KASUWANCI NA
6-10
Official
By
AsmaBaffa
AUTA kema wannan page Sadaukarwa ce gareki.
Tafiya nake ina tunani har na Isa bakin titi ina jiran na shiga Napep shuru shuru ba taxi ba Napep kowacce a cike suke,wata dalleliyar motace tayi parking a gabana tunanina Namiji ne irin samari yan iska masu ragewa mata hanya a nemesu nan take na kara tamke fuska na dauke kaina na kalli can gefen hanya,wani kamshi naji ya cika wajen sakamakon bude murfin motar dake Saitina da akayi sai lokacin na kalli me fitowar ba kowa bane face yan matan nan na gidan Saurayi Aayan wanda suka min dukan tsiya sune su biyu suka fito a zafafe kida na tashi a motarsu sunci uban kyau ko ina zasu je oho,ina cikin wannan tunani sai ji nayi an sharara min ruwa a jikina me sanyi,a firgice na kallesu da mamaki,nan suka sheke min da Dariya dayar ta fusgo min Hijab tare da shakeni,dayar ta duro min ashar tare da cewa ubanwa kika zaga har gidanmu?dama nace wlh duk ranar dana ganki sai kin San wa kika yiwa rashin kunya wato har iyayenmu ko?
Dayar data shakeni ta tsandara min mari tace Wai ke face to face harda zagin ya Aayan ke din banza kucaka yar matsiyata kin San su waye ubanmu har zaki bude rubabben bakinki ki zagi kakarmu who are u me kwakwalwar dusa banza gaja.
Wani bakin ciki da bacin rai ya taso min duk saurin kuka na haka na danne shi,dama cikin haushin masu kudi nake ga bacin ran halin da muke ciki,nan take na kasa hakuri nima nace kune dai gajoji yan iska tsinannu na shaki wacce ta shakeni nima na zuba mata Mari me lafiya,nan take ta shakeni tare da Dafe kuncinta, dayar ta taso a fusace kafin ta karaso na tsuguna tare da kwaso kafafunta ji kake Tim ta fadi gefen titi,na bita kuwa tare da jawo kafarta kaiiiii kowa yana kallo ina janta a kasa tana ihu,na hau kanta tare da Zama daram na rufeta da duka tako ina,wacce na mara kuwa da sauri tazo kaina itama ta hau dukana,muna ta faman yi,ga yara da mutane sun taru ana kokarin rabamu amma Sam munki Hakura yi kawai mukeyi,
Wata motace dalleliya ta kara parking a gaban ta yan mata wata budurwa itace wacce muka samu tare suna rawa ranar da muka je gidan Polio da gudu ta taho tana yiwa yan Uwanta magana Ku kyale matsiyata Ku zo mu tafi pls wannan ba Class dinku bace Ladies pls,babu wanda ya kulata da takalminta me shegen tsini,gani tayi babu me hakura kawai ta daga waya ta kira Babansu tare da fada masa Address din inda muke,Nan take sai ga arnayen Motocin Aayan sunyi parking sun kai su bakwai da securities,yana zuwa ya fito cikin Takun mashahurin Namiji yau sanye yake cikin farar shadda dinkin fitted dai dai jikinsa ya dau matukar kyau ga wani arnen glass Brown a fuskarsa ba karamin kyau yayi ba,ganinsa yana tahowa nayi matukar firgita kamar zanyi fitsari sabo da na tsorata bazan manta da dukan da yayi min ba,ban San sanda na hantsilar da dayar daga jikina ba na tashi daga kan dayar da nake zaune na gyara hijab dina na kwashe da uban gudu kamar zan tashi sama,ina danyin nesa dasu na tsaya ina maida Numfashi,shi kuwa baima tunani ba Sam bai gane ni ba amma ya tabbata ya sanni.
Ina kallonsa ya karasa wajensu ya kama yan matan nan ya dinka kwada musu mari ba ji ba gani yana ball dasu sai da ya canja musu kamanni sannan ya fada mota yace Securities su kamo ni,banyi tunanin wajena zasu zo ba ina ta kokarin tare Napep amma babu,kawai sai motoci na gani sun zagayeni,kafin kace me Sojoji sun zagayeni ba hanyar guduwa.
Saurayin ne ya fito cike da jin kai ya kalleni da kyawawan idonsa,kwarjininsa da haibarsa sun cika min zuciya nayi kasa da kaina har gabana ya matso tabbas nice ya gane nice naje har gida na zagesu da Iyayensu,nan take yace a sa masa ni a mota ko ta wanne Hali,Kuka na fashe dashi me karfi ina rokonsa wayyo uwata wlh ni ba yar uwarku bace baka da dalilin hukuntani,yana jina ko kallona baiyi ba nan take suka jefani a mota suka figi motocinsu dani a ciki,Su kuma yan matan da kyar suka shiga mota daya me jarabar son girma ta jasu sannan tayi waya aka zo tare da daukan motar tata da ta bari gefen titi,Hospital ta wuce dasu aka yi musu Dressing tare da magani sannan suka tafi gida.
Ina cikin bayan wata mota Sanyin Ac sai kadani yake na dunkule waje daya ina ta faman Rusa kuka cewar an saceni za a yanke min kai,ta window naga mun shigo wani katafaren Building na gasken gasken komai glass ne fadin tsaruwar wannan building bata baki ne ashe wai Office din wannan hadadden saurayin ne,harda su Lifter, ko ina Flowers kamar wani Hotel don a Hotel din ma sai shahararre,ina kallo suka sa Lock tare da kulleni ni kadai a motar tun 9am suka shige ciki ina ta sa ran zasu fito gashi motar taki budewa,na rasa yanda zanyi,11am shuru,12pm tuni nayi bacci a cikin motar,3pm dai dai na farka daga baccin daya saceni a cikin motar tun 12 na fara baccin,yunwa taci har ta cinye amma banga Alamar zasu fito ba Sam,tun ina kuka har na hakura gashi banyi ko Sallah ba ni da bana kauna na hada Sallah sabo da gaskiya Allah yasa min son Addini sosai,ganin basu da niyyar fitowa kawai na fara karatun Qurani a hankali sai da nayi ya kai izu biyu sannan na koma tasbihi da sauran Zikhri dana iya,ina ta yin abina bilhakki da gaskiya ina adduar Allah ya kawo silar samun kudin asibiti na Ammah kuma Allah yasa ta warke,yunwa ta addabeni da kishirwa,5pm naga hadadde ya fito cikin shigar 3qtr fari da riga Armless red kamar ka saceshi ka gudu sabo da haduwa ta ko ina,kallonsa nake tayi ina tasbihi ga yanda ya zubawa wannan Saurayi baiwar kyau,sura, ga iya daukan wanka,uwa uba ga nutsuwa Kwarjini da haiba,Securities suna take masa baya yana gaba da robar ruwa a hannunsa,da sauri suka bude masa mota ya shiga ga yan Jarida suna binsu da gudu suna jefa masa tambayoyi amma ko bude baki baiyi ba bare ya basu amsa haka aka bude masa mota ya shiga sannan Securities suka shiga nasu harda motar da nake ciki suka figa muka bar wajen,ina ta mamaki ko ya manta dani gashi nasan Ammah da yan uwana yanzu sun shiga wani a kan rashin dawowata,
Wata katafariyar Unguwa ta masu Hanu da shuni muka nufa ina mamaki nan kuma kamar a turai wacce GRA ce wannan haka?domin nasan Ba Unguwarsu bace wannan,Harga Allah wannan Saurayi wato Aayan ya manta dani a cikin mota,direct Gidansa wanda babu wanda yasan dashi nan ya nufa,gidan fadin haduwarsa da tsaruwarsa bata baki ne ya wuce duk inda ake tunani,gidane na fada wanda kafin a sami irinsa sai dai ko a turai ko Abuja watakil,sunayin parking a compound duk suka firfito aka bude masa ya kallesu tare da basu Umarnin su kwashe motocin su kaisu main Family House tunda yana da motoci iri iri a cikin wannan gidan kalarsu daban masu shegen kyau jibga jibga,daya daga ciki ne ya sanar dashi yarinyar fa? Sai lokacin ya tuna da ina ciki,tsaki yaja sannan yace a fito masa dani su kuma su tafi Gida.
