The following warnings occurred:
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "avatartype" - Line: 783 - File: global.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php 783 errorHandler->error
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined variable $awaitingusers - Line: 34 - File: global.php(844) : eval()'d code PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/global.php(844) : eval()'d code 34 errorHandler->error
/global.php 844 eval
/printthread.php 16 require_once
Warning [2] Undefined array key "showimages" - Line: 160 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 160 errorHandler->error
Warning [2] Undefined array key "showvideos" - Line: 165 - File: printthread.php PHP 8.0.30 (Linux)
File Line Function
/printthread.php 165 errorHandler->error



Forums
Je ki gidan ku - Printable Version

+- Forums (http://contripeople.com)
+-- Forum: Retired Forums (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=78)
+--- Forum: Retired Forums. Please Make Your Post Within The 3 Forums In General Discussion (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=49)
+---- Forum: Hausa Language Forum (http://contripeople.com/forumdisplay.php?fid=40)
+---- Thread: Je ki gidan ku (/showthread.php?tid=44)



Je ki gidan ku - Kabir Gidado - 08-25-2017

" Je ki gidan ku"

Furucine da maza kan ma matansu idan sun ɓata masu rai, ko sun masu wani laifin da suna ganin sai iyaye sun sa baki.
A zahirin gaskiya, wannan kalamin akan fassara shi a baibai, alouta da dama ana ɗauka kai tsaye saki ne muɗala'an,.wanda azahirin gaskiya, ba za a ɗauke shi ba a saki sai in an ji daga bakin mai furucin...domin ai akwai niyya a zuci kamin furuci, (duk da cewar in ka furta saki a gaban matarka, ko ba da niƴa ba , ta saku) don haka dole ne a san da wace niyya akayi furucin kamin a yanke hukuncin saki ne ko akasin shi.

Idan aka sa idon basira, Kalaman "tafi gidanku....kai tsaya , za a ga ba alamar saki a kalaman sam... Lura da sanadin furucin zai iya nuna hakan, shin  akan tsatsauran rashin fahimta a tsakanin juna ya sa aka yi maganar... kokuwa a saisa-saisan saɓani...irin wanda ake da bukatar wani magabbaci ya sa baki, ko kuwa?

Premise

Misali, sai gardama da rashin yarda ya shiga tsakaninka da uwargida, saɓani mai tsanani, sai ka ce tafi gidanku" kai tsaye ba ka kara wani abu ba daga nan, to anan ana iya tambayar ka, da wace niyyar ka ce hakan? Amma in cewa ka yi 'tafi gidanku, ga ni nan tafe...ko sai na neme ki, ko sai iyayenki sun nemi ni, ko sai na huta, ko sai gobe ko wani lokaci ki dawo, da sauran ire-iren irin waɗɗannan kalaman da ke tafiya tare da bayani, to ai anan ba a buƙatar a tambaye ka ya kake nufi, saboda wata jumla mai nuni da abinda kake nufi, ta biyo baya.

Hakazalika ma in cewa ka yi "tafi gidanku na sake ki" to ka ga ke nan ka gama magana, abinda za a tambayeka kawai shine, saki nawa? Shi ne abin tambayar ba kamar yadda wasu malamai ke cewa, shi wannan kalamin, ba makawa akan  saki uku ya ke nufi ba.

Amma idan ka ce ta tafi gidansu, aka tambaye ka da wace niyya ka ce hakan, to a gaskiya ka faɗi hakiƙanin halin da zuciyarka ta ke ciki a lokacin,... da kuma abinda ka aiyana a zuciyarka , kada  da niyyar saki ka yi, amma tunda ka huce, ka yi ƙarya ka ce ba da niyyar ka yi ba, to ka sani cewa duk sadda ka aiyana ka saki matar ka a zuci ko a  bayyane ( anan banda in kana shawara ne a zuci ta cewar ka saki ko ba ka saki ba( kuma wasu malamai na cewa saki a zuci ba saki bane, saboda sun dogara da shaidu, watau dole ya zamana sai in ta ji ko wani ya ji, sannan ta saku) to ta saku, sai ka sanar da ita, ka ce amma ka yi nadama ka mayar da ita in kana da sauran muradin ta... matuƙar ba a igiyar ƙarshe ne ba ka yi furucin, domin in a igiyar ƙarshe ne, to fa ba gyara, sai dai hakuri.

Ya ɗan uwa, ka sani fa duk inda kake kana tare da akibu wa atidu, koma Allah na sama na ganinka, idan da niyar saki ka yi, to ka faɗi gaskiya don gudun zaman zina da samun ƴaƴa da basu da gado,... ka mutu kuma  a raba gado da su , su ci haramun. Don haka sai a sa tsoron Allah a faɗi gaskiya.

Allahu a'alam

Rilwan A. Salisu
25/08/2017