
Sanarwar ta kuma ce ministan ya umarci hukumar PCN ta cigaba da tabbtar da cewa an bi dokar hana hadawa da kuma shigowa da kodin cikin kasar.
Minsitan ya ce ma'aikatarsa za ta tabbatar da cewa hukumomin NAFDAC da PCN, da NDLEA mai yaki da miyagun kwayoyi sun yi aiki tare domin tabbatar da cewa na bi dokokin da aka kafa kan amfani da kodin a Najeriya.
Alkaluman hukumomi sun bayyana cewa kimanin kwalbar kodin miliyan uku ake sha a kowacce rana a jihohin Kano da Jigawa kawai.
Da ma can doka ta haramta sayar da kodin a Najeriya sai ga wanda likita ya bai wa izini, amma BBC ta gano yadda ake hada baki da wasu masu kamfanonin hada magunguna da 'yan kasuwa wurin sayar da shi ba bisa ka'ida ba.
Wani wakilin BBC a Abuja ya ce babu tabbas kan tasiri ko akasin haka na wannan sanarwa da ministan ya bayar, ganin yadda saba doka da cin hanci suka zama ruwan dare a Najeriya.
http://www.bbc.com/hausa/labarai-43966694