Nan take aka yo waje dani suka figi motoci suka bar gidan daga ni sai wannan Matashi Aayan me cikar zati da kwarjini.
Shuru nayi tare da sunkiyar da kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna jikina yana bari kamar mazari,Kallo daya yayi min wani na mugun wulakanci tare da rainin hankali yana yatsina fuska kamar yaga kashi,nayi mugun raina kaina domin bani da maraba da Almajira mara galibu,juyawa yayi cike da takama hannunsa cikin aljihun wandonsa daya hannun kuma yana latsa waya yace let's go,bana jin turanci amma na gane go din kawai nabi bayan sa kamar Munafuka burina kawai ya kyaleni na tafi gida abina.
Code number ya danna nan take kofar ta bude ya shiga nima haka,Wow ai ciki Aljannar duniyace kawai komai na Alfarma abin ba a cewa komai domin shagala nayi wajen kallo ina mamakin kudin wannan matashin komai Allah ya bashi.
Steps ya hau na bene,har na taka zan bishi ya daga min hannu alamar na tsaya tare da zabga min uwar Harara yana tsaki,a tsorace na kame a wajen,tunda ya shiga ya mugun dadewa har ana shirin Magrib sannan ya fito sanye da farar jallabiya fara fitted a jikinsa yana sheka uban kamshi,ina tsaye kamar gunki yazo ya wuce ni kamar Allah bai halacci dan Adam ba haka ya wuce ya fita daga palon sai karar mota naji da alama ya fita Ashe Sallah ya tafi masallaci,nan take naga tsaiwa baza ta kaini ba kawai na fara duba dakuna gaba daya dake cikin palon kasa Allah ya taimakeni ina bude wata kofa na hango makeken daki dauke da lafiyayyan gado da mudubi tare da sip na Alfarma komai milk and Brown color ne a dakin,kofa na gani a cikin Bedroom din nan take na Murda Handle din toilet ce ta yan gayun gaske ban taba ganin irinsu ba dan Allah yasa a birni muke da bazan iya gwada yanda ake kunna tap din ba,ina shiga wajen sink na nufa abin mamaki ina mika hannuna sai ruwa ya fara zuba shaaa idan na janye hannuna sai ruwan ya dauke haka shower ma kai abin kamar Aljanu,ban San lokaci ya ja ba na shagala na manta da kowa ina ta tabe tabena har na gaji nayi fitsari da tsarki sannan na daura Alwala na fito Palo da sauri dan kar mugun ya dawo ya isheni na shigar masa wani waje,ina fitowa na duba gabas na shimfida dankwali na sai na fara jero salloli,Magrib na fara yi sai la'asar da Azahar ina zaune ina azkhar na Mike na gabatar da Sallar Isha da kyar kasancewar yunwa taci karfina gaba daya a kasa a zaune ina adduoina.
Motarsa naji da Alamar ya dawo lokacin ina yanda nayi Sallah ina adduo ina wanda ban san ma a fili nakeyi ba ina fadawa Allah ciwon Ammah da halin da muke ciki Allah ya yaye mana,kamshinsa naji alamar ya shigo da mamaki ya kalleni da alama Sallah nayi karfa ko Bedroom na shigar masa,wata mahaukaciyar tsawa ya buga min da tasa nan take na saki kuka,Keeeee a ina kika samu Ruwan Alwala? Jiki na rawa na nuna masa Bedroom din dana shiga da yatsa na, tsaki yaja tare da cewa Allah ya taimakeki wata leda ya wurgo min a jikina sannan ya haura Sama da nasa a hannu.
30 mnt ya fito da lemon gwangwani a hannunsa yana korawa nan ya fada saman kujera tare da nutsewa a ciki ya dauki remote yana kunna Tv ya kamo tashar wakokin turawa na yan Iska kusan ma kamar tsirara ake nuna su su Nicki Minaj etc.
Da kyar na Mike na karasa kusa da kafafunsa a hankali cikin ladabi da kwantar da murya nace Sir....Shuru ya min kamar bai San ina magana ba,Nace Sirr.....shuru,Sirrrrrr.....da wani mugun Bala'i ya juyo ba tare da yace komai ba,nan dai na daure da kyar sabo da kwarjininsa nace Dan girman Allah kayi Hakuri ka barni na tafi gida dan Allah,Ammah ta tana gida bata da lfy da kannena yanzu suna cikin damuwa dan Darajar Allah Sir,idan ma baza ka barni na tafi ba to ka kira min su a waya ka hadani dasu na kwantar musu da hankali kafin Lokacin da zaka barni na tafi.
Shuru naji yayi kamar ma ba dashi nake magana ba,na daure ina hawaye nace Sirrrr....sai lokacin ya juyo ya kalleni tare da dauke kai can yace me kike so kice? Wato duk maganar da nayi ma bai ji ba,wani bacin rai ya kamani cike da fushi na hayayyako masa nace ka barni na tafi idan baza ka barni ba ka kira min sis dina na fada mu......wani gigitaccen Mari naji a kumatu na,kafin na bude Ido ya kara min wani marin me masifar Radadi nan ba shiri na barke da kuka,mikewa naga yayi sai gashi ya fito da dalleliyar wuka a hannunsa,a wuyana yasa ta yace will u close tht ur dirty mouth or...kafin yayi Magana na hadiye kuka na sai shesheka duk da bana jin turanci amma na gane Close da mouth tunda Su Meenat suna koya min.
Dan kinga ban miki komai ba shine zaki raina min hankali am I ur mate or what?,baki da tarbiya na gama ganewa dama ina nemanki ke gaki marar kunya ke har kin isa ko kalleni ki zageni har gida,kin San ko ni waye who do u think u r? Murmushin takaici yayi tare da cewa dama bari nayi naga karshen rashin kunyarki,har kina min fada ni zaki kalla ki min maganar banza bayan kina hannuna ko yankaki nayi na yanka banza, shi dama Aayan haushin mata yake ji har jira yake mace ta masa abu yaga ya ci mata mutunci domin mata sun masa abinda bazai manta ba.
