The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 160 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 160 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 165 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 165 errorHandler->error



Forums
Rashin Aikin Yi Ke Sa Matasa Yi Wa Zaman Lafiyar Nijeriya Barazana –Sarkin Wandi - Printable Version

+- Forums (http://contripeople.com)
+-- Forum: Retired Forums (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=78)
+--- Forum: Retired Forums. Please Make Your Post Within The 3 Forums In General Discussion (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=49)
+---- Forum: Hausa Language Forum (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=40)
+---- Thread: Rashin Aikin Yi Ke Sa Matasa Yi Wa Zaman Lafiyar Nijeriya Barazana –Sarkin Wandi (/showthread.php?tid=6705)



Rashin Aikin Yi Ke Sa Matasa Yi Wa Zaman Lafiyar Nijeriya Barazana –Sarkin Wandi - Edoman - 05-01-2018

By Muazu Hardawa
An bayyana rashin wadatar masana’antu a kowace kusurwa ta Nigeria a matsayin babbar matsalar da ke barazana ga rayuwawar matasa lamarin da ke sa karuwar masu zaman kashe wando a tsakanin matasa lamarin da ke haifar da barazana ga zaman lafiyar Nijeriya ta hanyar jefa su cikin miyagun ayyukan cutar da kasa. Sarkin Wandi a karamar hukumar Dass Alhaji Mohammed Bello Manda Aliyu, shi ne ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilinmu a Bauchi, inda ya kara da cewa matukar ana son shawo kan matsalar tsaro da rashin aiki, dole sai gwamnatoci sun hada kai da masu hannu da shuni an saukaka hanyoyin kirkiro da manya da kananan masana’antu, wadanda kuma suka durkushe suma a samar da kudin farfado tallafi ko rance don farfado da su. Alhaji Mohammed Bello, yace duk kokarin da ake yi na bayar da tallafin dubu biyar ko goma ga matasa wanda yawanci ke cewa basa samu ba zai samar da mafita ba illa a dauke su aiki na dindindin kamar yadda aka saba yi a gwamnatocin baya, saboda idan an basu kudin a rana guda za su kashe su zauna ba wajen zuwa ba hanyar samun wasu kudin, daga karshe sai shaidan ya zamanto abokin shawarar su, daga nan sai jin haushin masu mulki da ‘yan siyasa da duk wani mai abin hannu. Matsala kadan idan ta taso sai matasan su dauki doka a hannun su, wasu kuma su rika tare mutane suna amshe musu dukiyoyi ko neman hanyoyin tayar da hankulan jama’a akan abin da bai kai ya kawo ba. Don haka ya shawarci shugabanni su sake tsarin hanyar samar da ayyukan yi ga matasa a fitar da kudi a rabawa ‘yan kasuwa da manoma tsakani da Allah ta yadda za su gina kamfanoni manya da kanana da gonakin noma da kiwon dabbobi da kifi da kaji don a samu hanyoyin samar da karin ayyukan yi ta yadda za a rage yawan matasa masu zaman kashe wando. Mohammed Bello, ya kara da cewa duk yawan abin da zaka ba matashi, idan ba ka samar da wajen da zai zauna na tsawon awoyi a wuni ba, to shaidan ne zai kasance abokin shawarar sa a duk lokacin da ya kasance shi kadai ba tare da sanin tudun dafawa ba, musamman idan ya cinye abin da aka bashi sai ya koma jin haushin wadanda basu cinye nasu ba, amma idan aiki ya ke yi ko don kar a kore shi zai kasance mai bin doka da oda. Haka kuma ya shawarci iyaye su tashi tsaye wajen tarbiyyantar da yaransu, musamman ganin an shiga cikin wani yanayi da a kullum aihuwa ake yi, abin da ake samu don bukatun yau da kullum kuma baya wadatarwa, hakan ke sa wasu iyayen basa sanin me ‘ya’yan su ke yi don gudanar da rayuwa, kowa ya zamo da inda ya sa gabansa. Don haka ya shawarci matasan da iyaye kowa ya koma kan noma da karatu da kuma sana’ar da aka gada tun farko don a magance matsalar da ake ciki ta lalacewar tarbiyya da aikata miyagun laifuka daga matasasan. Har wa yau ya shawarci ‘yan siyasa su daina amfani da matasa wajen banga da neman tayar da hankulan mutane saboda wasu muradu na kai ko na neman matsayi don a samu ciyar da kasa gaba da gina al’umma.

Read More at: https://leadershipayau.com/2018/05/01/rashin-aikin-yi-ke-sa-matasa-yi-wa-zaman-lafiyar-nijeriya-barazana-sarkin-wandi/