Ina gefe nayi mukus fuskata tayi jajir sai yatsunsa kwance a fuskata,wancen abincin ubanwa zai ci miki?da sauri na rarrafa na dauka na bude ledar jiki na mazari na bude Fried rice tasha hadi tare da kaza sai lemo,ruwa da Yogourt a ciki nan take na bude na kai lauma da bismilla kamar mayunwaciya haka nake afka abinci 5mnt kamar waccen ta zubar har na lashe abincin na shanye yogourt tare da lemon sannan na daga ruwan na shanye du,yana zaune mamaki ya rufeshi yana kallon ikon Allah ci kamar jaka,ya tabbata ko da yunwa ya kwana bazai iya cinye abincin ba,na gefensa ya kara jefo min a jikina nufinsa na cinye,ni ko dama ji nake kamar banci ba domin ba laifi akwai ci,haka na dauke na kara budewa yana bude baki da mamaki yaga na kara cinye nasan ruwan ne kawai ban Sha ba amma har yogourt din na shanye ta,da hannu ya min Alama na mike,zumbur na Mike tsaye,yace naje can bangon na dawo haka da sauri naje na dawo,yace yi tsalle na gani nayi tsalle ba shiri sabo da tsoronsa da nakeji,shi tunaninsa bazan iya tashi ba wannan uban abinci dana cinye amma sai yaga ras dani,a zuciyarsa yace bari ya kara gwadawa ya gani,nan ya Mike ya shiga kitchen ya fito dauke da fura tasha hadi a katuwar roba tare da Fruits a wani bowl,nan take yawuna ya tsinke naga dadi ban saba cin irinsa ba amma da shinkafa da wake ce ko plate daya bazan iya cinyewa ba,ko tuwo bazan sauraresu ba amma wannan kayan dadi haka ina zan barsu ko cikina zai fashe bare wannan dan abinci na take away kamar an roko gaba daya bazai plate daya ba,
Furar ya miko min ya tamke fuska yace shanyeta,da mamakinsa yaga na dauke da sauri har ina murmushi don ina son Fura a duniya,kawai na fara Sha cikin nishadi har lumshe ido nake ina addua ga Allah ina inama Ammah na kusa,ina Sha ina Santi a raina gata tayi sanyi a raina nace ah lallai wannan yana so aci a koshi Ashe ma bai cika mugu ba yo ni badan su Ammah ba ai da na rokeshi ya dauki rikona a gidansa,ina ta santina sai gashi na shanye harda lashe spoon din,wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke abinfa ya daure masa kai karfa ko Aljana ce,Nan ya mika min Bowl din Fruits dama su nake kallo cike da kwadayi nan ma na karba harda godiya na koma gefe na fara lunkuma su kankana a baki nace kai Allah me iko na yini banci ba Ashe tanadi Allah ya min harda kara'i yana kallo yaga na tashi Fruits tsaf,karkuce abubuwan masu yawa ne basu da wani yawa kun San dai Harkar yan gayu komai kadan kadan ba dole na cinye ba.
Yau kuwa yace sai ya kure yarinyar nan mayya,ya Mike ya koma kitchen sai gashi dauke da kaza tasha hadi tana tiriri da Alama warming dinta yayi ya turo min gabana,kamar nayi kuka sabo da dadi yaushe rabon naga kaza guda a gashe sabo da murna ban san sanda na kalleshi ba nace Dan Allah ka daukeni aiki ko share share da goge ne a gidan nan,wata uwar Harara ya zabgo min ban san sanda nace yi hakuri na fara yagar kazata ba ina aikata cikina,gani yayi fa da gaske zan iya cinyewa kawai yace karta je ta barke min da Zawo a gida kawai ya taso ya fisge plate din tare da cewa Mayya.
Yana dawowa ya mika min faskekiyar wayarsa nufinsa wai nasa Number na kira gida,ban iya ba amma gudun laifi na karba haka nan take nayi kamar zan iya na zuba yatsuna guda biyu na fara birkita screen din,naga Sam ban gane ba nasa yatsuna guda hudu na fara dirzawa a fuskar wayar,na juyata na juya na dukufa kamar Idona zai zazzago sabo da yanda na zarosu ni a dole me danna waya,shi kanshi da ya kalla yayi tunanin wannan yarinyar Aljanu gareta ko mahaukaciya ce bai San tsabar rashin zaman aji ne da rashin shiga mutane daga siye sai siyarwa, gani yayi zan masa barna ya fisge abarsa tare da cewa fada min Number cikin hasala kamar zai dakeni,to mu dai a gidanmu babu waya dama akwai wani Shehu me Kanti idan wani abu ya faru shi Muke kira a waya sai ya kai gidanmu ayi magana don Number dinsa na kaina,na iya da turanci amma wai dan kar nayi mistake ya dakeni sai naji tsoro nace gwara na fada da hausa nan na fara cewa
sifili takwas sifili...wait wait ths is bull shit ban san wannan abun ba,nan nace yi hakuri bari na Canja na firgita kawai maimakon na fada da turancin sai wai dan yafi ganewa sai nace..tayar mota.. takwas..tayar mota,wai gani nayi Zero (O) yana kama da tayar mota shine dan yafi ganewa nace haka,wani mugun dariya ce ta kamashi da ya gano me nake nufi da Zero ne Tayar mota lallai wannan yarinya dakikiyace amma sai ya daure fuska yace wlh zan kwada miki mari zan miki abinda baza ki manta ba,nan take nace 080 sannan na fada masa Numbers da turanci,yace amma ke dan Iskanci zaki raina min hankali kin iya fada dai dai nonsense tare da Jan tsaki yana dialing bugu daya aka daga ya mika min wayar nace Hello...Shehu Mufeeda ce,dan Allah dan kaiwa Ammah wayar mana minti daya,nan Shehu yace to Mufeeda ya fita da sauri yayi Sallama gidan tare da gaishe da su Ammah dasu Meenat suka gaisheshi suna cikin wani Hali sunyi jirim suna jimamin Ina Mufeeda ta shiga tun safe har dare hankalinsu ya tashi,Shehu yace gashi inji Mufeeda tace za kuyi magana ai da sauri Ammah ta karba jiki na bari,Mufeeda tace Ammahna kuna lfy? Ya jikin naki? Ammah tace ba ta wannan nake ba kina Ina Mufeeda lfy iceko,dariya ni Mufeeda na kakalo tare da cewa lfy lau Ammah kin ganni a gidan wannan kawar tawa wacce kika sani Naeema yar gidan me kudin nan kin San ai da sun tafi kasar waje to sun dawo shine muka hadu a kasuwa tace muje naga gidansu,
shine ma mamanta take tambayata ke nake basu labarin cutarki da aikin da za ayi miki shine Maman tace mijinta yayi tafiya gobe ko jibi zai dawo na zauna kar na tafi na jira zai iya biya mana kudin aikin da za ayi miki,kinga ai bazan taho ba shine na zauna ina jira kuyi addua Allah sa a dace,nan take Ammah wani farin ciki ya lullubeta tace Mufeeda kin tabbatar haka zancen yake ba karya?nace tabbas Ammah ai kin San halina dai ko kin San kuma dalilin fita ta Allah watakil ya amshi adduar mu,Ammah kinga dadin da naci harda Kaza da Yogourt,kuyi addua amma yau Ni ina cikin daula ina su Meenat bani su,nan ma aka bawa Meenat suka Sha labari aka mikawa Maeeshah ma tana Anty jambaki pink ya kare ki siyo min wani,kuma takalmi na ya tsinke Sis nace to Maeeshah zan siyo bawa Ammah,nan nace Ammah aci gaba da kular min da Kasuwanci na dan Allah Meenat tayi komai,Ammah tace kin San basu iya kosan sosai ba,Nace Ammah suyi haka koma yane a tara min kudin in na dawo za muyi magana sai goben idan ya dawo me gidan zan sanar dake idan Bai dawo ba zan fada miki komai dai,Allah yasa a dace cewar Ammah ta mikawa Shehu wayarsa Mufeeda tayi masa godiya ta kashe shima ya musu sallama ya tafi,nan Ammah tace Meenat ta kulle musu gida ta rufe suka yi kwanciyarsu cikin farin ciki.
Ni kuwa ina gamawa hankalina ya kwanta nan na saki ajiyar zuciya,shi kuwa da mamaki yake kallona yanda na iya fesa karya haka,lallai suna da matsala amma ina ruwansa,ni ko dama su Ammah nake ji kuma na gyara komai,idan na koma nasan karyar da zan kara shimfidawa, baki ya tabe nan take ya fisge wayarsa tare da wucewa samansa,ni kuwa yana tafiya na koma saman 3seater na kwanta a tsorace har bacci ya saceni, tunda ya shiga bedroom ya rasa wannan mugunta zai min wacce bazan manta ba ina cikin bacci naji ya harbo ni kasa daga saman sofa,a firgice na tashi, ba Imani yace sai nayi Kamun kunne,haka nayi na Dade ina yi har sai da na saki Kuka,sannan yace nayi kneel down sannan Hands up nan ma na fara ina tayi haka yayi tafiyarsa ya barni ina ta abinda ya sani har bacci ya kwasheni na bingire a wajen,ban farka ba sai da gari yayi haske na Mike a firgice tunawa da banyi Sallah ba yasa na Mike da sauri na fada bedroom din da nayi Alwala jiya,komai na kayan wanka da amfani a kwai a toilet din masu tsadar gaske,ba bata lokaci tube kayana na kai hannuna ruwa me dumi sosai yana zubowa gwanin dadi ban san sanda na fara wanke kaina da shampoo me kamshi da tsada ba,ina gamawa na dauki liquid soap na sheka wanka sai kamshi ina ta washe baki,ina dubawa naga harda sababbin tooth brushes da toothpaste na dauka kuwa na wanke bakina tas abinka da abu me tsada hakorana suka kara haske da kyau Malam nayi wani Fresh dani,Towel nasa tare da goge jikina tas,sa nan na daura Towel na fito ina kara tsane gashina,mirror ba abinda babu na shafawa masu tsada,na dauki lotion na shafa a jikina,babu powder sai wata fara kawai na shafa abata na dauki lipgloss na shafa me kyau red,ban san jagirar waye ba na dauka na zizara a Idona sai gashi nayi kyau sosai.
Gashi na wanda ya bushe na taje na shafe shi da Maya Mayan gashi yana sheki da kamshi dama gani Allah ya bani tsayin gashi,Daure abina nayi nan take nayi acuci da gashina sannan na shafa roll on tare da turaren jiki dana gani me arnen kamshi,kayana na kwaso na saka haka ina so na wanke pant dina amma ba dama kawai na maida abina sai lokacin na tuna banyi sallar Asuba ba da sauri nayi tare da Azkhar sannan na fito Palo cikin Jin dadi na zauna,ina jin motsi na sauka kasa tare da kneel down na daga hannu sama wai dan yace a haka na kwana inayi,kallo daya ya min yasan Lallai har wanka nayi,ko kallona baiyi ba ya fita,15mnt sai gashi ya dawo tare da take away leda hudu,ya zauna a saman Sofa tare da miko min leda uku da sauri na karba dama yunwa nake ji nan na zauna daram tare da bude ledar sai ga kwai da chips tare da gashashiyar Hantar rago, haba Malam nan na zaro harshe na lashe labbana na fara dagargazar Harka yi nake ba ji ba gani,nan na kau da Leda daya na bude daya na lashe na jawo ta Ukun na cinye komai tas tare da daukan ragowar ruwana na jiya na shanye tas nace Alhmdllh tare goge hannuna da tissue din dana gani ciki.
Mamaki ya gama kashe Aayan har firgita yayi yana mamakin a ransa kuma cikinta baya lalacewa,yana kallon TV yace tashi ki gyara gidan nan kaf yayi maganar kamar bada ni yake ba,Zumbur na Mike na kayan aikin,kitchen ya nuna min da yatsa ina shiga na gansu a shirye na hado da kayan mopping,yace na biyo shi haka yasa na gyara samansa Kas Kas, ko ina yana kyalli har su toilet,abin ya bashi mamaki baiyi zaton zan iya gyara haka ba,muka dawo kasa ko ina na gyara har room din da nayi wanka da toilet,haka ya dinga nuna min wasu sashen har wajen motsa jikinsa sai da na gyara tsab,ta window na hango maza suna ta aikin gyaran compound flowers tare da goge windows ni kuma na gyara ciki, nayi matukar jigata nasha wahala,yace sai na shiga kitchen haka na shiga na wanke na goge na gyara komai neat har store,haka fridge ma ya fitar da abinda suka lalace yace na gyara ciki tare da bani wasu abin na gyaran Fridge haka na gyara fes na kara Mopping kitchen din na wanke komai na shanya su sannan na fito,ina fitowa yace naci gaba da Kamun kunne ba Hutu,inayi ina kuka,sai da na kai 1pm sannan yace naje nayi Sallah na bar masa gida,cike da Murna na Mike na gyara jikina tare da Alwala nayi Sallah ta saida na kara gyara fuskata gudun tuhuma wajen Ammah sannan na fito tare da yin hanyar waje,Keee naji muryarsa me sanyi,juyowa nayi a rude nan naga ya daga waya yana magana Hello Abbi ka tashi lfy,ta ciki naji Muryar Abbi yace zo ka bude min kofa ina son magana da kai gani a gidan ka wato ni zaka rainawa Hankali ko,nan take ya firgita amma dake namijin duniya ne sai ya maze bai kawo komai ba ya raba ta gefe na wani kamshi ya dakeni nan take jiki na ya mutu na lumshe ido,kofar ya bude kawai sai ga Abbi ya bayyana a gabana da sauri na tsorata tare da ja baya.
Salati ya saki da salallalami yace dama nasan wlh ba abin kirki kake aikatawa a wannan gidan ba shi yasa nazo da kaina,ashe baka da kunya baka da mutunci ai jiya na tambaya ina ka kwana ance ba a sani ba nasan kana nan,ashe abinda kake aikatawa kenan munafiki ka nuna Sam kai baka kaunar mata Ashe abinda kake kenan,karuwai kake kawowa gidanka,ashe shi yasa baza ka iya zama da aure ba,wannan yaro kwai tsinanne in Allah ya yarda Cutar kanjamau ce ajalinka,baza ka jawo mana abin kunya ba wlh dole yau Hajja taji zancen nan kuma aure dole kayi zaka ga abinda zai biyo baya,nan Abbi ya min kallon Banza ya fice a fusace.
Shi kuwa Aayan ko a jikinsa haka ya nuna amma yaji zafin sharrin da Abbi ya masa,ni kuwa tausayinsa naji sabo da na tuno maganganunsu farkon ganina dasu,Driver ya kira a waya sai gashi yazo umarni ya bashi jeka wannan zata gwada maka gidansu ka,ka kaita can.Nace na gode wata uwar Harara ya balla min nan take nayi mukus tare da bin bayan Driver na shiga motar sai muka bar gidan ina jin dadi na rabu da jaraba.
11-15
Official
By
AsmaBaffa
Ths page is for u MARCYCOOL.
ina matukar Godiya da jinjina fans masu Sharhi aci gaba da gashi kuna birgeni.
Allah ya taimakeni Driver na da kirki cikin mutunci ya kaini har kofar gidanmu wanda kaf mutanen unguwar mamaki sukeyi na wannan arniyar mota amma wai sai suka ga Ni Mufeeda yar Kasuwa yar talakawa fitik wai ni aka sauke a wannan mota, ai fa sai mutane suka fara guna guni ga zahiri ai karuwancina ya girmama ni kuwa Allah sarki ban san ma sunayi ba, wata kawata a makwaftan mu Nawwara itama dai Nawwara yar malam Shehu ce talakawa amma sun fimu rufin asiri ita kadai ce kawata sai kuma wata yar gidan masu kudi Na'eema amma ita yanzu sun koma Kasar waje da karatu har iyayenta suna kasar waje abinsu,
A hanya Nawwara tace Mufeeda kece a wannan zundumemiyar mota haka duk da bana zarginki ki kiyaye ko sabo da sharrin yan Unguwa,Murmushi nayi tare da cewa Allah kadai nake tsoro ni,Allah yaga zuciyata.
cike da farin ciki na shiga gida da Sallama dauke a bakina,da fara'a suna min Oyoyo sannan na wuce wajen Ammah tare da gaisar da ita,tace Mufeeda kar ki kara yin irin wannan tafiyar kinji na fada miki,wannan ya Zama na karshe da zaki tafi wani gida ki kwana ba tare da Sanina ba sai dai ki bugo waya,bazan yarda da wannan shirmen ba,karki ga na yarda dake kice zakiyi abinda kika ga dama ko dan kina ci damu etc kice zaki juya ni baki isa ba,ni ba irin iyayen nan bace masu son abin duniya akan yara ne ke ci dasu sai su zauna yaran na juya su sai abinda suka ga dama zasu yi,ki nutsu wlh akan haka gwara mu daina karbar abin hannunki bana so neman Kudi ya kaiki ga halaka ko sabawa Allah,naji matukar ciwo da sai dare ma zaki bugo ki fada min ni har ga Allah ban yarda da zancenki ba kawai dan naji lafiya kike yasa na dan samu nutsuwa,nan Ammah ta dinga fada ba ji ba gani ina bata hakuri harda kuka na,nace bazan kara ba kiyi hakuri abinda na tsaya nema ma ba a dace ba domin me gidan yayi tafiya kasar waje nan ma na kara mako karya ta na fada,aiko nasha fada wajen Ammah,ni dai hakuri nake bayarwa har ta hakura.
Bayan kwana biyu tsakani naga sana'ar tawa ta danyi kasa don haka na tattara ragowar kudin dake hannuna na siyo kajin Hausa da Akuya guda daya wai zan gwada yin kiwo ko za a samu suyi albarka,Kaji biyu yan budurwa na kawosu,akuya tana meee...mee na samu na daure ta can karshen gidanmu,lokacin wake beans yana araha kawai na auni kwano biyar na boye ina jira yayi tsada na siyar naci riba,sannan na dan siyowa su Meenat kayan kwalliya tare da kayan makaranta Uniform na dinka musu sabo idan an koma schl suma su sa sabo,haka na siyo mana Atamfa muka raba yadi biyu kala Uku akayi mana dinki me kyau na talauci domin rabi wasu yadi ne na adon Atamfa akayi mana kari dashi,sai suka ba da ma'ana,dama bamu da kudin dinka shadda daga atamfa sai materials sai kuma kayan gwanjo da muke sawa,suma dinkin atamfar na talauci duk bamu da riga da zani ko daya daga skert damamme sabo da yadinma bai isa ba bare tela ya maka mana dinki dole sai dan fitted,sai ko dogayen riguna baza ka gammu cikin Tsumma ba Sam sabo da ina yawan yi mana dinki tare da yan takalma na roba yan Dari hudu zuwa biyar muna dasu da yawa dasu muke too match,haka mayafai ma ina siya mana da hijabai zaka ga muna canja abinmu iri iri mata sai da gyara ai,bani da burin da ya wuce naga Ammah cikin farin ciki Tare da kannena duk kudin da nake nema sabo da su nake nema.
Asalinmu
Sunana Mufeeda Adam Fatima, Asalin Shuwa Arab ne Babanmu,a Borno state suke da Zama tare da Family dinsa gaba daya,Bashi da Ilmin Boko sosai sai kasuwanci da yake y,Babanmu Adam yana da dangi da yawan gaske wanda mu bamu San dasu ba Sam,Iyayensa sun Dade da rasuwa tun yana yaro domin shi kadai suka Haifa Allah ya musu rasuwa ya taso a maraya,shi yasa ma ya taso da neman Kudi har Allah ya kawoshi Kano state,yana shiga kauyuka saro kayan Noma ya kai kasuwa,Har ya shiga Kauyen Ammah wato Kauyen Rimin Gado can rigar Fulani,Nan yaga Ammah cikin halin rashin gata tana Shan wahala hannun matar uba sabo da bata da Uwa sai Uba,danginta kuma fulanin tashi ne basa Zama Sam kullum a yawon daji suke basa Zumunci,bayan Adam Abban mu ya auri Ammah da shekara daya Allah ya dauki ran Baban Ammah wato Sulaiman,Haka Abba yaci gaba da kula da Ammah suna zamansu lfy a cikin birnin kano gwale,ko sunje kauyen ma ba wasu dangi sun tafi yawon Shanunsu har Ammah ta daina zuwa ma tunda duk yan Uwanta sai wanda suke uba daya kuma basa kulata sai ta kyalesu kawai amma duk da haka tana kaimu muna zuwa itama kafin lalura ta sameta tana zuwa musu.
Mu kuwa ganin basa zuwa basu damu da mu ba ko tace muje sai muki zuwa idan munje ma basa ganinmu da daraja,Shekarar Ammah da Abba biyu da Aure ta Haifeni aka sa min suna Mufeeda kowa yana yabon kyauna,sai da na cika shekara biyu sannan aka kara haifar Meenat,itama After 3years sai aka Haifi Ma'eeshah,Lokacin Babanmu ya samu wadata sosai ya siyi gida kato cikin Rijiyar Zaki muka koma ciki yana Business sosai sannan ya zana waec da Neco ya koma makaranta yayi NCE ya gama,lokacin tuni ina zuwa Primary schl amma ta Gomnati sabo da ba masu kudi bane mu sai rufin asiri domin munfi karfin ci da Sha bare sutura,ina primary 3 aka saka Meenat da Ma'eesha suma muna zuwa nice Babba, Da yamma muje Islamiyya, ina kula dasu sosai domin tun ina yarinya Allah yasa min son iyayena da yan uwana fiye da kaina,mun taso cikin kulawa da tarbiya muna jin dadinmu har na kusa gama Primary
sai kuma muka ga Abbanmu sam ya daina kula Ammah sai wulakantata yakeyi,ba irin wulakancin da Ammah bata gani ba a hannun Abba,idan suna fada har Kuka mukeyi,amma duk lokacin bamu da wayo bamu San akan me suke fadan ba,muna dai ji yana cewa idan ya gaji korarta zaiyi,tun abin baya damun mu har muke damuwa muna bashi hakuri,bamu San dalili ba dai sabo da Ammah bata bari mu San halin da suke ciki,sai dai muga tana kuka watarana Abbah yace zai fita wata state dake Kudu Abia state neman Kudi tun da Allah yasa ya tafi bamu kara Jin labarin Inda yake ba ko a waya.
Mun shiga damuwa me tsanani,Amma taje har garinsu wajen danginsa tare da mu amma sukace suma basu da labarinsa,haka abokanansa na business da sauransu duk an nemesu shuru suma basu sani ba,munyi kuka munyi bakin ciki har aka kwashe shekara guda lokacin na gama primary,anyi cigiyar Abbah har gidan Radio amma ba labari haka Ammah ta fara Sana'ar kosan siyarwa da Awara tare da sauran kanana nan sana'a gida dasu take mana komai na rayuwa,har na shiga Jss1 na gama na shiga jss 2,Katsam lalura ta samu Ammah haka kawai bata iya motsa kafafunta daga Hips zuwa toes,munci kuka gashi nice Babba ga karancin Shekaru haka makwafta suka taimaka mana muka kai Ammah asibiti mafi sauki,da yan kudin da Ammah ke Tarawa muka sai mata magunguna sannan suka ce dole akwai wani aiki da za ayi mata nan gaba,tun da muka dawo Ammah ta dan samu sauki ni kuma dama duk sana'oin nata na iya su sai naci gaba da yi na daina zuwa schl nake biyawa su Ma'eesha suna zuwa,ni ke kula da Ammah da gidan baki daya,akan sana'ar ma sai na kara wasu da yawa ina yi iri iri komai siyarwa nakeyi ba sauki,har Allah yasa Meenat na Ss1 Maeeshah na jss2 ga Islamiyya suna zuwa ni kuwa komai ya tsaya min sai neman kudin jaraba kamar zanyi sata.
har yau munyi munyi da Ammah ta fada mana fadan dake tsakaninta da Abba kafin ya bace amma taki fada mana sabo da haka muka kyaleta sannan muka kara tsanar Abba da ya gudu ya barmu,dan ni ko zancen wani Abba bana yi sam bama na so a ambaci Sunansa shi yasa a makaranta ma Sunana Mufeeda Adam Fatima sabo da sunan Ammah Fatima kawai nace ai bazan sa Kakanmu ba Ammah ta zan sa,haka Meenat Adam Fatima tare da Maeeshah Adam Fatima haka duk muke Amfani dashi da ace da halima sai dai nasa Mufeeda Fatima Adam to kawai dan da uba ake ado shi yasa ba kyau dole nake Sa Adam.
Za muji nan gaba Ina Abbah ya boye oho,ko da gaske ya bata,ko yana raye,ko yan Mafiya ne,mene ya hadasu da Ammah suke fada,wacce lalurace a jikin Ammah haka? Oho dai.
Ci gaban labari
bayan kwanaki kadan na yanke hukuncin zan fara zuwa gidan yan siyasa tare da yan kasuwa da sauran masu kudi na fara neman taimako ko Allah zai sa a samu me Imani ya tallafa a biyawa Ammah kudin magani,bayan na gama kosan siyarwata tare da gyaran gidan haka nayi girkin rana na kwashe a cooler sannan na fara daka lallen da nake siyarwa ina daurawa a leda ina saidawa ashirin,lallen ma ban barshi ba sai dana yi masa Algus na hada da gayyen bishiyar sabara na daka ya kara yawa na daura na ajiye,idan mutum ya siya lalle sai yaga lallen yaki yi masa ja yadda yake so to anyi masa Algus da wasu gayyen,wanka nayi na shirya cikin skert dina dan gwanjo tare da T-shirt dita nayi kyau nasa Hijab dina me hannu sunsha wanki da guga,ban shafa ko Powder ba na yiwa Ammah Sallama nace na tafi kasuwa siyo kaya,tayi mun a dawo lfy,ban zarce ko ina ba sai gidan Chairman din local government dinmu,ban san gidan ba da tambaya aka nuna min ni da me Napep,bayan na sauka mutane damkam a kofar gidan har da yan Sanda masu gadi gida me kyan gaske,maza yan siyasa sai kallo na suke domin sunga baiwar kyau wajena,da gani kuma sun San ba yar siyasa bace ni kamilalliyace ni yar mutunci,salamu alaikum nayi musu sallama tare da gaishesu sannan nace Dan Allah yau Hon yana nan? Suka ce ae kinyi sa'a yana gida muma shi muke jira,amma tunda ke macece bari mu rokar miki masu gadi ki shiga kice wajen matar Hon kika zo,ai kuwa haka akayi nan take yan Sanda sunga kyau suka ce na shiga,
nayi godiya na fada gidan cikin nutsuwa,wata yar aiki ce ta nuna min kofar shiga ciki,nace tayi min jagora zuwa wajen Hajiya,har nan ta kaini sannan ta shiga tare da sanarwa Matar Hon,cikin Sa'a aka ce na shiga har ciki yar aiki tayi min iso,matar Hon yarinya baza ta wuce 24yrs da ganin irin kyau da Allah ya min yasa ta tsaneni kar na kwace mata miji,nan take naga ta canja fuska ta Mike tare da miko min Dubu biyu tace na tafi an sallameni,babu bakin magana jiki ba kwari na karba na dau hanyar fitowa kenan kicif sai ga Hon ya sakko daga sama da katon cikinsa yana shafa tumbinsa,ya kalleni nan take ya lashe bakinsa tare da yi min signa da Ido kamar kwarto,ni dai na fice da sauri daga palon.
Matar Hon tana Alhaji ga abincinka amma tuni yace Hajiya na fita Office ana jirana ya fito da sauri yazo kusa dani a bakin gate,da sauri na durkusa na gaisar dashi sannan na fada masa abinda ya kawoni nan take yace ai karamar matsalace wannan ya bani card dinsa yace na samesa a guess house dinsa,na tsorata amma dai na karba nace sai nazo na fito daga gidan na tafi gida ina murna ta.
Ban fadawa Ammah inda naje ba nasan fada zata min kawai nayi shuru,washe gari kuwa dama yace 5pm zanje gidan da yace,ba tsoro na shirya na tafi ba wahala na gane gidan na fita daga Napep,Naga gida rafkeke na kwankwasa sai ko ga me gadi ya bude yana ganin budurwa yasan irin matan da Hon ke Tarawa kullum ne da fara'a ya tarbeni yace shiga yana ciki,nan ya min iso har cikin palon Hon,sai lokacin tsoro ya kamani,lokacin na hango Hon daga shi sai Singlet da gajeren wando yana latsa waya,da fara'a yana washe baki yace zauna mana kyakyawa me kyan sura,Nace ba sai na zauna ba idan zaka taimakeni to ka bani dan Allah,dariya yayi yace zo mana ke ya kike abu kamar bagidajiya ina ganinki wayayya zo muji dadi mana sannan na baki kudin a wuce wajen kawai,tsorata na karayi na fara ja da baya nace ni ance ba kyau namiji ya rike ma mace hannu nidai zan gudu,Hon yayi dariyar Kuruciyata yana lallabani yana hure min kunne amma naki matsawa ko kusa dashi,tasowa naga yayi ya taho jikina ya fara shafa min fuska yana kokarin cire min Hijab,yana sakin wani Gurnani ai da gudu na ja baya a rude na bude kofar na fice da gudin tsiya ko me gadi gani yayi kamar walkiya na bude kofa na fice wufff.
Ina Haki na fito da matsiyacin gudu na cukwikwiye Hijab dina na tattara skert dina ba takalmi a kafata tuni na watsar dasu,Na samu gefen titi kawai na Mike na dinga tsinka uban gudu ka rantse yan Mafiya ko Zaki ne suke Bina,ga unguwar shuru irin ta masu kudi ba kowa ba a ganin ko mota a titin,can naji karar mota ta bayana tunanina Hon ne haba ai sai na kara karfin gudu na yi nake kamar numfashina zai fita,a hankali motar take tafiya a saitina sai lokaci ina gudu na dan kalli glass din window din an sauke glass din ana ta min magana ta ciki gudu nake iya karfina da karfi nace wlh bazan tsaya ba Hon tsinanne dan Iska ina ta zagin me motar ji nake Hon ne ashe Aayan ne yake ta Bina da motar yana sheka dariya yanda yaga ina uban gudu kamar na tashin kiyama,tsabar mugunta sai yaki yin magana kawai yake ta Bina da mota duk inda nasha kwana sai yasha da motar yana ta dariya har sai da karfina ya kare tas na fara kokarin tsayawa Ashe ban sani ba idan gudu ya cika yawa yakai wani limit mutum kasa tsayawa yake da kansa sai an rikeshi kawai zai ta gudu ne,ina so na tsaya ina kokarin tirjewa amma ina gudu kawai nake falfalawa na fashe da kuka kuma ina ta gudu na kamar masifa har dai da kyar na samu na rike wata bishiya sannan na zube a kasa wajen ina maida numfashi,Dai dai lokacin Saurayi Aayan yana ta dariya harda kwalla sannan ya take birki a inda nake Kuuuuu yana ta dariya yana rike ciki,sai da na Huta sosai da sosai sannan na tashi tsaye ina karkade jikina,sai lokacin na hangoshi cikin motarsa Ashe shine ba Hon ba,kawai nima abin ya bani dariya kamar sabuwar Kamu na dinga sheka dariya harda kwalla,a ransa yace lallai yarinyar nan da alama mahaukaciya ce ko Aljanu gareta,na kalleshi saitin window na daure fuska sannan na maka masa harara,ai ko ya fito a fusace na firgita ba damar guduwa dan na gaji ina ji ina gani ya fito ya zabga min Mari sannan ya jefar dani a kasa keee ya daka min tsawa ba a min ko kallon Banza mind ur fucking Business,bana jin turanci tunanina yasan Business dina dana keyi a gida kawai sai nace dama ai ni Kasuwanci na nakeyi ina ruwanka dani haka kawai sai ka dinga cin zalina dan kaga bamu da kudi,ai kudin naku bana tsoron Allah bane tunda ba a taimako sai yawo a mota ana zalinci,tsaki yaja me karfi cikin takama ya koma labebiyar motarsa fuuuuuuu ya figi abarsa.
Ni kuwa na turo baki tare da cewa Allah ya isa wlh duk ranar daya mareni again Allah sai na rama za a gani ai,nan na gama Kuri na sannan na tafi gida abina.
Washe gari ban tsorata ba na kara shiri na tafi gidan Vice Chairman neman taimako amma haka na yini ban samu ganinsa ba sai yaronsa,Nace dan Allah wajen Vice nazo idan baza ka damu ba ka min hanya na ganshi,cikin daure fuska kamar zai bigeni ya hayayyako min da masifa ke malama an fada miki ya tafi Umrah bazai dawo yanzu ba,irinku dama yan mata makaryata da Iyayenku sabo da son abin duniya sai ku fara karya kuna zuwa Maula daga nan a lalata Ku yan iskan yara,har nawa kike amma har kinsan yawon Maula,nan dai yaron Vice ya min tatas na baro kofar gidan da takaici.
Ban dai kara hakura ba washe gari haka na kara shiryawa na nufi gidan wani Commissioner na Ilmi,a bakin gate kofar gidan na yini ina jira ko za bani dama na shiga ciki amma masu gadin ko kallona ba wanda yayi,har zan tafi sai ga wani ya taho da Jibgegiyar mota kida na tashi Malam nan take mukayi Ido hudu da wani Saurayi black Handsome dan gayu,sai kallona yake,ina tsaye aka bude masa gate,sai wani kallo yake Bina dashi kamar tsohon maye,nan take naga ya sauke glass yana murmushi tare da yafito ni da hannu wai naje,da sauri na karasa,sai kallo yake kare min tun daga sama har kasa yace yan mata wa kike nema?nace wajen Babanka nazo Commissioner na Ilmi da alama kai dansa ne ko?murmushi ya kara saki yana min kallon irin na yan duniya,yace ae dansa ne ni ya akayi?Nan na sanar masa taimakon da nake nema akan rashin lafiyar Ammah yace wannan ai karamar matsala ce Beauty,kawo na sa miki Number ta,nace ni bani da waya mu talakawa ne,baki ya tabe tare da dauke kai yana cewa ai kuna da amfani ta wani fannin,ban gane me yake nufi ba kawai naga ya miko min wata waya sabuwa dal a kwalinta amma karama ce Nokia me kyan gaske,yace kinci sa'a Baby na siyo wa yaron Mama waya karbi ki rike wannan ga sim card sabo bari na sa miki zamu dinga magana ta waya kafin Abba ya dawo sai a kaita asibiti.
Tunanina da gaske ne ba tunanin komai nace nidai ka bar wayarka amma ka bani Number dinka zan nemeka kaji,yace karbi karki damu kyauta na baki yan mata kamarki ba waya ai abin kunya ne,cike da tsoro dai na karba hannu na rawa garin zai miko min sai da ya shafi hannuna yana sani harda lumshe ido,da sauri na dauke hannuna ina godiya,da kansa ya hada min wayar da komai ya sa min Number dinsa ciki ya dauki number ta sannan ya miko min Dubu biyu wai na hau Napep,naki karba kawai sai ya zubar min da kudin a kasa yana shu'umin murmushi ya figi motarsa ya shimfida cikin wannan gida na alfarma,na dade a tsaye ina tunani kawai dai nace Allah gani gareka na kwashi kudin nayi gaba abina.
Danaje gida Ammah dan kar ta hanani amfani da wayar sai nayi karya nace Ammah yau dai na karbi kudin adashina na gidan Haule kinga na siyo waya sabo da baza a ace a gidan nan bamu da waya ko daya ba,nan suka dinga murna da tsalle,Ammah harda sa albarka tana murna dama yaran Zamani badai zuba karya a kifar da iyaye a corner can.
Next day ban hakura ba dai sabo da ina tsoro kar fa nazo ba a samu tallafi wajen Dan Commissioner ba kawai na shirya na Tafi gidan Dan Majalisa na tarayya da suke Zama Abuja,ni dai nasan ba lallai na sameshi da family dinsa ba domin wasu ma ba a Sanin inda gidansu yake buya suke su canja unguwa ko state dan kar a je musu Maula,ni kuwa tsabar jaraba sai da na kwakwulo gidan da tambaya tun daga unguwarmu nake bin gidajen manya ko wani ya sani,idan ance me zaki yi sai nace sako wasu zasu kai gidan da haka aka gwada min gidansa amma fa basu cika Zama a kano ba kawai dai zanje na gani ko me gadi na samu contact Dinsa ya min hanya, haka na fada Napep sai gidan Dan Majalisar tarayya Abuja,gidan kansa abin kallo ne sabo da ya hadu karshe.
Securities ko ina a gidan harda mutane a kofar gidan Yan maula,haka na kutsa kai cikinsu tare da tambaya ko me gidan yana nan suka ce ai rabon da yazo kano ma yau Shekara biyu kenan.
Baki na bude tare da mamaki wani ciki yace sai dansa Yarima Bobo da ake aikowa da sakon yan siyasa ana kawo musu,yanzu ma shi muke jira ya fito kin San shi a kwai gadara da wulakanci sai yaga dama yake fitowa ya bamu sakon Hon Rep,
Nan take nace aiko sai na jira dan nasa dan Ubansa ko shi waye,ina nan tsaye na gaji da jira har 2pm a wajen nayi Sallah saman dankwalina wata me tallan Fura tana zaune a kusa nace ta dama min ta Hamsim,haka ta dama furar tasha Nono me kyau da sugar, nace juye min ita a leda ki kulle,haka ta bani katon Dauri a farar leda na Fura da nono na bata ,sannan na siyi yogourt yar hamsim a leda tayi kankara,ina fara sha sai ga wani dan sanda yace Yarima yace Ku shigo ya ganku zai wuce Flight dinsa ya kusa tashi,da sauri mazan suka fada gidan yuuuuu,ni kadai ce mace haka na danna kai ciki ina Shan furata a leda yanda nake zuka kamar jariri ya kama Nonon uwarsa haka na lumshe ido ina tsotsa Malam ba ruwana.
Muna shiga ciki nan na hangame baki wajen kallon irin haduwa na gidan ba a magana,Saurayin muka hango chocolate dashi ya hadu sosai ga kyau ga iya wanka abin kallo yana kamshi yasha light blue shadda yana sheki ga motoci a gidan birjik,muka karasa gabansa yana zaune a wata farar kujera yana faman yanga da gadara,ido muka hada dashi yasha mamaki ganin harda yarinya haka,dan a wajensa bana Sahun yan mata
Ya fara sauraron wasu kawai muka ga Securities sun wani gigice sun nutsu waje daya tare da bude gate jikinsu na rawa,sai ga wasu motoci dalla dalla sun shugo gidan sun kai biyar kamar nasan motocin,ashe kuwa shine domin Saurayi Aayan ne me tashen kyau da Naira.
Gani mukayi Yarima ya fadada fara'arsa tare da mikewa ya tarbi Aayan da alama abokaine harda wani tafawa suna dariya,Yarima Bobo yace amma kai dan Iska ne Aayan tun safe kace zaka zo kasan yau zan koma Uk amma ka bata min time yanzu na daga flight dina sai 12am na dare,Murmushi Aayan ya saki cike da izza ya dage masa gira daya kana yace to ya akayi ne man sauri ka gama da mutanen nan naku kasan ban son jira,Yarima yace ai kai dan Iska ne ga sit can,kusa da mu ya zauna can nesa a wata kujera ta yan gayu,Juice aka kawo masa yana korawa,a raina nace Allah sarki talakawa mu ko ruwa babu me bamu.
Yarima yana ta ganin mutane yana sallamarsu da kudi,sai yace pls Ku mazane kuyi hakuri na sallami yarinyar can tunda macece,a raina nace Ashe yana da kirki,nan yace ke zo naji na sallameki sai lokacin Aayan ya kalli inda nake muka hada Ido,da mamaki ya kalleni lallai yarinyar nan wato har maula take zuwa gidan masu kudi sabo da son kudi,ko dai bata da iyaye ne oho,yana gani na karaso gaban Yarima ba tsoro na durkusa gaban Yarima tare da cewa ina yini?yace lfy tashi tsaye ki fadi abinda ya kawoki sauri nake ina da bako,ina durkushe a gabansa kaina a kasa kuma ina ta zukar Fura ta kamar yarinyar yaye,idan nayi magana daya biyu na zuki furata,babu wanda baiyi dariyar abinda nake ba kowa yana ganin ai yarinya ce,shi kuwa Gogan Aayan a zuciyarsa yake Dariyar kwadayi na,kuma sabo da kuruciya a gaban kowa ina mace ko dai bani da hankali ne. na karanta masa ciwon Mahaifiya ta,yaji tausayina kuma lallai yaga mu abin taimako ne,sai yace jirani a gefe bari na sallami sauran,
nan na Mike na koma gefe,Aayan ko kallona bai kara yi ba har Yarima ya gama da mutanen kaf suka tafi ya rage daga ni sai Aayan sai Yarima,yace zo ke,da sauri na karasa gabansu su biyu,yace ina babanki ko ya rasu? Bana so na fada a gaban Aayan wanda ke latsa waya,sai nace Sirri ne sai dai idan zamu koma gefe na fada ma,murmushi ya saki yace to ya Mike ya taso na kara kasa da murya da rada nace bacewa yayi ba a San inda yake ba,kawai ko guduwa yayi wa ya sani,dariya Yarima yayi yace to shike nan ki kawo takaddun asibitin naki mu gani,nace to ai naji ance zaka yi tafiya,no ki jira zamu fita da frnd dina sai mu saukeki ki dauko takardun,a tsorace nace tab wancan masifaffen ne zai yarda,kin sanshi ne?ya tambaya,nace ae na sanshi kullum sai ya mareni idan ya ganni,murmushi yayi yace to ki jira ai motata zaki shiga,murmushin da nayi shi ya tafi da Imaninsa ya tsaya yana kallona,sai can ya dawo hayyacinsa yace ina zuwa ya koma wajen Aayan dake ta faman cika yana batsewa,Yace kai Yarima kasan fa ban son jira wlh zan tafi ka tsaya kuyi hirar,ba class ba komai,Sorry let's go,Aayan da mamaki yaga na shiga Motar Yarima shima cike da takaici ya shiga nasa motar suka ja muka bar gidan cikin zugar motocinsu,sai da aka zo kusa da gidanmu suka tsaya,Yarima yace yarinya yisauri ki dakko mana na gani,ina fita na kwashe da gudu na karasa gida na fada daki na ebo kamar kiftawar Ido na fito da wani gudun kowa ya ganni sai ya tsorata ko wani abu ne ya biyoni,da gudu ina Haki na kawo masa takaddu ya sauke glass kasa ya karba ya gani tabbas da gaske nan ya miko min card dinsa yace ga Number ta na Nigeria dana waje ki kirani kiji,da sauri na daga kai sama,ya zaro Dubu goma ya bani yace gashi ki siyawa marar lfy ko ruwane,godiya nayi na karba, Yarima yace ki daina gudu kinji yarinya ba kyau mace tana gudu,da ladabi nace to na daina ai tsoro naji kar Ku tafi sannan na juya na dau hanyar shiga gidanmu,sai da naje bakin kofar gidanmu zan shiga na juyo baya sai naga Motar Yarima sunyi gaba sai Na Aayan yana kallon inda zan shiga kamar Munafuki muna hada Ido suka figi motarsu fiii suka kara gaba abinsu nima na shige gida.
Still ban gamsu da taimakon Yarima ba sabo da yan siyasa basu da tabbas ayi maka karya ka dauka gaske ne kayi ta jira ana ja ma rai,don haka kwana nayi ina tunanin cewar wanne gida kuma zanje nan take na tuno da wani dan kasuwa Hamshakin me kudi a GRA unguwar su Aayan,har matsuwa nayi gari ya waye na tafi,ga kuma gidan wata Mata nan ma Naji ance tana taimakon Talakawa.
Sannan Zan biya sakateriya ta unguwarmu wajen Kansila Adamu me tallafi ko Allah zai sa ya shigar da sunana cikin masu karbar tallafin Manoma na Gomnati.
Kuma duk a gobe zanje wani Training shima ko zan samu a dauki sunana cikin masu koyon sana'a idan ka gama a baka jari.gaskiya gobe ina da tsare tsare da yawa,don haka kosai ma kadan na soya na barwa su Meenat komai tare da shiryawa yau ba Hijab nasa ba mayafi na yafa nayi kyau yau doguwar rigar material nasa red and green mayafinta green da takalmin robata baki,Ammah nayiwa Sallama ta zuba min addua sannan na fita da addua a bakina.
AsmaBaffa
|